Line 818: | Line 818: | ||
Tafsiri: | Tafsiri: | ||
A nan Allah SWT ya bayyana mana | A nan Allah SWT ya bayyana mana yadda Banu Isra'ila suke iqrarin cewa, su sun yi imani ne da Attaura kawai, kuma ta wadatar da su, ba sa bukatar sai sun yi imani da Alkur'ani. To shi ne a nan Allah yake karyata su, yana bayyana cewa, hatta ita ma Attaurar ba wani cikakken imani suka yi da ita ba. Duk da cewa shi Alkur'ani Allah ya saukar da shi ne bayan Attaura, kuma yana gaskata abin da yake cikin Attaura na Tauhidi da rukunnan imani. Wannan magana tasu tubka da warwara ce, domin duk wanda ya karyata Alkur'ani, to ya karyata sauran littattafan ma gaba daya. | ||
Sannan sai Allah ya umarci Annabinsa Muhammad SAW da ya tambaye su, idan har da gaske suke sun yi imani da Attaura, me ya sa suke kashe annabawan Allah wadanda su ma suna gaskata abin da yake cikinta? Kuma a cikin Attaura an haramta kashe kowane Annabi. | |||
A karshe sai Allah ya nuna a fili cewa, karya suke yi, ba su yi imani da Attaurar ba, domin tun farko da Annabi Musa ya zo musu da hujjoji bayyanannu masu tabbatar da gaskiyar annabcinsa, sai suka koma suna bautar dan maraqi lokacin da ya tafi ganawa da Ubangijinsa saboda qetare iyaka da zalunci. | |||
Sannan Allah SWT ya sake tuna wa Banu Isra'ila labarin lokacin da ya dauki alkawarin mai karfi a wurinsu, har ya daga dutsen D'uri a samansu, kamar ya rufto ya fado musu, domin a tsoratasu a kan dole su yi aiki da umarnin da aka ba su na cewa lalle su rike Attaura gamgam da himma da nashadi, kuma su saurari maganar Allah, sauraro na karba da mika wuya, amma sai suka amsa wa Allah SWT da cewa, sun ji da kunnuwansu, amma kuma sun sab'a da ayyukansu. Son bautar dan maraqi ya riga ya ratsa zukatansu, sun kwankwad'e shi da gaske, kamar yadda mai jin qishirwa yake kwankwad'ar ruwa idan ya samu, har ya ratsa ko'ina a jikinsa. | |||
Bayanan da suka gabata sun tabbatar da cewa, imanin Yahudawa na jabu ne, tun da bai hana su kashe annabawan Allah ba, bai hana su bautar dan maraqi ba, bai kuma hana su bijire wa umarnin Ubangijinsu ba. Don haka sai Allah ya yi tir da wannan imani nasu, ya tabbatar da cewa, imani na qwarai shi yake sanya mai shi ya aikata alheri ya kuma kauce wa sharri. | |||
'''Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:''' | |||
# Qaryar Yahudu wajen da'awar sun yi imani da Attaura, alhalin suna sab'a mata a fili da ayyukansu. | |||
# Wajibi ne ga mumini ya karbi shari'ar Allah da karfi da nishadi, ba da kasala ba. | |||
# Wajibi ne mutum ya karbi gaskiya daga bakin duk wanda ya fad'e ta. | |||
== Baqara 94-96 == | |||
# Ka ce: | |||
pg99 | |||
[[Category:Quran]] | [[Category:Quran]] | ||
[[Category:Quran/2]] | [[Category:Quran/2]] | ||
[[Category:Rijiyar Lemo]] | [[Category:Rijiyar Lemo]] |