Suratun Nur Aya Ta 1-5 (Kashi Na 619)
Jama'a masu sauraro barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda, da a cikinsa muke kawo ayoyi da bayanai da suka kumsa, domin zame mana darasi a rayuwarmu ta yau da kullum da fatar Allah ya sa Kur'ani mai girma ya zama jagoranmu a rayuwarmu ta yau da kullum da kuma samin dacewa duniya da lahira amin. Kuma nine Tidjani Malam Lawali damagaram zan kasance tare da ku har zuwa karshen shirin nay au da tare da injiniya Aminu Ibrahim kiyawa.
- Music***********
To madallah za mu fara shirin nay au da faraway da aya ta farko a cikin suratul Nur da fatar masu saurare za su kasance tare da mu har zuwa karshen shirin na yau:
سُورَةٌ أَنزَلْنَاهَا وَفَرَضْنَاهَا وَأَنزَلْنَا فِيهَا آيَاتٍ بَيِّنَاتٍ لَّعَلَّكُمْ تَذَكَّرُونَ
1-Wannan sura ce da Muka saukar da ita Muka kuma wajabta hukunce-hukuncen da suke cikinta,Muka kuma saukar da ayoyin mabayyana a cikinta don ku wa'azantu.
Suratul Nur ta kumshi ayoyi 64 kuma an sabkar da ita a birnin Madina ne.An bawa wannan sura sunan Nur saboda aya ta 35 da ke cikin wannan sura inda ayar ta siffata Allah madaukakin sarki da hasken sammai da kassai.rabin wannan sura har zuwa aya ta Nur ta 35 ta gwadaitar da mumunai zuwa ga rungumar rayuwar aure da gina iyali da kamin kai da tsarki a dabra daya su kauracewa alfahasha da abubuwa da Allah ya hana . Bangare na biyu na wannan sura ayoyin surar na bayani ne kan sanin addini da mai addinin Allah madaukakin sarki ,yin biyayya ga manzonni da annaban Allah ,kafa hukumar adalci ta salihan bayu da wasu lamari na iyali da sauransu. Dukan ayoyin da ke cikin Alkur'ani daga Allah suke amma wannan sura ta fara da tunatar da mu da wannan lamari mai muhimmanci da lamura da suka shafi tauhidi da hukumce hukumce da ya shafi maza da mata mumunai da dangantakarsu ta gina iyali da zamantakewa. Abu ne a fili tabbatacce karfafa imani da Allah na shinfida nisantar sabo a tsakanin jama'a da kyautata lamuran rayuwa.
A cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka:
Na farako:Kur'ani mai girma littafi ne da ya kumshi dokoki ga musulmi kuma bin hukunce hukunce da dokokin da ke cikinsa wajibi ne.
Na biyu: Sanin kur'ani na kawar da sha'afa kuma yana tunatar da mutum abubuwa da suka yi daidai da fidira da hankalin na mutum na gari.
Yanzu kuma lokaci ne na sauraren karatun ayoyi na 2 da 3:
الزَّانِيَةُ وَالزَّانِي فَاجْلِدُوا كُلَّ وَاحِدٍ مِّنْهُمَا مِائَةَ جَلْدَةٍ وَلا تَأْخُذْكُم بِهِمَا رَأْفَةٌ فِي دِينِ اللَّهِ إِن كُنتُمْ تُؤْمِنُونَ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الآخِرِ وَلْيَشْهَدْ عَذَابَهُمَا طَائِفَةٌ مِّنَ الْمُؤْمِنِينَ
2- Mazinaciya da mazinaci idan suka yi zina sai ku bulali kowannen daya daga cikinsu bulala dari. Kada kuwa wani tausayi ya kama ku game da tabbatar da hukuncin addinin Allah idan kun kasance kun ba da gaskiya da Allah da ranar lahira ,kuma lallai ne wata kungiya daga muminai su halarci wurin yi musu haddin.
الزَّانِي لا يَنكِحُ إِلاَّ زَانِيَةً أَوْ مُشْرِكَةً وَالزَّانِيَةُ لا يَنكِحُهَا إِلاَّ زَانٍ أَوْ مُشْرِكٌ وَحُرِّمَ ذَلِكَ عَلَى الْمُؤْمِنِينَ
3- Mazinaci ba ya sha'awar aure sai na karuwa ko mushirika,karuwa kuma ba ta sha'awar aure sai na mazinaci ko mushriki,an kuma haramta wannan ga muminai.
A tsarin addinin musulunci tushen sakamako da azaba suna a ranar kiyama .Amma Allah domin kare al'umma da rayuwar zaman takewa da hana kaucewa hanya a wannan duniya ma yana bada umarnin ladabtar da mabannnata gurbattattu da yi masu hannunka mai sanda da zama darasi ga sauran masu banna. Abin lura idan mutum sabonsa da fasadinsa bai bayyana ba Allah ya hana yi masa shisshigi da bincike da tona masa asiri.Amma wadanda bas u jin kunya da bayyana alfahasha da sabo a bainar jama'a dole a ladabtar da su domin idan ba a yi haka ba za su fadada yada sabo da alfahasha a doran kasa. Ci gaban ayar ,Allah ya hana mumunan bayunsa salihai masu tsarki auran ko zama da mutane masu alfahasha da gurbacewa da kaucewa yada cututtuka iri-iri ta hanyar da ba ta dace ba a tsakanin jama'a.
Dole a lura wannan hukumci ne ga mutuman da bai yi aure ba ko wadda ba ta yi aure ba amma wadanda suka yi aure idan suka aikata wani mummunan aiki da bai dacewa wato zina hukuncinsu kisa ne kamar wanda ya yi zina da wata kan tilas ko saduwa da muharramarsa hukuncinsa kisa ne.
Daga wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa biyar kamar haka:
Na farko:A mahangar musulunci yanci a tsakanin jinsii mabanbanta da dangantaka da ba ta dace ba sabo ne mai girma.
Na biyu: dole a yi hukunci mai tsanani kan masu sabo da fasadi a tsakanin jama'a ba tare da tausayawa ba ko jin kai.
Na uku:Ladabtar da mabannata don gyara da kare al'umma ne da matsayinta.
Na hudu:aikata zina yana a matsayin yin shirka da fitar da mutun daga imani.
Na biyar: Wajen zabar matar aure ko mijin aure ana
- MUSIC**********
Yanzu kuma za mu saurari karatun ayoyi na hudu da biyar a cikin wannan sura ta Nur:
وَالَّذِينَ يَرْمُونَ الْمُحْصَنَاتِ ثُمَّ لَمْ يَأْتُوا بِأَرْبَعَةِ شُهَدَاء فَاجْلِدُوهُمْ ثَمَانِينَ جَلْدَةً وَلا تَقْبَلُوا لَهُمْ شَهَادَةً أَبَدًا وَأُولَئِكَ هُمُ الْفَاسِقُونَ
4-Wadanda kuwa suke jifan mata masu aure da zina sannan ba su kawo shaidu ba,sai ku bulale su bulala tamanin ,kuma kada ku karbi shaidarsu har abada,wadannan kuma su ne fasikai.
إِلاَّ الَّذِينَ تَابُوا مِن بَعْدِ ذَلِكَ وَأَصْلَحُوا فَإِنَّ اللَّهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ
5- Sai dai wadanda suka tuba bayan wannan suka kuma kyautata, to hakika Allah mai gafara ne Mai gafara ne Mai rahama.
Bayan ayoyin da suka yi bayani kan irin mace ko namji da ya kamata su yi aure da kuma hana yin zargi da binciken abin da yake boye .Wadannan ayoyi sun hana da yin tanadin hukunci mai tsanani kan masu yin zargi don cimma wata mummunar bukata tasu da cewa: ana bukatar shaidu hudu adilai kafin tabbatar da leifin da suka raya wani ya aikata da ya shafi yin zina idan suka kasa tabbatar da abin da suke zargin wani da aikatawa za a yi masu bulala tamanin kowannansu.
Har ila yau ba za kara karbar shaidarsu ba har abada sai dai idan sun yi tuba da aikata ayyukan alferi . Ya zo a cikin ruwaya wani ya tambayi Imam Sadik (AS) mi yasa ake bukatar shaidu biyu wajen tabbatar da kisa amma don tabbatar da aikata zina ana bukatar shaidu hudu? Sai Imam Sadik (AS) ya amsa masa da cewa: hukuncin kisa kan mutun daya ne amma hukuncin zina ya shafi mutune biyu mace da namiji.
Daga cikin wadannan ayoyi za ilmantu da abubuwa uku:
Na farko: zargin mata da zinna yana da muni da kuma azaba mai tsanani.
Na biyu: wanda yayi zargin wani da zina kan karya ana yi masa bulala 80 yayinda wanda aka samu da aikata zinar ana yi masa bulala 100 ma'ana tazara a tsakaninsu babu banbanci sosai.
Na Uku:matsayi da mutuncin mutane na da matsayi a gurin Allah don haka ma a cikin mutane hudu da za su bada shaida na aikata zina da suke zargin wani da aikatawa idan uku suka baya shaida na hudun ya kasa ana yi masu bulala da yin kage kuma Allah bai bas u iko da damar fallasa shi ba. Su sani shi Allah sattarul Uyub ne.
Da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin na yau a madadin wadanda suka tallafawa har shirin ya kamala ni Tidjani malam lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa wassalam
Suratun Nur Aya Ta 6-14 (Kashi Na 620)
Jama'a masu sauraro barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda, da a cikinsa muke kawo ayoyi da bayanai da suka kumsa, domin zame mana darasi a rayuwarmu ta yau da kullum da fatar Allah ya sa Kur'ani mai girma ya zama jagoranmu a rayuwarmu ta yau da kullum da kuma samin dacewa duniya da lahira amin. Kuma nine Tidjani Malam Lawali damagaram zan kasance tare da ku har zuwa karshen shirin nay au da tare da injiniya Aminu Ibrahim kiyawa
.
- Music**********
To madallah za mu fara shirin nay au da sauraren karatun ayoyi na 6 zuwa 10 a cikin suratul Nur:
وَالَّذِينَ يَرْمُونَ أَزْوَاجَهُمْ وَلَمْ يَكُن لَّهُمْ شُهَدَاء إِلاَّ أَنفُسُهُمْ فَشَهَادَةُ أَحَدِهِمْ أَرْبَعُ شَهَادَاتٍ بِاللَّهِ إِنَّهُ لَمِنَ الصَّادِقِينَ
6-Wadanda kuma suke jifan matayensu da zina kuma bas u da wasu shaida sais u kansu,to shaidar dayansu it ace ya shaida da Allah sau hudu a kan cewa shi lallai yana daga masu gaskiya.
وَالْخَامِسَةُ أَنَّ لَعْنَتَ اللَّهِ عَلَيْهِ إِن كَانَ مِنَ الْكَاذِبِينَ
7-Shaida ta biyar kuwa kan cewa tsinewar Allah ta hau kansa idan ya kasance daga makaryata.
وَيَدْرَأُ عَنْهَا الْعَذَابَ أَنْ تَشْهَدَ أَرْبَعَ شَهَادَاتٍ بِاللَّهِ إِنَّهُ لَمِنَ الْكَاذِبِينَ
8-Kuma abin da zai kawar mata da azabar haddi shi ne ta shaida sau hudu kan cewa shi lallai yana daga makaryata.
وَالْخَامِسَةَ أَنَّ غَضَبَ اللَّهِ عَلَيْهَا إِن كَانَ مِنَ الصَّادِقِينَ
9-Shaida ta biyar kuwa kan cewa lallai fushin Allah yah au kanta idan ya kasance daga masu gaskiya.
وَلَوْلا فَضْلُ اللَّهِ عَلَيْكُمْ وَرَحْمَتُهُ وَأَنَّ اللَّهَ تَوَّابٌ حَكِيمٌ
10-Ba don falalar Allah gare ku ba da rahamarsa ,da kuma cewa Allah Mai karbar tuba ne mai hikima to da ya kunyata makaryaci.
A cikin shirin da ya gabata mun bayyana cewa; idan wani ya zargi wani da aikata zina yana hukatar shaidu hudu idan ya kasa tabbatar da shaidun za a yi masa bulala tamanin ta yin kage . To amma wadannan ayoyi da muka saurara sabanin wadda ta gabace su ne da cewa; idan miji ya ce ya ga matarsa da aikata zina da wani namiji da kai kara wajen alkali .Ba ya bukatar kawo shaidu hudu a'a zai yi rantsuwa da Allah har sau hudu da cewa gaskiya yake fada sai cikon na biyar y ace idan karya yake yi Allah ya la'ance shi.
Bayan wannan rantsuwa da la'anta da mijinta yayi sai ta ya amince da abin da mijinta yake zarginta ko ta musanta .Idan musantawa ta yi .Domin kare kanta sai ta yi rantsuwa kamar yadda mijinta yayi tana cewa mijinta karya yake yi.A karo na biyar bayan rantsuwar ta ce: fushin Allah ya tabbata a kanta idan mijinta gaskiya yake fada.
Bayan sun yi wannan rantsuwa hukumcin tuhuma ba zai hau kan mijin ba ,ita ma matar haka hukuncin zina ba zai hau kanta ba. Har ila yau bayan wadannan rantsuwa ba a bukatar namjin ya furta Kalmar saki .Rabuwar aure ta tabbata a gare su kuma har karshen rayuwarsu ba za su yi aure a tsakaninsu ba.
Daga wannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa uku kamar haka:
Na farko: a lamari da ya shafi iyali domin kare mutuncin mata da miji da yada rundani da fasadi atsakanin jama'a rantsuwa daya daga cikinsu hujja ce ba a bukatar shaidu bare.
Na biyu:Dokar yin rantsuwa a musulunci domin inganta rayuwar jama'a da zamantakewa da rage zargin juna da kuma yin karya.
Na uku: A tsakanin musulmi rantsuwa da Allah nada matsayi da daraja musamman mai imani na hakika ba zai yi rantsuwa kan karya ba.
Yanzu kuma za mu saurari karatun aya ta 11 a cikin wannan sura ta Nur:
إِنَّ الَّذِينَ جَاؤُوا بِالإِفْكِ عُصْبَةٌ مِّنكُمْ لا تَحْسَبُوهُ شَرًّا لَّكُم بَلْ هُوَ خَيْرٌ لَّكُمْ لِكُلِّ امْرِئٍ مِّنْهُم مَّا اكْتَسَبَ مِنَ الإِثْمِ وَالَّذِي تَوَلَّى كِبْرَهُ مِنْهُمْ لَهُ عَذَابٌ عَظِيمٌ
11- Hakika wasu jama'a ne daga cikinku,suka zo da gurungudumar karya,to kada ku zace shi sharri ne a gare ku,a'a ,shi alheri ne a gare ku,kowanne mutum daga cikinsu yana da abin da ya aikata na zunubi.Wanda kuwa ya jibinci fara kwaza shi daga cikinsu yana da azaba mai girma.
Wannan aya ci gaban ayar da ta gabata ce kuma tana Magana ne kan zargin matar aure mai mutunci matar mai mutunci kuma dalilin sabkar wannan ayar zargin da munafikai suka yi kan daya daga cikin matan ma'aikin Allah . A tarihin musulunci ya zo cewa; A daya daga cikin bulaguron da ma'aikin Allah yake yi wata rana ya tafi da matarsa Aicha kuma a daidai lokacin da yake koma zuwa Madina ,Aicha domin yin bukata tawagar ma'aikin Allah ta barta a baya kuma aka yi katari shi ma daya daga cikin Sahabbai yana baya sai ya ga Aicha sai ya taho da ita zuwa ga wannan tawaga .wasu daga cikin munafikai da ke tare da tawagar manzon Allah sai suka tuhimce su da kirkiro karya kansu da yada hakan a tsakanin mutane.
Sai wannan ayar ta sabka domin kwantarwa da manzon Allah (SWA) da mumunai hankali kan wannan lamari da wanke Aicha (RD) daga wannan zargi da kage. Kuma kowane daya daga cikin munafikan ya sami hukunci daidai da yadda ya yada wannan zargi don shi Abdallah bin Uba shugaban munafikan Madina yafi kowa leifi wajen yada wannan tuhuma kuma azabarsa tafi girma.
Daga cikin wannan ayar za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka;
Na farko:Wani lokaci makiya na amfani da munafikai na cikin gida domin kai hari.
Na biyu: Leifin wani bay a shafar wani kuma kowa daidai da leifinsa ne ko da leifi ya shafi jama'a.
- MUSIC***********
Daga karshe za mu saurari karatun ayoyi na 12 zuwa 14 a cikin suratul Nur:
لَوْلا إِذْ سَمِعْتُمُوهُ ظَنَّ الْمُؤْمِنُونَ وَالْمُؤْمِنَاتُ بِأَنفُسِهِمْ خَيْرًا وَقَالُوا هَذَا إِفْكٌ مُّبِينٌ
12- Ina ma lokacin da kuka ji shi muminai maza ,da muminai mata ,sun zatar wa kawunansu alheri suka kuma ce,wannan ai kage ne bayyananne.
لَوْلا جَاؤُوا عَلَيْهِ بِأَرْبَعَةِ شُهَدَاء فَإِذْ لَمْ يَأْتُوا بِالشُّهَدَاء فَأُولَئِكَ عِندَ اللَّهِ هُمُ الْكَاذِبُونَ
13- Me ya hana su kawo shaidu hudu game da shi kagen ? To tun da yake bas u kawo shedun ba ,to wadannan a wurin Allh su ne makaryata.
وَلَوْلا فَضْلُ اللَّهِ عَلَيْكُمْ وَرَحْمَتُهُ فِي الدُّنْيَا وَالآخِرَةِ لَمَسَّكُمْ فِي مَا أَفَضْتُمْ فِيهِ عَذَابٌ عَظِيمٌ
14- Ba don kuwa falalar Allah a gare ku da rahamarsa ba a duniya da lahira ,to lallai da azaba mai girma ta shafe ku game da abin da kuka kutsa cikinsa.
Wadannan ayoyi ci gaban ayar da ta gabace su ne indasuke kiran mumunai da kar su rika gaggauwar amince da duk wani labara da zama masu saukin kai da amincewa da labarin tuhuma ba tare da bincike ba. Har ila yau me ya sa lokacin da suka ji munafikai na zargin Muminai bas u yi kyakyawan zato ba ga mumunai ? me ya sa bas u ce karya ne wannan labara ba da kage?. Ba kun san tsark da darajarta ba da kuma ta mijinta ba kuma a dabra da haka kun san yadda munafikai suke na kirkiro da karya da yaudara mi yasa kuka amince da maganarsu ?. Mi yasa ba ku nemi su kawo shaidu hudu ba kan wannan zargi idan sun kasa a yi masu bulala kan wannan zargi da tuhuma kan karya?. A gaskiya wannan ayar tana isar da sako ne ga mumunai da kar su yi mummunan zato kan wani ,kuma ko sun ji wani zargi kar su amince da kokarin kare mutanan kirki har sai sun samu dalili tabbatacce kan aikin da aka danganta da su.
Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa hudu :
Na farko: yada zargi da karya a tsakanin jama'a dole mu maida martini da ya dace ba yin shiru ko yada wannan karya ba.
Na biyu:Zargi ga wani bangare na jama'a tamkar zargi ne kan jama'ar baki daya.
Na uku: Tushe ne mai kyau yin kakkyawan zato ga mumunai musamman a tsakanin al'ummar musulmi.
Na hudu:Wajibi ne ga musulmi ya kare mutuncin Manzon Allah da iyalansa da matansa da tunkarar duk wani da zai ci mutuncinsu.
Da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin na yau a madadin wadanda suka tallafawa har shirin ya kamala ni Tidjani malam lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa wassalam.
Suratun Nur Aya Ta 15-20 (Kashi Na 621)
Jama'a masu sauraro barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda, da a cikinsa muke kawo ayoyi da bayanai da suka kumsa, domin zame mana darasi a rayuwarmu ta yau da kullum da fatar Allah ya sa Kur'ani mai girma ya zama jagoranmu a rayuwarmu ta yau da kullum da kuma samin dacewa duniya da lahira amin. Kuma nine Tidjani Malam Lawali damagaram zan kasance tare da ku har zuwa karshen shirin nay au da tare da injiniya Aminu Ibrahim kiyawa
.
- Music***********
To madallah masu saurare za mu fara shirin na yau da sauraren karatun ayoyi na 15 da 16 a cikin suratul Nur:
إِذْ تَلَقَّوْنَهُ بِأَلْسِنَتِكُمْ وَتَقُولُونَ بِأَفْوَاهِكُم مَّا لَيْسَ لَكُم بِهِ عِلْمٌ وَتَحْسَبُونَهُ هَيِّنًا وَهُوَ عِندَ اللَّهِ عَظِيمٌ
15- Yayin da kuke bayeyeniyarsa kagen da harasanku ,kuke fadar abin da ba ku sani ba da bakunanku,kuke kuma tsammaninsa abu ne mai sauki,alhali kuwa shi mai girma ne a wurin Allah.
وَلَوْلا إِذْ سَمِعْتُمُوهُ قُلْتُم مَّا يَكُونُ لَنَا أَن نَّتَكَلَّمَ بِهَذَا سُبْحَانَكَ هَذَا بُهْتَانٌ عَظِيمٌ
16- Ina ma da yayin da kuka ji shi cewa kuka yi : Bai dace da mu mu yi irin wannan Magana ba, kuma ku ce: Subuhanallahi ,Ai wannan kage ne babba.
A shirinmu na makon jiya mun bayyana cewa wani gungu na munafikai a birnin Madina sun kago da tuhumar daya daga cikin matan Manzo da danganta ta da aikin assha da wani daga cikin sahabbai ,amma Allah ya maida masu makircinsu su Munafikai .Su ma kansu mumunai daga cikin sahabban manzon Allah a maimakon su yaki wannan makirci da wannan tuhuma da ake yadawa sai suke yada abin da suka ji to wannan lamari ya batawa manzon Allah da rai matuka da kuma ita kanta matarsa Aicha .A cikin wadannan ayoyi da muka ji Allah yana cewa; mi yasa kuke yada abin da ba ku da sani wato ilimi a kansa kuma kuna wasa da hankalin mutane kan labarin karya da ya kumshi tuhuma? Shin ba ku sani ba bai dace ba mutun ya yada wani mummmunan abu da ya ji kan wani dan uwansa musamman lamarin da ya shafi tuhuma kuma daya daga cikin matan manzon Allah.
Wadannan ayoyi sun yi nuni da abubuwa biyu masu muhimmanci da ya shafi zamantakewarmu : Na farko: ba komi ba ne da muka ji da ya shafi rayuwarmu ta zamantakewa za mu aminci da haka za mu dakile mummunar manufa ta yada karya a tsakanin jama'a. Na biyu:ba duk abin da muka ji ko muka sani ne za mu fadiwa wasunmu domin kare mutunci da suturta wani abu ne mai kyau kuma idan muka fallasa yana iya shfar al'umma da kawo matsala alhali a mahanga ta musulunci abin hani ne.
Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa uku :
Na farko:A tamna Magana kafin furtawa da kuma bincike da nazari kafin amincewa.
Na biyu: Abu ne mai sauki na yadawa da zargi kan wani da zubda masu mutunci a tsakanin mutane amma a gurin Allah abu ne mai girma da tsananin muni.
Na uku: Karewa da hana zubar da mutunci wani ko wasu nauyi ne da ya rataya kan al'umma baki daya ta hanyar kadige yada labaran karya da tuhuma.
Yanzu kuma za mu saurari karatun ayoyi na 17 da 18:
يَعِظُكُمُ اللَّهُ أَن تَعُودُوا لِمِثْلِهِ أَبَدًا إِن كُنتُم مُّؤْمِنِينَ
17-Allah yana gargadin ku kada ku koma yin irinsa har abada idan kun zamanto muminai.
وَيُبَيِّنُ اللَّهُ لَكُمُ الآيَاتِ وَاللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٌ
18-Allah kuma Yana bayyana muku ayoyinsa ne,Allah kuwa Masani ne Gwani.
Zargi wani musamman lamarin da ya shafi matar aure da wanda bai dace ba nada matsayi da girma a gurin Allah kamar yadda wannan ayar ta sake cewa: Allah tamkar uba ne mai damuwa da halin da dansa yake ciki da yi masa wa'azi da galgadi kar ya sake fadawa tarko aikata kuskure haka yake yi maku galgadi ku mumunai kar ku sake aikata wannan kuskure a tsakanin jama'a saboda wannan aiki bay a tafiya da imani.Idan a baya kun aikata kan kuskure da rashin sani to yanzu an sanar da ku sai ku yi takatsantsan idan irin wannan ta samu kar ku maimaita abin da ya faru a baya kuma ku sani Allah masani ne kan ayyukanmu,tunaninmu da niyarmu.
A cikin wadannan ayoyin za mu ilmantu da abubuwa uku
Na farko: Mutum a kullum yana bukatuwa da wa'azi da tunatarwa kuma Kur'ani shi ne babban littafi na tunatarwa don haka mu yawaita karanta shi .
Na biyu:Tuhuma da zargin wasu wani bangare ne na mummunar niya da raunin imani.
Na uku: babbar tunatarwa it ace yin tuba ga Allah ta haka sai mutum ya goje leifinsa na baya ya kuma hana aikata leifi a nan gaba.
- MUSIC**********
Masu saurare daga karshe za mu saurari karatun aya ta 19 da kuma ta 20 a cikin wannan sura ta Nur:
إِنَّ الَّذِينَ يُحِبُّونَ أَن تَشِيعَ الْفَاحِشَةُ فِي الَّذِينَ آمَنُوا لَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ فِي الدُّنْيَا وَالآخِرَةِ وَاللَّهُ يَعْلَمُ وَأَنتُمْ لا تَعْلَمُونَ
19-Hakaka wadanda suke son yaduwar mummunan abu game da wadanda suka yi imani suna da sakamakon azaba mai radadi a duniya da lahira ,kuma Allah Shi yake da sani,ku kuma ba abin da kuka sani.
وَلَوْلا فَضْلُ اللَّهِ عَلَيْكُمْ وَرَحْمَتُهُ وَأَنَّ اللَّه رَؤُوفٌ رَحِيمٌ
20- Ba don kuwa falalar Allah a gare ku da rahamarsa ba ,da kuma cewa lallai Allah Mai tausayi ne Mai rahama,da kun fada cikin hallaka.
Allah madaukakin sarki a cikin wadannan ayoyiyayi nuni da muni babba kan danganta wani abin assha ga wani bawansa kan karya da cewa; ba wai kawai kirkiro da karyar tuhuma kan bawan Allah da yadawa a tsakanin jama'a sabo ne mai girma hatta wanda ya gudurta aibata wani mumuni a tsakanin jama'a na da muni mai girma ko da kuwa ba kai ga aikatawa ba. Idan mutum ya aikata wani leifi ne yake da zunufi sabanin kudurta niyar alheri ko mutum bai aikata ba yana da lada to amma kudurta mummuna kan mumuni ma yana da zunufi kamar yadda ya zo a cikin kur'ani mai girma Inna Ba'adul Zanni Ismun Ma'ana hakika wani zato zunufi ne.Babu wani da ya san abin da ke boye a cikin zukata sai Allah kuma saboda lutifinsa ne yabarwa kansa sani don haka a kullum mu rika kudurta alheri da fata ta gari ga bayun Allah na gari mumunai.
A cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka:
Na farko:So da kudurta aikata sabo wani bangare ne na sabo .Daga cikin ayyukan sabo, daya dayan sabon da hatta kudurtawa babban zunufi ne wato zargi da neman zubar da mutuncin wani.
Na biyu:Yada mummunan labara a tsakanin jama'a musulmi ko da ta fatar baki ne balantana a aikace mutum yana ruguza duniyarsa da lahirarsa.
Da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin na yau a madadin wadanda suka tallafawa har shirin ya kamala ni Tidjani malam lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa wassalam.
Suratun Nur Aya Ta 21-24 (Kashi Na 622)
Jama'a masu sauraro barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda, da a cikinsa muke kawo ayoyi da bayanai da suka kumsa, domin zame mana darasi a rayuwarmu ta yau da kullum da fatar Allah ya sa Kur'ani mai girma ya zama jagoranmu a rayuwarmu ta yau da kullum da kuma samin dacewa duniya da lahira amin. Kuma nine Tidjani Malam Lawali damagaram zan kasance tare da ku har zuwa karshen shirin nay au da tare da injiniya Aminu Ibrahim kiyawa.
- Music***********
To madallah masu saurare za mu fara shirin na yau da sauraren karatun aya ta 21 a cikin suratul Nur:
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لا تَتَّبِعُوا خُطُوَاتِ الشَّيْطَانِ وَمَن يَتَّبِعْ خُطُوَاتِ الشَّيْطَانِ فَإِنَّهُ يَأْمُرُ بِالْفَحْشَاء وَالْمُنكَرِ وَلَوْلا فَضْلُ اللَّهِ عَلَيْكُمْ وَرَحْمَتُهُ مَا زَكَا مِنكُم مِّنْ أَحَدٍ أَبَدًا وَلَكِنَّ اللَّهَ يُزَكِّي مَن يَشَاء وَاللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ
21- Ya ku wadanda kuka ba da gaskiya,kada ku bi hanyoyin shaidan ,wanda kuwa duk ya bi hanyoyin shaidan,to lallai shi umarni yake yi da aikata alfasha da abin kyama.Ba kuwa don falalar Allah a agre ku da kuma rahamarsa ba,da ba daya daga cikinku da zai tsarkaka har abada ,sai dai kuma Allah shi yake tsarkake wanda ya so,Allah kuwa Mai ji ne ,Masani.
Bayan da muka kawo karshen ayoyin da ke bayani kan zargi da tuhuma kan karya da danganta abin da bai dace bag a mutuman kirki to wannan ayar da muka saurara tana bayani kan wani lamarin mai muhimmanci da cewa: mu yi hankali da takatsantsa kar mu fada tarkon shaidan da kaucewa hanya madaidaiciya ta shiriya. Shi shaidan a kullum yana bin mutun sau da kafa da kokarin yaudararsa ta fada tarkonsa ta hanyoyin aikata sabo . Kuma Allah madaukakin sarki a cikin kur'ani mai girma ya nuna mana hanyoyin kaucewa fada wannan tarko na shaidan ,wato ya ba wa kowane mutun hankali na banbanta mai kyau da maras kyau ,lala da mai kyau ,cin amana ,da tuhuma da sata da kisa duka bas u da kyau kuma duk wanda ya yi riko da su ya san makomarsu. Ya kuma nuna mana hanyar da idan muka yi riko da ita za mu dace duniya da lahira amma shaidan yana yi mana waswasi da ingiza mu zuwa ga fasadi da aikata sabo.
A cikin wannan ayar za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka;
Na farko:Ma'abuta imani bas u yin dogaro da jiji da kai kan imani kadai domin jiji da kai yana daga shaidani da kaucewa hanya ta hakika.
Na biyu:shaidani da sannu a hankali yake yin tasiri a zucciyar mutum da ruhinsa sai mu yi takatsantsan.
Yanzu kuma za mu saurari karatun aya ta 22:
وَلا يَأْتَلِ أُوْلُوا الْفَضْلِ مِنكُمْ وَالسَّعَةِ أَن يُؤْتُوا أُولِي الْقُرْبَى وَالْمَسَاكِينَ وَالْمُهَاجِرِينَ فِي سَبِيلِ اللَّهِ وَلْيَعْفُوا وَلْيَصْفَحُوا أَلا تُحِبُّونَ أَن يَغْفِرَ اللَّهُ لَكُمْ وَاللَّهُ غَفُورٌ رَّحِيمٌ
22- Kada kluma masu hali da wadata daga cikinku su rantse a kan kin ba da abin hannunsu ga makusanta da miskinai da masu hijira saboda Allah .Lallai kuma su yafe ,su yi rangwami.Shin ku ba kwa so Allah ya gafarta muku ? Allah kuwa Mai gafara ne Mai rahama.
Ayoyin da suka gabata sun yin suka mai girma ga wadanda suka kirkiro da zargin karya suka danganta da daya daga cikin matan ma'aikin Allah (SWAW) bayan haka sai wasu daga cikin sahabbai masu hannu da shuni suka dauki niyar ba za su taimakawa wadanda suke da hannu wajen yada wannan zargi duk da cewa suna bukatuwa ga taimakon nasu .Sai wannan ayar ta sabka da yin hani a gare su masu hannu da shuni da kar su haramtawa mabukata daga abin da Allah ya arzita su ma'ana su ci gaba da taimaka masu da kare dangantaka ta zamantakewa a tsakaninsu kuma su yi aikin da za su yi nadama daga aikin da suka aikata a baya da mantawa da abin da ya wakana a baya kuma haka al'ummar musulmi ta gad aba ramuwa ba a tsakanin musulmi.Ci gaban ayar ta yi nuni da wani lamari mai muhimmanci da cewa; shin ku kanku ba ku taba yin kuskure ba a rayuwarku ku ka tuba Allah ya gafarta maku ?a kullum kuna fatar Allah y aba ku dama da lullube ku da rahamarsa da yi maku gafara bayan tuba .Ba ku fatar fushi da azabar Allah a gare ku .Kuma kullum kuna neman gafararsa to ku sani suma kamar ku bayun Allah ne.
A cikin wannan ayar za mu ilmantu da abubuwa uku ;
Na farkonsu: Wanda yake tausaya waninsa da taimaka masa da dukiyarsa ,Allah zai dube shi da rahamarsa
Na biyu:.Wajen fuskantar masu leifi mu kasance masu tausayawa ba masu tasanani ba.
Na uku: Dole a taimakawa mabukaci ba sai musulmi ko salihi ba.
- MUSIC*********
Daga karshe za mu saurari karatun aya ta 23 da 24 a cikin suratul na Nur:
إِنَّ الَّذِينَ يَرْمُونَ الْمُحْصَنَاتِ الْغَافِلاتِ الْمُؤْمِنَاتِ لُعِنُوا فِي الدُّنْيَا وَالآخِرَةِ وَلَهُمْ عَذَابٌ عَظِيمٌ
23-Hakika wadanda suke jifan mata masu kamewa wadanda ba ruwansu da wani shagali na duniya,muminai ,suke jifan su da zina ,to an la'ance su duniya da lahira,kuma suna da sakamakon azaba mai girma.
يَوْمَ تَشْهَدُ عَلَيْهِمْ أَلْسِنَتُهُمْ وَأَيْدِيهِمْ وَأَرْجُلُهُم بِمَا كَانُوا يَعْمَلُونَ
24- A ranar da harsunasu da hannayensu da kuma kafafunsu za sub a da sheda a kansu game da abin da suke aikatawa.
A cikin wadannan ayoyin za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka:
Ayoyin da muka saurara a shirin da ya gaba sun hana mumunai da yin tuhuma da danganta wani abu da bai dace ga matar ma'aikin Allah tsira da aminci Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa to wannan ayar ta kawo doka ta bai daya da cewa: duk wata mace mai kamin kai da tsarki mumina babu wani da yake da hakkin danganta wani zargi kanta da yin tuhuma da mummunan zato kanta da kuma yada karya da tuhuma da ya ji daga wasu .Yin zina ko wani lamari da zai bata mata suna.Mai yada karya da tuhuma ga salihan bayun Allah ya sani Allah yana kollonsa da sanin komi kuma a kullum yana taimakawa wadanda ake zalunta ne kuma yayi masa tanadin mummunar azaba .A wannan duniya ya haramta da rahamar Allah a lahira kuma zai shiga wuta mai tsananin kuna.
Na farko:Kare hakkin mata masu kamin kai yana daga cikin tsarin kur'ani da koyarwar addinin musulunci.
Na biyu: Mata ya kamata su kare mutuncinsu da dangantakarsu ta iyali da zamantakewa kar su sa kansu cikin zargin mai zargi.
Da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin na yau a madadin wadanda suka tallafawa har shirin ya kamala ni Tidjani malam lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa wassalam.
Suratun Nur Aya Ta 25-29 (Kashi Na 623)
Jama'a masu sauraro barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda, da a cikinsa muke kawo ayoyi da bayanai da suka kumsa, domin zame mana darasi a rayuwarmu ta yau da kullum da fatar Allah ya sa Kur'ani mai girma ya zama jagoranmu a rayuwarmu ta yau da kullum da kuma samin dacewa duniya da lahira amin. Kuma nine Tidjani Malam Lawali damagaram zan kasance tare da ku har zuwa karshen shirin nay au da tare da injiniya Aminu Ibrahim kiyawa.
- Music***********
To madallah kuma masu saurare za mu fara shirin nay au ne da sauraren karatun aya ta 25 a cikin suratul Nur:
يَوْمَئِذٍ يُوَفِّيهِمُ اللَّهُ دِينَهُمُ الْحَقَّ وَيَعْلَمُونَ أَنَّ اللَّهَ هُوَ الْحَقُّ الْمُبِينُ
25- A wannan ranar Allah zai ba su cikakken sakamakonsu na gaskiya kuma za su san cewa Allah Shi ne Mai gaskiya bayyananniya.
A cikin shirin da ya gabata mun kawo ayoyi da ke bayani kan tanadin wutar jahannama da aka yi wa masu kirkira zargi kan mutane kirki .To wannan ayar na cewa ne: a ranar kiyama lokaci sakamako a gaban babbar kotu ta adalci baa i kawai harshe zai yi Magana da amincewa da duk wani sabo da muka aikata ,hatta gabobin jikinmu za su yi Magana da yin shaida kanmu komin kankantar sabo da muka aikata da kuma alheri ka ji hikima daga Allah da kuma Adalcinsa.Karkashin wannan shaidar da gabobin jikinmu suka yi kanmu ba don mun so ba kowa za a yi masa hukumci daidai da aikin da ya aikata alheri ko lala a daidai wannan rana da babu wata dama ta mu sake da gyara halinmu kash.
A cikin wannan ayar za mu ilmantu da abubuwa uku :
Na farko:A ranar kiyama mutum ba shi da iko kan gabobin jikinsa kamar yadda yake da hakan a wannan duniya don haka za su yi shaida kan mutum na ayyukan da ya aika a wannan duniya.
Na biyu: duk wani abu da ke a doran kasa hatta tsirrai na fahimtar lamura da fahimtar abin da muke aikata idan Allah ya so za su bada shaida a kan mutum a gobe kiyama.
Na uku: A kiyama ne kawai duk wani aiki da mutum ya aikata zai ganshi alheri ko lala komin kankantarsa.
Ynzu kuma za mu saurari karatun aya ta 26 :
الْخَبِيثَاتُ لِلْخَبِيثِينَ وَالْخَبِيثُونَ لِلْخَبِيثَاتِ وَالطَّيِّبَاتُ لِلطَّيِّبِينَ وَالطَّيِّبُونَ لِلطَّيِّبَاتِ أُوْلَئِكَ مُبَرَّؤُونَ مِمَّا يَقُولُونَ لَهُم مَّغْفِرَةٌ وَرِزْقٌ كَرِيمٌ
26- Miyagun maganganu suna fita ne ga bakunan miyagun mutane,su kuma miyagun mutane su suke fadar miyagun maganganu,tsarkakan maganganu kuma suna fita ne daga bakunan tsarkakan mutane,su kuma tsarkakan mutane su suke fadar tsarkakan maganganu ,Su wadannan kuwa ba a akama su da abin da suka fada,suna da sakamakon gafara da arzik mai girma.
Wannan ayar tana bayani ne kan sunna ta dabi'a da fitira da shari'ar musulunci ta amince da ita da cewa; mutane idan za su yi aure da zabar matar aure su yi la'akari da mata ta gari mai mutunci da sanin ya kamata mata saliha .Dokoki da koyarwar addinin musulunci sun hana mutum salihi ya auri mata fasika ko kuma mata saliha ta auri mutum fasiki domin hakan gurbata iyali ne sai dai idan ya tuba da gyara halinsa. Abin lura a nan shi ne rashin tsarki da mutum zai yi la'akari da shi wajen aure shi ne shirka da kafirci domin shari'a ba ta amince a auri mishriki ko kafiri ba ma'ana babu aure tsakanin misriki da ma'abucin imani.
A cikin wannan ayar za mu ilmantu da abubuwa biyu :
Na farko: Hatta wajen zabar matar aure ko mijin aure ana bukatar mutum yay i bincike da zabar na gwarai mai imani .
Na biyu: Zuriya ta gari tana kumshi a cikin zabar na gari wajen aure.
- MUSIC***********
Daga karshe kuma za mu saurari karatun ayoyi na 27 zuwa 29 a cikin surar ta Nur:
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لا تَدْخُلُوا بُيُوتًا غَيْرَ بُيُوتِكُمْ حَتَّى تَسْتَأْنِسُوا وَتُسَلِّمُوا عَلَى أَهْلِهَا ذَلِكُمْ خَيْرٌ لَّكُمْ لَعَلَّكُمْ تَذَكَّرُونَ
27- Ya ku wadanda kuka ba da gaskiya,kada ku shiga gidajen da ba naku ba har sai kun nemi izini ,kuma kun yi sallama ga masu su,wannan kuwa shi ya fi alheri a gare ku don ku wa'azantu.
فَإِن لَّمْ تَجِدُوا فِيهَا أَحَدًا فَلا تَدْخُلُوهَا حَتَّى يُؤْذَنَ لَكُمْ وَإِن قِيلَ لَكُمُ ارْجِعُوا فَارْجِعُوا هُوَ أَزْكَى لَكُمْ وَاللَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ عَلِيمٌ
28- Sannan idan ba ku sami kowa a cikinsu ba to kada ku shige su har sai an yi muku izini,idan kuwa aka ce da ku ku koma sai ku koma ,wannan shi ya fi tsarki a gare ku,Allah kuwa Masanin abin da kuke aikatawa ne.
لَّيْسَ عَلَيْكُمْ جُنَاحٌ أَن تَدْخُلُوا بُيُوتًا غَيْرَ مَسْكُونَةٍ فِيهَا مَتَاعٌ لَّكُمْ وَاللَّهُ يَعْلَمُ مَا تُبْدُونَ وَمَا تَكْتُمُونَ
29- Babu wani laifi a kanku ku shiga gidaje wadanda ba wani zaune a cikinsu kuma akwai kayanku a cikisu kuma akwai kayanku a cikinsu ,kuma Allah Yana sane da abin da kuke bayyanawa da abin da kuke boyewa.
Wadannan ayoyi na bayani ne kan wasu dokoki na zamantakewar jama'a a musulunce da yadda za a kyautata dangantaka a tsakani da cewa;kar ku shiga gidanjen da ba na ku ba sai kun yi sallama da sanar da masu gidan .Ba kawai ku shiga gida haka katsam ba tare da yin sallama da sanar da masu gidan ba .Idan aka amsa maku sai ku shiga idan kuma ba a amsa maku ba sai ku koma sai wani lokaci .kuma idan aka ce ku koma to ku koma kar ku yi wani zato da zargi da bas hi ba da ganin kun fice a ce ku koma ko nuna isa da shiga ba tare da sallama ba don takama da nuna dangantaka a gidan wani ko aboki ko makobci.Wannan shi ne rashin tsari da sanin ya kamata da kuma uwa uba rashin bin tsarin da addinin musulunci ya shinfida na yin sallama kafin shiga cikin gida .
Daga wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa uku :
Na farko: Gida wani guri ne na zama da samin nucuwa da hutawa babu wani da ke da hakkin kawo cikas da mutanan da ke cikin wannan gida da hana su hutawa da takura masu.
Na biyu:Gida wani guri ne da ya kebantu da mutanan gidan wani bas hi da hakkin shiga wannan gida ba tare da izininsu ba idan suka ce mu koma mu koma ba tare da wani kace n ace ba.
Na uku: Yin sallama na cikin koyarwar addinin musulunci a duk lokacin da muka gamu da wani musulmi kuma akwai lada da falala cikin hakan.Ma'ana yin sallama da amsa sallama.
Da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin na yau a madadin wadanda suka tallafawa har shirin ya kamala ni Tidjani malam lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa wassalam.
Suratun Nur Aya Ta 30-34 (Kashi Na 624)
Jama'a masu sauraro barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda, da a cikinsa muke kawo ayoyi da bayanai da suka kumsa, domin zame mana darasi a rayuwarmu ta yau da kullum da fatar Allah ya sa Kur'ani mai girma ya zama jagoranmu a rayuwarmu ta yau da kullum da kuma samin dacewa duniya da lahira amin. Kuma nine Tidjani Malam Lawali damagaram zan kasance tare da ku har zuwa karshen shirin nay au da tare da injiniya Aminu Ibrahim kiyawa.
- Music***********
To madallah za mu fara shirin nay au da sauraren karatun aya ta 30 a cikin wannan sura ta Nur:
قُل لِّلْمُؤْمِنِينَ يَغُضُّوا مِنْ أَبْصَارِهِمْ وَيَحْفَظُوا فُرُوجَهُمْ ذَلِكَ أَزْكَى لَهُمْ إِنَّ اللَّهَ خَبِيرٌ بِمَا يَصْنَعُونَ
30- Ka ce da muminai maza su kawar da idanuwansu kuma su kiyaye farjinsu,wannan shi ya fi tsarki a gare su. Hakika Allah Masanin abin da suke aikatawa ne.
Wannan ayar da yar da ke bayanta sun kirayi maza da mata masu imani da su ci gaba da kamin kai a rayuwarsu ta zamantakewa ta wannan za su rage yaduwar fasikanci da kaucewa hanay a tsakanin jama'a da zama abin koyi ga sauran jama'a.Shi mutum nada dabi'ar lura da ganin abin da ke faruwa a kewayensa ko da lamarin bai shafe shi wasu ma na yadawa karya ba tare da tamtancewa ba don haka wannan ayar ta ke cewa: masu imani suna takaita ganinsu duk wani abu da Allah bai amince bas u kalla bas u kollonsa suna rufe idonsu kamar yadda ya zo a cikin ruwayoyi da suka yi daidai da abin da wannan ayar ke Magana kansa :Kollon mace wadda ba maharumiyar mutum ba musamman ba tare da kayan sutura ba Haramin ne idan kuwa tana da kayan sutura kollon fuskarta ya kasance daidai haddin da addini ya amince .Ba kollon sha'awa ba ko kura mata ido.Wannan ayar ta nuna mana yadda ya kamata mu kiyaye ganinmu kar wannan ni'ima ta ido ta zame mana bala'I da kai mu ga hallaka. Hadewa guri guda tsakanin mata da maza ba ta hanyar da sha'ari'a ta amince ba ko lalura abin kauracewa ba .A mahangar musulunci da koyarwar musulunci dangantaka tsakanin mace da namiji da ta sabawa ta aure haraminne ta kowace hali. Ci gaban ayar ta galgadin mutane musamman mumunai kar su yi zaton Allah bay a ganinsu a'a duk abin da suke yi da kudurtawa a zahiri da badini Allah yana ganinsu.
A cikin wannan sura za mu ilmantu da abubuwa uku kamar haka:
Na farko: Imani na tabbata da kaucewa da duk wata dangantaka da ba dace ba da kollon haramin .
Na biyu:Tsarkake gani daga haramin mataki ne na tsarkin imani.
Na uku: Idan mun san Allah yana ganinmu da sanin abin da muka bnoye a zucciyarmu sai mu kiyaye ganinmu da tsarkake ganinmu daga kollon abin da bai dace ba.
- MUSIC***********
Daga karshe kuma za mu saurari karatun aya ta 31 a cikin wannan sura ta Nur:
وَقُل لِّلْمُؤْمِنَاتِ يَغْضُضْنَ مِنْ أَبْصَارِهِنَّ وَيَحْفَظْنَ فُرُوجَهُنَّ وَلا يُبْدِينَ زِينَتَهُنَّ إِلاَّ مَا ظَهَرَ مِنْهَا وَلْيَضْرِبْنَ بِخُمُرِهِنَّ عَلَى جُيُوبِهِنَّ وَلا يُبْدِينَ زِينَتَهُنَّ إِلاَّ لِبُعُولَتِهِنَّ أَوْ آبَائِهِنَّ أَوْ آبَاء بُعُولَتِهِنَّ أَوْ أَبْنَائِهِنَّ أَوْ أَبْنَاء بُعُولَتِهِنَّ أَوْ إِخْوَانِهِنَّ أَوْ بَنِي إِخْوَانِهِنَّ أَوْ بَنِي أَخَوَاتِهِنَّ أَوْ نِسَائِهِنَّ أَوْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُهُنَّ أَوِ التَّابِعِينَ غَيْرِ أُولِي الإِرْبَةِ مِنَ الرِّجَالِ أَوِ الطِّفْلِ الَّذِينَ لَمْ يَظْهَرُوا عَلَى عَوْرَاتِ النِّسَاء وَلا يَضْرِبْنَ بِأَرْجُلِهِنَّ لِيُعْلَمَ مَا يُخْفِينَ مِن زِينَتِهِنَّ وَتُوبُوا إِلَى اللَّهِ جَمِيعًا أَيُّهَا الْمُؤْمِنُونَ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ
31-Kuma kace da muminai mata su kawar da idanuwansu kuma su kiyaye mutuncinsu,kada kuma su fito da adonsu sai dai abin da ya bayyana daga gare shi,kuma su dora mayafansu a kan wuyan rigunansu kada kuma su fitar da adonsu sai ga mazajensu ko iyayensu ko yayayen mazajensu,ko yan uwansu mata ko kuma mata yan uwansu ko kuma abin da hannayensu suka mallaka watau bayi ,ko kuma masu bin su don neman abinci ba kuma masu bukatar mat aba,ko kuma kananan yara wadanda bas u san sha'awar al'aurar mata ba,kada kuma su buga kafafuwansu don a gane abin da suka boye na adon kafafunsu watau mundaye,kuma ku tuba ga Allah gaba dayanku yak u wadannan muminai don ku rabauta.
A cikin ayar da ta gabata Allah madaukakin sarki ga mu maza ya umarce mu da abubuwa biyu: Na farko mu kiyaye ganinmu na biyu lura da sha;awarmu. To wannan ayar ma da farko ta yi wa mata umarni da wadannan abubuwa biyu sai kuma galgadi mata kan kiyaye abubuwa uku da za su kare su daga kollon matane masu mugun nufi . Na farko su kiyayi sanya kayan da za su fito masu da kyawan da Allah yayi masu kamar fito da gashinsu da kirjinsu ga wadanda ba muharramansu ba.Na biyu: Sanya warwaro da dan kunne na kayatarwa da bayyana hakan mutane ba muharramsu ba. Na uku: Idan su tafi a kan titi kar su rika tafiyar takama da buga kafarsu don a lura suna taho wa da daukan hankalin mutane. A takaice Magana ,tafiya da kayan da maza da mata za su sanya yana tasiri ga rayuwar zamantakewar jama'a da kare al'umma daga fadawa fasadi idan aka kiyaye za a kare al'umma da samar da rayuwar zamantakewa mai tsafta .Duk wani abu da zai tada gariza da sha'awar mutane an yi hani kansa. Muna iya yin dubi da halin da duniyarmu take ciki a yau .A turai ta hanyar fakewa da yancin mata da yadda suke sanya kaya da bas u dace ba a bainar jama'a abin yayi muni da kuma ke haddasa fasadi babu iyaka kan mata da yan mata babu banbanci.yawaitar yi masu fyade,zubar da ciki ya zama ruwan dare kuma matsalar sai kamari ke ci gaba da yi.
Daga wannan ayar za mu ilmantu da abubuwa hudu:
Na farko: babu banbanci tsakanin mace da namiji wajen kiyaye ganinmu.
Na biyu:Musulunci bay a hani ga mace ta yi ado da gyara jikinta amma ga mijinta kuma ba a bainar jama'a ba ko wani muharraminta ya gani.
Na uku: Duk wata tafiya da mace za ta yi kuma ta dauki hankalin maza an yi hani kansa.
Na hudu:Hijabi da suturta jiki wajibi ne kamar yadda Allah da kur'ani suka yi umarni da shi da bayanin yadda za a suturta jiki sai a kiyaye.
Da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin na yau a madadin wadanda suka tallafawa har shirin ya kamala ni Tidjani malam lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa wassalam.
Jama'a masu sauraro barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda, da a cikinsa muke kawo ayoyi da bayanai da suka kumsa, domin zame mana darasi a rayuwarmu ta yau da kullum da fatar Allah ya sa Kur'ani mai girma ya zama jagoranmu a rayuwarmu ta yau da kullum da kuma samin dacewa duniya da lahira amin. Kuma nine Tidjani Malam Lawali damagaram zan kasance tare da ku har zuwa karshen shirin nay au da tare da injiniya Aminu Ibrahim kiyawa.
- Music***********
To madallah masu saurare za mu fara shirin na yau da sauraren karatun aya ta 32 a cikin suratul Nur:
وَأَنكِحُوا الأَيَامَى مِنكُمْ وَالصَّالِحِينَ مِنْ عِبَادِكُمْ وَإِمَائِكُمْ إِن يَكُونُوا فُقَرَاء يُغْنِهِمُ اللَّهُ مِن فَضْلِهِ وَاللَّهُ وَاسِعٌ عَلِيمٌ
32- Kuma ku aurar da marasa aure daga cikinku da kuma nagari daga bayinku da kuyanginku. Idan sun zamanto matalauta to Allah zai wadata su daga falalarsa,Allah kuwa Mai yalwatawa ne Masani.
Ayoyin da suka gabata sun yi Magana da bayani kan kamin kai a tsakanin jama'a da gani da suturta jiki da tafiyarmu da hanakn zai kare rayuwarmu ta zamantakewa daga fadawa cikin fasadi.To wannan ayar da muka saurara na kiranmu zuwa da yin aure da ke taka muhimmiyar rawa da babban matsayi wajen samar da rayuwa mai tsafta ta zamantakewa da samar da zuriya mai tsarki.
Wasu kirsitoci suna ganin gariza a wani sashe da shadanci kuma aure abin kama don haka wasu maluman kiristoci suke kauracewa aure da fakewa da wasu abubuwa maras tushe kamar talauci rashin abin hannu domin kaucewa yin aure dukan wannan na nuni da gurbacewar akida da jahiltar muhimmancin yin aure da kamin kai .Amma addinin musulunci na karfafa mana guiwa da yin riko da rayuwar aure hatta talauci da rashin abin hannu bay a hana mu yin aure domin shi mutum ba a raba shi da gariza don haka hanyar aure nada muhimmanci matuka.
A cikin wannan ayar za mu ilmantu da abubuwa uku kamar haka;
Na farko: a karfafa matasa da rungumar yin aure hakan zai taimaka wajen rage fasadi alfahasha a tsakanin jama'a.
Na biyu:Yin aure a musulunci abu ne mai daraja da aka yi umarni da jinjinawa kansa.
Na uku:Allah yayi alkawali ga wadanda suka rungumi rayuwar aure da sanya albarka da sa'ada a rayuwarsu kuma kar talauci ya zama shinge a tsakaninsu da yin aure.
Yanzu kuma za mu saurari karatun aya ta 33 :
وَلْيَسْتَعْفِفِ الَّذِينَ لا يَجِدُونَ نِكَاحًا حَتَّى يُغْنِيَهُمْ اللَّهُ مِن فَضْلِهِ وَالَّذِينَ يَبْتَغُونَ الْكِتَابَ مِمَّا مَلَكَتْ أَيْمَانُكُمْ فَكَاتِبُوهُمْ إِنْ عَلِمْتُمْ فِيهِمْ خَيْرًا وَآتُوهُم مِّن مَّالِ اللَّهِ الَّذِي آتَاكُمْ وَلا تُكْرِهُوا فَتَيَاتِكُمْ عَلَى الْبِغَاء إِنْ أَرَدْنَ تَحَصُّنًا لِّتَبْتَغُوا عَرَضَ الْحَيَاةِ الدُّنْيَا وَمَن يُكْرِههُّنَّ فَإِنَّ اللَّهَ مِن بَعْدِ إِكْرَاهِهِنَّ غَفُورٌ رَّحِيمٌ
33- Wadanda kuma bas u sami wadatar yin aure bas u kame kansu har Allah ya wadata su daga falalarsa, wadanda kuwa suke neman daura fansa daga wadanda kuka mallaka,sai ku daura musu fansar idan kun san suna da halin iya biya,kuma ku bar musu wani yanki daga dukiyar Allah da y aba ku,kada kuma ku tilasta wa kuyanginku da yin zina idan sun nemi kame kai don ku nemi amfanin rayuwar duniya . Wanda kuwa duk ya tilasta su, to lallai Allah mai gafara ne mai rahama bayan tilastawa da aka yi musu.
Wannan ayar ci gaban ayar da ta gabat ce da cewa:Idan ka kokarta wajen yin aure amma b aka kai ga dacewa b aba z aka fake da wannan ba wajen aikata sabo domin allah da ya sanya gariza ga mutum haka kuma y aba shi ikon lura da ita .Banbancin mutum da dabba shi ne: dabba idan ta koshi ba ta iya kaucewa gariza amma shi mutum ko yana koshe ko yana cikin yanayi na yunwa yana iya kula da garizarsa.Kamar yadda mutum yake yin azumi a watan azumin Ramadan ya hana kansa daga ci da sha to haka ma gariza yana iya hana kansa daga kusantar aikata haramin ko da kuwa garizarsa ta taso.Kuma a hada da neman taimakon Allah da tunawa da girma da daukakarsa kamar yadda Annabi Yusuf (AS) yayi lokacin da Zulakha ta bukace shi amma ya kiya da neman Allah yak are shi da wannan mummunan aiki.Ci gaban ayar na Magana ne ga wadanda suke da bayu da baiwa a gidajensu da cewa; idan yantar da su ya dace da amfani ne a gare su za su iya rayuwa da kafafunsu to su taimaka masu wajen yantar da su da ba su jari don rayuwa ta yanci da walwala. Na biyu Kar ku tilastawa bayunku aikata zina da maida su hanyar samar maku da kudin shiga.Azaba mai radadi na jiran mai aikata wannan aiki amma wanda aka tilastawa bas hi da leifi Allah ya gafarta masa.
A cikin wannan ayar za mu ilmantu da abubuwa hudu:
Na farko:Wadanda ba su da aure su kiyaye aikata sabo su lizanci hakuri da kamin kai daga aikata sabo.
Na biyu: a kullum mu rika lura da amfanin wadanda ke rayuwa karkashinmu ba amfanin kanmu kadai ba da tilasta masu aikata aikin da bai dace ba a addinance ko a hankalce ba.
Na uku:Dokokin musulunci ya karfafa mu zuwa ga yantar da bayu ne
Na hudu: Addinin musulunci ya hana tara dukiya ta hanyar da ba ta dace ba.
- MUSIC***************
Daga karshe za mu saurari aya ta 34 a cikin surar ta Nur:
وَلَقَدْ أَنزَلْنَا إِلَيْكُمْ آيَاتٍ مُّبَيِّنَاتٍ وَمَثَلا مِّنَ الَّذِينَ خَلَوْا مِن قَبْلِكُمْ وَمَوْعِظَةً لِّلْمُتَّقِينَ
34- Hakika kuma Mun saukar muku da ayoyi mabayyana da kuma izina daga wadanda suka wuce gabaninku kuma da gargadi ga masu tsoron Allah.
Wannan it ace aya ta karshe daga jerin ayoyin nur a wannan sura ta Nur inda Allah yake cewa: mun sabkar maku da ayoyi da suka yi maku bayani dalla-dalla kan rayuwa da kuma abubwan da suka faru a baya a tarihi domin daukan darasi a rayuwarsu kuma mu sani da cewa sai mun hada da takawa da tsoran Allah da kuma yin riko da galgadin Allah yake yi mana .
A cikin wannan ayar za mu ilmantu da abubuwa biyu:
Na farko:Kur'ani littafi ne mai tsarki da hasken rayuwa ,kuma hatta ta hanyar tarihin al'ummomin da suka gabata na galgadi da wa'azzartar da mu.
Na biyu: Kowane mutum a wannan doran kasa na bukatuwa da galgadi da wa'azi komin matsayi da daukakarsa .
Da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin na yau a madadin wadanda suka tallafawa har shirin ya kamala ni Tidjani malam lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa wassalam.
Suratun Nur Aya Ta 35-38 (Kashi Na 625)
Jama'a masu sauraro barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda, da a cikinsa muke kawo ayoyi da bayanai da suka kumsa, domin zame mana darasi a rayuwarmu ta yau da kullum da fatar Allah ya sa Kur'ani mai girma ya zama jagoranmu a rayuwarmu ta yau da kullum da kuma samin dacewa duniya da lahira amin. Kuma nine Tidjani Malam Lawali damagaram zan kasance tare da ku har zuwa karshen shirin nay au da tare da injiniya Aminu Ibrahim kiyawa.
- Music***********
To madallah yanzu kuma za mu saurari karatun aya ta 35 a cikin wannan sura ta Nur:
اللَّهُ نُورُ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ مَثَلُ نُورِهِ كَمِشْكَاةٍ فِيهَا مِصْبَاحٌ الْمِصْبَاحُ فِي زُجَاجَةٍ الزُّجَاجَةُ كَأَنَّهَا كَوْكَبٌ دُرِّيٌّ يُوقَدُ مِن شَجَرَةٍ مُّبَارَكَةٍ زَيْتُونَةٍ لّا شَرْقِيَّةٍ وَلا غَرْبِيَّةٍ يَكَادُ زَيْتُهَا يُضِيءُ وَلَوْ لَمْ تَمْسَسْهُ نَارٌ نُّورٌ عَلَى نُورٍ يَهْدِي اللَّهُ لِنُورِهِ مَن يَشَاء وَيَضْرِبُ اللَّهُ الأَمْثَالَ لِلنَّاسِ وَاللَّهُ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمٌ
35- Allah ne Mai haskaka sammai da kassai. Misalin haskensa tamkar alkuki ne da fitila take a cikinsa,fitilar kuma tana cikin karau,karan kuma tamkar tauraro ne na lu'ulu'u,ana kunna ta da man bishiya mai albarka ta zaituni, ita ba daga mahudar rana take ba kuma ba ta daga mafadarta, kuma man kamar zai kama da kansa ko da wuta ba ta taba shi ba. Haske kan haske .Allah Yana shiryar da wanda yake so zuwa ga haskensa,kuma Allah Yana buga misalai ne ga mutane .Allah kuwa Masanin komai ne.
Wannan ayar it ace ayar da aka sani da Nur kuma a dalilin wannan ayar ce aka sanyawa wannan sura sunar Nur wato haske . Wannan ayar ta bayyana Allah a matsayin Nur wato haske saboda shi ne ya haskaka wannan duniya da duk wani abu da ya halitta don haka wannan ayar ta siffanta Allah da ba su sunan haske.Duk wani abu da ke kewaye da jikin mutum haske ne ya haskaka masa shi har ya fahimci kyau da hikima da di'ar wannan abu. Haske shi ne tushen duk wani alheri ba z aka samu haske tare da sharri da cutarwa.rayuwa ta tsirre da dabbobi da mutane ta dogara da haske ne ba tare da haske ba rayuwa ba ta da wata ma'ana.Shi haske yana haskaka kansa ya kuma haskaka duk wani abu da ke kusa da shi.Allah shi ne haske na hakika mai haskaka komi da samar da rayuwa ga halittunsa baki daya. Kuma rayuwa da mutuwa tana hannunsa Allah.Bugu da kari shi ne mai tafiyar da lamuran sammai da kassai kamar yadda aya ta 50 a cikin suratul Daha ke cewa: Wanda ya halicci komi kuma ya shiryar da shi.
Ci gaban ayar ta Nur ta siffanta shiriyar Allah da hasken fitila da ke haskaka kowane gida da haskenta da kawar da duhu daga mazauna wannan gida. Wannan fitila an sanya ta a gurin da ya dace da bata kariya ta gilashi don kar ta mutu ana sanya mata kanazir don ci gaba da kuma kara haskakawa. Haka wannan hasken fitila zai ci gaba haskaka wannan gidan to hasken shiriya daga Allah fiye da haka yake da yake sabka ta hanyar wahayi da littafi daga Allah daga sama zuwa Manzonninsa daga mu bil adama da kuma a cikin zukatan mumunai da haskaka zukatansu da kawar da duhun jahilci da zalunci. Kamar yadda ayar kur'ani ke cewa yana fitar da su daga duhu zuwa haske. Ya Allah ka fitar da mu daga duhu zuwa hasken shiriya ameen.
A cikin wannan ayar za mu ilmantu da abuwa da dama amma za mu takaita da abubuwa uku kamar haka:
Na farko: duk wata halitta a doran kasa tana bukatuwa da haske daga Allah musamman a rayuwarmu ta yau.
Na biyu: Shiriya daga Allah c eke tafiyar da sammai da kassai zuwa da burin a hakika kuma mutum yana son kai wag a kamala.
Na uku: Imani yana karfafa da abinci na halal da hanya madaidaiciya sabanin haka kaucewa hanya ne.
Yanzu kuma lokaci ne da za mu saurari karatun aya ta 36 a cikin suratul ta Nur:
فِي بُيُوتٍ أَذِنَ اللَّهُ أَن تُرْفَعَ وَيُذْكَرَ فِيهَا اسْمُهُ يُسَبِّحُ لَهُ فِيهَا بِالْغُدُوِّ وَالآصَالِ
36- Hasken yana cikin dakuna watau masallatai wadanda Allah Yay i umarni a daukaka a kuma ambaci sunansa a cikinsu. Wasu mazaje suna tasbihi gare Shi a cikinsu safe da yamma.
Wannan ayar ta kamala bayanin hasken shiriya daga Allah inda wannan ayar take cewa: a doran kasa akwai fitilar shiriya daga Allah da ke haskaka gidaje da ke haskaka kowa da haskenta. Ma'abuta wannan gida ma'abuta imani ne da salla da ambaton allah . Gidajen da Allah ya fifita mutanen gidan fiye da wasunsu kuma suna da matsayi mai girma a tsakanin mumunai. A fili yake dakin ka'aba dake Makka da sauran masallatai da guraren addini a doran kasa suna da wannan matsayi mutane idan suna son gamuwa da shiriyar Allah sai su gaggauta zuwa irin wannan guri.
A cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa biyu:
Na farko:Masallatai dole su kebanta da sauran gidaje wajen ambaton Allah da ibadodi da taimakon jama'a.
Na biyu: Ambaton Allah a kowane gida na musulmi ana yi amma fiffikon gidan manzon Allah yafi kowane gida ambaton Allah.
- MUSIC**********
Daga karshe za mu saurari karatun aoyi na 37 da 38 a cikin wannan sura ta Nur:
37- Su mazaje ne wadanda kasuwanci da saye da sayarwa bas a shagaltar da su daga ambaton Allah da kuma tsai da salla da ba da zakka suna tsoron ranar da zukata da idanduna suke raurawa.
38 – Suna haka ne don Allah Ya saka musu mafi kyan abin da suka aikata ,kuma Ya kara musu daga falalarsa.Allah kuwa Yana arzuta wanda ya so ba da iyaka ba.
Maza da mata ma'abuta imani suna albakuwa da shiriyar Allah. Suna iya kacin kokarinsu wajen neman halaliyarsu a wannan duniya da abin da za su sanya a bakin salati suna aiki tukuru da kasuwanci ta hanyar da ta dace amma wadannan ayyuka bas u hana su ayyukansu na addini da neman kusancin Allah kuma a kullum suna tunanin makomarsu da karshen rayuwarsu da yadda za su kasance a babbar kotu a gobe kiya Alkalinta kuwa Allah ne masani komi da kowa zahiri da badini kuma za su amsa ayyukan da suka aikata a wannan duniya komin kankantarsa.Wadannan na daga cikin abubuwa da ke karfafawa ma'abuta imani karfin guiwa da kara kauracewa kusantar sabo sai dai kara kusantar aikata alheri da kyawawa. Kuma Shi Allah yana kyautata wa masu aikata alheri da kollonsu da idon rahama da sakayawa wasu aikata banna da adalcinsa.Aikin alheri ana rubinya ladansa wani karon har so dari bakwai amma shi aikin banna ba a rubinya sakayyarsa kaji wani rangwamai da tausayawar Allah ga bayunsa da buyawarsa. Lutifin Allah ga ma'abuta aikin alheri ba a wannan duniya ya tsaya ba hatta a lahira ya saka masu da mafi alherin sakayawa da ko su kansu bas u zaton hakan .Karkshin wata ruwaya bayun Allah na gari lokacin da suka ji kiran salla ,suna barin duk wani aiki da suke yi su nufi masallaci ko gurin salla kuma lokacin da suke salla bas u tunanin wani abu sai Allah da sallar da suke yi.
A cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa hudu:
Na farko:Kudi ,dukiya da abubuwan more rayuwar duniya da karfin iko idan mutum sai mutum ya kula da su ke hana shi ambaton Allah.
Na biyu: Kasuwanci nada amfani idan aka hada ta da ambaton Allah ,salla a kan lokaci a tsunace da fittar da zakka. Yawancin mutane na rungumar rayuwar duniya sun gafala akwai rayuwar lahira.ma'ana kasuwanci da tara dukiya kar su zama shinge da Katanga tsakaninmu da ambaton Allah idan haka ta faru babu wani amfani. A gaskiya ambaton allah da yin salla a komi yana tattare da albarka da samar da al'umma ta gari.
Na uku: a ranar kiyama komi bas hi da amfani sai ayyukan alheri da mutum ya aikata da fatar mun gane hakan.
Na hudu: Masu neman halaliyarsu saboda Allah a kasuwaci ne ko duk wani aiki ba za su taba ci ko karbar haramin ba .
Da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin na yau a madadin wadanda suka tallafawa har shirin ya kamala ni Tidjani malam lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa wassalam.
Suratun Nur Aya Ta 39-42 (Kashi Na 626)
Jama'a masu sauraro barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda, da a cikinsa muke kawo ayoyi da bayanai da suka kumsa, domin zame mana darasi a rayuwarmu ta yau da kullum da fatar Allah ya sa Kur'ani mai girma ya zama jagoranmu a rayuwarmu ta yau da kullum da kuma samin dacewa duniya da lahira amin. Kuma nine Tidjani Malam Lawali damagaram zan kasance tare da ku har zuwa karshen shirin nay au da tare da injiniya Aminu Ibrahim kiyawa.
- Music***********
To madallah za mu fara shirin nay au ne da sauraren karatun ayoyi na 39 da 40 a cikin suratul Nur:
وَالَّذِينَ كَفَرُوا أَعْمَالُهُمْ كَسَرَابٍ بِقِيعَةٍ يَحْسَبُهُ الظَّمْآنُ مَاءً حَتَّى إِذَا جَاءَهُ لَمْ يَجِدْهُ شَيْئًا وَوَجَدَ اللَّهَ عِندَهُ فَوَفَّاهُ حِسَابَهُ وَاللَّهُ سَرِيعُ الْحِسَابِ
39 – Wadanda kuwa suka kafirtar ayyukansu,kamar kawalwalniya ce a fako wadda mai jin tsananin kishirwa yake zaton ruwa ne ,har lokacin da yake zo gare ta ba zai samu komai ba,sai ya sami Allah a wurinta, sai Ya cika masa hisabinsa.Allah kuwa Mai saurin hisabi ne.
أَوْ كَظُلُمَاتٍ فِي بَحْرٍ لُّجِّيٍّ يَغْشَاهُ مَوْجٌ مِّن فَوْقِهِ مَوْجٌ مِّن فَوْقِهِ سَحَابٌ ظُلُمَاتٌ بَعْضُهَا فَوْقَ بَعْضٍ إِذَا أَخْرَجَ يَدَهُ لَمْ يَكَدْ يَرَاهَا وَمَن لَّمْ يَجْعَلِ اللَّهُ لَهُ نُورًا فَمَا لَهُ مِن نُّورٍ
40 – Ko kuma kamar duffai a cikin kogi mai zurfi da kumfa ta lullube shi,daga samansa kuma akwai rakumin ruwa,daga samansa kuma akwai wani hadari.Duffai wasu a kan wasu,idan ya fito da hannunsa ba zai iya ganin sa ba .Wanda kuma Allah bai sanya wa haske ba ,to bas hi da wani haske.
A cikin shirin da ya gabata mun yi bayani ne kan shiriya daga Allah da kuma wadanda suka shiryu da yadda suke rayuwar sa'ada a wannan duniya da kuma samin sakamakon alheri a gobe kiyama sakamako mai girma daga Allah. Wadannan ayoyi na auna matsayi da halin da kafirai ke ciki da kwatamtawa da na ma'abuta imani da cewa; Kafirai a lokacin da kishirwa ke daminsu na kollon hatta tabkin aljannu wato kawalwaniya a matsayin ruwa kuma haka za su ci gaba da neman ruwan ba za su samu ba har sai kishirwa ta kais u ga hallaka. Su kuwa mumunai suna sha ne daga diddigo na shiriya ba tare da rudu ya rude sub a ,Mumunai a kullum suna tare da hasken shiriya daga Allah wato haske bias haske amma su kafirai su kansu duhu ne cikin duhu ma'ana bata cikin bata ciki da bai.Allah ya kiyashe mu ameen.
A cikin wadannan ayoyi Allah ya bada misali biyu wajen siffanta kafirai da halin da suke ciki. Na farko yadda suke neman ruwa don tsananin kishirwa. Na biyu: yadda suke neman tsira a lokacin da suke tsakiyar teku da kolloon bakin duhu a matsayin iggiyar ruwa da dabarbarcewa. Duka misalan biyu na nuni da mummunan halin da kafiri da karicinsa .
A cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa hudu:
Na farko:Ayyukan kafirai zai yu a zahiri muga kyaunsa amma a badini yafi komi muni .
Na biyu: Ayyuka maras kyau na kafirai ta ko ina yayi hannun riga da gaskiya domin ya samo tushe ne daga zalunci da duhun kafirci.
Na uku: Ayyuka masu kyau na kafirai tamkar kawalwainiya ne yayin da ayyukansu maras kyau zalunci ne.
Na hudu: im ba don hasken imani ba ,hasken ilimi dahankali ba za su wadatar ba kuma ba za su kai mutum ga tsira ba.
- MUSIC***********
Yanzu kuma za mu saurari karatun ayoyi na 41 da 42 :
أَلَمْ تَرَ أَنَّ اللَّهَ يُسَبِّحُ لَهُ مَن فِي السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ وَالطَّيْرُ صَافَّاتٍ كُلٌّ قَدْ عَلِمَ صَلاتَهُ وَتَسْبِيحَهُ وَاللَّهُ عَلِيمٌ بِمَا يَفْعَلُونَ
41 – Ba ka gani cewa Allah duk abin da yake sammai da kasai yana tasbihi ne gare Shi, haka tsuntsaye kuma suna masu bude fukafukansu,kowanne dayansu ya san sallarsa da tasbihinsa.Allah kuwa Masanin abin da suke aikatawa ne.
وَلِلَّهِ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ وَإِلَى اللَّهِ الْمَصِيرُ
42- Kuma mulkin sammai da kassai na Allah ne makoma kuma zuwa ga Allah take.
Bayan ayoyin da suka kwatamta ayyukan kafirai da na mumunai to wadannan ayoyi da muka saurara kuwa na cewa ne: Allah bay a bukatuwa da ibadodin bayunsa da d cewa; duk wata jhalitta hatta mala'iku da ke sama masu tasbihi ga Allah ba iyaka da sauran halittu masu rai da maras rai suna cikin tasbihi da godiya ga Allah kamar yadda kur'ani ya tabbatar da hakan. A cikin wannan ayar da wasu ayoyin kur'ani sun yi nuni da halittu da tasbihin mala'iku a sammai suna tasbihi da kadaita Allah da bauta.Tsintsaye na tashi sama abin sha'awa da neman abinci da yawo cikin hikimar Allah kuma Allah ya san da wanzuwarsu kuma suma suna tasbihi ga Allah kuma yawancin mutane irina bas u fahimtar hakan sai waliyan Allah da Annabawa da manzonni da Allah y aba su karfin sanin abin da ke cikin zucciya kamar yadda Allah ya fada a cikin aya ta 44 a cikin suratun Israa cewa: ba mu fahimta da sanin tasbihin da suke yi .
To wadannan ayoyi na fadakar da mu ne sanin cewa duk halittun da Allah ya halitta na tasbihi a gare Shi amma shi mutum ya shagala don haka Allah yake tunatar da shi da tabbatar masa da cewa Allah bay a bukatuwa da tasbihinmu face mune muke bukatuwa da tasbihin da muke yi Allah sa mu gane da aiki da hakan.
A cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa uku kamar haka:
Na farko: Dukan halittun da Allah ya halitta yana sane da su da halin da suke ciki kuma suna yin salla da tasbihi a gare Shi kuma Allah ne yak e daukaka kowa daga cikinsu.
Na biyu: Yin sallah da godiya ga Allah abu ne mai kyau amma su kasance karkashin ilimi da imani na hakika.
Na uku:Wannan duniya da abin da ke cikinta suna tafiya ne karkashin ikon Mahaliccinsu kuma kowane yana son cimma burin da aka halicce shi don shi.
Da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin na yau a madadin wadanda suka tallafawa har shirin ya kamala ni Tidjani malam lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa wassalam.
Suratun Nur Aya Ta 43-47 (Kashi Na 627)
Jama'a masu sauraro barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda, da a cikinsa muke kawo ayoyi da bayanai da suka kumsa, domin zame mana darasi a rayuwarmu ta yau da kullum da fatar Allah ya sa Kur'ani mai girma ya zama jagoranmu a rayuwarmu ta yau da kullum da kuma samin dacewa duniya da lahira amin. Kuma nine Tidjani Malam Lawali damagaram zan kasance tare da ku har zuwa karshen shirin nay au da tare da injiniya Aminu Ibrahim kiyawa.
- Music***********
To madallah kuma za mu fara shirin nay au ne da sauraren karatun ayoyi na 43 da 44 a cikin surar ta Nur:
أَلَمْ تَرَ أَنَّ اللَّهَ يُزْجِي سَحَابًا ثُمَّ يُؤَلِّفُ بَيْنَهُ ثُمَّ يَجْعَلُهُ رُكَامًا فَتَرَى الْوَدْقَ يَخْرُجُ مِنْ خِلالِهِ وَيُنَزِّلُ مِنَ السَّمَاء مِن جِبَالٍ فِيهَا مِن بَرَدٍ فَيُصِيبُ بِهِ مَن يَشَاء وَيَصْرِفُهُ عَن مَّن يَشَاء يَكَادُ سَنَا بَرْقِهِ يَذْهَبُ بِالأَبْصَارِ
43- Ba ka gani cewa Allah Yana tsakaninsu sannan Ya harhada tsakaninsu sannan ya mai da su masu hawan juna ,sai ka ga ruwan sama yana fitowa ta tsakankaninsu,kuma Yana saukar da wasu tasake na giragizai daga sama wadanda a cikinsu akawai kankara,sai Ya samar da shi ruwan ga wanda Ya so Ya kuma kautar da shi daga wanda Ya so,hasken walkiyarsa Yana kusa da ya fauce idanu.
يُقَلِّبُ اللَّهُ اللَّيْلَ وَالنَّهَارَ إِنَّ فِي ذَلِكَ لَعِبْرَةً لِّأُولِي الأَبْصَارِ
44 – Allah Yana jujjuya dare da rana.Hakika game da wannan lallai akwai izina ga ma'abota basira.
Wadannan ayoyi na bayani ne daukaka da girman Allah wajen kula da ikon tafiyar da halittunsa da cewa; tafiya da zagayowar dare da rana cikin tsari da tsarin tafiyar da wata da rana duk suna hannun Allah . Ba haka kwacam aka samar da sub a .Shin hankali da tunani na hakika zai amince da samuwarsu haka kwacam ,tamkar a ce wake da tsarin rubutu da mutum key i haka ne kawai babu mai tsara su suka samar da kansu.To babu wanda zai yarda to haka tsari da tafiyar da wannan duniya da abin da ke cikinta dare da rana suna karkashin kudura da iradar Allah hatta girgizar kasa da ambaliya da iska mai karfi suna cikin masaniya da iradar Allah da dalilin abkuwarsu kamar yadda wani yanki a yi ruwan sama wani yanki kuma a yi fari yana sane kuma cikin tsari da hikimarsa ne. Tafiya da zagayowar dare da rana a tsawon shekara ba su canjawa amma tafiyar giza-gizai da sabkar ruwan sama da yankuna daban daban na sauyawa ko wata shekarar a samu fari wannan ma cikin hikima da masaniyar Allah ne .
A cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka;
Na farko:Lamura na dabi'a a tsarin tafiyar da wannan duniya na karkashin iko da iradar Allah ne kuma cikin hikima da amfani yake kawo duk wani sauyi a tafiyar da su.
Na biyu: Samar ruwan sama da kankara da tsawa zai sama rahama kamar yadda kuma zai iya sabanin haka amma dukansu Allah yana sane da iradarsa a cikin hakan.
Yanzu kuma za mu saurari karatun aya ta 45:
وَاللَّهُ خَلَقَ كُلَّ دَابَّةٍ مِن مَّاء فَمِنْهُم مَّن يَمْشِي عَلَى بَطْنِهِ وَمِنْهُم مَّن يَمْشِي عَلَى رِجْلَيْنِ وَمِنْهُم مَّن يَمْشِي عَلَى أَرْبَعٍ يَخْلُقُ اللَّهُ مَا يَشَاء إِنَّ اللَّهَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ
45- Kuma Allah Ya halicci kowace dabba daga ruwa ,sannan daga cikinsu akwai wadanda suke jan cciki,kuma daga cikinsu akwai wadanda suke tafiya a kan kafa biyu,akwai kuma wadanda suke tafiya a kan kafa hudu.Allah Yana halittar abin da Yake so.Hakika Allah Mai iko ne a kan komai.
Ayoyin da suka gabata sun yi bayani kan sabkar ruwan sama da sabawar dare da rana to wannan ayar tana bayani kan rayuwa da nau'in rayuwar da cewa:duk halittar da Allah ya halitta mai rai a doran kasa da sammai da taku cikin hikima da kudurar Allah y halicce su ne daga ruwa da samar da dugon halitta a ruwan da sanya rayuwa a cikinsu wasu na tafiya da jan ciki wasu na tafiya da kafa biyu wasunsu kuwa da kafafu hudu ga dai halittu iri iri da tafiyar da lamuransu cikin hikima kuma Allah wanda Ya halicci halittunsa daga ruwa da kasa Shi ne kuma mai tafiyar da lamuransu.
A cikin wannan ayar za mu ilmantu da abubuwa uku :
Na farko:Allah shi ne Mahalicci masani kuma halittarsa ba ta da iyaka.
Na biyu: Tushen abin da Allah ya halicci komi shi ne ruwa wannan kuwa na nuni da karfin kudura ta Allah yadda Allah ya halicci halittu iri iri daga ruwa.
Na uku:Idan mutum ya nisanta da ma'anawiya a lamarinsa na isa ga kamala bas hi da banbanci da dabba.
- MUSIC***********
Daga karshe za mu saurari karatun ayoyi na 46 da 47 a cikin suratul Nur:
لَقَدْ أَنزَلْنَا آيَاتٍ مُّبَيِّنَاتٍ وَاللَّهُ يَهْدِي مَن يَشَاء إِلَى صِرَاطٍ مُّسْتَقِيمٍ
46 – Hakika Mun saukar da ayoyi masu bayyana komai da komai. Allah kuwa Yana shiryar da wanda Ya so ne zuwa tafarki madaidaici.
وَيَقُولُونَ آمَنَّا بِاللَّهِ وَبِالرَّسُولِ وَأَطَعْنَا ثُمَّ يَتَوَلَّى فَرِيقٌ مِّنْهُم مِّن بَعْدِ ذَلِكَ وَمَا أُوْلَئِكَ بِالْمُؤْمِنِينَ
47 – Kuma suna cewa: Mun ba da gaskiya da Allah da kuma Manzo kuma mun bi,Sannan wata kungiya daga cikinsu takan ba da baya bayan wancan imanin .Wadannan kuwa ba muminai ba ne.
Ayoyin da suka gabata na bayani kan yadda Allah ke tafiyar da halittunsa da yadda ya halicce su to wadannan ayoyin na bayani kan sabkar wahayi da hukumce-hukumcen shari'a domin shiryar da mutum zuwa ga kamala da sa'ada ta karshe da cewa; Ayoyin bayyanannu a cikin littafai da Allah ya sabkar ta hanyar manzonninsa zuwa ga mutane na bayani a fili yadda mutum zai rayuwa rayuwa mai inganci ba tare da kasawa ko wuce gona da iri ba. Suna kiran mutum zuwa ga yin riko da hanyar Allah hanya madaidaici da za ta kai mu ga kamala da burin a hakika .Kuma su Annabawa da manzonni su ne Allah ya umurata da yi mana jagoranci a wannan hanya madaidaiciya.
A cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa uku :
Na farko: Allah madaukakin sarki ta hanyar aiko da annabawa da manzonni da sabkar da wahayi ya samar da duk wani yanayi na shriyar da mutum da kuma kafa masa hujja ta karshe.
Na biyu: Munafinci mummmuna ne da kuma yake yi wa duniyar musulmi barazana da kuma ke cutar da su.
Na uku: Kar mu zamanto masu saukin kai da amincewa da duk wani mai yaudara da fadawa tarkon shaidan.
Da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin na yau a madadin wadanda suka tallafawa har shirin ya kamala ni Tidjani malam lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa wassalam.
Suratun Nur Aya Ta 48-52 (Kashi Na 628)
Jama'a masu sauraro barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda, da a cikinsa muke kawo ayoyi da bayanai da suka kumsa, domin zame mana darasi a rayuwarmu ta yau da kullum da fatar Allah ya sa Kur'ani mai girma ya zama jagoranmu a rayuwarmu ta yau da kullum da kuma samin dacewa duniya da lahira amin. Kuma nine Tidjani Malam Lawali damagaram zan kasance tare da ku har zuwa karshen shirin nay au da tare da injiniya Aminu Ibrahim kiyawa.
- Music***********
To madallah za mu fara shirin na yau ne da sauraren karatun ayoyi na 48 zuwa 50 a cikin suratul Nur:
وَإِذَا دُعُوا إِلَى اللَّهِ وَرَسُولِهِ لِيَحْكُمَ بَيْنَهُمْ إِذَا فَرِيقٌ مِّنْهُم مُّعْرِضُونَ
48 – Idan kuwa aka yi kiran su zuwa ga Allah da Manzonsa dan yayi hukunci a tsakaninsu sai ka ga wata kungiya daga cikinsu tana bijirewa.
وَإِن يَكُن لَّهُمُ الْحَقُّ يَأْتُوا إِلَيْهِ مُذْعِنِينَ
49 – Idan kuwa suna da wani hakki da suke nema sai su zo wurinsa suna masu kaskantar da kai.
أَفِي قُلُوبِهِم مَّرَضٌ أَمِ ارْتَابُوا أَمْ يَخَافُونَ أَن يَحِيفَ اللَّهُ عَلَيْهِمْ وَرَسُولُهُ بَلْ أُوْلَئِكَ هُمُ الظَّالِمُونَ
50 – Shin raunin imani ne a cikin zukatansu ko kuwa suna tababa ne,ko kuma suna tsoro ne kada Allah da Manzonsa su zalunce su ne ? A'a wadannan su ne azzalumai.
A cikin shirin da ya gabata mun yi nuni da hadarin munaficci a tsakanin al'ummar musulmi to wadannan ayoyin ma na yin nuni da dalilan da masu imani suka kamu a cikin tarkon munafinci da cewa; a duk lokaci da wani sabani ya abku a tsakanin musulmi. Munafikai daga cikinsu duk da cewa alkalin maznon Rahama ne tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa idan hukumcin y aba su gaskiya sais u amince da hukuncin amma idan hukuncin da ma'aikin Allah ya fitar ya sabawa manufarsu sais u yi watsi da hukuncin duk da cewa sun sani manzon Allah (SWA) yana bayani ne kan hukuncin Allah. To a yau ma haka lamarin yake yawancin masu raya imani suna bin manufofi da anfanin kansu ne kawai. Duk wani abu da yayi daidai da amfaninsu shi ne gaskiya idan kuwa ya saba shi ne bata a mahangarsu bata ne . To wannan ya sabawa tushe na imani na hakika. Ci gaban wayoyin na nuni da tushen wannan mummunan lamari da cewa: wannan lamari ya samo asali ne daga jiji da kai da son kai da zucciya da ke sanya mutum idonsa ya rufe da kin fahimta da gane gaskiya hatta hukuncin Allah ya hanyar manzonsa bas u amincewa da shi bas u gani komi sai abin da yayi daidai da son rai da amfaninsu kuma komi suna dora shi kan wannan ma'auni ne.
A cikin wadannan ayoyin za mu ilmantu da abubuwa uku :
Na farko:alama ta imani na hakika it ace amincewa da hukuncin Allah da na manzonsa ko da kuwa ya sabawa tunani da son ranmu.
Na biyu: Hukunci na adalci bay a bin son rai da bukatar wani bangare ko gungu na mutane.
Na uku: Shakku da mummunan zato ga hukuncin Allah zalunci da tabewa ne duniya da lahira.
- MUSIC**************
Daga karshe za mu saurari karatun ayoyi na 51 da 52 a cikin suratul Nur:
إِنَّمَا كَانَ قَوْلَ الْمُؤْمِنِينَ إِذَا دُعُوا إِلَى اللَّهِ وَرَسُولِهِ لِيَحْكُمَ بَيْنَهُمْ أَن يَقُولُوا سَمِعْنَا وَأَطَعْنَا وَأُولَئِكَ هُمُ الْمُفْلِحُونَ
51 – Mumini ba su da wata Magana idan aka kira su zuwa ga llah da Manzonsa don yayi hukunci a tsakaninsu sai fadar: Mun ji kuma mun bi .adannan kuwa su ne masu babban rabo.
وَمَن يُطِعِ اللَّهَ وَرَسُولَهُ وَيَخْشَ اللَّهَ وَيَتَّقْهِ فَأُولَئِكَ هُمُ الْفَائِزُونَ
52 – Duk kuwa wanda ya bi Allah da Manzonsa kuma yake tsoron Allah kuma yake kiyaye dokokinsa.To wadannan su ne masu rabauta.
A cikin ayoyin da suka gabata suna bayani ne kan halayan wasu masu raya imani amma bas u yarda da hukuncin Allah da manzonsa da ganin hukuncin manzon rahama (SWA) ya sabawa gaskiya da tauye masu hakkinsu idan hukuncin ya sabawa abin da suke so.To wadannan ayoyi da muka saurara na bayani ne kan mumunai na hakika da cewa; mumunai na hakika hatta a maganganunsu sun yi imani da amincewa da hukuncin manzon Allah (SWA) haka a ayyukansu ma suna tabbatar da amincewarsu da hukuncinsa da yi masa da'a ma'ana bas u saba masa a baki ko a aikace. A fili yake masu irin wannan hali bayan takawa da Allah da tsoron abin da zai biyo bayan sabawa umarnin Allah suna fatar kuma isa ga kamala. Yin da'a ga Allah da bin hukuncin gaskiya na tafiya ne da tsoron Allah kuma idan mutum ya jurewa tsanani don tsoron Allah zai samu dacewa duniya da lahira. Kamar yadda ya zo a cikin ruwaya Imam Ali (AS) yana bin umarni da hukuncin Allah da manzonsa kuma shi ne yayi daidai da abin da wannan ayar ke Magana kansa .
A cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa uku :
Na farko:Isa ga matsayin bayun Allah na gari na bukatar mika kai baki daya ga hukuncin Allah da manzonsa kuma ta haka ne ake auna karfi ko raunin imanin mutum.
Na biyu: Ga mumuni lamari mai muhimmanci aiki da nauyin da ya rataya kansa ku amfaninsa ko zai cutar da shi ,umarnin Allah kawai yake kollo.
Na uku: bin Umarnin Allah na kai mutum ga sa'ada da matsayi mai girma.
Da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin na yau a madadin wadanda suka tallafawa har shirin ya kamala ni Tidjani malam lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa wassalam.
Suratun Nur Aya Ta 53-57 (Kashi Na 629)
Jama'a masu sauraro barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda, da a cikinsa muke kawo ayoyi da bayanai da suka kumsa, domin zame mana darasi a rayuwarmu ta yau da kullum da fatar Allah ya sa Kur'ani mai girma ya zama jagoranmu a rayuwarmu ta yau da kullum da kuma samin dacewa duniya da lahira amin. Kuma nine Tidjani Malam Lawali damagaram zan kasance tare da ku har zuwa karshen shirin nay au da tare da injiniya Aminu Ibrahim kiyawa.
- Music***********
To madallah za mu fara shirin na wannan mako ne da sauraren karatun ayoyi na 53 da 54 a cikin suratul Nur:
وَأَقْسَمُوا بِاللَّهِ جَهْدَ أَيْمَانِهِمْ لَئِنْ أَمَرْتَهُمْ لَيَخْرُجُنَّ قُل لّا تُقْسِمُوا طَاعَةٌ مَّعْرُوفَةٌ إِنَّ اللَّهَ خَبِيرٌ بِمَا تَعْمَلُونَ
53 – Suka kuma rantse da Allah ya iyawarsu cewa lallai idan ka umarce su da fita wallahi za su fita .Ka ce da su : Ku daina rantsw-rantse,biyayya ta gari it ace abin nufi.Hakika Allah Masanin abin da keke aikatawa ne.
قُلْ أَطِيعُوا اللَّهَ وَأَطِيعُوا الرَّسُولَ فَإِن تَوَلَّوْا فَإِنَّمَا عَلَيْهِ مَا حُمِّلَ وَعَلَيْكُم مَّا حُمِّلْتُمْ وَإِن تُطِيعُوهُ تَهْتَدُوا وَمَا عَلَى الرَّسُولِ إِلاَّ الْبَلاغُ الْمُبِينُ
54 – Ka ce da su : Ku bi Allah kuma ku bi Manzo,sannan idan kuka ba da baya, to hakika baa bin da yah au a kansa sai abin da aka dora masa,kuma baa bin da yah au a kanku sai abin da aka dora muku. Idan kuwa kuka bi shi kwa shiriya ,ba kuwa abin da yake kan Manzo sai isar da aike mabayyani.
Munafikai mutane masu raya imani a zahiri amma a badininsu bah aka ne ba .Ana gane su ta hanyar yawan yin rantsuwa a duk lokacin da suka fahimci al'ummar musulmi ta fahimci abin da suke boyewa a zucciyarsu na munafinci ta hanyar mummunar manufa da fakewa da abubuwa masu daraja suna rantsuwa da bayyana a shirye suke su bada dukiyarsu kan tafarkin Allah amma sais u yi kasa a guiwa wajen zartar a umarnin Allah da manzon Allah (SWA). Amma tarihi ya tabbatar wadanda suke rayawa da nuna zafin kai da tsanantawa a baki suna nuna kasawa wajen aikatawa kuma bas u jurewa wahala idan ta zo sabanin abin da suke rayawa. Allah madaukakin sarki ya bawa masu irin wannan hali amsa da cewa: ba dole ba ne su yi rantsuwa kawai ku tabbatar da abin da kuke rayawa a aikace da bin umarni da gaskata imanin da kuke rayawa.kuna zaton za ku yaudari mutane ta hanyar raya imani to ku sani Allah ya san abin da kuka boye a badini babu abin da yake boyuwa a gare shi. Ci gaban ayar ya jaddada cewa bin umarni Manzon allah ko bijirewa umarninsa akwai lada da cutarwa a gare mu ba manzon Allah ba. Idan a aikace muka yi biyayya ga manzon Allah zai shiryar da mu da yi mana jagora zuwa dacewa da shiriya duniya da lahira a rayuwarmu da kuma ba mu aminci daga tabewa.Amma idan muka bijirewa umarnin manzon Allah (SWA) ba za a tambaye shi domin ya isar da sakon Allah amma mu kuwa za a azabtar da mu saboda kin bin umarnin Allah da aiki da shi.
A cikin wadannan ayoyin za mu ilmantu da abubuwa uku:
Na farko:Kar rantse rantsen mayaudara ya yaudare mu domin wata alama ce ta munafikai ba mumune ba domin a aiki ne ake banbata mumuni da kafiri.
Na biyu: Manzon Allah aikinsa isar da sakon allah ba tilastawa mutane karbar sakon ba.
Na uku: yin biyayya ko bijirewa umarnin manzon allah tamkar yin biyayya ne ga hukumce –hukuncen Allah ne kuma wajibi ne kuma bijirewa umarnin Manzon Allah tamkar bijirewa hukuncin Allah ne.
Yanzu kuma za mu saurari karatun aya ta 55 a cikin suratul Nur:
وَعَدَ اللَّهُ الَّذِينَ آمَنُوا مِنكُمْ وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ لَيَسْتَخْلِفَنَّهُم فِي الأَرْضِ كَمَا اسْتَخْلَفَ الَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ وَلَيُمَكِّنَنَّ لَهُمْ دِينَهُمُ الَّذِي ارْتَضَى لَهُمْ وَلَيُبَدِّلَنَّهُم مِّن بَعْدِ خَوْفِهِمْ أَمْنًا يَعْبُدُونَنِي لا يُشْرِكُونَ بِي شَيْئًا وَمَن كَفَرَ بَعْدَ ذَلِكَ فَأُولَئِكَ هُمُ الْفَاسِقُونَ
55 – Allah kuwa Yayi wa wadanda suka ba da gaskiya daga cikinku suka kuma yi aiki na gari alkawarin lallai zai sanya su masu mayewa a bayan kasa kamar yadda Ya sanya wadanda suke gabaninsu masu mayewa,kuma lallai zai tabbatar musu da addininsu wanda Ya yadar musu amincewa bayan zamantowarsu cikin tsoro.To su bauta mini ,kar su yi shirka komai da Ni. Wanda kuwa ya kafirta bayan wannan ,to wadannan su ne fasikai.
Ayoyin da suka gabata na nuni da imani na hakika shi ne mika wuya dari bias dari ga umarnin Allah da manzonsa da yin biyayya .To wannan ayar na cewa; sakamakon yin biyayya ga umarnin Allah ba wai sai a lahira ba hatta a wannan duniya za mu ga sakamakon alheri a rayuwarmu ta daidaiku ko ta jama'a da kubutar da mu daga duk wani zalunci da tsoro da samin kwanciyar hankali da nucuwa ta hakika. Wannan wani alkawali ne da Allah yay i wa muminan bayunsa salihai.Alkawalin da ya tabbata a al'ummomin da suka gabata salihai. Kuma kafin wannan duk wata al'umma ma'abuciyar imani da aiki na gari Allah zai cika mata alkawalin da yayi mata da kare su da kudurarsa. Karkashin ruwayoyi wannan tana bayani ga daular imama Mahdi (AS) da zai bayyana a karshen zamani. Da fatar Allah ka sanya mu daga cikin bayunka salihai ma'abuta imani da bin umarninka da na manzonsa da kuma Imam Mahdi (AS).
A cikin wannan sura za mu ilmantu da abubuwa uku:
Na farko: Duk gwamnati da al';ummar da ta riki tafarkin manzon Allah da riko da gaskiya da aiki na gari Allah zai kare ta daga duk wani bala'I kuma Allah zai cika mata alkawarinsa.
Na biyu: addinin ba ya rabuwa da siyasa kuma hukuma da siyasa dole su kasance kan tafarkin gaskiya da kare addinin Allah ba yaudara ba.
Na uku: nasara ta karshe tana ga ma'abuta imani da tabbatar da hukumar adalci ta salihan bayun Allah da kawo karshen mulkin kafirai azzalumai wannan alkawari ne daga Allah sai ya tabbata.
- MUSIC***************
Daga karshe za mu saurari karatun ayoyi na 56 da 57 a cikin suratul Nur:
وَأَقِيمُوا الصَّلاةَ وَآتُوا الزَّكَاةَ وَأَطِيعُوا الرَّسُولَ لَعَلَّكُمْ تُرْحَمُونَ
56 – Kuma ku tsai da sallah ku kuma ba da zakka ku kuma bi Manzo don a ji kan ku.
لا تَحْسَبَنَّ الَّذِينَ كَفَرُوا مُعْجِزِينَ فِي الأَرْضِ وَمَأْوَاهُمُ النَّارُ وَلَبِئْسَ الْمَصِيرُ
57 – Kada kuma ku yi tsammanin wadanda suka kafirta za su gagara a bayan kasa ,kuma a makomarsu wuta ce ,makoma kuwa ta munana.
Wadannan ayoyi ci gaban ayoyin da suka gabata ne da ke jaddada yin biyayya da aiki da umarnin Allah da manzonsa (SWA) da cewa; mu karfafa dangantakarmu da Allah ta hanyar salla ,mu karfafa dangantakarmu da mutane ta hanyar fitar da zakka ga mabuka.Karfafa dangantakarmu da Allah ta hanyar bin umarnin Allah nauyi ne da ya rataya kan duk wani mumini na hakika. Abu ne a fili idan hakan sun tabbata lutihi da rahamar Allah da tabbatar da hukumar adalci ta shafi dukan muminai. Haka kuma abu a fili makiya kafirai da mushrikai suna iya kacin kokari da makircinsu na ganin Muminai ba su kai ga nasara ba don haka ci gaban ayar ke cewa: Allah ba zai bari makiya su kai ga cimma burinsu ba ,Allah zai cikawa bayunsa salihai alkawarin da yay i masu kuma nasara tana gare su ne.
A cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka:
Na farko:A mahangar muslunci lamura da suka shafi ibada ,tattalin arziki ,siyasa ,hukuma da zamanatakewa bas u rabuwa da juna.
Na biyu: Kafirai duk irin karfin da suke da shi ba za su iya hana yaduwa musulunci a duniya ba kuma musulunci ne zai mamaye duniyar nan da kafa adalci a doran kasa karkashin salihan bayun Allah.
Da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin na yau a madadin wadanda suka tallafawa har shirin ya kamala ni Tidjani malam lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa wassalam.
Suratun Nur Aya Ta 58-61 (Kashi Na 630)
Jama’a masu saurare Assalamu alikum, barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda, inda muke gabatar muku sharhin ayoyin alkur’ani mai tsarki, tare da fitar da darussan da suke koyar da mu, da fatan za a kasance tare da mu a cikin shirin na yau.
……………………………………..
To har yanzu dai muna cikin surat Nur, sai a saurari karatun ayoyi na 58 da kuma 59:
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لِيَسْتَأْذِنكُمُ الَّذِينَ مَلَكَتْ أَيْمَانُكُمْ وَالَّذِينَ لَمْ يَبْلُغُوا الْحُلُمَ مِنكُمْ ثَلاثَ مَرَّاتٍ مِن قَبْلِ صَلاةِ الْفَجْرِ وَحِينَ تَضَعُونَ ثِيَابَكُم مِّنَ الظَّهِيرَةِ وَمِن بَعْدِ صَلاةِ الْعِشَاء ثَلاثُ عَوْرَاتٍ لَّكُمْ لَيْسَ عَلَيْكُمْ وَلا عَلَيْهِمْ جُنَاحٌ بَعْدَهُنَّ طَوَّافُونَ عَلَيْكُم بَعْضُكُمْ عَلَى بَعْضٍ كَذَلِكَ يُبَيِّنُ اللَّهُ لَكُمُ الآيَاتِ وَاللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٌ
58: Ya ku wadanda kuka ba da gaskiya ,lallai ne wdanda hannayenku suka mallaka da kuma wadanda ba su isa mafarki ba a cikinku wato wadanda bas u balaga ba,su nemi izininku sau uku: kafin sallar asuba,da sanda kuke tube tufafinku a lokacin garjin rana,da kuma bayan sallar lisha. Lokatai ne guda uku tsiraicinku. Babu laifi a kanku ko a kansu bayansu wadannan lokatan .Masu shige da fice ne a gare ku sashinku bisa sashi. Kamar haka Allah Yake bayyana muku ayoyi . Allah kuma Masani ne gwani.
وَإِذَا بَلَغَ الأَطْفَالُ مِنكُمُ الْحُلُمَ فَلْيَسْتَأْذِنُوا كَمَا اسْتَأْذَنَ الَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ كَذَلِكَ يُبَيِّنُ اللَّهُ لَكُمْ آيَاتِهِ وَاللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٌ
59: Idan kuma yara daga cikinku suka isa mafarki wato suka balaga ,sais u nemi izini kamar yadda wadanda suke gabaninsu suka rika neman izini.Kamar haka Allah yake bayyana muku ayoyinsa.Allah kuwa Masani ne Gwani.
Wadannan ayoyi masu albarka suna yin ishara ne da matsayin dangantaka tsakanin iyali, da kuma lamurran da ya kamata a kiyaye domin kada a shiga cikin hakkin mahaifa, manya da kuma yara daga cikin ‘ya’ya da kuma wadanda suke karkashin kulawar ma’aurata, wajibi ne koyar da su tarbiya da za ta dace da dabi’un musulunci na zamantakewa, da hakan ya hada sanin lokutan hutwar mahaifa, kuma dole su nemi izini kafin shiga wajen mahaifansu, hatta kananan yara da suke tare da mahaifansu a kowane lokaci, dole a koyar da su hakan, su san cewa a lokutan da hakkin mahaifansu ne kawai.
Darussan da za a koya daga wadannan ayoyi nsu ne:
1 – Aalaka tsakanin ma’auarata tana da ladubba da ya kamata a kiyaye tsakanin ma’auratan da kuma ‘ya’yansu har da wadanda suke karkashin kulawarsu.
2 – Dole ne a koyar da yara ladubban zamantakewa.
3 – Dole ne mutum ya kiyaye lokutan iyalansa tare da basu hakkokinsu.
Yanzu kuma sai a saurari karatun aya ta 60 a cikin surat Nur:
وَالْقَوَاعِدُ مِنَ النِّسَاء الَّلاتِي لا يَرْجُونَ نِكَاحًا فَلَيْسَ عَلَيْهِنَّ جُنَاحٌ أَن يَضَعْنَ ثِيَابَهُنَّ غَيْرَ مُتَبَرِّجَاتٍ بِزِينَةٍ وَأَن يَسْتَعْفِفْنَ خَيْرٌ لَّهُنَّ وَاللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ
60: Tsofaffin mata kuwa wadanda bas a tsammanin yin aure to babu laifi a kansu su dan saukaka lullubinsu,amma ba masu fitar da adonsu ba,amma kuma su yi lullubi shi ya fi zama alheri a gare su. Allah kuwa Mai jin ne Masani.
Wannan aya mai albarka tana yin nuni ne da matsayin hijabi a cikin addinin muslunci, amma kuma tana nuna irin saukin da addini ya yi ga mata wadanda suka tsufa, da cewa babu laifi a kansu idan suka ajiye hijabinsu suka zauna a cikin tufafin da ke jikinsu kawai, koda kuwa suna cikin wadanda ba muharramansu ba, amma bisa sharadin cewa ba za su yi wani abu na nuna kwalliya da kawa ba.
Darussan da za mu koya a cikin wadannan ayoyi su ne:
1 – A kowane lokaci dokokin addinin muslunci sukan kiyaye yanayi da kuma yadda za a iya aiwatar da su a cikin yanayin, saboda hakan a wasu lokuta dokokin sukan canja bisa wasu dalilai a wasu wurare, kamar yadda saka hijabi yake wajib ga dukkanin mata a cikin addini, amma kuma ga mata tsoffi ba wajibi ba ne bisa sharuddan da aka ambata.
2 – Bai halasta ga mata su yi kwalliya da nuna kawa a cikin mutanen wadanda ba muharramansu ba.
Yanzu kuma sai a saurari karatun aya ta 61 a cikin surat Nur:
لَيْسَ عَلَى الأَعْمَى حَرَجٌ وَلا عَلَى الأَعْرَجِ حَرَجٌ وَلا عَلَى الْمَرِيضِ حَرَجٌ وَلا عَلَى أَنفُسِكُمْ أَن تَأْكُلُوا مِن بُيُوتِكُمْ أَوْ بُيُوتِ آبَائِكُمْ أَوْ بُيُوتِ أُمَّهَاتِكُمْ أَوْ بُيُوتِ إِخْوَانِكُمْ أَوْ بُيُوتِ أَخَوَاتِكُمْ أَوْ بُيُوتِ أَعْمَامِكُمْ أَوْ بُيُوتِ عَمَّاتِكُمْ أَوْ بُيُوتِ أَخْوَالِكُمْ أَوْ بُيُوتِ خَالاتِكُمْ أَوْ مَا مَلَكْتُم مَّفَاتِحَهُ أَوْ صَدِيقِكُمْ لَيْسَ عَلَيْكُمْ جُنَاحٌ أَن تَأْكُلُوا جَمِيعًا أَوْ أَشْتَاتًا فَإِذَا دَخَلْتُم بُيُوتًا فَسَلِّمُوا عَلَى أَنفُسِكُمْ تَحِيَّةً مِّنْ عِندِ اللَّهِ مُبَارَكَةً طَيِّبَةً كَذَلِكَ يُبَيِّنُ اللَّهُ لَكُمُ الآيَاتِ لَعَلَّكُمْ تَعْقِلُون
61 : Bãbu laifi a kan makãho, kuma bãbu laifi a kan gurgu, kuma bãbu laifi a kan majiyyaci, kuma bãbu laifi a kan kõwanenku, ga ku ci (abinci) daga gidãjenku, kõ daga gidãjen ubanninku, kõ daga gidãjen uwãyenku, kõ daga gidãjen 'yan'uwanku mazã, kõ daga gidãjen 'yan'uwanku mãtã, kõ daga gidãjen baffanninku, kõ daga gidãjen gwaggwanninku, kõ daga gidãjen kãwunnanku, kõ daga gidãjen innõninku kõ abin da kuka mallaki mabũɗansa kõ abõkinku bãbu laifi a gare ku ku ci gabã ɗaya, kõ dabam- dabam. To, idan kun shiga wasu gidãje, ku yi sallama a kan kãwunanku, gaisuwã ta daga wurin Allah mai albarka, mai dãɗi. Kamar wancan ne Allah Yake bayyana muku ãyõyinSa, tsammãninku ku yi hankali.
Wannan aya mai albarka tana yin bayani ne dangane da irin sauki da addinin muslunci yakan yi a cikin dokokinsa kamar dai yadda ayar da ta gabata ta yi nuni a wani bagiran, haka ita wannan aya mai albarka tana nuna sauki da addini ya yi ga wasu mutane masu fama da wata matsala ta musamman, kamar makafi da guragu da ma marassa lafiya, wadanda ba za su iya aiwatar da wasu ayyuka na wajibi ba saboda yanayin da suke ciki, sai aka yi musu sauki, kamar jihadi ko tafiya aikin hajji da sauran makamntan hakan. Haka nan kuma wannan aya ta tabo irin halascin da ke tattare da cin abinci a gidajen dangi wadanda aka ambata a jere a cikin wanann aya, da kuma gidan aboki, da wadanda suke karkashin kulawar mutum, haka nan kuma ta bayyana matsayin sallama ga juna da alkhairi gami da albarkar da ke tattare da hakan a cikin rayuwar zamantakewar jama’a.
Darussan da za a iya koyo daga wannan aya mai albarka su ne:
1 – Hukumomin muslunci dole ne su samar da wani shiri na kula da masu fama da matsaloli na musamman, tare da dauke musu nauyi kan wasu lamurra saboda halin da suke ciki, kamar yadda addinin muslunci ya dauke musu musu wasu daga cikin ayyukan na wajibi da ba za su iya ba.
2 – Dangi suna da hakkoki na musamman a tsakanin junansu da ya kamata su kiyaye.
3 – A cikin addinin muslunci abokai suna da matsayi wanda har aka kwatanta shi da dangataka ta jinni.
4 – Yin sallama ga juna yana kawo alkhairi da albarka a cikin jama’a.
Da wannan muka kawo karshen shirin, sai Allah ya hada mu a saduwa ta gaba wassalamu alikum wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Suratun Nur Aya Ta 62-64 (Kashi Na 631)
Jama’a masu saurare Assalamu alikum, barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda, inda muke gabatar muku sharhin ayoyin alkur’ani mai tsarki, tare da fitar da darussan da suke koyar da mu, da fatan za a kasance tare da mu a cikin shirin na yau.
……………………………………..
To har yanzu dai muna cikin surat Nur, sai a saurari karatun aya ta 62 a cikin wannan sura.
إِنَّمَا الْمُؤْمِنُونَ الَّذِينَ آمَنُوا بِاللَّهِ وَرَسُولِهِ وَإِذَا كَانُوا مَعَهُ عَلَى أَمْرٍ جَامِعٍ لَمْ يَذْهَبُوا حَتَّى يَسْتَأْذِنُوهُ إِنَّ الَّذِينَ يَسْتَأْذِنُونَكَ أُوْلَئِكَ الَّذِينَ يُؤْمِنُونَ بِاللَّهِ وَرَسُولِهِ فَإِذَا اسْتَأْذَنُوكَ لِبَعْضِ شَأْنِهِمْ فَأْذَن لِّمَن شِئْتَ مِنْهُمْ وَاسْتَغْفِرْ لَهُمُ اللَّهَ إِنَّ اللَّهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ
62: Waɗanda ke mũminai sõsai, su ne waɗanda suka yi ĩmãni da Allah da ManzonSa, kuma idan sun kasance tãre da shi, a kan wani al'amari na aikin gayya, bã su tafiya sai sun nẽme shi izni. Lalle ne, waɗanda suke biɗar ka izni waɗancan sũ ne suke yin ĩmãni da Allah da ManzonSa. To, idan sun nẽme ka izni sabõda wani sha'aninsu, to, ka yi izni ga wanda ka so daga gare su, kuma ka nẽmã musu gãfara daga Allah. Lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai .
Ayoyin da suka gabata a cikin wannan sura sun yi nuni da yadda ya kamata musulmi su kasance a cikin harkokinsu na zamantakewa daidai da koyarwa irin ta addinin musulunci, haka nan ita ma wannan aya mai albarka tana yin nuni ne da cewa, yin biyayya ga manzon Allah shi ne hakikanin yin biyayya ga Allah madaukakin sarki, haka nan kuma saba masa shi ne saba ma umarnin Allah, daga cikin ayyuka na biyayya ga manzon Allah kuwa har da neman izini daga gare shi kafin barin wurinsa a lokacin da ake cikin wani lamari na al’umma, ta yadda Allah ya bayyana masu neman izininsa domin tafiya wajen lamurransu a matsayin cewa su ne masu imani na hakika da Allah da manzonsa. Hakika wannan yana yin nuni ne da matsayin shugabanci a cikin musulmi, dole ne musulmi su zama masu tsari da bin shugabanci guda karkashin koyarwa ta addini.
Malaman tafsiri da dama sun sun kawo bayani kan dalilin safkar wannan aya da cewa, daya daga cikin sahabban manzon Allah (SAW) wato Hanzalah, ya nemi izini daga manzon Allah a lokacin da ake shirin tafiya yakin Uhudu, kan cewa a ba shi dama ya yi jinkiri, domin a daren ne matarsa za ta tare, kuma ya yi alkawarin yin sammako domin hadewa da rundunar musulmi a kan hanyarsu ta zuwa Uhudu, sai manzon Allah ya ba shi iznin hakan, rundunar musulmi ta fita zuwa Uhudu da dare, shi kuma ya bi su ta asubahi kuma ya riske su amma ba tare da ya yi wankan janaba ba, kuma a lokacin yakin ya yi shahada, sai manzon Allah ya ce mala’iku sun yi masa wanka kuma sun tafi da shi aljanna.
Darussan da za a dauka daga ayar su ne:
1 – Kiyaye tsari a cikin lamarin al’umma wajibi ne.
2 – Yin sahawara kafin kafin daukar matsaya kan wani lamari mai muhimmanci.
3 – Dole ne al’ummar musulmi ta zama mai biyayya ga shugaba na musulunci.
4 – Dole ne shugabannin musulmi su zama masu kaifin hankali tare da sanin yadda za su tafiyar da mutane, su zama masu taushin hali da bayar da uzuri.
Yanzu kuma sai a saurari karatun ayoyi na 63 da kuma 64 a cikin wannan sura ta Nur:
لا تَجْعَلُوا دُعَاء الرَّسُولِ بَيْنَكُمْ كَدُعَاء بَعْضِكُم بَعْضًا قَدْ يَعْلَمُ اللَّهُ الَّذِينَ يَتَسَلَّلُونَ مِنكُمْ لِوَاذًا فَلْيَحْذَرِ الَّذِينَ يُخَالِفُونَ عَنْ أَمْرِهِ أَن تُصِيبَهُمْ فِتْنَةٌ أَوْ يُصِيبَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ
63: Kada ku sanya kiran Manzo a tsakãninku kamar kiran sãshenku ga sãshe. Lalle ne Allah Yanã sanin waɗanda ke sancẽwa daga cikinku da saɗãɗe. To, waɗanda suke sãɓãwa daga umurninSa, su yi saunar wata fitina ta sãme su, kõ kuwa wata azãba mai raɗãɗi ta sãme su.
أَلا إِنَّ لِلَّهِ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ قَدْ يَعْلَمُ مَا أَنتُمْ عَلَيْهِ وَيَوْمَ يُرْجَعُونَ إِلَيْهِ فَيُنَبِّئُهُم بِمَا عَمِلُوا وَاللَّهُ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمٌ
64: To! Lalle Allah ne Yake da mulkin abin da ke a cikin sammai da ƙasa, haƙĩƙa, Yanã sanin abin da kuke a kansa kuma a rãnar da ake mayar da su zuwa gare shi, sai Yanã bã su lãbãri game da abin da suka aikata. Kuma Allah, ga dukkan kõme, Masani ne.
Wadannan ayoyi suna yin nuni da ci gaban bayanin ayar da ta gabata, wadda kan wajabcin daukar lamarin manzon Allah a gaba fiye da komai, domin kuwa lamarin mamnzon Allah lamarin Allah, saba masa kuma sabon Allah kai tsaye, wanda hakan ke jefa ma’abocin wanann aiki cikin azabar Allah mai radadi a ranar kiyama, a kan haka Allah yake jan hankalin masu aikata haka da su shiga taitayinsu, domin kuwa Allah madaukakin sarki shi ne masani a kan komai da ke cikin sammai da kassai, shi ne masanin kowa da kuma ayyukansa, a ranar da dukkanin talaikai za su koma gare shi, a ranar Allah zai sanar da su abin da suka aikata dalla-dalla.
Daga wadannan ayoyi za mu iyakoyon darussa kamar haka:
1 – Manzon Allah (SAW) mutum ne mai tsarki da kuma matsayi na musamman a wajen Allah, kiyaye matsayinsa da martabarsa wajibi ne a cikin addinin muslunci, dole ne musulmi ya kira sunan manzon Allah a cikin girmamawa, kamar yadda ya zama wajibi ga musulmi su zama masu yin koyi da shi da bin umarninsa. Haka kuma lamarin yake ga wasiyyansa.
2 – Saba ma umarnin Allah ko na manznsa, yana jaza matsaloli na duniya da lahira.
3 – Yin imani da cewa Allah madaukakin sarki masani ne kan dukkanin ayyukan da mutum yake aikatawa, kuma a gobe kiyama kowa zai ga sakamakon abin da ya aikata.
Da wannan muka kawo karshen shirin, sai Allah ya hada mu a saduwa ta gaba wassalamu alikum wa rahmatullahi wa barakatuhu.