Overview
- CONTENT SOURCE: Reporter (Ibrahim Ka-Almasih Garba); Maryam Abubakar Adamu, leader of an NGO and a freelance journal (2007 January 4). Vox Populi. Washington D.C.: Voice of America, Hausa Service.
- Objective: Demonstrate your core comprehension.
- Lesson Title: Vox Populi - This report from Voice of America Radio discusses the reaction of Nigerians to a conflict between their president and vice president.
- Language: Hausa
- Topic: Culture/Society
- ILR Level: 2+/3
- ACTFL Proficiency: Superior, Advanced-High; This ACTFL rating is an approximation based on the ILR level
- Modality: Listening
- Learning Objective: Maintenance & Improvement
- Subject Area: Language
- Material Type: LO
- Publication Year: 2007
- ObjectID: HAUS_11909
Transcript
Original | Translation |
---|---|
Vox Populi A: Ga wasu ‘yan Nijeriya, shekara da ta gabata ta kasance shekara ce ta takaici da shuwagabannin ƙasan nan suka kau da hankalinsu daga ayyukan da aka zabe su su yi, watau shugabanci na gari na samar da ingantaccen yanayin tsaro da ruwan sha da wutar lantarki da dai sauransu. A maimakon haka, a ganin irin wadannan ‘yan Nijeriya, shuwagabannin sun himmantu ne da yin faɗa da juna da kwancewa juna zani a kasuwa da yin zagon kasa wa juna da yin Bita da kulli wa juna da shimfiɗa gadar zare wa juna da ƙage wa juna da dai sauran nau’oi na sharri. Hasali ma dimokaraɗiyyar ta rikiɗ e ta zama makaraɗ iyya, ta yadda ‘yan fashi da makami da ‘yan fashi da muƙ ami, suka sa talakan Nijeriya a tsakiya, suna ta gallaza mar. Don haka ne ma, irin wadannan 'yan Nijeriyan da abun ya damesu , suka shiga bayyana fargabarsu. Da kuma kiraye-kiyaren da suke wa manyan ‘yan siyasa, musamman ma shugaban kasa da mataimakinsa, da su yi sulhu ganin yadda irin wannan rishin jituwa tasu ke barazana ga ƙasar baki daya. Daga cikin masu irin wannan damuwar, akwai Hajiya Maryam Abubakar Adamu, shugabar wata kungiya mai zaman kanta ta inganta rayuwar jama’a, MERO a taƙ aice, wadda ta ce: B: Ina kokanton yanayin yiwuwar al'amura su…. dawo su kasance daidai. Kaga na farko dai, {last quarter[English]} na tafiya, sai ƙ ananan abubuwa na mulki, sai ya zo ya shiga To, abunda nake gani shine, tun da shi shugaban ƙ asa kaman shi ne kome da kome ya ɗ oru akan shi: da jakunan da suke ƙasan nan, da kiyashen da suke ƙasan nan, da mutanen da suke ƙasan nan, da Hausawan da suke ƙasan nan, da Filanin da suke ƙasan nan, kowa da kowa, muna hannun Allah ne, muna hannun shi, shi a matsayin shi na..na.. shugaban ƙasa. Aka ce babba juji ne, me zai sa ba zai rungumi wannan girman ba? Ya ɗauki girmanshi ya kwada da ƙasa. Abin da nake nufi, Mallam Ibrahim, da cewar ya ɗauki girmanshi ya kwaɗ a da kasa: bawan Allan nan, suna tare. A: To, shi shugaban ƙasa yana zargin cewar mataimakensa ba ya mai biyayya. B: To, rashin biyayya, wani lokaci tirsasawan na sama ne. Idan na sama ya tirsasa ya kai gaci dukkammu nan fa, ’yan Adam ne. Idan ya kasance shugaba yana so yai amfani da kowane irin ƙarfi da yake da shi. Idan ni, ina mabiya, idan naga wannan biyayya ba zai fitad da ni ba, zan iya ƙi. Maiyuwa abin da yake faruwa tsakaninsu da mataimakin shugaban ƙasa ke nan? A cikin wannan jami'yya, sun yi {suspending [English] } ɗinshi, sun yi wannan, sun yi wannan. To, Mallam Ibrahim, mutum ko gidan babanshi ne, Idan aka ce, uba ya ce, da ya fita ya bar mishi gida. Idan kuma, ɗannan na da gaskiya, zai iya fita yaje, gidan ƙanan babanshi. A: To, yanzu, ina mafita? B: Mafita, shi ne … kana ji, ko? A: Mmm … B: … Mu fa, a bar mu muji da abin da yake damun mu na.. yanayin ma tukuna sa tuwo a baki, ya zo ya zama damuwa. Balantana idan kana da ‘ya’ya yau biyar. Malam Ibrahim, ba za ka dauki ɗaya! Daya cikin ƙwanciyan hankali ka kaishi yayi makaranta daga {nursery [English]} nan ko {primary [English]}, har zuwa, ah {university level [English]}, sai ka nemi tallafi ko wajen wannan ko zuwa wajen wancan,to, su bar mu muji da wannan, su sasanta. A: Hajiya Maryam Abubukar Adamu ke nan, shugabar ƙungiyar kyautatta rayayuwar al’umma MERO a taƙaice, mai {headquarter [English]} a garin Kaduna. Shi kuwa, Alhaji Tajuddin Tijjani, wani ɗan jarida mai zaman kansa, cewar ya yi: C: Wannan rikici na tsakanin shugaban ƙasa da mataimakenshi … bai dace ba. Abun ba zai … zai kawo cigaba bane a ƙasan nan. Saboda … in ka ga irin wannan mutane guda biyu ɗin, suna faɗa, suna jaki injaka, jama'a zasu sa wuya. Kuma kowa ya gani abun yake faru yanzu. Abun nikeso in gaya ma shi turaki Adamawa. In kana tare da mutum shekara takwas, ya kamata ka san irin ali wannan mutum din. To, kuma baba, ya kamata ya san irin hali wanda yaro nashi yake. To, in ka lura, in kana so wani abu a hannun wani, in ya fika, Allah yasa ya fika. Ka bi shi da hankali, ka samu abun kake nema, ka biya bukata. Kai nai yau, ba kai ne gobe ba. Obasanjo ne yau, zai bari. A ce -- A: To, to … to, kana ganin koran da yace ya kori mataimakinsa, kuma ya ce ba zai yafe mashi ba, kana ganin bai laifi ba, shi shugaban kasa? Yana da iko ya kore shi? C: Ah … doka na kasar nan, bai ce kome ba akan wannan … ina kora-kora din. Abun … ah … {Constitution [English]} namu ya ce, shine wanda suke majalisa. In suka beri aiki nasu, suka beri {party [English]} wanda ya kaisu wannan kujeru, in zasu beri, su beri wannan {party [English]} din wanda ya kaisu wurin. Amma {Constitution [English]}, wanda suka yi {Constitution [English]} din suka yi kuskure. Ba’a a yi magana ba akan me ne zai faru in {President [English]} ne ya beri {party [English]} nashi, ya shiga wani {party [English]}, ko {Vice President [English]} ya bari, ya shiga wani {party [English]} nashi. A: To, me ce ce shawararka gare su dukansu biyu? B: To, ni dai a ganina, ina so ne su sa santa, saboda Obasanjo uba ne a wajen Atiku. A: Alhaji Tajuddin Tijjani ke nan, wani ɗan jarida mai zaman kansa. Ibrahim Ka’alamasi Garba, Murya Amurka, daga Kaduna a Nijeriya. |
Vox populi A: To some Nigerians, the past year has been a year of frustration, when the leaders of this country turned their attention away from the activities that they were elected to undertake, that is to provide security, drinking water and electricity and other things. Instead of this, in the eyes of these Nigerians, the leaders strove to attack each other, undo each other’s plans, sabotage each other, fight and argue with each other, spread accusations against each other, and other types of wickedness. In fact, the democracy has transformed and become a “dally-ocracy,” in which highway robbers and political bandits put the common Nigerian in the middle and kept forcing themselves on him. As such, Nigerians who have worried about this have started appearing fearful. And they made complaints to the major politicians, especially the President and Vice-President, and they sought reconciliation by seeing how this disagreement of theirs was threatening the entire country. Among those worried is Hajiya Maryam Abubakar Adamu, the head of an independent organization for improving the public life, abbreviated as MERO, who says: B: I doubt that it is possible for matters to … return to normal. You see, first of all, the last quarter went by, then matters of government came and started up. So what I see is this: since the President is the way he is, everything is dependent on him: this country’s donkeys, this country’s ants, this country’s people, this country’s Hausas, this country’s Fulani, all of them, we are in God’s hands, we are in his hands, as one who’s in the position of President. We consider him the great judge, so why is it that he will not embrace this greatness? He takes his greatness for granted. What I mean to say, Mallam Ibrahim, is he takes up his greatness for the abundance of the country: and he has been with this servant of God for a while. A: But, the President is accusing his Vice-President of disloyalty. B: Yes, disloyalty, sometimes the humiliation is at the top. If the one at the top humiliates, he causes the problem for all of us. If he is a leader, he wants to use every power that he has. If I am loyal, if I see this loyalty will not benefit me, I can refuse. What can possibly happen between them and the Vice-President? In this party, they suspended him, they did such-and-such. So, Mallam Ibrahim, a person in his father’s house, if the father tells him to leave the house, when he goes away he leaves the house to him. But if he’s a real son, he will be able to go out and arrive at his uncle’s house. A: So, now, what’s the way out? B: The way out is this … are you listening? A: Mmm … B: … We here, we should be left to understand what is worrying us about … the conditions, first of all, of feeding ourselves, it comes and becomes worrying. It’s a disaster if you have five children these days. Mallam Ibrahim, you can’t even raise one! One in easy circumstance, you can bring him up in his education from this nursery or primary, all the way to, ah, university level, without looking for support from this place or that place, and they leave us to worry about such things. A: That was Hajiya Maryam Abubakar Adamu, head of an independent organization for improving lives in the community, known by the initials MERO, with headquarters in Kaduna. Another one, Alhaji Tajuddin Tijjani, an independent journalist, had this to say: C: This dispute between the President and Vice-President … it’s not right. Nothing will … it will not bring progress to this country. Because … if you see these two people fighting like donkeys, the public will suffer difficulty. And everyone sees what is going on now. Here’s what I’d like to say to the Turaki of Adamawa: If you’ve been together with someone for eight years, you must be familiar with this person’s character. And sir, he must be familiar with the kind of character his son has. So, if you pay attention, if you want something that’s beyond your reach, God makes it beyond your reach. You should follow him slowly to get what you’re looking for and fulfill your needs. If you are today, you are not tomorrow. Obasanjo is today, he will leave. One says -- A: OK, OK … OK, do you see this removal, that he said he removed his Vice-President, and he said he would not forgive him. Do you think he’s not at fault, the President? Does he have the authority to remove him? C: Ah … the law of this country doesn’t say anything about this … removal. What … ah … our Constitution says, refers to the legislature. When they resign from their party, they resign from their office; if they resign, they must resign from the party that put them there. But the Constitution, when they made the Constitution, they made a mistake. It doesn’t mention what would happen if the President resigns from his party to join another party, or if the Vice-President resigns to join another party. A: So, what’s your advice to these two? B: Well, as I see it, I want them to make peace, because Obasanjo is the father in relation to Atiku. A: That was Alhaji Tajuddin Tijjani, an independent journalist. Ibrahim Ka’alamasi Garba, Voice of America, from Kaduna, Nigeria. |
Glossary
Hausa | Hausa Meaning | English Meaning |
---|---|---|
Kwancewa juna zani a kasuwa | Wannan karin magana na hausa na nufin tona ma juna asiri. | This Hausa proverb means revealing each other's secrets |
Yin bita da ƙuli | Wannan na nufin kai hari. | Damaging attack |
shinfiɗa gadar zare | Wannan karin magana ne mai nufin yin tarko. | This is a proverb that means setting a trap |
ƙage wa juna | Yi ma juna sharhin da ba daidai ba. | False allegations |
Mai zaman kansa | Wanda bai buƙata taimako. | One who is independent |
Babba juji ne | Babba ne mai ɗaukar nauyi da laifufuka. | A leader takes all the responsibility and blame for a situation |
Ƙwaɗa ga ƙasa | Bai ba kanshi daraja ba. | Did not show his integrity |
Notes
Hausa Notes | English Notes |
---|---|
Dangantaka dake tsakanin Obasanjo da Atiku ta ɓace ne lokacin da Obasanjo ya nemi gyara tsarin mulkin Nijeriya don ya ƙara lakocin shi na shugabancin ƙasa, sai bai ci nasara. Kafin wannan sun yi aikin bautar ƙasa tare amma ba cikin suna so ba. Kishi da ƙiyayya kuma ta shiga tsakanin shugabanin biyu tun lokacin da majalisa ƙasa ta ƙi yarda da shirin doka na maimaitawa shugabanci na uku da Obasanjo ya so yi. Obasanjo bai taɓa ɓoyewa ba cewa bai son Atiku ya shugabanci Nijeriya bayan shi. Kwana nan ma ya fito fili ya faɗa cewa sai dai a bayan ranshi Atiku zai iya zama shugaban ƙasa mai zuwa. Lokaci kaɗan bayan fitowar sunayen masu takarar shugaban ƙasa na Aprilu da hukuma zaɓe ta bayar kuma bata sa sunan Atiku ciki ba, Obasanjo ya yabi hukumar da cewa sun kyauta da suka hana mazambata da ke son komawa mulki don su ɓanatar da arzikin ƙasa ba cikin ka'ida ba. Ɓaraka da ke tsakanin su ta kara lalacewa lokacin da Atiku ya bar jam'iyyashi ta PDP ya koma jam'iyya ƴan adawa inda yake dan takara shugaban ƙasa. Wata Babbar hukuma ƙasa mai zargin masu cin arzikin ƙasa da aka kafa mai suna EFCC ta zarge shi da karɓar rashawa. Hukumar ta zarge shi da laifin amfani da asusun jama'a ƙasa yana juyawa zuwa milliyoyin dalar don yin harakokin shi. Amma mataimakin shugaban ƙasa ya yi musun wannan zargi. |
The relationship between Obasanjo and Atiku went sour after the former's bid to prolong his tenure through constitutional amendment failed. They had managed to work together before then, albeit grudgingly. However, since the tenure elongation bill -- popularly known as the "the third-term project" -- was rejected and discountenanced by the country's legislature in May 2006, there has been a bitter rivalry between the two leaders. President Obasanjo has never hidden the fact that he does not want Atiku to succeed him. He recently made that plain when he stated that Atiku would succeed him "over his dead body." A few hours after last Thursday's release of the list of candidates for the April presidential polls by Nigeria's electoral commission, which clearly omitted Atiku's name, Obasanjo issued a statement praising the commission for stopping the "bad eggs and corrupt elements" that want to "resume the unbridled looting of our national wealth." The rift between the two worsened in late 2006 when Atiku decamped from the ruling People's Democratic Party (PDP) to join the opposition. He is currently the presidential candidate of the Action Congress and has since being facing allegations of corruption by the Economic and Financial Crimes Commission (EFCC), the country's leading anti-graft body. A report by the commission accuses Atiku of diverting public funds running into several millions of dollars for private business. The embattled vice-president has since denied the allegation. |
XML
<activity>
<problemset>
<problem correctindex="2">
<choices>
<opt>
<response>Cikin wannan rahoto na Ibrahim Ka'almasi Garba daga Muryar Amurka, wajan ƙarshen kwata na shekara dubu biyu da shida 'yan Nijeriya sun fuskanci wanin halin takaici.Shugabannin Nijeriya sun zaɓi kauce ma ayyukansu na bauta ma ƙasa ta wajen faɗace-faɗace tsakankannin su gaban jama'a da wulaƙantar da tallakawa. Shugaban ƙasa da mataimakinshi suna yaƙi da juna kuma yawancin ƴan Nijeriya sun ba shugaban ƙasa laifi da cewa bai da kamun kai da girmama mataimakin shi. Wasu sun ba tsarin mulkin Nijeriya laifin cewa babu rubutatta ƙa'ida ko manufa bisan abun da zai faru idan shugaban ƙasa ya yi anfani da ikon shi wajen huƙunta ma mataimakinshi. Wasu ƴan Nijeriya kuma suka ce ya kamata mataimakin shugaban ƙasa ya iyya gane shugabansa bayan shekara takwas suna aiki tare, ya bi dukan ƙa'idodin shugaban don a ceci jama'a kuma a guje ma faɗace-faɗace gaban su.</response>
<fdbk>A'a! wannan amsa ba daidai ba ce saboda rahoton bai yi bayyani ba bisa mataimakin shugaba ya bi ƙa'idodin shugaban ƙasa ba. Ƙara sauraren rahoton kuma ku yi lura da bayyanin masu magana bisa rigima da ke tsakanin shugabannin biyu.</fdbk>
<eng-fdbk>Incorrect! This is not the right answer because the report did not talk about the vice president following the president's instructions. Listen to the report again and pay attention to the speakers' comments on the conflict between the two leaders.</eng-fdbk>
<eng-response>According to this report by Ibrahim Ka'almasi Garba of Voice of America, Nigerians have experienced an unusual situation in the last quarter of 2006. Nigerian leaders chose to go against their duty to serve the country by fighting with each other in public places and humiliating the poor. The president and the vice president were also against each other, and most Nigerians blamed the president for being irresponsible and disrespectful towards his vice president. Some pointed fingers at the Nigerian constitution which has no written policy on a situation where the president uses his power against his vice president. Other Nigerians also believe that, after eight years of service together, the vice president should have known the president better and followed all of his instructions to avoid public disputes, thus sparing the population.</eng-response>
</opt>
<opt>
<response>Ana zaton shekara ta dubu biyu da shida ce shekara mai ban kunya cikin tarihin Nijeriya saboda rikice-rikicen da suka faru tsakankanin shugabanan Nijeriya. Ƴan siyasa sun sa talakawa tsaka suna yi ma junansu ƙaƙe da sharhi gaban jama'a. Maryam Adamu na ɗaya daga cikin ƴan ƙasa da suka bayyana ƙyamar su cikin rahoton Ibrahim Ka'almasi Garba. Ta roƙi kanun faɗan watau shugaban ƙasa da mataimakinshi da su sasanta don rayuwar jama'a ta bunƙasa da abinci da kuma tsayayyen albashin da zai tamaka ma yaransu su je makaranta boko. Ƴan Nijeriya sun bayyana ma ɗan jarida wajen ganawasu cewa mafita ɗaya ita ce shugaban ƙasa ya mutunta waɗanda ke ƙasa gareshi don su yi aiki tare.</response>
<fdbk>A'a! wannan ba daidai ba ne saboda rahoton bai yi bayyani ba akan bunƙasa rayuwar ƴen Nigeria.Yi tunani bisa amsa da tafi bada hanyoyin da za bi don yin maganin matsalolin shugabanci a Nijeriya.</fdbk>
<eng-response>The year 2006 is considered a shameful year in the history of Nigeria because of the conflicts that occurred among Nigerian leaders. Politicians publicly accused and blamed each other of wrongdoing, and the poor became the victims of these circumstances. Maryam Adamu was one of the citizens who expressed her disgust in this report presented by Ibrahim Ka'almasi Garba. She requested that the key players in the fight (the president and his vice president) settle their differences so that lower class citizens can live a better life with food and a stable income, so their children can go to school. Based on the reporter's interview, Nigerians believe that the only way out is for the president to accept those under him and work with them as a team.</eng-response>
<eng-fdbk>Incorrect! This is not correct because the report does not talk about a better way of life for Nigerians. Think of a choice that better captures the proposed ways to improve the Nigerian leadership problem.</eng-fdbk>
</opt>
<opt>
<response>Yawancin wanna rahoton na Ibrahim Ka'almasi Garba ya ƙunshi rikici tsakanin shugaban ƙasa da mataimakin shi. Ƴan Nijeriya sun nuna fargaba su da takaicin su saboda shugabaninsu ba su maida hankali ba ga wajibin su na ingantar da yanayin tsaron jama'arsu da ruwan sha da wutar lantarki. Wasunsu da suka bayyana ma mai bada rahoton damuwarsu sun ba masu yin tsarin mulki laifi da cewa basu bayyana abun da zai faru ba idan shugabannin siyasa sun sake jam'iyyasu ko sun ɗauki wata shawara ba zato ba tsammani kamar yadda shugaban ƙasa ya dakatar da mataimakin shi daga aiki. Biyu daga cikin waɗanda suka gana da mai bada rahoton suna da guri iri ɗaya, watau shugaban ƙasa da mataimakinshi su sasanta tsakaninsu su yi zaman lafiya.</response>
<fdbk>Wannan daidai ne! Jama'a Nijeriya suna fushi da rashin jituwa shugabanninsu kuma ya na shafa su ta hanyoyin rayuwasu ta yau da kullum.</fdbk>
<eng-response>This report by Ibrahim Ka'almasi Garba mostly talks about the misunderstanding between the president of Nigeria and his vice president. Nigerians expressed their fear and anger because their leaders paid no attention to their duty of protecting the people and providing water and electricity, among other necessities. Some of those who expressed their concerns to the reporter blame the makers of the constitution for not stating what happens in cases where leaders switch political parties or make sudden decisions, as in the case of the president suspending his vice president. Two of the speakers interviewed had the same desire: for their president and vice president to make peace with each other.</eng-response>
<eng-fdbk>Correct! The Nigerian public is angry about the misunderstanding between the leaders and how it is affecting their daily lives.</eng-fdbk>
</opt>
</choices>
</problem>
</problemset>
<instr type="eng">INSTRUCTIONS:
Choose the best summary.</instr>
<instr type="target">Umurni:Zaɓi taƙaitawa mafi dacewa.</instr>
<finish>How do you think the Nigerian government can prevent conflicts between a leader and his assistant?</finish>
<finish>What do you think should be the main focus of the political leaders in Nigeria?</finish>
<finish>What do you think the Nigerian population needs to do to prevent the election of self-seeking leaders?</finish>
<finishtl>Yaya kuke ganin gwamnatin Nijeriya ke iya rigaƙafin rikice-rikice tsakanin shugaba da mataimakinshi?</finishtl>
<finishtl>Minene ya kamata 'yan siyasa Nijeriya su hanga a matsayin shugabanni?</finishtl>
<finishtl>Mi kuke ganin ya kamata jama'ar Nijeriya ta yi don guje ma zaɓen shugabanni masu son kai?</finishtl>
</activity>