Overview
- Lesson Title: Teachers Strike in Nigeria - This is a report about teachers' efforts in Nigeria.
- Language: Hausa
- Topic: Culture/Society
- ILR Level: 1+/2
- ACTFL Proficiency: Advanced-Mid, Advanced-Low, Intermediate-High; This ACTFL rating is an approximation based on the ILR level
- Modality: Listening
- Learning Objective: Maintenance & Improvement
- Subject Area: Language
- Material Type: LO
- Publication Year: 2008
- ObjectID: HAUS_12651
Transcript
Original | Translation |
---|---|
Majalisa datijan Nigeriya da kuma majalisa wakilai ta tarraya suna kokarin kawo karshen yajin aiki da malamai suke yi a can Nijeriya A: Kwamatin kula da harkar ilimi a majalisar dattawa a karkarshin shugabancin Madam Joy Emordi ya gayyaci ministan ilimi Igwe Aja-Nwachuku akan yajin aiki da malaman makarantu ke yi a Nijeriya, wanda a yanzu ya shiga mako na hudu ke nan. Kafin wannan gayyata na ministan, kwamitin kula da harkar ilimi bangaren majalisar dokoki, sun yi taro da shugabannin kungiyar malaman, inda kwamitin ya ce zai jagoranci kungiyar zuwa fadar shugaban kasa inda za su gana da shugaba Umar Musa Yar'Adua a kan maganar biyar malaman albashi na musamman. Faruk Lawan, shi ne shugaban kwamitin. B: To, kasancewar abin yaki ci-yaki cinyewa kuma kowa ya sani yaranmu da iyaye da ma tattalin arzikin kasa, shi ne ke kwaruwa a kan wannan abu da ke ciki. Wannan ita ta sa muka ga ya zama wajibi, mu sake kira, mu sake zaunawa da su kungiyar malaman makaranta, domin mu ji na farko ko akwai wani abu da ya faru tsakanin lokacin da mukai meeting (English) na baya da su, da kuma yanzu tsakaninsu da bangaren zartaswa na gwamnati. Na biyu, mu sake jaddada kiranmu a garesu, na ba mu damar mu cigaba da takarar wadda muke ganin ta zama wajibi a kanmu, na jawo kan hankalin gwamnati a kan a fara biyan malaman makarantun kasar nan shi kanshi wannan matakin albashi wanda kamar yanda na fada, tuni mu a majalisa muka tanadi kudin a kasafin kudi na shekara ta dubu biyu da takwas. A: Shi kuwa, Nuhu Dogo Makama na majalisar dokokin Kaduna, yace kamata yayi a yi wa malamai adalci tun a nan duniya. C: To, ba karamin abu ba ne. Dole a horad da malamai, da kuma inda malamai za su zauna, da jin dadinsu, da sauran abubuwansu. Don haka dole mu hakura, mu bi abubuwan nan a hankali, a hankali, a hankali, mu kuma bi gwamnati a hankali, a hankali – A: A halin yanzu, daliban na zaman hutun dole har sai an cimma maslaha akan yajin aikin da malaman suke yi. |
The Nigerian Senate and House of Representatives are trying to bring an end to the on going teachers' strike in Nigeria A: The Senate Committee on Education, under the leadership of Madam Joy Emordi, summoned the Minister of Education Igwe Aja-Nwachuku regarding the teachers strike in Nigeria, which has now entered its fourth week. Before this invitation to the minister, the House of Representatives Committee on Education met with the leaders of the teachers' union, where the committee said it would lead the teachers’ union organization to the State House, where they would meet with President Umar Musa Yar'Adua on the issue of special salaries for teachers. Faruk Lawan is committee chairman. B: Well, since the dispute continues unabated, and as everyone knows, our children, their parents and even the country's economy, are suffering as a result of the current situation. This made it necessary for us to issue another appeal, to sit again with the teachers' union in order to hear, first, if anything had happened between our last meeting with them and now, between them and the executive arm of the government. Secondly, to renew our appeal for them to give us the opportunity to continue with the role that we believe has become incumbent upon us, to draw the government’s attention on the need to start paying the country's teachers this salary structure, for which as I have said before, we in the legislature have since allocated funds in the 2008 budget. A: Meanwhile, Nuhu Dogo Makama of the Kaduna State House of Assembly says teachers must be treated fairly in these circumstances. C: Well, this is no small issue. Teachers must be trained and their shelter, welfare and other issues must be provided for. Therefore, we must be patient and attend to such matters very, very carefully, and also pursue the government very patiently-- A: For now, students are on mandatory break until the teachers' strike is finally resolved. |
Glossary
Hausa | English Meaning |
---|---|
taka rawa… | "Playing a part", "taking responsibility" (literarily, to step dance) |
yajin aiki | "Strike" |
kwaruwa | "Suffer", "to be in pain" |
ya ki ci ya ki cinyewa | "Inability to solve a problem" (literally, something has refused to be eaten completely) |
a hankali,a hankali | "Slowly, slowly" |
jagoranci | "Guidance", "leadership" |
shuagabanai [shugabani] | "Leaders" |
jaddada | "Renew", "reform" |
hora da.. | "Instruct" |
Notes
1. Teaching is one of the lowest paying jobs in Nigeria, a country known for its oil and other natural resources. Although it is only the teachers who are on strike, the masses believe this should be everybody’s strike because of the exploitation by the corrupt ruling class.
The recent strike was another back-up to the demand that has been on for about 20 years. The same demand was also agreed upon by the government in 2003 but never signed.
On the 30th of June, Nigerian primary and secondary school teachers went on a strike to push the government into honoring their promise of increasing teachers' salaries. The federal government agreed to increase federal school teachers’ salaries but said they cannot compel the state and local governments to do the same for their teachers. The Teachers Union, however, insists that all teachers benefit from the new pay.
http://www.marxist.com/nigerian-teachers-strike-beginning-wider-movement.htm