Toggle menu
24K
663
183
158.1K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Talk:bringing

Discussion page of bringing

Glosbe's example sentences of bringing [1]

  1. Misalin kalmar da jimlolin turanci da Hausa na kalmar bringing:
    1. (Romans 5:12) Besides bringing death, sin has impaired our relationship with our Creator and has affected us physically, mentally, and emotionally.
      (Romawa 5:12) Bayan mutuwa, zunubi ya raunana dangantakarmu da Mahaliccinmu kuma ya shafe mu a zahiri, a tunani da kuma a motsin rai. [2]

    2. 5:32; 7:6) Their three sons grew up and married, bringing the family up to “eight souls.”
      5:32; 7:6) Yaransu maza uku suka yi girma kuma suka yi aure, hakan ya sa adadin waɗanda suke cikin iyalin ya kai “masu-rai takwas.” [3]

    3. Jesus instructed his disciples: “If, then, you are bringing your gift to the altar and you there remember that your brother has something against you, leave your gift there in front of the altar, and go away; first make your peace with your brother, and then, when you have come back, offer up your gift.”
      Yesu ya umurci almajiransa: “Idan fa kana cikin miƙa baiwarka a wurin bagadi, can ka tuna ɗan’uwanka yana da wani abu game da kai, sai ka bar baiwarka can a gaban bagadi, ka yi tafiyarka, a sulhuntu da ɗan’uwanka tukuna, kāna ka zo ka miƙa baiwarka.” [4]

    4. 6:10) Then we will have the joy of bringing glory to our heavenly Father. —Matt.
      6:10) Hakan zai sa mu farin ciki domin muna ɗaukaka Ubanmu wanda ke sama. —Mat. [5]

    5. Bringing good news to others makes me happy
      Yaɗa bishara ga mutane yana sa ni murna [6]

    6. Instead of bringing multiple printed publications to the meeting, use your device to follow the various parts and to sing the songs.
      Maimakon zuwa taro da littattafai da yawa, za ka iya zuwa da na’urarka kawai kuma ka riƙa bin sashe dabam-dabam na taron har da waƙoƙinmu ma. [7]

    7. Ephesians 6:4: “Do not be irritating your children, but go on bringing them up in the discipline and mental-regulating of Jehovah.”
      Afisawa 6:4: “Kada ku yi ma ’ya’yanku cakuna har su yi fushi: amma ku goye su cikin horon Ubangiji da gargaɗinsa.” [8]

    8. None of the 10,000 Israelite volunteers could boast about bringing this deliverance.
      Babu wani cikin Isra’ilawa 10,000 da zai buga kirji cewa shi ya sa aka yi wannan nasarar. [9]

    9. (Matthew 24:3; Luke 21:31) The Kingdom of God, a heavenly government of God’s making, will bring about big changes on the earth, even bringing natural elements under control.
      (Matta 24:3, LMT; Luka 21:31) Mulkin Allah, wanda gwamnati ce ta samaniya da Allah ya kafa, zai kawo gagarumin canje-canje a duniya, har da sarrafa ruwa, iska da makamantansu a yadda ba za su yi wa kowa illa ba. [10]

    10. The verses that follow explain that in a series of long periods, figuratively called days, God went on to prepare our earthly home, bringing into existence all the wonders of our natural world.
      Ayoyin da suka biyo bayanta sun bayyana cewa a cikin dogon lokaci, waɗanda aka kira ranaku a alamance, Allah ya tsara duniya don mu rayu a cikinta, kuma ya halicci dukan abubuwa masu ban al’ajabi da ke duniyarmu. [11]

    11. Jeremiah prophesied: “This is what Jehovah has said, ‘In accord with the fulfilling of seventy years at Babylon I shall turn my attention to you people, and I will establish toward you my good word in bringing you back to this place.’”
      Irmiya ya annabta: “In ji Ubangiji, bayan shekara saba’in sun cika domin Babila, zan ziyarce ku, in cika maganata mai-alheri gareku, ina komo da ku a wurin nan.” [12]

    12. If men have a purpose in bringing forth their comparatively insignificant inventions, surely Jehovah God had a purpose in his awesome creations!
      Idan mutane suna da dalilin da ya sa suka ƙera abubuwa da ba su da muhimmanci, hakika Jehovah Allah yana da dalilin halitta da ya yi, masu ban mamaki! [13]

    13. By bringing back to life those who sleep in death.
      Ta wajen ta da waɗanda suka rasu daga matattu. [14]

    14. He instructed Moses to tell the Israelites: “On your coming into the land where I am bringing you, it must also occur that when you eat any of the bread of the land, you should make a contribution to Jehovah.”
      Ya ce wa Musa ya gaya wa Isra’ilawa: “Kadan kun shiga cikin ƙasa inda zan kawo ku, za ya zama, kadan kun ci abincin ƙasa, za ku kawo ma Ubangiji hadaya ta cirawa.” [15]

    15. It is the One who is bringing forth the army of them even by number, all of whom he calls even by name.
      Shi wanda yake musu ja-gora kamar sojoji, ya sani ko su guda nawa ne, yana kiran dukansu, kowanne da sunansa! [16]

    16. Usually, it stimulates us to make additional progress, bringing out the best in us.
      Hakan yana sa mu ci gaba da ƙwazo. [17]

    17. It will also draw you close to God, bringing you peace of mind and heart.
      Zai kuma jawo ka kusa da Allah, kuma ka samu kwanciyar hankali da zuciya. [18]

    18. Yes, Jehovah has heavenly angelic armies, which he will use in bringing warlike peoples and nations to nothing!
      I, Jehovah yana da rundunar mala’iku na samaniya, da zai yi amfani da su ya wofintar da mutane da kuma al’ummai masu shirin yaƙi! [19]

    19. Unlike the foolish ones, though, five virgins truly prepared themselves, bringing extra oil in their flasks along with their lamps.
      Budurwai masu hikima ba kamar marasa azancin ba don sun shirya da kyau, sun je da mai a cikin fitilunsu da kuma saura a cikin kwalabansu. [20]

    20. Such non-Christians used the cross “as a magic sign . . . giving protection, bringing good luck,” wrote Sven Tito Achen, Danish historian and expert on symbols, in the book Symbols Around Us.
      Arna sun yi amfani da gicciya “Alama sihiri ce . . . da take ba da kāriya, da sa’a,” haka Sven Tito Achen, ɗan tahiri kuma ƙwararren masani kan alamu, ya rubuta a littafinsa Symbols Around Us (Alamu da Suke Tare da Mu). [21]

    21. 7 Jehovah’s ability to adapt to new circumstances while in the process of bringing his purpose to completion is in harmony with a description he gave of himself.
      7 Yadda Jehobah yake daidaitawa zuwa sabon yanayi don ya cim ma nufinsa ya jitu da kwatancin kansa da ya yi. [22]

    22. We could not help but think of the words: “How comely upon the mountains are the feet of the one bringing good news, the one publishing peace, the one bringing good news of something better, the one publishing salvation.” —Isa.
      ga ƙafafun mai-kawo bishara, daɗin gani garesu bisa duwatsu! mai-shelan salama, yana kawo bishara ta alheri, mai-shelan ceto.”—Isha. [23]

    23. Consider his response when his disciples reprimanded people for “bringing him young children.”
      Ka lura da amsarsa sa’ad da almajiransa suka kwaɓi mutane da suke kawo “yara ƙanƙanana” wurinsa. [24]

    24. What does Jesus accomplish in fulfilling his role as the Messiah, bringing what results for obedient mankind?
      Menene Yesu ya cim ma wajen cika hakkinsa a matsayin Almasihu, wane sakamako ne hakan zai kawo ga ’yan adam masu biyayya? [25]

    25. Seeing this, King Achish rebuked his servants for bringing a “crazy” man before him.
      Da ganin haka, Sarki Akish ya yi wa bayinsa faɗa domin sun kawo masa “mahaukaci.” [26]


Retrieved August 07, 2020 10:23 PM