SANARWA DAGA ƘUNGIYAR “BANN”
Ƙungiyar Mawallafa a Intanet ta Arewacin Najeriya (Bloggers Association of Northern Nigeria, BANN) tana goyon bayan kanfe na neman zaman lafiya a Arewacin Najeriya, ƙarƙashin hashtag na #SecureNorth. Wannan yunƙurin na da burin ankarar da gwamnatin Najeriya game da alƙawarinta na tsare duka yankunan Najeriya baki-ɗaya. A shekarun baya- bayan nan, masu garkuwa da mutane, da mahara, da ‘yan ta’addar Boko Haram sun addabi yankin Arewacin Najeriya. Sakamakon haka, an samu asarar rayuka da salwantar dukiyoyi, da ƙone-ƙonen makarantu, da tagayyara mutane musamman mazauna karkara.
A sane muke da ƙoƙarin da jami’an tsaro ke yi wanda hakan ke janyo rasu rayukansu da jikkata su. Sai dai muna kira ga gwamnati da ta ƙara ƙaimi wajen magance wannan mummunar matsala. Muna kira da a sauya tunani kan tsarin tunkarar wannan matsala, kuma a fito da sabbin dabarun wannan yaƙi. Akwai buƙatar shigo da sabbin kwamandojin soji na ƙasa, tare da inganta aikin leƙen-asiri don ruguza aniyar masu tallafawa waɗanann ‘yan ta’adda. Wannan duka zai fi sauƙin yiwuwa idan aka samar wa jami’an-tsaro kayan aiki masu inganci.
Ƙungiyar BANN na alfari da matasan Najeriya da suka haɗa ƙarfi wajen rajin kawo ƙarshen ta’annatin rundunar ‘yan-sanda ta SARS, musamman a kudancin Najeriya. Muna jinjina ga ma’abota kafafen sada zumunta da suka ɗaukaka batun kawo ƙarshen SARS ta amfani da #EndPoliceBrutality da #EndSARS. Haka nan, mun yi maraba da sanarwar Shugaba Buhari a ranar Litinin, 12 ga watan Oktoba, 2020, inda ya jaddada hukuncin rushe rundunar SARS. Wannan wata nasara ce ga masu rajin kare rayuka da mutuncin ‘yan Najeriya.
Sai dai kuma, Arewacin Najeriya na cigaba da fuskantar matsanancin rashin tsaro da kasancewar tarin ƙungiyoyin ta’adda dake gallabawa mazauna Arewa. Muna tunatar da gwamnatin Shugaba Buhari da ta tuna alƙawarin kawar da ƙungiyar Boko Haram da magance matsalar tsaro da ya yi a shekarar 2015. Sanin kowa ne wannan alƙawari bai cika ba har zuwa yau, a yayin da sabbin ƙungiyoyin mahara ke cigaba da cin karensu ba babbaka. Hakan kuma na faruwa haɗe da koma-bayan da Arewa ke samu a ɓangaren ilimi, da masana’antu, da yaɗuwan ƙananan laifuka.
Kanfen ɗin #SecureNorth kuka ne ga gwamnatin Buhari da ta ɗauki mataki kan matsalar tsaro a Arewacin Najeriya, kamar yadda ta gaggauta ɗaukar mataki kan neman rushe SARS. Arewa ba za ta taɓa cigaba ba matuƙar matsalar tsaro ta cigaba da yaɗuwa a garuruwan yankin. Muna jan-hankalin cewa Ƙungiyar BANN ba ta ada’wa da kanfen ɗin #EndSARS, haka nan ba ta goyon bayan karya doka da oda ko cin zarafin mutane. Hasali ma zanga-zanga kan matsalar tsaro an fara ta ne a Jihar Katsina tun watan Satumba, inda har mutum ɗaya ya rasa ransa a ƙaramar hukumar Jibia, aka kuma kame mutane 43.
Ƙungiyar BANN na goyon bayan duk ’yan najeriya wajen neman cin gajiyar ayyukan cigaban ƙasa, da kare rayuwa, da dukiyoyin ‘yan Najeriya. Muna addu’ar samun sauƙi da haɗin-kan ‘yan Najeriya cikin walwala da yancin faɗin albarkacin-baki a fili ko ta kafafen sadarwar zamani, ƙarƙashin tsarin mulkin ƙasa.
Allah ya albarkaci Najeriya, amin.