Toggle menu
24.1K
670
183
158.6K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Talk:fixed

Discussion page of fixed

One scholar says that scarlet “was a fast, or fixed colour.

Wani manazarci ya ce mulufi “launi ne da ba ya wankewa.



While we keep our eyes firmly fixed on the Paradise ahead, let us share fully in the spiritual privileges that Jehovah is granting us now.

Da muke kafa idanunmu sosai a kan Aljanna na nan gaba, bari mu shagala sosai cikin gata na ruhaniya da Jehovah yake ba mu a yanzu.



What can distract us from keeping our eyes fixed on Jehovah?

Mene ne zai iya janye hankalinmu daga zuba ido ga Jehobah?



Illustrations can breathe life into words, teaching lessons that become fixed in our memory.

Misalai sukan ƙara ma’ana ga kalmomi, suna koyar da darussa da zai yi wuya mu manta.



15:6) Yes, he fixed his mind on the things above in that he concentrated on God’s promises.

15:6) Hakika, ya mai da hankali ga abubuwan da ke sama, wato ya sa rai ga alkawuran Allah.



4:6) In so doing, we keep our eyes fixed on Jehovah.

4:6) Idan muna yin hakan, za mu nuna cewa muna zuba idanunmu ga Jehobah.



3:1) So in order to remain spiritually alert, we must keep our minds fixed on the right things.

3:1) Saboda haka, don mu ci gaba da kasancewa da dangantaka mai kyau da Jehobah, yana da muhimmanci mu ƙallafa ranmu ga abubuwan da suka dace.



11:28, 30, 31) Imagine how each Israelite family must have fixed their eyes on their firstborn as “there began arising a great outcry” in one Egyptian household after another.

11:28, 30, 31) Ka yi tunanin yadda kowace iyalin Baisra’ila za ta riƙa kallon ɗansu na fari sa’ad da ake “kuka mai-zafi” a kowace iyalin Masarawa.



They are to keep their minds “fixed on the things above, not on the things on the earth.” —Col.

Da yake za su zama amarya a sama, an bukace su su ‘ƙalafa ransu ga abubuwan da ke bisa, ba wajen na ƙasa ba.’—Kol.



To remain in God’s love, we need to keep our “minds fixed on the things above.” —Colossians 3:2.

Idan muna son mu tsare kanmu cikin ƙaunar Allah, muna bukatar mu “ƙalafa ran[mu] ga abubuwan da ke bisa.”—Kolossiyawa 3:2.



In contrast to tithing, which was a requirement with a clearly defined commitment, voluntary contributions and the gleaning arrangement did not require a fixed amount.

Dabam da zakka, da aka tsara ta ainihi, ba da kyauta ta yardan rai da kuma yin kala ba sa bukatar a ambata ainihin yawansu ba.



What will help us to keep our minds fixed on spiritual things?

Menene zai taimake mu mu sa zuciyarmu a kan abubuwa na ruhaniya?



All eyes were fixed on the tomb.

Kowa ya zuba ido ga kabarin.



In the meantime, God’s servants must keep their hope fixed on what is everlasting.

Kafin lokacin, wajibi ne bayin Allah su kasance da bege cewa lokaci yana zuwa da za mu rayu har abada.



11:13) No doubt, such prophets as Elijah, Jeremiah, and other faithful ones of pre-Christian times who boldly stood up for true worship were likewise helped to endure by keeping their eyes fixed on Jehovah’s promises. —Titus 1:2.

11:13) Babu shakka, an taimaki annabawa kamar su Iliya, Irmiya, da wasu masu aminci kafin zamanin Kiristanci, waɗanda da ƙarfin zuciya suka yin tsayin daka don bauta ta gaskiya su jimre ta wajen dogara ga cikar alkawuran Jehobah.—Tit. 1:2.



In what ways can we keep our minds fixed on the things above?

Ta yaya za mu ƙallafa ranmu ga abubuwan da ke sama?



And how can we make sure that our eyes remain fixed on him as we face life’s complex challenges?

Kuma ta yaya za mu iya tabbatar da cewa muna dogara gare shi don ya magance matsalolinmu?



▪ “Keep Your Minds Fixed on the Things Above”

▪ ‘Ku Ƙallafa Ranku ga Abubuwan da Ke Bisa’



We can flee from temptation by prayerfully keeping our eyes fixed on Jesus.

Za mu iya guje wa jaraba ta wurin kira bisa ga Yesu.



15 Moses allowed the actions of others to distract him from keeping his eyes fixed on Jehovah.

15 Musa ya ƙyale halayen wasu ya hana shi zuba ido ga Jehobah.



This study will help us to endure by encouraging us to keep our minds fixed on Jehovah God and his Kingdom.

Wannan talifin zai taimaka mana mu jimre da kuma ƙallafa rai ga Jehobah Allah da kuma Mulkinsa.



“Keep Your Minds Fixed on the Things Above”

‘Ku Ƙallafa Ranku ga Abubuwan da Ke Bisa’



Although the stars could be huge distances from one another, their relative positions remain fixed from earth’s perspective.

Ko da yake nisan taurarin suna da yawa ainu da juna, ba sa kauce wa matsayinsu a duniya.



We bought it, fixed it up, and pulled it to our new territory.

Muka saye ta, muka gyara ta, kuma muka kai ta sabon yankinmu.



(Jeremiah 9:17, 18; Matthew 9:23) Jesus’ gaze, however, became fixed on the grief-stricken mother, no doubt walking near the bier that carried the body of her son.

(Irmiya 9:17, 18; Matta 9:23) Sai Yesu ya kafa ido wa uwar da take baƙin ciki, babu shakka tana tafiya kusa da makara da aka ɗauki ɗanta a kai.