Toggle menu
24K
663
183
158.1K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.
Revision as of 12:39, 7 November 2021 by Admin (talk | contribs) (Created page with "(Isaiah 9:6, 7) The dying patriarch Jacob prophesied about this future ruler, saying: “The scepter will not '''turn''' aside from Judah, neither the commander’s staff from...")
(diff) ← Older revision | Latest revision (diff) | Newer revision → (diff)

(Isaiah 9:6, 7) The dying patriarch Jacob prophesied about this future ruler, saying: “The scepter will not turn aside from Judah, neither the commander’s staff from between his feet, until Shiloh comes; and to him the obedience of the peoples will belong.” —Genesis 49:10.

(Ishaya 9:6, 7) Da yake so ya mutu Yakubu uban iyali ya yi annabci game da wannan sarki na nan gaba, yana cewa: “Kandirin ba za ya rabu da Yahuda ba, Sandar mai-mulki kuma daga tsakanin sawayensa, har Shiloh ya zo; zuwa gareshi kuma biyayyar al’ummai za ta nufa.”—Farawa 49:10.

jw2019

18 It is instructive to compare how Jehovah reacted with how Jonah reacted to this turn of events.

18 Gwada yadda Jehovah ya ji da yadda Yunana ya ji game da wannan canji zai koyar da mu.

jw2019

We need to turn to God for protection.

Muna bukatar mu je wurin Allah don kāriya.

jw2019

2 Whether we think about the atom or turn our attention to the vast universe, we are impressed by Jehovah’s awesome power.

2 Ko mun yi tunani a kan atam ko kuma mun juya hankalinmu ga sararin samaniya mara iyaka, iko mai ban mamaki na Jehovah yana burge mu.

jw2019

Habakkuk had an exemplary attitude, for he said: “Although the fig tree itself may not blossom, and there may be no yield on the vines; the work of the olive tree may actually turn out a failure, and the terraces themselves may actually produce no food; the flock may actually be severed from the pen, and there may be no herd in the enclosures; yet, as for me, I will exult in Jehovah himself; I will be joyful in the God of my salvation.”

Habakkuk yana da hali da ya kamata mu yi koyi da shi, don ya ce: “Gama ko da shi ke itacen ɓaure ba za ya yi fure ba, ba kuwa ’ya’ya a cikin kuringar anab ba; wahalar zaitun ta zama banza, gonaki ba su bada abinci ba: ko da za a raba tumaki da wurin zamansu, ba a iske shanu a dangwalinsu ba; duk da haka zan yi murna cikin Ubangiji; zan yi murna a cikin Allah mai-cetona.”

jw2019

In the mid-1980’s, what turn of events took place in Zaire?

Tsakanin shekara ta 1984 da 1986, yaya abubuwa suka canja wa bayin Jehobah a ƙasar Zaire ba zato ba tsammani?

jw2019

Sending money to the governments of poor countries may start another cycle: Aid is easy to steal, so it can lead to corruption, and corruption, in turn, can lead to more poverty.

Aika kuɗi zuwa ga gwamnatin ƙasashe marar arziki yana kuma jawo waɗannan abubuwa: Kuɗin da aka ba da don taimakon agaji yana da sauƙin sacewa, saboda haka yakan kai ga rashawa, kuma rashawa, yakan kai ga ƙarin talauci.

jw2019

Even if most or all of them were true worshippers, God’s direction through Moses was that a king of Israel should “not multiply wives for himself, that his heart may not turn aside.”

Ko da yawanci ko kuma dukansu suna bauta wa Jehobah, amma Allah ya umurci Musa cewa kada sarki a Isra’ila ya “auri mata da yawa don kada zuciyarsa ta karkace.”

jw2019

God thus went on to warn that the unbelievers “will turn your son from following me, and they will certainly serve other gods.”

Shi ya sa Allah ya gargaɗi mutanensa cewa al’umman za su iya “juyarda ɗanka ga barin bina, domin su bauta wa waɗansu alloli.”

jw2019

This wholesome fear, in turn, gave him outstanding courage, as was demonstrated immediately after Jezebel murdered Jehovah’s prophets.

Wannan tsoron ya sa ya kasance da gaba gaɗi na musamman kamar yadda ya nuna nan da nan bayan Jezebel ta kashe annabawan Jehobah.

jw2019

Do not become upset and turn to doing evil. —Ps.

Kada ka yi fushi, wannan ba ya kome sai mugunta.—Zab.

jw2019

Turn the page and let’s see.

Ka juya zuwa shafi na gaba.

jw2019

Turn from your burning anger and feel regret over the evil against your people.

Ka juyo ga barin zafin fushinka, ka tuba ga barin wannan mugunta bisa mutanenka.

jw2019

Since you appreciate it when you receive commendation, should you not, in turn, do your best to give commendation to others? —Read Matthew 7:12.

Tun da kana jin daɗi idan aka yabe ka, bai kamata ba ne ka yi iya ƙoƙarinka ka yabi wasu?—Karanta Matta 7:12.

jw2019

In turn, such faith can give you a joyful outlook and fill you with courage to speak about your hope.

Irin wannan bangaskiya za ta sa ka yi farin ciki kuma ta sa ka kasance da gaba gaɗin yin magana game da begenka.

jw2019

Job refused to turn his back on Jehovah, even when he did not understand why things had suddenly gone wrong.

Ayuba ya ƙi ya juya wa Jehobah baya, duk da cewa bai fahimci dalilin da ya sa abubuwa suka same shi ba.

jw2019

His first miracle was to turn water into wine, and on two occasions he fed multitudes with a few loaves and fish.

Mu’ujizansa na farko shi ne mai da ruwa zuwa anab, kuma sau biyu ya ciyar da mutane masu yawa da gurasa da kuma kifi kaɗan.

jw2019

10. (a) Explain what it means to turn away from what is bad. (b) What is involved in doing what is good?

10. (a) Ka bayyana abin da guje wa mugunta ke nufi? (b) Menene yin nagarta ya ƙunsa?

jw2019

[Turn to lesson 2 and point out the subheadings.]

[Ka buɗe darasi na 2 kuma ka nuna masa ƙananan jigon.]

jw2019

This, in turn, contributes to our happiness.

Wannan zai sa mu yi farin ciki.

jw2019

Jehovah warned him that he was heading for trouble and advised him to “turn to doing good.”

Jehovah ya yi masa gargaɗi cewa zai shiga masifa idan “ba ya kyauta ba.”

jw2019

As a member of “the division of Abijah,” Zechariah was then serving his turn at the temple.

Tun da yana cikin “ƙungiyar Abaija,” Zakariya a lokacin yana hidima tasa a haikali.

jw2019

How did her move turn out?

Shin haƙarta ya cim ma ruwa ne?

jw2019

Why did Jesus turn down one man’s request?

Me ya sa Yesu ya ƙi roƙon wani mutum?

jw2019

(James 1:2, 3) Similarly, Romans 5:3-5 informs us: “Let us exult while in tribulations, since we know that tribulation produces endurance; endurance, in turn, an approved condition; the approved condition, in turn, hope, and the hope does not lead to disappointment.”

(Yaƙub 1:2, 3) Hakan nan ma, Romawa 5:3-5 sun ce: “Mu yi farinciki kuma cikin ƙuncinmu: muna sane ƙunci yana faradda haƙuri; haƙuri kuma, gwadawa; gwadawa kuma, bege: bege kuma ba ya kunyatarwa.”

jw2019

0