Line 645: | Line 645: | ||
== Baqara 62 == | == Baqara 62 == | ||
Kuma lalle | Kuma lalle waɗanda suka yi imani da Yahudawa da Nasara da Sabi'awa, duk wanda ya yi imani da Allah da ranar Lahira kuma ya yi aiki na ƙwarai, to suna da ladansu a wurin Ubangijinsu, kuma babu tsoro a tare da su, kuma ba za su yi baƙin ciki ba. | ||
Tafsiri: | |||
Hikimar kawo wannan ayar ana tsakiyar bayanin laifuffukan Banu Isra'ila ita ce, don a nuna musu cewa, ƙofar tuba gare su a buɗe take matuƙar za su tuba su inganta imaninsu da ranar lahira su yi kyakkyawan aiki, to Allah zai ba su ladansu cikakke kuma babu wani tsoro a tare da su game da abin da za su je lahira su iske, kuma babu wani baƙin ciki da za su yi na abin da suka tafi suka bar shi a nan duniya. | |||
Wadanda suka yi imani a nan ana nufin al'ummar Annabi Muhammadu SAW wadda ta yi imani da shi, ta yi imani da dukkan littafan Allah da manzanninsa. An ware su da wannan suna domin ƙarfin imaninsu da cikarsa. | |||
Yahudawa kuwa ana nufin mabiya Annabi Musa AS wadanda suka yi imani da shi, suka yi aiki da abin da aka saukar masa kafin a shafe aiki da addininsa, ko kuma kafin su gurɓata shi. | |||
Nasara kuma, ana nufin mabiya Annabi Isa AS kafin a shafe addininsa ko kafin su jirkita shi. | |||
Sabi'awa kuwa wasu ƙungiyoyi ne, daga cikinsu akwai wadanda suka kasance a kan aƙidar kaɗaita Allah da haramta duk wata alfasha da zalunci, duk da kasancewarsu ba bisa wani addini suke ba, to amma ba sa aikata kafirci. To duk wanda ya kyautata aiki daga cikin wadannan al'ummomi da suka gabata, yana da kyakkyawan sakamako a wurin Allah, ba zai ɓata masa rayuwarsa ta lahira ba. | |||
'''Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:''' | |||
# Falalar imani da aiki na ƙwarai. Duk mai wannan siffa zai samu aminci a nan gaba, kuma ba zai yi bakin cikin abin da ya bari a bayansa ba. | |||
# Muhimmancin yin bayanin hukuncin Allah ga mabiya wasu addinai da ba Musulunci ba. | |||
# Yahudawa da Nasara da Sabi'awa wadanda suka yi imani da Kadaitakar Allah, suka yi aiki da shari'un annabawansu, har suka mutu a kan haka kafin aiko Annabi Muhammadu SAW, ko kuma wadanda suka riski Musulunci daga cikinsu suka musulunta suka bar addininsu na farko, to duk wadannan sun tsira sun kuma rabauta. | |||
== Baqara 63-66 == | |||
# Kuma | |||
pg77 | |||
[[Category:Quran]] | [[Category:Quran]] | ||
[[Category:Quran/2]] | [[Category:Quran/2]] | ||
[[Category:Rijiyar Lemo]] | [[Category:Rijiyar Lemo]] |