Suratu Hud, Aya Ta 1-5 (Kashi Na 339)
Jama'a masu saurare barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke yin dubi kan irin nasihohin da ke tattare a cikin irin wadannan ayoyi kuma babu wani tushe ko madogara da yafi kur'ani yin riko da matukar mutum ya yi aiki da shi ko shakka babu zai samu tsira duniya da lahira. Kuma haka akasin haka yak e ma'ana duk wanda ya yi watsi da shi to ko shakka babu ya tabe duniya da lahira da fatar Allah ya kiyashe mud a tabewa duniya da lahira.
Bayan a makon da ya gabata mun kawo karshen yin dubi a cikin ayoyin da ke tattare a cikin suratu Yunus to a wannan karo za mu fara da yin dubi a cikin suratul Hud .Kuma abin sani a nan ita wannan sura an sabkar da ita ne a shekaru na karshe da ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare da kuma alayan gidansa ya yi a birnin Makka kafin daga bisani ya yi hijira zuwa birnin Madina. Ayoyin da ke cikin wannan sura sun maida hankali wajen yin bayanin a cikin tarihin annabawan da suka gabata musamman annabi Nuhu (AS). Kuma Annabin rahama da Sahabbasa ake kiransu zuwa ga gwagwarmaya da makiya da tsayin daka kan hanyar imani. har ila yau bayan Annabi Nuhu (AS) shi ma Annabi Hud (AS) da aka aiko shi zuwa ga al'ummarsa ya kiraye su zuwa ga bautawa Allah daya tilo wanda babu wani abin bautawa sai shi daya kuma ba shi da abokin tarayya da kuma su yi watsi da duk wani abin da suke bautawa na shirka da sanin yin haka babban laifi ne da ke tattare da mumunan sakamako duniya da lahira kuma idan muka yi dubi a cikin ayoyi na hamsin zuwa ayoyi na sattin na wannan sura ta Hud za mu gani da fahimtar yadda tattaunawa ta kasance tsakanin Annabi Hud (AS) da kuma mutanansa wato al'ummarsa da kuma yin bayani kan mummunan sakamakon da ya same su bayan bujirewa.
To madallah yanzu kuma za mu saurari aya ta 1 da ta 2 a cikin wannan sura ta Hud (AS) kamar:
الَر كِتَابٌ أُحْكِمَتْ آيَاتُهُ ثُمَّ فُصِّلَتْ مِن لَّدُنْ حَكِيمٍ خَبِيرٍ{1} أَلاَّ تَعْبُدُواْ إِلاَّ اللّهَ إِنَّنِي لَكُم مِّنْهُ نَذِيرٌ وَبَشِيرٌ{2}
Alif Lam Ra Allah ne Ya San abin da yake nufi da wannan.(Wannan) Littafi ne da aka kyautata ayoyinsa sannan aka rarraba su,daga wurin Allah Mai hikima Masani yake.
Yana umarninka da cewa kada ku bauta wa kowa sai Allah .Ka ce: Hakika ni mai yi muku gargadi ne da albishir daga gare shi (Allah).
Wannan sura kamar sauran takwarinta gona ashirin da takwas a cikin kur'ani da suke faraway da Haruffan da babu wanda ya san ma'anarsu sai Mahalicci ya sani ma'ana ya barwa kansa sanin abubuwan da suka kumsa wannan ma wata mu'ijizar ce daga Allah madaukakin sarki gashi a zahiri sun fara ne da haruffan Alif ba amma mun gagara fahimtar ma'anarsu kuma babu wani da zai iya kawo wata sura hatta wata aya guda daya tilo da ta yi kama da ayoyi ko ayar Kur'ani.Wannan ma wata mu'ijizar ce da ke nuni da yadda wadannan ayoyi sun zone daga masani, gwani, mahalicci, mabuwayi abin dogaro sarkin halitta, masanin abubuwan da ke sammai da kassai ,sarari da taku. A wani bangare idan muka yi dubi a cikin ayoyin kur'ani za mu fahimci yadda dukan ayoyin da ke cikin wannan littafi mai tsarki sun kumshi ruhin tauhidi kuma a ayoyi daban-daban za a ga hakan ya bayyana da kuma yawanci ke magana kan ilmomi,wa'azi da hukumce-hukumce. Wani babban kalubale ga mutane da aljannu da duk wani mahaluki dake lunfashi a doran kasa babu wanda zai iya yin gyara ko canja wata aya da wata ko ma ya soke ta baki daya ko ya yi karin wata ayar a cikin kur'ani.Domin Allah ne da kansa ya yi alkawalin kare Kur'aninsa daga duk wani kari ko ragi a cikin ayoyinsa da hakan ko shakka babu na nuni da cewa wannan Littafi Mai Tsarki ya zone daga gwani Ubangijin talikai kuma dukan ayoyin da ke cikinsa bayyanannu ne kuma masu karfi.
A cikin wadannan ayoyi za mu iya ilmantuwa da kuma fahimtar abubuwa guda uku kamar haka;
Na farko: Kur'ani littafi ne na dokokin Allah da cikin hikima da ilmi maras musaltuwa yake bayani dalla-dalla kan hakika da dokokin da ke cikinsa.
Na biyu: Falsafar sabkar da littafi daga sama shi ne tsarkake al'umma, mutane da aljannu daga shirka tare kiran su zuwa tauhidi.
Na uku: Salon annabawa da manzonnin Allan (AS) na isar da sakon Allah shi ne tsoratarwa da bada bushara ma'ana tsoratarwa da kwadatarwa kamar yadda yan iya magana hausawa ke cewa cizawa da hurawa.
Sai a saurari karatun aya ta 3 da ta 4 a cikin suratul Hud kamar:
وَأَنِ اسْتَغْفِرُواْ رَبَّكُمْ ثُمَّ تُوبُواْ إِلَيْهِ يُمَتِّعْكُم مَّتَاعاً حَسَناً إِلَى أَجَلٍ مُّسَمًّى وَيُؤْتِ كُلَّ ذِي فَضْلٍ فَضْلَهُ وَإِن تَوَلَّوْاْ فَإِنِّيَ أَخَافُ عَلَيْكُمْ عَذَابَ يَوْمٍ كَبِيرٍ{3} إِلَى اللّهِ مَرْجِعُكُمْ وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ{4}
3- An sanar da ku kuma cewa ku nemi gafarar Ubangijinku sannan ku tuba gare shi, zai jiyar da ku dadi,kyakkyawar jiyarwa zuwa wani lokaci kayyadadde, ya kuma bai wa duk wani wanda ya yi abin kirki sakamakon kirkinsa. Idan kuwa kuka ba da baya ,to hakika ni ina tsorartar da ku azabar rana mai girma.
4- zuwa ga Allah ne makomarku ,shi kuwa Mai iko ne a kan komai.
A nan ma ana umartar Annabi ne kan ya gaya wa mutanensa cewa su yi watsi da kudure-kudure na jahiliyya da kuma sabo da barna da suke yi a bayan kasa,su koma ga Allah su dinga yin nadama da tuba.To idan suka yi shakka za su same shi mai yalwar gafara ne zai ko gafarta amsu. Idan ko suka bijire wa wannan gargadin,to za su gamu da mutsananciyar azaba ta lahira.
Kowa da kowa zai koma ne ga Allah,Sannan kuma shi zai saka wa kowa game da abin day a aikata. Kada wani ya zaci cewa zai tsira daga azabar Allah wai don ganin zai mutu ya zama turbaya ya rududduge. Allah mai ikon tayar da komai kamar yadda ya halicce shi a da ,shi ne kuma zai tattara kowa a wuri daya don yi musu hisabi game da abin da kowa ya aikata.
Sai kuma aya ta 5 a cikin wannan sura ta Hud:
أَلا إِنَّهُمْ يَثْنُونَ صُدُورَهُمْ لِيَسْتَخْفُواْ مِنْهُ أَلا حِينَ يَسْتَغْشُونَ ثِيَابَهُمْ يَعْلَمُ مَا يُسِرُّونَ وَمَا يُعْلِنُونَ إِنَّهُ عَلِيمٌ بِذَاتِ الصُّدُورِ{5}
5- Ku gane ba shakka suna kautar da zukatansu don su boye masa Allah.Kaico" Ai lokacin da suke lulluba da tufafinsu Yana sane da abin da suke bayyanawa. Hakika Shi Allah Masanin abin da yake cikin zukata ne.
Wannan ayar tana kunyata kafirai ne amsu tsammanin za su iya yi wa Allah dabara ta boye kafircinsu, da shiryar makirce-makirce don karya addinin Musulunci. To shi ne Allah ya nna musu cewa shifa yana sane da duk abin da yake boye kamar yadda ya san na sarari. Saboda haka boyewarsu ba za ta kare su ba kuma ba za ta amfana musu komai ba.
Da wannan ne kuma muka kawo karshen abubuwa da za mu iya yin bayani akansu a cikin wannan shiri nay au sai kuma mako na sama inda za ku ji mu dauke da wasu ayoyin a cikin wannan sura ta Hud kafin lokacin ni Tidjani malam lawali da na shirya kuma na gabatar na ke cewa wassalam alaikum wa rahamatullahi wa
Suratu Hud, Aya Ta 6-8 (Kashi Na 340)
Jama'a masu sauraren mu barkarmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke yin dubi da nazari a irin nasihohi da galgadin da ke cikin ayoyin alkur'ani mai girma kuma babu wani abu ko madogara da tafi yin riko da alkur'ani a rayuwarmu ta yau da kullum kama daga akida,zamantakewa,tattalin arziki,ma'amala da dai sauran bangarori na rayuawa .Kuma ya kamata mu yi wa kanmu nasiha da galgadi tun kafin wani ya yi mana ko lokaci ya kure mana kuma babu wafi dacewa daga cikin kamar wanda zai yi wa kansa nasihi da galgadi da fatar Allah ya ba mu karfi da ikon yin hakan.
Za mu fara shirin ne da sauraren aya ta 6 a cikin wannan sura ta hud:
وَمَا مِن دَآبَّةٍ فِي الأَرْضِ إِلاَّ عَلَى اللّهِ رِزْقُهَا وَيَعْلَمُ مُسْتَقَرَّهَا وَمُسْتَوْدَعَهَا كُلٌّ فِي كِتَابٍ مُّبِينٍ{6}
6- Kuma babu wata dabba a bayan kasa face arzikinta yana hannun Allah, kuma Yana sane da matabbatarta da ma'ajiyarta. Dukkanin wannan yana nan a cikin littafi mabayyani shi ne Lauhul –Mahafuzu.
Wannan ayar tana tabbatar da cewa duk wani abu da yake da rai a bayan kasa, mutum ne ko dabba ko kwaro,To Allah Shi ne mai kula da shi da kuma ba shi abinci. Kuma ya san duk abin da yake a tsatson maza da kuma na mahaifar mata. Haka kuma ya san lokacin fitowarsu duniya da lokacin komawarsu gare Shi.wannan duk yana kunshe cikin bayanin littafin Lauhul Mahafuzu.
Ga kuma karatun aya ta 7 da 8 a cikin wannan sura ta Hud:
وَهُوَ الَّذِي خَلَق السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضَ فِي سِتَّةِ أَيَّامٍ وَكَانَ عَرْشُهُ عَلَى الْمَاء لِيَبْلُوَكُمْ أَيُّكُمْ أَحْسَنُ عَمَلاً وَلَئِن قُلْتَ إِنَّكُم مَّبْعُوثُونَ مِن بَعْدِ الْمَوْتِ لَيَقُولَنَّ الَّذِينَ كَفَرُواْ إِنْ هَـذَا إِلاَّ سِحْرٌ مُّبِينٌ{7} وَلَئِنْ أَخَّرْنَا عَنْهُمُ الْعَذَابَ إِلَى أُمَّةٍ مَّعْدُودَةٍ لَّيَقُولُنَّ مَا يَحْبِسُهُ أَلاَ يَوْمَ يَأْتِيهِمْ لَيْسَ مَصْرُوفاً عَنْهُمْ وَحَاقَ بِهِم مَّا كَانُواْ بِهِ يَسْتَهْزِئُونَ{8}
7-Shi ne kuma wanda ya halicci sammai da kassai cikin gwargwadon kwana shida, Alarshinsa kuwa ya kasance a kan ruwa,don ya jarraba ku ya ga a cikinku wa yafi kyakkyawan aiki wallahi idan ka ce da su: Hakika za a tashe ku bayan mutuwa,ba shakka kafirai za su ce : Ai wannan ba wani abu ban e sai tsafi kuru-kuru.
8-Hakika da Mun jinkirta musu azaba zuwa ga wani lokaci kayyadadde,wallahi da za su ce: Me ya tsare zuwanta/ Na'am ,ranar da za ta zo musu baa bin da zai kare su daga gare ta,kuma abin da suke yi wa izgili zai saukar musu.
Bujirewa umarni da hukumcin Allah a wannan duniya na haddasa fushi da azabar Allah.kuma aika sabo na daya daga cikin abubuwa masu haddasa fushin Allah kuma musamman masu aikata sabon cikin girman kai da dagawa.Abin fadakarwa da sani shi ne a duk lokacin da wani ke yin izgili kan akida da ayyukan alheri da bujirewa kuma su sani jinkirta azabtar da su a wannan duniya wani lutifi da rahama ce daga Allah madaikakin sarki kuma hakan ba yana nufin an kawar da yi masu azabar ban e .Illa iyaka an jinkirta ne kawai.Kuma a fili lamarin yake cewa; jinkirta azaba yana nufin sake bas u damar gyara ayyukansu da yin tuba .Amma matukar bas u yi aiki da wannan sabuwar dama da aka bas u ba to za su yi nadama ta karshe da babu wata nadama bayanta.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da fahimtar abubuwa guda biyu kamar:
Na farko; Allah yana yi mana jinkiri da babu wata dama domin mu gyara kura-kuranmu da leifuffukan da muka aikata a baya.
Na biyu mu fahimci cewa yin izgili da kaskantar da mumunai da kafirai suke yi wata rana za ta zo da za su raina kansu da fahimtar kurakuransu.
Da wannan ne kuma muka kawo karshen abubuwa da za mu iya yin bayani akansu a cikin wannan shiri nay au sai kuma mako na sama inda za ku ji mu dauke da wasu ayoyin a cikin wannan sura ta Hud kafin lokacin ni Tidjani malam lawali da na shirya kuma na gabatar na ke cewa wassalam alaikum wa rahamatullahi wa
Suratu Hud, Aya Ta 9-12 (Kashi Na 341)
Jama'a masu sauraren mu barkarmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke yin dubi da nazari a irin nasihohi da galgadin da ke cikin ayoyin alkur'ani mai girma kuma babu wani abu ko madogara da tafi yin riko da alkur'ani a rayuwarmu ta yau da kullum kama daga akida,zamantakewa,tattalin arziki,ma'amala da dai sauran bangarori na rayuawa .Kuma ya kamata mu yi wa kanmu nasiha da galgadi tun kafin wani ya yi mana ko lokaci ya kure mana kuma babu wafi dacewa daga cikin kamar wanda zai yi wa kansa nasihi da galgadi da fatar Allah ya ba mu karfi da ikon yin hakan.
To yanzu kuma za mu saurari aya ta 9 da kuma ta 10 a cikin wannan sura ta Hud kamar haka:
وَلَئِنْ أَذَقْنَا الإِنْسَانَ مِنَّا رَحْمَةً ثُمَّ نَزَعْنَاهَا مِنْهُ إِنَّهُ لَيَؤُوسٌ كَفُورٌ{9} وَلَئِنْ أَذَقْنَاهُ نَعْمَاء بَعْدَ ضَرَّاء مَسَّتْهُ لَيَقُولَنَّ ذَهَبَ السَّيِّئَاتُ عَنِّي إِنَّهُ لَفَرِحٌ فَخُورٌ{10}
9-Kuma ba shakka idan muka dandana wa mutum wata rahama tamu sannan Muka karbe ta daga gare shi,hakika zai yanke kauna ya kuma kafirce.
10- Idan kuwa Muka dandana masa dadi bayan ya sha wahala da ta same shi,wallahi zai rika cewa: Ai munanan abubuwa sun bar ni,hakika zai dinga jiji da kai yana alfahari.
Ya kamata mutum ya kasance mai dogaro da Allah a rayuwarsa idan ya samu wata ni'ima ya kasance mai yin godiya ga wanda ya yi masa wannan ni'ima domin ba karfinsa ko dubarasa bane kuma idan ya rasa wata ni'imar ya kasance mai haguri da hangen nesa a rayuwarsa domin ya sa a kansa ba dole bay a kasance ya yi wa Allah wani leifi ne ya amshe da hana shi wannan ni'ima tana yuyuwa Allah mai hikima yana son jarraba shi ne da ganin iyakacin hagurinsa .Idan ya kasance mai haguri sai samu rabo mai girma kamar yadda Allah yak e cewa idan kunkasance masu godiya sai kara muku idan kuwa muka bijire to azabar Allah yanada tsananin kuna. Yin girman kai da nuna dagwawa a kullum na cutar da mai wannan hali ko shakka babu. Kuma duk mai girman kai a rayuwarsa ko wace iri ce babu abin da yake samu sai wahala da karin dinbin matsaloli dab akin jini a tsakanin sauran yan uwansa da yake rayuwa da su a wannan duniya balantana uwa uba ta fuskar akida da addinin Musulunci day a yi hani da wannan mummunan hali.
A cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa guda uku akalla kamar haka;
Na farko mutum halitta ce da ta sha banban da sauran halittu a duk lokacin da wata rahama ko ni'ima ta gushe masa sai ya yi kasa a guiwa da rahamar Allah mai fadi maras karewa.
Na biyu; Ni'imomin Allah wata falala da rahama ce ba don mun cancanta ba saboda haka a kullum mu kasance masu yin godioya ga Allah madaukakin sarki.
Na uku; mu sa a kanmu har kullum wahala da jjin dadi abubuwa ne masu saurin karewa da gujewa saboda haka kar mu kasance masu tunanin dauwama a cikin wannan duniya.
Sai aya ta 11 a cikin wannan sura ta Hud kamar haka:
إِلاَّ الَّذِينَ صَبَرُواْ وَعَمِلُواْ الصَّالِحَاتِ أُوْلَـئِكَ لَهُم مَّغْفِرَةٌ وَأَجْرٌ كَبِيرٌ{11}
11-Sai dai wadanda suka yi hakuri suka kuma yi aiki na gari wadannan suna da sakamakon gafara kana da lada mai girma.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu kamar haka na farko: shi mutum mumuni a kowane yanayi da hali ma'abucin aikata aikin alheri ne ko yana cikin jin dadi ko yana cikin wahala da kumci.
Na biyu haguri da ya samo asali daga imani babu wani abu da yafi dadi da karbuwa domin yana tattare da sakamako babba daga Allah.
Yanzu kuma sai aya ta 12:
فَلَعَلَّكَ تَارِكٌ بَعْضَ مَا يُوحَى إِلَيْكَ وَضَآئِقٌ بِهِ صَدْرُكَ أَن يَقُولُواْ لَوْلاَ أُنزِلَ عَلَيْهِ كَنزٌ أَوْ جَاء مَعَهُ مَلَكٌ إِنَّمَا أَنتَ نَذِيرٌ وَاللّهُ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ وَكِيلٌ{12}
12-Don me za ka bar wani abu daga abin da ake yo maka wahayi da shi, kuma zuciyarka ta kuntata don kada su ce: Me ya hana a saukar masa da wata taska,ko kuma wani mala'ika ya zo tare da shi? Hakika kai dai mai gargadi ne kawai.Allah kuma Mai kula ne da komai.
A cikin wannan aya za mu yi la'akari da abubuwa guda uku na farko: duk mai yada addinin Allah dole ya akasance a ya samu nucuwa da tabbaci a lokacin da yake isar da sakon Allah kuma kar ya yi la'akari da maganganu da sukan mutane.
Na biyu: Mu kasance masu isar da sako ba tare da yin la'akari da sakamakonsa ba face mu kasance masu kokarin isar da sakon da yin hidima don Allah a tsawon rayuwarmu.
Na uku:Nauyin day a rataya a kan manzonni da Annabawa isar da sako da wahayin Allah ga mutane da wai tilasta masu yin imani ba
Da wannan ne kuma muka kawo karshen abubuwa da za mu iya yin bayani akansu a cikin wannan shiri nay au sai kuma mako na sama inda za ku ji mu dauke da wasu ayoyin a cikin wannan sura ta Hud kafin lokacin ni Tidjani malam lawali da na shirya kuma na gabatar na ke cewa wassalam alaikum wa rahamatullahi wa barkatuhu.
Suratu Hud, Aya Ta 13-16 (Kashi Na 342)
Jama'a masu sauraren mu barkarmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke yin dubi da nazari a irin nasihohi da galgadin da ke cikin ayoyin alkur'ani mai girma kuma babu wani abu ko madogara da tafi yin riko da alkur'ani a rayuwarmu ta yau da kullum kama daga akida,zamantakewa,tattalin arziki,ma'amala da dai sauran bangarori na rayuawa .Kuma ya kamata mu yi wa kanmu nasiha da galgadi tun kafin wani ya yi mana ko lokaci ya kure mana kuma babu wafi dacewa daga cikin kamar wanda zai yi wa kansa nasihi da galgadi da fatar Allah ya ba mu karfi da ikon yin hakan.
To madallah yanzu kuma za mu farad a sauraran aya ta 13 da 14 a cikin wannan sura ta Hud:
أَمْ يَقُولُونَ افْتَرَاهُ قُلْ فَأْتُواْ بِعَشْرِ سُوَرٍ مِّثْلِهِ مُفْتَرَيَاتٍ وَادْعُواْ مَنِ اسْتَطَعْتُم مِّن دُونِ اللّهِ إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ{13} فَإِن لَّمْ يَسْتَجِيبُواْ لَكُمْ فَاعْلَمُواْ أَنَّمَا أُنزِلِ بِعِلْمِ اللّهِ وَأَن لاَّ إِلَـهَ إِلاَّ هُوَ فَهَلْ أَنتُم مُّسْلِمُونَ{14}
13- A'a, ko cewa suka yi: Ya kirkire shi ne ? Ka ce da su: Ku kawo sura goma kamarsa kagaggu kuma ku kira duk wanda za ku iya wanda ba Allah ba ya taimake ku in kun kasance masu gaskiya. 14-To idan ba su amsa muku ba,to ku tabbatar cewa; lallai an saukar da shi ne (alkur'ani da sanin Allah, kuma babu wani sarki,sai Shi. To ko yanzu za ku mika wuya?.
Alkur'ani ya ci gaba da maida martani a kan riyawar da kafirai suke yi cewa Annabi ne ya kagi Alkur'ani da kansa,ba daga wajan Allah yak e ba .Saboda haka sai Allah ya kalubalance su game da wannan a wurare da dama cikin Alkur'ani.Da farko a cikin Surar Isra'I aya ta 88. Ya neme su da su kogo wani irinsa,sannan da suka gaza sai ya neme su da su kirkiro sura goma kacal,kamar yadda ya bayyana a wannan sura.Sannan da suka gaza sai ya neme su da su kirkiro ko da sura day ace tak,kamar yadda ya zo a cikin Surar Bakara,aya ta 23,da kuma Surar Yunusa,aya ta 38,amma ina sun kasa.Abin lura a nan shi ne :Surar Isra'I ta sauka ne gabanin Surar Hudu,sannan ita Surar Hudu take bin ta,sai kuma Surar Yunus,sannan Surar Bakara.Shi wannan Alkur'ani,a yadda yake din nan cike da hikima da fusaha,yana nunawa a fili cewa ba wanda ya isa ya yi shi in ban da Allah Madaukakin Sarki dab a wani abin bautawa wanda ya cancanta sai Shi .Shi ne ya aiko Annabinsa da wannan Alkur'ani.Irin abubuwan day a kunsa na fasaha da hikimomi da tsarinsa da hukunce-hukuncensa da kuma labarun gaibu na al'ummun da suka shude da masu zuwa masu karyatawa.Wadannan sun isa su tabbatar da cewa wannan ya fi karfin aikin mutum.Saboda haka wannan mu'ujiza tasa za ta ci gaba da wanzuwa har karshen duniya.Wannan kalubalantar da aka yi wa kafirai ma ta isa ta tabbatar da haka,domin sun kasa kawo ko da aya daya irinsa,duk da kasancewarsu kwararru wajen sarrafa harshen larabci cikin hikima da fasaha.
A cikin wadannan ayoyi za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu na farkonsu: Mu sani Kur'ani mu'ujiza neb a wai kawai wannan mu'ujiza ta kebantu da lokacin sabkarsa ba .a'a mu'ujiza ne a tsawon lokaci a jiya,a yau da kuma a gobe har ranar tashin kiyama daga Allah zuwa halittunsa musamman mutum.
Na biyu mu sani wannan mu'ujiza daga Mahaliccin halittun tana karkashin ilimi daga Mabuwayi saboda haka ta shafi dukm wani zamani da guri da yanayi da halitta baki daya a sarari da teku.
Yanzu kuma lokaci ne da za mu saurari ayaya ta 15 da 16 a cikin suratul Hud kamar haka;
مَن كَانَ يُرِيدُ الْحَيَاةَ الدُّنْيَا وَزِينَتَهَا نُوَفِّ إِلَيْهِمْ أَعْمَالَهُمْ فِيهَا وَهُمْ فِيهَا لاَ يُبْخَسُونَ{15} أُوْلَـئِكَ الَّذِينَ لَيْسَ لَهُمْ فِي الآخِرَةِ إِلاَّ النَّارُ وَحَبِطَ مَا صَنَعُواْ فِيهَا وَبَاطِلٌ مَّا كَانُواْ يَعْمَلُونَ{16}
-Wadanda suke rayuwar duniya da kawace-kawacenta su ne manufarsu,to za mu bas u cikakken sakamakon ayyukansu a cikinta kuma sub a za a tauye musu komai ba. -Wadannan su ne wadanda ba su da komai a lahira sai wuta, kuma abin da suka aikata a cikinta duniyar ya saraya, kuma abin da suke aikatawa ya lalace.
Wanda ya yi imani da ranar tashin kiyama da sakama a wannan rana shi ne zai samu ladan da rabo da aka yiwa wadanda suka aika ayyukan alheri a wannan rana amma wadan bai yi imani da ranar mi'adi ranar tashin kiyama da sakamako wace fata gares hi ta samun sakamako da rabo a wannan rana dominant baki daya bas u yi imani da wannan rana ko adalcin mahalicci ba saboda haka wane rabo gare su . Wannan rana tanada muhimmanci da matsayi mai girma kuma yin imani da ita yana daga cikin shika-shikan Musulunci domin a wannan rana mai girma ranar hisabi duk abin da mutum ya aikata zai ga sakamakon abin day a aikata komin kankantarsa alheri ne ko lala.Wanda ayyukan day a aikata na alheri suka fi yawa bayan imani zai shiga gidan aljanna da aka yiwa wadanda suka aiakta alheri tanadi yayin da kuma wanda ayyukan da ya aikata na lala da sabo suka fi yawa zai samu kansa a cikin wutar Jahannawa da aka yiwa irin wadanda suka aikata aiki irin nasa ko suka ka kafircewa wannan rana tanadi. Da fatar Allah ya kiyashe mu amin.
A cikin wadannan ayoyi za mu iya ilmantuwa da fahimtar abubuwa guda uku na farko; mu sani duk wani aikin alheri da mutum ya aikata don neman abin duniya ba don Allah ba babu wani sakamako a lahira ga wanda ya aikata shi.
Na biyu; Yin adalci da aikata gaskiya a wannan duniya bayan abubuwa ne da ke kyatata rayuwar dan adam da faranta masa rai a wannan duniya zai kuma samu lada da rabo mai girma a gobe kiyama da kuma girmamawa a tsakanin mutane.
Sai kuma na ukunsu cewa; wadanda suka rungumi wannan duniya babu wani abu da za su samu a gobe kiyama kuma makomarsu wutar jahannawa ce mai tsananin kuna.
Da wannan ne kuma muka kawo karshen abubuwa da za mu iya yin bayani akansu a cikin wannan shiri nay au sai kuma mako na sama inda za ku ji mu dauke da wasu ayoyin a cikin wannan sura ta Hud kafin lokacin ni Tidjani malam lawali da na shirya kuma na gabatar na ke cewa wassalam alaikum wa rahamatullahi wa barkatuhu.
Suratu Hud, Aya Ta 17-19 (Kashi Na 343)
Jama'a masu sauraren mu barkarmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke yin dubi da nazari a irin nasihohi da galgadin da ke cikin ayoyin alkur'ani mai girma kuma babu wani abu ko madogara da tafi yin riko da alkur'ani a rayuwarmu ta yau da kullum kama daga akida, zamantakewa,tattalin arziki, ma'amala da dai sauran bangarori na rayuawa. Kuma ya kamata mu yi wa kanmu nasiha da galgadi tun kafin wani ya yi mana ko lokaci ya kure mana kuma babu wafi dacewa daga cikin kamar wanda zai yi wa kansa nasihi da galgadi da fatar Allah ya ba mu karfi da ikon yin hakan.
To madallah yanzu kuma za mu fara ne da sauraren aya ta 17 a cikin wannan sura ta Hud kamar;
أَفَمَن كَانَ عَلَى بَيِّنَةٍ مِّن رَّبِّهِ وَيَتْلُوهُ شَاهِدٌ مِّنْهُ وَمِن قَبْلِهِ كِتَابُ مُوسَى إَمَاماً وَرَحْمَةً أُوْلَـئِكَ يُؤْمِنُونَ بِهِ وَمَن يَكْفُرْ بِهِ مِنَ الأَحْزَابِ فَالنَّارُ مَوْعِدُهُ فَلاَ تَكُ فِي مِرْيَةٍ مِّنْهُ إِنَّهُ الْحَقُّ مِن رَّبِّكَ وَلَـكِنَّ أَكْثَرَ النَّاسِ لاَ يُؤْمِنُونَ{17}
Shin wanda yake a kan hujja daga Ubangijinsa,kuma shaidar haka tana biye da shi Alkur'ani .A gabaninsa kuma wanda yake abin koyi ne, kuma rahama ne,zai yi daidai da wanda ba haka ba? Wadancan suna bad a gaskiya da shi. Daga sauran kafirce da shi, to fa wuta ce makomarsa. Don haka kada ka kasance cikin kokwantonsa Alkur'ani. Hakika shi gaskiya ne daga Ubangijinka yake, sai dai yawayawan mutane ba sa bada gaskiya.
A nann ana son a tabbatar da cewa duk wanda ya dauki duniya ya mayar da ita abin burinsa ,ya huskanci kawace-kawacenta,ya kuma yi watsi da neman lahira da ni'imominta to ya sani cewa ko ya sami duniyar ko ma bai same taba, a lahira ba zai tarar da komai ba domin kuwa ba abin da ya tanada.
Bayan an ambaci wadanda suke yin ayyuka don duniya da adonta kawaio suka bar lahira a ayat da ta wuce sai kuma a wannan aya aka ambaci wadanda suke a kan tafarki na gari ,suna tsare da ayyukan da Allah yake so irin na lahira,kuma suka bi hasken Alkur'ani da littattafan da suka gabata, suna yi musu jagora. To a nan sai ayar ta ci gaba da kira ga mutum mai hankali da tsinkaya cewa; ya zamo cikin kokwanton komai game da wannan Alkur'ani, saboda shi gaskiya ne, kuma duk wata barna ba za ta taba zuwa riskar sa bat a ko'ina,don kuwa saukakke ne daga Ubangiji Gwani Mai hikima.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu kamar haka:
Na farkonsu: kasancewar sabbai na gari da masu karfin imani da sadaukar da kai da yin biyayya ga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa yana daya daga cikin dalilan da ke nuni da gaskiyar manzonnin Allah.
Na biyu mu sani ita gaskiya bat a bukatuwa da amincewar kowa ko yawancin al'umma ko a amince da ita ko a'a tana nan a matsayinta na gaskiya saboda haka ko mutane su yi imani da ma'aikin Allah da sakon da ya zo da shi ko su karyata ya rage nasu, shi dai yana kan gaskiya.
Yanzu kuma za mu saurari ayoyi na 18 da 19 a cikin wannan sura ta hud kamar:
وَمَنْ أَظْلَمُ مِمَّنِ افْتَرَى عَلَى اللّهِ كَذِباً أُوْلَـئِكَ يُعْرَضُونَ عَلَى رَبِّهِمْ وَيَقُولُ الأَشْهَادُ هَـؤُلاء الَّذِينَ كَذَبُواْ عَلَى رَبِّهِمْ أَلاَ لَعْنَةُ اللّهِ عَلَى الظَّالِمِينَ{18} الَّذِينَ يَصُدُّونَ عَن سَبِيلِ اللّهِ وَيَبْغُونَهَا عِوَجاً وَهُم بِالآخِرَةِ هُمْ كَافِرُونَ{19}
18-Kuma ba wanda ya fi zalunci kamar wanda ya kirkira wa Allah karya,wadannan za a kawo su a gaban Ubangijinsu,shedu kuma wato, Mala'iku su ce: Wadannan su ne suka yi wa Ubangijinsu karya.To la'anar Allah ta tabbata bisa azzalumai. 19-Wadanda suke toshe hanyar Allah ,suna kuma son ta karkace, su kuma masu kafircewa ne da ranar lahira.
Wadannan ayoyin Allah ya siffanta wadanda suka kafirce masa ,da siffofi iri-iri kamar kira wa Allah karyada hana bin hanyar Allah,da musanta tashin alkiyama da sauransu.Wadannan munanan halayen nasu sai Allah ya toshe basirarsu da hankulansu ya zamana ba sa jin gaskiya, ba sa kuma iya yin tunani su gane ta, ballantana ta yi musu jagora zuwa ga bin hanyar Allah, Ba shakka a lahira sun e za a ribanyawa azaba kuma su fi kowa tabewa.
A cikin wadannan ayoyi za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu kamar haka; Na farko a kullum mu rika yin takatsantsan da abin da za mu furta da sanin abin da za mu furta domin kankanan abu daga cikin abin da za mu furta na bata na iya batar da yawancin mutane kuma makiya na amfani da maganganun karya domin batar da mutane ta hanyaoyi da dama kamar kawo shubha,ko tambayoyi na yaudara domin batar da mutane ko sanya shakku a cikin lamura na hakika.
Na biyu a kullum mu kasance masu yin tunani da aiki da hankali a cikin abubuwan da za mu fada ko kuma a cikin abubuwan da muke saurare da bin gaskiya da kuma yin nisa daga bata da maganganu maras amfani.
Da wannan ne kuma muka kawo karshen abubuwa da za mu iya yin bayani akansu a cikin wannan shiri na yau sai kuma mako na sama inda za ku ji mu dauke da wasu ayoyin a cikin wannan sura ta Hud kafin lokacin ni Tidjani malam lawali da na shirya kuma na gabatar na ke cewa wassalam alaikum wa rahamatullahi wa barkatuhu.
Suratu Hud, Aya Ta 20-24 (Kashi Na 344)
Jama'a masu sauraren mu barkarmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke yin dubi da nazari a irin nasihohi da galgadin da ke cikin ayoyin alkur'ani mai girma kuma babu wani abu ko madogara da tafi yin riko da alkur'ani a rayuwarmu ta yau da kullum kama daga akida,zamantakewa,tattalin arziki,ma'amala da dai sauran bangarori na rayuawa .Kuma ya kamata mu yi wa kanmu nasiha da galgadi tun kafin wani ya yi mana ko lokaci ya kure mana kuma babu wafi dacewa daga cikin kamar wanda zai yi wa kansa nasihi da galgadi da fatar Allah ya ba mu karfi da ikon yin hakan.
To madallah yanzu kuma za mu shiga cikin shirin gadan-gadan tare da sauraren aya ta 20 a cikin wannan sura ta Hud kamar haka;
أُولَـئِكَ لَمْ يَكُونُواْ مُعْجِزِينَ فِي الأَرْضِ وَمَا كَانَ لَهُم مِّن دُونِ اللّهِ مِنْ أَوْلِيَاء يُضَاعَفُ لَهُمُ الْعَذَابُ مَا كَانُواْ يَسْتَطِيعُونَ السَّمْعَ وَمَا كَانُواْ يُبْصِرُونَ{20}
20-Wadanda ba su zamo masu gagara ba a bayan kasa, kuma ba su da wasu masu jibintar lamarinsu wadanda ba Allah ba,kuma za a ninka musu azaba. Ba za su sami damar jin gaskiya ba,ba kuma za su sami ganin ta ba.
Wadannan ayaoyin Allah ya siffanta wadanda suka kafirce masa ,da siffofi iri-iri kamar kira wa Allah karyada hana bin hanyar Allah,da musanta tashin alkiyama da sauransu.Wadannan munanan halayen nasu sai Allah ya toshe basirarsu da hankulansu ya zamana bas a jin gaskiya,bas a kuma iya yin tunani su gane ta,ballantana ta yi musu jagora zuwa ga bin hanyar Allah,Ba shakka a lahira sun e za a ribanyawa azaba kuma su fi kowa tabewa. Wannan sakamako mafi muni domin babu wata tabewa da tafi tabewar lahira muni balantana uwa uba a ce wa mutum shi ne yafi kowa tabewa a wannan rana da kowa hatta kafirai da munafikai ke nema da fatar ganin ya sami sausauci dad an linfasawa da rabuwa da damshin wani daga cikin bayun Allah da suka aikata aikin alheri a wannan duniya bayan imani da riko da dukna umarnin Allaha madaukakin sarki da kuma umarnin annabwansa da manzonninsa masu shiryar da al'umma amincin Allah ya tabbata a gare su .Da kuma nasihar waliyan Allah.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa biyu masu muhimmanci da kan iya zama darasi a rayuwarmu:
Na farko duk wani kokari ya kamata mu yi shi a wannan duniya da hakan zai taimaka mana a rayuwar gobe kiyama kuma babu wani guzuri kamar takawa da ta hadu da aikata alheriri da gujewa banna.
Na biyu: duk wata nadama mu yi ta a nan duniya da gyara kura-kuranmu a wannan duniya tun kafin lokaci ya kure mana domin a lahira babu wata dama da hanyar yin gyara.
Yanzu kuma za mu ci gaba da shirin na hannunka mai sanda da sauraren ayoyi na 21 da 22 a cikin wannan sura ta Hud:
أُوْلَـئِكَ الَّذِينَ خَسِرُواْ أَنفُسَهُمْ وَضَلَّ عَنْهُم مَّا كَانُواْ يَفْتَرُونَ{21} لاَ جَرَمَ أَنَّهُمْ فِي الآخِرَةِ هُمُ الأَخْسَرُونَ{22}
21- Wadanda sun e wadanda suka yi wa kansu hasara,abin da suke kirkira kuma ya bace musu.
22- Ba shakka su suka fi tabewa a lahira.
Jarinmu shi ne jari mafi girma da daraja domin kuwa alkawali ne daga mai duka Allah madaukakin sarki wanda ya yi wutar Jahannama haka kuma wanda ya yi aljanna mai cike da rahama da ni'imomi maras karewa.Kuma idan mun kasance muna dogaro da wani ko takama da ayyukan da muka aikata to mu san da sanin duk wani tanadi da tsimi a wannan duniya mai karewa ne kuma za mu kasance mabukata a gobe kiyama da fatar Allah ya kare mu da duk wata bukatuwa a lahira da kuma fatar Allah fanshe mud a magance mana wannan kunci mafi muni a lahira da saka mana da ni'imar da yayi wa muminai wadanda suka aikata aikin alheri.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu kamar haka:
Na farko: mun sani duk wata hasara ta kudi da makami hasara amma babu babbar asara mafi muni kamar ta rashin mutunci da dan'adamtaka.
Na biyu : Duk wata asara a wannan duniya ana iya samar da mafakarta dam aye gurbinta amma shi kwanaki idan ta wuce yawuce ba za a koma baya ba an yi asararsa har abada. Da fatar Allah ya sa mu amfanu da kwanakinmu da rayuwarmu a wannan duniya da aikata ayyukan alheri tun daga yarinta da kurciya da samartakarmu da kuma lokacin tsufarmu kuma karmu yi nadama irin ta karin maganar larabawa cewa:laitasshababa ya uda yauman.. ma'ana wani tsoho balarabe ne bayan tsufa ya kama shi yake fatar dama a ce ya koma lokacin samartakarsa bayan hurhura ta cika masa kai .har ila yau akwai nadama mafi muni da a lahira kafirai ke fatar Allah ya sake bas u wata damar ta komawa wannan duniya domin su aikata aikin alheri da yin imani amma ina bakinalkalami ya bushed a fatar kar ya bushe a kanmu duniya da lahira amin.
Sai a saurari karatun aya ta 23:
إِنَّ الَّذِينَ آمَنُواْ وَعَمِلُواْ الصَّالِحَاتِ وَأَخْبَتُواْ إِلَى رَبِّهِمْ أُوْلَـئِكَ أَصْحَابُ الجَنَّةِ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ{23}
23- Hakika wadanda suka ba da gaskiya suka yi aiki na gari, suka kuma kaskantar da kansu ga ubangijinsu to wadannan su ne yan aljanna,su masu dawwama ne a cikinta.
Bayan bayanin irin azabar da za ta sami kafirai a lahira ayoyin da suka gabata a wannan ayar kuma sai Allah ya yi wa muminai nagari albishir da irin ribar da za su samu a lahira,don ya zama sakamakon abin da suka aikata a duniya,wanda kuwa shi ne Aljannar dawwama. Ita rayuwar lahira da fadawa cikin azaba a wannan rana karshen lamari da duk wata dubara maana ko ciki gaba ni'ima har abada ko ci gaban azaba har abada .Su muminai salihai masu sadaukar da kai da kaskantar da kai ga Allah madaukakin sarki sunada rabo mai girma na har abada. Lamarin da wannan aya take jinjinawa a kansa shi ruhi na imani da wadatar zucci a dabra da haka mumuni ya gujewa duk wani abu day a shafi girman kai da dagwawa .Alhali shi kafiri munanan halayansa sun kumshi girman kai da dagwawa da kin bin umarnin mahalicci sabanin mumini mai bin umarni da tawadu'u ga Mahalicci.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa biyu na farko: aiki da abubuwa na zahiri ba su wadatarwa .kudurtawa a zucci wato niya da abubuwa na badini na taka muhimmiyar rawa wajan samun sakamako da rabo mai girma daga Allah kamar yadda hadisi ke cewa niyatul mu'umin kheirun min amalihi. Ma'ana niya da kudurtawa ta mumini da ba shi da damar aiakta wannan aikin alheri ladan da zai samu daga Allah yafi wanda idan ya aikata wannan aikin yawa a wajan Allah mai rahama.
Na biyu: Mu sani cewa su masu dagwa da kafirai a kullum ana tsauratar da su ne da zaba yayin da mutanan kwarai ana kwadaitar da sun e da karfafa masu guiwa.
Yanzu kuma za mu saurari aya ta 24 a cikin wannan sura ta Hud kamar haka;
مَثَلُ الْفَرِيقَيْنِ كَالأَعْمَى وَالأَصَمِّ وَالْبَصِيرِ وَالسَّمِيعِ هَلْ يَسْتَوِيَانِ مَثَلاً أَفَلاَ تَذَكَّرُونَ{24}
24-Misalin wadannan jama'a guda biyu mumini da kafiri kamar makaho ne da kurma da kuma mai gani da mai ji.Shin a misali za su zama daidai kuwa? To ,e ya sa ba kwa wa'azantuwa?
A wannan ayar an kwatanta makaho da mai gani da kuma da mai ji wadanda suke nuna mumini a matsayin mai ji da mai gani, kafiri kuma a matsayin makaho da kurma. Mutum mai hankali da basira ba zai kwatanta amfanin mai ji da gani da kuma kurma da makaho ba. Wancan shi ne mai amfanar kansa da waninsa wannan kuma ba zai amfana wa kansa komai ba ballantana ya amfana wa waninsa.Wannan shi ne misali mafi sauki da ke bayyana hakikar kowa ne daga cikin biyu wato Kafiri da kuma mumini .Shi Kafiri a kullum baya ganin gaskiya da kuma saurarenta alhali ga shi da ido kwado-kwado da kuma kunnuwa tabka-tabka dab a su da amfani wanda ba shi da banbanci da makaho ko kurma.Shi kuwa mumini da basirarsa yake fahimtar gaskiya da aiki da ita da kuma saurarenta saboda haka muminai sune masu gani da saurara na gaskiya sai dai kashe yawa-yawan mutane ba su fahimtar wannan gaskiya. Shi ido da kunne suna fahimtar abubuwa na zahiri kamar yadda ruhin mutum yake da ido da kunne na fahimtar abubuwa na badini.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu.
Na farko mutum da dabba kowa ne yada da kune da ido da kafa da sauran abubuwa makamantan haka amma shi mutum ya banbanta da dabba ta hanyar fahimtar abubuwa na badini dab a a iya ganinsu da abubuwa makamantan ido da saurarensu ko dafa su to amma wani hamzari ba gudu ba idan mutum ya kasa fahimtar haka ba shi da banbanci da daba koma yafi ta muni kamar yadda ayar Kur'ani da hadisai suka yi nuni.
Na biyu:hanyoyin kwatamtawa tsakanin mai kyau da maras kyau , mai muni da mai haske salon e da kur'ani yake amfani da shi da kuma yayi tasiri mai girma a rayuwa da tarbiyar al'umma a daidai ku da a jama'ance.
Da wannan ne kuma muka kawo karshen abubuwa da za mu iya yin bayani akansu a cikin wannan shiri nay au sai kuma mako na sama inda za ku ji mu dauke da wasu ayoyin a cikin wannan sura ta Hud kafin lokacin ni Tidjani malam lawali da na shirya kuma na gabatar na ke cewa wassalam alaikum wa rahamatullahi wa barkatuhu.
Suratu Hud, Aya Ta 25-27 (Kashi Na 345)
Jama'a masu sauraren mu barkarmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke yin dubi da nazari a irin nasihohi da galgadin da ke cikin ayoyin alkur'ani mai girma kuma babu wani abu ko madogara da tafi yin riko da alkur'ani a rayuwarmu ta yau da kullum kama daga akida, zamantakewa,tattalin arziki,ma'amala da dai sauran bangarori na rayuawa .Kuma ya kamata mu yi wa kanmu nasiha da galgadi tun kafin wani ya yi mana ko lokaci ya kure mana kuma babu wafi dacewa daga cikin kamar wanda zai yi wa kansa nasihi da galgadi da fatar Allah ya ba mu karfi da ikon yin hakan.
To madallah yanzu kuma za mu fara shirin da sauraren aya ta 25 da 26 a cikin wannan sura ta huda kamar haka;
وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا نُوحاً إِلَى قَوْمِهِ إِنِّي لَكُمْ نَذِيرٌ مُّبِينٌ{25} أَن لاَّ تَعْبُدُواْ إِلاَّ اللّهَ إِنِّيَ أَخَافُ عَلَيْكُمْ عَذَابَ يَوْمٍ أَلِيمٍ{26}
-Hakika kuma mun aiko annabi Nuhu zuwa ga mutanansa ya ce da su : hakika ni mai gargadi bayyananne ne a gare ku.
-Cewa kada ku bauta wa kowa sai Allah .Hakika ni ina tsorace muku azabar rana mai radadi.
Al'adar Allah ta gudana a duk lokacin day a aiko wa kafirai ayoyi da hujjoji bayyanannu to hannun manzanninsu,sannan suka karyata sai kuma ya biyar musu da wasu kassoshi na al'ummun da suka gabata da annabawansu,don su zamo masu karfafa wadannan hujjojin, don kuma su zama rarrashi ga Annabi Muhammadu mai tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka.Daga wannan aya har zuwa karshen aya ta 130 kissoshi ne na annabawa.watau su Annabi Nuhu,da Hudu da Salihu da Ibrahima da Ludu da shuaibu da Musa tsira da amincin Allah ya tabbata a gare su. Ya farad a kisser Annabi Nuhu shi da mutanansa ,yayin day a kirawo su zuwa ga bautar Allah shi kadai.Daga nan har zuwa aya ta 48 bayanin abubuwan da suka auku ne tsakaninsa da jama'arsa ne.
To wadannan ayoyi na nuni da sakonn da manzoncin da aka aiko Annabi Nuhu zuwa ga mutanansa inda ya yi kiransu zuwa ga bautawa Allah da babu wani abin bauta face shi kadai.Kuma Annabi Nuhu shi ne farkon mamzonni Ulul Azm wanda a lokacinsa shirka da bautawa gumaka ya zauna da gindinsa da yin kamari kuma bayan share shekaru koma karnoni yayi isar da sakon Allah zuwa ga mutanansa kawai yan tsurarun mutane ne suka yi imani da shi.Bayan da ya fahimci ba za su yi imani da shi ba ga bakar gallazawa da suke yi masa sai ya yi addu'a ina ruwa dubana na azaba ya sabka a kan mutane mushrikai kafirai idan ruwa azaba daga kasa yake sabka daga kasa ma yake diddigowa da hallaka mushrikai face wadanda suka yi imani. Tun farko Annabi Nuhu (AS) ya shaidawa mutanasa da galgadinsu kan su guji fushin Allah da sabkar azaba da ke biyo bayan fushin mahalicci maturkar suka bijirewa umarninsa amma tamkar ana magani kai na gaba domin kuwa babu wanda ya amsa wannan kiran nasa sai dan abin da ba za a rasa ba duk da cewa sun san kashedin annabawa gaskiya neb a wai wani abu ne na shaci fadi da jin dadin magana a'a su Annabawa da Manzonni (AS) na kashedi ne da karshen lamari kuma daya daga cikin Nauyin da ya rataya a kansu shi ne fadakarwa da wayar da kai da kuma shiryar da al'umma zuwa ga tafarki madaidaici na samun tsira duniya da lafira.
Kama daga Annabi Adama zuwa Annabi Nuhu da muke magana kan labarinsa da mutansa da kuma sauran Annaba (AS) zuwa Annabin Rahama Muhammadu Dan Abdullahu tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da kuma alayan gidansa suna fadakar da jama'a da al'ummar da aka turo su domin su samu shiriya da kubutar da su daga hanyar bata ta shirya da ke gurbata masu rayuwa duniya da lahira.Kuma ke tattare da fushin Allah a wannan duniya inda azaba ke sabka a kansu da kuma fuskantar wata azabar a gobe kiyama .Sabanin su mumunai da suka yi imani da bin umarnin Annabawa da mamzonni (AS) da aiki da sakonnni da suka zo da shi. Har ila yau Annabawa da manzonni (AS) sun e sukafi kowa hakuri domin kafin su yi wata Adduwa sai guri ya kure babu wani da zai yi imani da bin gaskiya kuma barin irin wannan kafirai da mushrikai a doran kasa za su toshe kofar imani da sauran al'umma da za su zo da kuma yayansu.
A cikin wadannan ayoyi za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu kamar haka:
Na farko al'ummar da ke cikin gafala tafi bukatuwa da yi mata galgadi da fadakarwa ko a yi sa'a ta tashi daga barci da fahimtar gaskiya.
Na biyu: Dukan annabawa da manzonni kira ne zuwa ga tauhidi na bautawa Allah shi kadai domin kubutar da jama'a daga shirka da tabewa.
Sai a sauraren aya ta 27 a cikin suratul Hud (AS)
فَقَالَ الْمَلأُ الَّذِينَ كَفَرُواْ مِن قِوْمِهِ مَا نَرَاكَ إِلاَّ بَشَراً مِّثْلَنَا وَمَا نَرَاكَ اتَّبَعَكَ إِلاَّ الَّذِينَ هُمْ أَرَاذِلُنَا بَادِيَ الرَّأْيِ وَمَا نَرَى لَكُمْ عَلَيْنَا مِن فَضْلٍ بَلْ نَظُنُّكُمْ كَاذِبِينَ{27}
- Sai manya-manya daga mutanensa,wadanda suka kafirta suka ce da shi: Mu fa mun dauke ka kawai mutum ne kamarmu,kuma ba ma ganin wani ya bi ka in ban da wulakantattun cikinmu gidadawa.Kuma ba ma ganin ku da wani fifiko a kanmu,kai muna ma tsammanin ku makaryata ne.
A tsawon tarihi haka lamarin yake ma'ana farkon masu adawa da bijirewa kiran manzonni sune shugabanni da sarakunan al'umma da suke yi wa sakon manzonni (AS) mummunan kallo da ganinta a matsayin wadda ta sabawa manufofinsu na zalunci kuma suke jin matukar aka amince da sakonnin da mamzonni suka zo da su to mutane ba za su gan su da kima da daraja ba kuma karfin fada a ji da matsayinsu a tsakanin al'ummomin da suke jan akalarta zai kawar kuma zaluncinsu ya bayyana a fili karara.Ita ma wannan aya tana nuni ne kan haka da cewa: mamyan kafirai da mushirikai sun kalubalanci da fuskantar duk wani kira na Annabi Nuhu (AS) da yin fito na fito da shi kuma sun yi ta kulla makirci na ganin mutane daga cikin al'ummar da aka turo shi zuwa gare ka ba su yi imani da shi bad a kuma yin nesa da shi.Ta hanyoyi da dama da cewa kama mutum ne kamar mu kamar kowa ,ba kafi kowa daga cikinmu bad a har za mu bi kiranka.Wannan fada tasu ba daidai take bad a fadar Annabawa da ke muma mutane ne kamarku domin korewa fadar mutane su mala'iku ko danganta wani dad an Allah daga cikinsu.Kawai bambanci Annabawa dam u su Allah ne ya aiko su da sakon shiriya kuma ta hanyar sun e za mu saurari wahayi kuma nauyi ne a kanmu mu saurari umarnin Allah ta hanyarsu da kuma irin kashedin da ke kumshe a cikin wannan sako daga Allah madaukakin sarki.
Su kafirai ba a nan suka tsaya ban a muzanta Annabawa da manzonni (AS) suna kuma muzanta da kaskantar da duk wanda ya yi imani da su. Kamar yadda kafirai ke muzantawa da kaskanta yan tsuraru da suka yi imani da Annabi Nuhu (AS) da kollonsu a matsayin kaskanci maras daraja a cikin al'umma.Alhali su maras galihu a cikin al'umma idan sun saurari da bin shiriyar Annabawa bayan sun fahimci gaskiya da shiriya a ciki da koyarwa irin ta Annabawa ya biyo bayan fahimta da hakikancewa cewa Annabawa za su kubutar da su ko shakka babu daga zaluncin azzaluma sarakunan kafirai da masu kudinsu dab a su yi masu rahama ko kadan.Wannan shi ne dalilin day a sa yawancin mau bin umarni da sakon da Allaha ya turo Annabawa da manzonni (AS) da shi suna fitowa ne daga cikin wannan gungun na mutane da a zahiri shugabannin kafirai da mushrikai ke kollonsu a matsayin kaskantun al'umma.Wani lokaci kuma masu adawa da sauraren gaskiya da shiriya na karyata Annabawa (AS) da danganta duk wani abu da za su fadawa jama'a na shiriya a karya kum asu makaryata ne da yi masu lakabi da makaryata da yin kirkira ko wani lokaci su danganta su da masu sihiri bokaye kuma duk wani abu da za su fada ba shi da daraja ko fa'ida.Kuma ta wannan salo su samu hanyar da za su sa mutane su yi nisa da Annabawa da Manzonni (AS) Amma ita gaskiya da hanya madaidaiciya ko sun ki sun so tana nan a matsayinta ba za su iya dushe haskenta ba tamkar salon maganan ne da ke cewa idan rana ta fito tafin hannu bay a kare ta to fiye da haka yake kuma ita karya da bata komi bajima ko ba dade sai ta bayyana kowa ya gane karya ce hatta yaro karami. Da fatar Allah Madaukakin sarki ya tabbatar da diga-diganmu kan tafarkin gaskiya, tafarkin Annabawa da manzonnin Allah (AS) kuma ya bam u karfin yin bara'a da mushrike da kafirai da azzalumai.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa biyu na fadakarwa kamar haka;
Na farko: su wadanda ba a shirye suke ba su bi gaskiya da yin aiki da ita ,suna bin salon cin fuska, kaskantarwa da raunana gaskiyar.
Na biyu; Su kuma wadanda bas u sarkafa kansu da wannan duniya ba sun fi saurin yin imani da kiran gaskiya na Annabawa da Manzonni (AS) kuma sune suke sahun gaba wajen jihadi da gwagwarmaya tare da sahu guda da Annabawa da Manzonni sabanin masu kallon kansu masu daraja da girman kai ko da kuwa mumunai ne. Da fatar Allah ya kiyashe mud a duk wani lamari day a shafi girman kai da jiji da kai duniya da lahira.Da kuma wannan fatar ce ni Tidjani Malam Lawali Damagaram ke cewa; wassalam alaikum wa rahmatullahi wa barkatuhu.
Suratu Hud, Aya Ta 28-30 (Kashi Na 346)
Jama'a masu sauraren mu barkarmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke yin dubi da nazari a irin nasihohi da galgadin da ke cikin ayoyin alkur'ani mai girma kuma babu wani abu ko madogara da tafi yin riko da alkur'ani a rayuwarmu ta yau da kullum kama daga akida,zamantakewa,tattalin arziki,ma'amala da dai sauran bangarori na rayuawa .Kuma ya kamata mu yi wa kanmu nasiha da galgadi tun kafin wani ya yi mana ko lokaci ya kure mana kuma babu wafi dacewa daga cikin kamar wanda zai yi wa kansa nasihi da galgadi da fatar Allah ya ba mu karfi da ikon yin hakan.
Yanzu kuma za mu fara wannan shiri da sauraren aya ta 28 a cikin suratul Hud (AS) kamar haka:
قَالَ يَا قَوْمِ أَرَأَيْتُمْ إِن كُنتُ عَلَى بَيِّنَةٍ مِّن رَّبِّيَ وَآتَانِي رَحْمَةً مِّنْ عِندِهِ فَعُمِّيَتْ عَلَيْكُمْ أَنُلْزِمُكُمُوهَا وَأَنتُمْ لَهَا كَارِهُونَ{28}
-Annabi Nuhu ya ce da su Ya mutanena,ku ba ni labari,yanzu idan na zamanto ina rike da hujja daga Ubangijina,Ya kuma ba ni rahama ita ce annabci daga gare shi,sai aka boye muku ita,yanzu ma tilasta muku karbar ta,alhali kuwa kuna kin ta?
Domin maidawa kura aniyarta bayan bakaken kalamai da batanci da nuna rashin adalci da nuna bakar tsana da kafirai da mushrikai ke nuna wa Annabi Nuhu (AS) d ace masu:idan ni mutum ne kamar ku amma ina dauke dalilai da hujja daga Mahalicci mai duka mahaliccin duk wani abu mai linfashi a doran kasa da kuma a tekun da sarari kuma ina dauke da mu'ujiza da ke gaskata duk wani abu da na ke fada da kuma ta yi daidai da maganganu na hakika.Har ila mantiki ta hankali a fili ke tabbatar da gaskiyar Allah ne ya aiko ni zuwa gare kuma domin kiran ku zuwa ga bautawa Allah abin bauta bil hakki da gaskiya shi kadai da kuma nisantar da ku daga yin shirka kuma duk wani mutum mai hankali zai iya fahimta da gaskanta wannan kira na gaskiya. Abin day a kamata ku sani da fahimta duk wani abu d azan fada da kiran ku zuwa gare shi ko zan hane ku ba daga ni yake ba kuma ba ina kiran ku ne ba zuwa gare ni a'a ina kiran ku ne zuwa ga wanda ya halicce mu duka baki daya.Allah ne ya yi mani wannan lutufi na musamman ya bani wannan matsayi na isar da sakonsa da yada addininsa ta hanyata kuma wannan it ace babbar falala da daukaki kuma wannan shi ne banbancina da ku. Sai dai wani hamzari ba gudu ba idan kuna tunanin in tilasta maku amincewa da kiran da nake yi maku ku kuma Allah mai karfi da iko da kudura ya tilasta maku da karfi yin biyayya da bin abin da na ke kiran ku zuwa gare shi to wannan kuskure ne da tunanin hakan ya sabawa hankali da hikima ta Allah.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu kamar haka:
Na farko: mu sani da'awa wato kira zuwa ga shiriya da annabawa da manzonni (AS) ke yi wa al'ummominsu kan dalili da hujjoji ne bayyanannu ba wai maganganu da suka sabawa hankali da tunani da kuma suka kauce hanya madaidaciya ta mizanin hankali da tunani.
Na biyu: Ita sunnar Allah kan dan adam haka take tun fil azal mutum yana da ikon zabar makomarsa ko alheri ko lala ,kuma yana da ikon zabar addini da mazhabarsa ba tilastawa kan haka kuma Allah bay a tilasta masa yin imani.kawaia ya rage ga mutum yin imani ko kafircewa illa iyaka yak wan da sanin zai ga sakamakon abin da ya shubka alheri ko akasin hakan.
Yanzu kuma za mu saurari aya ta 29 da 30 a cikin wannan sura ta Hud kamar haka;
وَيَا قَوْمِ لا أَسْأَلُكُمْ عَلَيْهِ مَالاً إِنْ أَجْرِيَ إِلاَّ عَلَى اللّهِ وَمَا أَنَاْ بِطَارِدِ الَّذِينَ آمَنُواْ إِنَّهُم مُّلاَقُو رَبِّهِمْ وَلَـكِنِّيَ أَرَاكُمْ قَوْماً تَجْهَلُونَ{29} وَيَا قَوْمِ مَن يَنصُرُنِي مِنَ اللّهِ إِن طَرَدتُّهُمْ أَفَلاَ تَذَكَّرُونَ{30}
- Kuma ya ku mutanena, ba na tambayar ku wata dukiya a kansa,ladana a wurin Allah kawai yake. Ni kuwa ba zan kori wadanda suka ba da gaskiya ba. Hakika su masu saduwa ne da Ubangijinsu, sai dai ni ina ganin ku mutane ne da kuke jahiltar gaskiya.
-Ya ku mutanena,wa zai kare ni daga Allah idan na kore su? Me ya sa ne ba kwa wa'aztuwa?
A cikin shirin da ya gabata mun bayyana cewa: Hadarat Nuhu ya kirayi al'ummarsa zuwa ga bautawa Allah shi kadai ,amma shugabanni da masu fada a ji da danne al'umma manyan mushrikai da kafirai na al'ummar da yake kira zuwa ga tauhidi sun yi ta kaskantar da shi da duk wani ya yi imani da shi da bayyana su a matsayin kaskantun al'umma da ba su da wani galihu a zamantakewarsu.To wadannan ayoyi na 29 da 30 a cikin wannan sura ta hud sun bas u amsa da cewa; na farko dangane da kiran da Annabi Nuhu(AS) yake yi baya bukatar wani lada ko kudi a gare ku ko saka masa da wani mukami to baya bukatar haka a gare ku. Na biyu ba dalili ne ya share matalauta da maras galihu domin ya samu yardarku saboda a wajan Allah ku ba ku da wani fifiko kansu kuma idan da za su koka a ranar tashin kiyama Annabi Nuhu (AS) ba shi da wata amsa kan hakan.Karkashin haka ya kamata ku san cewa babu wani da yafi wani a wajan Allah sai wanda yafi tsoran Allah da aiki na alheri.A karshen ayar an maida masu martani da cewa; irin wannan bukatu na kaucewa hanya suna nuni dab akin jahilci da rashin fahimtar hakikanin Allah da abubuwa na badini saboda haka kuke auna komi da ma'auni na duniya da abubuwa maras kima na duniya kuma kuke tunanin ku ne kuka fi kowa fifiko a gurin Allah.
A cikin wannan ayoyin za mu ilmantu da abubuwa guda biyu kamar haka:
Na farko: rashin neman wani lada a gurin mutane daya ne daga cikin dalilan gaskiyar Allah ne ya turo su.Kuma dalilin cin nasararsu yadda suka yi watsi da kwadayin dukiya da makami a wannan duniya.
Na biyu:Hukuma ta gaskiya kar ta danne talakkawa da maras galihu a cikin al'umma domin jan hankali dukiya da kwadayin jawo su a jika.Wafi a'ala watsi da duk wata bukata da ta sabawa hankali da tafarkin gaskiya na mizanin hankali.
To masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai kuma mako na sama da yardar Allah inda za mu ji mu dauke da wani sabon shirin na hannunka mai sanda kafin wani makon ni tidjani malam lawali damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa wassalamu aliakum warahmatullahi wa barkatuhu.
Suratu Hud, Aya Ta 31-32 (Kashi Na 347)
Jama'a masu sauraren mu barkarmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke yin dubi da nazari a irin nasihohi da galgadin da ke cikin ayoyin alkur'ani mai girma kuma babu wani abu ko madogara da tafi yin riko da alkur'ani a rayuwarmu ta yau da kullum kama daga akida,zamantakewa,tattalin arziki,ma'amala da dai sauran bangarori na rayuawa .Kuma ya kamata mu yi wa kanmu nasiha da galgadi tun kafin wani ya yi mana ko lokaci ya kure mana kuma babu wafi dacewa daga cikin kamar wanda zai yi wa kansa nasihi da galgadi da fatar Allah ya ba mu karfi da ikon yin hakan.
za mu saurari aya ta 31 a cikin suratul Hud (AS) kamar haka:
وَلاَ أَقُولُ لَكُمْ عِندِي خَزَآئِنُ اللّهِ وَلاَ أَعْلَمُ الْغَيْبَ وَلاَ أَقُولُ إِنِّي مَلَكٌ وَلاَ أَقُولُ لِلَّذِينَ تَزْدَرِي أَعْيُنُكُمْ لَن يُؤْتِيَهُمُ اللّهُ خَيْراً اللّهُ أَعْلَمُ بِمَا فِي أَنفُسِهِمْ إِنِّي إِذاً لَّمِنَ الظَّالِمِينَ{31}
31-Ba kuma zan ce da ku ina da taskokin Allah ba, ban kuma san gaibu ba,kuma ba zan ce ni malaika ne ba, ba kuma zan ce wa wadanda idanuwanku suke wulakantawa Allah ba zai bas u wani alheri ba.Allah ne ya fi sanin abin da yake zukatansu.In haka ne,to hakika na zamanto daga cikin azzalumai.
Hadarat nuhu (AS) a ci gaba da jawabinsa da kira zuwa ga al'ummarsa ya bada amsa kan bukatu maras tushe na jayayya da wasu daga cikin kafiran lokacinsa suka gabatar masa da cewa: suna jiran Annabi Nuhu (AS) ya arzuta su da tilin zinariyoyi da rarrabawa a tsakaninsu wani lokaci suna jiran ya bas u labaran gaibu da hassashen abin da za su kasance a nan gaba ko ya magance masu matsalolinsu da za su fuskanta a nan gaba. Fiya da haka kafirai sun bukaci mala'ika ya kasance tare da Annabi Nuhu (AS) ko shi Annabi nuhun ya kasance tamkar mala'ika bay a bukatuwa da cid a shad a sauran bukatu na dan adam domin a tunaninsu hakan ne zai tabbatar day a fi su fifiko a jahilcinsu.Amma Annabi Nuhu (AS) sai ya amsa masu da cewa; ni mutum ne mai rayuwa kamar kowa daga cikinku kawai banbancina da ku ,Ni Allah ne ya aiko ni da wahayi kuma ni mia isar da sako ne daga Ubangiji.Saboda haka ba ni da zinariya ko arzikin d azan baku ko ilimin gaibu sai dai kawai Abin da Ubangiji ya sanar da ni shi ne zan sanar da ku ku Allah ne mafi sanin abin da yafi alheri a gare ku.
Dangane da wadanda suka yi imani da ni kuwa b azan biya muku bukatar abin da kuka bukata ba dangane da su kuma kun yi kuskure a tunanin da kuke yi dole mumunai su kasance daga cikin mutane masu matsayi da arziki na zahiri. Kum imanin mutum shi ne abin lura ba arziki da matsayinsa ba .Allah shi ne masani abin da kowa ya boye a zucciyarsa kuma shi ne mai bayar da alheri ya kuma hana maku shi.Kuma ku sani korarsu da hana su rayuwa zalunci ne kuma ni ba zan iya yin hakan ba.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa biyu kamar haka:
Na farko:Sunnar Annabawa da manzonni (AS) haka ta gada suna kiran mutane zuwa ga shiriya da dora su kan madaidaiciyar hanya sabanin abin da manyan kabilu ke bayyanawa cewa suna kokarin jan hankulan jama'a don yawaita magoya bayansu.
Na biyu: kar mu zurfafa a soyayya da kaunar da za mu nunawa Annabawa da waliyan Allah kuma kar mu wuce gonad a iri dangane da abin da za mu fada kansu.
Sai aya ta 32:
قَالُواْ يَا نُوحُ قَدْ جَادَلْتَنَا فَأَكْثَرْتَ جِدَالَنَا فَأْتَنِا بِمَا تَعِدُنَا إِن كُنتَ مِنَ الصَّادِقِينَ{32}
32-Suka ce: Ya nuhu ,hakika ka ja da mu ,ka kuma yawaita jayayya da mu: sai ka zo mana da abin da kake yi mana narko da shi in ka zamo daga masu gaskiya.
Mutanan dab a su aiki da hankali da hujjoji idan bas u da amsar bayarwa sai su fara jayayya da jidali da maganar gaskiya da yin bankora.Masu adawa da Annabi Nuhu (AS) a maimakon yin la'akari da jawabin gaskiya kuma a fili sai suke bayyana cewa: jawabin ya isa haka idan abin da kake rayawa gaskiya ne sai ka sabkar mana da azaba.Shi suna tinani ne cewa sabkar azaba tana karkashin umarnin Annabawa da Manzonni ne.Allah ne yake da iko kan haka da sabkar da ita duk lokacin da yaga ya dace kuma tushen sakayya tana ranar tashin kiyama ne kuma duk wata azaba a wannan duniya wani dandano ne daga Allah da fatar Allah ya kiyashe mu amin.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da fadakuwa da abubuwa guda biyu na farko:dama da falala daga Allah wata dam ace ta gyara kura-kure da suka gabata ba wai ci gaba da tabka kuskure ba da yin riko da hanyar bata ko mu sakankance saboda azaba ba ta sabka ba mu ta aikata banna.
Da wannan ne kuma muka kawo karshen abubuwa da za mu iya yin bayani akansu a cikin wannan shiri nay au sai kuma mako na sama inda za ku ji mu dauke da wasu ayoyin a cikin wannan sura ta Hud kafin lokacin ni Tidjani malam lawali da na shirya kuma na gabatar na ke cewa wassalam alaikum wa rahamatullahi wa barkatuhu.
Suratu Hud, Aya Ta 33-37 (Kashi Na 348)
Jama'a masu saurare mu barkarmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na Hannunka mai sanda da a cikinsa muke yi wa kawunanmu nasiha da galgadi a harkokinmu na yau da kullum da suka shafi dukan bangarori kama daga akida ,tattalin arziki,siyasa da zamantakewa.Kuma matukar muka yi aiki da irin galgadi da nasihohin da ke cikin ayoyin kur'ani ko shakka babu za mu samu dacewa a rayuwarmu ta duniya da lahira da fatar Allah ya sa mu dace amin.
Yanzu kuma za mu fara ne da sauraren aya ta 33 da 34 a cikin wannan sura ta Hud kamar haka:
قَالَ إِنَّمَا يَأْتِيكُم بِهِ اللّهُ إِن شَاء وَمَا أَنتُم بِمُعْجِزِينَ{33} وَلاَ يَنفَعُكُمْ نُصْحِي إِنْ أَرَدتُّ أَنْ أَنصَحَ لَكُمْ إِن كَانَ اللّهُ يُرِيدُ أَن يُغْوِيَكُمْ هُوَ رَبُّكُمْ وَإِلَيْهِ تُرْجَعُونَ{34}
33-Ya ce : Ai Allah ne zai zo muku da ita in ya so,ku kuma ba za ku gagara ba.
34-Nasihata kuma ba za ta amfane ku ba ,ko da na so yi muku nasihar,idan har da ma can Allah Yana nufin ya batar da ku. Shi ne Ubangijinku,kuma wurinsa za ku koma.
A cikin shirin makon da ya gabata mu bayyana cewa masu adawa da kafircewa Annabi Nuhu (AS0 a maimakon fahimtar jawabi na hankali da karbar gaskiya sai suka shiga bankora da yin jayayya da shi har ta kai inda suke yi masa ba'a da bukatar gaggauta sabkar azabar Allah kansu a wannan duniya. Sai Annabi Nuhu (AS) ya amsa masu da cewa;Azaba ba a hannu da ikona take ba amma ku sani idan Allah ya yi niya ya sabkar da azabarsa babu wani karfi da zai kare ta kuma ba za ku iya jurewa hallaka ba. Annabi Nuhu (AS)ya ci gaba da yi masu tuni cewa shi kawai mai isar da sako da wahayin Allah ne da kuma nuna masu hanyar shiriya sauran lamura ba su hannu da ikonsa kamar yadda a cikin wannan kira na shiriya, aikinsa yi maku nasiha da galgadi da damuwa da halin da kuke ciki da nuna maku hanya madaidaiciya idan kuka kafirce da nuna taurin kai da bujirewa hanyar shiriya babu abin da zan iya yi muku na shiryar da ku.
A cikin wadannan ayoyi za mu ila ilmantuwa da abubuwa guda biyu na farko:Manzonni suna damuwa ne da kumci da al'umma ke ciki ko za ta shiga kuma salon kiran jama'a ya nuna haka inda suke gabatar masu da nasiha da wa'azi.
Na biyu: Kafirai da masu adawa kar su yi tunanin cewa idan fushin Allah da azaba ba su riske su ba a wannan duniya shi ke nan sun tsira to akwai ranar lahira ranar sakamako da makomar kowa takasance zuwa ga Allah ce.
Yanzu kuma za mu saurari aya ta 35 a cikin wannan sura ta Hud kamar haka;
أَمْ يَقُولُونَ افْتَرَاهُ قُلْ إِنِ افْتَرَيْتُهُ فَعَلَيَّ إِجْرَامِي وَأَنَاْ بَرِيءٌ مِّمَّا تُجْرَمُونَ{35}
35-A'a ko da cewa suke kagar sa ya yi ? wato Alkur'ani. Ka ce: Idan kagar sa na yi,to alhakin kagewa yana kaina ne,ni kuma ba ruwana da laifin abin da kuke aikatawa.
Daya daga cikin salon kafirai da mushrikai na juyawa kiran manzonni da annabawa (AS) baya shi ne zarginsu da karya da kirkire da cewa; duk wani abu da za ku fadi da jawabin da za ku gabatar daga gare ku ne ba daga Allah ba. Suna yin wannan zargi ne ba tare da sun gabatar da wani dalili ko da na hankali ne kuma sun sani cewa ko da sun so gabatar da wani dalili da tabbatar da gaskiyar abin da suke karyatawa ba za su iya ba.Sabanin Manzonni da tun farko sun gabatar da dalilai da mu'ujizoji da tabbatar masu da dalilan abin da suke fadi da wanda suka zo da shi gaskiya ne daga Mahalicci.Amsar da wannan ayar ta bayar kan maganganu maras tushe na kafirai da mushrikai shi ne abin da kuke dangantawa da Manzonnin Allah (AS) ba dalili ne na fakewa ba domin kuwa ko da a ce manzonni sun aikata abin da bai dace ba leifin kansu zai koma kamar yadda wadanda suka yi adawa da bijirewa kiransu leifinsu yana kansu.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa biyu na farko: mu lura a tattaunawa da masu adawa da mum u kaucewa maganganu maras kyau da batanci kuma a cikin wannan aya kur'ani yana koyar da mumunai hanya da salon fuskantar masu adawa.
Na biyu: mu sani kowa shi ne jagoran aikin da ya aikata kuma kar mu damu da adawar da wasu ke nuna mana face aikin da muke aikatawa.
Aya ta 36 da 37 a cikin suratul Hud.
وَأُوحِيَ إِلَى نُوحٍ أَنَّهُ لَن يُؤْمِنَ مِن قَوْمِكَ إِلاَّ مَن قَدْ آمَنَ فَلاَ تَبْتَئِسْ بِمَا كَانُواْ يَفْعَلُونَ{36} وَاصْنَعِ الْفُلْكَ بِأَعْيُنِنَا وَوَحْيِنَا وَلاَ تُخَاطِبْنِي فِي الَّذِينَ ظَلَمُواْ إِنَّهُم مُّغْرَقُونَ{37}
36-Aka kuma aiko wa Annabi Nuhu cewa; Ba wanda zai bada gaskiya daga mutanenka sai wadanda suka riga suka bada gaskiya.To kada ka yi bakin ciki game da abin da suke aikatawa.
37-Ka kuma sassaka jirgin ruwa tare da kularmu da koyarmu,kada kuma ka yi mini maganar komai game da kafirai.Hakika su nutsar da su za a yi.
Karkashin ayoyin kur'ani mai girma ya kwashe kusan shekaru dubu daya yana kiran al'ummarsa zuwa ga Allah Ubangijin talikai amma a tsawon wannan shekaru yan tsuraru ne suka yi imani da shi har lokacin da wahayi daga Ubangijin talikai ya zo masa cewa daga yanzu babu wani da zai yi imani da kai kuma azabar Allah za ta sabka babu makawa kan kafirai.Wannan azaba ita ce zuba da diddigowar ruwan dufana da yin ambaliyar ruwan azaba kuma babu wani guri na tsira da kubuta daga wannan azaba face shiga cikin wannan jirgin ruwa da Annabi Nuhu (AS) ya kera da hannunsa karkashin umarnin Allah madaukakin sarki kamar yadda wannan aya ke nuni kuma shi da mumunai da suka yi imani da shi sun shiga wannan jirgi inda Allah ya kubutar da su da azabar Dufana su kuma kafirai da mushrikai suka hallaka.
A tsawon shekaru kusan dubu da Annabi Nuhu (AS) ya yi yana kiran al'ummarsa zuwa ga yin riko da addinin Allah tabaraka wata'ala bai ga jib a ya ci gaba da kokarinsa na ganin ya shiryar da al'ummarsa domin samin tsira duniya da lahira da yin dace da gidan aljannar da aka yiwa wadanda suka yi imani tanadi. Yayin da a dabra da haka aka yi wa wadanda suka kafirta da yin riko da shirka tandai da wutar jahannama da kuma makomarsu duniya da lahira ta munana da yin nadama a ranar da duk wata nadama bata da wani amfani saboda babu wata hanya ko dama ta gyara kayanka da mutum zai samu.A nana bin koyi ne ga malamai magadan Annabawa da kuma masu ayyukan tabligi na yada addinin Musulunci da ayyukan alheri kamar umarni da kyakkyawa da hana da mummuna da su ci gaba da yin aikin da suka saba ba tare da nuna kasawa ba kamar yadda kakanmu Annabi Nuhu (AS) ya yi shekarau masu yawa shekara daya na bin daya har shekara dubu dari tara da hamsin yana kiran al'ummarsa zuwa ga Allah madaukakin sarki babu kasawa duk da duka,azabtarwa da tsangwamamkaskantarwa da karyata shi da duk wani nau'I na azaba babu wadda bai gani ba daga mushrikan al'ummarsa. Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah da iyalan gidansa tsarkaka haka ya yin a hakuri da duk wani nauyin azaba da mushirikan birnin Makka suka nuna masa lokacin day a zo masu da hasken addinin Musulunci da kiransu zuwa shiriya duniya da lahira amam suka bijire masa da yin watsi da wannan kira nasa da kuma bin duk hanyoyi na azabtarwa da kutata masa amma ba tare da ya nuna kasawa daidai da kwayar zarra.
A cikin wannan ayoyi za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda uku:
Na farko: shi mutum wani lokaci na fadawa cikin wani yanayi mai muni da babu fatar kubutar da shi ko yi masa jawabi da galgadin da zai yi tasiri kansa har ya gyara halinsa hatta addu'a bata aiki a kansa.
Na biyu:Manzonni ba wai kawai suna dogara da jawabai da tabligi wajan shiryar da jama'a a'a suna aiki da duk salon day a dace domin kubutar da jama'a da al'ummarsu kamar kera jirgin ruwa da Annabi Nuhu (AS) don kubutar da wadanda suka yi imani da shi yayin da kafirai suka hallaka a ruwan dufana.
Na uku: Azabar Allah tana sabka ne kan wadandan suka aikata laifi da sabo .
Da wannan ne kuma muka kawo karshen abubuwa da za mu iya yin bayani akansu a cikin wannan shiri nay au sai kuma mako na sama inda za ku ji mu dauke da wasu ayoyin a cikin wannan sura ta Hud kafin lokacin ni Tidjani malam lawali da na shirya kuma na gabatar na ke cewa wassalam alaikum wa rahamatullahi wa barkatuhu.
Suratu Hud, Aya Ta 38-41 (Kashi Na 349)
Jama'a masu saurare barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hanunnka mai sanda, shirin da a cikinsa muke yin bayani da dubi a cikin ayoyin alkur'ani mai girma da domin ya zama jagora a rayuwar ta dukkan bangarori .Kuma babu wani littafi da hanyar da tafi yin riko da alkur'ani da kuma tafarkin ma'aikin Allah tsira da aminci ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka kuma ko shakka babu duk wanda ya yi riko da wadannan abubuwa biyu zai samu tsira da dacewa duniya da lahira bugu da kari ya samu sauki da walwala a rayuwarsa ta wannan duniya da samin hisabi mai sauki a ranar da tsanani da kunci da damuwa ya lullube zukata da tunanin kowa. Da fatar Allah ya lullube mud a rahama da lutifinsa duniya da lahira amin.
Ga karatun ayoyi na 38 da 39:
وَيَصْنَعُ الْفُلْكَ وَكُلَّمَا مَرَّ عَلَيْهِ مَلأٌ مِّن قَوْمِهِ سَخِرُواْ مِنْهُ قَالَ إِن تَسْخَرُواْ مِنَّا فَإِنَّا نَسْخَرُ مِنكُمْ كَمَا تَسْخَرُونَ{38} فَسَوْفَ تَعْلَمُونَ مَن يَأْتِيهِ عَذَابٌ يُخْزِيهِ وَيَحِلُّ عَلَيْهِ عَذَابٌ مُّقِيمٌ{39} حَتَّى إِذَا جَاء أَمْرُنَا وَفَارَ التَّنُّورُ قُلْنَا احْمِلْ فِيهَا مِن كُلٍّ زَوْجَيْنِ اثْنَيْنِ وَأَهْلَكَ إِلاَّ مَن سَبَقَ عَلَيْهِ الْقَوْلُ وَمَنْ آمَنَ وَمَا آمَنَ مَعَهُ إِلاَّ قَلِيلٌ{40} وَقَالَ ارْكَبُواْ فِيهَا بِسْمِ اللّهِ مَجْرَاهَا وَمُرْسَاهَا إِنَّ رَبِّي لَغَفُورٌ رَّحِيمٌ{41}
38- Ya kuma rika sassaka jirgin,duk sanda kuma wasu shugabanni daga mutanensa suka wuce ta wajansa sai suka rika yi masa ba'a.ya ce idan kun yi mana ba'a,to ba shakka muma wata rana za mu yi muku ba'a kamar yadda kuke yi mana ba'ar.
39- To bad a dadewa ba za ku san wanda azaba mai kunyatarwa za ta zo masa a duniya,kuma wata azaba madawwamiya ta saukar masa a lahira.
40-Har dai zuwa lokacin da umarninmu ya zo,kuma tanderu ya bubbugo da ruwa,Muke ce : Ka dauki ma'aura bibbiyu,daga kowace halitta a cikinsa jirgin hade da iyalinka ina ban da wanda maganar halakar da shi ta gabata a kansa watau dansa kan'ana da matarsa da kuma wadanda suka bad a gaskiya su ma a dauke su.Ba kuwa wadanda suka bad a gaskiya da shi sai yan tsirari.
41-Ya kuma ce:Ku shiga cikinsa.Bismillahi ne tafiyarsa,shi ne kuma tsayawarsa,Hakika Ubangijina Mai gafara e mai rahama.
Lokacin da a zaba ta sabka kan mutanan annabi Nuhu ya kirayi mumunai da suka yi imani da shi kan su shiga cikin jirgin haka kuma suka yi yayin da kafirai dab a su shiga ba cikin jirgin day a kera suka hallaka.Su kuwa mumunai suka samu tsira tare da shi.Kamar yadda ya zo a cikin ruwaya duk wanda ya bi tafarkin ma'aiki da iyalan gidansa tsarkaka tamkar jirgin Annabi Nuhu (AS) duk wanda ya shiga ya tsira wanda kuwa bai shiga bay a hallaka.Kuma girgin yak era shi ne da tashinsa da sunan Allah da kuma tsayuwarsa.
A cikin wannan ayar za mu ilmantu da abubuwa biyu.
Na farko duk aikin da mutum zai fara ya farad a sunan Allah ya kuma kare shi da gode masa.
Na biyu:Fatar bismillahi a farkon aiki wata sunna ce ta Annabawan Allah sai mu yi koyi da haka.
Da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin nay au kafin wani mako da yardarm Allah mai ikon linfashin taliakai ,ni tidjani malam Lawali damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barkatuhu.
Suratu Hud, Aya Ta 42-44 (Kashi Na 350)
Jama'a masu saurare barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hanunnka mai sanda ,shirin da a cikinsa muke yin bayani da dubi a cikin ayoyin alkur'ani mai girma da domin ya zama jagora a rayuwar ta dukkan bangarori .Kuma babu wani littafi da hanyar da tafi yin riko da alkur'ani da kuma tafarkin ma'aikin Allah tsira da aminci ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka kuma ko shakka babu duk wanda ya yi riko da wadannan abubuwa biyu zai samu tsira da dacewa duniya da lahira bugu da kari ya samu sauki da walwala a rayuwarsa ta wannan duniya da samin hisabi mai sauki a ranar da tsanani da kunci da damuwa ya lullube zukata da tunanin kowa. Da fatar Allah ya lullube mud a rahama da lutifinsa duniya da lahira amin.
Sai karatun aya ta 42
وَهِيَ تَجْرِي بِهِمْ فِي مَوْجٍ كَالْجِبَالِ وَنَادَى نُوحٌ ابْنَهُ وَكَانَ فِي مَعْزِلٍ يَا بُنَيَّ ارْكَب مَّعَنَا وَلاَ تَكُن مَّعَ الْكَافِرِينَ{42}
42_Shi Kuma jirgin yana tafiya da su cikin rakuman ruwa kamar duwatsu,Annabi Nuhu kuwa sai ya kirawo dansa yak o zamanto a ware waje daya yace: Kai dan nan ,hawo man ka zamo tare dam u,kada ka zama tare da kafirai.
A shirin da ya gabata mun kawo labarin azabar da ta sabka kan kafirai daga cikin mutanan Annabi nuhu (AS) masu jayayya da fito da kafirci afili da yadda suka hallaka a azabar ruwan dufana to ita ma wannan ayar ci gaban ayar da ta gabata da ke bayani kan yadda dan annabi Nuhu (AS) ya hallaka da kin karbar shiriya da kiran da ma'aifinsa ya yi masa ya kuma kasance tare da kafirai suka hallaka. A cikin wannan ayar za mu iya ilmantuwa da abubuwa biyu:
Na farko : Uwaye nada nauyi mai girma a kansu dangane da tarbiyar yayansu a rayuwa irin ta zamantakewa. Na biyu: Aikin mutum shi n eke bayyana da su yake tare kamar yadda hatta dan annbi daga karshe an fahimci da suwa yake ta fuskar aiki da hallaka tare da su.
A saurari aya ta 43 a cikin suratul Hudu kamar haka:
قَالَ سَآوِي إِلَى جَبَلٍ يَعْصِمُنِي مِنَ الْمَاء قَالَ لاَ عَاصِمَ الْيَوْمَ مِنْ أَمْرِ اللّهِ إِلاَّ مَن رَّحِمَ وَحَالَ بَيْنَهُمَا الْمَوْجُ فَكَانَ مِنَ الْمُغْرَقِينَ{43}
43- Dan y ace: Ai zan fake ne a wani dutse wanda zai kare ni daga rowan .Annabi Nuhu y ace : Yau kam babu wani mai kariya daga al'amarin Allah sai dai wanda ya yi wa rahama kawai.Sai rakumin ruwa ya shiga tsakaninsu,ya zamanto cikin wadanda suka nutse.
A maimakon ya karbi kira da shiryarwar ma'aifinsa ya komo daga rakiyar kafire da kafirci ta hanyar shiga wannan jirgin ruwa shiriya ,kuma a maimakon ya yi dogon tunani da nazari kan jawabi da nasihar ma'aifinsa sai ya nace da yin riko da hanyar bata da hassashen cewa idan yah au kan kololuwar dutse zai samu kubuta da tsira daga fushin Allah.Lamarin day a wakana sabanin bakin tunaninsa ne ya kuma manta da cewa hatta dutsen da ya nemi mmakewa da shi yana karkashin umarnin Allah ne kuma idan Allah ya so dutsen day a hau mai tsawo zai kasance sanadiyar hallakarsa ne. Kuma tattaunawar da yake yi da ma'aifinsa bat a kare ba sai iggiyar ruwa ta zo ya nitsar da shi da hallakar da shi tare da sauran kafirai da mushrikan mutanan Annabi Nuhu (AS).
A cikin wannan aya ta 43 a cikin suratul hudu za mu iya ilmantuwa da abubuwa uku kamar haka:
Na farko: al'adam mutum ce idan ya fuskanci hadari yana kadaita Allah da neman taimakonsa,amma a kokarinsa na neman mulki da jin dadin abubuwan zahiri da na madda a wannan duniya sai ya rungumi hanyar yin shirka. Na biyu: Dabi'ar ruwa it ace rayawa amma karkashin umarnin Allah ya hallakar da mutanan Nuhu da suka kafirce wa bin umarnin Allah.
Sai kuma na ukunsu shi ne; a tsari irin na adalci azabtar da wanda ya kafirce ko sakawa wanda ya aika alheri daga Allah ,ba shi da dangantaka ko tasirin dangantaka ta jinni.idan dan ma'aiki ya kasance kafiri daya ne dad an kafiri ya ya kafircewa Allah zai azabtar da shi kamar kowa babu banbanci wannan shi ne adalci.
To madalla to za mu ci gaba da shirin nay au da sauraren aya ta 44 a cikin wannan sura ta Hudu:
وَقِيلَ يَا أَرْضُ ابْلَعِي مَاءكِ وَيَا سَمَاء أَقْلِعِي وَغِيضَ الْمَاء وَقُضِيَ الأَمْرُ وَاسْتَوَتْ عَلَى الْجُودِيِّ وَقِيلَ بُعْداً لِّلْقَوْمِ الظَّالِمِينَ{44}
44-Aka ce : ke kasa ,ki hadiye ruwanki,aka kuwa kafar da rowan, kuma aka gama al'amrin,jirgin kuma ya tsaya a kan dutsen judiyu,aka kuma ce: Can dai ga mutane wadanda suke azzalumai.
Wannan aya tana bayani abin da ya wakana a tarihi ne inda a lokacin Annabi Nuhu (a.s) daya daga cikin annabawa da manzonnin Allah masu daraja azabar Allah ta afkawa mutanansa da suka kafirce inda ambaliyar rowan azaba ta Dufana mai girma ta wanke kasa daga kafirci da shirka kuma bayan afkuwear wannan azaba da wanke doran kasa daga shirka ,kwanciyar hankali da ni'ima suka maye gurbinsu kuma zuriyar mumunai ta ci gaba da rayuwa a doran kasa a wannan guri da jirgin Annabi Nuhu (AS) ya tsaya tare da zuriyar da ke cikinsa. Malaman tafsiri sun samu sabani kan wannan guri da jirgin Annabi Nuhu (AS) ya tsaya wasu na cewa ne an a duwatsun Ararat da ke kasar Turkiya ne yayin da wasu kuwa ke cewa; yana nan a kewayen yankin Mausul na kasar Iraki wasu ma cewa suke yi ya wani guri ne na daban. Amma muhimmi kowa ya yai ammanar lamarin ya abku kuma Alkur'ani mai ya ambato da suna fushin Allah kan wadanda suka kafircewa umarninsa daga cikin mutanan Annabi Nuhu (AS) kuma ya zame mana darasi da sanin cewa abubuwan dabi'a kamar ambaliyar ruwa,girgizar kasa na iya zama alama ta fushin Allah a wannan duniya. A dabra da haka ta fuskar adabi da kuma masanan addabin larabci wannan aya tana daya daga cikin ayoyi mafi balaga da fasaha daga cikin ayoyin kur'ani domin a cikin wannan gajeriyar aya an yi bayani babban lamari mai girma day a abku a tahiri.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu kuma sune :
Na farko:Sammai da kasai suna karkashin kulawa da umarnin Allah tabaraka wata'ala kuma Allah ne mai hukumci kan dokokin dabi'a da wanzar da dabi'a a doran kasa.
Na biyu:Ta hanyar hallaka azzalumai bay a nufin zalunci da danniya da babakere sun kawar ba ne a'a ana bukatar ci gaba a tsawon tarihi da yin bara'a da ayyukan zalunci da azzalumai.
Da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin nay au kafin wani mako da yardarm Allah mai ikon linfashin taliakai ,ni tidjani malam Lawali damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barkatuhu.
Suratu Hud, Aya Ta 45-49 (Kashi Na 351)
Jama'a masu saurare barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hanunnka mai sanda, shirin da a cikinsa muke yin bayani da dubi a cikin ayoyin alkur'ani mai girma da domin ya zama jagora a rayuwar ta dukkan bangarori .Kuma babu wani littafi da hanyar da tafi yin riko da alkur'ani da kuma tafarkin ma'aikin Allah tsira da aminci ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka kuma ko shakka babu duk wanda ya yi riko da wadannan abubuwa biyu zai samu tsira da dacewa duniya da lahira bugu da kari ya samu sauki da walwala a rayuwarsa ta wannan duniya da samin hisabi mai sauki a ranar da tsanani da kunci da damuwa ya lullube zukata da tunanin kowa. Da fatar Allah ya lullube mud a rahama da lutifinsa duniya da lahira amin.
To madallah yanzu kuma za mu fara shirin a yau da sauraren aya ta 45 da 46 a cikin suratul Hudu (AS) kamar:
وَنَادَى نُوحٌ رَّبَّهُ فَقَالَ رَبِّ إِنَّ ابُنِي مِنْ أَهْلِي وَإِنَّ وَعْدَكَ الْحَقُّ وَأَنتَ أَحْكَمُ الْحَاكِمِينَ{45} قَالَ يَا نُوحُ إِنَّهُ لَيْسَ مِنْ أَهْلِكَ إِنَّهُ عَمَلٌ غَيْرُ صَالِحٍ فَلاَ تَسْأَلْنِ مَا لَيْسَ لَكَ بِهِ عِلْمٌ إِنِّي أَعِظُكَ أَن تَكُونَ مِنَ الْجَاهِلِينَ{46}
45- Annabi Nuhu kuma ya kira Ubangijinsa sai y ace: Ya Ubangijina,hakika dana day a nutse yana daga iyalina,hakika kuma alkawarinka gaskiya ne ,kuma kai ne kafi kowa iya hukunci. 46-Allah Y ace: Ya nuhu,hakika shi bay a daga cikin iyalinka.Hakika shi rokokn naka aiki ne marar kyau,to kada ka kara tambaya ta abin dab a ka da sani a kai,hakika Ni ina gargadin ka da zamnatowa cikin jahilai.
A shirin da ya gabata mun bayyana cewa; dan annabi Nuhu ya kid a hau jirgin rowan da ma'aifinsa yak era domin kubutar da wadanda suka yi imani da shi daga azabar rowan dufana kan haka ya hallaka da nucewa a cikin rowan azaba kamar sauran kafirai. To wadannan ayoyi na bayani ne kan tunin da Annabi Nuhu (AS) ya yiwa mahaliccinsa masanin abin da yake boye alkawalin day a yi masa da cewa; Allah ka yi mani alkawalin za ka tsiratar da iyalina wato Ahlina kuma ni na san alkawalinka gaskiya ne saboda haka mene ne yasa dana da yake daya daga cikin iyalaina ya nuce da hallaka a cikin ruwa. Nan ne sai Allah ya amsa ma Annabi Nuhu (AS) da cewa; Alakawali na gaskiya ne amma abin day a kamata ka sani danka bay a cikin iyalaika wato Ahlinka saboda bai yi imani ba kuma yana tare ne da mutane kafirai da baranta daga mutane salihai.Yadda Annabi Nuhu (AS) ya yi wannan tambaya da amsar da Allah ya ba shi na nuni da cewa kafin haka bai fahimci dansa yana daga cikin jerin mutanan da suka kafirce masa ba sai bayan ya nuce da hallaka ya fahimci abin da dansa yake shibkawa a cikin zucciyarsa. Kuma dalilin ken an day a say a bukaci dansa ya hau jirgin ruwa duk da an umarce su da ya umarci mumunai kawai su hau wannan jirgin jiriya.Hatta lokacin da dansa ya bijirewa wannan kira nasa nay a hau jirgin shiriya bai yi masa lakabi da yi masa hannunka mai sanda da cewa kar ka kasance daga cikin kafirai sai dai y ace masa kar ka yi wa kafirai rakiya karkashin haka ne Allah masani mabuwayi ke cewa Annabi Nuhu (AS) kar ka bukaci abin dab a ka sani ba domin wannan salon e na jahiliya.
To madallah a cikin wadannan ayoyi za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda hudu kamar haka na farko: Dangantakar imani ta fi dangantakar jinni ,wadanda suka yi imani da amsa kiran Annabi Nuhu (AS) sun samu tsira yayin da dan Annabi Nuhu day a kasance daga cikin kafirai da suka kafircewa kiran ma'aifinsa ya zamanto ba daga cikin ahlinsa kuma bai samu tsira ba.
Na biyu: a al'adar Mahalicciimani shi ne sama da mafi daraja da yan uwantaka na jinni saboda haka babu wani fifiko kasancewar mutum dan Annabi ko waliyin Allah face fifiko na imani da aikin da Allah da ma'aikinsa suka yarda da umurta kansa.
Na uku: Mu sani cewa lokacin da muka daga hannu muna addu'a da neman wani abu daga Allah idan bai amsa mana ba kar mu yi fushi da bata rai domin Allah ne ya san abin da bam u sani ba kuma ya san abin da yafi mana alheri duniya da lahira.
Na hudu: shi dan adam yana da zabi karkashin haka ne ko dad a matar annabi ko waliyin Allah da shekhin malami ba a tilasta masu yin imani kuma haka lamarin yake dan babban kafiri da mishriki na iya zama waliyin Allah da yin imani da umarnin Allah da ma'aikinsa bayan ya yi wa mummunan tafarkin ma'aifinsa na kafirci.
A saurari aya ta 47 a cikin suratul Hud:
قَالَ رَبِّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ أَنْ أَسْأَلَكَ مَا لَيْسَ لِي بِهِ عِلْمٌ وَإِلاَّ تَغْفِرْ لِي وَتَرْحَمْنِي أَكُن مِّنَ الْخَاسِرِينَ{47}
-Ya ce: Ya Ubangiji,hakika ni ina neman tsarinka a kan in tambaye ka abin dab a ni da sani a kai,idan kuwa ba ka yafe mini ba,ka kuma ji kai na ,to zan zamo cikin wadanda suka yi asara.
Bayan da Annabi Nuhu (AS) ya ji amsa daga Mahalicci masanin abubuwan da ke boye a cikin zukata da tunani halittunsa sai ya nemi gafara daga bukatar abin dab a ya da sani kansa da kuma bai dace ba ya bukaci hakan don haka nan take ya nemi gafara da rahamar mahaliccinsa. Saboda manzonni da Annabawa (AS) sun sani dole ne lokacin sauraren wa'azi daga Allah madaukakin sarki sun yi ladabi da tawadu'u da mika wuya dari bias dari.dalili Ubangijin talikai shi ne shi ne masanin alheri da maslahar kowa da komi kuma masanin komi da kowa kuma tafiyar da lamura suna karkashin hikimarsa da maslaha ko da kuwa hakan ya buya a gare mu.
A cikin wannan aya ta 47 a cikin suratul Hudu za iya ilmantuwa da muhimman abubuwa guda biyu.
Na farko :tuba da neman gafarar Ubangiji hanya ce da ke bawa mutum tabbaci da lamani a duk lokacin da ya fuskanci tsanani da damuwa da wahalhalu da kuma zai iya fuskanta a nan gaba.
Na biyu:Hatta manzonni da annabawa ba za su iya isa da inda suka tunkara da cimma burinsu face da taimako ,lutifi da kuma rahamar Allah kuma mu sani babu wani mahaluki da aka haramta ma wannan falala da fatar Allah a kullum ko tsanani ko cikin wadata Ya albarkace mu da taimako,rahama da lutifinsa da kuma yi mana gafara duniya da lahira.
Yanzu kuma za mu saurari aya ta 48 da kuma ta 49 a cikin wannan sura ta hud kamar haka:
قِيلَ يَا نُوحُ اهْبِطْ بِسَلاَمٍ مِّنَّا وَبَركَاتٍ عَلَيْكَ وَعَلَى أُمَمٍ مِّمَّن مَّعَكَ وَأُمَمٌ سَنُمَتِّعُهُمْ ثُمَّ يَمَسُّهُم مِّنَّا عَذَابٌ أَلِيمٌ{48} تِلْكَ مِنْ أَنبَاء الْغَيْبِ نُوحِيهَا إِلَيْكَ مَا كُنتَ تَعْلَمُهَا أَنتَ وَلاَ قَوْمُكَ مِن قَبْلِ هَـذَا فَاصْبِرْ إِنَّ الْعَاقِبَةَ لِلْمُتَّقِينَ{49}
- Aka ce: Ya Nuhu,ka sauka cikin aminci daga gare Mud a albarka a gare ka da kuma ga al'ummomin da suke tare da kai .Wasu al'ummun kamu za mu jiyar da su dadi,sannan kuma azaba mai radadi daga gare mu ta same su. - Wadannan suna daga labaran gaibu da Muke yi maka wahayi da su,don kai da mutanenka ba ku san su ba,kafin wannan labarin ,sa ka yi hakuri,hakika kyakkyawan karshe yana ga masu tsoron Allah.
Bayan da ruwa ya mamaye doran kasa da kuma shayewar ruwa karkashin umarnin Allah da kuma tsayuwar jirgin rowan tsira, sai Annabi Nuhu (AS) da halittun da ke tare da shi suka ce: mun wadatu da ni'ima da albarkar Allah kuma kowane daga cikin wannan halitta ya zamanto tushen al'ummar da za ta zo bayansa.Kuma babban abin lura a nan shi ne kamar yadda yazo dangane da Annabi Adam (AS) ya zo kan Annabi Nuhu (AS) cewa; Annabi Nuhu (AS) shi ne uban al'umma na biyu a wannan zamani kuma bayansa ne yan adam suka rarrabu gida biyu mumunai da kuma kafirai kuma haka lamarin ya ci gaba han wannan lokaci da muke ciki.
A cikin wadannan ayoyin na suratul Hudu za iya ilmantuwa da muhimman abubuwa guda uku . Na farko: mu sani ni'imomin da mumuni ke samu a rayuwarsa suna kara masa karfi lafiya da albarka ne amma shi kafiri suna kara masa son duniya da dauwama a cikinta da kara nutsewa cikin duhun sabo da banna.
Na biyu; hakuri da juriya shi ne tushen cin nasarar da Annabi Nuhu (AS) inda ya yi hakuri da takurawar kafiran mutanansa na tsawon karnoni inda daga karshe ya ci nasara
Na uku: Allah madaukakin sarki da hikima ba ya lissafin wadanda ke son duniya da jin dadinta a cikin jerin kafirai ,sai dai sunnar Allah ce ta hanayr ni'imarsa ya bawa kowa damar aikata abin day a zaba wa kansa ko alheri ko kafircewa ni'imarsa kuma duk wanda ya gode masa zai kara masa ni'imarsa. Allah mun gode maka da wannan ni'ima da ka wadatar dam u ta samu cikin jeri mumunai da musulmi mabiya zuriyar ma'aikinka Muhammadu dan abdullahi tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa da kuma ka sanya mu cikin jerin limaman tsirara da fatar Allah ka dauwamar da mu a kan wannan tafarki madaidaici amin ko ta shirya da duk bayunka kan tafarki madaidaici amin.
A nan ne kuma ya kamata in dakata saboda lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe sai kuma mako na sama da yardarm Allah za ku ji mu dauke da wani sabon shirin kafin lokacin Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa; wassalam alaikum warahmatullahi wa barkatuhu.
Suratu Hud, Aya Ta 50-56 (Kashi Na 352)
Jama'a masu saurare barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hanunnka mai sanda ,shirin da a cikinsa muke yin bayani da dubi a cikin ayoyin alkur'ani mai girma da domin ya zama jagora a rayuwar ta dukkan bangarori .Kuma babu wani littafi da hanyar da tafi yin riko da alkur'ani da kuma tafarkin ma'aikin Allah tsira da aminci ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka kuma ko shakka babu duk wanda ya yi riko da wadannan abubuwa biyu zai samu tsira da dacewa duniya da lahira bugu da kari ya samu sauki da walwala a rayuwarsa ta wannan duniya da samin hisabi mai sauki a ranar da tsanani da kunci da damuwa ya lullube zukata da tunanin kowa. Da fatar Allah ya lullube mud a rahama da lutifinsa duniya da lahira amin.
A sauraren aya ta 50:
وَإِلَى عَادٍ أَخَاهُمْ هُوداً قَالَ يَا قَوْمِ اعْبُدُواْ اللّهَ مَا لَكُم مِّنْ إِلَـهٍ غَيْرُهُ إِنْ أَنتُمْ إِلاَّ مُفْتَرُونَ{50}
50- Haka kuma mun aiko wa adawa dan uwansa Hudu, yace: Ya ku mutanena,ku bauta wa Allah,ba ku da wani Ubangiji waninsa, ba abin da kuke yi sai kirkira karya kawai.
Bayan a shirin da ya gabata muka kawo karshen ayoyin da suke Magana kan kissar Annabi Nuhu (AS) da kuma mutanansa to a cikin wannan aya za mu fara ne da bayani kan kisser Annabi Hud (AS) da mutanansa kuma dalilin day a sama wannan sura aka sanya mata sunan Hud .Karkashin ruwayoyi masu inganci lokacin da Annabi Nuhu (AS) zai yi bankwana da wannan duniya sai ya shaidawa mutanasa da suka yi imani da shi cewa; bayana za a samu tazara da mutane za su koma ga bautawa gumaka da aikata sabo har zuwa lokacin da Allah madaukakin sarki zai aiko wani manzo daga zuriyata mai suna Hud da zai kubutar da tsiratar da jama'a da kiransu zuwa ga bautawa Mahalicci.
A cikin wannan aya ta 50 a cikin suatul Hud za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu masu muhimmanci kamar haka;
Na farko: kira zuwa ga tauhidi da kadaita Allah shi abin da kiran Annabawa da manzonni baki daya ya kumsa,Sun kirayi mutane da al'ummomi zuwa ga Allah da kadaita bauta a gare shi.
Na biyu:yin shirka ga Allah wani nau'I ne na tuhuma da kirowa ga Allah kuma alama ce da ake dangantawa da kasawarsa wajan jan akalar duniya sai ya nemi abokin tarayya da yin haka babban sabo ne mai girma.
To madallah yanzu kuma za mu saurari ayoyi na 51 da 52 a cikin wannan sura ta hud:
يَا قَوْمِ لا أَسْأَلُكُمْ عَلَيْهِ أَجْراً إِنْ أَجْرِيَ إِلاَّ عَلَى الَّذِي فَطَرَنِي أَفَلاَ تَعْقِلُونَ{51} وَيَا قَوْمِ اسْتَغْفِرُواْ رَبَّكُمْ ثُمَّ تُوبُواْ إِلَيْهِ يُرْسِلِ السَّمَاء عَلَيْكُم مِّدْرَاراً وَيَزِدْكُمْ قُوَّةً إِلَى قُوَّتِكُمْ وَلاَ تَتَوَلَّوْاْ مُجْرِمِينَ{52}
-Ya ku mutanena, ba na tambayar ku wani lada game da shi wannan sako,ladana dai yana ga wanda ya halicce ni .Yanzu ba za ku hankalta ba ?. - Kuma ya ku mutanena, ku nemi gafarar Ubangijinku sannan ku tuba gare shi,zai sauko muku da makadin (ruwhin) sama,zai kuma kara muku karfi a kan karfinku,kada kuma ku ba da baya kuna masau aikata laifi.
A ci gaba da kira zuwa ka gadaita Allah da bauta da kuma yin bara'a ga ayyukan shirka da bautawa gumaka,Annabi Hud (AS) ya bukaci al'ummarsa da su ringumi istigfari da yin tuba domin tsarkake doran kasa daga ayyukan sabo da gurbacewa ayyukan sabo ,bayan haka rahamar Allah ta sabka a doran kasa. Karkashin wannan aya yin tuba daga aikata sabo yana daya daga cikin abubuwan da ke kawar da fari da wahala da kuma ke sanadiyar sabkar rowan sama daga sama da sai kara arziki da wadata ga mutane da dabbobi da sauran halittu.Tattalin arzikin mutane ya binkasa a samu cimakada wadatar abinci da ta dabbobi da tsirre. A takaice yin tuba daga aikata sabo yana tasiri a wannan rayuwa ta duniya ya samu wadata ta arziki da kuma samin tsira da sauki a rayuwar gobe kiyama.
A cikin wadannan ayoyi za mu iya ilmantuwa da abubuwa biyu ,na farkonsu :babbar kyauta a wannan duniya iata ce toba da komawa zuwa ga Allah da hakan ke kara yawan arziki da karfin al'umma. Na biyu: samara da al'umma salima tsarkakkiya mai karfi da wadatuwa da ni'imomo daya ne daga cikin buri da hadafin Annabawa da manzonni a wannan duniya da kuma ddinan da suka zo da su.
A sauraren ayoyi na 53,54 da kuma 55 a cikin surar ta Hud kamar haka:
قَالُواْ يَا هُودُ مَا جِئْتَنَا بِبَيِّنَةٍ وَمَا نَحْنُ بِتَارِكِي آلِهَتِنَا عَن قَوْلِكَ وَمَا نَحْنُ لَكَ بِمُؤْمِنِينَ{53} إِن نَّقُولُ إِلاَّ اعْتَرَاكَ بَعْضُ آلِهَتِنَا بِسُوَءٍ قَالَ إِنِّي أُشْهِدُ اللّهِ وَاشْهَدُواْ أَنِّي بَرِيءٌ مِّمَّا تُشْرِكُونَ{54} مِن دُونِهِ فَكِيدُونِي جَمِيعاً ثُمَّ لاَ تُنظِرُونِ{55}
-Suka ce: Ya Hudu ba ka zo mana da wata hujja ba,kuma ba za mu bar iyayen gijinmu ba saboda maganarka,ba kuma za mu bad a gaskiya da kai ba. - Ba abin da za mu ce sai dai kawai wasu iyayen gijinmu ne suka sa muka tabuwa saboda zaginsu da kake yi. Ya ce: Ni ina shaida wa Allah,ku kuma ku shaida cewa; ni hakika ba ruwana da abin da kuke tarayya da shi. - Wanda ba shi ba watau Allah,to ku shirya min makirci gaba dayanku,kar kuma ku saurara mini.
Duk da kira da kokarin da Annabi Hud (AS) ya yin a kiran mutanansa da galgadinsu dam u yi nisa da ayyukan da suka shafi Shirka su tuba daga ayyukan sabo da suke aikatawa su komo su yi riko da kadaita Allah,Sun bujirewa wannan kira nasa inda suka ci gaba da yin riko da hanyar bata da sabo da cewa Annabi Hud: mu ba za mu yi barin Allolin da muke yi wa bauta saboda kawai wadannan maganganu naka kai mu yi imani ma kai kanka za ka gamu da fishinsu saboda wannan cin fuska da mutunci da ka ke yi wa Allolinmu kuma hankalinka ya gushe ne don haka kake yi wadannan maganganu. Abin mamaki ne mutum ya bautawa abin day a kera da hannunsa daga itatuwa da duwatsu kuma ba tare day a kawo wani dalili na hankali kan wannan aiki nasa amma ya nemi dalili ga wanda ya yi Magana ta hankali da hujja bayyananna kuma daga karshe ya yi watsi karara da wannan bayani na hankali saboda jayayya.
A cikin wadannan ayoyi za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda uku ;
Na farko: Manzonni sun fuskanci adawa mai tsanani da jayayya ta mushrikai amma ko daidai da dakika daya bas u daina yin kira da kokarin shiryar da al'ummarsu ba ko nuna kasawa ba .
Na biyu: danganta mutanan kirkiri masu daraja da daukaka da masu tabuwar hankali da masu banna da danniya a cikin al'umma ke yi ba wani sabon al'amari ba ne.
Na uku:Manzonni da Annabawa (AS) bas u ji tsoron duk wani karfi sai na Allah don haka suke yin gwagwarmaya kan masu adawa da su saboda sun yi imani da yakini kan gaskiyar hanyar da suka yi riko da ita madaidaiciya.
To madallah yanzu kuma za mu saurari aya ta 56 a cikin wannan sura ta hud:
إِنِّي تَوَكَّلْتُ عَلَى اللّهِ رَبِّي وَرَبِّكُم مَّا مِن دَآبَّةٍ إِلاَّ هُوَ آخِذٌ بِنَاصِيَتِهَا إِنَّ رَبِّي عَلَى صِرَاطٍ مُّسْتَقِيمٍ{56}
- Hakika ni na dogara ga Allah,Ubangijina kuma Ubangijinku.Babu wata dabba face shi ne Yake rike da makwankwadarta watau yake sarrafa ta .Hakika Ubangijina a kan tafarki madaidaici yake.
Domin fuskantar barazana da zargi babu iyaka da mushrikan mutanansa ke yi kansa Annabi Hud ya shaida masu cewa; ku hada karfinku baki daya guri guda da azanci da dubarunku domin kulla mani makirci babu abin da zai razana ni domin na yi riko da Allah kuma da Allah ya yi dogaro kuma kar ku yi zaton Ubangijina ne ni kadai ku kun fita daga karfi da kudurarsa a'a ba wai kawai ni da ku ba ,duk wani abu mai liffashi da wanda ba ya liffashi yana karkashin iko da kudurarsa ne kuma shi adali ne wanda bay a zaluntar halittunsa daidai da kwayar zarra.
Za iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu a cikin wannan aya kamar haka:
Na farko: Fifikon mumuani kan kafirai shi ne suna tare da taimako da riko da tafarkin Allah wanda suke mika lamari zuwa gare shi lamarin da mushrikai suka rasa.
Na biyu: mu yi dogaro da wanda bayan shi ma'abucin karfi ne ya hada adalci kuma ba ya kaucewa daga hanya madaidaiciya.
A nan ne kuma ya kamata in dakata saboda lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe sai kuma mako na sama da yardarm Allah za ku ji mu dauke da wani sabon shirin kafin lokacin Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa; wassalam alaikum warahmatullahi wa barkatuhu.
Suratu Hud, Aya Ta 57-60 (Kashi Na 353)
Jama'a masu saurare barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hanunnka mai sanda, shirin da a cikinsa muke yin bayani da dubi a cikin ayoyin alkur'ani mai girma da domin ya zama jagora a rayuwar ta dukkan bangarori .Kuma babu wani littafi da hanyar da tafi yin riko da alkur'ani da kuma tafarkin ma'aikin Allah tsira da aminci ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka kuma ko shakka babu duk wanda ya yi riko da wadannan abubuwa biyu zai samu tsira da dacewa duniya da lahira bugu da kari ya samu sauki da walwala a rayuwarsa ta wannan duniya da samin hisabi mai sauki a ranar da tsanani da kunci da damuwa ya lullube zukata da tunanin kowa. Da fatar Allah ya lullube mu da rahama da lutifinsa duniya da lahira amin.
To madallah yanzu za mu shiga cikin shirin gadan-gadan tare da sauraren aya ta 57 a cikin wannan sura ta Hud
فَإِن تَوَلَّوْاْ فَقَدْ أَبْلَغْتُكُم مَّا أُرْسِلْتُ بِهِ إِلَيْكُمْ وَيَسْتَخْلِفُ رَبِّي قَوْماً غَيْرَكُمْ وَلاَ تَضُرُّونَهُ شَيْئاً إِنَّ رَبِّي عَلَىَ كُلِّ شَيْءٍ حَفِيظٌ{57}
- To idan kuka ba da baya, hakika na isar muku abin da aka aiko ni da shi zuwa gare ku,kuma Ubangijina zai iya musanya wasu mutanen ba ku ba ,kuma ba kwa cutar da Shi da komai.Hakika Ubangijina Mai kiyo ne a kan komai.
A shirin da ya gabata mun bi diddigin yadda tattaunawa ta kasance tsakanin annabi Hud (AS0 da kuma mutanansa amma a cikin wannan ayar Annabi Hud ya ci gaba da shaida masu cewa;Allah madaukakin sarki wanda ya halicci sammai da kassai da abubuwan da ke cikinsu da tsakaninsu ne ya aiko ni in shiryar da ku da fadakar da ku zuwa ga in riko da hanya madaidaiciya ta tauhidi na kadaita Allah da bauta kuma yanzu na cika sakon da aka aiko ni kuma ni ban yi kasa a guiwa ba ko nuna kasawa kan aikin da aka turo ni saboda haka idan kun ki karbar sakon da na zo da shi da bijirewa wannan sakon alheri to ku kwan da sanin cewa: a wannan duniya ba sai an je ko ina ba fushi da azabar Allah za ta riske ku da kawar da ku daga doran kasa da zuriyarku bayan haka sabuwar al'umma da zurriya ta rayu a doran kasa a maimakonku. Kar ku yi zaton za ku cutar da Allah da kafirci da jayayyar da ku yi to ku kwa da sanin Allah shi ne mabuwayi mai karfi da kudura.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da fahimtar abubuwa guda biyu masu muhimmanci na farkonsu:Annabawa da manzonni an umarce su da isar da sakon allah tare da kafawa al'ummar da aka turo su cikakkun hujjoji da dalilai yayin da a dabra ba a dora masu nauyin tilastawa da matsawa mutane yin imani da karfi kowa nada yancin yin imani cikin yanci da zabi.
Na biyu: Adawa da kiyayyar da al'umma suke nunawa jagororin da Annabawa da manzonni ba yana nuni da kasawar annbawa da manzonni wajan isar da sakon da aka aiko su da shi sai dai zabin da aka bawa kowa ne mutum da yanada zabin zabar alkheiri ko sharri a rayuwarsa.
Yanzu kuma za mu saurari aya ta 58 a cikin suratul hud kamar haka;
وَلَمَّا جَاء أَمْرُنَا نَجَّيْنَا هُوداً وَالَّذِينَ آمَنُواْ مَعَهُ بِرَحْمَةٍ مِّنَّا وَنَجَّيْنَاهُم مِّنْ عَذَابٍ غَلِيظٍ{58}
58-Lokacin kuwa da umarninmu ya zo Sai Muka tserar da Hudu shi da wadanda suka bada gaskiya da shi,saboda wata rahama daga gare Mu,Muka kuma tserar da su daga azaba mai gwabi.
Bijirewa da nuna kafirci tsantsa da yin watsi cikin ganganci da koyarwar Annabi Hud (AS)da kuma jawaban da ya yi masu na hankali amma sai suka ci gaba da zarginsa da kulla masa makircin kasha shi ,wannan mummanan halayai na sun e ya sa allah madaukakin sarki ya zabkar masu da azaba mai radadi da zafin kuna kamar yadda ya zo a cikin suratul Fusilat aya ta goma sha biyar: sai muka aiko musu da wata iska mai kara da tsananin sanyi a ranakun nahisa marasa alheri don Mu dandana musu azabar kunyatarwa a rayuwar duniya,azabar lahira kuma ta fi kunyatarwa ,ba kuma za a taimake su ba.
Amma lamari mai muhimmanci adalcin Allah a wannan lamari shi ne yadda azaba tana shafar wanda ya aika sabo da bijirewa kiran Annabi Hud daidai da sabon day a aikata na kafirci duk da cewa azabar ta saba kan al'umma amma Allah ya cici da tsirar da Annabi Hud (AS) da kuma mutanan da suka yi imani da shi. A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu na farko"Mumunai na gaskiya kamar Annabawa da Manzonni (AS) suna kubuta da tsirar da su daga fushi da azabar Allah.
Na biyu: Allah madaukakin sarki a daidai lolkacin guda da yake sabkar da azaba da fushinsa kan azzalumai, rahamarsa ya tabbatuwa kan wadanda suka yi imani da taimakawa wajan ciyar da addininsa.
yanzu kuma za mu saurari aya ta 59 da 60 a cikin wannan sura ta hud kamar haka:
وَتِلْكَ عَادٌ جَحَدُواْ بِآيَاتِ رَبِّهِمْ وَعَصَوْاْ رُسُلَهُ وَاتَّبَعُواْ أَمْرَ كُلِّ جَبَّارٍ عَنِيدٍ{59} وَأُتْبِعُواْ فِي هَـذِهِ الدُّنْيَا لَعْنَةً وَيَوْمَ الْقِيَامَةِ أَلا إِنَّ عَاداً كَفَرُواْ رَبَّهُمْ أَلاَ بُعْداً لِّعَادٍ قَوْمِ هُودٍ{60}
59-Wadancan kuwa sun e Adawa,da suka musanta ayoyin Ubangijinsu,suka kuma saba wa manzanninsa,kuma suka bi umarnin duk wani mai girman kai kangararre. 60-Aka kuma biyar musu da la'ana a duniya, haka kuma a ranar alkiyama,Haka fa,hakika Adawa kam sun kafirce wa Ubangijinsu.To fa,nisanta ta tabbata ga Adawa mutanen Hudu.
A karshen wadannan ayoyi ana Magana kan Adawa da cewa; jayayya da bijirewa kiran gaskiya da shirya da adawa suka yi shi ne sanadiyar da ta sa a maimakon yin biyayya da Annabawa da manzonni (AS) da za su tabbatar masu da sulhu da adalci sun gambace su ci gaba da yin riko da zalunci da kaucewa gaskiya da adalci kan wannan dalili ne a wannan duniya suka gamu da fishi da azabar Allah inda rahama ta kubuce masu yayin da a rayuwar gobe kiyama har ila yau bas u tsira ba saboda za su shiga wutar jahannama mai zafin kuna. Tana yuyuwa Adawa sun nace kan yin riko da kafirci a wannan duniya saboda suna rayuwa ne a wani tsibiri da larabawa suka kewaye da suka rayu shekaru saba'in kafin zuwan annabi Isa (AS) a yankin da ake kira da Ihkaf kuma Adawa mutane ne na girma da tsawo kuma sun ci gaba da samin wadata kamar yadda kur'ani a cikin ayoyin farko na suratul Fajr ke cewa; shin ba ku ga yadda Ubangijinku ya yi da mutanan adawa kuma birnin da suka rayuwa duk da girmansa ya bace kamar sauran biranai? Allah mai hikima ta hanyar yin tuni da abin day a faru da Adawa yana yi wa larabawan lokacin ma'aikin Allah Muhammad Tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi kashadi cewa idan kuka bijire da yin riko da kafirci abin day a faru kan adawa zai iya zama makomarku
A cikin wadannan aya za mu iya ilmantuwa da fahimtar abubuwa biyu kamar haka:
Na farko:yin tuni da waiwayen abin day a faru kan na baya zai zama darasi ga na gaba kamar yadda hausawa ke cewa; waiwaye adon tafiya.
Na biyu: tsinuwa kan azzalumai da ya zama al'adarmu a yau wani take ne day a samo asali daga Kur'ani.
Wata fadakarwa a nan da za mu iya lura it ace duk da cewa su mutanan adawa sun kasance ma'abuta karfi da girma domin su al'umma ce da Allah ya halitta da ke rayuwa a cikin wani tsibiri a yankin guda da larabawa kuma Allah ya banbanata su da sauran kabilun da ke rayuwa a yankin da su ma suke rayuwa ta siffan da tsarin gangar jikinsu da tsayin da suke da shi. Amma a maimakon sun yi godiya ga Allah da ya yi masu wannan falala dab a su wannan ni'ima da za su iya kare kansu daga duk wani hari a daidai wancan lokaci na rayuwar zalunci da danniya da yake-yake amma sai suka gambace ci gaba da yin riko da kafirci da dagawa kuma duk kokarin da manzon da aka turo masu domin ya shiryar da su sai suka yi watsi da hanya madaidaiciya ta gaskiya da sulhu da adalci har zuwa lokacin da fishin Allah madaukakin sarki da azabarsa ta sabka a kansu da kawar da su da birnin da suke rayuwa daga doran kasa kuma lamarin day a faru kansu ya zama darasi kan sauran al'ummomi da kabilun da suka rayu tare da su a yankin da kuma sauran al'ummomi da za su zo a nan gaba. Kuma wadannan ayoyi guda biyu ne suka kawo karshen kissar mutanan adawa inda da yardar Allah a cikin shirinmu na gaba za mu farad a kissar Annabi Salihu (AS) da kuma mutanan Samud da ake cewa samudawa. Amma kafin lokaci a maidadin wanda ya hada mana sauti har shirin ya kammla ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa a huta lafiya wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barkatuhu.
Suratu Hud, Aya Ta 61-63 (Kashi Na 354)
Jama'a masu saurare barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hanunnka mai sanda, shirin da a cikinsa muke yin bayani da dubi a cikin ayoyin alkur'ani mai girma da domin ya zama jagora a rayuwar ta dukkan bangarori .Kuma babu wani littafi da hanyar da tafi yin riko da alkur'ani da kuma tafarkin ma'aikin Allah tsira da aminci ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka kuma ko shakka babu duk wanda ya yi riko da wadannan abubuwa biyu zai samu tsira da dacewa duniya da lahira bugu da kari ya samu sauki da walwala a rayuwarsa ta wannan duniya da samin hisabi mai sauki a ranar da tsanani da kunci da damuwa ya lullube zukata da tunanin kowa. Da fatar Allah ya lullube mud a rahama da lutifinsa duniya da lahira amin.
To madallah yanzu kuma za mu shiga cikin shirin gadan gadan tare da sauraren aya ta 61 a cikin wannan sura ta hud:
وَإِلَى ثَمُودَ أَخَاهُمْ صَالِحاً قَالَ يَا قَوْمِ اعْبُدُواْ اللّهَ مَا لَكُم مِّنْ إِلَـهٍ غَيْرُهُ هُوَ أَنشَأَكُم مِّنَ الأَرْضِ وَاسْتَعْمَرَكُمْ فِيهَا فَاسْتَغْفِرُوهُ ثُمَّ تُوبُواْ إِلَيْهِ إِنَّ رَبِّي قَرِيبٌ مُّجِيبٌ{61}
61-Haka kuma Muka aiko wa Samudawa dan'uwansu Salihu. Y ace: Yak u mutanena,ku bauta wa Allah, ba ku da wani Ubangiji waninsa,shi ne Ya halicce ku daga kasa,Ya kuma ba ku damar ku raya ta,to ku nemi gafararsa sannan ku tuba gare Shi. Hakika Ubangijina Makusanci ne ,Mai amsawa.
Bayan da muka kawo karshen kissar mutanan adawa a shirin da ya gabata a makon jiya a shirinmu nay au za mu farad a kissar samudawa da manzon da aka aiko masu Annabi salihu (AS) da za mu yi nazari a cikin ayoyin da suka yi Magana kan kissarsu. Kuma shi Annabi Salihu (AS) ya zone domin shiryar da al'ummarsa bayan Annabi Nuhu Da Hud (AS).
Farkon kiran da Annabi Salihu (AS) ya yi wa mutanasa kamar ta sauran Annabawa da manzonnin da suka gabace shi ce kiran zuwa ga tauhidi da nisanta daga shirka da bautawa gumaka. Amma abin lura a koyarwa ta annabawa da Manzonni (AS) lahira da duniya tare su suna tafiya tare ne kuma shi bawan allah mumuni kamar yadda yake tunanin shiga aljanna a ayyukansa da tunaninsa haka kuma yake tunanin rayuwa a wannan duniya cikin yanayi mai aminci da wadata da tsaro. Saboda haka Annabi Salihu (AS) jawabinsa na farko ga mutanansa ya yi nuni da wannan lamari cewa: Allah madaukakin sarki ya mallaka mana duniya dab a mu zabi da umurtarmu kan gina rayuwa mai inganci da amfanuwa da arzikin da ke cikin wannan duniya ta hanyar da ta dace da cewa mene ne ya sa a maimakon mu yi kokari da nuna kuzari ta fuskar nomad a kiwo da amfanuwa da arzikin da Allah ya huwace mana ta wadannan hanyoyi na halaliya mun gambace mu tara dukiya da kudi ta mummunar hanya. Saboda haka ku tuba daga wannan aiki kuma Allah zai karbi tubarku.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu masu matukar muhimmanci .
Na farkonsu; dangantakar Annabawa da mutanansu dangantaka ce ta yan uwantaka ba dangantaka ce ta uban gida da ke kollon sauran kasa da shi.
Na biyu:Raya kasa da kare dabi'u wata bukata ce ta Allah ga bil adama baki daya.
To madallah za mu ci gaba da shirin tare da sauraren aya ta 62 a cikin wannan sura ta Hud kamar haka;
قَالُواْ يَا صَالِحُ قَدْ كُنتَ فِينَا مَرْجُوّاً قَبْلَ هَـذَا أَتَنْهَانَا أَن نَّعْبُدَ مَا يَعْبُدُ آبَاؤُنَا وَإِنَّنَا لَفِي شَكٍّ مِّمَّا تَدْعُونَا إِلَيْهِ مُرِيبٍ{62}
62-Suka ce : Ya Salihu,hakika a da ka zamanto abin kauna a cikinmu kafin ka zo mana da wannan,yanzu ka rika hana mum u bautawa abin da iyayenmu suke bautawa? Hakika mu kam lallai muna shakka game da abin da kake kiran mug are shi muna masu tababa.
Mutanan annbi Salihu (AS) da yawancinsu suna kan akidar uwayensu kafirai da tunani irin na uwayensu mushriki sun amsa kiran da Annabi Salihu (AS) ya yi masu kuma a maimakon sun yi tunani da nazari kan wannan jawabi na Annabi salihu na hankali da fadakarwa da cewa: wannan kira nasa ya sabawa sunnar uwayensu da tuhumarsa da cewa; ka kasance kana da dangantaka mai kyau dam u a baya kuma ka kasance abin kauna a gare mu da kuma muke dogaro da kai amma wannan jawabi da maganganu naka ya sa muna shaku da dora ayar tambaya kanka .wannan amsa da suka bayar kan Magana ta hankali ba tare da sun yi tunani bay a nuna baker jayayya da kiyayya ta jahilci da bayar da amsa ta rashin hankali da tunani don bakin kafirci da shirka. A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa fa abubuwa biyu kamar haka: Na farko: masu yada addini su kwan da san ice yawancin al'umma ba za su bar tunani da akidar da su saba ta bata cikin sauki saboda haka kar su nuna kasawa su ci gaba da juriya da ci gaba da kokarin shiryar da al'umma.
Na biyu: idan shakku bai gabaci bincike da bin diddigin hakika ba to zai ruguza burin dad an adam ke son cimma a rayuwarsa.
Sai karatun aya ta 63
قَالَ يَا قَوْمِ أَرَأَيْتُمْ إِن كُنتُ عَلَى بَيِّنَةً مِّن رَّبِّي وَآتَانِي مِنْهُ رَحْمَةً فَمَن يَنصُرُنِي مِنَ اللّهِ إِنْ عَصَيْتُهُ فَمَا تَزِيدُونَنِي غَيْرَ تَخْسِيرٍ{63}
63- Yace: ya ku mutanena, ku ba ni labari,yanzu idan na kasance a kan bayyananniyar hujja daga Ubangijina,ya kuma ba ni rahama ta annabci to wa zai kare ni daga azabar Allah idan na sabe shi ? Ai baa bin da kuke karat a da shi in ban da tabewa.
Annabi Salihu ya amsawa samudawa manager rashin hankali da suka yi masa lokacin da ya kiraye su zuwa ga kadaita Allah da bauta da cewa; rahama da lutifin Allah ne suka riske ni da bani wannan dama ta isar da sakonsa a matsayin ma'aiki manzonsa kuma Allah ne ya umarce ni da in isar da sakon addini da kiranku zuwa ga Tauhidi kuma ku kwan da sanin cewa idan na yi kasa a guiwa wajan isar da wannan sako to ku kanku ba za ku iya taimaka mani da komi ba to saboda haka ba ni da wani dalili da zai fasa kiranku zuwa ga kadaita Allah da bota ko kwadayin yardarku in yi shiru da yin kiranku ko isar da wannan sako.
A gaskiya abin da mutanan Annabi Salihu (AS) suka so a ayar da tag abaci wannan aya sun bukaci ya bar wannan kira da zuwa ga shiriya day a zo da shi shi ne ya sa suka bullo masa da yabo da jinjina masa kan halayansa da matsayinsa a tsakaninsu daga karshe suka nuna mamakinsu da shakku kansa saboda ya zo masu da wani abin da suke adawa da kiyayya da jayayya da shi.Amma Annabi Salihu (AS) sai ya amsa masu da cewa wannan wani lamari ne da nauyi a kansa daga Allah babu damar ya daina ba wai wani abu ban e na bukata ko son raid a idan ya ga dama ya ci gaba ko kuma ya daina. Kuma ku kanku idan da kuna da dalili mai karfi na hankali to da kun yi abin da nake yi kuma dab a ku yi kasa a guiwa ba ko yin sako-sako da jayayya kan bata.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da fahimtar abubuwa biyu kamar haka:
Na farko: addainai da Allah ya aiko manzonni da annabawa da su suna kan dalilai na hankali da hujjoji a bayyanai kuma karkashin wanna hujjoji ne suke kiran mutane zuwa ga yin riko da hanya madaidaiciya ta shiriya ba wait a hanyar yi masu barazana ko kwadaitar da su ba.
Na biyu:a tafarkin Allah dukan mutane matsayi daya suke da shi babu wani banbanci su kansu Annabawa idan suka sabawa umarnin Allah ko su ka yi kasa a guiwa da sako sako wajan isar da sakon da aka turo su da shi za su fuskanci fushin Allah ko shakka babu.
Da kuma wannan ne muka kawo karshen abin da za mu iya bayani a cikin wannan shiri saboda lokacin da aka daibar mana ya kawo karshe. Na ke cewa wassalamu alaikum wa rahmatullah.
Suratu Hud, Aya Ta 64-68 (Kashi Na 355)
Jama'a masu saurare barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hanunnka mai sanda, shirin da a cikinsa muke yin bayani da dubi a cikin ayoyin alkur'ani mai girma da domin ya zama jagora a rayuwar ta dukkan bangarori .Kuma babu wani littafi da hanyar da tafi yin riko da alkur'ani da kuma tafarkin ma'aikin Allah tsira da aminci ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka kuma ko shakka babu duk wanda ya yi riko da wadannan abubuwa biyu zai samu tsira da dacewa duniya da lahira bugu da kari ya samu sauki da walwala a rayuwarsa ta wannan duniya da samin hisabi mai sauki a ranar da tsanani da kunci da damuwa ya lullube zukata da tunanin kowa. Da fatar Allah ya lullube mud a rahama da lutifinsa duniya da lahira amin.
To yanzu kuma za mu saurari aya ta 64 a cikin wannan sura ta Hud kamar haka:
وَيَا قَوْمِ هَـذِهِ نَاقَةُ اللّهِ لَكُمْ آيَةً فَذَرُوهَا تَأْكُلْ فِي أَرْضِ اللّهِ وَلاَ تَمَسُّوهَا بِسُوءٍ فَيَأْخُذَكُمْ عَذَابٌ قَرِيبٌ{64}
- Kuma ya ku mutanena,wannan fa taguwar Allah ce a gare ku, sai ku bar tat a ci a kasar Allah,kada kuwa ku shafe tad a wata cuta, sai azaba makusanciya ta afka muku.
A cikin ayar da ta gabata da kuma shirin day a gabata mun bayyana cewa; duk da bayanai na hankali da kira cikin hikima da Annabi Salihu ya yi wa mutanansa sai suka zarge shi da kirkiro karya a maimakon gaskanta shi da cewa yana daga cikin wadanda suka sabawa al'adarsu da abubuwan da suka yi gado daga uwaye da kakannu. Amma da ke su annabawa da manzonni a kullum bayan bayanai na hankali da kiran al'umma cikin hikima suna gabatar masu da mu'ujiza domin kawar da duk wani shakku da rashin tabbas da suke da shi komin kankantarsa. Karkashin umarnin Allah madaukakin sarki sai taguwa ta fito daga tsakiyar dutse kuma ba tare da ta sadu da rakumi bat a dauki ciki da shayar da mutanansa annabi Salihu (AS) da madara .Saboda yin godiya ga Allah Annabi Salihu (AS) ya bukaci mutanansa da kar su kuntatawa wannan rakuma ko cutar da ita da kuma bat a damar yin kiwo da shan rowan rijiya daidai bukatarta a wata ruwayar kwana daya na takuwa kwana daya na mutane idan kuma ba haka ba fushi da azabar Allah ta sabka a kansu ma'ana idan suka cutar da ita wannan taguwa.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa biyu na farko: mu sani karfi da kudurar Allah ta fi karfin dalili da illoli na zahirin abubuwan duniya kuma halittar taguwa daga tsakiyar dutse na daya daga cikin alamomin kudura da iradarsa.
Na biyu: mu sani cin fuska da cin zarafin abubuwa masu daraja da kadasa da Allah ya samara a cikin wannan duniya da ke haskaka sammai da kassai ya iya haddasa sabkar azabar Allah cikin gaggauwa. Da fatar Allah ya kiyashe mu da azabar Allah duniya da lahira amin summa amin.
To madallah yanzu kuma za mu saurari aya ta 65 a cikin wannan sura ta Hud kamar haka;
فَعَقَرُوهَا فَقَالَ تَمَتَّعُواْ فِي دَارِكُمْ ثَلاَثَةَ أَيَّامٍ ذَلِكَ وَعْدٌ غَيْرُ مَكْذُوبٍ{65}
-Amma sai suka sare ta ,sai y ace da su: Ku ji dadi cikin gidajenku kwana uku rak . Wannan alkawari neb a abin karyatawa ba.
Samudawa ba wai kawai sun ki karba da amsa kiran Annabi Salihu da kuma mika wuya da amincewa da mu'ijizar day a zo da ita a'a sai ma daya daga cikinsu ya kuduri aniyar kasha taguwar day a zo da ita a matsayin mu'ijiza kuma haka ya aikata.Su kuwa sauran mutane bayan sun ki hana shi aikata wannan mummunan aiki sun kasance tare da shi a zucci da amincewa da wannan aiki day a aikata ma'ana sun karfafa masa da kasancewa tare da shi wajan aikata wannan aiki.Saboda haka fushi da azabar Allah ta hau kan dukan mutanan da suka kafirce da cika alkawalin sabkar azabar da aka yi masu. Amma duk da haka an bas u damar su tuba a cikin kwana uku daga mummunan aikin da suka aikata.A cikin wannan kwanaki uku sun kasance cikin damuwa da kunci da tunanin sabkar azaba da hakan ya cutar da su kafin azabar ta sabka a kansu.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu na farkonsu shi ne :Amincewa da sabon da wasu suke aikatawa tamkar taimakawa ne a cikin aikata sabon da suke yi da kuma karfafa masu karfin guiwar aikata wannan sabo.
Na biyu kuwa:A kullum mu rike yin riko da kashedin Allah domin yin sako sako da haka wani cin fuska ne ga abubuwa masu kima da daraja na addini da kuma hakan na iya haddasa sabkar azaba.
Yanzu kuma za mu ci gaba da shirin nay au tare da sauraran aya ta 66 a cikin wannan sura ta hud (AS) kamar haka;
فَلَمَّا جَاء أَمْرُنَا نَجَّيْنَا صَالِحاً وَالَّذِينَ آمَنُواْ مَعَهُ بِرَحْمَةٍ مِّنَّا وَمِنْ خِزْيِ يَوْمِئِذٍ إِنَّ رَبَّكَ هُوَ الْقَوِيُّ الْعَزِيزُ{66}
- To lokacin da umarninmu ya zo sai Muka tserar da Salihu shi da wadanda suka bada gaskiya tare da shi saboda wata rahama daga gare Mu,kuma muka tserar da su daga kunyatar wannan rana.Hakika Ubangijinka Shi ne Mai karfi mabuwayi.
Sauran bala'o'i na dabi'a irin su ambaliyar ruwa,girgizar kasa,guguwa mai karfi tana shafar kowa da kowa kama da shi kansa kafiri da kuma mumuni ba tare da wani banbanci ba a tsakaninsu amma idan irin wadannan bala'o'I sun kebantu da azaba da fushin Allah suna shafar wadanda suka aikata wannan sabo da ya yi sanadiyar sabkar azabar domin Allah yana kare mumunai daga shafuwa da wannan azaba kawai tana shafar kafirai da mushrikai ne. Saboda haka lokacin sabkar azaba kan mutanan samuda, Allah ya kubutar da manzonsa da mumunai da sahabbansa da tsiratar da su inda kawai ya hallaka wadanda suka aikata sabo kuma wannan na nuni da ilimi da kudurar Allah da kuma hikimarsa gami da lutifinsa.
A cikin wannan sura za mu iya ilmantuw ada abubuwa guda biyu .
Na farko : yin biyayya ga Annabawa da Manzonnni babban jari ne da ke kubutar da mutum daga kaskanci da tabewa ya kuma daukaka shi .
Na biyu: kubutar day an tsuraru daga cikin mutane kafirai masu yawa wani abu ne mai sauki.
To madallah yanzu kuma za mu shiga cikin shirin gadan gadan tare da faraway da sauraren ayoyi na 67 da 68 a cikin suratul hud kamar haka;
وَأَخَذَ الَّذِينَ ظَلَمُواْ الصَّيْحَةُ فَأَصْبَحُواْ فِي دِيَارِهِمْ جَاثِمِينَ{67} كَأَن لَّمْ يَغْنَوْاْ فِيهَا أَلاَ إِنَّ ثَمُودَ كَفرُواْ رَبَّهُمْ أَلاَ بُعْداً لِّثَمُودَ{68}
67- kuma tsawa ta kama wadanda suka kafirta,sai suka wayi gari a cikin gidajensu a duddurkushe watau suna matattu.
68-Sai ka ce bas u taba zama a cikinsu ba watau gidajensu ba.Haka fa, Hakika Samudawa kam sun kafirce wa Ubangijinsu. To fa, Nesanta ta tabbata ga Samudawa.
Wa'adi da alkawalin da Annabi Salihu ya yi mutanansa da suka kafirce masa daga Allah ya tabbata domin kuwa sun fuskanci tsawa daga sama da girgizar kasa da hallakar da su kuma kafin su hallakar sun fuskanci azabar tarwatsa da walkiyar azaba da tsananin kara na ban tsoro da mutane suka mace don tsananin tsoro da damuwa tamkar mutuman da wutar lantarki ta kama shi da nan take ke jikinta yak e azabtuwa da rasa ransa.
A cikin wadannan ayoyi za mu iya ilmantuwa da fahimtar abubuwa guda biyu masu fadakarwa kamar haka:
Na farko: sabkar azaba da musabbabin sabkar azaba sanadiyar ayyukan sabo da zalunci da girman kan mutum ne kuma Allah ba tare da wani dalili ba ba ya sabkar da azabarsa haka kawai sudda.
Na biyu:Azabar allah ba wai kawai ta kebantu da ranar kiyama ba sun kafirai da mushrikai na fuskantar azaba da fushin Allah tun a wannan duniya.
Da fatar Allah ya ba mu karfi da ikon yin sallama a kullum da kuma girmama bako cikin mutunci da shinfidar fuska da ta zucciya da tunani da kuma abin hannu amin. Da kuma wannan fatar ce a mamadin wanda ya hada mana sauti har shirin ya kan kama daram wato Muhammad Amin Ibrahim kiyawa ni Tidjani Malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassallam……
Suratu Hud, Aya Ta 69-73 (Kashi Na 356)
Jama'a masu saurare barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hanunnka mai sanda, shirin da a cikinsa muke yin bayani da dubi a cikin ayoyin alkur'ani mai girma da domin ya zama jagora a rayuwar ta dukkan bangarori .Kuma babu wani littafi da hanyar da tafi yin riko da alkur'ani da kuma tafarkin ma'aikin Allah tsira da aminci ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka kuma ko shakka babu duk wanda ya yi riko da wadannan abubuwa biyu zai samu tsira da dacewa duniya da lahira bugu da kari ya samu sauki da walwala a rayuwarsa ta wannan duniya da samin hisabi mai sauki a ranar da tsanani da kunci da damuwa ya lullube zukata da tunanin kowa. Da fatar Allah ya lullube mud a rahama da lutifinsa duniya da lahira amin.
To madallah yanzu kuma lokaci ne da za mu saurari ayoyi na 69 da 70 a cikin wannan sura ta Hud (AS) kamar haka:
وَلَقَدْ جَاءتْ رُسُلُنَا إِبْرَاهِيمَ بِالْبُـشْرَى قَالُواْ سَلاَماً قَالَ سَلاَمٌ فَمَا لَبِثَ أَن جَاء بِعِجْلٍ حَنِيذٍ{69} فَلَمَّا رَأَى أَيْدِيَهُمْ لاَ تَصِلُ إِلَيْهِ نَكِرَهُمْ وَأَوْجَسَ مِنْهُمْ خِيفَةً قَالُواْ لاَ تَخَفْ إِنَّا أُرْسِلْنَا إِلَى قَوْمِ لُوطٍ{70}
- Hakika kuma manzanninmu sun zo wa Ibrahimu da albishir,suka ce: Aminci a gare ka ,ya ce: Aminci a gare ku. To bai zauna ba sai da ya kawo musu soyayyen dan maraki.
- To lokacin da ya ga hannayensu bas a isa gare shi wato soyayyen dan marakin ,sai ya soma yin dari-dari da su,kuma ya boye jin tsoronsu a zuciyarsa,suka ce: kar ka tsorata, mu an aiko mu ne zuwa ga mutanen Ludu.
A cikin shirye shiryen da suka gabata mun yi bayani a cikin ayoyin da suka yi bayani kan yadda makomar mutanen annabi Hud da Salihu (AS) ta kasance da yadda azaba ta sabka a kansu saboda bijirewa da adawar da suka nuna karara kan kiran wadannan annabawa to a yau za mu fara ne da ayoyin da ke bayani kan yadda lamari ya wakana tsakanin Annabi Ibrahima (AS) da mala'ikan da Allah ya tura zuwa ga mutanan Annabi Lud (AS) domin hallakar da su kan bijirewar da suka yi da kiran manzon da aka turo don shiryar da su. Ganin shi wannan mala'ika da aka turo ya zowa Annabi Ibrahima cikin siffar mutane sai ya yanka masa dan marake da yi masa balangunsa amma da yake shi bay a cin abinci da sha ruwa bai ci wani abu daga cikin kayan cid a na marmari da Annabi Ibrahima (AS) ya yi masa tanadi don girmama bako lamarin day a sa Annabi Ibrahima ya tambayi kansa tambaya ban mamaki cewa kar fa wannan na da niyar aikata wani abu maras kyau don haka ya ki cin komi saboda kar ya zama mun bi shi bashi kamar yadda al'ada take duk wanda ya girmama ka abin kunya net a ci zarafinsa ko aikata wani laifi kansa. Amma da wannan mala'ika ya fahimci abin da ke wakana a tunani da fuskar Annabi ibrahima (AS) sai suka ce masa mu muna tafe ne da Albishir da kuma alkawalin hallakar da wasu.
Busharar da Allah yak e yi maka it ace idan tsufa ya kama ka zai arzuta ka dad a . Dayan labari kuwa na hallaka mutanan lud da suka bijirewa kiran shiriya .
Ganin annabi Lud (AS) manzo ne dake karkashin shari'ar Annabi Ibrahima (AS) saboda haka ne Allah ya sanar da Annabi Ibrahima abin da zai wakana kan mutanan Annabi Lud kafin ya sanar da Annabi Lud (AS).
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu:
Na farko: Mu sani cewa: su kansu mala'iku suna fara Magana ne bayan yin sallama kuma wannan it ace sira da dabi'ar mutane da da duk wani mai tsarki da mutane salihai .Kuma ya kamata mu fahimci muhimmancin yin sallama da amsa sallama da alherin da ke tattare da hakan.
Na biyu: mu sani girmama bako wata babbar sunna da al'adar Annabawan Allah (AS) ce.
To yanzu kuma za mu fara shirin ne da sauraren ayyoyi na 71 da 72 a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda kamar haka;
وَامْرَأَتُهُ قَآئِمَةٌ فَضَحِكَتْ فَبَشَّرْنَاهَا بِإِسْحَاقَ وَمِن وَرَاء إِسْحَاقَ يَعْقُوبَ{71} قَالَتْ يَا وَيْلَتَى أَأَلِدُ وَأَنَاْ عَجُوزٌ وَهَـذَا بَعْلِي شَيْخاً إِنَّ هَـذَا لَشَيْءٌ عَجِيبٌ{72}
Matarsa kuwa tana tsaye sai ta yi dariya sai Muka yi mata albishir da Ishaka ,bayan kuma Ishaka sai yakubu Dan Ishaka.
Ta ce : Kaicona" Yanzu zai yiwu kuwa in haihu ,gani tsohuwa wannan miji nawa kuwa tsoho ? Ba Shakka wannan abin mamaki ne.
Tattaunawar da Annabi Ibrahima (AS) yak e yi da mala'iku ta kai ga kunnan matarsa Saratu kuma al'ajabi ya kamata da mamaye tunaninta saboda yaya za a ce za ta samo da a daidai lokacin da tsufa ya kamata kuma uwa uba hatta a lokacin da take cikin kurciya da yarintarta ta kasa samin da saboda matsalar daga gare tan e na rashin aifuwa ba daga Annabi ibrahima ban e .Har iya yau shi kansa Annabi Ibrahima (AS) a daidai lokacin tsufa ya kama shi don haka karkashin dabi'a abu ne mai wuya wadda tsufa ya kamata da kuma wanda tsufa ya kama shi su samu da . Amma a gurin Allah madaukakin sarki mai iko da kudura mai badawa da hanawa babu wani abu da zai iya hana abkuwar abin day a ga dama kuma a kullum bukatarsa c eke galaba kan komi.
Wannan ayoyi na ilmantar da mu da fadakar da mu wasu abubuwa da lamura guda biyu akalla:
Na farko: Afuwar da salihi mai albarka wata babbar ni'ima ce da Allah yak e yiwa halittun da ke sammai da kassai bushara.Idan Allah ya bamu yaya salihai sai mu yi godiya ga Allah Madaukakin sarki da wannan ni'ima idan kuma aka bam u akasin haka Allah ya kiya sai mu yi masu addu'ar alheri da gode masa domin hakan ma ni'ima ce babba.
Na biyu:Mu sani kkudurar Allah ta zarta wasu dokoki na zahiri kuma bas u tafiya tare yana zartar da Abin day a ga dama cikin hikima.
To yanzu kuma za mu saurari aya ta 73 a cikin wannan sura ta Hud kamar haka;
قَالُواْ أَتَعْجَبِينَ مِنْ أَمْرِ اللّهِ رَحْمَتُ اللّهِ وَبَرَكَاتُهُ عَلَيْكُمْ أَهْلَ الْبَيْتِ إِنَّهُ حَمِيدٌ مَّجِيدٌ{73}
Suka ce: Yanzu kya rika mamaki game da alamarin Allah ? Rahamar Allah da albarkarsa su tabbata a gare ku mutanan wannan gidan. Hakika Shi Allah abin godewa ne Mai girma.
Al'ajabin da matar Annabi Ibrahima (AS) saratu ta yi wani lamari ne na dabi'ar mutum musamman ga tsohuwa da aka ce za ta sami da bayan shekaru da ta yi tana jiran wannan lamari don haka karba da amincewar wannan lamari a gare ta lamari ne mai wuya a lokaci guda.Ganin haka sai mala'iku suka tunatar da ita cewa wannan wata bukata ce daga Allah mai zartar da abin da yaga dama don haka babu wani mamaki a cikinsa musamman kai da kike rayuwa a cikin gidan annabtaka da kuma Allah yake sabkar da albaraka da rahamarsa ga iyalan wannan gida mai albarka.
Ya zo a cikin ruwayar da aka nakalto daga Imam Ali (AS) cewa idan za mu amsa sallamar da aka yi mana kamar yadda Mala'iku suka Ammasawa Annabi Ibrahima cewa.Alaikar salam wa rahmatullahi wa barkatuhu.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu: Na farko: Da alama ce ta rahamar Allah da Albaraka da yaduwar iyalin wannan gida.
Na biyu: a kullum kar mu kasance daga cikin masu fidda tsammahani daga rahamar Allah, Allan da ya sanyaya wuta ta sama sanyi da salama ga Annabi Ibrahima (AS) na iya bawa tsohuwa da tsoho dad a arzuta su da zurriya babu abin mamaki a cikin hakan.
Da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin na yau kafin mako da sama da yardar Allah ni Tidjani malam lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar da kuma Malam Aminu Ibrahim Kiyawa day a daoki shirin kamar yadda kuka ji shi na ke cewa huta lafiya wassal….
Suratu Hud, Aya Ta 74-78 (Kashi Na 357)
Jama'a masu saurare barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hanunnka mai sanda, shirin da a cikinsa muke yin bayani da dubi a cikin ayoyin alkur'ani mai girma da domin ya zama jagora a rayuwar ta dukkan bangarori .Kuma babu wani littafi da hanyar da tafi yin riko da alkur'ani da kuma tafarkin ma'aikin Allah tsira da aminci ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka kuma ko shakka babu duk wanda ya yi riko da wadannan abubuwa biyu zai samu tsira da dacewa duniya da lahira bugu da kari ya samu sauki da walwala a rayuwarsa ta wannan duniya da samin hisabi mai sauki a ranar da tsanani da kunci da damuwa ya lullube zukata da tunanin kowa. Da fatar Allah ya lullube mud a rahama da lutifinsa duniya da lahira amin.
Yanzu kuma za mu fara wannan shirin na yau da sauraran ayoyi na 74 da 75 a cikin wannan sura ta Hud kamar haka:
فَلَمَّا ذَهَبَ عَنْ إِبْرَاهِيمَ الرَّوْعُ وَجَاءتْهُ الْبُشْرَى يُجَادِلُنَا فِي قَوْمِ لُوطٍ{74} إِنَّ إِبْرَاهِيمَ لَحَلِيمٌ أَوَّاهٌ مُّنِيبٌ{75}
74- To lokacin da tsoro ya yaye ga Ibrahimu,kuma albishir ya zo masa ,sai ya zama yana muhawara da Mu game da lamarin mutanen Ludu.
75-Hakika Ibrahimu kam ba shakka mai hakuri ne mai yawan kaskantar da kai mai yawan komawa ga Allah.
A cikin shirin day a gabata mun bayyana cewa: mala'ikun da Allah ya tura gurin Annabi Ibrahima (AS) sun yi shigar mutane kuma ba su ci abinci da rowan shay a yai masu tanadi kamar yadda al'ada take ta karbar baki lamarin day a sa Annabi Ibrahima (AS0 ya shiga damuwa da tambayar kansa dalilin day a hana su cin abinci amma albishir da suka ba shi zai samu da a nan gaba ya baranta masa rai da kwantar masa da zucciya da samin damar tattaunawa da su mala'ikun da Allah aiko su takanasa. Har ila yau mun bayyana cewa Annabi Ludu da mutanansa suna karkashin shari'ar annabi Ibrahima (AS) ne dalilin day a sa mala'iku suka fara sanar da Annabi Ibrahima abin da yake tafiye da su daga Allah ya sabkar azaba kan mutanan Annabi Ludu da suka kafirce da kubutar da Annabi Ludu (AS) da wadanda suka yi imani da shi daga wannan azaba.To wannan aya tana bayani ne kan tattaunwa da neman rahama a maimakon sabkar azaba kan mutanan Ludu da suka kafirce kamar yadda aya ta 32 a cikin suratul Ankabutu ke cewa: Sai Ibrahimu y ace: Hakika a cikinta akwai Ludu.Sai suka ce Mu muka fi sanin wadanda suke cikinta,ba shakka za mu tserra da shi tare da iyalinsa,sai matarsa kawai da ta kasance cikin wanzazzu da za a hallaka.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu:
Na farko: kar ni'ima da wadata su sa mu sha'afa da matsalolin da wasu ke ciki domin duk da albishir din da aka bawa Annabi Ibrahim amma bai say a manta da mummunan halin da mutanan annabi Ludu (AS) za su fada.
Na biyu: Addu'a da tawassili ko ceton waliyan Allah na tasiri kan abin da bai zama tabbas ba kamar yadda tattaunawar da Annabi Ibrahima (AS) ya yi da mala'iku bai haifar da komi ba kan sabkar azaba da fushin Allah kan mutanan Ludu babu makawa.
To yanzu kuma za mu saurari aya ta 76 a cikin suratul Hud (AS) kamar haka;
يَا إِبْرَاهِيمُ أَعْرِضْ عَنْ هَذَا إِنَّهُ قَدْ جَاء أَمْرُ رَبِّكَ وَإِنَّهُمْ آتِيهِمْ عَذَابٌ غَيْرُ مَرْدُودٍ{76}
- Ya Ibrahimu ,ka kau da kai daga wannan .Hakika umarnin Ubangijinka ya zo ,hakika kuwa azaba wadda ba mai kawar da ita za ta zo musu.
Bukatar Annabi Ibrahima (AS) na dauke sabkar azaba ko jinkirta ta kan mutanan Annabi Ludu (AS) yana karkashin damuwa da halin al'umma neb a wai yana karkashin shaku kan sabkar azaba ko wani abu makamancin haka ba ammada ya fahimcin fushin Allah da azaba ba makawa sai sun sabka ,ceton Annabi Ibrahima (AS) bai yi nasara ba da fadakar da shi day a daina neman ceto ga kafirai da mushirikai da babu makawa azaba sai ta sabka kansu.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu:
Na farko:Manzonni da Annabawa na damuwa da halin da jama'a ke ciki kuma suna iyakacin kokarinsu wajan kubutar da su iyakacin karfinsu.
Na biyu: Wasu azabobin Allah kan kafirai abkuwarsu tabbas ne babu makawa hatta ceton Annabawa da manzonni ba ya iya jinkirtar da abkuwarsu.
A saurari aya ta 77 a cikin wannan shiri na Hannunka mai sanda.
وَلَمَّا جَاءتْ رُسُلُنَا لُوطاً سِيءَ بِهِمْ وَضَاقَ بِهِمْ ذَرْعاً وَقَالَ هَـذَا يَوْمٌ عَصِيبٌ{77}
- Lokacin kuma da manzanninmu suka zo wa ludu ,sai aka bata masa rai saboda su ,kuma zuciyarsa ta yi kunci saboda su,ya kuma ce: Wannan ran ace mawuyaciya.
Mala'ikun da aka tura don hallaka mutanan Annabi Ludu (AS) sun yi shigar mutane ga kyawon fuska da yanayi mai kyau suka isa gurin annabi Ludu (AS) inda ya sabke su amma Annabi Ludu (AS) yana cikin damuwa da fargaba saboda mutanansa masu aika sabo da luwadi idan suka ga wadannan matasa masu kyau da tsarin jiki wa'iyazu billahi suna iya nemansu su da mummunan aiki na sabon da suka saba ga kuma wannan baki amanarsa ne;Wannan lamari ya na damin Annabi Ludu (AS) saboda yanada masaniya kan mummunar niyar mutanasa kafirai ganin haka sai ya rurrufe kofofin inda ya sabke bakin amma duk da haka yana cikin damuwa.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu:
Na farko: matakin farko na gwagwarmaya da masu nuna kafirci shi ne damuwa ta zucci da ke bakanta ran mutum idan ya ga matakin da wasu ke dauka na aikata sabo da banna.
Na biyu: bawa mako kariya yana wuyan mai masabki ne shi kuwa mai bakunta ya kiyaye bacin ran mai masabki kar wani abu ya same shi.
Yanzu kuma za mu fara ne da sauraren aya ta 78 a cikin wannan sura ta hud (AS) kamar haka:
وَجَاءهُ قَوْمُهُ يُهْرَعُونَ إِلَيْهِ وَمِن قَبْلُ كَانُواْ يَعْمَلُونَ السَّيِّئَاتِ قَالَ يَا قَوْمِ هَـؤُلاء بَنَاتِي هُنَّ أَطْهَرُ لَكُمْ فَاتَّقُواْ اللّهَ وَلاَ تُخْزُونِ فِي ضَيْفِي أَلَيْسَ مِنكُمْ رَجُلٌ رَّشِيدٌ{78}
-Mutanensa kuwa suka zo masa suna gaggawa,da ma ko can sun zamanto suna yin munanan ayyukan. Y ace : ya mutanena,ga yayana mata ,su suka fi tsarkaka a gare ku ba maza ba,sai ku ji tsoron Allah,kada kuma ku kunyata ni cikin bakina.Yanzu a cikinku ba wani mutum shiryayye?
A cikin ayar da ta gabata mun bayyana cewa: Annabi Ludu (AS) yana cikin damuwa saboda masaniyar da yake da ita kan mummunar niyar mutanansa kafirai kuma lokacin day a ga sun zo gurinsa mutanasa kafirai masu aikata mummunan aiki sai Annabi Ludu (AS) y ace masu idan kuna son ku biya bukatarku ce to wadannan yayana ne mata sun e suka fi dacewa idan kuna bukatar aurensu sai ku aure su ta haka za ku biya bukatarku da samin lada kuma ku samu tsarkin jiki da na ruhu da samin kusanci.Wai ma mene ne ya sa kuke ku santar sabo da mummunan aiki ne? kuma lamarin kun a da daurin kai da ke bin maza da aika mummunan aikin da Allah ya haramta aikatawa kuma hatta baki dab a ku san ko su wane ba ba ku yi masu adalci da rahama da girmama baki.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu:
Na farko: wasu daga cikin al'ummomi na gasa da rige-rige wajan aikata sabo da banna da fadawa cikin sabo da banna dumu-dumu.
Na biyu: domin hana banna da sabo a tsakanin jama'a dole a samara da hanyoyi da fadakar da su sannu a hankali har lamarin ya fadada.
Da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri nay au sai kuma mako na sama da yardarm Allah za ku ji mud a ci gaban wannan kissar da yadda ta kaya a tsakanin Annabi Ludu (AS) da mutanansa da kuma Mala'iku a gefe daya. Kafin lokacin a madadin wanda ya hada mana sauti.Ni Tidjani Malam Lawali damagaram na ke cewa wasss….
Suratu Hud, Aya Ta 79-84 (Kashi Na 358)
Jama'a masu saurare barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hanunnka mai sanda, shirin da a cikinsa muke yin bayani da dubi a cikin ayoyin alkur'ani mai girma da domin ya zama jagora a rayuwar ta dukkan bangarori .Kuma babu wani littafi da hanyar da tafi yin riko da alkur'ani da kuma tafarkin ma'aikin Allah tsira da aminci ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka kuma ko shakka babu duk wanda ya yi riko da wadannan abubuwa biyu zai samu tsira da dacewa duniya da lahira bugu da kari ya samu sauki da walwala a rayuwarsa ta wannan duniya da samin hisabi mai sauki a ranar da tsanani da kunci da damuwa ya lullube zukata da tunanin kowa. Da fatar Allah ya lullube mud a rahama da lutifinsa duniya da lahira amin.
To madallah yanzu kuma za mu fara shirin na yau na hannunka mai sanda tare da sauraren ayoyi na 79 da 80 a cikin suratul Hud:
قَالُواْ لَقَدْ عَلِمْتَ مَا لَنَا فِي بَنَاتِكَ مِنْ حَقٍّ وَإِنَّكَ لَتَعْلَمُ مَا نُرِيدُ{79} قَالَ لَوْ أَنَّ لِي بِكُمْ قُوَّةً أَوْ آوِي إِلَى رُكْنٍ شَدِيدٍ{80}
-Suka ce: Hakika ka sani bam u da wani hakki na sha'awa ga yayanka mata,hakika kuma lallai ka san abin da muke nufi.
- Y ace : Ina ma ina da karfin da zan hana ku ,ko kuwa ina da wata kakkarfar majingina d azan dogara da ita?"
A cikin shirin day a gabata mun bayyana cewa; lokacin da mala'iku da allah ya tura gurin Annabi Ludu (AS) sun yi shiga da siffar matasa cikin tsari da kyauwon siffa kuma sun kasance tare da Annabi Ludu (AS) amma masu mummunar niya da aiakata aikin sabo da kazanta daga cikin mutanan annabi Ludu kafirai sun tafi gurin wadannan mala'iku da suka yi shigar mutane da gabatar masu da bukatar neman aikata mummunan aiki da suka saba dasu .babu kumya balantana tsoran Allah .Kuma lokacin da Annabi Ludu (AS) y ace masu a maimakon wadannan matasa ga yayana mata ku aure su da biyan bukatarku ta sunna sai suka amsa masa da cewa; mu bam u da wata bukata dangane da yayanka mata kuma mu kawai muna son biyan bukatarmu da muka saba don haka sai ka bamu wadannan baki naka mu tafi mu biya bukatunmu.
Bayan da suka fadi haka ,da bayyana maganganu na rashin tunani da sanin ya kamata da rashin girmama bako balantana wannan bawon Allah latijo salihin mutum ko da a ce bas u dauke shi da kollonsa a matsayin Annabi ba ai ya kamata su girmama shi. Bayan haka sai annabi Ludu (AS) ya sami kansa cikin tsaka mia wuya da tunanin yadda zai magance wannan matsala.Sai ya fara tunani a cikin kwalluwa da kudurawa a cikin zucciyarsa cewa; dama ace ina da mataimaka mumunai da za su iya tsayawa su fuskance ku domin kare mutunci da darajar wadannan baki nawa ko kuma su boye su a wani guri mai aminci.
Abin mamaki a nan duk da yake wadannan ayoyi na kur'ani mai girma na bayani ne kan abubuwan assha da mummunan aikin da mutanan Annabi Ludu kafirai suka aikata a shekaru dubbai da suka gabata amma irin wannnan bukata ta jahilci da kazanta da Allah ya haramta tun wancan lokaci a yau a duniyarmu da aka ci gaba da raya wayewa an amince da aikata wannan sabo da kazanta a dokance .Ba a nan lamarin ya tsaya ba ganin saduwa a tsakanin masu jinsi daya bai dace ba kuma haramin ne a addinance da kuma abin kama a tsakanin al'umma da zamantakewarta sai gashi wasu gwamnatoci n ayammacin Turai sun amince da yin aure a tsakanin jinsi daya a cikin kundin tsarin mulki. Amma auren mace sama da daya ya sabawa dokokinsu kuma suna yaki da hakan da tsananta doka da hukumci kan duk wanda aka samu ya auri mace sama da daya da dai sauran dokoki makamantan haka.
A kwai ayoyi da dama a cikin alkur'ani da suka haramta wannan mummunan aiki na luwadi kuma domin siffanta mana munin wannan aiki alkur'ani ya yi amfani da kallomi kamar haka: jahilci,mummunan aiki,zalunci,aikata leifi,banna,fasikanci da kuma alfahasha.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu:
Na farko:nacewa kan aikata sabo na iya kawar da mutum daga doran kasa da shafe zurriyarsa kamar yadda mummunan aiki ke shafe ayyuka masu kyau ko kuma mai kyau ya shafe maras kyau.
Na biyu: idan muna iyawa to ya zama wajibi mu hana aikata sabo ,kuma idan bam u iyawa sai mu yi gudun hijira zuwa wani guri mai aminci da babu fasikanci da aikata sabo.
To madallah yanzu kuma za mu saurari aya ta 81 a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda.
قَالُواْ يَا لُوطُ إِنَّا رُسُلُ رَبِّكَ لَن يَصِلُواْ إِلَيْكَ فَأَسْرِ بِأَهْلِكَ بِقِطْعٍ مِّنَ اللَّيْلِ وَلاَ يَلْتَفِتْ مِنكُمْ أَحَدٌ إِلاَّ امْرَأَتَكَ إِنَّهُ مُصِيبُهَا مَا أَصَابَهُمْ إِنَّ مَوْعِدَهُمُ الصُّبْحُ أَلَيْسَ الصُّبْحُ بِقَرِيبٍ{81}
- Bakin suka ce: Ya Ludu, hakika mu manzannin Ubangijinka ne , ba za su iso gare ka ba don bata mana,to sai ka tafi da iyalinka cikin wani yanki na dare, kada kuwa daya daga cikinku ya waiwaya,sai matarka kawai. Hakika ita kam abin day a same su zai same ta. Ba shakka lokacin da aka debar musu asuba ne kawai,shin asuba ba kurkusa take ba ?.
Annabi Ludu (AS) ya fuskanci matsin lamba da kuma barazana daga masu mummunan aiki daga cikin mutanasa kafirai da suka bijirewa umarni da hukumcin Allah. Ganin halin da yake ciki sai mala'iku suka kwantar masa da rai da fayyace masa gaskiyar abin da yake tafe da su cewa ba za su iya cutar dam u da kuma kai ba kuma asali ma Allah ya aiko mu ne domin azabtar da su da azaba mai radadi kuma a daren yau din nan ka fice daga gari kuma kar ku yi waiwaye da kallace-kallace harzuwa asubahi lokacin da azabar Allah za ta sabka saidai matarka za ta kasance daga cikin kafiran da azaba za ta sabka a kansu saboda a maimakon ta damu da halin da ke ciki da yin imani da abin da aka aiko ka da shi ta kasance tare da masu aikata sabo da mummunan aiki.
Wannan aya tana jinjina banbanta matsayin mutane masu imani da dangantaka ta jinni kuma da tunatar dam u sanin babu wani amfani kasancewa daya daga cikin iyalan gidan annabi kuma hakan ba zai zama sanadiyar kubutarmu da tsiratar da mu face ayyukan da muka aikata da kuma imani da muka yi da annabi da manzo.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu:
Na farko: Mace tana da yancin zabar abin da taga dama a tunani da akida hatta matar manzo da annabi da take rayuwa da shi tana da yancin zabar abin day a sabawa akidar mijinta.
Na biyu:A tsarin da sunnar Allah kimar mutum tana karkashin aiki da imaninsa ba wai dangantaka ta jini ba.
A saurari aya ta 82 da 83
فَلَمَّا جَاء أَمْرُنَا جَعَلْنَا عَالِيَهَا سَافِلَهَا وَأَمْطَرْنَا عَلَيْهَا حِجَارَةً مِّن سِجِّيلٍ مَّنضُودٍ{82} مُّسَوَّمَةً عِندَ رَبِّكَ وَمَا هِيَ مِنَ الظَّالِمِينَ بِبَعِيدٍ{83}
82- Lokacin da umarninmu ya zo sai Muka maida samanta kassa wato alkarya Muka kuma yi mata rowan duwatsu irin na soyayyen yunbu wasu bayan wasu.
83- wadanda aka yi wa alama daga Ubangijinka . Ba kuwa nesa take (Alkarya da azzalumai ba watau kuraishawa.
Wadannan ayoyi na yin bayani ne kan kumci da wahalwalun da mutanan Annabi Ludu da suka kafirce masa da kin amincewa da kiransa su day a yi zuwa ga Tauhidi suka fada. Ruwan duwatsu daga sama da kuma girgizar kasa da ta ruguza gidajansu da rubta masu.Tun a wannan duniya azaba da fushin Allah sun abkawa wadannan mutane. Kur'ani ta kawo mana wannan kissa ta hakika da ta wakana a tarihi domin hakan ya zame mana darasi a rayuwa da sanin cewa wannan azaba ba wai kawai ta abkawa mutanan annabi Ludu kafirai ban e a'a duk wata al'umma da mutanan da suka kafirce da kaucewa hanya da aikata ayyukan assha irin nasu za su gamu da fushi da azabar Allah mai radadi da zafin kuna da kuma ke hallaka duk wanda ya kafircewa ni'imar Allah .
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu:
Na farko:rashin godiya da kafircewa ni'imomin Allah na haddasa sabkar azaba kuma shi kafiri a kullum zai ganu da azabar da aka yi masa tanadi.
Na biyu:Kudura da hikimar allah ta fi karfin tunaninmu ,allah ne mai sabkar da rowan sama ya zama rahama a gare mud a albarka yana iya sabkar da zaba domin ta zama darasi da fadakarwa ga masu aikata saboda da banna a doran kasa.
Wadannan ayoyi sune na karshe a cikin wannan sura ta hud (AS) da ke bayani kan abubuwan da suka wakana a tsakanin annabi Ludu (AS) da kuma mutanan da aka turo shi zuwa gare su domin shiryar da su da kuma fadakar da su zuwa ga Tauhidi da kadaita Allah tabaraka wata'ala amma suka bijire da ci gaba da aikata banna da fasadi a doran kasa na saduwa a tsakaninsu yan jinsi daya maza da hakan babban sabo ne a hankalce da kum a dokoki na Allah da addinin shiriya.duk da tsawon shekaru da Annabi Ludu (AS) ya yi yana wa'azi da kokarin shiryar da mutanansa sun ki amincewa da kiransa da yin tubada daga aika wannan aiki mummuna sai yan kadan daga cikinsu da suka yi imani da shi ,Hatta matarsa da ke rayuwa tare da shi bat a yi imani da shi ba domin kuwa kamar yadda ayoyi suka yi bayani da kuma yadda mala'ikun da aka turo don hallaka kafiran mutanan Annabi Ludu (AS) suka gaya masa cewa matarsa tana daga cikin wadanda za a hallaka to wannan na nuni da yadda ya fuskanci izgili da rashin mutunci daga wadannnan kafirai.To sama da shekaru dubbai da wannan lamari ya wakana amma Alkur'ani yana tunatar dam u da kuma fadakar dam u munin wannan aiki da mummunan sakamakon day a biyo baya.amma kash a yau wasu gwamnatoci da daidaikun mutane da kungiyoyi da ke raya kare hakkin dan adam na kokowa da yin kiraye-kirayen karwa ba kunya balantan asanin abin day a kamata na a bawa yan luwadi da madugo dama da yancin aikata wannan mummunan aiki da ke ruguza rayuwar Allah da ci gabanta hatta wasu kasashe da gwamnatoci sun amince da yin aure a tsakanin yan jinsi daya a wannan karni na ashirin da daya da muke raya wayewa da ci gaba da sanin ya kamata da raya kare hakkin dan adam da addini.Amma duk da waka wani nauyi ne kan shugabannin addini musamman malaman magadan Annabawa da su ci gaba da aikin da suka saba babu gajiyawa na fadakar da al'umma da wayar da ita da kuma ilmantar da ita sanin munin aikata sabo da kuma abubuwan da kan iya biyo bayan haka ko a wannan duniya ko kuma a gobe kiya kuma kar su fidda tsamma'anin yin nasara a wannan kokari nasu na shiryar da al'umma.
Da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau na hannunka mai sanda kuma kafin mako na sama da yardar Allah ni Tidjani Malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa wassalamu………
Suratu Hud, Aya Ta 84-86 (Kashi Na 359)
Jama'a masu saurare barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hanunnka mai sanda, shirin da a cikinsa muke yin bayani da dubi a cikin ayoyin alkur'ani mai girma da domin ya zama jagora a rayuwar ta dukkan bangarori .Kuma babu wani littafi da hanyar da tafi yin riko da alkur'ani da kuma tafarkin ma'aikin Allah tsira da aminci ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka kuma ko shakka babu duk wanda ya yi riko da wadannan abubuwa biyu zai samu tsira da dacewa duniya da lahira bugu da kari ya samu sauki da walwala a rayuwarsa ta wannan duniya da samin hisabi mai sauki a ranar da tsanani da kunci da damuwa ya lullube zukata da tunanin kowa. Da fatar Allah ya lullube mu da rahama da lutifinsa duniya da lahira amin.
Yanzu kuma za mu fara da shiga cikin kwaryar shirin gadan gadan tare da sauraren aya ta 84 a cikin wannan sura ta Hud kamar haka:
وَإِلَى مَدْيَنَ أَخَاهُمْ شُعَيْباً قَالَ يَا قَوْمِ اعْبُدُواْ اللّهَ مَا لَكُم مِّنْ إِلَـهٍ غَيْرُهُ وَلاَ تَنقُصُواْ الْمِكْيَالَ وَالْمِيزَانَ إِنِّيَ أَرَاكُم بِخَيْرٍ وَإِنِّيَ أَخَافُ عَلَيْكُمْ عَذَابَ يَوْمٍ مُّحِيطٍ{84}
84- Kuma Mun aiko wa mutanen Madiyana dan uwansu Shu'aibu ,y ace Ya mutanena ,ku bauta wa allah ,ba ku da wani Ubangiji waninsa,kada kuma ku tauye mudu da ma'auni,hakika ni ina ganin ku da alheri watau wadata,kuma hakika ni ina tsoratar muku azabar rana mai kewayewa.
Bayan bayani kan karshe da mummunar makomar kafirai daga cikin mutanan Annabi Nuhu ,annabi Hud,annabi Salihu da Annabi Ludu (AS) yanzu kuma za mu fara ne da kawo ayoyin da ke bayani kan abin da ya wakana a tsakanin Annabi Shu'aibu (AS) da mutanansa da suka rayu a yankin Madyana a arewacin kogin Akaba wato da ake kira kasar Jodan a yanzu inda Allah ya aiko shi da sakon shiryar da mutanan wannan yanki domin kiransu zuwa ga Tauhidi na kadaita Allah da bota kuma su rika yin gaskiya da adalci a harkokinsu na saye da sayarwa idan sun yi haka Allah zai wadata su. Idan muka yi dubi za mu fahimci cewa dukan Annabawa da Manzonni an aiko sun e domin yin kira zuwa ga Tauhidi da shiryar da mutane kan hanya madaidaiciya kuma idan mutane suka amince da wannan kira na Annabawa ko wani daga cikin Annabawa da manzonni zai samu yanci da kubutar da kansa daga zalunci da danniyar dagutu da shugabanni azzalumai kuma zai bautawa mahaliccinsa da shi ne masani wanda ya yi duniya da lahira da halittun da ke cikinsu da kuma shi ne ya cancanci a bota masa to idan mutum ya kai wannan matsayi a dabi'ance bay a wuce iyakokin da shari'a da dokoki na hankali suka shata masa kuma zai kiyaye da mutunta hakkokin sauran mutane da halittun da yake rayuwa tare da su. Sai dai wani abin lura da la'akari a nan bautawa Allah madaukakin sarki ba wai kawai yana nufin yin Sallah da Azumi da zuwa hajji da sauran ayyukan ibada kamar addu'a da dai sauransu a'a ana bukatar hadawa da kiyaye dokokin Allah a rayuwa ta daidaiku ko ta jama'a da zaman takewa day a shafi dukan bangaren rayuwa kama daga harkokin tattalin arziki,siyasa da zamantakewar al'ummma to wannan na daga cikin abubuwan da imani ke bukatarsu .Saboda da haka Annabi Shu'aibu (AS) bayan kiran mutanansa zuwa ga kadaita Allah da bauta domin shi ne ya cancanci haka ba waninsa ya kuma yi kiransu da su daina da tuba daga mummunan aiki day a sabawa hanya ta adalci a saye da sayarwa kuma rashin ciniki da suke fuskanta wata azaba ce daga Allah sakamakon mummunan aikinsu na zaluntar mutane.
Wannan yana bayyana mana cewa tarihun bani adam yana cike da darasi da misalai daga wannna yanki zuwa wancan yanki kuma akwai nauy'nauyi na sabo da fasadi da aka aikata a baya da kuma wadanda ake aikatawa a yanzu .Mutanan Annabi Ludu sun kasance masu fasikanci da saduwa a tsakanin yan jinsi daya maza yayin da mutanan Annabi Shu'abu (AS) suka kasance sun yi fice ta fuskar fasadin tattalin arziki hart a kai an aiko Annabi takanas domin ya fadakar da su da yin tuba a saye da sayarwa.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu:
Na farko: manzonni ba wai kawai suna yin fadakarwa ne kan abubuwa da suka shafi akida da akhalaki a'a hatta bangaren rashin adalci a tattalin arziki da sauran matsaloli na rayuwa suna fadakarwa a kansu domin samin daidaito da isa ga kamala.
Na biyu: tunatarwa da fadakarwa da lahira da ranar hisabi na iya sawa mai banna ya komo cikin hayyacinsa da samin shiriya.
To madallah yanzu kuma za mu saurari aya ta 85 a cikin suratul Hudu kamar haka;
وَيَا قَوْمِ أَوْفُواْ الْمِكْيَالَ وَالْمِيزَانَ بِالْقِسْطِ وَلاَ تَبْخَسُواْ النَّاسَ أَشْيَاءهُمْ وَلاَ تَعْثَوْاْ فِي الأَرْضِ مُفْسِدِينَ{85}
85-Kuma ya mutanena ,ku cika mudu da ma'auni da adalci ,kada kuwa ku tauye wa mutane abubuwansu ,kada ku yi barna da gangan a bayan kasa.
Annabi Shu'aibu (AS) yana kiran mutanansa zuwa ga yin adalci da kwatamta gaskiya a saye da sayarwa ta hanyar kiyaye dokoki da ka'idodin saye da sayarwa babu rage mudu da cika mudu idan su nne za su saya amma idan za su sayar sai su rage inda ya jinjina masu cewa; boye cimaka da kin sayar da ita ga jama'a ko tauye mudu da yin zalunci a cikin saye da sayarwa wani nauyi ne na fasadi a doran kasa kuma mai yin haka fasidi ne domin mummunan aikinsa yana yaduwa a tsakanin jama'a da kuma gurbata rayuwa da ci gaban jama'a.
Shi sabo da mu mutane muke aikatawa iri biyu ne . Na farko sabon da muke aiaktawa ko wani ke aikatawa da yake cutar da shi karan kansa da kuma yin tasiri kansa ba waninsa ba kuma ko da zai yi tasirin kan waninsa tasirin kadan ne. Amma dayan biyun sabon zalunci ne kan wasunsa da tauye masu hakkokinsu kuma wannan sabo yafi muni da girma a gurin Allah.Domin Shi da kansa Allah y ace idan ya yafe wa wanda ya aikata lefi a cikin sabo nauyi na farko wannan tsakanisa ne da mahaliccinsa Amma shi nauyi na biyu ko da Allah ya yafewa bawansa yana bukatar sauran bayun Allah da yawa leifi su yafe masa.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu
Na farko:tattalin arzikin jama'a da dukiyar jama'a dole a tafiyar da ita cikin adalci da daidaito kuma dole a kiyaye dukiyoyin daidaikun mutane da jama'a cikin adalci da gaskiya.
Na biyu:gurbataccen tattalin arziki da ya dogara kan zalunci yana tilastawa jama'a cunduma cikin fasadi saboda haka ya rataya kan jagororin jama'a da su kiyaye.
To madallah yanzu kuma za mu ci gaba da sauraren aya ta 86 a cikin wannan sura ta hud:
بَقِيَّةُ اللّهِ خَيْرٌ لَّكُمْ إِن كُنتُم مُّؤْمِنِينَ وَمَا أَنَاْ عَلَيْكُم بِحَفِيظٍ{86}
86-Abin da zai wanzu a gare kun a alheri a wurin Allah shi ya fi muku in kun kasance muminai.Ni kuma ba mai gadin ku ba ne.
Annabi Shu'aibu (AS) bayan da ya hana mutanansa aikata sabo da rashin gaskiya a saye da sayarwa tare da kiransu zuwa ga kiyaye dokokin saye da sayarwa da cewa;duk ribar da kuka sami ta hanyar saye da sayarwa karkashin gaskiya da adalci za ta dawwama kuma Allah ya albarkace ta kuma idan kuka yi imani da bada gaskiya da Shi zai wadatar da ku da gamsuwa da abin da kuke samu na halaliya ba za ku yi kwadayin samin wani abu ta barauniya da haramtacciyar hanya ba. Annabi Shu'aibu ya ci gaba da cewa : Ni nauyina isar da sakon Allah ne zuwa gare ku .ni ba mai gadinku ban e kan ayyukan da kuke aikatawa ban e ,idan kun hallaka sakamakon mummunan aikin da kuka aikata babu abin da zan iya yi maku ko baku kariya. Wannan bangare na aikata gaskiya da adalci a saye da sayarwa yana da muhimmanci a wannan zamani na mu kuma a karshen zamani kamar yadda hadisai da dama suka yi bayani da nuni cewa: Imam Mahdi (AJ) zai bayyana domin tabbatar da gaskiya da adalci a daidai lokacin da zalunci da banna ya lullube duniya.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda uku
Na farko:arziki da dukiya kadan mai tsafta ta halaliya tafi dukiya mai yawa gurbatacciya ta haramtacciyar hanya.
Na biyu:Wannan duniya ke karewa ce cikin sauri saboda haka sai mu yi tunani da tanadin kasancewarmu a gurin Allah da ranar kiyama da aiki mai kyau n eke fishe mu.
Uku: duk wanda yake raya imani bai kamata ba ya rika nuna rashin gaskiya a saye da sayarwarsa ba.
Da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau na hannunka mai sanda kuma kafin mako na sama da yardar Allah ni Tidjani Malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa wassalamu………
Suratu Hud, Aya Ta 87-89 (Kashi Na 360)
Jama'a masu saurare barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hanunnka mai sanda, shirin da a cikinsa muke yin bayani da dubi a cikin ayoyin alkur'ani mai girma da domin ya zama jagora a rayuwar ta dukkan bangarori .Kuma babu wani littafi da hanyar da tafi yin riko da alkur'ani da kuma tafarkin ma'aikin Allah tsira da aminci ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka kuma ko shakka babu duk wanda ya yi riko da wadannan abubuwa biyu zai samu tsira da dacewa duniya da lahira bugu da kari ya samu sauki da walwala a rayuwarsa ta wannan duniya da samin hisabi mai sauki a ranar da tsanani da kunci da damuwa ya lullube zukata da tunanin kowa. Da fatar Allah ya lullube mud a rahama da lutifinsa duniya da lahira amin.
To madallah yanzu kuma za mu shiga cikin shirin gadan gadan tare da sauraren aya ta 87 a cikin suratul Hudu kamar haka;
قَالُواْ يَا شُعَيْبُ أَصَلاَتُكَ تَأْمُرُكَ أَن نَّتْرُكَ مَا يَعْبُدُ آبَاؤُنَا أَوْ أَن نَّفْعَلَ فِي أَمْوَالِنَا مَا نَشَاء إِنَّكَ لَأَنتَ الْحَلِيمُ الرَّشِيدُ{87}
Suka ce: "Yã Shu'aibu! Shin sallarka ce take umurtar ka ga mu bar abin da ubanninmu suke bautãwa, kõ kuwa mu bar aikata abin da muke so a cikin dũkiyõyinmu? Lalle, hakĩka kai ne mai hakuri shiryayye!"
A cikin shirin da ya gabata mun bayyana cewa: annabi Shu'aibu (AS) ya bukaci mutanansa da su kiyaye halaliya da haramin a cikin ma'amalarsu ta tattalin arziki da saye da sayarwa da kuma su kiyayi tauye hakkokin mutane da cewa; dan kadan din da za ku samu ta halaliya daga Allah yafi maku alheri da samin yawa ta haramiyar hanya.Amma mushirkan Madyana bayan ba a shirye suke su saurari wannan kira na gaskiya balantana su amsa masa sai ma suke ce masa;muna ganinka mutum mai wayewa da fahimta da tsinkayen nesa amma abin mamaki kana irin wannan magana da jawabi na ban mamaki.shin kana nufin mu bara sarrafa dukiyarmu yadda muka ga dama da barin abin da muka gada iyaye da kakanmu yau ga abin mamaki. Wani abin mamaki duk abin da annabi Shu'aibu ya bukaci mutanansa na alaheri da aikatawa sai su danganta da yawan ibada da sallarsa.To su sani haka ibada da salla ta gaskiya take tana hana mutum aikata sabo da sanyawa ya zama mutuman kirki na gari abin kaunar kowa.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu
Na farko:salla da addu'oin sun ahada dukan addainai tun fil azal kuma duk mabiya addinai suna saduwa da Allah ne ta hanyar salla da addu'a.
Na biyu:Biyayya da tunani da akidar iyaye da kakanmu ba zai zama dalili da hujja kan kiran annabawa da manzonni da fakewa da hakan .
N uku:Mallakar abin bai zama dalilin yin abin da mutum yaga dama da dukiyarsa dole a kiyaye dokokin Allah da na zamantakewa.
Yanzu kuma za mu saurari aya ta 88 a cikin wannan sura ta Hud kamar haka:
قَالَ يَا قَوْمِ أَرَأَيْتُمْ إِن كُنتُ عَلَىَ بَيِّنَةٍ مِّن رَّبِّي وَرَزَقَنِي مِنْهُ رِزْقاً حَسَناً وَمَا أُرِيدُ أَنْ أُخَالِفَكُمْ إِلَى مَا أَنْهَاكُمْ عَنْهُ إِنْ أُرِيدُ إِلاَّ الإِصْلاَحَ مَا اسْتَطَعْتُ وَمَا تَوْفِيقِي إِلاَّ بِاللّهِ عَلَيْهِ تَوَكَّلْتُ وَإِلَيْهِ أُنِيبُ{88}
Ya ce: "Ya mutãnena! Kun gani idan no kasance a kan hujja bayyananniya daga Ubangijina, kuma Ya azurta nĩ da arzikimai kyãwo daga gare Shi? Kuma bã ni nufin in sãba muku zuwa ga abin da nake hana ku daga gare shi. Bã ni nufin kõme fãce gyãrã, gwargwadon da na sãmi dãma. Kuma muwãfakãta ba ta zama ba fãce daga Allah. A gare shi na dõgara, kuma zuwa gare Shi na wakkala."
A wannan ayar Annabi Shu'aibu (AS) ya amsawa mutanansa wannan maganaganu na rashin hankali da cewa; idan ina hana ku sarrafa dukiyoyinku ta hanyoyin da ba su dace ba ,ba don komi bane sai gyara a rayuwa da zamantakewarku, ba wai don kashi da ahssada ba ne kun fahimta.Allah ne ya aiko ni da hujjoji mabayyanu domin shiryar da ku kuma ni ina dogaro da Allah ne a wannan nauyi na isar da sakonsa ko ku amince da yin imani ko kuma ku yin watsi , Ni dai ba zan bijirewa umarnin allah ba.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu
Na farko: rayuwa mai inganci ba ta samuwa ta hanayr tara dukiya ta haramin saboda haka a nemi dukiya ta halaliya kamar yadda Allah ya umurce mu.
Na biyu:Burin manzonni gyaran al'umma da rayuwa jama'a da dora bil adama kan tafarki na madaidaici kuma karkashin dogaro da Allah suna iyakacin kokarinsu na cimma nasara.
Yanzu kuma za mu saurari aya ta 89 a cikin wannan sura ta Hud kamar haka
وَيَا قَوْمِ لاَ يَجْرِمَنَّكُمْ شِقَاقِي أَن يُصِيبَكُم مِّثْلُ مَا أَصَابَ قَوْمَ نُوحٍ أَوْ قَوْمَ هُودٍ أَوْ قَوْمَ صَالِحٍ وَمَا قَوْمُ لُوطٍ مِّنكُم بِبَعِيدٍ{89}
"Kuma ya mutãnena! Kada sãba mini ya dauke ku ga misãlin abin da ya sãmi mutãnen Nũhu kõ kuwa mutãnen Hũdu kõ kuwa mutãnen Sãlihu ya sãme ku. Mutãnen Lũdu ba su zama a wuri mai nĩsa ba daga gare ku."
Annabi Shu'aibu (AS) a ci gaba da gabatar da dalilai da hujjoji a kokarinsa na shiryar da al'ummarsa ya yi masu kashedi da tsoratar da su da azabar Allah a salon fadakarwa da kashedi da cewa; abin da ya faru kan al'ummar annabi Ludu (AS) bai yi nisa da ku ba kuna da masaniya kan abin da ya faru da su ko ba komi sai ku yi tunani da nazari a cikin tarihin al'ummomin da suka gabata da ganin mai ya faru da karshen wadanda suka yi adawa da bijirewa kiran Annabawa da manzonni (AS).Shin me yasa ba ku daukan darasi kan abin da ya faru a baya sai ku rika yin abin da zai gaggawa sabkar azabar Allah kan ku a wannan duniya, har ila yau kar ku yi zaton adawa da ni da abin da na zo maku da shi alheri ne a gare ku ,a'a adawa da ni yana a matsayin adawa da Allah da haka kuma ku haddasa sabkar azaba a kanku.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu
Na farkoTarihin rayuwar dan adam tana kama da juna saboda haka yin nazari a cikin tarihin al'ummomin da suka gabata zai taimaka mana inganta rayuwa da sakamakonmu a nan gaba.
Na biyu:Azabar Allah a kullum za ta fadawa wadanda suka bijirewa umarninsa kuma za su hallaka kamar yadda mutanan Annabi Nuhu aka nutsar da su .ko mutanan Hud da Dubanu ya shafe su ko mutanan Salihu da aka tsoratar da su da kara ko mutanan Annabi Ludu da aka durkusar da su a gidajansu.
Da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shirin na yau sai kuma shiri na gaba da yardar Allah kafin lokacin Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram na na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalamu alaikum warahmatullahi wa barkatuhu.
Suratu Hud, Aya Ta 90-95 (Kashi Na 361)
Jama'a masu saurare barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hanunnka mai sanda, shirin da a cikinsa muke yin bayani da dubi a cikin ayoyin alkur'ani mai girma da domin ya zama jagora a rayuwar ta dukkan bangarori .Kuma babu wani littafi da hanyar da tafi yin riko da alkur'ani da kuma tafarkin ma'aikin Allah tsira da aminci ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka kuma ko shakka babu duk wanda ya yi riko da wadannan abubuwa biyu zai samu tsira da dacewa duniya da lahira bugu da kari ya samu sauki da walwala a rayuwarsa ta wannan duniya da samin hisabi mai sauki a ranar da tsanani da kunci da damuwa ya lullube zukata da tunanin kowa. Da fatar Allah ya lullube mud a rahama da lutifinsa duniya da lahira amin.
To madallah yanzu kuma za mu shiga cikin shirin gadan gadan tare da sauraren aya ta 90 a cikin suratul Hudu kamar haka;
وَاسْتَغْفِرُواْ رَبَّكُمْ ثُمَّ تُوبُواْ إِلَيْهِ إِنَّ رَبِّي رَحِيمٌ وَدُودٌ{90}
"Kuma ku nẽmi Ubangijinku gãfara, sa'an nan kuma ku tũba zuwa gare shi. Lalle Ubangijĩna Mai Jin kai ne, Mai nũna sõyayya."
A shirin da ya gabata mun bayyana cewa; mutanan garin Madyana ba a shirye suke ba su amsa kiran Annabi Shu'aibu (AS) sai ma suka nuna masa bakar adawa da kiyayya amma duk da haka Annabi Shuaibu (AS) ya ci gaba da yi masu nasiha da yi masu fatar alheri da ce masu idan ba ku yi a hankali ba da gyara rayuwarku za ku iya fuskantar azaba da fushin Allah. To ita ma wannan ayar tana magana ne kan ci gaba da kiran da Annabi Shu'aibu (AS) yake yiwa al'ummarsa da cewa guri bai kure masu ba su tuba domin Allah mai karbar tuba ne kuma mai rahama da jin kai ne .Kuma ku sani hanyar tuba wata babbar rahama ce daga Allah ga bayunsa.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu
Na farko: A daidai lokacin da ake tsoratar da masu banna ana bukatar nuna masu hanyar tuba da gyara ayyukansu .
Na biyu:Allah bayan yana karbar tuba yana kuma kaunar masu tubar.
Yanzu kuma za mu saurari aya ta 91 a cikin wannan sura ta Hud kamar haka
قَالُواْ يَا شُعَيْبُ مَا نَفْقَهُ كَثِيراً مِّمَّا تَقُولُ وَإِنَّا لَنَرَاكَ فِينَا ضَعِيفاً وَلَوْلاَ رَهْطُكَ لَرَجَمْنَاكَ وَمَا أَنتَ عَلَيْنَا بِعَزِيزٍ{91}
Suka ce: "Yã Shu'aibu! Bã mu fahimta da yawa daga abin da kake fadi, kuma munã ganin ka mai rauni a cikinmu. Kuma bã dõmin jama'arka ba dã mun jẽfe ka, sabõda ba ka zama mai daraja a gunmu ba."
Duk da kauna da damuwar da Annabi Shu'aibu (AS) ya nunawa mutansa ,kafirai daga cikinsu sun ci gaba da yin jayayya da nuna bakar kiyayya da shi da yi masa barazanar kashe shi ,bugu da kari suka ka yi zargin cewa abubuwan da yake fada da jawabinsa ba a iya fahimata ,Alhali kuwa daya daga cikin abubuwan da Annabawa da manzonni suka yi fice shi ne sauki da salon bayani da kowa zai fahimta tare da kawo dalilai da hujjoji da mu'ujiza. Amma kafirai sai suka kaskantar da annabi shua'aibu (AS) da nuna kokarin da yake yi ba kan komi ba yake.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu
Na farko:Annabawa da manzonni (AS) sun jurewa mafi munin cin fuska da tozartarwa ta fatar baki da ta duka da ma'amala.
Na biyu:Masu adawa da Annabawa ba su da wani dalili na hankali sai kawai cin fuska da azabtarwa da kuma aikata kisa.
Yanzu kuma za mu saurari aya ta 92 da 93 a cikin wannan sura ta Hud kamar haka
قَالَ يَا قَوْمِ أَرَهْطِي أَعَزُّ عَلَيْكُم مِّنَ اللّهِ وَاتَّخَذْتُمُوهُ وَرَاءكُمْ ظِهْرِيّاً إِنَّ رَبِّي بِمَا تَعْمَلُونَ مُحِيطٌ{92} وَيَا قَوْمِ اعْمَلُواْ عَلَى مَكَانَتِكُمْ إِنِّي عَامِلٌ سَوْفَ تَعْلَمُونَ مَن يَأْتِيهِ عَذَابٌ يُخْزِيهِ وَمَنْ هُوَ كَاذِبٌ وَارْتَقِبُواْ إِنِّي مَعَكُمْ رَقِيبٌ{93}
Ya ce: "Ya mutãnena! Ashe, jama'ãta ce mafi daraja a gare ku daga Allah, kuma kun rikẽ Shi a bãyanku abin jẽfarwa? Lallene Ubangijĩna Mai kẽwayẽwa nega abin da kuke aikatãwa."
"Kuma ya mutãnena! Ku yi aiki a kan hãlinku. Lalle nĩmai aiki ne. Da sannu zã ku san wãne ne azãba zã ta zo masa, ta wulakanta shi, kuma wãne ne makaryaci. Kuma ku yi jiran dãko, lalle ni mai dãko ne tãre da ku."
Lokacin da kafirai da mushrikai suka aikata da fadar duk abin da za su fada masu muni kan annabi Shu'aibu (AS0 kuma ya fahimci babu wata fatar yin imani a gare su sai ya ce masu to duk wani abu da kuke son aikatawa sai ku aikata , Ni ma zai yi riko da hanyar da naga tafi yi mani alheri ko ba da jimawa ba za a ga wake kan gaskiya ku wane ne daga cikinmu zai isa ga sa'ada kuma kar ku yi zaton don kuna al'ummata da kabilata nake gaya maku haka.Idan ba don haka ba ai da mun kashe ka .Ku aikata duk abin da kuka ga dama ni dai na dogara da Allah. Kuma Allah masani ne kan abubuwan da kuke aikatawa kuma kune mabukata a gare shi.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu
Na farko: Idan wa'azi da nasiha sun gagara sai a isa ga tsoratarwa da bayyana mummunan sakamako ga mabannata.
Na biyu:Idan guiwarmu ta yi sanyi a kokarin shiryar da mutane sai mu riki hanyar juriya da dogaro da Allah.
Yanzu kuma za mu saurari aya ta 94 da 95 a cikin wannan sura ta Hud kamar haka
وَلَمَّا جَاء أَمْرُنَا نَجَّيْنَا شُعَيْباً وَالَّذِينَ آمَنُواْ مَعَهُ بِرَحْمَةٍ مَّنَّا وَأَخَذَتِ الَّذِينَ ظَلَمُواْ الصَّيْحَةُ فَأَصْبَحُواْ فِي دِيَارِهِمْ جَاثِمِينَ{94} كَأَن لَّمْ يَغْنَوْاْ فِيهَا أَلاَ بُعْداً لِّمَدْيَنَ كَمَا بَعِدَتْ ثَمُودُ{95}
Kuma a lõkacin da umurninMu yã je, Muka kubutar da Shu'aibu da wadanda suka yi ĩmãni tãre da shi, sabõda wata rahama daga gare, Mu. Kuma tsãwa ta kama wadanda suka yi zãlunci. Sai suka wãyi gari guggurfãne a cikin gidãjensu.
Kamar ba su zaunã ba a cikinsu. To, halaka ta tabbata ga Madyana kamar yadda Samũdãwa suka halaka.
Haka makomar kafiran mutanan Madyana ya kasance kamar ta sauran kafirai da mushirikan da suka gabace su domin azaba ta sabka masu da hallakar da su.Duk wani mutum da ke doran kasa zai rasa ransa ta hanyarmutuwa ta dabi'a ko hadari amma mutuwar da ta biyo bayan azaba da fushin Allah ta nisanta da rahamar Allah sabanin kin karabar gaskiya karshe ne mai muni Alhali kuwa rahamar Allah nada fadi kamar yadda karfi da kudurarsa da fushinsa suke.Misali idan azabar Allah ta sabka a wani yanki kan wasu mutane sai ka ce da daya babu wani abu da ya taba rayuwa a gurin.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu
Na farko:Fushi da zabar Allah ko ba jima ko ba dade na sabka kan masu banna a doran kasa.
Na biyu:Imani wata hanya ce ta samin tsira kamar yadda kafirci ke zama wata hanayr hallaka.
Na uku: Nisantar masu banna wani umarni ne na Allah a cikin kur'ani .
Da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shirin na yau sai kuma shiri na gaba da yardar Allah kafin lokacin Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram na na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalamu alaikum warahmatullahi wa barkatuhu.
Suratu Hud, Aya Ta 96-101 (Kashi Na 362)
Jama'a masu saurare barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hanunnka mai sanda, shirin da a cikinsa muke yin bayani da dubi a cikin ayoyin alkur'ani mai girma da domin ya zama jagora a rayuwar ta dukkan bangarori .Kuma babu wani littafi da hanyar da tafi yin riko da alkur'ani da kuma tafarkin ma'aikin Allah tsira da aminci ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka kuma ko shakka babu duk wanda ya yi riko da wadannan abubuwa biyu zai samu tsira da dacewa duniya da lahira bugu da kari ya samu sauki da walwala a rayuwarsa ta wannan duniya da samin hisabi mai sauki a ranar da tsanani da kunci da damuwa ya lullube zukata da tunanin kowa. Da fatar Allah ya lullube mud a rahama da lutifinsa duniya da lahira amin.
To madallah yanzu kuma za mu shiga cikin shirin gadan gadan tare da sauraren aya ta 96 da 97 a cikin suratul Hudu kamar haka;
وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا مُوسَى بِآيَاتِنَا وَسُلْطَانٍ مُّبِينٍ{96} إِلَى فِرْعَوْنَ وَمَلَئِهِ فَاتَّبَعُواْ أَمْرَ فِرْعَوْنَ وَمَا أَمْرُ فِرْعَوْنَ بِرَشِيدٍ{97}
Kuma hakĩka Mun aiki Mũsã da ãyõyinMu, da dalĩli bayyananne.
Zuwa ga Fir'auna da majalisarsa. Sai suka bi umurnin Fir'auna, amma al'amarin Fir'auna bai zama shiryayye ba.
Bayan mun kawo karshen ayoyi da suke magana kan mutanan Annabi Shu'aibu da yadda karshensu ya munana to yanzu kuma za mu fara ne da bayanin ayoyin da ke bayani kan abubuwan da suka faru tsakanin Annabi Musa (AS) da kuma fir'auna da cewa: sabanin al'ummomin da suka gabata da yawanci aka aika annabawa da manzonni zuwa ga mutanan da suke rayuwa a lokacinsu ,Shi Annabi Musa (AS) da farko a aika shi ne kai tsaye zuwa ga fir'auna da daura masa nauyin tunkararsa kana daga bisani ya yi kokarin shiryar da Bani Isra'ila.Kuma wannan lamari ne da ya ke a fili matukar bani Isra'ila na karkashin mulkin fir'auna ba bu damar su shiriya da karbar kiran Annabi Musa (AS).Don haka amatakin farko sai an ruguza makircin fir'auna da mukarrabansa da kiran su zuwa ga karbar gaskiya da shiriyar da Annabi Musa (AS) ya zo da ita amma babu daya daga cikin fir'auna ko mukarrabansa da ya yi imani da wannan kira na shirira da Annabi Musa (AS) ya zo da shi.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu
Na farko" gwagwarmaya da daguti domin intar da mutum ne daga killacewar bauta da kuntatawar bayun Allah kuma wannan daya ne daga cikin shirin annabawa na intar da mutum.
Na biyu:Duk wata doka da umarni daga Allah zuwa ga mutane don isar mutum ne zuwa ga kamala da daukaka ta mutum da al'umma kuma babu wata doka da take da wannan siffa face dokokin Allah.
Yanzu kuma za mu saurari aya ta 98 a cikin wannan sura ta Hud kamar haka
يَقْدُمُ قَوْمَهُ يَوْمَ الْقِيَامَةِ فَأَوْرَدَهُمُ النَّارَ وَبِئْسَ الْوِرْدُ الْمَوْرُودُ{98}
Yanã shũgabantar mutãnensa a Rãnar Kiyãma, har ya tuzgar da su a wuta. Kuma tir da irin tuzgãwarsu.
Tabewar Fir'auna ba wai kawai ya hana shi kai wa ga kamala da ci gaba rayuwarsa ta shi kansa ko ta jama'a a'a zai kara gamuwa da fushin Allah da shiga wutar Jahannama kuma wadanda suke bin umarnin fir'auna makomarsu zata munana tare da shi a gobe kiyama.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu
Na farko:Lahira ce gurin girbi duk abin da mutum ya aikata a wannan duniya zai girbe shi da tayar da shi tare da abin da yake bautawa da kuma ya mamaye masa tunani.
Na biyu:shiri da guzuri na gari da ayyuka masu kyau na ci gaba na taimakawa mutum shiga aljanna da gamuwa da rahamar Allah a ranar kiyama.
Yanzu kuma za mu saurari aya ta 99 da 100 a cikin wannan sura ta Hud kamar haka
وَأُتْبِعُواْ فِي هَـذِهِ لَعْنَةً وَيَوْمَ الْقِيَامَةِ بِئْسَ الرِّفْدُ الْمَرْفُودُ{99} ذَلِكَ مِنْ أَنبَاء الْقُرَى نَقُصُّهُ عَلَيْكَ مِنْهَا قَآئِمٌ وَحَصِيدٌ{100}
Kuma aka biyar musu da la'ana a cikin wannan dũniyada Rãnar Kiyãma. Tir da kyautar da ake yi musu.
Wancan Yanã daga lãbãran alkaryõyi. Munã bã ka lãbãrinsu, daga gare su akwai wanda ke tsaye da kuma girbabbe.
Karshen fir'auna a wannan duniya shi ne nutsewa a tekun nilo da hakan ke nuni da tsinuwa da fushi da la'antar Allah kansa da mukarrabansa kafin su gamu da azabar ranar tashin kiyama kuma duk wani da ya yi riko da aiki irin nasa zai gamu da fushin Allah da zabarasa. Kawo labarin al'ummomin da suka gabata a cikin kur'ani mia girma don hakan ya zama darasi ne ga al'ummomi masu zuwa ne ba wai kur'ani tamkar littafin tarihi ne da kawo labari haka kawai ko kissoshi saboda haka ci gaban ayar yake cewa; bilbidin abubuwan mutanan da suka gabata don zama babban misali da darasi kan mu ne da fahimtar yaya suka hallaka.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu
Na farko: Kur'ani ne babban littafi abin dogaro na sanin tarihin mutanan da suka gabata.
Na biyu:Kawo kissa na babban tasiri ga wadanda ake karantawa saboda haka mu rika bin diddidigi da saurarre ko karanta kissoshin da kur'ani ya kawo a matsayinsu na kissoshi na hakika kuma babbar hanayr wa'azantuwa da fadakarwa.
Yanzu kuma za mu saurari aya ta 101 a cikin wannan sura ta Hud kamar haka:
وَمَا ظَلَمْنَاهُمْ وَلَـكِن ظَلَمُواْ أَنفُسَهُمْ فَمَا أَغْنَتْ عَنْهُمْ آلِهَتُهُمُ الَّتِي يَدْعُونَ مِن دُونِ اللّهِ مِن شَيْءٍ لِّمَّا جَاء أَمْرُ رَبِّكَ وَمَا زَادُوهُمْ غَيْرَ تَتْبِيبٍ{101}
Kuma ba Mu zãlunce su ba, amma sun zãlunci kansu sa'an nan abũbuwan bautawarsu wadanda suke kiran su, baicin Allah, ba su wadãtar musu kõme ba a lõkacin da umurnin Ubangijinka ya je, kuma (gumãkan) ba su kãra musu wani abu ba fãce hasãra.
Wasu daga cikin hadurra na dabi'a kamar ambaliyar ruwa da girgizar kasa da tarwatsa da suka hallakar da wasu al'ummomi kamar yadda ayoyin kur'ani suka nuna alama ce ta fushi da azabar Allah an wadannan al'ummomi.Saboda haka hadarin da zai yi sanadiyar mutuwar gungun mutane ko ya zamanto azaba ko kuma wata jarrabawa daga Allah ga mutane. Abin da kawai mutum ya fahimta Allah ba ya cutar bawa ko bayunsa.Mutum shi ne mai cutar kansa da kansa ta hanayr aikata sabo da fasadi a doran kasa da hakan ke gaggauta sabkar azaba.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu
Na farko:Makomar mutum tana a hannunsa karkashin gwalgwadon aiki da niyarsa ne.
Na biyu: babu wani mutum ko wani abu da zai iya canja kudura da iradar Allah ko fuskantar lamarinsa.
Da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shirin na yau sai kuma shiri na gaba da yardar Allah kafin lokacin Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram na na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalamu alaikum warahmatullahi wa barkatuhu.
Suratu Hud, Aya Ta 102-108 (Kashi Na 363)
Jama'a masu saurare barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hanunnka mai sanda, shirin da a cikinsa muke yin bayani da dubi a cikin ayoyin alkur'ani mai girma da domin ya zama jagora a rayuwar ta dukkan bangarori .Kuma babu wani littafi da hanyar da tafi yin riko da alkur'ani da kuma tafarkin ma'aikin Allah tsira da aminci ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka kuma ko shakka babu duk wanda ya yi riko da wadannan abubuwa biyu zai samu tsira da dacewa duniya da lahira bugu da kari ya samu sauki da walwala a rayuwarsa ta wannan duniya da samin hisabi mai sauki a ranar da tsanani da kunci da damuwa ya lullube zukata da tunanin kowa. Da fatar Allah ya lullube mud a rahama da lutifinsa duniya da lahira amin.
To madallah yanzu kuma za mu shiga cikin shirin gadan gadan tare da sauraren aya ta 102 da 103 a cikin suratul Hudu kamar haka;
وَكَذَلِكَ أَخْذُ رَبِّكَ إِذَا أَخَذَ الْقُرَى وَهِيَ ظَالِمَةٌ إِنَّ أَخْذَهُ أَلِيمٌ شَدِيدٌ{102} إِنَّ فِي ذَلِكَ لآيَةً لِّمَنْ خَافَ عَذَابَ الآخِرَةِ ذَلِكَ يَوْمٌ مَّجْمُوعٌ لَّهُ النَّاسُ وَذَلِكَ يَوْمٌ مَّشْهُودٌ{103}
Kuma kamar wancan ne kãmun Ubangijinka, idan Ya kãma alkaryõyi alhãli kuwa sunã mãsu zãlunci. Lalle kamũnSa mai radadi ne, mai tsanani.
Lalle ne a cikin wancan akwai ãyã ga wanda ya ji tsõron azãbar Lãhira. Wancan yini ne wanda ake tãra mutãne a cikinsa kuma wancan yini ne abin halarta.
A shirin da ya gabata sun kawo labarin karshen fir'auna da mukarrabansa na nutsewa a cikin ruwan maliya to suma wadannan ayoyin na cewa ne: kar mu yi zaton cewa fushin Allah da azabarsa ta kebanta da su ne kawai a'a duk wata al'umma ko mutuman da ya aikata sabo da wuce gona da iri makomarsa za ta kasance kamar ta fir'auna da mkarrabansa da gamuwa da fushin Allah.Kuma babu mai daukan darasi daga abubuwan da suka wakana kan mutane da al'ummomin da suka gabata kamar wadanda suka yi imani da ranar tashin kiyama.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu
Na farko:Lutifi da fushin Allah wata sunna ce dawamammiya ba wai wani abu ban e da ke abkuwa kwacam bat sari.
Na biyu:Duk wani zalunci yanada sakamako da sakayya wannan wani alkawali ne daga Allah.
Na uku:Ranar tashin kiyama ran ace ta shaida da ganin sakamako kuma karkashin umarnin Allah gabobi za su yi shaida kanmu.
Yanzu kuma za mu saurari aya ta 104 da 105 a cikin wannan sura ta Hud kamar haka
وَمَا نُؤَخِّرُهُ إِلاَّ لِأَجَلٍ مَّعْدُودٍ{104} يَوْمَ يَأْتِ لاَ تَكَلَّمُ نَفْسٌ إِلاَّ بِإِذْنِهِ فَمِنْهُمْ شَقِيٌّ وَسَعِيدٌ{105}
Ba Mu jinkirtã shi ba fãce dõmin ajali kidãyayye.
Rãnar da za ta zo wani rai ba ya iya magana fãce da izninSa. Sa'an nan daga cikinsu akwai shakiyyi da mai arziki.
Ayoyin da suka gabata suna magana ne ga mutane kan lamarin tashin kiyama to amma wasu na iya cewa; wannan rana ba za ta zo ba kuma wani abu ne da ba shi da tabbas saboda haka kur'ani ke cewa; ranar tashin kiya yanada lokaci takamammai kuma zata wakana idan lokacinta ya zo kuma Allah ne ya barwa kansa sani saboda hikima ,don haka kar ku ce me yasa za mu bar rayuwar duniya da rungumar lahira kan haka sai ci gaban ayar ke siffanta mana ranar tashin kiyama da cewa; a wannan rana babu wani da zai yi magana ko neman uzri da yin nadama sai da izinin Allah saboda Allah ya san komi da ayyukan da muka aikata kuma mai shaida ne kan hakan. Bayan Allah gabobinmu su bada shaida kanmu kuma mala'iku masu rubuta abubuwan da muke aikatawa a wannan duniya suma su bayar da ta su shaidar .A wannan rana ta kiyama komi zai bayyana wanda muka boye ko muka bayyana ma'ana babu wani abu komin kankantarsa da za a boye a wannan rana. Wannan shi ne adalci.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu
Na farko:Lokacin tashin kiyama da karshen rayuwa a wannan duniya wani abu ne tsararre a gurin Allah.
Na biyu:guzurin tashin kiyama shi ne aikata alheri da ganin haka a aikace ba a Magana babu cikawa ba.
Yanzu kuma za mu saurari aya ta 106 da 107 a cikin wannan sura ta Hud kamar haka
فَأَمَّا الَّذِينَ شَقُواْ فَفِي النَّارِ لَهُمْ فِيهَا زَفِيرٌ وَشَهِيقٌ{106} خَالِدِينَ فِيهَا مَا دَامَتِ السَّمَاوَاتُ وَالأَرْضُ إِلاَّ مَا شَاء رَبُّكَ إِنَّ رَبَّكَ فَعَّالٌ لِّمَا يُرِيدُ{107}
To, amma wadanda suka yi shakãwa, to, sunã a cikin wuta. Sunã mãsu kãra da shẽka acikinta.
Suna madawwama a cikinta matukar sammai da kasa sun dawwama, fãce abin da Ubangijinka Ya so. Lalle Ubangijinka Mai aikatãwa ne ga abin da Yake nufi.
Kamar yadda aka yi nuni kuma karkashin aya ta dari da biyar mutane a ranar tashin kiyama gungu biyu ne da cewa: gungu na farko yana cikin ni'ima da wadata yayin da gungu na biyu yana cikin kumci da tabewa ma'ana gungun wadanda suka aikata ayyukan kwarai da kuma gungun mabannata. A fili lamarin yake Allah ya halicci mutane ba tare da wani bambanci ba da bawa kowa zabin bin shiriya da samar masa da yanayi na bin hanya madaidaiciya amma wasu daga cikin mutane sai suka zabi bin hanyar tabewa da aikata banna kuma su ne umul aba'isar fadawa cikin kumcin da suka samu kansu a ci a wannan rana .Amma dayan bangare ya yi aiki da hankali da hangen nesa da cin nasarar rayuwa cikin aminci. A nan za mu iya fahimtar cewa; aminci da kumci ba wasu ababai ba ne da Allah ya tsara da kebanta su da wasu ba wasu ba idan haka ne babu alfanin daura mana takalifi da ba mu lada ko azabtar da mu kuma ranar tashin kiyama ba ta da wata ma'ana.Amma Allah ya ba mu zabi da nuna mana hanyoyi na alheri da kuma mummuna duk wanda ya aikata alheri zai samu lada kmar wanda ya aikata sabo zai gamu da fushi da azaba a wannan duniya da kuma gobe kuya karkashin zabi da ayyukan da ya aikata don radin kansa babu tilastawa.Mummunan aikin da muka aikata zai zama wuta a gobe kiyama da kunnar da wanda ya aika ma'ana duk abin da muka aikata na sabo shi ne zai kunna mu kuma wadanda za su dauwama a cikin wutar Jahannama saboda aikin da suka aikata ne har sai a goje mummunan aikin da suka aikata idan da sauran aikin alheri a gare su da samin ceto amma wasu daga cikin mujirimai za su dauwa a cikin wuta kamar yadda da za a dawwamar da su a rayuwar duniya za su dawwama ne cikin banna da aikata sabo.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu
Na farko: Sa'ada da kunci karkashin ayyukan da mutum ya aikata da zabinsa ne kuma makomar kowa yana a hannunsa ne.
Na biyu:Idan Allah ya so cikin hikima yana iya yantar da bawansa daga cikin wuta kuma yin hakan bay a gagararsa kuma yana yin e cikin hikima da dalili.
Da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shirin na yau sai kuma shiri na gaba da yardar Allah kafin lokacin Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram na na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalamu alaikum warahmatullahi wa barkatuhu.
Suratu Hud, Aya Ta 109-110 (Kashi Na 364)
Jama'a masu saurare barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hanunnka mai sanda, shirin da a cikinsa muke yin bayani da dubi a cikin ayoyin alkur'ani mai girma da domin ya zama jagora a rayuwar ta dukkan bangarori .Kuma babu wani littafi da hanyar da tafi yin riko da alkur'ani da kuma tafarkin ma'aikin Allah tsira da aminci ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka kuma ko shakka babu duk wanda ya yi riko da wadannan abubuwa biyu zai samu tsira da dacewa duniya da lahira bugu da kari ya samu sauki da walwala a rayuwarsa ta wannan duniya da samin hisabi mai sauki a ranar da tsanani da kunci da damuwa ya lullube zukata da tunanin kowa. Da fatar Allah ya lullube mu da rahama da lutifinsa duniya da lahira amin.
To madallah yanzu kuma za mu shiga cikin shirin gadan gadan tare da sauraren aya ta 108 a cikin suratul Hudu kamar haka;
وَأَمَّا الَّذِينَ سُعِدُواْ فَفِي الْجَنَّةِ خَالِدِينَ فِيهَا مَا دَامَتِ السَّمَاوَاتُ وَالأَرْضُ إِلاَّ مَا شَاء رَبُّكَ عَطَاء غَيْرَ مَجْذُوذٍ{108}
Amma wadanda suka yi arziki to, sunã a cikin Aljanna sunã madawwama ,a cikinta, matukar sammai da kasa sun dawwama, fãce abin da Ubangijinka Ya so. Kyauta wadda bã ta yankẽwa.
A shirin da ya gabata mun bayyana cewa mutane a ranar kiyama Allah ya kasa su gida biyu :ma'abuta aminci da sa'ada da kuma ma'abuta kumci da azabtuwa kuma a cikin ayoyin da suka gabata ma'abuta kumci sune wadanda wuta za ta kuna yayin da a wannan aya ke yin nuni da ma'abuta aminci wadanda za su shiga gidan aljanna da samin ni'imomin da Allah ya yi masu tanadi.Don haka abin lura a nan rahamar Allah tana da yalwa da fadi ko muna cikin aljanna ko kuma muna cikin wuta Allah ya yi mana tsari Allah yana yi mana rahama da jin kai .Dalili hatta aljanna wata kyauta ce daga gare shi ya yi mana bawai aikinmu ba .Hatta wadada za su shiga da dawwama a cikin aljanna wata rahama ce daga gare shi da karfin aikinmu ba domin ba za mu iya biyan ni'ima da falalar da ya yi mana.Kan haka duk halin da muka samu kanmu a ciki mu kasance masu yin godiya ga Allah madaukakin sarki.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu
Na farko:Sa'ada da aminci ya samu asali daga aikin mutum da kuma falala da rahamar Allah
Na biyu:Aljanna wata falala da lutfi da kyautar Allah ce ba wai cancantar mutum ba.
Yanzu kuma za mu saurari aya ta 109 a cikin wannan sura ta Hud kamar haka
فَلاَ تَكُ فِي مِرْيَةٍ مِّمَّا يَعْبُدُ هَـؤُلاء مَا يَعْبُدُونَ إِلاَّ كَمَا يَعْبُدُ آبَاؤُهُم مِّن قَبْلُ وَإِنَّا لَمُوَفُّوهُمْ نَصِيبَهُمْ غَيْرَ مَنقُوصٍ{109}
Sabõda haka kada ka kasance a cikin shakka daga abin da wadannan suke bautawa. Bã su wata ibãda fãce kamar yadda ubanninsu ke aikatãwa a gabani. Kuma hakĩka Mũ, Mãsu cika musu rabon su ne, bã tãre da nakasãwa ba.
Daya daga cikin abubuwan da ke yi wa Mumunai barazana shi ne shakku da kwakwaton hanyar da suka yi riko ko kan gaskiya suke ko bata da hakan ya ke sawa su yi kasa a guiwa wajan sabke nauyin da ya rataya a kansu na addini.Kan haka wannan ayar domin bayyana muhimmancin wannan lamari ta cewa Manzo ya gayawa mumunai kar su yi shakku kan batan hanyar mushrikai ma'ana suna cikin bata da tabewa duniya da lahira. A lura shi shakku a cikin lamura da suka shafi tunani da akida na wani lokaci yanada kyau da zai sa mutum ya yi bincike da zai kai shi ga samin nucuwa amma dawwama cikin shakku yanada hadari .
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu
Na farko:Dole mu yi tsayin daka kana bin da muka yi amanna gaskiya ne ko da kuwa dukan mutane na adawa da shi.
Na biyu:Babu alheri yin riko da abubuwan da muka gada daga iyaye da kakannu matukar ya sabawa addini.
Yanzu kuma za mu saurari aya ta 110 a cikin wannan sura ta Hud kamar haka
وَلَقَدْ آتَيْنَا مُوسَى الْكِتَابَ فَاخْتُلِفَ فِيهِ وَلَوْلاَ كَلِمَةٌ سَبَقَتْ مِن رَّبِّكَ لَقُضِيَ بَيْنَهُمْ وَإِنَّهُمْ لَفِي شَكٍّ مِّنْهُ مُرِيبٍ{110}
Kuma hakĩka, Mun bai wa Mũsã littãfi, sai aka sãbã wa jũna a cikinsa. Kuma bã dõmin wata kalma wadda ta gabãta daga Ubangijinka ba, hakĩka, dã an yi hukunci a tsakãninsu. Kuma hakĩka, sunã a cikin wata shakka, game da shi, mai sanya kõkanto.
Kamar ayar da ta gabata da ke bayanin kan shakku da mumunai suka yi da hadarin da ke tattare da hakan ita ma wannan ayar na cewa: wadanda suka yi imani da sakon Annabi Musa (AS) sun samu sabani da shakku dangane da littafin da aka sabkar masu watau Attaura kamar yadda wasu daga cikin mumunai suka yi kan Alkur'ani.Abin sani a nan idan shakku da kwankwanto ya shafi sanin gaskiya da bincike babu laifi ba wai kawai shakku ba wata hujja da dalili ko kuma mutum ya kirkiro shakku kan littafin Allah don nuna jayayya da kafirci ko mutum ya yi shkku kan azaba da fakewa cewa mai yasa ba ta shafarsu a wannan duniya don haka sai ya yi shaku kan azabar ranar lahira. A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu
Na farko:kar sabanin mutane a cikin addini da imani ya kai mug a shakku da kwankwanto cikin akida domin wannan ba wani abu ba ne sabo a'a akwai haka a tsawon tarihi.
Na biyu:Jinkirta azabtar da masu banna a doran kasa har sai ranar kiyama wata sunna ce ta Allah don haka kar ya taimaka mana mu sha'afa ko nuna dagawa.
Na uku:Duk da cewa Attaura da Kur'ani littafai daga Allah kuma haske amma wasu bas u ganin wannan haske sai ma su yi shakku kansu.
Da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shirin na yau sai kuma shiri na gaba da yardar Allah kafin lokacin Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram na na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalamu alaikum warahmatullahi wa barkatuhu.
Suratu Hud, Aya Ta 111-115 (Kashi Na 365)
Jama'a masu saurare barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hanunnka mai sanda, shirin da a cikinsa muke yin bayani da dubi a cikin ayoyin alkur'ani mai girma da domin ya zama jagora a rayuwar ta dukkan bangarori .Kuma babu wani littafi da hanyar da tafi yin riko da alkur'ani da kuma tafarkin ma'aikin Allah tsira da aminci ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka kuma ko shakka babu duk wanda ya yi riko da wadannan abubuwa biyu zai samu tsira da dacewa duniya da lahira bugu da kari ya samu sauki da walwala a rayuwarsa ta wannan duniya da samin hisabi mai sauki a ranar da tsanani da kunci da damuwa ya lullube zukata da tunanin kowa. Da fatar Allah ya lullube mud a rahama da lutifinsa duniya da lahira amin.
To madallah yanzu kuma za mu shiga cikin shirin gadan gadan tare da sauraren aya ta 111 a cikin suratul Hudu kamar haka:
وَإِنَّ كُـلاًّ لَّمَّا لَيُوَفِّيَنَّهُمْ رَبُّكَ أَعْمَالَهُمْ إِنَّهُ بِمَا يَعْمَلُونَ خَبِيرٌ{111}
Kuma lalle, hakĩka, Ubangijinka Mai cika wa kõwa (sakamakon) ayyukansa ne. Lalle Shĩ, Mai kididdigewa ne ga abin da suke aikatãwa.
Daya daga cikin sunnonin Allah shi ne sabkar da azaba ko rahama karkashin ayyukan da mutum ko al'umma ta aikata ne kan zabi kuma Allah masani ne kan ayyukanmu da niyar da muka kudurta wajan aikata wani aiki mai kyau ko mummuna ma'ana babu wani abu da ke boyuwa a gare shi komin kankantarsa.Tushen tsarin sakayya yana da dangantaka da ranar tashin kiyama duk da cewa a wannan duniya ma Allah yana yin sakayya ko ta alherin da mutum ya aikata ko mummuna.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu
Na farko: A gurin Allah babu wani aiki mai kyau ko maras kyau da ba shi da sakayya.
Na biyu:Azabtarwa ko bayar da lada a gurin Allah daidai da ayyukanmu ne babu kari ko ragi balantana a zalumci wani.
Yanzu kuma za mu saurari aya ta 112 a cikin wannan sura ta Hud kamar haka:
فَاسْتَقِمْ كَمَا أُمِرْتَ وَمَن تَابَ مَعَكَ وَلاَ تَطْغَوْاْ إِنَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ بَصِيرٌ{112}
Sai ka daidaitu kamar yadda aka umurce ka, kai da wadanda suka tũba tãre da kai kunã bã mãsu kẽtara haddi ba. Lalle shĩ, Mai gani ne ga abin da kuke aikatãwa.
A daidai lokacin da ayoyin da suka gabata na magana kan adawar da mushrikai da ma'abuta litta ke yi wa ma'aikin Allah da mumunai ita kuwa wannan ayar na yin magana ne ga Manzon Allah da Sahabbansa da cewa; kar maganganu da ma'amalar masu adawa da ku da sanya shaku cikin tafarkin Allah ya raunana zukatanku kawai ku ci gaba da yin riko da hanyar gaskiya da tafarki madaidaici kuma a dabra da haka kar ku wuce gona da iri da dokokin Allah kan masu adawa da ku ,ku sani Allah ya san halin da kuke ciki kuma Shi ne mai sakayya. Ya zo a cikin rawayoyi ma'aikin Allah (SWA) na cewa Suratul Hud ta tsufar da ni yana nufin wannan aya a cikin suratul Hud bawai kawai ma'aikin Allah take umurta da yin hakuri da tsayin daka hatta sahabbansa da mukarrabansa ta umurtarsu da yin hakuri da ci gaba da yin riko da tafarki madaidaici.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu
Na farko:tsayin Dakar jagora yana tafiya tare da tsayin Dakar al'ummarsa ne kuma da farko ana bukatar jagora abin koyi da zama misali.
Na biyu:A duk lokacin da za mu maida martini mu yi adalci kar mu wuce gona da iri.
Yanzu kuma za mu saurari aya ta 113 a cikin wannan sura ta Hud kamar haka
وَلاَ تَرْكَنُواْ إِلَى الَّذِينَ ظَلَمُواْ فَتَمَسَّكُمُ النَّارُ وَمَا لَكُم مِّن دُونِ اللّهِ مِنْ أَوْلِيَاء ثُمَّ لاَ تُنصَرُونَ{113}
Kada ku karkata zuwa ga wadanda suka yi zãlunci har wuta ta shãfe ku. Kuma bã ku da wadansu majiɓinta baicin Allah, sa'an nan kuma bã zã a taimake ku ba.
Bayan da Allah ya umarci mumunai da yin tsayin daga da ci gaba da yin riko da tafarkin gaskiya ita kuwa wannan ayar ta cewa ne: idan muka nuna kauna da soyayya ga masu adawa da addinin Allah ko muka dogara da su kar mu yi zaton za su taimaka mana da zama abukkanmu idan mu shiga kumci da bukatar taimako ba za su taimak mana da tabaka mana da komi ba .Abin da ya kamata mu sani Allah ne kawai majibinci mai taimakonmu da kasancewa tare da mu a kullum.Kusantar makiyan Allah da aikata sabo babu wani alheri sai haddasa fushin Allah da rura wutar kuna mu duniya da lahira.Ya zo a cikin ruwaya cewa: kar mu kusanci masu sabo da kaunar su da wani buri ko da kuwa makusantanmu ne domin daidai kusantarsu da amincewa da su daidai aikata sabo tare da su ne.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu
Na farko: a maimakon mu dogara da masu karfin zalunci da sabo ,mu dogara da Allah da yafi kowa karfi da kudura da taimaka mana.
Na biyu:A tsari irin na siyasar musulunci an hana dogaro da karfi da ya kafu kan zalunci da kafirci don haka babban sabo ne.
Na uku:Sakamkon dogaro da ma'abuta salunci da kafirci kadaici a ranar neman taimako.
Yanzu kuma za mu saurari aya ta 114 da 115 a cikin wannan sura ta Hud kamar haka
وَأَقِمِ الصَّلاَةَ طَرَفَيِ النَّهَارِ وَزُلَفاً مِّنَ اللَّيْلِ إِنَّ الْحَسَنَاتِ يُذْهِبْنَ السَّـيِّئَاتِ ذَلِكَ ذِكْرَى لِلذَّاكِرِينَ{114} وَاصْبِرْ فَإِنَّ اللّهَ لاَ يُضِيعُ أَجْرَ الْمُحْسِنِينَ{115}
-Kuma ka tsai da salla a gẽfe guda biyu na yini da wani yanki daga dare. Lalle ne ayyukan kwarai sunã kõre mũnãnan ayyuka. wancan ne tunãtarwa ga mãsu tunãwa. -Kuma ka yi hakuri. Allah bã Ya tõzartar da lãdar mãsu kyautatãwa.
Bayan da ayar da ta gabata ke kiranmu ga kauracewa kasancewa tare da masu sabo da kafirai ita kuwa wannan ayar ta umurtar ma'aikin Allah da sahabbansa da mumunai daga wancan lokaci har zuwa yau da kuma gobe da yin riko da salla da addu'o'o da tunawa da Allah a kullum da ambatonsa domin kasancewa tare da Allah a aikace da tunani na kawo aminci da kanciyar hankali da ta zucii da uwa uba ta ruhi da karfin fuskantar makiyan addini da tafrakin gaskiya kuma hakan zai taimaka a yafe mana zunubbanmu da sabkar rahamar Allah bayan kuma ayar ta kiraye mu ga yin riko da salla an kuma nanata mana muhimmancin yin hakuri da tsayin daka da hakan ke nuna dangantaka tsakaninsu da tsaida salla.
Ya zo a cikin ruwaya Imam Ali (AS) ya zo gurin wasu daga cikin gungun mutane suna zaune sai ya tambaye su a ganinku wace aya ce a cikin Kur'ani tafi kara mana karfin guiwar yafe mana .kowa ne daga cikinsu ya ce wannan aya ce wani ya ce wacce ce.sai Imam Ali (AS) ya ce na ji ma'aikin Allah (SWA) abin kauna ta na cewa: Ayar da tafi sanyaya mana rai da fatar yafe mana ita ce: ka tsaida salla a wani bangare na rana da wani sashe na dare hakika kyawawa ta wanke kazamta.Bayan da Ma'aikin Allah ya karanto wannan aya sai ya ce: Ya Ali na rantse da Allah a duk lokacin da mutum yayi alwalla domin yin salla ana yaye masa zunubbansa idan ya kalli Kibla ana tsarkake shi.Ya Ali misalin masallata tamkar mutuman da yake yin wanka ne so biyar a rana a cikin maliya shin wani abu zai yi saura na dauda a jikinsa.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu
Na farko:Salla wani tsari ne da ya kumshi lokaci da tsari na gari kuma kowa ce salla a yi ta daidai da lokacinsa.
Na biyu: Sallah it ace babban dalili na ayyuka masu kyau kuma gimshin ayyukan alheri.
Da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shirin na yau sai kuma shiri na gaba da yardar Allah kafin lokacin Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram na na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalamu alaikum warahmatullahi wa barkatuhu.
Suratu Hud, Aya Ta 116-118 (Kashi Na 366)
Jama'a masu saurare barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hanunnka mai sanda, shirin da a cikinsa muke yin bayani da dubi a cikin ayoyin alkur'ani mai girma da domin ya zama jagora a rayuwar ta dukkan bangarori .Kuma babu wani littafi da hanyar da tafi yin riko da alkur'ani da kuma tafarkin ma'aikin Allah tsira da aminci ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka kuma ko shakka babu duk wanda ya yi riko da wadannan abubuwa biyu zai samu tsira da dacewa duniya da lahira bugu da kari ya samu sauki da walwala a rayuwarsa ta wannan duniya da samin hisabi mai sauki a ranar da tsanani da kunci da damuwa ya lullube zukata da tunanin kowa. Da fatar Allah ya lullube mud a rahama da lutifinsa duniya da lahira amin.
To madallah yanzu kuma za mu shiga cikin shirin gadan gadan tare da sauraren aya ta 116 a cikin suratul Hudu kamar haka;
فَلَوْلاَ كَانَ مِنَ الْقُرُونِ مِن قَبْلِكُمْ أُوْلُواْ بَقِيَّةٍ يَنْهَوْنَ عَنِ الْفَسَادِ فِي الأَرْضِ إِلاَّ قَلِيلاً مِّمَّنْ أَنجَيْنَا مِنْهُمْ وَاتَّبَعَ الَّذِينَ ظَلَمُواْ مَا أُتْرِفُواْ فِيهِ وَكَانُواْ مُجْرِمِينَ{116}
To, don me mãsu hankali ba su kasance daga mutãnen karnõnin da suke a gabãninku ba, sunã hani daga barna a cikin kasa? fãce kadan daga wanda Muka kubutar daga gare su (sun yi hanin). Kuma wadanda suka yi zãlunci suka bin abin da aka ni'imtar da su a cikinsa, suka kasance mãsu laifi.
A shirin da ya gabata mun kawo ayoyin da ke kiran ma'aikin Allah da mumunai kan su yi tsayin daka da yin riko da tafarkin gaskiya da kuma tsaida salla to ita kuwa wannan ayar tana magana ne ga ma'abuta ilimi da kudura da aiki da hankali da hangen nesa da kar su zama sun yi wani abu da zai hana ci gaba al'umma ko yada fasadi a doran kasa kuma me yasa al'umma ba ta hana yaduwar zalumci da fasadi ta hanyar karfin ilimi da imani? Kamar wannan aya akwao ayoyin da ke kashedi ga makiya addini masu yaudarar jama'a kan aikata sabo da mamakin wannan lamari.Kur'ani ba ya na kashedi ne kan kowa da kowa a'a kan masu aikata sabon da ake magana tare da yin la'akari da yan tsuraru masu aiki da nauyin da ya rata a wuyansu masu kokarin tsiratar da jama'a amma masu son rai da bin dodar duniya na kokarin ganin sun batar da jama'a ta hanyar aikata sabo da fasadi a doran kasa.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu
Na farko:Ma'abuta ilimi da karfin iko babban nauyi ya rrataya kansu na kokarin kubutar da jama'a daga fasadi ba wais u zama sune ummul aba'isar fadawar al'umma cikin fasadin ba.
Na biyu:Babban dalilin fadawar al'ummar da ta gabat cikin fasadi shi ne shuru da halin ko in kulan magabata.
Yanzu kuma za mu saurari aya ta 117 a cikin wannan sura ta Hud kamar haka
وَمَا كَانَ رَبُّكَ لِيُهْلِكَ الْقُرَى بِظُلْمٍ وَأَهْلُهَا مُصْلِحُونَ{117}
Kuma Ubangijinka bai kasance Yanã halakar da alkaryu sabõda wani zãlunci ba, alhãli mutãnensu sunã mãsu gyãrãwa.
Bayan da ayar da ta gabata ke bayar da labarin hallakar al'ummomin da suka gabata to ita kuwa wannan ayar na cewa: kar mu yi zaton haka kawai Allah ya hallakar da su babu wani dalili ,saboda sunnar Allah haka ta gada na hallakar da azzalumai kuma ba za ta taba yuyuwa ba Allah ya hallaka mutane salihai .Ya zo a cikin ruwayoyi cewal abin nufi da gyaran al'umma shi ne adalci a cikin dangantaka da fatar kauna da laheri kowa idan al'umma ta kasance kan haka da rayuwa a haka Allah zai sabkar masu da rahamarsa ko da kuwa akwai bata gari fasikai da ke rayuwa a cikinsu. A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu
Na farko:Kasancewa salihin mutum kawai bai wadatar ba ana bukatar ayyukan gyaran al'umma kuma kowa yana da nauyin gyaran al'umma.
Na biyu:Azabar Allah ba wai kawai ta kebantu da lahira ne ba ,fushin Allah a wannan duniya yana shafar azzalummai.
Yanzu kuma za mu saurari aya ta 118 a cikin wannan sura ta Hud kamar haka:
وَلَوْ شَاء رَبُّكَ لَجَعَلَ النَّاسَ أُمَّةً وَاحِدَةً وَلاَ يَزَالُونَ مُخْتَلِفِينَ{118}
Kuma dã Ubangijinka Ya so, dã Yã sanya mutãne al'umma guda. Kuma bã zã su gushe ba sunã mãsu sãbã wa jũna.
Wannan ayar ta yi nuni da daya daga cikin siffofin Allah wato kudura da iradarsa a cikin ruhin mutum da gangar jjikinsa a dabra da haka kuma ya bawa mutum zabi da cewaa; duk da cewa: Allah ne mai zartarwa a duk wani abu da mutum ya kudurta da aikatawa kuma babu wani da zai fi karfin kudurar Allah .Amma duk da haka domin isar mutum ga kamala Allah ya bawa mutum falala ta zabar abin da ya yi niya da zabar makomarsa kuma sabanin banbancin akida nadaga cikin wannan dalili na zabi da aka bamu. Idan da Allah ya so dukan mutane za su zama mumunai da bin tafarkin gaskiya amma irin wannan imani a hadin kai ba shi da amfani da matsayi kamar mutum ya yi imani da zabar tafarkin gaskiya cikin yanci.Idan mutum ya zabi tafarkin gaskiya cikin ilimi da zabi ba bu tilastawa duk da akidu da fahimta iri iri wannan yafi daraja . Duk lokacin da aka yi maganar zabi dole a samu sabani da hanyoyi mabanbanta hanyar gaskiya da ta karya . Bugu da kari Allah ta hanyar bamu hankali da aiko da annabawa da manzonni ya shinfida ma mutum da sauwake masa hanayr shiriya da kuma yadda akwai lada ga wanda ya aikata alheri da kuma azaba ga wanda ya aikata sabo.Amma duk wannan ba su da dangantaka da tilastawa ,babban dalili shi ne yawancin mutane sun zabi tafarkin da ya sabawa na Allah amma duk da haka babu wanda Allah ya tilastawa bin tafarkinsa bil asali ma ya cewa ma'aikinsa cewa: ka kawai aikinka fadar gaskiya baka da izinin tilasta masu yin imani da addinin Allah .
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu
Na farko:Sunnar Allah ga mutum ita ce bawa mutum zabi da yancin zabar akida da tunanin da yaga ya dace da shi.
Na biyu:Sabani a cikin ra'ayoyi da tunani da akida a tsakanin mutane ya sabo asali da zabin da aka waba mutum ne.
Da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shirin na yau sai kuma shiri na gaba da yardar Allah kafin lokacin Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram na na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalamu alaikum warahmatullahi wa barkatuhu.
Suratu Hud, Aya Ta 119-123 (Kashi Na 367)
Jama'a masu saurare barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hanunnka mai sanda, shirin da a cikinsa muke yin bayani da dubi a cikin ayoyin alkur'ani mai girma da domin ya zama jagora a rayuwar ta dukkan bangarori .Kuma babu wani littafi da hanyar da tafi yin riko da alkur'ani da kuma tafarkin ma'aikin Allah tsira da aminci ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka kuma ko shakka babu duk wanda ya yi riko da wadannan abubuwa biyu zai samu tsira da dacewa duniya da lahira bugu da kari ya samu sauki da walwala a rayuwarsa ta wannan duniya da samin hisabi mai sauki a ranar da tsanani da kunci da damuwa ya lullube zukata da tunanin kowa. Da fatar Allah ya lullube mud a rahama da lutifinsa duniya da lahira amin.
To madallah yanzu kuma za mu shiga cikin shirin gadan gadan tare da sauraren aya ta 119 a cikin suratul Hudu kamar haka;
إِلاَّ مَن رَّحِمَ رَبُّكَ وَلِذَلِكَ خَلَقَهُمْ وَتَمَّتْ كَلِمَةُ رَبِّكَ لأَمْلأنَّ جَهَنَّمَ مِنَ الْجِنَّةِ وَالنَّاسِ أَجْمَعِينَ{119}
Sai wanda Ubangijinka Ya yi wa rahama, kuma dõmin wannan ne Ya halicce su. Kuma kalmar "Ubangijinka" Lalle ne zã Ni cika Jahannama da aljannu da mutãne gaba daya" ta cika.
A cikin shirin da ya gabata mun bayyana cewa: Allah babu wanda ya ke tilastawa yin imani sai dai ya bawa kowa hankali na gane gaskiya da karya da kuma ba shi zabi da yancin zabar abin da yaga ya dace da shi kuma abu ne da ke a fili kowane zabi yana da sakamako da ya yi daidai da shi da kuma ya sabawa waninsa.Wannan ayar tana cewa: wadanda suka riki hanayr kafirci da jayyaya daga cikin mutane da aljannu ko da kuwa a wannan duniya ba a haramta masu ni'imomi na zahiri su kwan da sanin za su gamu da fushi da azabar Allah a gobe kiya.Sai wanda yayi aikin da zai kai shi ga Rahama da shiriya daga Allah.Wannan ayar na nuni da lamari mai muhimmanci da cewa; halittarmu alama ce ta rahama da lutifin Allah kuma karkashinn wannan dalili ne ya yi mana wata rahamar ta shiryar da mu don haka mu yi aikin da zai sa mu yi dace da rahama da kuma lutifin Allah a ranar kiyama.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu
Na farko:rahama da fushin Allah sun danganta da zabi da ayyukan da muka aikata ne ma'ana sakamokon aikin alheri alheri kamar yadad sakamakon mummunan aiki mummuna.
Na biyu:Allah ta hanyar bamu hankali da aiko da manzonni da littafi ya karre kafawa mutum hujja kuma yanada hujjar azabtar da kafirai bayan wadannan dalilai.
Yanzu kuma za mu saurari aya ta 120 a cikin wannan sura ta Hud kamar haka
وَكُـلاًّ نَّقُصُّ عَلَيْكَ مِنْ أَنبَاء الرُّسُلِ مَا نُثَبِّتُ بِهِ فُؤَادَكَ وَجَاءكَ فِي هَـذِهِ الْحَقُّ وَمَوْعِظَةٌ وَذِكْرَى لِلْمُؤْمِنِينَ{120}
Kuma dũbi dai Munã bã da lãbãri a gare ka daga lãbarun Manzanni, abin da Muke tabbatar da zuciyarka da shi. Kuma gaskiya ta zo maka a cikin wannan da wa'azi da tunãtarwã ga mãsu ĩmãni.
A cikin wannan sura ta Hud an kawo labarin annabawa da manzonni da yadda karshen wadanda suka kafirce daga cikin al'ummominsu don haka a karshen wannan sura Allah ya ke cewa: mun kawo labaransu ne domin ka samu nucuwar zucci su ma mumunai su samu nucuwar zuccin da zama darasi ga kowa kuma ku ci gaba da yin riko da tafraki na gaskiya da kuke a kai har ila yau kawo labarai matsalolin wadanda suka gabata domin zama darasi ga na gaba kuma su sani idan sun juya wa tafarkin gaskiya baya da karyatawa makomarsu za ta zama daya da ta wadanda suka gabace su ma'ana azabar Allah za ta sabka kansu.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu
Na farko: Kissoshin kur'ani kissoshi ne na gaskiya da suke tattare da hadafi sabanin sauran tatsinniyoyi da almara don kawai nashadantarwa .
Na biyu: karance-karance da nazarin tarihi yana taimakawa wajan fahimtar gaskiya da kwantar da zucciya ko akasin haka.
Yanzu kuma za mu saurari aya ta 121 da 122 a cikin wannan sura ta Hud kamar haka:
وَقُل لِّلَّذِينَ لاَ يُؤْمِنُونَ اعْمَلُواْ عَلَى مَكَانَتِكُمْ إِنَّا عَامِلُونَ{121} وَانتَظِرُوا إِنَّا مُنتَظِرُونَ{122}
Kuma kace wa wadanda bã su yin ĩmãni, "Ku yi aiki a kan hãlinku, lalle mũ mãsu aiki ne.
"Kuma ku yi Jiran dãko, lalle mu mãsu Jiran dãko ne."
Ayar da ta gabata tana magana ne kan yadda mumunai ke daukan darasi a cikin tarihin al'ummomin da suka gabata amma ita wannan ayar tana cewa; amma ma'aiki ka gayawa wadanda ba su yi imani ba ,su aikata duk abin da suka ga dama sai kuma su shiryawa sakamakon abin da suka aikata.Muna za mu aikata abin da muke so muna jiran sakamakon aikin da muka aikata kamar ku.
A cikin wadannan ayoyi za mu iya daukan darasin abubuwa guda biyu kamar haka:
Na farko : ana bukatar yin kashedi da barazana ga wadanda ba su yi imani ba ko zai yi tasiri kuma ko ba komi an kafa masu hujja.
Na biyu:a tafarkin yada addini kowa ana yi masa bayani da magana ne gwalgwadon fahimta da aikinsa misali ga mutane masu jayayya da tsananin riko dole a yi amfani da kalmomi masu zafi da barazana.
Yanzu kuma za mu saurari aya ta 123 kuma aya ta karshe a cikin wannan sura ta Hud kamar haka:
وَلِلّهِ غَيْبُ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ وَإِلَيْهِ يُرْجَعُ الأَمْرُ كُلُّهُ فَاعْبُدْهُ وَتَوَكَّلْ عَلَيْهِ وَمَا رَبُّكَ بِغَافِلٍ عَمَّا تَعْمَلُونَ{123}
Kuma Allah ne masanin abubuwan boye a cikin sammai da kassai kuma a gare shi makomar komi sai ku bauta masa da yin tawakkali da shi kuma Ubangijinka ba marabkani ba kan abubuwan da kuke aikatawa ba.
Aya ta karshe a wannan sura ta Hud tana magana ne ga ma'aikin Allah da sahabbansa da cewa: dukan lamura suna hannun Allah ne kuma bawai kawai yanada masaniya kan aikin da kowa yake aikatawa ba hatta sirri abubuwan da muka boye a zucci da tunani yanada masaniya kansu.Saboda haka babu wata hanay sai hanayr tafarkinsa da bauta masa da yin dogaro da shi idan muna cikin tsanani da kuma ta haka ne za kasance daga cikin masu gaskiya.Wani abin lura a dabi'ance kasance bawon Allah da kuma mai dogaro da shi ba su yi sabani ba da kokari da himmar mutum kawai wani abu ne da ke karfafawa dayan karfi ma'ana tawakkali ta hanyar kokari ba tawakkali ba ba kokari da ke a matsayin rashin tawakkali na hakika.
A cikin wannan ayar za mu iya ilmantuwa da fahimtar abubuwa guda biyu kamar haka:
Na farko: Mutum yanada matsayi da fuska biyu bayan wannan matsayi da fuska tasa ta zahiri yanada matsayi da daraja ta boye da kuma wannan bangare ne mumunai suka fi bawa muhimmanci.
Na biyu : Imani da gaibi yana shinfida hanyar bautawa Allah da kuma ke kubutar da mutum daga bautawa waninsa.
Da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shirin na yau sai kuma shiri na gaba da yardar Allah kafin lokacin Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram na na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalamu alaikum warahmatullahi wa barkatuhu.