VOA Hausa Safe [1]
- Hosts: Muhammad Hafiz Baballe, Surfilu Hashim Gumel
Labaran Duniya <> World News
- 🇺🇸🇺🇦 Jiya Laraba, shugaban Amurka ya ce Amurka tana baiwa Ukraine wani kunshin tallafi na dalar Amurka miliyan dari bakwai ($700M) na karin manyan na'uroruka na zamani da (alk'usai?).
- Yesterday Wednesday, American president said that the US is giving Ukraine $700M in aid for tech and modern weapons.
- Biden sends Ukraine $700M more military aid including key rockets to repel Russian advances [2].
- 🇺🇸🇹🇼 Amurka ta kaddamar da sabuwar yarjejeniyar kasuwanci da Taiwan jiya Laraba, da fatan kulla alaka ta kud-da-kud tattalin arziki da yankin da kasar China ta yi ikirarin mallakarta ne.
- The United States will launch new trade talks with Taiwan, U.S. officials said on Wednesday... [3]
- 🇮🇷🇺🇳 Haka kuma za a ji cewa Iran ta yi gargadi jiya Laraba cewa, za ta mayar da martani ga duk wani matakin da bai dace ba ga hukumar sa ido kan makaman nukiliya ta MDD.
- Iran Warns of Response to IAEA 'Unconstructive Actions' [4]
Labaran Najeriya <> Nigerian News
- Wasu 'yan siyasa na cigaba da bayyana damuwa, kan yadda kudi ke tasiri wajen fitar da 'yan takara a cikin jam'iyyun siyasa na kasar.
- "Domin daga karshe, ciniki aka rinka yi. Wannan ya tayawa wannan kaza, wannan ya tayawa wannan kaza. Wadda shi ne babban hadarin. Ni na ji kunya. Ni, duk sanda dan kasa ta yi abin kunya, ni ma kunyar kama ni take. Ba wai iya kudin ba a yi dariya a yi komai, zai zama abin kunya ne..."
- Muhawara ta barke sakamakon hukuncin da wata babbar kotu a Abuja ta yanke na karawa shugabannin kananan hukumomi na birnin tarayyar Abuja wa'adin shekara hudu a maimakon uku.
- "Abin da zan ce a nan shine: bai kamata a ce dokar zabe, ta sha karfin dokar kasa ba. Don haka, kuma bai kamata a ce dokan zabe za ta yi aiki akan wasu yanki daban ko wasu sassa daban... a ce za ta banbanta ta yi aiki akan... kananan hukumomi kuma ta banbanta da na babban birnin tarayya ba."
- Kamar kowace ranar Alhamis, da shirin Domin Iyali da Alheri Grace Abdu ke gabatarwa.
BBC Hausa Safe [5]
- Host: Badariya Tijjani Kalarawi
- A Birtaniya, za a fara bikin kwanaki hudu domin tayawa Sarauniya Elizabeth murnan shekaru 70 akan karagar mulki.
- Wani dan bindiga ya kashe akalla mutum hudu a wani asibiti da ke wata jami'a a kasar Amurka.
- Wasu 'yan majalisar wakilan jihar Zamfara a Najeriya, sun fice daga jam'iyyar APC tare da komawa tsohuwar jam'iyyar su.
- "Ra'ayin mutanen mu, wadanda muke wakilta, wadanda suka turo mu daga constituency daban-daban, guda 7, muka zanna da su, suka ce mana mu komo PDP don abinda ake yi a wannan gwamnatin, ba gaskiya bane."
- ('Yan Akada?) na cigaba da ficewa daga jihar Legas, sakamakon karewar wa'adin haramta ayyukansu da gwamnatin jihar ta yi.
- "Gaskiya... an takurawa mutane. An kori jama'a, an ba mu deadline. Duk wanda aka kama da mashin, da direban mashin da fasinja... kuma mashin d'in, bai sake ganinsa. Amma in kaga mashina yadda suke wucewa, abin sai Allah Sarki!"
- Za mu je jamhuriyar Niger, inda manoma ke shirye-shiryen noman wannan lokaci.
- (3:57 - 4:33) Labarin murabus din ma'aikaciyar Facebook tun shekaru 14 da suka wuce, COO Sheryl Sandberg. Daya daga cikin manyan masu karfin fada a ji a duniya shafukan zumunta, Sheryl Sandberg, ta ajiye aikinta bayan shafe shekaru 14 tana rike da babban mukami a kamfanin Meta da Facebook ke cikinsa. A lokacin da ta fara aiki da kamfanin dai yana da kudaden shiga (revenue) na daruruwan miliyan daloli. Amma a yanzu kuma Meta na da sama da biliyan $4. Sheryl dai za ta cigaba da kasancewa cikin manyan shugabannin Facebook, wadanda za su kula da zamanantarwa da cigaban kamfanin. A baya dai ta fuskanci matsin lamba, lokacin da Facebook din ke fuskantar tuhuma kan batun kare bayanan sirri. <> Wednesday Meta COO Sheryl Sandberg posted on Facebook that after 14 years with the company, she will step down from her role but remain on Meta's board. She says she wants to focus on philanthropic work. And while she denied they played a part in her decision, Sandberg will avoid having to deal with declining ad revenues or and FTC antitrust lawsuit. --English blurb by Tom Merrit
Pars Hausa 2021-06-02 1900 GMT [6][7][8]
Summary of programme broadcast on Iranian state radio's external service on 2 June at 19:00 GMT
- Headlines.
- 🇹🇳 Powerful Tunisian UGTT trade union calling for a national strike on 16 June to demand increase in wages. The union said all staff in the 159 state institutions and public companies will join the strike, a statement revealed.
- 🇮🇷 Iranian President Ebrahim Raisi in a phone convo with his Senegalese counterpart Macky Sall on Tue (31 May) said Africa is one of the main priorities of Iranian foreign policy. President Raisi also congratulated President Sall on the African National Day.
- 🇮🇱🇵🇸 Israeli forces have shot and killed a Palestinian woman at the Arroub refugee camp in the southern Israeli-occupied West Bank.
DW Shirin Safe [9]
- Host: Muntakahiwa?
- Shirin ya kunshi kokarin mahukuntan Najeriya na shawo kan sace-sacen mutane da dabbobi a Najeriya da yaye wasu tubabbun mayakan Boko Haram a Diffar Jamhuriyar Nijar da kokarin yaki da kyandar biri da ke yaduwa yanzu a duniya.
- Abinda ke sanya wasu 'yan takaran neman mukamai daban-daban a Nigeria yake iya jurewa neman mulki tsawon lokaci ba tare da sun karaya ba.
- A Nijeriyar, masana kiwon lafiya na cigaba da jan hankalin jama'a a gama da hanyoyin kaucewa kamuwa da cutar nan ta kyanda biri.
- Idan muka je Niger, za a ji yadda ake horar da wasu tubabbun mayakan Boko Haram wasu sana'o'i na musamman domin dogaro da kai.