اللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنْ عَذَابِ الْقَبْرِ ، وَمِنْ عَذَابِ جَهَنَّمَ ، وَمِنْ فِتْـنَةِ الْمَحْيَا وَالْمَمَاتِ ، وَمِنْ شَرِّ فِتْـنَةِ الْمَسِيحِ الدَّجَّالِ
allaahumma innee a‛oodhu bika min ‛adhaabil-qabri, wa min ‛adhaabi jahannam, wa min fitnatil-maḥyaa wal-mamaat, wa min sharri fitnatil-maseeḥ-id-dajjaal [1]
- O Allah, I seek refuge with You from the torment of the grave, from the torment of the Fire, from the trials and tribulations of life and death, and from the evil affliction of Al-Maseeh Ad-Dajjal (the Antichrist).
Ya Allah, Ina neman tsarin Ka daga azabar kabari, da azabar Jahannama, daga fitina na rayuwa da kuma na mutuwa, kuma daga fitinar Maseehid-dajjal. - O Allah, I seek refuge with You from <> Ya Allah, Ina neman tsarin Ka daga
Book 4, Number 1219: Abu Huraira reported: The Messenger of Allah (may peace be upon him) said: When any one of you completes the last tashahhud. he should seek refuge with Allah from four (trials). I.e. from the torment of Hell, from the torment of grave, from the trial of life and death.-and from the mischief of Masih at-Dajjal (Antichrist). This hadith has been narrated by al-Auza�i with the same chain of transmitters but with these words: "When any one of you completes the tashahhud" and he made no mention of the words "the last". [2] [3] [4]
KA RINKA NEMAN TSARIN ALLAH DAGA ABUBUWA GUDA HUDU: A cikin littafin Bukhari da kuma littafin Muslim akwai wani hadisi wanda Abu Hurairah ya ruwaito Daga Manzon Allah (S.A.W) wata rana Annabi (S.A.W) yace ma Sahabbai Duk lokacin da kukayi Sallah kukayi tahiyya to kafin kuyi Sallama ku nemi tsarin Allah daga Abubuwa guda Hudu mutum yace 'ALLAHUMMA INNI AUZU BIKA MIN AZABIL QABRI, WA MIN AZABI JAHANNAM, WA MIN FITNATIL-MAHYAAWALMAMATI, WA MIN SHARRI FITNATIL-MASEEHID-DAJJAL'. Annabi yace ko wannen ku yace ya Allah ina neman tsarin ka daga azabar kabari, da Azabar Jahannama, ina neman tsarin ka ya Allah daga Fitina na Rayuwa da kuma na Mutuwa,kuma ina neman tsarin ka daga fitinar Maseehid-dajjal. Wainnan abubuwa guda hudu mu tabbata duk wanda yayi sallah ya rinka neman tsarin Allah daga garesu. Hadisi yazo cikin littafin Muslim akace Annabi yana tsananta Umurni akan Sahabbai akan lallai su koyi wannan addu'a, kamar yadda yake tsananta Umurni garesu wurin koyon Alqur'ani. [5]