Line 836: | Line 836: | ||
== Baqara 94-96 == | == Baqara 94-96 == | ||
# Ka ce: | # Ka ce: "Idan gidan lahira ya kasance kebantacce a gare ku a wurin Allah ku kadai ban da sauran mutane, to ku yi burin mutuwa idan har ku masu gaskiya ne." --[[Quran/2/94]] | ||
# Ba za su tab'a burin mutuwa ba har abada, saboda abin da hannayensu suka aikata. Kuma Allah Masani ne ga azzalumai. --[[Quran/2/95]] | |||
# Kuma za ka same su sun fi kowa kwad'ayin tsawon rai, fiye ma da wadanda suka yi shirka. Kowane d'ayansu yana burin ina ma za a raya shi shekara dubu. Kuma Allah Mai ganin abin da suka kasance suna aikatawa ne. --[[Quran/2/96]] | |||
Tafsiri: | |||
A nan Allah yana fada wa Annabinsa cewa, idan Yahudawan Madina suna da'awar cewa, don su kadai Allah (SWT) ya tanadi ni'imar gidan Aljanna a lahira, ban da sauran mutane, to ga wata hanya da za a bi a gane mai gaskiya, ita ce su hadu su yi addu'ar tsinuwa, wato su roqi Allah ya halaka maqaryaci daga cikinsu. Allah SWT ya nuna cewa, sam-sam Yahudawa ba za su tab'a karb'ar wannan kira nasa ba, saboda suna sane da irin laifuffukan da suka tabka na kafirce wa Annabi da boye gaskiya, kuma suna sane da cewa hanyar haduwa da mummunan sakamakon miyagun ayyukansu ita ce mutuwa; da zarar sun mutu, to sun fada cikin abin qi ke nan har abada. Wannan kadai ya isa ya hana su son mutuwa. To amma fa kada su manta da cewa, Allah yana sane da duk wani azzalimi mai keta dokarsa a bayan qasa, kuma komai dadewa sai Allah ya damqe shi ya nuna masa sakamakonsa. | |||
Daga nan sai Allah ya tabbatar da cewa, ai babu wani jinsi na mutane da yake gudun mutuwa irin jinsin Bayahude, domin ya san abin da yake jiran sa a lahira na azaba, don haka za ka ga kowane dayansu yana son ya yi tsawon rai a duniya, ta yadda soyayyarsu da rayuwa a nan duniya, har ta zarce ta mushrikai wadanda ma ba su yi imani da akwai ranar lahira ba, ballantana har su yarda da cewa akwai wani sakamako da zai biyo baya. | |||
pg101 | |||
[[Category:Quran]] | [[Category:Quran]] | ||
[[Category:Quran/2]] | [[Category:Quran/2]] | ||
[[Category:Rijiyar Lemo]] | [[Category:Rijiyar Lemo]] |