Toggle menu
24.1K
670
183
158.5K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

sandbox1

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Revision as of 20:05, 20 July 2017 by Admin (talk | contribs)

ƁɓƊɗƘƙƳƴ Notes to self

caf

==Adverb==

  1. kalma mai nuna gwaninta wajen cafe abin da aka jeho. <> {adv.}. Used with cafe q.v. to express the idea of making an adroit catch of something thrown. e.g.
    1. caf ya cafe. (= caraf)
    2. ya cafe lemo caf.

cafa

  1. REDIRECT cafe

cafala

==Noun== m

  1. {n.f.}. (Katsina) A young pullet. (= shafala.) <> 'yar tsakon kaza.

caf-caf

==Noun== m

  1. kalma mai nuna yawautar mai, musamman cikin abinci. {n.f.}. Used in:
    1. caf-caf da mai ta fi caf-caf da ruwa <> 'tis better to choose a friend who is a man of substance than a poor person.
    2. caf-caf da mai ba ta 'bata tuwo <> however good a thing may be it will not be spoilt by being improved.

==Adverb==

  1. (adverb) kalma mai nuna tsananin sayuwar abu. <> Readily (of or for sale). e.g.
    1. yana sayuwa caf-caf kamar waina. <> it is being quickly bought up.
    2. in an kai kasuwa, caf-caf sai ku'din <> if it is taken to the market it will be readily bought.
  2. kalma mai nuna dacewar ado da mutum. <> expresses being fashionable.
    1. ya yi ado caf-caf <> he was smartly dressed.

cafdi, cafd'i

  1. REDIRECT cafɗi

cafɗi

  1. Kalmar da ake amfani da ita wajen nuna ƙi ko rashin yarda da wata magana ko faruwar wani abu.
  2. kalma mai nuna mamakin abu. <> expresses surprise e.g. wow, woah.

cafe

==Hausa Verb==

  1. kame abin da ya faɗi ko aka jefo. <> to catch, swoop.
    1. ɗan was an hoto ya jefa garma sama ya cafe.
  2. ribce wani abu.
  3. karɓe magana.
  4. yin ciniki cikin ciniki.
See also cafa

==Hausa Noun== m

  1. yi wa gida ado daga waje da makuba ko bagaruwa ko wata laka. <> cover outside walls of a mud-brick house with mud so as to protect it from eroding during the rain.

caffa

==Noun== f

  1. yin mubaya'a ga wani mutum da ya sami sarauta.
  2. [caffa"; cappa"] {n.f.}. Attaching oneself to a person of influence for the advantage of his protection, and in return being to a certain extent at his call; volunteering one's allegiance to p. e.g.
    1. ya kai masa caffa. = ya yi caffa. gare shi <> he pledge allegiance to him.. (= cafha. capha.)

cafi

  1. yaɓe.

cafiya

==Noun== f

  1. kame abin da ya faɗo ko aka jefo. <> catching something thrown in the air.
  2. [cafiya/] {n.f.}. catching a thing thrown, &c. (Vide cafe I.) e.g.
    1. cafiya ya yi <> he caught it.
    2. cafiya gare shi <> he is a good catcher.

cagada

  1. karkiya.

cagade

  1. cecekuce.

cagwade

  1. REDIRECT cagade

cai

  1. [cai] {adv.}. emphasizes <> kalma mai nuna tsananin wayon mutum ko zaƙin abu...
    1. (a) cunning.
      1. yina da wayo cai. <> he is quiet cunning.
    2. (b) The flavour described under zak'i. e.g. yina da zak'i cai. (= cwai; cwan; cai-cai.)
      1. shayi ya yi zaƙi cai! <> the tea's very sweet I tell ya!
See also zaƙwai, and cai-cai

caja

==Noun== m

  1. bincikar mutum ko kaya. <> a search or investigation of a person or object.

==Verb== caja | caje | caji (also means to charge) | cajo | caju

  1. bincike mutum ko kaya. <> searching or investigating a person or thing.
  2. gasa baturin mota a wutar lantarki don ya ƙara ƙarfin wuta.

caji

==Noun== m

  1. bincike ko tuhuma. <> investigation.
  2. caji ofis = caj ofis <> police station. wato ofishin 'yan sanda.
  3. (English) charge.

cak

  1. kalma mai nuna ɗaukewar abu ko tsayawarsa gaba ɗaya. <> Completely.
    1. Ruwan sama ya ɗauke cak. <> the rain has completely ceased.
  2. [cak] {adv.}. Completely. e.g. [ruwa/ ya/ 'da>uka/+ ca+k], ya/ tashi daga gari cak. he left the town with all his household and belongings. an 'dauke kaya cak, the loads have all been taken. (Vide cancak; 'dan'dak; kacokan; tak.) ya yi kama da shi cak, he is just like him. (= daidai; yak; sak.)

caka

==Noun== f

  1. ɗaya daga cikin nau'o'in katuna irin na wasan karta mai alamar rassa guda uku. <> clubs (in playing cards).

==Verb== caka | caki | cako | caku | cake

  1. to stab, poke. hit with a sharp point, prick. <> soke abu da mashi ko wani abu mai tsini.
    1. ya caka caki dan-wake da tsinke. <> he poked around the beans with stick.
  2. peck (by fowl)

cakaɗiɗi

==Noun== m

  1. surutun banza. <> useless banter or discussion.
  2. fallasa.
  3. [ca"ka"'di/+'di/+] {n.m.}. chatter; harping on a thing. e.g.
    1. ana cakaɗiɗi da raina <> I am being talked about; my faults are being exaggerated.

cakadidi, cakad'id'i, cakaɗi

  1. REDIRECT cakaɗiɗi

cakaftu

==Noun== m

  1. surutun da ba ya da kai da gindi.
  2. shagali da kuɗi.
  3. fifiƙewa a magana.
  4. {n.m.}. Monopolizing a conversation, incessant chatter by one person in a company. (Vide tsattsarewa.)

cakaikai

  1. mutum mai yawan surutu. <> talkative, verbose.

cakalkale

  1. caɓe.

cakankami

==Noun==

Singular
cakankami

Plural
cakankamai

m

  1. wata irin munduwa mai 'yan kacau-kacau da ake sa wa yara a ƙafa. <> {n.m.} Metal anklets worn by children. (= barambajau; cf. k'oroso.)

cakaniya

  1. hayaniya <> noise.

cakansami

==Noun==

Singular
cakansami

Plural
cakansamai

m

  1. wani irin abu da 'yan rawa ke ɗaurawa a ƙafa mai kacau-kacau. <> A kind of rattle, metal or otherwise, worn round the ankles by dancers. (Vide koroso.)
  2. wasu ƙarafa masu amo da ke yi wa doki ado da su. <> Small metal tinkling ornaments for a horse's headgear. (=(Go.) camankashi; (K.) cika-saura.)
  3. A form of bird-scarer. (= rorami.)

cakansamai

==Noun==

Singular
cakansami

Plural
cakansamai

  1. The plural form of cakansami; more than one (kind of) cakansami.
  2. Litter of leaves and other rubbish.

cakara

==Noun== f

  1. wata irin saiwar wani tsiro a daji da ake ci. <> [ca"ka"ra/+] {n.m.}. A wild edible root. (Vide Dal under tsakara.)

cakarkari

==Noun==

Singular
cakarkari

Plural
cakarkarai

cakarkari = m | cakarkara = f

  1. kwarkwaro na tare zare ko na jan igiya a bakin kwakware.
  2. gawar da ake ɗaurawa a kan dabino don korar tsuntsaye.
  3. mutum-mutumin da ake kafewa a gona don korar tsuntsaye.
  4. {n.m. no pl.} Part of a wide loom, made from metal and the kernel of dum palm fruit. (= cakarkara; (Go.) mac'iriri; (Mar.) mak'iriri; cf. kwalankwalama; kwarkwaro; 'dan butsil; burar gwauro)

cakarkara

  1. female (f) version of cakarkari
  2. The name of a variety of nightjar. (= takarakara; dauga.)
  3. A revolving cylinder for helping in drawing water from a well.
  4. A device for scaring birds from date trees. (= hana makara.)

cakasam

  1. duguzum.

cakau

  1. cakansami.

cakaura

==Noun== f

  1. haƙoran da suka fito waje. <> outward facing visible teeth. Protuberant teeth, also the possessor of same.
  2. goron-biri wanda aka gasa. <> Any roasted monkey-nuts. Monkey nuts shelled; boiled, salted, and then roasted.
  3. cakkyare ko lalaje/lalajo.
  4. Cadging at feasts by professional beggars.
  5. wata irin ƙasa. <> a type of sand. A kind of soil. (= karka.)

caki

==Noun== m

  1. goran da aka saka tsakuwa a ciki don kaɗawa.
  2. yin maguɗi wajen cacar wuri.
  3. kaɗa wutsiyar da doki ke yi.

==Noun 2==

Singular
caki

Plural
none

Singular
check

Plural
checks

m

  1. takardar da ake ba mai ajiyar kuɗi a banki don amfani da ita yayin da yake son karɓar kuɗi.

cakina

==Noun== m

  1. wata irin cuta da ke kama ƙafar kuturu. <> A word which, occurring only in songs, refers to a leper's diseased foot.
  2. = tunkuza q.v.

cakine

  1. REDIRECT caɓe