Toggle menu
24K
663
183
158.1K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

UMD NFLC Hausa Lessons/112 Law and Order

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Revision as of 13:28, 4 November 2017 by Admin (talk | contribs) (Glossary)
(diff) ← Older revision | Latest revision (diff) | Newer revision → (diff)

Overview

  1. Lesson Title: Law and Order
  2. This interview gives a perspective on the fundamental laws in Nigeria, and the distortion they are subject to from a constitutional law expert's point of view.
  3. Language: Hausa
  4. Topic: Economics/Politics
  5. ILR Level: 2+/3
  6. ACTFL Proficiency: Superior, Advanced-High
  7. This ACTFL rating is an approximation based on the ILR level
  8. Modality: Listening
  9. Learning Objective: Maintenance & Improvement
  10. Subject Area: Language
  11. Material Type: LO
  12. Publication Year: 2007
  13. ObjectID: HAUS_11721

Transcript


Original Translation

Law and Order

A: Mene ne ra’ayinka dangane da irin wanɗannan abubuwan da suke faruwa a Nijeriya idan ake yi la’akari da … bin doka da oda, wanda shi ne kamar … ginshiƙin ɗorewa dimukuraɗiyya?

B: To, ai … Malam Umaru, ka gama magana da kake cewa … bin doka da oda, shi ginshiƙin … dimukuraɗiyya. Kai ba ma dimukuradiyyar ba, duk wani tsari na mallakar mutane …

A: Mmm …

B: Idan ba doka, ba oda, babu yadda za a yi ta bi daidai, domin kuwa, idan ba doka, ba oda, to fa kowa zai iya tashi ya nuƙushe wanda ya ga dama, ya yi abin da ya gaddama.

A: Mmm …

B: Kuma, randa aka ce gwamnati, wadda ita ce take a hakku, wajen tabbatar da doka da oda ta shiga tana aiki na ta’adanci, tana kama ƙarya. To, babu yadda za a yi, mutane tsakanin su da su, su zauna lafiya, ba su yi kama ƙarya ba. Ah … abu… mutane da yawa wataƙila za su san cewa akwai hadisi na manzo Allah {salalahu alaihu wassalam [Arabic]} yake cewa: akwai wata zuciya a cikin jiki wadda idan ta yi lafiya, duk jiki ya yi lafiya, idan kuma ta lalace, to babu abin da zai yi lafiya a cikin jiki.

A: Mmm ...

B: To, wannan … ah … jijiya, ita ce zuciya.

A: Mmm …

B: Sai kamanta ita wannan … ah … jijiya --

A: Mmm …

B: --da shari’a, yake cewa duk abin da ake ci a kasa , idan shari’a ba ta gyaru ba, babu abin da zai gyaru. To babu yanda za a yi shari’a ta gyaru, idan wanda aka ba su haƙin tafiyadda shari’an, su kama su yi ƙunci bisa kan abin da shari’a ta ce, laifin da yake akwai shi ba wai ... aka ƙirƙiroshi ba. Abin da yake kuma, wanda yake … ga yadda za a yi tuhuma, ga yadda za a kai mutum gaban shari’a, ga yadda za a yi mishi shari’a, ga laifin da zai yi ga kuma abin laifin zai ja masa. Idan ba wannan, babu yadda za a zauna a ƙasa lafiya. Kuma ni ba na mamaki in ana yin wannan domin lokacin da aka shigo waɗannan kama ƙarya ake yi mutane sun maida abun, abun wasa ne.

A: Mmm …

B: Ita kuma, dimukuraɗiyya da shari’a ba … ba abun wasa ba ne. Ana ɗauka waɗansu a kama a ƙarye a yi abun da aka ga dama. A zo yin zaɓe, wanda bai ci ba a ce, a ce ya ci wanda ya yi ci, a ce bai ci ba. A zo, a ce kuma, za a zauna a yi dimukuraɗiyya, na san ƙariya ne, saboda haka ba na mamaki. Amma duk da ba na mamakin abin da ke faruwa, ina ɓa- ... matuƙar ɓacin rai abin da ke faruwa, domin kuwa mutanen Nijeriya da suke ruɗin dimokuraɗiyya, ba su ɗauka cewar dimukuraɗiyya, za ta zo ta zama kama ƙarya, da yin abun da aka ga dama ba.

Ka yi maganar gwamnan Plateau, da gwamnan Ekiti. A bisa shari’a ta bature da kuma tamu, shari'a ta musulumci, duk mutumin da ba a kama shi, aka kai shi gaban shari’a, mai shari’a ya ce ya yi laifi ba. Kuma aka ba shi dama ya kare kansa aka tabbata da cewa ya yi wannan laifi, idan an masa hukunci ba a yi mashi adalci ba.

Ni a fahimtata, idan mutum yana a gaban shari'a, ko da an yanke masa hukunci, idan ya ɗaukaka kara … ko mutuntashi ba ta ƙare ba. Sai an gama duk dama da shari’a ta ba shi ya ɗauka kara, har zuwa ƙarshen kotun ƙasa na ƙoli ga baki ɗaya a Nijeriya. Daga nan ne, idan an ƙare shi za a ce shi ke nan, an gama da shi … a yi masa kwance wadda … ah … shari’a ta a yarda masa.

A: Mmm …

B: Amma, waɗannan mutane: wasunsu suna gaban ko kotutuka ma a tsige su. Wasu kuma, an tsige su ko kuwa za a ce ba bisa gaskiya aka tsige su ba. Amma an zo, an ci gaba, kuma ana ma abin nan kamar ƙasar mahaukata, wanda ba su san abun da suke ba. Ni ina jin tsoron wannan abu zai jawo: rushewar dimukuraɗiyya, ko kuma rushewar Nijeriya ga baki ɗaya.

A: To, me ka- … ina mafita?

B: Wannan mafita! Ni abin da na fahimta shi ne: duk lokacin da aka soma gini da … bulo na toka --

A: Mmm …

B: -- to, babu yadda za a yi wannan gini ya zauna! Kuma ya yi inganci. Mafitar ta farko shi ne a sami gwamnati wadda jama’a ce suka zaɓe ta. Duk mutumin da yake Nijeriya kuma, kai malam Umaru na san kana Nijeriya lokacin da aka yi zaɓe … na dubu biyu da uku.

A: Mmm …

B: An san mutumin nan da yake ƙare shi ne ke shugaban Nijeriya, ba zaɓe ya ci ba. Haɗawa aka yi da soja da ƴan sanda, aka yi kama ƙarya. Wanda ya ci bai ci ba, wanda … ya … ya … bai ci ba aka ce ya ci. Saboda haka, duk gwamnatin da ta samo da wannan mummunan … ah … ɗalibi, wanda ba zaɓe ta ci ba, watau a turanci, ba su da {mandate [English]}, kuma ba su da {legitimacy [English]}. Ba gwamnati ba ce ga baki ɗaya, to duk abin da ta yi, na sharri, da kama ƙarya ba mamaki.

To, abun da za a yi na farko ni a wajena shi ne, a koma inda aka somo aka yi ba daidai ba. A haƙe wannan bulo na toka, a sa bulo na gaskiya. A zo a yi zaɓe na gaskiya ... wanda yake a ba shi ya ci, sannan a ba shi dama ya je ya tsaya, ya zama shi ne shugaban ƙasa. Ya naɗa mutanensa, su kuwa ƴan minista su zo, su yi aikinsu na kula da shi wannan shugaban ƙasa domin kuwa an ba shi {power [English]}, ko kuwa … ta yin abubuwa da dama, amma kuma aka ce … su ne za su ja ja masa linzami, to su masu linzamin su kansu …

A: Mmm ...

B: … iskance suke yi, kurum kuɗin su suke karɓa.

A: To, idan ma ka juya ta fuskar kuma … zaɓe, hukuma zaɓe, hukumar zaɓe ta ba da sanarwa cewar … ta jawo ranar zaɓan ƙananan hukumomi baya daga watan Afrilu, ta dawo da shi watan Fabrairu; waɗansu kuma --

B: Mmm …

A: -- suna ganin cewar hukuma zaɓe ba ta da wannan dama saboda harka zaɓen. Ƙananan hukumomi harka ce ta jihohi …

B: To … bari …

A: Me- … me- … mene ne kake ganin … ah … ra’ayinka akan wannan?

B: Yau, ai ba magana ra’ayi abin da za a tambaya shi ne, malam Umaru --

A: Ai …

B: -- me doka ta sa hana, me doka ta ce?

A: To …

B: Doka yadda na sani --

A: Ai …

B: -- bisa ga ɗauka zaɓe yanzu … ina da … ina da … ina da {copy [English]} gaba ɗaya nan … na za ... na zaɓe na bana --

A: Ai …

B: -- k- {electoral [English]} na {two-thousand-and-six [English]}, yana gaba na.

A: To

B: Da kuma kotocin Nijeriya bai ba ai ita ainihin dama ta yi wannan ba. Saboda haka idan an yi, shi ma naushin mai zama kama ƙarya, na ayi abin da aka ga dama. Kuma tun da har su sun soma shiga abin da ai ba horaminsu ba, --

A: Mmm …

B: -- to akwai wani tsari a baya. Mutumin nan ba ya da niyya tafiya, yana son ya dagula al'amarin nan, ya zo ya halaka ƙasar ga baki ɗaya. Idan {Nigerians [English]} sun damu su tashi su yanke ma kansu ƙunci. Idan ba su yi ba duk abin da na faɗa na ce mutumin nan zai yi shi zai yi, kuma idan ba a yi hankali ba abun da ma ban faɗa ba sai ya zo ya yi. Kuma sai kowa ya zo yana wayo, Allah.

Amma maganar zaɓe na ... na ... na ... na jihohi, ba hurumin … ainun ba ne. Hurumin kowace jiha ne … da kuma ainihin … kwamishin da ta zaɓa ko kuma … {National [English]} da ake kiran ƴan wadda ake sa ta yi wannan aiki. Saboda haka ba su da dama su yi wannan.

To, amma kuma, abin da nake ji shi ne idan an kai abun … gaban kotu.

A: Mmm ...

B: Kotun su kansu alƙalan kuɗi suke karɓa, su yi abun da suka ga dama. Kuma sun zama ƴan bara na gwamnati. Daga sama har ƙasa, duk ƙarya suke yi. To, ka … duk abin da ake yi yanzu, za a zo a yi ta jan magana ne har lokacin ya zo ya ƙure mu shiga ruɗani, kuma a sa na yadda … wa … a sa yadda, a rasa yadda za a yi.

Kuma ni, na yi imani ma tukuna, ba a da niyya a yi zaɓen. Tun da ya so ya … yi ta zarce abun ya gagara, an yi masa can aka, ƴan majalisa su ga halaka, ana binsu ana so a kashesu kamar … kamar … kamar karnuka. Sun zo sun ce ba su yarda ba. To, yanzu-yanzu ya zai yi ta zarce ɗin … ba tare da sa hannu ƴan majalisa ba, kuma ba tare da sa hannu masu shari’a ba. Dama masu shari’a kuwa banzaye ne.

Law and Order

A: What is your opinion regarding things that are happening in Nigeria where there is carelessness in … following law and order, which are … the foundations of a lasting democracy?

B: Well … Malam Umaru, you said it all, that … following law and order is the foundation of … democracy. In fact, not just democracy but all aspects of administration …

A: Mmm …

B: When there’s no law and no order, nothing will work, because when there’s no law and no order, everyone can rise up, ripe with a sense of opportunity, and do whatever he sees the chance to do.

A: Mmm …

B: And when the government, which says it has the right to enforce law and order, starts to engage itself in what seems like terrorism and dictatorship: There’s nothing that can be done, people between themselves, living peacefully, not acting oppressive. Ah … the thing … perhaps many people will know that there is a hadith from God’s Messenger, {salalahu alaihu wassalam [Arabic]}, which says: There is a heart inside the body, which if it is healthy, the whole body is healthy; but if it has deteriorated, then nothing will be healthy in the body.

A: Mmm ...

B: So, this … ah … muscle is the heart.

A: Mmm …

B: So, this … ah … muscle corresponds --

A: Mmm …

B: -- to the law, such that anything that one eats in the country, if the law is not working properly, nothing will work properly. Nothing will restore the law, if the custodians of the law disregard what the law says, one will be falsely accused. This would be, the one who ... look at how there would be suspicion, look at how someone would be brought before the law, look at how he would be sentenced, look at his crime and what it would bring him. If not for this, we wouldn’t be able to live peacefully in this country. And I’m not surprised that it is like this because of the times we’ve entered, with these oppressive activities that people have done, it’s like a game.

A: Mmm …

B: But democracy and law are not … are not games. They’re taking things up and lying about it, to do whatever they see an opportunity for. We had an election, and whoever lost was said to have won, and whoever won was said to have lost. We came and said, let’s live in a democracy, but I know it’s a lie, and therefore I’m not surprised. But even though I’m not surprised by what is happening, it saddens … it deeply saddens me, what’s happening, because when the Nigerian people are manipulating democracy, they don’t realize that democracy will turn into dictatorship, for doing whatever one sees an opportunity to do.

You talked about the governor of Plateau and the governor of Ekiti. According to European law as well as our own Islamic law, anyone who is not caught and brought before the law, the judge will pronounce his crime. We give him the opportunity to acquit himself so we are certain that he committed this crime, but when we reach a verdict in his case, we don’t give him justice.

In my understanding, when someone is before the law, even if his sentence has been given, if he appeals ... then this case is not over. Until one has finished every opportunity that the law gives for him to appeal, all the way to the last court in the country, the highest in the whole of Nigeria. From here, if he is acquitted, they tell him that’s it, they’re finished with him ... and he is given whatever settlement that ... ah ... the law allows him.

A: Mmm …

B: But other people: when they go before the courts and they are impeached. Others, they are impeached in contravention of the law. But we come and then press forward, and we have this thing that’s like a country of crazy people. I’m fearful as to what this will bring about: the collapse of democracy, or even the collapse of Nigeria in its entirety.

A: So, what would you-- … what’s the solution?

B: The solution! What I understand is this: every time we start to build with … cement blocks made from ashes --

A: Mmm …

B: -- there’s nothing we can do to make this building stand properly! And it’s durable. The first solution is to have a government that the people have chosen. Every person in Nigeria ... you, Malam Umaru, I know that you were in Nigeria when we had the election in 2003.

A: Mmm …

B: We know a person here who helped the president of Nigeria; he didn’t win the election. They conspired with the soldiers and police to crack down. The one who won, didn’t win, and the one who ... who ... didn’t win, they said he won. Because of this, every government that supplied that evil ... ah ... student, that didn’t win the election: as you would say in English, they had no mandate, they had no legitimacy. No government among them all, and everything that they did was evil, and their dictatorship is no surprise.

So, the thing that I think should be done first is this: return to where we started to go wrong. Dig up that cement block made of ashes, and use real cement blocks. Come and have a real election … one that is given to the mandate, then give him a chance to go and stand, and become the country’s leader. Let him appoint his people, and let the ministers come and do their work, and see to it that this president is given power, and give things a chance, but also … if they pull on his bit, then they should do likewise to themselves …

A: Mmm ...

B: … it’s immoral what they’re doing, they’re always receiving money.

A: Alright, if you turn to consider … the election, the Electoral Commission, the Electoral Commission, which made the announcement that … it had changed the date of the local authority elections from April to February; and some --

B: Mmm …

A: -- are saying that the Electoral Commission didn’t have an opportunity because of election matters. Local authority matters in the states …

B: OK … let …

A: What … what … what do you think … ah … your opinion on this?

B: Today, well, no opinion, but what I, we should ask Malam Umaru ...

A: OK …

B: -- what does the law prevent, what does the law say?

A: Alright …

B: The law that I know --

A: Yes …

B: -- on holding the election now … I have … I have … I have a copy of it right here … the elect-- ... the election from last year --

A: Yes …

B: -- k- electoral of two-thousand-and-six, it’s here in front of me.

A: Alright.

B: The Nigerian courts do not give it any opportunity to do that. Therefore, if it was done, that’s a measure that verges on legality, which is what we saw before. And since they started going into this, well, it’s not in their power --

A: Mmm …

B: -- and there was an arrangement behind it. This person had no intention of leaving office; he wanted to spoil this matter, so he came and destroyed the whole country. If Nigerians had a chance, they’d rise up and slap him themselves. If they don’t do it, everything that I’ve said that this person would do, he would do, and if we’re not careful, he might even come and do the things that I didn’t mention. So everyone will suffer the consequences, crying to God.

But speaking of the election in … in … in the states, there’s no real … opportunities. The only chances in each state are … and the real … commission that it elected, or … “National,” as they call those who are appointed to do this work. Because of this, there were many of them doing this.

But then, I heard that when they brought it … before the court.

A: Mmm ...

B: The court itself, the judges, take money, to do as they saw fit. They became the government’s little servants. From top to bottom, they are all lying. So, you see … everything that’s going on now, they’ll come and keep this up until there is little time left for us to avoid confusion, and we let it happen … and … let it happen, and fail to do anything about it.

As for me, I’ve always had strong faith, but I have no intention of voting. Ever since he attempted a second term and it failed, they ignored him, with legislators who saw destruction, and they followed them and wanted to kill them like … like … like dogs. They came and said, we don’t agree with this. Well, soon he’ll be pulling ahead … without agreement from the legislators, and without agreement from the judiciary. Those judiciary members are just as bad.

Glossary

Hausa Hausa Meaning English Meaning
Gini da bulo toka. Salon magana cikin hasa ne; ana nufin takarar yin wani abin da ba za ya ƙarko ba. This is a saying in Hausa, meaning to start something that will not last or something that will fail for sure (literarily means building with blocks/bricks made of mud)
Ja lizame. A ja gora. A nan ana nufin a sa bisa hanya mai kyau kuma tsauta lokacin da an kauce daga hanyar mai kyau. This is an expression that means to guide or advice.
Kowa ya zo yana wayyo Allah. Kowa ya zo yana kukan matsala ɗaya. A nan shi mai magana ya jawo hankalin mutane ga su ɗauki mataki kafin a yi ɓana wadda za ta sa su ce inda mun sani. This is a Hausa saying which means everybody would be complaining.
Kowa zai iya tashi ya nuƙushe wanda ya ga dama. Kowa zai iya yin abin da yake so bisa sauran mutane. Manufar wannan cikin hirar ita ce: a shiga cikin wani hali na mulkin ruɗu. People would do whatever they want. The meaning of the sentence in this context is: without law and order, there will be anarchy.
Su yi abin da sun ga dama. Su yi yadda suke so. They do as they wish. People do what they want to do regardless of how others think or feel.

Notes

An yi mulkin soja da dama a Nijeriya bayan da ƙasar ta sami yancin kanta cikin shekara ta 1960.

Zaɓen watan Afrilu ya zama na farko inda aka juya mulkin ta hanya jefa ƙuri'a tun wannan lokacin samun yancin.

Shugaban ƙasar yo so ya sake tsarin mulkin ƙasar domin ya samu tsayawa ga mulkin ƙarin wasu shekaru huɗu.

Wannan niyya tashi ta samu rashin goyo bayan jama'a da kuma majalisar dattijai wadda ba ta goyin bayan shirin dokar gyaran ba a shekara ta 2006.

Nigeria has seen a succession of military regimes for decades after independence in 1960.

April's polls would be the first transfer of power from an elected leader to another since then.

The outgoing President faced resistance to his attempt to make changes to the constitution in order to get to stay in office for a third term.

The amendment bill was rejected by the Senate in 2006.

XML



<activity>
   <instr type="eng">INSTRUCTIONS:
Choose the best summary.</instr>
   <instr type="target">Umurni:Zaɓi taƙaitawa mafi dacewa.</instr>
   <problemset>
      <problem correctindex="2">
         <choices>
            <opt>
               <eng-response>This interview addresses an expert’s interpretation of law and order in relation to the Nigerian government’s attitude. Dr Janaidu agrees with the journalist that law and order are the foundation of democracy but he strongly criticises the government for disappointing the people it should be serving. A fair trial is not guaranteed by the court. Also, because the government came to power through rigged and fraudulent elections, there is no respect for the law, he explains. He recommends a return to the principles of law with a democratic  change of government in spite of the President's reluctance to organize elections. He compares the government to a brick made of ashes to imply its weakness. He says that there is a need for a change in order to avoid the worst.</eng-response>
               <response>Wannan tattaunawa na bada ra'ayin wani gwani na harakokin doka ta tsarin mulki a Nijeriya game da yadda gwamnati take aiki. Shi Dr Janaidu ya amince da maganar ɗan jaridar cewa da doka da oda suna tabbatar da tahiyar dimokuraɗiyya amma, ya soki gwanatin saboda rashin riƙa maganarsu ga jama'ar da ya kamata su yi wa aiki, domin ratsewa daga doka da oda cikin ayyukansu. Ya nuna cewa idan ba a iya shara'a ta hanyar da doka ta tsaida ba, kuma saboda gwamnatin ya zo ga iko ta hanya rikicin zaɓe, ba a iya cewa ana bin doka. Ya kawo shawarar a sake gwamnatin da ya kwattamtar da bulo toka don rashin amincinshi, domin a koma ga kiyyaye doka ko ma shugaban ƙasa bai sa niyya  ba  a kare ƙasar daga wasu abubuwa masu muni.</response>
               <eng-fdbk>Incorrect. Please listen again to the speaker when he speaks about the justice system. Does this choice capture his comments about the reality of the system?</eng-fdbk>
               <fdbk>Ba daidai ba. Ku ƙara sauraren mai magana, inda yake zancen shara'a da kotu. Ana samun bayyani bisa halin da ake ciki kuwa?</fdbk>
            </opt>
            <opt>
               <eng-response>An expert speaks out about the extortion of fundamental laws by Nigerian leadership in this interview. He says that law and order are pillars to a democratic or any governing system but, in this case, they are broken in many aspects by the same government that is supposed to guarantee their respect. Dr Junaidu proposes a change of leadership with an elected team of trustworthy President and ministers who will work in an honest way to restore law and order. With contemptuous remarks, he reiterates his opinion about the way the President is handling the preparations for future elections that will assure a transfer of power he is not yet ready to give up. People are disappointed by the leaders. They need a change with a true democracy.</eng-response>
               <response>Wani masani na doka ya fito a fili cikin wannan tattaunawa yana magana bisa yadda ikon Nijeriya yake yin sharri ga ƙa'ida. Ya ce doka da oda suna da mahimmanci cikin dukan tsarin mulki, amma a nan gwanatin da ya yakamata ta kiyyaye su, tana taka su. Dr Junaidu, yana kira da a sake shugannin kuma a naɗa wani shugaba na gari da mataimanka
da za su sa shi ga hanya ta kiyyaye doka da oda ba azzalumai ba. Bai ɓoye ƙyashinshi ba bisa ga yadda Shugaban ƙasa yana sanyi-sanyi da shirin zaɓen da za ya kawo canjin iko wanda baya so ya bari tukuna. Jama'a na buƙatar canji saboda shugabannin sun ɓata masu rai.</response>
               <eng-fdbk>Incorrect. Think about the speaker's interpretation of the fundamental law and how it is not considered in reality. What indicates the wrongdoing of the authorities?</eng-fdbk>
               <fdbk>Ba daidai da. Ku yi tunani bisa fasarar doka da mai magana ya bada kuma, yadda ake banzattar da ita cikin ayyukan yau da kullum. Minene ya ke bayyana saɓon shugabani?</fdbk>
            </opt>
            <opt>
               <eng-response>In this interview, Dr Junaidu, a constitutional law expert, denounces the alarming facts:  the repressive practices of Nigerian authorities, their unconstitutional aspects, and the risks they pose to the country’s stability and democracy. The judicial system fails to respect or follow Islamic or western legal procedure during judgements. Elections are rigged with the implication of the army and the police, bringing illegitimate leaders to power. Corruption is prevalent amongst ministers who are supposed to fight it, he cited. According to him, the alternative is to have democratic elections that will bring change with a new reliable leadership that will meet Nigerian people's expectations. It is necessary to return to the respect of law which is the key to stability. Junaidu draws attention on the President’s attempt to delay his departure from the office.</eng-response>
               <response>Cikin wannan tattaunawa, Dr Junaidu, wani gwani cikin harakokin doka, yana Allah waddai kan karhi da kama karya da ikon Nijeriya ke yi, da kuma rashin gaskiyar tabi'ar, da irin lahanin da yake iya kawowa ga zaman lafiya da dimukuraɗiyya. Ya ce fannin shara'a ba ta bin ƙa'idodin Musulumci, ko na bature; wurin zaɓe kuma ana sa zalumci tare da sa hannun 'yan sanda da soja. Haka kuma ana sa mutanen da ba lallai jama'a ta zaɓe su ba bisa mulki . Ya bayyana harakar kuɗi ta ministoci, da alƙalan da su ya kamata su hukumci rashawa. Ya ce kuma wajibi ne a yi zaɓe, inda za a kawo canjin da shugabannan da za su gyara wa jam'a da rai, kuma a yi tattalin doka da kwanciyar hankali. Junaidu na jan hankali ga niyar shugaba ta ƙara lokaci bisa mulki.</response>
               <eng-fdbk>Correct. You understand the expert's description of the law and the practice that breaks it in the Nigerian judicial system. This choice also reflects the angry tone of the interview. It uses strong words that imply extortion.</eng-fdbk>
               <fdbk>Daidai ne. Kun gane da yadda mai magana ya bayyana abin da doka ta ƙumsa, da yadda ake taka
ta a cikin fannin aikin shara'a Nijeriya. Wannan zaɓen kuma na nuna karin sautin tattaunawar yadda yake nuna rashin jin daɗi cikin anfani da kalmomi masu ƙarfi wajen yin sharhi.</fdbk>
            </opt>
         </choices>
      </problem>
   </problemset>
   <finishtl>Yaya kuke ganin mutanen Nijeriya za su duba shugabannin da za su zaɓa ganin yadda mai magana yake bayyani bisa tafiyar da doka da oda a ƙasar, kuma da zaɓen da za a yi a gaba?</finishtl>
   <finish>How do you think Nigerians would feel about their next leaders considering how the speaker describes the legal situation in the country and the upcoming elections?</finish>
   <finishtl>Wace hanya ake iya bi domin a tabbatar da kiyyaye doka bayan an yi zaɓe a Nijeriya domin a yi maganin matsalolin da mai maganar ya faɗa?</finishtl>
   <finish>How can law and order be restored and respected after the elections in Nigeria, in order to solve the problems cited by the speaker?</finish>
   <finishtl>A ganinku yaya ra'ayoyin mai bada amsoshin tambayoyin tattaunawa za su iya kawo gyara ga halin da ake tafiyar da doka da oda cikin Nijeriya a hali da yake maganar?</finishtl>
   <finish>The interviewee seems to speaks freely and with confidence. How would his comments help to restore law and order in the present situation of Nigeria?</finish>
</activity>