Toggle menu
24K
663
183
158.1K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

UMD NFLC Hausa Lessons/22 Breastfeeding Awareness Week

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Revision as of 12:31, 20 December 2017 by Admin (talk | contribs) (Created page with "==Overview== # Lesson Title: Breastfeeding Awareness Week - This report is about the benefits of nursing infants. # Language: Hausa # Topic: Culture/Society # ILR Level: 1+/2...")
(diff) ← Older revision | Latest revision (diff) | Newer revision → (diff)

Overview

  1. Lesson Title: Breastfeeding Awareness Week - This report is about the benefits of nursing infants.
  2. Language: Hausa
  3. Topic: Culture/Society
  4. ILR Level: 1+/2
  5. ACTFL Proficiency: Advanced-Mid, Advanced-Low, Intermediate-High; This ACTFL rating is an approximation based on the ILR level
  6. Modality: Listening
  7. Learning Objective: Maintenance & Improvement
  8. Subject Area: Language
  9. Material Type: LLO
  10. Publication Year: 2009
  11. ObjectID: T8LHA20

Transcript


Original Translation

A: In kunne ya ji.

B: Hausawa suka ce, jiki ya tsira. Yau saboda muhimmancin cewar shekaran jiya ɗin nan bakwai ga wata muka shiga Makon Tunawa da Shayar da Jarirai Nonon Uwa, ya sanya na zanta da [Dr. {English}] Halima Adamu.

C: Ba ƙananan yara nonon uwarsu zalla har su kai wajen wata shida, sannan bayan sun wuce wata shida nonon uwa ya yi kaɗan kuma a ɗan ƙara masa wani abu mai muhimmanci mai daraja mai tsafta ba tare da amfani da [feeding bottle {English}] ba wato robar tsotso. Mutum ɗan Adam kusan sai ya kai shekaru ɗai-ɗai da rabi zuwa biyu yakan kai ga ya tafi ya rabu da uwarshi, saboda haka sai Allah ya yi mishi shiri na abincinshi wadatacce ingantacce wanda zai amfani da shi, ko da akwai talauci ko kuma ko da uwar ba ta da shi, ka fahimta to wannan shi ne nonon uwa, sai aka yi shi daidai wa daida aka yi mishi isasshen ruwa saboda buƙatar ruwa na ƙaramin yaro, kusan kashi tamanin da bakwai bisa ɗari na nonon uwa ruwa ne, duk abin da za ka ba wa jariri, to ba zai fi nonon uwa ruwa-ruwa ba, ka fahimta? To sha uku bisa ɗari to shi fa ya ƙunshi fanni na abinci na riga-kafi na allura na magani saboda nonon ya ishi yaro, lokacin garkuwar jikinshi kuma ta ɗan fara kafuwa, to za ka ga kuma da wata shida ake fara haƙori ɗai ɗai ɗai har a gama haƙoran shan mama, daidai wata shida ‘yar garkuwarshi ta haɗu, to sai kuma daidai wata shida nonon uwa ya fara yi mishi kaɗan, saboda buƙatunshi na girma, sai kuma Ubangiji yasa yana buƙatar ruwa saboda duk abin da zai ci bayan wata shida aka ɗura mai ya fi nonon uwa kauri, kuma da ka ga ana matsawa a ba ƙaramin yaro ɗan wata shida nonon uwa tsantsa abu biyu ne, muna guje ma najasa, ƙazanta, su kuma ƙwayoyin cuta babu abin da suke so irin abu mai danshi-danshi mai ɗumi-ɗumi, ka fahimta, sai kuma ruwa, duk abu mai ruwa-ruwa ya fi saurin rubewa, duk abu mai ruwa-ruwa ya fi ɗaukar ƙwayar cuta, haka kuma abu mai ɗumi-ɗumi. To shi ya sa ka ga muke yaƙi da kar a ba su komai sai nonon uwarsu. Saboda a lokacin garkuwar jikinsu ba ta ishe su ba, kuma a lokacin in ƙwayoyin cuta suka same su za su sami kansu cikin wahala kuma yadda ka ga duk wani ruwaye da ake ajiyewa ba mai tsabta ba ne ko wanda ake yi na kamfanoni ɗin ba ka da tabbacinsu, saboda haka in ƙaramin yaro ba shi da garkuwar jiki wadatacciya kar ma ka haɗa shi, da [possibility {English}] ne zai sami ƙwayoyin cuta.

B: Wato in na fahimce ki ke nan nonon wato ya ƙunshi duk sinadaren da za su taimaka wajen kare shi daga ƙananan cutuka da sauransu ke nan.

C: Ka ga na ɗaya dai [direct {English}] ake shan su, ba ýan hannu ba ýan kamasho ba cokulla, tsakanin bakin yaro da nonon uwa, ka ga duk an raba shi da hanyoyi da ake samun ƙazanta ta yau da kullum, ka fahimta, sannan ga ɗuminshi daidai wa daida ga kuma tabbacin ya sha ya ƙoshi tun da ba batun a ce ya ƙare ko a tsaya, ba batun a kuma raba ɗa da uwarshi, don ko inda ake sakin aure ko yaji, za ka ga duk yadda akai in tana da ƙaramin ɗa ta yi yaji ko aure ya mutu za ta tafi da ɗanta, ka gane, to wannan cibin na waje shi ne shan nono da runguman, cibin waje ke nan, wanda yana da muhimmanci wajen wayonshi da wani tunaninshi da basirarshi ta nan gaba, shi ya sa za ka ga yaran da ba su sami ingantaccen shayarwa ba da ingantacciyar runguma ta iyaye in suka balaga suka girma su ne za a ga halayensu wani abu dai bai yi daidai wa daida ba.

B: [Dr. {English}] Halima Adamu ke nan ƙwararriyar likitar mata da yara game da muhimmancin shayar da yara nonon uwa.

Benefits of Breastfeeding Infants

A: “If the ear hears . . .”

B: . . . as the Hausa say, “the body will follow.” Today, to mark the significance of Breastfeeding Awareness Week, which began two days ago, I am speaking with Dr. Halima Adamu.

C: Give small children pure mother’s breast milk until they are about six months old. Then, after the age of six months, mother’s milk may not be sufficient, and other substantial, nutritious, and clean food should be added little by little without using a feeding bottle. Up to the age of one-and-a-half or two, when a child begins to walk and is weaned from his mother, God provides enriching and fortifying food for him whether in poverty or even if the mother doesn’t have, you see—mother's milk. It is produced precisely to provide sufficient liquid for the fluid needs of a small child, as nearly 87 percent of breast milk is water, and, you see, nothing else you could give an infant is better than the moistness of breast milk. The other 13 percent contains protective nutrients. The milk alone will begin to establish his immune system. You will also see that from six months, he starts getting teeth one by one until he has all his baby teeth. All his immune defenses have formed by the sixth month, which is the same time that the child may need more than mother’s milk because his needs are increasing—unless the Lord deems that the child needs to continue nursing because anything he is fed after six months may be too substantial. And when you see someone squeezing out pure mother’s milk to give to a small, six-month-old child, there are two things: we may be exposing him to excrement or contaminants or to germs—which like nothing more than dampness, you see—and milk, among all warm liquids, goes bad the quickest and picks up the most germs. So, you see, this is why we insist that infants not be given anything but their mother's milk. Because if their immune system is not fully developed when they come into contact with germs, they will find themselves in trouble; and, as you know, not all bottled liquids are sanitary, or they may be made by companies that you are not sure about. So, if a small child hasn’t developed sufficient immune defenses, you shouldn’t expose him to the possibility of contact with germs.

B: So, if I understand you correctly, the milk contains all the ingredients that will help to protect him from diseases and the like.

C: You see, at first, they should be fed directly without the hands or spoons coming between the child’s mouth and the mother’s breast, which, you see, will keep him from being exposed to everyday contaminants. And then, you see, there is its warmth, which assures that he will drink until he is satisfied, and no matter when he is weaned, even if there is a divorce or the wife leaves the marriage, you will see that any time she has a small child, if she leaves the marriage or the marriage ends, she will take the child with her. You see? This is the maternal connection: breastfeeding and cuddling. It’s the maternal connection that is so important to the child’s future growth and psychological development. And this is why, when children who have not received sufficient nursing and parental cuddling reach puberty and grow up, you’ll see that there is something not quite right about their character.

B: That was Dr. Halima Adamu, a professional gynecologist and pediatrician, on the importance of breastfeeding children.

Glossary

Hausa English Meaning
in kunne ya ji, jiki ya tsira (lit: when the ear listens, the rest of the body escapes) listen and take appropriate action 

This proverb is commonly used to remind a person of the importance of heeding warnings. The first part of the proverb, in kunne ya ji, is being used as the title of this radio program.

ba ƙananan yara nonon uwarsu zalla pure mother's breast milk 

This refers to the "exclusive breastfeeding" practice when a baby is fed only breast milk and nothing else for his or her first six months.

flimbotil, robar tsotso feeding bottle (from English)
garkuwar jiki (lit: body shield) the immunity system
ta yi yaji (lit: she is on strike) she leaves 

This is an expression used to refer to a married woman who leaves her matrimonial home to fight back against her husband's wrongdoing.

daidai wa daida just, right, fit 

Daidai means "correct," "exact," or "straight," and this expression emphasizes the appropriateness of what is being conferred.

isashen ruwa adequate, plenty 

This expression is from isa, which means "to be sufficient."

Notes

1. World Breastfeeding Week

Breastfeeding is endorsed by many health and scientific organizations as the best way to feed infants. Research has shown that the benefits of breastfeeding are not limited to the child but extend to the mother as well. According to the World Alliance for Breastfeeding Action (an advocate group working to promote breastfeeding globally), World Breastfeeding Week is celebrated August 1-7; the theme for this year’s observance is breastfeeding’s role in providing relief in emergency and disaster situations (“World Breastfeeding Week,” 2009).

World Breastfeeding Week. (2009). World Alliance for Breastfeeding Action. Retrieved June 17, 2009, from http://worldbreastfeedingweek.org/

2. Breastfeeding in Nigeria

In Nigeria, breastfeeding is strongly encouraged for economic and hygienic reasons: because of the high cost of baby formulas and because of the lack of reliably clean water needed to mix with the formulas. Breastfeeding is seen as a means to ward off needless infant fatalities.

3. More Information

To read more about the breastfeeding issue in Nigeria, please see Geoffrey Njoku’s “A Nigerian Father Shows His Support for His Wife’s Breastfeeding” at the following link:

http://www.unicef.org/infobycountry/nigeria_45166.html