#
|
English
|
Hausa
|
Internal Source Link
|
1
|
Scientists in a race to discover why our Universe exists [1]
|
Masana kimiyya na fafutukar binciko dalilin samuwar sammai da ƙassai [2]
|
<small>--[[bbchausa verticals/106 why our Universe exists]]</small>
|
2
|
A vast cavern in South Dakota shielded from the outside world will house sensitive equipment to detect tiny changes in sub-atomic particles
|
Maka-makan koguna da aka gina a ƙarƙashin ƙasa a jihar South Dakota da ke Amurka wadanda suka zamo kariya daga duk wata hayaniya da ke faruwa a doron ƙasa za su zamo wurin da za a ajiye na'urorin da za su gano sauye-sauyen da aka samu a ƙananan ƙwayoyin zarra
|
<small>--[[bbchausa verticals/106 why our Universe exists]]</small>
|
3
|
Inside a laboratory nestled above the mist of the forests of South Dakota,
|
A cikin wani ɗakin bincike da ke jihar South Dakota ta ƙasar Amurka,
|
<small>--[[bbchausa verticals/106 why our Universe exists]]</small>
|
4
|
scientists are searching for the answer to one of science's biggest questions:
|
masana kimiyya sun duƙufa wajen samo amsar ɗaya daga cikin manyan abubuwan da suka shige wa ɗan'adam duhu:
|
<small>--[[bbchausa verticals/106 why our Universe exists]]</small>
|
5
|
why does our Universe exist?
|
mene ne ya sa sarari da duniyarmu suka samu?
|
<small>--[[bbchausa verticals/106 why our Universe exists]]</small>
|
6
|
They are in a race for the answer with a separate team of Japanese scientists – who are several years ahead.
|
Waɗannan masana na rige-rigen gano wannan amsa ne da wasu gungun masana kimiyya na ƙasar Japan - waɗanda suka fara irin wannan bincike shekaru da dama da suka gabata.
|
<small>--[[bbchausa verticals/106 why our Universe exists]]</small>
|