Toggle menu
24K
663
183
158.1K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Talk:extreme

Discussion page of extreme
Revision as of 23:50, 28 September 2020 by Maintenance script (talk | contribs) (Quick edit: appended Category:Glosbe (pid:10601))
(diff) ← Older revision | Latest revision (diff) | Newer revision → (diff)

Glosbe's example sentences of extreme [1]

  1. Misalin kalmar da jimlolin turanci da Hausa na kalmar extreme:
    1. Through obedience under extreme adversity, Jesus was “made perfect” for the new position God had in mind for him, that of being King and High Priest.
      Da yake ya koyi biyayya ta wurin wahala mai tsanani da ya sha, Yesu “ya zama cikakke” don sabon matsayin da Allah zai ba shi, wato, zama Sarki da Babban Firist. [2]

    2. When thinking about a past mistake, we may feel “crushed to an extreme degree.”
      Sa’ad da muke tunani a kan laifuffukan da muka yi a dā, mukan “ƙuƙuje ƙwarai.” [3]

    3. Challenges to such loyalties have resulted in competition and rivalry and, in extreme cases, bloodshed and genocide.
      Abin baƙin ciki shi ne, irin wannan ƙishin ya hadassa gasa da ƙiyayya, kuma a wasu lokatai ya kai ga zub da jini har ma da kisan kāre dangi. [4]

    4. Extreme poverty is the result when nations, governments, and individuals act only to promote and protect self-interest.
      Abin da ke jawo matuƙar talauci shi ne son kai da al’ummai, gwamnatoci, da mutane suke nunawa. [5]

    5. Extreme physical abuse.
      Cin zali. [6]

    6. As a shepherd, David knew the extreme cold of night.
      Da yake makiyayi ne, Dauda ya san tsananin sanyi da ake yi daddare. [7]

    7. With extreme violence!
      Ya yi faɗā sosai! [8]

    8. Extreme hardship or frustration may cause people to lash out at whoever is around them.
      Yawan wahala ko kuwa taƙaici na iya sa mutane su yi magana cikin fushi ga duk wanda suka gani. [9]

    9. A magazine from a prosperous European land recently noted: “If keeping undesirable impulses under control requires an inner struggle on the part of those living under the agonizing circumstances of extreme poverty, how much more so is that true of those living in the land of milk and honey in today’s affluent society!”
      Wata jarida daga wata ƙasar Turai mai arziki a kwanan baya nan ta lura: “Idan waɗanda suke zama cikin yanayi na mugun talauci suna bukatar kokawa don su kawar da muguwar sha’awa, haka wannan yake musamman ga waɗanda suke zama a ƙasashe masu arziki a yau!” [10]

    10. How did Jehovah’s Witnesses respond to the extreme pressures brought on during the second world war?
      Menene Shaidun Jehovah suka yi game da matsi mai tsanani da suka fuskanta a yaƙin duniya na biyu? [11]

    11. Even under the most extreme tests, Jesus never sinned nor broke any of God’s laws.
      Ko a lokacin da ya fuskanci jaraba mai tsanani, Yesu bai yi zunubi ba kuma bai taka dokar Allah ba. [12]

    12. It reasoned that the right to freedom of religion should prevent the State, except in extreme cases, from assessing the legitimacy of religious beliefs or the way they are expressed.
      Kotun ya ce idan babu wani abin da ya saɓa wa doka, ya kamata ’yancin addini ya hana gwamnati bincika cancantar imanin addini ko kuma yadda masu bin addinin suke gudanar da ibadarsu. [13]

    13. (1 Peter 5:9) Today, Satan is putting extreme pressure on every servant of God.
      (1 Bitrus 5:9) A yau, Shaiɗan yana sa matsi mai tsanani a kan kowanne bawan Allah. [14]

    14. The heat and humidity in Somalia and Eritrea were often extreme.
      Zafi da laima da suke ƙasar Somaliya da Eritrea sau da yawa suna da tsanani ainun. [15]

    15. Certainly, we would not want to think too highly of ourselves to the point of becoming conceited; nor would we want to go to the other extreme and think nothing of ourselves.
      Hakika, bai kamata mu ɗauki kanmu da muhimmanci fiye da yadda ya kamata ba, ko kuma mu faɗa tunanin cewa ba mu isa kome ba. [16]

    16. In extreme cases, acceptance or rejection of uncomfortable treatment could be a matter of life and death.
      A yanayi mai tsanani, karɓa ko ƙin allura da ba ka so zai zama batun rai da mutuwa. [17]

    17. Because of the critical times in which we live, some servants of Jehovah experience extreme hardships that break their heart and crush their spirit, as it were.
      Domin lokacin wahala da muke ciki, wasu bayin Jehobah suna fuskantar wahalolin da ke sa su baƙin ciki kuma suna sa su sanyin gwiwa. [18]

    18. Like the psalmist David, at times we may even grow “numb and become crushed to an extreme degree.”
      A wasu lokatai kamar mai Zabura Dauda, zai zama kamar ‘an ragargaza mu sarai an ci nasara a kanmu’ ne. [19]

    19. Parchment is more durable than papyrus, but it too degrades if mishandled or exposed to extreme temperatures, humidity, or light.
      Fata kuma ta fi takarda da aka yi da ganye jurewa, amma shi ma yana iya lalacewa idan aka bar shi a rana ko a wurare masu danshi ko kuma wuri mai zafi sosai. [20]

    20. Am I inclined to dismiss this admonition as irrelevant or extreme, perhaps offering excuses or justification for my ways?
      Ina yin banza da wannan gargaɗi ko kuma in ba da hujja na yin hakan? [21]

    21. Jacob assured them that if they did so, the raiders would make a humiliating retreat, with the Gadites pursuing their extreme rear.
      Yakubu ya ba su tabbacin cewa idan sun yi haka nan, masu kawo harin za su koma da gudu, ’yan Gad kuwa su bi su. [22]

    22. Jesus proved that a perfect man can be loyal to God even if he suffers to the extreme.
      Yesu ya nuna cewa cikakken mutum zai iya kasancewa da aminci ga Allah kome tsananin wahalar da ya sha. [23]

    23. In poor countries, even when foreign aid provided roads, schools, and clinics, people still suffered extreme poverty because those countries lacked business, natural resources, and access to trade routes.
      Ko da ana amfani da kuɗaɗen agajin da ake samu daga ƙasashen waje don taimakawa ƙasashe marar arziki su gina hanyoyi, makarantu, da asibitoci, mutane suna ci gaba da kasancewa cikin matuƙar talauci saboda waɗannan ƙasashen sun rasa aikin yi kuma ba su da arzikin ƙasa, da kuma hanyoyin zuwa wuraren yin kasuwanci. [24]

    24. The mass murders, rapes, and pillaging mentioned in the preceding article are extreme examples of what happens when people allow wrong desires to dictate their actions.
      Kisan kiyashi, fyaɗe, da kuma kwasan ganima da aka ambata a talifi da ya gabata misalai ne masu tsanani na abubuwa da suka faru sa’ad da mutane suka ƙyale muguwar sha’awarsu ta rinjayi ayyukansu. [25]

    25. Acute grief may include: Memory loss and insomnia; extreme fatigue; abrupt changes of mood; flawed judgment and thinking; bouts of crying; appetite changes, with resultant weight loss or gain; a variety of symptoms of disturbed health; lethargy; reduced work capacity; hallucinations —feeling, hearing, seeing the deceased; in the loss of a child, irrational resentment of your spouse.
      Baƙinciki mai-tsanani zai iya haɗa da: Raba hankali da rashin barci; gajiya na ainun; canjin hali na farat; rashin shari’a mai-dacewa da kuma tunani; yawan kuka; canjin marmarin ci, da rashin jiki ko kuwa kiɓa; ire-iren rashin lafiyar jiki; nauyin jiki; ragin halin aiki; jin bori—jiye-jiye, ji, ganin mataccen; a rashin wani yaro, riƙon kumburin abokin aurenka. [26]


Retrieved September 28, 2020, 7:50 pm via glosbe (pid: 10601)