Toggle menu
24K
665
183
158.2K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

dafi

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Revision as of 16:08, 11 March 2019 by Maintenance script1 (talk | contribs) (Quick edit: appended Category:Hausa lemmas)
(diff) ← Older revision | Latest revision (diff) | Newer revision → (diff)

Noun

Tilo
dafi

Jam'i
babu (none)

m

  1. venom, poison. <> wani ruwa da kan fito daga haƙoran maciji yayin da ya sari mutum.
  2. a lethal tranquilizer. <> maganin da akan saka a kibiya don kashe dabba.

Glosbe's example sentences of dafi

  1. dafi. <> secretes poison, person, naphtha, poisonous, poisonous, poisonous snakes, poisonous, lethal, poisonous, poisoning, poisonous snake, poisoning.
    1. Kashegari za ka ji kamar maciji mai dafi ne ya sare ka. <> At its end it bites just like a serpent, and it secretes poison just like a viper.
    2. Muddin mutane sun amince da su, suna kawo ƙiyayya, dafi, da ra’ayoyi masu haɗari—sau da yawa da sakamako na bala’i, yadda tarihi na ƙarni na 20 ya nuna.—Misalai 6:16-19. <> Once people accept them, they produce some very jaundiced, poisonous, and dangerous beliefs—often with disastrous consequences, as the history of the 20th century has shown.—Proverbs 6:16-19.
    3. Saboda haka Jehobah ya aika da waɗannan macizai masu dafi su yi musu horo. <> So Jehovah sends these poisonous snakes to punish the Israelites.
    4. Sai Jehovah ya sa macizai masu dafi su yi musu horo. <> Jehovah sends poisonous serpents to punish them.
    5. (Karin Magana 23:31-33) Yin maye na kama ne da saran maciji mai dafi, yana jawo rashin lafiya, yana ɗimauce hankali, har da fita hayyaci. <> (Proverbs 23:31-33) Excessive drinking bites like a poisonous serpent, causing sickness, mental confusion, even unconsciousness.
    6. 3. Menene mutanen suka ce Musa ya yi bayan Jehobah ya tura majizai masu dafi su yi musu horo? <> What do the people ask Moses to do after Jehovah sends poisonous snakes to punish them?
    7. Jariri ma zai yi wasa kusa da maciji mai dafi kuma ba zai yi masa kome ba.’ <> Even a baby will not be harmed if it plays near a poisonous snake.’
    8. DAFI na abinci bai da daɗi ko kaɗan. <> FOOD poisoning is very unpleasant.
    9. Amma daina cin abinci gabaki ɗaya domin guje wa dafi na abinci ba shawarar kirki ba ce. <> But to give up food entirely so as to avoid the risk of food poisoning is not a realistic option.
    10. Wanda dafi na abinci yake damunsa yana bukatar ya mai da hankali da irin abinci da yake ci. <> A person who repeatedly experiences it needs to be more careful in his eating habits.
    11. A lokacin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki, sojoji suna amfani da kibiya da aka yi da kyauro da ƙananan ƙarafa da aka jika da dafi. <> In Bible times, soldiers used darts made out of hollow reeds having small iron receptacles that could be filled with burning naphtha.
    12. Gwanaye sun kammala cewa likitar ya ziyarci Robert a gidansa, kuma ba da sanin Robert da iyalinsa ba, likitar ya yi masa allurar dafi. <> The authorities concluded that the doctor had visited Robert in his home and, unbeknownst to Robert and his family, had given him a lethal injection.