1 Fassarar Farko | Fassara ta 2 | Fassara ta 3 | Fassara ta 4 | ||
1 | 2 | Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin halittu; | Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, Ubangijin halittu, | Godiya ta tabbata ga ALLAH, Ubangijin talikai. | Yabo da godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin Halittu, |
1 | 3 | Mai rahama, Mai jin ƙai; | Mai rahama, Mai jinƙai. | Mafi rahamah, Mafi jinqai. | Mai rahama Mai jin kai, |
1 | 4 | Mai nuna Mulkin Rãnar Sakamako. | Mai iko da Ranar Sakamako, | Mamallakin ranar Sakamako. | Mai mulkin Ranar sakamako, |
1 | 5 | Kai muke bauta wa, kuma Kai muke neman taimakonKa. | Kai kaɗai muke bauta wa, kuma taimakonKa kaɗai muke nema. | Kai kadai muke bautawa, kuma kai kadai muke neman taimako. | Kai kadai kawai Mu ke bautawa, Kuma kai kadai Mu ke neman taimako, |
1 | 6 | Ka shiryar da mu ga hanya madaidaiciya. | Ka shiryar da mu hanya madaidaiciya. | Ka shiriyad da mu ga hanya madaidaiciya. | Ka shiryad da mu hanya madaidaiciya, |
1 | 7 | Hanyar waɗanda Ka yi wa ni'ima, ba waɗanda aka yi wa fushi ba, kuma ba ɓatattu ba. | Hanyar waɗanda Ka yi ni'ima gare su, ba waɗanda aka yi fhshi da su ba, kuma ba waɗanda suka ɓata ba. | Hanyar wadanda Kayi wa nilima, ba wadanda aka yi wa fushi ba,kuma ba batattu ba. | Hanyar wadanda ka yi ni'ima a gare su ba wadanda ka yi fushi akansu ba, kuma ba batattu ba |
Zaɓi fassarar da ta fi a http://www.strawpoll.me/42227676