Toggle menu
24K
663
183
158.1K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Quran/2/Rijayar Lemo Tafsir: Difference between revisions

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Line 740: Line 740:
Tafsiri:
Tafsiri:


Bayan Allah ya ba da labarin yanayin da zukatan Banu Isra'ila suka zama, yadda suka taurare kamar duwatsu ko ma fiye da duwatsu, sai ya dawo kan muminai a waɗannan ayoyi yana faɗa musu cewa, su fitar  
Bayan Allah ya ba da labarin yanayin da zukatan Banu Isra'ila suka zama, yadda suka taurare kamar duwatsu ko ma fiye da duwatsu, sai ya dawo kan muminai a waɗannan ayoyi yana faɗa musu cewa, su fitar da rai game da imanin wadannan mutane, domin babu wata alama da ta nuna suna shirye da karbar shiriya. Hasali ma malamansu ma wadanda suke karanta musu Attaura da abin da yake cikinta na maganar Allah, suna canja ta, suna gurbata ta, bayan kuwa sun fahimce ta, sai suka canza ma'anoninta zuwa wata ma'ana daban da za ta yi daidai da son ransu.
 
Sai kuma Allah ya fadi mummunan hali na wasu Yahudawa, wadanda suka yafa rigar munafinci a jikinsu. Wato duk lokacin da suka hadu da Annabi SAW da sahabbansa, sai su ce: "Ai mu muminai ne", amma idan sun koma cikin 'yan uwansu Yahudu, sai sauran Yahudawan da ba su yafa rigar munafinci ba, su rika zargin wadancan munafukan Yahudawan, suna ce musu: "Me ya sa za ku rika fada wa Musulmi abin da Allah ya sanar da mu a Attaura na siffofin Annabi ko labarin irin azabar da Allah ya saukar wa kakanninmu saboda kangararsu ko kuma abin da ya sanar da mu na cewa, akwai Annabin da zai bayyana mai siffofi iri kaza da kaza? Domin fa yin haka ai wata hujja ce kuke ba su da za su kafa mana ita gobe kiyama a gaban Allah cewa mun san gaskiya, kawai mun ki yin imani ne da gangan. Wannan abu da kuke yi rashin hankali ne." Sai Allah ya ce, Yahudawa suna irin wadannan maganganu da 'yan uwansu a boye, kamar ba su san Allah ya san duk abin da suke bayyanawa, da abin da suke boyewa ba, shi a wurinsa babu wani bambanci tsakanin abin da suke bayyanawa, da abin da suke boyewa a zukatansu.
 
Sanna Allah SWT ya bayyana cewa,