Line 791: | Line 791: | ||
# Suka ce kuma: "Zukatanmu rufaffu ne." A'a ba haka ba ne, Allah dai Ya la'ane su ne saboda kafircinsu, don haka kaɗan ne waɗanda suke yin imani. --[[Quran/2/88]] | # Suka ce kuma: "Zukatanmu rufaffu ne." A'a ba haka ba ne, Allah dai Ya la'ane su ne saboda kafircinsu, don haka kaɗan ne waɗanda suke yin imani. --[[Quran/2/88]] | ||
# Yayin da kuma wani littafi ya zo musu daga Allah, yana mai gaskata abin da yake tare da su, alhali kuma a da sun kasance suna addu'ar neman nasara a kan wadanda suka kafirta (mushrikai). To yayin da abin da suka sani ya zo musu sai suka kafirce masa. Don haka la'anar Allah ta tabbata a kan kafirai. --[[Quran/2/89]] | # Yayin da kuma wani littafi ya zo musu daga Allah, yana mai gaskata abin da yake tare da su, alhali kuma a da sun kasance suna addu'ar neman nasara a kan wadanda suka kafirta (mushrikai). To yayin da abin da suka sani ya zo musu sai suka kafirce masa. Don haka la'anar Allah ta tabbata a kan kafirai. --[[Quran/2/89]] | ||
# Tir | # Tir da wadannan abu da suka sayar da kawunansu da shi, wato suka kafirce wa abin da Allah Ya saukar, don hassadar cewa, (don me) Allah zai saukar da falalarsa ga wanda Ya ga dama daga bayinsa, sai suka wayi gari da fushin Allah a kan wani fushin. Kuma azaba ta wulakanci ta tabbata ga kafirai. --[[Quran/2/90]] | ||
Tafsiri: | |||
A wadannan ayoyi, Allah SWT yana fada mana cewa, ya ba wa Annabi Musa AS littafin Attaura, sannan a bayansa ya ci gaba da aiko wasu manzannin zuwa ga al'ummar Banu Isra'ila, wadanda suka ci gaba da aiki da shari'ar Annabi Musa AS, har zuwa lokacin da ya aiko Annabi Isa AS, ya kuma bayyana gaskiyarsa ta hanyar ba shi mu'ujizoji daban-daban, kamar tayar da matattu, da warkar da marasa lafiya da izinin Allah, hakanan ya karfafa shi da Mala'ika Jibrilu AS wanda ya rika taimaka masa. | |||
Sannan Allah ya nuna mana kyamar irin ta'annutin da Banu Isra'ila suka rika yi wa annabawa da ya aika musu. Wato duk sa'adda wasu manzanni suka zo musu da hukunce-hukuncen da suka saɓa wa soye-soyen zukatansu, sai su ji cewa wadannan manzanni suna matsa musu ne, kuma sun rena musu wayo, don haka sai girman kansu ya ingiza su, sai su karyata wasu daga cikin wadannan manzannin, wasu kuma ma su kashe su. Sai kuma sai suka rika fadar wata karyar cewa, wai su abin da ya hana su su yi imani shi ne, zukatansu a rufe suke rif, don haka ba sa iya fahintar wani abu da manzanninsu suke fada mus. Sai Allah ya karyata su, ya nuna abin da suke inkari ba haka yake ba; kafircinsu ne kawai ya jawo Allah ya la'ance su, ya nisantar da su daga rahamarsa, sakamakon abin da suka zaba na bijire wa koyarwar manzanninsu da annabawansu. Saboda haka sai ya kasance 'yan kadan ne a cikinsu suka ba da gaskiya, ko kuma abin da suka yi imani da shi kadan ne kwarai. | |||
Sai Allah SWT ya ba mu labarin wani hali na Yahudawa tun sa'adda wani fada ya barke tsakaninsu da Larabawa mutanen Madina masu yin shirka, sukan ce musu: "Akwai wani Annabi da za a aiko nan ba da jimawa ba; idan ya bayyana za mu bi shi, mu hada karfi da shi, mu yi muku irin kisan da aka yi wa Adawa da Samudawa." Wato suna nufin kisan ƙare-dangi. Su Yahudawa a zatonsu Annabin zai bayyana ne daga cikinsu, sai kuma ya bayyana daga cikin Larabawa kuma Quraishawa, abokan fadansu. | |||
Yayin da Annabi Muhammad SAW ya zo da littafin Alkur'ani, wanda yake gaskata abin da Annabi Musa da sauran annabawa suka zo da shi na Tauhidi, kuma Banu Isra'ila suka gane shi ne Annabin da suke fadar zai bayyana, suka kuma fahimci gaskiyar da ya zo da ita, to maimakon su yi imani kamar yadda suka kasance suna shelantawa, sai kawai suka kafirce masa, a dalilin haka sai Allah SWT ya la'ance su, ya nisantar da su daga rahamarsa. Wannan kuma shi ne sakamakon kowane kafiri a duniya. | |||
Sannan Allah SWT ya yi tir da irin wannan mugun zabi da Yahudawa suka yi wa kawunansu, wato suka zabi su kafirce wa Annabin da suka san gaskiyarsa, suka zabar wa kawunansu shiga wutar Jahannama, ba don wani abu ba, sai don kawai tsabar hassada da kabilanci da suke yi wa Larabawa, wai don me Allah SWT zai aiko da Annabi a cikinsu ba a cikin Banu Isra'ila ba, tare da cewa sun san shi Allah SWT yana bayar da falalarsa ne ga wanda ya ga dama daga cikin bayinsa bau mai iya hana shi. Wannan ne ya sa Yahudawa suka cancanci wani fushi daga Allah (SWT) a kan fushin da suka cancanta a baya na laifukan da suka rika tabkawa. Don haka ne duk wadanda za su bijire wa sakon Annabi Muhammadu SAW a kowane zamani ne to suna da wata azaba mai wulakantarwa. | |||
'''Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:''' | |||
# Annabawan da suka zo daga cikin Banu Isra'ila bayan Annabi Musa AS sun rika aiki ne da shari'arsa. | |||
# Daga cikin ayyukan mala'iku akwai karfafar manzannin Allah. | |||
# Asali zukatan 'yan'adam a bude suke, gaskiya na iya shigar su, kafircin dan'adam ne yake musabbabin Allah ya la'ance shi, sai ya kulle masa kofofin shirya. | |||
# Annabya falala ce daga Allah SWT da yake bayar da ita ga wanda ya zaba. | |||
== Baqara 91-93 == | |||
# Idan aka ce da su: "Ku yi imani da abin da Allah Ya saukar", sai su ce: "Mu muna yin imani ne da abin da aka saukar mana". Kuma suna kafircewa da duk wani abu da ba shi ba, alhalin shi gaskiya ne, kuma mai gaskata abin da ke tare da su ne. To ka ce: "Me ya sa a da kuke kashe annabawan Allah idan kun kasance muminai?" --[[Quran/2/91]] | |||
# Hakika | |||
pg96 | |||
[[Category:Quran]] | [[Category:Quran]] | ||
[[Category:Quran/2]] | [[Category:Quran/2]] | ||
[[Category:Rijiyar Lemo]] | [[Category:Rijiyar Lemo]] |