No edit summary |
|||
Line 613: | Line 613: | ||
== Baqara aya ta 60 == | == Baqara aya ta 60 == | ||
Kuma ka tuna lokacin da Musa ya roƙa | Kuma ka tuna lokacin da Musa ya roƙa wa mutanensa ruwan sha, sai Muka ce: "Ka bugi dutse da sandarka", sai idanuwan marmaron ruwa goma sha biyu suka ɓuɓɓugo daga cikinsa. Haƙiƙa kowaɗanne mutane sun san mashayarsu. (Muka ce): "Ku ci kuma ku sha daga arzikin Allah, kuma kada ku yaɗa ɓarna a bayan ƙasa. | ||
Tafsiri: | |||
Sannan Allah ya ƙara tuna musu lokacin da suka nemi ruwan sha daga Annabi Musa yayin da suka tsinci kansu a saharar Sina, sai Annabi Musa ya roƙi Allah ya shayar da su ruwa, sai Allah ya umarce shi da ya doki dutse da sandarsa, da ya aikata hakan, nan take kuwa Allah ya fitar musu da idanuwan marmaro na ruwa har guda sha biyu, wato adadin yawan ƙabilar Banu Isra'ila. Kowace ƙabila ta gane mashayarta. Sannan ya umarce su da su ci su sha daga abin da Allah ya azurta su da shi, kuma kada su kuskura su yaɗa ɓarna a bayan ƙasa. Watau dai Allah ya hore musu ci da sha ba tare da wata wahala ba, kuma ya hore musu ruwan sha isasshe ba tare da wani [[tirmitsitsi]] ba. | |||
'''Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:''' | |||
# Allah ne kadai mafakar bayinsa yayin da suka shiga cikin wata matsala. | |||
# Tabbatar da mu'ujiza ga Annabi Musa AS. Allah ya fitar masa da ruwa mai yawa daga dutse ba tare da wata wahala ba bayan ya doke shi da sandarsa, kuma ya fitar musu da idanuwar ruwa goma sha biyu adadin ƙabilun Banu Isra'ila. | |||
# Bayanin girmar Ƙudurar Allah SWT mai aikata abin da ya ga dama a sanda ya ga dama. | |||
# Wata babbar ni'imar da Allah SWT ya yi wa Banu Isra'ila a nan shi ne gusar musu da duk wani abu da zai haddasa gaba da husuma a tsakaninsu da samar musu da buƙatarsu ta ruwa ba tare da wata takura ba. | |||
# Allah SWT yana iya arzuta bawa ba tare da wata wahala ko wani aiki mai yawa ba. | |||
# Bayanin cewa Yahudawa wasu mutane ne da suka shahara da ɓarna a bayan ƙasa, shi ya sanya Allah SWT ya hane su da ɓarna a nan. | |||
== Baqara aya ta 61 == | |||
Kuma ku tuna lokacin da kuka ce: "Ya Musa, ba za mu iya haƙuri a kan abinci iri ɗaya ba, | |||
pg72 | |||
[[Category:Quran]] | [[Category:Quran]] | ||
[[Category:Quran/2]] | [[Category:Quran/2]] | ||
[[Category:Rijiyar Lemo]] | [[Category:Rijiyar Lemo]] |