Suna
m
- ɗan tudun baya tsakanin kafaɗu har ya sa mutum ya ɗan ranƙwafa in yana tafiya. Wani tozo da ke fitowa a bayan mutum a sakamakon wata cuta <> Bent posture of back.
- Synonym: ƙusumbi
- tsirin baya irin na raƙumi ko zabo. <> a hump like a camel's hump-back
- Doron raƙumi duk tozo ne.
- gadon baya; shimfiɗar da ake ɗorawa sirdi bayan an ɗaura shi
- Synonym: jalala
- Doron magana = haƙiƙanin yadda maganar take <> the fact of the matter; the reality or truth, what it is actually
- ranƙwafar da abu don samansa ya yi bayan zabo.
- Ana yin doro a rufin ɗaki don kada ruwan sama ya taru.
- Magana: Doron mage = tanadin yadda za a gocewa yadda aka yi yardajjeniya da; watau kauce wa abu ko ƙin ba da amsar tambaya. <> deflecting, deviating from the original topic
- Ya yi maka doron mage.
- Doron wuya = dokin wuya.
- Doron ludayi = ludayin du wanda wutsiyarsa ta takura a lanƙwashe.
- Doron hanya = tsakiyar hanya <> the middle of the road, the middle path
- labbati
- Doron ƙasa = surface, on top of, on the face of the earth
Suna 2
Jam'i |
f
- wani irin wasa na hauri da ƙafa
- Synonym: mangare