Toggle menu
24K
663
183
158.1K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

UMD NFLC Hausa Lessons/36 2006: The Unresolved Issues

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Revision as of 20:07, 6 December 2017 by Admin (talk | contribs) (Created page with "==Overview== # Lesson Title: 2006: The Unresolved Issues - This report gives a retrospective of the important events of the year 2006 in the socioeconomic and political life o...")
(diff) ← Older revision | Latest revision (diff) | Newer revision → (diff)

Overview

  1. Lesson Title: 2006: The Unresolved Issues - This report gives a retrospective of the important events of the year 2006 in the socioeconomic and political life of Nigeria, and in Obasanjo's legacy.
  2. Language: Hausa
  3. Topic: Culture/Society
  4. ILR Level: 2+/3
  5. ACTFL Proficiency: Superior, Advanced-High; This ACTFL rating is an approximation based on the ILR level
  6. Modality: Reading
  7. Learning Objective: Maintenance & Improvement
  8. Subject Area: Language
  9. Material Type: LO
  10. Publication Year: 2007
  11. ObjectID: HAUS_12051

Transcript


Original Translation

2006 The Unresolved Issues:

2006 Ta Bar Baya Da Ƙura:

Duk da cewa an ji-jiki a bakiɗayan ƙasar ta fuskar tattalin arziki da siyasa, a ɗaya fuskar kuma an cimma abubuwan jin daɗi a shekarar da ta gabata.

Abin da za a fi tunawa da shi, shi ne samun sauyi a yanayin siyasar ƙasar. A shekarar ne dai INEC ta faɗaɗa fagen siyasa ta hanyar yiwa jam’iyyun siyasa masu tarin yawa rajista, wanda ya kawo yawunsu zuwa guda 50. Wannan wani abu ne da ya faɗaɗa ikon tsoma hannun kowa cikin harkokin siyasa.

An yi shirye-shiryen miƙa hannu ga sabuwar zaɓaɓɓiyar gwamnati. Idan har zaɓen 2007 ya yiwu, to za a ce an karya ƙwarin da ke hana miƙa mulki daga zaɓaɓɓiyar gwamnatin farar hula zuwa wata sabuwar zaɓaɓɓiyar gwamnatin farar hula a Najeriya,wanda hakan zai ƙarfafa ɗora Najeriya a tafarkin dimukraɗiyya mai ɗorewa.

Sannan a shekara mai ƙarewa ne, yunƙurin da fadar shugaban ƙasa ta yi na tsawaita wa’adin mulki ya sanya ’yan Najeriya yin magana da yawu ɗaya. ‘Yan Najeriya sun fito ƙwansu da ƙwarƙwata sun yaƙi shirin tsawaita wa’adin mulkin shugaba Olusegun Obasanjo. Fuskokin ’yan ƙasa a 2006 ya ba wa ’yan majalisar dokokin hujjar yin watsi da ƙudirin gyaran tsarin mulki na ƙasa,wanda ke ƙunshe da shaɗarar da ke neman ƙarin wa’adi karo na uku ga shugaban ƙasa.

Wani abin da a ka cimma kuma shi ne, janye shirin rajistar zaɓe ta hanyar amfani da inji mai wutar lantarki, wato ‘Electronic Voting System’(EVS), wanda hukumar zaɓe mai zaman kanta, INEC, ta shirya yi a manyan zaɓukan ƙasa na wannan shekara ta 2007.

Ta fuskar tattalin arziki kuwa, akwai faraga a ayyukan banki. Umarnin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayar na mallakar Naira biliyan 25 ga banki ko kuma a rufe shi, ya haifar da samun ƙarfafar bankuna, ababan dogaro ga masu ajiya da masu zuba kudi.

A shekara ta 2006 kuma an shaida yadda kamfanin ‘Transnational Corporation of Nigeria’ da a ka fi sani da TRANSCORP, ya rikiɗe daga sigal kasuwanci zuwa cikakken kamfanin gudanar da hada-hadar kasuwanci. A na kallon kamfanin a matsayin wata muhimmiyar masana’anta da za ta fitar da ƙasa kunya a harkokin otal-otal da karɓar baƙi a Najeriya. Kamfanin, wanda a ka yi wa hasashen samun Naira biliyan 6 cikin shekara guda, amma sai ya kai ga samun har Naira biliyan 19.

A shekarar da ta gabata ne, Najeriya da ƙungiyar Paris Kulob suka sanya hannu kan yarjejeniyar da ta yafewa ƙasar fiye da kashi 50 bisa ɗari na bashin da Paris ɗin ke bin ta. Ma’ana, ƙungiyar Paris Kulob ta tafewa Najeriya bashin dala biliyan 18 daga cikin dala biliyan 30 da ta ke bin ta a 2006. Haƙiƙa wannan abu ne mai bayar da ƙarfin gwiwa.

Idan aka taɓo ɗaya ɓangaren, sai a ce shekarar ta fara ne da alamu na abubuwan ƙi, inda tun da farkonta ’yan Najeriya su ka shiga halin ni-’yasu sakamakon faɗuwar jirgin Bellview a Lisa ta jihar Ogun,inda fasinjoji da ma’aikatan jirgin 169 su ka rasa rayukansu.

Abu kamar wasa, sai haɗurran jiragen saman suka ci gaba da afkuwa a gurare da daban-daban cikin faɗin ƙasar. Wannan ya haɗa da hatsarin jirgin soji na ‘Hercules’wanda ya faɗi a jahar Benue daya lashe rayukan manyan janar-janar ɗin soji. Ko a halin yaƙi ba’a taɓa samun lokacin da manyan jami’an soja suka rasu haka tashi ɗaya ba. Kafin a gama makokinsu kuma,sai jirgin kamfanin sufurin jirage sama na ADC ya sake faɗuwa a Abuja, wanda ya ɗauki ran sarkin musulmi na 19, Alhaji Muhammadu Macciɗɗo da sauran fasinjoji 95, ciki harda fitaccen Sanata nan ɗan kishin ƙasa, Sule Yari Ghandi.

A shekarar ne dai Najeriya ta tsinci kanta cikin badaƙalar siyasar tsawaita wa’adin mulkin Obasanjo.Kafin shigowar shekarar an yi ta jin jita-jitar shirin sama-sama, sai bayan da shekarar ta miƙa sai lamarin ya zafafa.

Wannan ya fito fili ne lokacin da taron ƙasa kan gyara tsarin muƙaman siyasa,wanda gwamnatin tarayya ta shirya, ba tare da izinin majalisar dokoki ba, inda taron ya sauya fuska zuwa faɗi-tashin neman tsawaita wa’adin mulki. A duk tsahon watannin da a ka kwashe a na yin taron babu wata muhimmiyar muhawara da ta mamaye shi tamkar batun tsawaita wa’adin mulki. Duk da cewa Obasanjo ya ƙi yarda da hannunsa cikin wannan ƙulle-ƙulle, amma lamarin ya ci gaba da raba kan wasu ’yan ƙasa, inda ya ƙara zafafa ta yadda hatta ƙasashen duniya sai da su ka yiwa Najeriya barazana, matuƙar Obasanjo ya zarce kan mulki har bayan 29 ga watan Mayun 2007.

Shekara ta 2006 ta fara, ta kuma ƙare cikin yawaitar kashe-kashen siyasa. A cikin fitattun da a ka yi imanin cewa an bayar da kwangilar kashe su ne, sun haɗa da ɗan takarar gwamnan jihar Lagos a ƙarƙashin tutar jam’iyyar PDP, Mista Funsho William. ‘Yan bindiga-daɗi waɗanda har yau ba a kama su ba ne su ka kashe shi a gidansa da ke birnin Ikko. Shi ma wani ɗan takarar gwamna a PDP da ke gaba-gaba, wato Dakta Ayo Daramola, wani mutum da a ke zargin ya na yiwa tsigaggen gwamna Ayo Fayose aiki ne ya yi masa kisan sunƙuru. Kafin kuma shekarar ta ƙare a ka sake kashe wani na hannun ɗan takarar gwamnan PDP ɗin a birnin Ikko.


Ita dai shekarar 2006 na cike da tsige-tsigen gwamnonin da a ke zargin fadar shugaban da ɗaukar nauyi; abin da bai yi wa gwamnoni da dama daɗi ba. Abin ya fara ne da Gwamna Rashidi Ladoja na jihar Oyo, wanda ’yan majalisa 18 daga cikin 32 su ka kawar a ranar 26 ga watan Janairu sai Gwamna Peter Obi na jihar Anambra da gwamna Joshua Dariye, waɗanda su ma a ka tsige su cikin yanayi mai cike da ruɗani. Daɗin daɗawa, bayan doguwar shari’a, Kotun ƙolin Najeriya ta mayar da Ladoja kan muƙaminsa a cikin watan Disamba. Sannan Babbar kotun jihar Anambra da ke zama a garin Akwa ta yanke hukuncin dawo da Gwamna Obi kan muƙaminsa a ƙarshen shekarar ta 20067, yayin da Gwamna Dariye ke cigaba da ƙalubalantar tsige shi da a ka yi a gaban kotu.

Doguwar jayayya dake tsakanin Obasanjo da Mataimakinsa Atiku Abubakar wani abu ne daya mamayi shekarar .Tun daga lokacin da Obasanjo ya fito bainar jama’a ya soki mataimakinsa da laifin rashin biyayya agare shi cikin watan Agusta, 2005, su ka farraƙa da juna. Al’amarin ya sake ɗaukar sabon salo yayinda fadar shugaban ƙasa ta ayyana sakar Atikun daga muƙaminsa, bayan da shi Atikun ya koma jam’iyyar AC a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa.

A 2006 ɗin ne dai aka samu alamomin dake nuni da cewa, an ƙulla hana yiwuwar hana babban zaɓen ƙasa da za’a yi cikin 2007; ma fi girma daga alamomin shine , sakalin tanadin da INEC ta yiwa zaɓen.Hukumar dai ta dage kan cewa sai ta aiwatar da tsarin rigistar zaɓe ta hanyar amfani da na’urar lantarki,inda a ƙarshe ƙasa da mutum miliyan 5 suka samu yin rigista a cikin fiye da miliyan 70 da ya kamata a yi wa.

Tsaron ƙasa ya shiga halin ha’ula’i shi ma, saboda ƙaruwar aikata munanan laifuka,musamman a yankin Niger-Delta. ‘Yan bindiga-daɗi sun sha cafke ’yan ƙasashen waje da ke aiki da kamfanonin mai a yankin, su na yin garkuwa da su, wanda hakan ya janyowa Najeriya ɓacin suna da ɗari-ɗari a ƙasashen duniya. Buƙatar masu garkuwar dai ita ce, a bar masu iko da yankin mai cancakat!

Korar ma'aikata, a matsayin wani sashe na shirin sauya akalar tattalin arziki da wannan gwamnatin tarayya ke yi, ya haifar da mummunan sakamako ga iyalai da dama a faɗin ƙasar nan cikin shekara ta 2006.

Su ma wasu mazauna babban birnin tarayya, Abuja shekarar ba zo musu da daɗi ba, a lokacin da hukumomin Abuja, suka farfaɗo da shirinsu na dawo da taswirar birnin ta asali, ta hanyar rushe dukkan gine-ginen da a ka yi ba bisa ƙa’ida ba. Tuni dai an yi waje da waɗanda a ka rushewa gidaje da shaguna zuwa wasu gurare da ke wajen birnin. Hana achaba da a ka yi a birnin, shi ma wani abu ne da ya jawo ɓaɓatu da kace-nace, wanda ke addabar masu zuwa aiki a birnin. A daidai ƙarshen shekarar kuma, doguyen layuka a gigajen man fetur ne su ka mamaye garin,wanda ya haifar da mushaƙƙa ga ma’aikata.

A cikin satin ƙarshe na shekarar kuma, ƙasar ta faɗa halin jimami da makokin mutuwar ɗaruruwan ’yan Najeriya da suka rasu a gobarar bututun man fetur da ta afku a Lagos; gobarar da a ke zargin jami’an tsaro da yi wa ɓarayin man nakiya, inda su ka tsere su ka bar shi ya na kwarara, har wuta ta tashi sakamakon talaucin da ake ganin ya sanya mutane dakawa man wawa a matsayin ganima.

Ɗaya da ɗaya dai, 2006 na daga cikin shekarun da Najeriya ta tsinci kanta a abubuwa masu tarin yawa. Ta sha ƙalubale da karsashi ta fuskar tattalin arziki, siyasa da hulɗa da jama’a. ‘Yan Najeriyar da suka yi sa’a su ka rayu har zuwa ƙarshen shekarar za su yi sambarka da su ka tsira,saidai kawai mu hangi abin da zai iya wakana a wannan sabuwar shekara ta 2007.

2006 The Unresolved Issues:


Although the entire country feels exhausted by the economy and politics, in another regard we have achieved certain things we can feel good about in the past year.


The most memorable is the political change that has taken place in the country.

It was a year in which INEC [Independent National Electoral Commission] widened the field of politics by registering a vast array of political parties, which now number up to 50. This is something that helped to increase the ability of all citizens to participate in political activities.

Plans were drawn up for a hand-over to a new, elected government. When the 2007 election takes place, it will be said that we have broken the curse that has been preventing a transfer of power from one elected civilian government to another elected civilian government in Nigeria, and this will securely put Nigeria on the path of lasting democracy.

Then, when the year was ending, the attempt that the office of the president made to prolong the administration’s tenure caused Nigerians to speak with one voice. Nigerians emerged from their shells, , and fought the plan to prolong the tenure of President Olusegun Obasanjo’s administration. The look on the faces of the mass of citizens in 2006 forced members of the national legislature to reject any changes to the country’s constitution that sought to prolong the president’s tenure to a 3rd term.

Another thing that was achieved was the withdrawal of a plan to use an electronic mechanism that is “Electronic Voting System” (EVS), which the independent electoral commission, INEC, had proposed for conducting the 2007 national elections. From an economic angle, there was apprehension as well as we also had an opportunity to reform the banking sector. The new regulation from the Central Bank of Nigeria (CBN) mandating that banks must have at least 25 billion naira to operate or they would be shut down strengthened the banking industry upon which both depositors and investors depend.

In 2006, we also witnessed how the “Transnational Company of Nigeria” – better known as TRANSCORP –transformed itself from a marketing agency to a full-fledged investment company for financial transactions. The firm is viewed as an important industry that could lift the country out of lackluster performance in the hotel and tourism fields. The company, which was expected to make just 6 billion Naira in one year, ended up making a whopping 19 billion Naira.

In the preceding year, Nigeria and the Paris Club signed an agreement that forgave the country more than 50 percent of the debt that it owed to the Paris Club. This means that the Paris Club forgave Nigeria 18 billion dollars out of 30 billion dollars in 2006. Undoubtedly, this was very encouraging.

If we look at other events, we would say that the year began on a bad note and a great deal of shock for Nigerians due to the tragic air crash of a Bellview flight at Lisa in Ogun State, in which 169 passengers and crew lost their lives.

It was the year in which Nigeria found itself immersed in the controversy surrounding the alleged attempt by the Obasanjo administration to extend its tenure in office. Before the beginning of the year, we kept hearing rumors of a high-level plan for a third term; then, after the year started, the matter heated up.

The issue became public during a national conference on restructuring government positions, which the federal government had arranged without permission from the national assembly. Suddenly, the conference switched gears and focused more on prolonging, the administration’s tenure. Throughout the many months of the conference, no other issue got more attention than the issue of prolonging the administration’s tenure. Although Obasanjo refused to admit he had a hand in these discussions, Nigerians continued to be divided on the matter, and the issue kept heating up to such a level that even the world community issued warnings to Nigeria, should Obasanjo stay in power beyond 29 May 2007.

As the year 2006 began, so it ended with an increase in political assassinations. One of the cases believed to have involved hired killers was the murder of the PDP governor candidate for Lagos State, Mr. Funsho William. Trigger-happy hoodlums who have yet to be caught killed Mr. William at his house in Lagos. So it was with another leading PDP candidate for governor, Doctor Ayo Daramola: someone who was accused of working for the ousted governor Ayo Fayose allegedly murdered him. . Before the year ended, someone killed a close associate of the Lagos PDP candidate for governor in Lagos.

The year 2006 was full of governors who were impeached, allegedly with the full backing and possible involvement of the presidency, something that the other, remaining governors were not at all happy about. It started with Governor Rashidi Ladoja of Oyo State, whom 18 out of 32 legislators removed on 26 January, then Governor Peter Obi of Anambra State and Governor Joshua Dariye, who were both ousted under chaotic circumstances. But after long legal maneuverings, the High Court of Nigeria restored Ladoja to his position in December. Then the Supreme Court of Anambra State at Akwa ordered the restoration of Governor Obi to his position at the end of 2006, while Governor Dariye continued to challenge his own impeachment before the court.

The long-running dispute between Obasanjo and his vice-president Atiku Abubakar was another major controversy that dominated discourse during the year. Ever since Obasanjo publicly accused his vice president of disloyalty to him in August 2005, they became estranged from each other. The matter took on a new, uglier turn when the presidency chose to force president out of his office, after which Atiku decamped to the AC [Action Congress] party as its presidential candidate.

It was in 2006 that certain emerging signals suggesting a conspiracy to stop the general national elections planned for 2007 from happening. The most serious indication was the flawed preparations that the INEC was making for the election. The Commission took a firm stand in saying that it would go ahead with organizing the election electronically, while in the end fewer than five million people had been registered out of the more than 70 million who were eligible.

The country’s security also suffered due to an increase in the incidence of serious crimes, especially in the Niger-Delta area. Gun-toting gangs kidnapped foreigners working for oil companies in the area and took them hostage, which brought Nigeria a bad name and reluctance by the world community to do business with the country. The hostage-takers’ motive was to gain more freedom for their region.

Firing workers from their jobs was part of a plan by the federal government to shift control of the economy, and it only produced hardships for many families throughout this country in 2006.

And for those who resided in the federal capital city of Abuja, the year was not particularly pleasant, when the Abuja authorities revived their plan to restore the original layout of the city by demolishing all illegally-constructed buildings. Houses and kiosks had earlier been demolished, and their owners relocated to various places outside the city. The prohibition of scooter-taxis was also something that caused an uproar and heated arguments, and brought suffering to commuters. And at the very end of the year, long lines at petrol stations congested the city, which produced anger and frustration from workers.

During the last week of the year, the country fell into a state of shock and mourning over the deaths of hundreds of Nigerians who perished in the blaze of an oil pipeline in Lagos; a blaze that was blamed on security officials, who created an explosive situation for the petrol thieves, when the officials allowed the oil to flow, until fire broke out; a result of the poverty that is thought to motivate people to tap this fool’s oil for loot.

Based on the events that took place in it, 2006 is among those years in which Nigeria has found itself immersed in too many controversial situations. It has seen great challenges to its economy, politics and public affairs. Nigerians who have been lucky enough to live to the end of the year will give thanks that they survived. Now we only have to worry about what awaits us in this new year of 2007.

Glossary

Hausa Hausa Meaning English Meaning
An ji-jiki a bakiɗayan... Wannan yana nuna a faƙaice, ƙasar ta ga lokutta na wuya ko ɓacin rai. This implies that, in general, the country has gone through hard times
INEC Wannan suna ne na da ake kiran hukumar zaɓe mai zaman kanta, a Nijeriya. Independent National Electoral Commission
Yin magana da yawu ɗaya. Nuna haɗin kai game da magana bisa wani hali ko kuma a taru a tsayayya ga abokin gaba. This expression means speaking with one voice, or stand in unity against an adversary
Ababan dogaro. Wannan yana nufin akwai abubuwa waɗɗanda mutane basu iya wani aiki in ba da su ba. This means things that people depend on
Ya ci gaba da raba kan wasu ƴan ƙasa. Wannan magana tana nufin al'amarin ya kawo hargitsi tsakanin mutane yayinda sun kasa haɗa kai bisa halin. The people could not agree on one point; the situation brings about dissension amongst people
Ƴan bindiga-daɗi. Mutane da suke aiki da bindiga kamar da wani abin wasa su kashe mutane. The expression is used for people who take pleasure in shooting; it can mean gangs or guerrillas in this context
Kisan sunƙuru A sa wani ko kuma wasu mara imani su kashe mutane, kamar a yi sari ka noƙe. A murder that looks like a guerrilla carried it out
Daɗin daɗawa. Ƙari bisa ga abin da an sani. A cikin wannan labarin ana nufin ƙarin laifi ga wanin abin da mutane suna kuka da shi tun farko. This expression means to add something to an existing situation; it means to make things worse in this context
Hana achaɓa... Hana yin jigila ta babur don kasuwanci kamar taksi. This means making it illegal or forbidding the use of motorcycles as taxis, as they are used for that purpose
Ɓaɓatu da kace-nace. A nan ana nufin mutane suna gunaguni da nuna rashin amincewa da jin daɗin hana achaba. To manifest unhappiness, to dispute; in the context of the text, forbidding motorcycle taxi business caused a tumult from unhappy riders and customers
Dogayen layuka a gigajen man fetur. Ana cikin wannan labarin ana nufin dogayen layuka a gidajen man fetur wanda shike nufin jeri masu tsawo na motoci a gidajen mai. The term means long lines or queues of vehicles at gas stations
Ni- 'yansu. Wannan magana ce da ake faɗa lokacin da wani abu ya faru wanda ba mai kyau ba, ko kuma in akwai matsala This is an expression used when something sad happens suddenly, or in the presence of a problem

CONTENT SOURCE: Newspaper Commentary (2007 January 18). 2006 The Unresolved Issues:. N/A: Leadership Newspapers Group Limited.

Objective: Demonstrate your core comprehension.

Content description: This report gives a retrospective of the important events of the year 2006 in the socioeconomic and political life of Nigeria, and in Obasanjo’s legacy.

XML



<activity>
   <problemset>
      <problem correctindex="1">
         <choices>
            <opt>
               <eng-response>Happy and unfortunate events happened in the course of the year 2006, as this report shows in the struggles, the achievements, and the hopes of Nigerians for the best of the country. Democracy has progressed, people are more and more involved in politics and decision making on matters that determine the future of the country, like blocking the President from manipulating his way to another term, the efforts of the INEC to give an opportunity to a greater number of candidates and paving the way to elections. In the economic sector, corporate businesses and banks are booming, even debt relief is obtained. Tragedies have struck the country, adding to the number of deaths from unrest and crime. Oil, the national wealth, is also a problem with supply shortages locally, and insecurities surrounding it. Small business owners and workers are also dissatisfied and pessimistic.</eng-response>
               <response>Al'amura na alheri da kuma maras alheri sun faru cikin shekarar 2006, kamar yadda wannan rahoton yake nunawa cikin kokowa, da abubuwan yabo, da kuma fatan alheri na ƴan Nijeriya. Dimukuraɗiyya ta ci gaba; mutane suna daɗa shiga cikin harakokin siyasa da shawarwari bisa muhimman harakokin ƙasa, kamar yadda sun tsaida shugaban ƙasar daga ƙoƙarin canji ga tsarin mulki domin ya tsawaita wa'adin mulkinshi, kuma da ƙoƙarin hukumar zabe na ba mutane da dama ƴancin takara da buɗe wa dimukuraɗiyya hanya. Bisa fanni tattalin arziki, mayyan kamfanoni suna ƙaruwa, haka kuma bankuna, ga kuma samun yafewar bashi. Bala'i ya faru a ƙasar yayinda ya ƙara yawa rasuwa da aka samu a tarzomai, ko kuma kashe-kashe. Arzikin ƙasar mai, ya zama matsala yayinda akwai ƙaramci shi da kuma tashin hankali. Ƙananan ƴan kasuwa da ma'aikata basu jin daɗi kuma suna shakka.</response>
               <eng-fdbk>Incorrect! The choice is not correct because it misinterprets some of the report's statements. Please read the last paragraph again. What conclusion does the writer draw?</eng-fdbk>
               <fdbk>Ba daidai ba ne! Wannan amsa ba daidai take ba saboda tana ƙari bisa ga yadda aka rubuta. Ku ƙara karanta sakin layi na ƙarshe. Minene jawabin mai rubutun a ƙarshe?</fdbk>
            </opt>
            <opt>
               <eng-response>This report depicts the different aspects of Nigerian political and socioeconomic life in a balanced series of fortunate and unfortunate events that marked the year 2006. The INEC paves the way and lays a solid foundation for democratic elections, through hardship, yet there is another battle for transparency in the appointment of governors. The attempt of the President to change the constitution in order to get another term in power is overturned by the people with the support of the Senate after months of confusion. The debt relief, the booming banking system and corporate businesses are significant achievements, although small local businesses are undermined by decisions that affect ordinary citizens who are striving to make ends meet as well. Although the year started and ended with tragedies, the people who live should be grateful, the writer said.</eng-response>
               <response>Wannan rahoton yana bayyana fannoni na zaman mutane, da tattalin arziki  da kuma al'amarin siyasa a Nijeriya, cikin daidaitaccen zane na abubuwa masu kyau da maras kyau da sun maki shekara ta 2006. Hukumar zaɓe ta share hanya kuma ta ƙarfafa zabe da za a iya yi cikin hanya ta dimukuraɗiyya duk da aikin ba mai sauki ba amma, akwai kokowa a wajen tsige gwamnoni da riƙe su a matsayinsu ko fitar da su. Ƙoƙarin shugaban ƙasa na canza tsarin mulki domin ya tsawaita wa'adi ikonsa ya samu hamayya har an tsaida shi da sa bakin majalisar dokoki  bayan gardamomi. Yafewar bashi, da ƙarfafar bankoki, da haɓakar kamfanoni muhimman ayyuka ne ko  ƙananan sana'oi suna da matsala don wasu dokoki, waɗɗanda ba ƴan kasuwa kaɗai suke shafa ba, amma har da talakawa da ma'aikata da suke fama da rayuwar kullum, Duk da bala'i, farko da karshen shekarar, marubucin ya ce masu raid,sambarka ce tasu.</response>
               <eng-fdbk>Correct! This is the best choice because it cites the main ideas of the text in giving both positive and negative events of the year and their social, political and economical importance for the country and democracy. It also gives the writer's objective point of view.</eng-fdbk>
               <fdbk>Daidai ne! Wannan daidai ne saboda yana bin yadda karatun ya bayyana abubuwan masu kyau
da maras kyau  da suka faru cikin shekarar da kuma muhimmacin su ga ƙasar da dimukuraɗiyya.Yana bada maganar mai rubutun wadda take tsayawa ga al'amuran ba ra'ayin kanshi ba.</fdbk>
            </opt>
            <opt>
               <eng-response>This is a report on the positive and negative events that marked the year 2006 in Nigeria. Many changes have occurred in the political realm, which in the long run will benefit the country’s economic and social stability. The interdependence of citizens through small business and work has been affected by new regulations that are not welcomed and could spark unrest and violence that may affect foreign workers in the oil industry. The legal system is corrupt and unfair in the sense that governors are covered by the authorities even when they are believed to have committed crimes. Democracy has not progressed in spite of some improvement in the economic sector with corporations and banks growing, and significant debt relief available.</eng-response>
               <response>Wannan rahoto ne bisa muhimman abubuwa masu kyau, da abubuwa na ɓacin rai waɗanda sun maki shekarar ta 2006 a Nijeriya. A wajen fannin siyasa, akwai canji da dama waɗɗanda zasu kawo alheri zuwa gaba, bisa tattalin arziki da  tattalin zaman lafiyar jama'a. Dogaro da juna tsakanin ƙananan ƴan kasuwa da ma'aikata ya samu cikas saboda sabobin dokoki da an tsara waɗɗanda ba lalle an yi marhaba da su ba, kuma da suke iya kawo hargitsi da tarzoma ga yanki da mai yake, da suke iya   shafar ma'aikatan ƙasashen waje masu aiki cikin kamfanonin man. Wajen shara'a akwai rashawa da rashin gaskiya inda gwamnoni suna da garkuwa ga a fitar da su daga matsayinsu kome girman laifinsu. Dimukuraɗiyya bata samu  ci gaba ba ko da shike akwai  gyara ga tattalin arziki, ga bankoki, kamfanoni, da kuma yafewar bashi da kasar ta samu.</response>
               <eng-fdbk>Incorrect! This choice is not the best answer because it does not reflect the events of the year in an objective way like the original text. Please think about the unfortunate events that marked the year. How does the text present them?</eng-fdbk>
               <fdbk>Ba daidai ba ne! Wannan amsa ba daidai take ba saboda
taƙaitawar bata bada bayyanin abubuwa da suka faru kamar yadda labarin yake nunawa daidai yadda suke, ba da ƙari ko ragi ba. Ku yi tunani bisa abubuwa maras kyau da sun faru. Yaya karutun ya bayyana su?</fdbk>
            </opt>
         </choices>
      </problem>
   </problemset>
   <instr type="eng">INSTRUCTIONS:
Choose the best summary.</instr>
   <instr type="target">Umurni:Zaɓi taƙaitawa mafi dacewa.</instr>
   <finishtl>Ana iya cewa dimukuraɗiyya tana tafiya da kyau a Nijeriya game da abinda muke karantawa nan? Donmi? ku bada bayyani bisa ra'ayin naku.</finishtl>
   <finish>Would you say that democracy is progressing in Nigeria from what we read? Why or why not?</finish>
   <finishtl>A ganinku wane irin aiki yake jiran sabon gwamnatin Nijeriya a wajen tattalin arziki da jama'a, in an duba abubuwan da an riga an yi?</finishtl>
   <finish>What economic and social issues would a new Nigerian government have to address, considering what has already been done?</finish>
   <finishtl>Kuna iya ganin dalilai da za su sa a samu matsalar mai har da za a yi dogon layi a gidajen mai a ƙasa mai arzikin man fetur kamar Nijeriya</finishtl>
   <finish>What are possible reasons that would justify long lines at the gas stations in an oil-rich country like Nigeria?</finish>
</activity>