Toggle menu
24K
665
183
158.2K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Talk:image

Discussion page of image

During that war, God’s people declared that according to the prophecy in Revelation, the image of the wild beast would ascend again.

A lokacin wannan yaƙin, mutanen Allah sun bayyana cewa ƙungiyar za ta sake tasowa kamar yadda littafin Ru’ya ta Yohanna ya annabta.



Three young men who refuse to worship a towering image are thrown into a superheated furnace, yet they survive unsinged.

An jefa samari uku da suka ƙi bauta wa wani gunki mai tsawo a tanderu mai ƙuna, duk da haka sun tsira babu wani taɓo.



Why does the Bible say that Jesus is “the image of the invisible God”?

Me ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce Yesu “surar Allah marar ganuwa” ne?



32:1, 4) Then they held what they called “a festival to Jehovah” and bowed down and sacrificed to their man-made image.

32:1, 4) Suka soma bauta wa gunkin, suna miƙa masa hadaya, amma kuma wai Jehobah ne suke bauta wa.



Now, when you hear the music, fall down and worship the image I have made.

Idan kuka ji kiɗa, ku durƙusa ku bauta wa gunkin da na yi.



5 Adam was made “in God’s image.”

5 An halicci Adamu cikin “surar Allah.”



These two articles will examine the prophecies of the immense image in Daniel chapter 2 and the wild beast and its image in Revelation chapters 13 and 17.

Waɗannan talifofi biyu za su tattauna annabce-annabcen da ke littafin Daniyel sura ta 2 game da babbar sifa da dabba da kuma gunkinta da ke littafin Ru’ya ta Yohanna sura ta 13 da 17.



The image of gold that this Babylonian king set up on the plain of Dura may have been dedicated to Marduk.

Mai-yiwuwa ne an keɓe siffar zinariya da wannan sarkin Babila ya kafa a filin Dura, ga Marduk.



According to Daniel chapter 2, the dream involved an immense image with a head of gold, breasts and arms of silver, belly and thighs of copper, legs of iron, and feet of iron mixed with clay.

Daidai da abin da Daniel sura 2 ta ce, mafarkin ya ƙunshi babban siffa mai kan zinariya, ƙirji da damutsa na azurfa, ciki da kuma cinyoyi na jan ƙarfe, ƙafafu na ƙarfe, da kuma sawaye na ƙarfe haɗe da tabo.



At the time of creation, Jehovah spoke these words, evidently to his Son: “Let us make man in our image, according to our likeness.”

A lokacin halitta, Jehovah ya yi wannan maganar, a bayyane, ga Ɗansa ne: “Bari mu yi mutum a cikin surarmu, bisa ga kamaninmu.”



3 Remember that man was created “in God’s image” and likeness.

3 Ka tuna cewa an halicci mutum cikin ‘surar’ Allah da kuma kamaninsa.



This requires that you “strip off the old personality with its practices, and clothe [yourself] with the new personality, which through accurate knowledge is being made new according to the image of the One who created it.” —Colossians 3:9, 10.

Kana bukatar ka ‘tuɓe tsohon mutum tare da ayyukansa, ka yafa kuma sabon mutum, wanda a ke sabonta shi zuwa ilimi bisa ga surar mahaliccinsa.’—Kolossiyawa 3:9, 10.



(See opening image.) (b) What accounted for Peter’s courage on that occasion?

(Ka duba hoton da ke wannan shafin.) (b) Me ya sa Bitrus ya kasance da gaba gaɗi a lokacin?



(See opening image.) (b) What is it about Jehovah’s kingship that draws us to him?

(Ka duba hoton da ke wannan shafin.) (b) Me ya sa muke so Jehobah ya mulke mu?



According to some scholars, the image expressed is that of erasing handwriting.

In ji wasu manazarta, ma’anar furcin na goge rubutun hannu ne.



The Son of God also cooperated with his Father when Jehovah designed and created the huge variety of animal and plant life here on earth and when He prepared the Paradise that would be home to creatures made in Jehovah’s image and likeness.

Ɗan Allah ya haɗa hannu da Ubansa Jehobah sa’ad da ya tsara ya kuma halicci dabbobi da shuke-shuke iri-iri a nan duniya da kuma sa’ad da ya kafa Aljanna da za ta zama gidan ’yan adam da aka halicce su cikin surar Jehobah.



However, three Hebrews —Shadrach, Meshach, and Abednego— refused to bow to the image, even on pain of death. —Daniel, chapter 3.

Amma, Ibraniyawa uku, Shadrach, Meshach, da Abednego, suka ƙi yin sujada, har a bakin ransu.—Daniel, sura ta 3.



At Armageddon that stone will strike the image and grind it to powder.

A Armageddon dutsen zai mangare siffar kuma ya niƙa ta ta zama gari.



In that year Roman armies, holding high their standards emblazoned with the image of the eagle, swooped down upon Jerusalem to inflict a terrible slaughter.

A wannan shekara sojojin Roma, suna riƙe da mizanansu ta yin biki da sifar gaggafa, suka sauƙo wa Urushalima suka halaka ta.



One day he commanded that when music was played, everyone should bow down to the image.

Wata rana ya ba da doka cewa idan aka yi kiɗa, kowa ya yi sujjada ga gunkin.



During that time, Jesus acquired such a thorough knowledge of Jehovah that he could be described as the very “image of the invisible God.”

A wannan lokaci, Yesu ya zo ga sanin Jehobah sosai da aka kwatanta shi a matsayin “surar Allah marar-ganuwa.”



8 To most people, the expression “the real life” conjures up an image of luxury and pleasure.

8 Ga yawancin mutane, furcin nan “hakikanin rai” yana nufin tara kayan alatu da kuma jin daɗi.



It may be that he, like other Pharaohs, worshipped his own image.

Wataƙila, kamar sauran Fir’auna, ya bauta wa siffarsa.



To his Master Worker, his firstborn Son, Jehovah stated his specific purpose: “Let us make man in our image, according to our likeness, and let them have in subjection the fish of the sea and the flying creatures of the heavens and the domestic animals and all the earth and every moving animal that is moving upon the earth.”

Jehobah ya gaya wa Gwani-Mai-Aikinsa wato, Yesu dalilin da ya sa ya halicci mutane. Ya ce: “Bari mu yi mutum a cikin surarmu, bisa ga kamaninmu: su yi mulki kuma bisa kifaye na teku, da tsuntsaye na sama, da bisashe, da kuma bisa dukan duniya, da kowane abu mai-rarrafe wanda ke rarrafe a bisa ƙasa.”



17 Paul wrote to anointed Christians: “We with unveiled faces reflect like mirrors the glory of Jehovah [and] are transformed into the same image from glory to glory.”

17 Bulus ya rubuta wa shafaffun Kiristoci: “Mu dukanmu kuma fuska ba lulluɓi muke nuna ɗaukakar Ubangiji kamar madubi, ana sauya mu mu ɗauki kamanninsa cikin ɗaukaka mai hauhawa.”



0