https://gloss.dliflc.edu/products/gloss/hua_soc408/hua_soc408_source.html
<> | ||
Mace: Kafin mu ci gaba, ga wata 'yar matashiya. | <> | Woman: Before we continue, here is a little reminder. |
Namiji 1: Masauraro ku ɗauko alkalami da takarda kusa domin ga wani babban albishir daga sashen Hausa na Muryar Amirka. | <> | Man 1: Listeners, get a pen and paper ready for an important announcement from the Hausa Service of Voice of America. |
Namiji 2: Sashen Hausa na Muryar Amirka ya kirkiro da wata hanya da za ku rinƙa jin muryoyinku kai tsaye, kuna bayyana ra’ayoyinku kullum a cikin shirye-shiryenmu. | <> | Man 2: The Hausa Service of Voice of America has created a way where you can hear your voices directly. You can express your opinions at all times in our programs. |
Namiji 1: Abinda kawai za ku yi, sai ku kira wannan lamba, watau: biyu, sifili, biyu, biyu, sifili, biyar, tara, tara, huɗu, biyu. | <> | Man 1: All that you have to do is call this number: 220-205-9942. |
Namiji 2: To malam Ibrahim bari in sake maimaita musu wannan lamba. Watau: biyu, sifili, biyu, biyu, sifili, biyar, tara, tara, huɗu, biyu. | <> | Man 2: Okay, (Mister) Ibrahim, let me repeat the number to them. It is 202-205-9942. |
Namiji 1: Idan an kira lambar za a ji wata gaisuwa kamar haka: (waƙa) “VOA, Washington.” | <> | Man 1: When you call the number you will hear this greeting: (singing) “VOA Washington.” |
Namiji 2: To, da zarar an ji wannan gaisuwa, sai a matsa ɗaya da biyu a jikin wayar. Sai a ji wannan gaisuwa: | <> | Man 2: Okay, as soon as you hear that greeting press one and then two on the telephone. Then, you will hear this greeting: |
Muryar Wata Mace: A haƙiƙa nan ne Sashen Hausa na Muryar Amirka a birnin Washington DC. Kuma kun faɗa a akwatinmu na barin saƙo a wayar tarho. Ku bada ra’ayi a takaice. Kuma don Allah kada ku manta ku bar suna da cikakken adireshi. (sautin na’ura) | <> | Voice of another woman: Yes, this is the Hausa Service of Voice of America in the city of Washington D.C., and you have reached our voicemail service. Give your opinion briefly, and please do not forget to leave your full address. (beep) |