Overview
- Lesson Title: Pascal Sevran - This is an interview with Nuhu Arzika, president of the Coalition of Civil Society in Niger, about his reaction to Pascal Sevran's controversial statement about hunger in Niger.
- Language: Hausa
- Topic: Culture/Society
- ILR Level: 2+/3
- ACTFL Proficiency: Superior, Advanced-High; This ACTFL rating is an approximation based on the ILR level
- Modality: Listening
- Learning Objective: Maintenance & Improvement
- Subject Area: Language
- Material Type: LO
- Publication Year: 2007
- ObjectID: HAUS_12023
Transcript
Original | Translation |
---|---|
Pascal Sevran A: Munyi Allah wadai da wannan zancen, shi am mafarin muka kawo haɗ in kai da goyon banyanmu bisa kan yadda gwamnatin Nijer ya ɗauki niyya bisa kan wannan irin abin da ya faɗi zuwa ga Nijer da 'yan Nijer. Kuma abinda ya faɗi zuwa ga ɗan Adam ba Ƙin mutum, na faɗ in duniya gaba ɗaya, ya kamata lalle a tar da Ƙara zuwa gare shi domin a hukuntashi, saboda wanda ma ya ke da niyyar lissai irin nashi, saboda gobe kada yasamu dama irin wannan. Dan munyi imani da irin wannan masu irin hankali irin wannan, su ne … tun zamani itirel, a kai irin wannan masu hankali su kawo tashin duniya gaba ɗaya. B: Mmm … A: Kuma ya kawo ma mutane,kashe-kashe da wani irin tashin hankali, wanda a yau bai kamata a ce yau bai kamata ace a yau ya ɗauki…ya ɗ auki… mutane gaba ɗaya hakanan ya … ya zagesu. Yau matsayin da baƘin mutum yake, duk inda ake shiga a duniya na wani ilimin kimiyya, kowani sani, kowane abun na'ora, kowane abu can, ana samun 'yan Ƙabila kowace irin wanda suke dashi. Wanda su ganeshi, kuma ana samun baƘin mutun da dama a nan. Yau in ka yi ɗ auka… hatta…Naza ana samun baƘin mutum da yake tun cikin naza, kowa ya sani su Sheik Diyara yana can, . Kowa ya sani, akwai su da dama, a nan yanzu su {Colin Powell [English] } ai duk babbaƘun mutanene, sun yi zamanto hafshen-hafsoshi na Ƙasar Amurka gaba ɗaya. Yanzu {Condoleeza Rice [English]} tana nan,ai baƘar mace ce. Lalle sunso suyi amfani da abin da ake faɗi a nan Nijer. An ce mun samu yunwa, yunwar da ake Nijer .Yau ai yunwa kamin ayi yunwa Nijer. an yi yunwa a duniya ko'ina-ko'ina. Ƙasar Amurka, an yi yunwa. Kowa ya sani Ƙasar Indiya an yi yunwa. Kamin ayi yunwa na nanga namu, an yi ta ko'ina. A Ƙasar bahaushe ma an taba yin yunwa. A Ƙasashen doran duniya duk ko'ina ba inda ba'a inda wannan abun bai samu mutaneba. kenan, abin da yayi ya zamanto an kawo goyon baya wadda zai bada dama. Ba zance wani yace aa ya roƘi gafara ba, a’a ko ya roƘi gafara, aka ce aba matacce kashi saboda mai rai yayi tsoho. Saboda haka muka gani ya kamata zancen Ƙararnan a yankeshi. B: Anya kuwa … ah … watau, ba shugabannin Ƙasashenmu na Afirka bane suka bada kai bori ya hau shi wannan Pascal Sevran ya samu damar rubuta wannan littahi. Tun da idan da suna gudunar da mulki fisabilillahi tsakani da Allah, bai kamata a ce akwai wanda zai rasa abinciba, akwai wanda zai rasa magani, akwai wanda zai rasa wurin kwana a irin Ƙasashenmu. Duk da talaucin da ake cewa muna da su. A: Wannan ba shakka, nayi imanin da hakanan. Nayi imanin da yau akwai matsala da dama na tahiyadda alamuran mulki a cikin Ƙasa. A yi a Afirka gaba ɗ ai kuma misalin kamar a cikin Ƙasar Nijer gaba ɗaya da yake, muna tare da mashi.. magabata, muna tare da shugabanni wanda yawancin kokowar da suke duk dare, da ini, kokowa suke yi, kansu su ke wa kokowa. Abin da suke fata su samu arziki da su da iyalensu su bar wa iyalensu. Yau a Nijer zaman da muke yi, lalle … ai, koda wancan ya goya mana shi, bamu iya cewa yana da gasikiyar ya goya mana hakanan. Amma, akwai wannan zance na cewa a nan Nijer yanzu akwai mu da matsala dama, Lakwal ta ta ɓar ɓare, zancen likita ya ta ɓar ɓare, kuma talauci ya haddabi mutane. A yi kuma tsayi yadda ake tahiyar da al'amuran Ƙasa, abu ne ake wanda yake Ƙara cima da mutane tuwo a kwarya, tun daga irin arzikin da Allah ya yi muna. To, lalle a yau akwai su magabata da dama cikin Afirka inda yawanci kansu suke ma, kowar kashe kihi goranai, wannan ba a ra'ayi ba ne wanda ya kamata a ce ana tahiyar da al'amuran irin Ƙasashenmu gaba daya, bisa kan hakanan. Yanzu nan Nijer, irin arzikin da Allah ya yi muna, muna da {uranium [English]}, muna da feterol, muna da duk wani abunbuwa dama wanda ya kamata a ce a faɗin duniya dukka su ne a arzikin da ake bugun gaba dasu a ko'ina. Amma matsalar da muke da ita yau, sai ya ta zamanto matsala na tsarin mulki na tahiyadda al'amura tsarin tahiyadda … ah, ah … wallafa arzikin Ƙasa, wadda zai unfanin Ƙasa gaba ɗaya, ba wanda zai zamanto … ah … unfanin kawai magabata ba daga su sai iyalen su sai mukar...mukar...muƘarrabansu. Wannan ya zamanto babban zalunci ne, wanda yake ba da dama ire-iren waɗannan 'yan iska kaman su {Pascal [English]}su zama suna ɗaukarmu mun zama kamar dabba bamu san cewan kammuba,bamusan abin da muke so ba, watau mun zamanto kamar mutane masu-tafiya hakanan da hankalin raƘumma. B: Yawwa, to Nuhu Arzika ganin cewa kana ma'amalada talakawa, kana tattauna da su, me kaji suna cewa game da wannan littahi, summa san an rubuta? A: Wanna har yanzu magana ce wadda take ai sai ince sama sama tsakanin mu muda munkai karatu, ai da kuma su sauran ma'aikata manya manyan ma'aikata da mutanen gwamnati, gare su ne zance yake. Har yanzu zancen wanga bai kawo wajen talakawa wanda su talakawa abin da yaddamesu yau,abin da yaddamesu talaucin da ya,suka fuskanta duk sahiya, ka tashi da sahe, kana dattijo bakada abin da zaka bada cefane. Ba ka san inda za ka shiga ba. Yanzu nan muna na zaune, a nan ay mutane hankalinsu ya tashi, na talaucin daya kai musu karo. Ana gobe, ana jibi za'a salla, mutane ba susan wadda za suyi su samu rago ba, wani bai san wadda zaiyi ya samo kayan cefane ba, wani bai san wadda zai ya sai ma 'yan yaranshi wani abin tufafi ba. Bakin abin da yaddamesu kenan ba wannan zancen wani rubutu ba. B: Yawwa, to a horkon wannan tattaunawa tamu,Nuhu Arzika ka nuna a cewa lalle ra'ayinku ya zo daya da na gwamnati game da wannan littahi da aka rubuta, game da kuma Ƙarar da ake shirin shigarwa akan shi marubucin littahin. Shin kuwa, akwai wata gudunmawa taƘamaimai ban da shi goyon bayan a watau da kuka ba da? Akwai wani shiri taƘamaimai - A: Ai … B: -- gudunmawa da Ƙungiyar taku za ta ba da game da wannan Ƙara da ake shirin shigarwa? A: Ai, ba shakka. A cikin kungiyoyinmu na farar wula, muna nan muna tsaye-tsaye, kuma a yanzu haka muna nan muna da … muna kuma … ai, saduwa da sauran … ai … Ƙungiyoyina … ai, Ƙasar faransi wanda su kansu suma suna kokowa da kare haƘin ɗ an adam kuma suna kokowa da irin wannan bambancin Ƙabila da ake yi, wad na, na..na, raina wayo. Kaman misalin boƘarasisin da ake yi, a ake yi. Akwai wasu Ƙungiyoyin wanda mukenan muna hulda da su, muna jibin mugani,ire iren wannan abu waje hanya ya kamata mubi. Kuma wancan ai, na Ƙasar faranci da na nan ga namu na Nijer, muna neman tun da zancen da ya kawo, ba zance ne da ya shahi 'yan Nijer kawai ba. Zan ce ne wanda ya shahai duk ɗan Adam baƘin mutum a duniya, kuma wanda ya shahi duk ɗ an Adam wanda yake fata a yi kwanciyar hankali a rayuwa a ta zaman duniya ta ɗ an Adam. To, don a kan hakane, ke nan muka ganin maganar ce wadda a yau duniyar nan, ba wanda anka hidda ciki. Kowa daidai ne ya sa bakinshi ciki, kuma kowa daidai ne ya kawo gudunmuwar shi a cikin kokowar da akeyi domin a yi abin da zai kawo, a ce a faɗ in zaman da muke a nan duniyar nan, mutane masu irin wannan hankali irin na Pascal. Sun daina shi, sun bar wannan irin wannan tunanin da wannan irin lissahi, saboda a yi su gane da cewa, rayuwa ta ɗan Adam, babu wani ɗ an Adam wanda yafi wani, sai wanda ya yi raggon kaya kawai. Translation Pascal Sevran A: We have this damnable matter; this utterance is the reason we have come together and given our support to what the government of Niger has determined to do regarding what he has said about Niger and its people. And what he has said about black people, he has been saying to the entire world, and we must certainly join in the complaint to pass judgment on him, because of those intent on his kind of reckoning, so that more of this kind of thing doesn’t happen in the future. So we have commented on people with this kind of sensibility, who are … since time immemorial, have brought those with this kind of sensibility to cause a worldwide uproar. B: Mmm … A: And it makes people of all kinds very angry, who, nowadays it mustn’t be said, nowadays it mustn’t be said, that he regards all people this way and … insults them. Today, the status that black people have, wherever one goes in the world, in science, any kind of knowledge, any kind of technology, anything out there: one finds every kind of ethnic group that has it. Among those who understand it, you will find plenty of black people. Today, if you consider … even … NASA, you will find black people even in NASA; everyone knows Sheikh Diyara’s people are there. Everyone knows, there are a lot of them, right now those like Colin Powell - yes all of them black people - he was the chief-of-staff of the entire U.S. Now Condoleezza Rice is here, and she is a black woman. Certainly they want to benefit from what is being said here in Niger. We are said to have famine, the famine that we have in Niger. But today, the famine like we have in Niger, there is famine like this everywhere in the world. In the U.S. there is famine. Everyone knows there is famine in India. As there is famine here like ours, so there is famine everywhere. In Hausaland they have had famine. In countries all around the world, there’s no place where people don’t have this kind of thing. So that is what turns out to bring support which will provide opportunity. It’s not a matter of one saying no, he begs for forgiveness, no or he begs for forgiveness; the youth will be given a hard time because the one who survives is old. Because of this, we must proceed to prosecute him. B: One could also … ah … that is, couldn’t it be said that our African leaders made it possible for this guy, Pascal Sevran, to write this book? Because if they were running their governments as God instructs, one mustn’t say that there is someone who will lack food, there is someone who will lack medicine, there is someone who will lack a place to sleep in our countries. Even with the poverty that the world claims we have. A: No doubt about that, I believe in that. I believe that today there’s a comparable problem in managing government affairs in the country. They are occurring all over Africa, just as they are occurring throughout Niger: we all have those … top officials, we all have those top officials, most of whose effort throughout the day and night, is effort on behalf of themselves. What they are hoping to get is wealth that they and their families can leave to their families. Today in Niger, that’s certainly the difficult life we lead … but even if that one tied us to it, we can’t say he’s right to tie this to us. But there is this matter that here in Niger today, we have many problems that keep breaking out; there are problems with our schools, the matter of doctors keeps breaking out, and poverty has stymied the people. We have stopped managing the country’s programs that would increase food for the population, despite all the kind of wealth that God has blessed us with. Well, certainly today there are many top officials in Africa, where most are inclined to have a policy that “whoever catches the fish, puts it in his gourd”; but this is not conducive to running the affairs of our kinds of countries all together, according to this. Today in Niger, with the kind of wealth that God has given us, we have uranium, we have petrol, we have all of the many things that all so-called wealthy nations boast of. But the problem that we have today is turning out to be a constitutional problem of managing affairs, management of producing wealth in our country, as would benefit the whole country, not which would turn out to … ah … benefit just the top officials and their families and their … meddlesome associates. This has turned out to be a huge tyranny, which gives an opportunity to those kinds of idiots like Pascal and his like to come along and regard us as if we were animals, who don’t know self-restraint, who don’t know what we want; in other words, that we have turned out to be like people going along with the intellect of camels. B: Indeed, so Nuhu Arzika, seeing that you have interactions with the common people, and that you converse with them, what do you hear them saying about this book? Are they even aware of its existence? A: Up to now, this talk that has been going on, well, I’d say it’s really just been between those of us who are capable of reading, and also those other high-level workers and people in government who have the matter before them. Until now, the matter has not reached the common people, who are preoccupied with the here-and-now of their poverty, who face it every morning: you get up in the morning, you are an elderly person with nothing to spend on groceries. You don’t know where you’ll go in. Right now, we’re sitting here, and people here are worried about the poverty they’re up against. One goes on tomorrow and the next day praying, but people don’t know what they will do to get meat, one doesn’t know how he will go about getting groceries, another doesn’t know how he’s going to buy his little children some clothing. That’s what concerns them, not the matter of books. B: Alright, on the issue of this conversation of ours, Nuhu Arzika, you have certainly shown that your opinion is one with the government regarding this book that has been written, and also regarding the lawsuit that is being prepared against the book’s author. That said, is there some other assistance besides the support that you are providing? Is there another plan for certain -- A: Yes … B: -- assistance that your organization will give regarding this lawsuit that they are preparing to institute? A: Yes, without a doubt. In our organizations, in the first place, we are standing firm, and now we here have … we have also … ah … been meeting with other organizations in France that are themselves trying to protect human rights, and trying to fend off this kind of bigotry that is shown between different peoples. For example, they do in-depth investigations into what is done. There are other organizations that we have here, with whom we have relations, and we work together to understand these kinds of things and what course should be followed. And that one in France, and ours here in Niger, we have been finding since the matter came about that it’s not a matter that concerns only the people of Niger. I would say it is something that concerns all black peoples of the world, as well as all people who are hoping for peace in the world for humanity. So, it is on this account that we have seen discussion of how today, in this world, no one can stand apart. Everyone is right to have his say in it, and everyone is right to assist in the effort being made to do something that will bring a conversation on the life that we lead in this world to those with Pascal’s sort of mindset: so that they give it up and stop this kind of thinking and this kind of reckoning, and so they are made to understand that in human life, there is no person who is better than another, except those who choose to be lazy. |
Glossary
Hausa | Hausa Meaning | English Meaning |
---|---|---|
Lakwal | Wannan kalma ta fito daga harshen faransanci "ecole" wanda ya ke nunfin makaranta. | This word comes from the French word "ecole" which means school |
Rena wayo. | Nuna rashin ban girma, ko rashin ladabi ga wasu mutane. | Disrespect, insult to others |
Tarda ƙara | A kai mutun gaban kotu. | To sue, to make charges against somebody |
Tahiya da hankalin raƙumma. | A aikata rashin hankali. A yi wani abu cikin rashin lisafi. | Lacking intelligence in one's actions; being stupid |
A ba mattace kashi saboda mai rai ya yi tsoro. | A yi horo ga kowane mai laifi kan karhin laifi domin ya zama abin tunani ga wasu har da za su ƙi su yi laifi. | This is a proverb that means nobody is above the law |
Suka bada kai bori ya hau. | Ayyukansu sun zama mafarin magana wadda ba ta girmamawa daga bakin wasu. | They draw forth unpleasant reactions from others through their acts, provoke |
Kowa kashe kihi goranai. | Kowa yana neman arzikin kansa kaɗai. | Being selfish |
Notes
Hausa Notes | English Notes |
---|---|
Farin da ya buga ƙasashen sahel( ɓangare na Afrika da yake tsakanin hamada Sahara da daji mai ciyawa a kudu) cikin shekara ta 2005, game da mamayewar fara da suka kawo yunwa, ya ja hankalin duniya duka. Mutane sun ɗauke su kamar alloba na halin lokaci, amma sun yi Allah waddai da maganar ɗan jarida na gidan jarida Faransa France2 Pascal Sevran: La bite des noirs est responsable de la famine en Afrique", azzakarin baƙaƙe shi ne mafarin yunwa a Afirka, domin sun ce ƙabilanci ne da kuma wariyar jinsi.Ya kuma ƙara nanata wannan magana da zana sunan ƙasar Nijer cikin wani littafi da ya rubuta. Gwamnatin Nijer da wata Ƙungiya mai kula da hakin ɗan adam sun kai ƙarar Sevran a kotu. Wasu ƙungiyoyi na wasu ƙasashe sun riga sun kai ƙararshi saboda irin waɗɗanan magganganu na wariyar al'umma da ya faɗi a kansu. Shara'a wannan kuma za ta iya nisan da za ta shiga cikin hannun Majalisar Ɗinkin Duniya. Ana anfani da karin magana dayawa a Africa. Mutane suna iya su yi hira da karin magana kawai, ya kan zama da wuya a gane su wani lokaci. Samun taimako ga wasu ƙasashe kamar Nijer ya kan danganta da yarda da an yi da shugabanin ƙasar saboda yawancin lokaci suna kasawa ga biyan bukatun jama'a kuma suna jawo ma jama'arnan gori na ƙasahen waje. |
The drought that hit the sahel (transition zone between the Sahara desert and the savannah grasslands) in 2005, along with the locust invasion, lead to a famine that drew worldwide attention. The plight was seen as a natural catastrophe, but the remarks of the French television France2 commentator Pascal Sevran: "la bite des noirs est responsable de la famine en Afrique" (the black penis is responsible for famine in Africa) were condemned because of their racist and sexist implications. He cited Niger in his book to support his argument. The government of Niger and an international human rights organization, Ligue Internationale contre le Racisme et l'Antisemitisme, brought court charges against Sevran, adding yet another complaint for racist comments from other countries, which may go as high as the United Nations. The use of proverbs is common in many parts of Africa. A whole conversation can consist of proverbs and sayings, making it sometimes hard for other people to understand. International aid for countries like Niger is sometimes based on the credibility of their leaders, who fail to provide for their people, exposing them to pressure and outside humiliation. For more information, please refer to: http://www.afrik.com/article10877.html www.afrik.com/niger |
CONTENT SOURCE: Interviewer (Halima Djimrao-Kane); Interviewee (Nuhu Arzika, president, Coalition of Civil Society G (2006 December 22). Pascal Sevran. Washington, D.C.: Voice of America, Hausa Service.
Objective: Demonstrate your core comprehension.
Content description: This is an interview with Nuhu Arzika, president of the Coalition of Civil Society in Niger, about his reaction to Pascal Sevran's controversial statement about hunger in Niger.
XML
<activity>
<problemset>
<problem correctindex="2">
<choices>
<opt>
<eng-response>Pascal Sevran's interpretation of the causes of hunger in Africa, and Niger in particular, has sparked strong reactions from people such as Arzika, the angry human rights advocate in this interview. The French commentator's outrageous comments have connotations that would incite the sort of racial discrimination seen in Hitler's era, Arzika points out. Such an attitude should be discouraged, and Sevran should be reprimanded. Arzika affirms his idea of racial equality, presenting a list of well-known blacks participating in all aspects of development from science to politics. Although he acknowledges the failure of some African leaders to satisfy their people's needs because of selfishness and greed, he maintains that Sevran has no right to insult a people or a race striving to live in dignity, and expect to get away with it.</eng-response>
<response>Magana wadda ɗan jarida na France2 Pascal Sevran, ya yi bisa dalilin yunwa cikin ƙasashen Afrika har dai Nijer, ta tasar da hasalar mutane dayawa kamar yadda shi wannan mamba na wata ƙungiya mai kula da tara haƙƙin ɗan adam,watau Arzika, yake nunawa cikin wannan tattaunawa.Wannan wulaƙanci da ɗan jaridan ya yi, yana iya kawo wariyar launin fata kamar yadda Hitler ya yi; domin haka ya daidaitu a yi wa Sevran jinƙai don wasu su koya, Arzika ya ce. Ya zana sunaye na mutane, baƙar fata da suke cikin harakokin ilimin kimiyya ko siyasa domin shi nuna cewa babu banbanci tsakanin baƙar fata da wani launi.
Ya yi imani da cewa shugabannin ƙasa su kan jawo ma jama'arsu sharhi saboda son kansu, da rashin kula da arzikin jama'a , amma ya maimaita cewa duk da haka Sevran, ko kuma wani bai da ikon zagin Niger ko baƙar fata.</response>
<eng-fdbk>No, this is not the correct answer. Please listen again to the speaker's tone and his use of idioms. Specifically, listen to what Arzika thinks the world community should do as a response to Sevran's comments by the world community.</eng-fdbk>
<fdbk>A'a! wannan ba daidai ba ne. Ƙara sauraren muryar mai maganan da kuma yadda yana anfani da karin magana. A saurari a ji yadda Arzika ya ke tunanin ya kamata duk duniya ta yi bisa ga maganar Sevran.</fdbk>
</opt>
<opt>
<eng-response>Racial discrimination is at the center of this interview. Allegedly racist and sexist comments made by the French commentator andwriter Pascal Sevran have been taken to court by Niger, backed by some human rights organizations. An advocate from one of the organizations reiterates the gravity of Sevran's words and the necessity of punishing him in order to let people with similar intentions know that discrimination is no longer tolerated. According to Arzika, hunger is a plight that can affect any country, regardless of its wealth or color. All nations should come together and join the people of Niger in their determination to win the case, and thus prevent any racist incident from taking place in the country.</eng-response>
<response>Wariyar launin fata ita ce kan maganar wannan tattaunawa. Gwamnatin Nijer, tare da goyon bayan wasu ƙungiyoyi masu kula da kare haƙin ɗan adam ya kai kukansa a wani kotu game da sharhin da Pascal Sevran ya yi wa ƙasar bayan yunwar da taɓe ta. Wani cikin masu goyon bayan ya nanata girman lahanin da Sevran ya kawo cikin magana, da rubutun da ya yi. Ya kwatamta cewa da ko da Sevran yo roƙi gafara, ya kamata a yi masa hukumci don wasu mutane masu niya irin tashi su sani da ba ƙaramin lahani ba ne da za a bari ya wuce. Ya kuma nuna cewa da ita yunwa, alloba ce da ba ta bambanci launin ko arzikin ƙasa; tana buga kowa. Ya kamata dukan ƙasashe su taru su ba yan Nijer hannu domin su cika gurinsu na cin nasara, ta haka kuma a hana faruwa rigima ta bambanci launi cikin ƙasar</response>
<eng-fdbk>No, this is not the correct answer. Think about the speaker's answer to the final question. Does the summary represent the speaker's point of view?</eng-fdbk>
<fdbk>A'a! wannan ba daidai ba; ƙara tunani bisa amsa da mai maganan ya bada a ƙarshen hiran. Taƙaitawar tana bada ra'ayin mai maganan kuwa?</fdbk>
</opt>
<opt>
<eng-response>This interview is about the reaction of the government of Niger as well as human rights associations to France2 television commentator Pascal Sevran’s correlation of hunger, sexuality in Niger, and black people. Developed countries have experienced hunger, and black people are equal to other races, Arzika said in the interview, considering their presence in technology and politics; he cites names as example. Old beliefs characteristic of Hitler's era should not be accepted in this century, indicates Arzika. The lack of good honest leadership has turned some African countries, even the ones with natural resources, into societies in permanent need of food and literacy. He reaffirms vehemently that their failure does not give anyone a right to racial discrimination. Sevran should not be spared, despite his apology. Arzika calls for global action against racism.</eng-response>
<response>Wannan tattanawa ta ƙunshi koma -bayan gwamnatin ƙasar Nijer da wasu ƙungiyoyi masu yaƙi da taka haƙin ɗan adam ga Pascal Sevran ɗan jarida na France2 bisa ga haɗa yunwa da ya yi da jinsin mutanen Nijer, da kuma Africa gaba ɗaya.Ƙasashe masu ci gaban masana'antu sun ga alloban yunwa, Arzika shugaba na tarayya ƙungiyoyi masu kula da hakin ɗan adam ya ce. An gani da cewa baƙar fata su ma daidai suke da kowace fata da shike akwai su ko'ina cikin ayyukan fasaha da siyasa ya ƙara nunawa da sunayen wasu babbaƙu mutane na yau; domin wannan bai cancanta ba a bar mutane masu tsohon lisahi irin na lokacin Hitler su ci gaba da nuna bambancin ƙabila Arzika ya ce. Rashin shugabanci da gaskiya ya sa wasu ƙasashen Afrika sun tsaya cikin bukata ta abinci da karatu koma suna da albarkatu .Ya ƙara nuna rashin amincewar shi da ƙarhin, ga nuna banbanci ga kowane ɗan adam kuma ya yi kira ga kowa ya yi tsayyaya ga irin wannan tabi'a.</response>
<eng-fdbk>Correct! The interview demonstrates the impact of Sevran's comments on the African and world community. By selecting this choice, you have correctly identified the breadth of the interviewee's reaction to Sevran's racist comments.</eng-fdbk>
<fdbk>Daidai ne! Tattaunawar tana nuna irin yadda maganar Pascal Sevran ta shafi mutanen Afirka da na duniya. Zaɓen wannan amsa ya nuna an gano da
faɗin ɗaukar da mai maganar ya yi wa</fdbk>
</opt>
</choices>
</problem>
</problemset>
<instr type="eng">INSTRUCTIONS:
Choose the best summary.</instr>
<instr type="target">Umurni:Zaɓi taƙaitawa mafi dacewa.</instr>
<finishtl>A ganin ku mai maganar nan ya yi zugugu cikin ɗaukar da ya yi wa maganar Sevran? Donmi?</finishtl>
<finish>Do you think the speaker's reaction is exaggerated? Why or why not?</finish>
<finishtl>Waɗɗane abubuwa ke sa yunwa cikin ƙasashe masu tasowa. A ganinku, yaya ake iya maganin wannan matsala?</finishtl>
<finish>What are the contributing factors to hunger in the developing world and what do you think could be done to solve the problem?</finish>
<finishtl>A gani ku, yaya wannan jayyaya za ta ƙarewa?</finishtl>
<finish>How do you think this dispute will end?</finish>
</activity>