Toggle menu
24.1K
670
183
158.5K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

saɓa

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Revision as of 20:06, 11 March 2019 by Maintenance script1 (talk | contribs) (Quick edit: appended Category:Hausa lemmas)
(diff) ← Older revision | Latest revision (diff) | Newer revision → (diff)

Verb

  1. to be inconsistent, on the contrary, disagreement. <> kasa dacewa wajen samun mutum.
  2. gota.
    kujerar nan ta saɓa da sauran.
  3. rashin jituwa tsakanin mutane. <> inability for people to come to an agreement.
  4. karya. <> to infringe, break (a law/rule).

Verb 2

  1. rataya ko ɗora sanda ko wani abu a kafaɗa.
  2. cin laya ko rantsewa.
    ya saɓa Alƙur'ani.
  3. goga sabulu ga tufa <> rubbing soap against clothing.
  4. yin taku a wasan ƙwado ko caca.

Noun

f

  1. matacciyar fata da take barin jiki.
    Maciji ya yi saɓa.

Glosbe's example sentences of saɓa

  1. saɓa. <> against, conflict between, conflict with, conflict, conflicts, contradictions between, contrary, contrast, differences, odds, robbing, run contrary, runs contrary, to, unlawful, unscriptural.
    1. Mu yi ƙoƙari mu cika alkawarin mu, ko da yana da wuya, sai dai idan muka fahimci cewa ya saɓa wa Nassosi. <> Unless we come to the realization that we have made an unscriptural promise, we should do all we can to fulfill our word, even if it is very difficult to do so.
    2. Kalmar Allah ta ba da damar yin zaɓi bisa lamiri a tsakanin Kiristoci idan zaɓin bai saɓa wa dokar da ke cikin Littafi Mai Tsarki ba. <> Where no Bible law is at stake, God’s Word allows for differences of conscience among Christians.
    3. Muka tambaye su: “Me ya sa Kiristoci suke bauta wa Yesu da Maryamu da gicciye da dai sauran gumaka duk da cewa hakan ya saɓa wa Dokoki Goma?” <> We asked them: “How can Christians worship Jesus, the cross, Mary, and other idols when that is against the Ten Commandments?”
    4. Amma, da na fara karanta Littafi Mai Tsarki cikin natsuwa, sai na ga cewa koyarwar addinin Mormon sun saɓa wa wasu abubuwan da Littafi Mai Tsarki ya faɗa. <> But when I began to read the Bible in earnest, I noticed contradictions between Mormon teachings and statements in the Bible.
    5. Kamar yadda manzo Bulus ya annabta ta wurin hurewar Allah, mutane da yawa cikin waɗannan “kwanaki na ƙarshe” suna da halin ibada amma suna saɓa wa ikonta. <> As foretold by the apostle Paul under divine inspiration, many people in these “last days” have a form of godly devotion but prove false to its power.
    6. Kuma muna bukatar mu guji lalata, mu yi kokawa da ayyuka na jiki, kuma mu guje wa son abin duniya, ussan ilimi na duniya, da kuma al’adu da suka saɓa wa Nassosi. <> We also need to reject immorality, combat the works of the flesh, and avoid materialism, worldly philosophies, and unscriptural traditions.
    7. Ta yaya ruhun duniya ya saɓa wa koyarwar Yesu, kuma waɗanne tambayoyi za mu yi wa kanmu? <> How does the spirit of the world run contrary to Jesus’ teaching, and what questions should we ask ourselves?
    8. A yanayi da yawa sa’ad da bukatar ƙasa ta saɓa wa ta jama’a bukata ta ƙasa take yin nasara. <> In one case after another, when national interests conflict with global interests, national interests win out.
    9. Amma, idan ba su saɓa wa dokokin Allah ba, mace mai yin biyayya za ta kasance a shirye ta bi shawarwarin da mijinta ya yanke. <> Yet, if his decisions do not conflict with God’s laws, a submissive wife is willing to yield.
    10. Shaidu da suke ƙarƙashin mulkin kama karya sun fahimci cewa abin da Gwamnati take bukata a wasu lokatai sun saɓa wa imaninsu. <> Witnesses living under totalitarian dictatorships have found that the demands of the State and the requirements of their faith are sometimes at odds.
    11. (Romawa 13:1-7) Idan bukata ta mutane ta saɓa wa nufin Allah, suna tsayin daka: “Dole sai mu fi biyayya ga Allah da mutane.” <> (Romans 13:1-7) If there is a conflict between a human demand and the divine will, they take the stand: “We must obey God as ruler rather than men.”
    12. (1 Tassalunikawa 5:19) Hakika, ayyuka da halaye da suka saɓa da ƙa’idodin ibada sa iya hana ayyukan ruhu mai-tsarkin dominmu. <> (1 Thessalonians 5:19) Yes, actions and attitudes that run contrary to godly principles could impede the activity of the holy spirit in our behalf.
    13. Ko da yake mutane sun amince da muhimmancin kalmomin Yesu, bayanan da suka ba da game da mana’arsu sun saɓa wa juna. <> Though people agree about the importance of Jesus’ words, they disagree about the meaning.
    14. Ƙari ga haka, yin hakan zai saɓa wa ruhu mai tsarki da ke taimaka wa mutanen Allah su kasance da salama da kuma haɗin kai.—Karanta Romawa 16:17, 18. <> They would be working against the holy spirit, which helps God’s people to have peace and unity.—Read Romans 16:17, 18.
    15. Waɗanne munanan ayyuka da suka shafi haikalin a Urushalima ya yi daidai da saɓa wa haikali? <> What wrong practices involving the temple in Jerusalem might have been much the same as robbing the temple?
    16. Keɓe kai da mutumin ya yi zai kasance tabbatacce ne kawai ga Jehobah idan ya riga ya daina wannan halin da ya saɓa wa nassi. <> Such an individual would have been in a position to make a valid dedication to Jehovah only if the unscriptural conduct had been discontinued.
    17. 12 Muna manne wa Jehobah sa’ad da muka yi biyayya ga Kalmarsa, wadda ta saɓa wa hikimar ’yan Adam. <> 12 We cling to Jehovah when we heed his Word, which often runs contrary to human wisdom.
    18. 18:25) Kuma, barin maƙiyansa su halaka bayinsa gabaki ɗaya zai saɓa wa Kalmar Allah, wadda ta ce: “Ubangiji ba za ya yar da jama’atasa ba sabili da sunansa mai-girma.” <> 18:25) Moreover, permitting the extermination of his servants as a body would be contrary to God’s Word: “Jehovah will not desert his people for the sake of his great name.”
    19. 3:6) Wannan ya saɓa wa yadda Yesu ya bi da gwaje-gwaje uku da ya fuskanta! <> 3:6) What a contrast to Jesus’ reaction to the three temptations!
    20. Shaidun Jehobah sun gaskata cewa yin amfani da irin waɗannan abubuwan sun saɓa wa umurnin da ke cikin Littafi Mai Tsarki na “ku guje ma bautar gumaka.” <> Jehovah’s Witnesses believe that the use of such items conflicts with the Bible’s command to “flee from idolatry.”
    21. Shaidun Jehobah suna son su nuna cewa hanin da aka yi ga aikinsu na wa’azi a Moscow ya saɓa wa dokar. Saboda haka, a watan Disamba 2004, lauyoyinmu sun kai ƙara a Kotun Turai na ’Yancin ’Yan Adam. <> To establish that the Moscow ban was unlawful, in December 2004 our lawyers sought relief from the European Court of Human Rights.

Related

  • saɓar da / saɓad da.