Toggle menu
24K
663
183
158.1K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.
Revision as of 03:47, 10 September 2021 by Admin (talk | contribs) (Text replacement - "jw2019" to "<br><br>")
(diff) ← Older revision | Latest revision (diff) | Newer revision → (diff)

(Revelation 12:12) During this period, Satan wages war with the anointed followers of Christ.

(Ru’ya ta Yohanna 12:12) A wannan lokacin, Shaitan ya yi yaƙi da shafaffu mabiyan Kristi.



No longer will people fight and die in war.

Mutane ba za su riƙa yaƙi ko kuma su mutu a yaƙi ba.



See what’s happening to the horses and war chariots of the Egyptians.

Ka dubi abin da yake faruwa da karusa da dawakai na Masarawa.



The Medes and the Persians regarded the glory resulting from a conquest more highly than the spoils of war.

’Yan Midiya da ’yan Fasiya sun fi son darajar da ake samu daga cin yaƙi fiye da ganimar yaƙi.



Why Do Jehovah’s Witnesses Not Go to War?

Me Ya Sa Shaidun Jehobah Ba Sa Zuwa Yaƙi?



During that war, God’s people declared that according to the prophecy in Revelation, the image of the wild beast would ascend again.

A lokacin wannan yaƙin, mutanen Allah sun bayyana cewa ƙungiyar za ta sake tasowa kamar yadda littafin Ru’ya ta Yohanna ya annabta.



If we follow him, he will help us to gain inner peace, which includes a confident expectation of seeing in the future total peace —which will mean the absence of violence, war, and crime.

Idan muka bi shi, zai taimake mu mu sami kwanciyar hankali, wanda ya haɗa da tabbacin fata na samun cikakken salama a nan gaba—wanda zai nufi ƙarshen nuna ƙarfi, yaƙi, da kuma aika laifi.



IMAGINE how fear-inspiring “the war of the great day of God the Almighty” will be!

KA YI tunanin yadda “yaƙin babbar rana ta Allah Mai-iko duka” za ta kasance da ban tsoro!



(Zephaniah 2:3) It reaches its climax in “the war of the great day of God the Almighty . . . , called in Hebrew Har–Magedon [Armageddon],” in which “the kings of the entire inhabited earth” are annihilated.

(Zephaniah 2:3) Zai kai iyakarsa a “yaƙin babbar rana ta Allah Mai-iko duka. . . . da ake ce da shi da Ibrananci Har–Magedon [Armageddon],” inda za a halaka “sarakunan dukan duniya.”



He became a Witness in 1939 at the beginning of World War II, and he gave up a flourishing press photography business in order to take up the full-time ministry.

Ya zama Mashaidi a shekara ta 1939 a farkon Yaƙin Duniya na II, ya bar harkokinsa na kuɗi na buga hotuna, domin ya fara aikin hidima na cikakken lokaci.



Human history has consistently been characterized by war, injustice, oppression, and suffering.

Tarihin ’yan Adam ya cika da yaƙi, rashin gaskiya, zalunci, da wahala.



During the war that broke out that year, the few thousand anointed Christians, “the sons of the Kingdom,” were in spiritual captivity to Babylon the Great.

A lokacin da yaƙin ya ɓarke a shekarar nan, shafaffun Kiristoci ko kuma “’ya’yan Mulki,” wajen dubu biyar ne kawai a lokacin, kuma Babila Babba ta hana su yin ibada.



Also, that idea may sound convincing because —according to some studies— war, crime, disease, and poverty are all decreasing.

Ban da haka ma, mutane suna iya tunani cewa hakan gaskiya ne don wani bincike ya nuna cewa yaƙi da mugunta da cututtuka da kuma talauci suna raguwa.



We were assigned to Korea, though three years of war had just ended in the summer of 1953, leaving that country devastated.

An aika mu hidima a Koriya, ko da yake bai daɗe ba da yaƙin da aka yi shekara uku a ƙasar ta ƙare a cikin rani ta shekara ta 1953, kuma hakan ya ɓata ƙasar.



One reason is that they live in a world full of hatred, war, and suffering.

Dalili ɗaya shi ne domin duniya ta cika da ƙiyayya, yaƙi, da kuma wahala.



In 1918, what pestilence claimed more lives than World War I?

A shekara ta 1918, wace annoba ce ta ci rayuka da ta ɗara na Yaƙin Duniya na I?



“ABOVE all other things, the twentieth century was shaped by war,” says author Bill Emmott.

“FIYE da kome, yaƙi ne ya cika ƙarni na ashirin,” in ji mawallafi Bill Emmott.



The Greek historian Herodotus recorded some examples from Xerxes’ war against Greece.

Wani ɗan tarihi mai suna Herodotus ya rubuta wasu abubuwa game da yaƙin da Xerxes ya yi da Girkawa.



Health problems, death, unemployment, war, food shortages, and poverty will be no more. —10/1, pages 6-7.

Rashin lafiya, mutuwa da rashin aiki da yaƙi da ƙarancin abinci da kuma talauci ba za su ƙara kasancewa ba.—11/1, shafuffuka na 6-7.



After World War II, our work could again be carried on without legal restraint.

Bayan Yaƙin Duniya na Biyu, muka soma aikinmu kuma ban da hani na doka.



IN A world where disasters happen daily, it is truly comforting to know that as the Bible proclaims, war, crime, hunger, and oppression will soon end.

ADUNIYA da kullum bala’i ke aukuwa, abar ƙarfafa ce sanin cewa kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya yi shela, yaƙi, laifi, yunwa, da kuma zalunci za su ƙare ba da daɗewa ba.



Everlasting life in peaceful, pleasant conditions, without the threat of illness, war, famine, or death, would surely open the door to endless happiness and blessings.

Babu shakka, zama a duniya har abada a cikin lumana, ba tare da jin tsoron yiwuwar rashin lafiya ko yaƙi ko yunwa ko kuma mutuwa ba, zai sa mu farin ciki sosai.



Just as World War II was ending, Greek communists rebelled against the Greek government, triggering a bitter civil war.

Da aka kusan gama Yaƙin Duniya na Biyu, ‘yan kwaminis na Girka suka yi wa gwamnatin Girka tawaye, kuma hakan ya jawo yaƙin basasa.



Then there is Günther, who was a German soldier stationed in France during the second world war.

Günther ma wani misali ne, sojan Jamus ne da aka aika Faransa a lokacin yaƙin duniya na biyu.



The Bible reveals that the time is near when God will eliminate the wicked world during his war of Armageddon.

Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa lokaci ya yi kusa da Allah zai kawar da duniyar nan ta mugunta a yaƙinsa na Armageddon.