|
|
1 Fassarar Farko
|
Fassara ta 2
|
Fassara ta 3
|
Fassara ta 4
|
1
|
2
|
Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin halittu;
|
Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, Ubangijin halittu,
|
Godiya ta tabbata ga ALLAH, Ubangijin talikai.
|
Yabo da godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin Halittu,
|
1
|
3
|
Mai rahama, Mai jin ƙai;
|
Mai rahama, Mai jinƙai.
|
Mafi rahamah, Mafi jinqai.
|
Mai rahama Mai jin kai,
|
1
|
4
|
Mai nuna Mulkin Rãnar Sakamako.
|
Mai iko da Ranar Sakamako,
|
Mamallakin ranar Sakamako.
|
Mai mulkin Ranar sakamako,
|
1
|
5
|
Kai muke bauta wa, kuma Kai muke neman taimakonKa.
|
Kai kaɗai muke bauta wa, kuma taimakonKa kaɗai muke nema.
|
Kai kadai muke bautawa, kuma kai kadai muke neman taimako.
|
Kai kadai kawai Mu ke bautawa, Kuma kai kadai Mu ke neman taimako,
|
1
|
6
|
Ka shiryar da mu ga hanya madaidaiciya.
|
Ka shiryar da mu hanya madaidaiciya.
|
Ka shiriyad da mu ga hanya madaidaiciya.
|
Ka shiryad da mu hanya madaidaiciya,
|
1
|
7
|
Hanyar waɗanda Ka yi wa ni'ima, ba waɗanda aka yi wa fushi ba, kuma ba ɓatattu ba.
|
Hanyar waɗanda Ka yi ni'ima gare su, ba waɗanda aka yi fhshi da su ba, kuma ba waɗanda suka ɓata ba.
|
Hanyar wadanda Kayi wa nilima, ba wadanda aka yi wa fushi ba,kuma ba batattu ba.
|
Hanyar wadanda ka yi ni'ima a gare su ba wadanda ka yi fushi akansu ba, kuma ba batattu ba
|