Toggle menu
24K
663
183
158.1K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Quran/6/IRIB Hausa Tafsir

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations

Suratul An'am, Aya Ta 1-3 (Kashi Na 187)

Bismillahir Rahmanir Rahim. Assalamu alaikum masu saurare. Barkan mu da sake saduwa a shirin Hannunka mai Sanda shirin da yake kawo muku bayani na wasu ayoyin Alkurani mai girma. A shirin da ya gabata mun kawo karshen tafsirin Surar Maaidah, a yau zama fara shirimma da surar An'ami. Surar An'ami tana da ayoyi 165 kuma a Makka ta sauka. Daga cikin abubuwan da take koyarwa akwai kira zuwa ga tauhidi wato kadaita Allah. Da kuma kokarin kawar da shirka kuma mafi yawan ayoyinta suna bayani ne a kan camfe-camfe da surkullen da masu bauta wa gumaka suke yi. Har'ila yau ayoyin surar An'amma suna maida martani a kan wadannan akidu na bata ta hanyar bayyana hujjoji na hankali. An sayawa surar suna "Suratul An'am" wato "Dabbobin Ni'ima" saboda an yi bayanin hukunce-hukuncen da suka shafi cin naman dabbobi. Da fatar masu saurare zamu kasance tare da mu.

To madalla. Yanzu bari mu fara shirimmu da sauraron aya ta farko (1) na surar An'aam kamar haka:

الْحَمْدُ لِلّهِ الَّذِي خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضَ وَجَعَلَ الظُّلُمَاتِ وَالنُّورَ ثُمَّ الَّذِينَ كَفَرُواْ بِرَبِّهِم يَعْدِلُونَ{1}

"Dukkan yabo ya tabbata ga Allah wanda Ya halicci sammai da kasa, Ya kuma sanya duffai da haske, sannan kuma wadanda suka kãfirce suna daidaita wani da Ubangijinsu."

Wannan ayar ta fara da bayani kan Ubangiji tana cewa: Allah shi ne wanda ya halicci sammai da kasa kuma shi ke da iko da karfi wadanda basa da iyaka. Shi ne ya hallici rana da wata da taurari masu haske. Rana tana ba ku haske da dumi, kuma saboda jujjuyawarta dare zai biyo yini, domin ku sami hutu. Alkurani yana tambayar mushrikai: shin gumakanku da kuke bauta wa suna iya halittar wadannan? Kamar yadda kowa ya sani dai gumaka ba zasu iya halitta ba. Saboda haka Allah mabuwayin sarki shi ne ya halicce su, saboda haka kuma ku bauta masa shi kadai kada ku sanya masa abokin tarayya, ku kuma yi masa godiya kan ya yi muku wannan tsari mai amfani a rayuwarku. A wani gefe kuma wannan ayar tana maida martani kan akidar yan maddiya masu ganin cewa babu wani abinda yake da samuwa idan ba abubuwa na zahiri ba, kuma suna ganin babu wani mahallici. Har'ila yau ayar tana maida martani ga masu akidar bauta wa tagwayen iyayen giji kamar mabiya addinin Zartosh, masu imanin da cewa haske da duhu wadanda ake iko dasu daga asali guda biyu. Abin lura a nan shi ne a duk inda Alkurani ya ambaci haske yana ambaton shi ne da sigar mufradi wato daya, shi kuma duhu yana zuwa ne da sigar jam'i. Saboda hanyar gaskiya - wacce ita ce hasken - daya ta ce, amma hanyoyin bata da yawa suke, kuma sune alkur'ani yake kwatantansu da duhu. Ta wata fuska kuma haske alam ce ta hadin kai, a yayinda duhu kuma yake zama alama ta rarraba. Wannan aya ta kunshi darusa kamar haka: 1-Allah shi ne mahaliccin talikai kuma shi ne yake samar da hanyar bunkasar su da kaiwarsu ga kamala ko kuma cika a dukkan bangarorin halittarsu, wato samuwar abubuwa tun farko da kuma wanzuwarsu duk suna hannun sa ne. 2-Sanya wa Allah abokin tarayya wani nau'i ne na kafirci, saboda idan mutum ya dauki wani abu a matsayin abin bauta tare da Allah wato ya yi inkarin ikon da Allah yake da shi na gudanar da dukkan halittu shi kadai ne.

Sai mu saurari aya ta 2 daga cikin surar ra an'aam kamar haka:

هُوَ الَّذِي خَلَقَكُم مِّن طِينٍ ثُمَّ قَضَى أَجَلاً وَأَجَلٌ مُّسمًّى عِندَهُ ثُمَّ أَنتُمْ تَمْتَرُونَ{2}

"Shi ne wanda Ya halicce ku daga tabo sannan kuma Ya yanka ajali, da kuma wani ajali ambatacce a wurinsa, sannan duk da haka kuwa kuna jayyaya."

Ayar da gabata ta yi bayani kan ikon Allah dangane da halittar sammai da kasa, ita kuma wannan ayar tana bayyana cewa an halicci dan Adam ne daga kasa wacce bata da rai, tana cewa: 'Rayuwarku da mutuwarku a hannun Allah suke, to ta yaya ne zaku yi shakkar samuwar Allah?' wannan aya ta nuna cewa rayuwar mutum tana da ajali biyu; ajali ayyananne wanda Allah kadai ya san shi, da kuma wani ajalin wanda shima ba'a bayyana ba, amma yana da dangantaka da yanayin rayuwar mutum da abubuwan da suke aukuwa a cikinta. Allah ya sanya wa kowane mutum iya karfin da zai iya samu a rayuwa idan kuma wannan karfi ya kare sai rayuwar tasa ma ta kawo karshe, tamkar dai fitila, idan makamacinta ya kare to dole ne ta mutu. Amma a wani lokaci mutum yana iya kamuwa da wata cuta ko wani hadari ya same shi kuma hakan sai ya zama karshen rayuwarsa kafin wancan ayyanannen lokacin da Allah ya ajiye masa. Kamar fitilar da take da mai amma idan iska ta kada sai ta kashe fitilar. Dukkan ajali biyun da wannan aya ta yi bayani, da ayyanannen da wanda ba ayyanannen ba duk dai suna karkashin ikon Allah.

Saboda haka hadisai suna bayyana muhimmancin kiyaye tsabta wanda hakan yana kawo tsawon rai, sannan kuma suna bayyana wasu abubuwan masu kara tsawon rai kamar sadaka da sada zumunci da biyayya ga iyaye. Muna iya koyon wadannan darusa daga wannan aya: 1-Ba da son rammu ne muka zo duniya ba, ballantana muce da radin kanmu zamu dauki rayukanmu. Farkon rayuwarmu da karshensa, duk ba a hannunmu suke ba, to da yake yanzu muna da samuwa ta yaya ne zamu yi shakkar mafarimmu (wato halittar Allah) da kuma makomarmu wato ranar alkiyama? 2-Wannan duniya da muke raye a cikinta tana tafiya ne bisa tabbataccen tsari kuma karshen kowane samammen abu zai zo a lokaci ayyananne, kuma Allah shi ne ya mahalicci wannan tsari kuma yana da cikakken saninsa.

Sai mu saurari aya ta 3:

وَهُوَ اللّهُ فِي السَّمَاوَاتِ وَفِي الأَرْضِ يَعْلَمُ سِرَّكُمْ وَجَهرَكُمْ وَيَعْلَمُ مَا تَكْسِبُونَ{3}

"Kuma Shĩ ne Allah a sammai da kasa, Ya san abin da ku ke boyewa da kuma abin da kuke bayyanawa, kuma Yanã sane da abin da kuke aikatawa."

Bayan bayani a kan kudurar Ubangiji wajen halittar sammai da kasa, a cikin ayoyin da suka gabata, wannan ayar tana ishara da cewa: Ai Allah daya ne mai iko da dukkan abinda yake cikin sammai da kasa kuma komai a hannunsa yake, sabanin akidar masu daukar cewa kowane abu yana da ubangijin da yake iko da shi. Har'ila yau wannan ayar tana nuna cewa sanin Allah ba shi da iyaka, wato shi ne mahallici kuma shi ne masanin dukkanin abinda kuke ciki, saboda haka kada ku zaci bai san abinda kuke aikatawa ba. Wannan aya tana koyar da mu darusa kamar haka: 1-Idan mun yi imani da cewa Allah masani ne a kan komai, wannan imani zai hana mu aikata munanan ayyuka, zai kuma ba mu karfin guiwar aikata kyawawan ayyuka. 2-Abinda yake bayyane da abin da yake boye a garemu na sammai da kasa, a wurin Allah a bayyane suke babu abinda ya boyu gare shi.

      • To a nan zamu dakata a shirin na mu na Hannunka mai Sanda sai kuma shiri na gaba da yardar Allah zaku ji bayanai akan wasun ayoyin na surar An'am. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi taala wa barakatuhu.

Suratul An'am, Aya Ta 4-9 (Kashi Na 188)

Bismillahir Rahmanir Rahim. Assalamu alaikum jamaa masu saurare. Barkan mu da sake saduwa a shirin Hannunka mai Sanda shirin da yake kawo muku sharhi na ayoyin Alkurani mai girma. Zamu ci gaba da bayani ne a cikin Surar An’am, ta fatar Allah ya bamu hasken Alkur’ani mai girma ya kuma taimaka mana wajen aiki da koyarwarsa.

To madalla. Da farko bari mu saurari aya ta 4 da ta 5:

وَمَا تَأْتِيهِم مِّنْ آيَةٍ مِّنْ آيَاتِ رَبِّهِمْ إِلاَّ كَانُواْ عَنْهَا مُعْرِضِينَ{4} فَقَدْ كَذَّبُواْ بِالْحَقِّ لَمَّا جَاءهُمْ فَسَوْفَ يَأْتِيهِمْ أَنبَاء مَا كَانُواْ بِهِ يَسْتَهْزِئُونَ{5}

"Babu wata ãyã daga ayoyin Ubangijinsu da zã ta zo musu sai sun zamanto suna mãsu bijirẽwa gare ta." "Sannan hakika sun karyata gaskiya lõkacin da ta zo musu; to ba da dadewa ba lãbãrin abin da suka zamanto sunã yi masa izgili zai zo musu."

A shirin da ya gabata mun ji wasu sifofin Allah madaukakin sarki kamar iko da sani, mun jin cewa shui ne ya halicci sammai da kasa, kuma mun ji yanda ayoyin suka bayyana rayuwar dan Adam a mnatsayin takaitacce mai karewa. Wannan aya kuma tana cewa wasu mutane kam duk da yawan alamomi ko ayoyi da suke gani a cikin halittu, hatta ma a halittarsu, amma basa daukar darasi su yi imani da Allah, domin basu son karbar gaskiya. Suna kama da mutumin da yake cikin barci mai zurfi baya fahimtar abinda yake faruwa a kewayensa kuma ko da ka kira shi ko ka taba shi ba zai farka ba. Alhali mutumin da yake barci na hakika idan an kira shi ko an girgiza shi zai farka. Sai dai fa wannan yanayi na masu karyatawa ba zai dawama ba, saboda wata rana zata zo da sakamakon mugun tunani da aiki da irin wadannan mutane suke yi zai riske su kuma zasu farka daga barcin karya da suke yi su gane kuskurensu amma lokacin gyara ya riga ya kubuce musu. Wannan aya tana koyar da darusa kamar haka: 1-Mutabne masu jayayya wadanda basu neman gaskiya, kawo dalili ko aya ba zai gamsar da su ba domin kuwa ba zasu saurare dalalai na hankali ba. 2-Kafirai da masu jayayya ta banza basu dogara kan wata hujja ta hankali ba, abinda kawai suke yi shi ne izgili wa muminai da akidarsu da yi musu wulakanci.

Sai kuma mu saurari aya ta 6 ta wannan sura ta An’am:

أَلَمْ يَرَوْاْ كَمْ أَهْلَكْنَا مِن قَبْلِهِم مِّن قَرْنٍ مَّكَّنَّاهُمْ فِي الأَرْضِ مَا لَمْ نُمَكِّن لَّكُمْ وَأَرْسَلْنَا السَّمَاء عَلَيْهِم مِّدْرَاراً وَجَعَلْنَا الأَنْهَارَ تَجْرِي مِن تَحْتِهِمْ فَأَهْلَكْنَاهُم بِذُنُوبِهِمْ وَأَنْشَأْنَا مِن بَعْدِهِمْ قَرْناً آخَرِينَ{6}

"Shin ba su sani ba ne alumma nawa ne muka hallaka daga wadanda suka zo a gabaninsu? Wadanda kuwa muka kafa a bayan kasa suka yi karfi irin wanda ba mu yi muku ba, muka kuma kwarar musu ruwan sama isasshe, Muka kuma sanya musu koramu sunã ta gudãna ta karkashinsu, (daga karshe) sai Muka hallakã su sabõda laifukansu, Muka kuma halicci wadansu alumma a bayansu?"

Wannan aya tana magana ne da masu taurin kai wadanda basu karbar gaskiya. Tana ce da su: Shin baku ji tarihin wadanda suka gabace ku ba ne? Shin baku ji labarin alummomi da gaabce ku ba, ko kuna zaton kun fi su karfi ne ko kun fi su dukiya, ta yadda zaku fi karfin ikon Allah? Alal hakika wasu alummomin daga wadancan sun ma fi ku karfi da dukiya da mulki amma da yake sun saba wajen yin amfani da niimomin da Allah ya basu a mamaimakon su aikata alheri da niimomin, sai Allh ya hallakasu ya kawo wasu a makwafinsu. Kamar yanda Allah zai yi wa mutane hisabi da a lahira da sakamakon mai kyau ko mummuna, haka ma alummomin za a yi musu hisabi, kuma suna da makoma wacce zata dogara kan ayyukan da akasarin jamaarta suke aikatawa, kuma kowace alumma ba zata iya retse wa wannan makoma ba. Darusan da zamu koya daga wannan aya: 1-Karanta tarihi da daukan darasi daga makomar alummomi da suka shude, daya daga cikin han yoyin da Alkurani yake koyar da mutane da yi musu tarbiya ne. 2-Halayen mutane da ayyukan da suke aikata suna tasiri kan sauye-sauyen da ake samu a tarihi, shi kuma hakala alummomi saboda sabo kaidace da Allah a sanya mai iko kan abubuwan da suke faruwa a tarihi, kuma irin wadannan kaidoji ana kiransu Sunnar Allah. 3-Yawan dukiya da abinda aka mallaka ta zahiri ba suke tabbatar da jin dadi da saada domin kuwa sau da yawa sukan zamo musabbabin gafala da jiji da kai da kuma aikata zalunci wadanda kuma suke janyo halakar mutane ko alummomi.

Sai mu saurari aya ta 7:

وَلَوْ نَزَّلْنَا عَلَيْكَ كِتَاباً فِي قِرْطَاسٍ فَلَمَسُوهُ بِأَيْدِيهِمْ لَقَالَ الَّذِينَ كَفَرُواْ إِنْ هَـذَا إِلاَّ سِحْرٌ مُّبِينٌ{7}

"Da Mun saukar maka da littãfi rubutacce a takarda har suka taba shi da hannayensu, to ba shakka dã wadanda suka kãfirta sun ce: 'Ai wannan ba komai ba ne in ban da sihiri bayyananne."

A hadisai da suke Magana kan tarihi, an ruwaito cewa wasu jamaa na mushrikan Makka sun fadi wa Annabi cewa: ba zasu yi imani da shi ba sai Allah ya sauko masa da maganarsa wato Alkurani a rubuce a takardu kamar yanda aka saukar da Attaura wa Annabi Musa a rubuce a alluna, shi kuma ya daukosu daga duten Turi Sina ya kai wa mutanensa. Alkurani ya ba da amsa yace ai ko an sauko da Alkurani a rubuce kamar yanda mushrikan suka nema, zasu nemi wani dalilin kuma domin sukar abinda Allah ya saukar, zasu ce ai sihiri ne kawai da Annabi ya yi ba mujiza daga Allah ba. Kamar dai yanda wasu mutanen Annabi Musa (a.s.) suka ce allunan Attaura da Allah ya saukar masa sihiri kawai ba wahayi ba. Sai mu saurari aya ta 8 da ta 9:

وَقَالُواْ لَوْلا أُنزِلَ عَلَيْهِ مَلَكٌ وَلَوْ أَنزَلْنَا مَلَكاً لَّقُضِيَ الأمْرُ ثُمَّ لاَ يُنظَرُونَ{8} وَلَوْ جَعَلْنَاهُ مَلَكاً لَّجَعَلْنَاهُ رَجُلاً وَلَلَبَسْنَا عَلَيْهِم مَّا يَلْبِسُونَ{9}

"Suka kuma ce: 'Me ya sa ba a saukar masa da malã'ika ba?' Da kuwa Mun saukar da malã'ika, to ai da ta faru ta kare (watau da an hallaka su), sannan kuma ba zã a saurara musu ba." "Da Mun yi wo shi malã'ika ne to da kuwa Mun mayar da shi mutum, kuma dã lallai Mun sanya musu abin da zai dada rudar da su (game da shi)."

Daga cikin hujjoijin kauce wa gaskiya da kafirai suke kawo a matsayin sharadi kafin su yi imani, akwai batun cewa sai sun ga malaika ko kuma annabin da Allah zai aiko ya kasance malaika. A wadannan ayoyi Alkurani yana mayar musu da martini cewa idan ma malaika ne Allah zai aiko ai zai sanya shi mutum ne kuma idan an yi haka, gane cewa shi malaika ne zai yi muku wahala kuma zaku ce ai mutum kamar mu. Idan ma kun gane cewa malaika ne kuma ya zama dole ku yi imani das hi, Allah ya san cewa saboda yawan jayayyarku ba za ku yi imanin ba, kuma idan haka ya faru, to ba makawa azaba zata sauko muku kuma zaku halaka, saboda haka rashin kawo malaika rahama ce ta Allah a gare ku. Wadannan ayoyi suna bayyanawa a sarari cewa girman kai da halin jayayya da wasu mutane suke das u ba zasu kyale su su yi iamni da wani mutum kamarsu a matsayin annabi ba. Wadannan mutane suka tsammanin cewa dole ne annabi ya zo daga malaika ko wani jinsin halitta da suka fi mutane, amma bas u sani bas u annabawa suna kawo wahayi kuma suna zama abin koyi da mutane, kuma ba zai yiwu malaiku su zama abin koyi ga mutane ba saboda halitar dan Adam da bukatunsa da Allah ya halitta masa kamar ci da sha da aure da sauransu sun bambantasu da halittar malaiku. Wadannann ayoyi suna koya mana cewa: 1-Idan mutum yana shirya ya kartbi gaskiya bayani kadan da mujiza zasu gamsar das hi amma idan mutum ya sa taurin kai da jayayya ko da malaika zai sauka daga sama yana ganinsa, sai ya nemi hanyar kaucewa gaskiya. 2-Wajen kiran jamaa da koyar da abin da wahayi ya kawo annabawa suna bin hanyar jinkirtawa da bada lokaci, kuma idan da za a kawo mujiza nan take, alumma zata halaka domin kuwa mutane suna da saurin karyatawa.

      • To a nan zamu dakata a shirin Hannunka mai Sanda sai kuma shiri na gaba da yardar Allah zaku ji bayanai akan wasun ayoyin na surar An’am. Tare da fatar Allah Madaukakin Sarki ya haskaka zukatanmu da hasken Alkurani. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi taaala wa barakatuhu.

Suratul An'am, Aya Ta 10-14 (Kashi Na 189)

Bismillahir Rahmanir Rahim. Assalamu alaikum jamaa masu saurare. Barkan mu da sake saduwa a shirin Hannunka mai Sanda shirin da yake kawo muku sharhi na ayoyin Alkurani mai girma. Zamu ci gaba da bayani ne a cikin Surar An’am, ta fatar Allah ya bamu hasken Alkur’ani mai girma ya kuma taimaka mana wajen aiki da koyarwarsa. Sharhin namu zai fara ne daga aya ta 10 zuwa ta 14

To madalla. Da farko bari mu saurari aya 10:

وَلَقَدِ اسْتُهْزِئَ بِرُسُلٍ مِّن قَبْلِكَ فَحَاقَ بِالَّذِينَ سَخِرُواْ مِنْهُم مَّا كَانُواْ بِهِ يَسْتَهْزِئُونَ{10}

"Ba shakka an yi wa wasu manzanni izgili gabaninka, sai abin da suka kasance suna yi wa izgilin ya saukar musu." A shirin da ya gabata mun ce mutanen da suke da yawan jayayya domin kin gaskiya kada su karbi su yi imani sukan ce me yasa wannan wani malaika ba zai sauko domin ya bad a shaidar gaskiyar annabcin wannan annabi ba kluma mu da kanmu mu ganshi? Wannan aya tana amsa wannan tambaya da cewa: Ya kai Annabi, a duk tsawon tarihi an yi ta samun mutane irin wadannan wadanda basu karbar gaskiya, suna ma yin izgili da ita; annabawan da suka gabata sun yi fama da irin wadannnan mutane kuma kai ma ka yi hakuri da wadannan domin Allah ne zai amsa musu wadannan tambayoyi na izgili, kuma a ranar lahira zasu gane cewa abinda suek yi wa izgili a duniya gaskiya ne. Wannan aya tana koyar da mu darusa kamar haka: 1-Masu sabawa gaskiya basu da wata magana ta hankali da zasu fada, hanyarsu it ace izgili da wulakanta gaskiya da mabiyanta. 2-Mu nisanci izgili da wasu mutane domin wannan dabi’a ce ta mushirikai da kafirai.

Sai mu saurari aya ta 11:

قُلْ سِيرُواْ فِي الأَرْضِ ثُمَّ انظُرُواْ كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ الْمُكَذِّبِينَ{11}

"Ka ce: 'Ku yi tafiya mana a bayan kasa sannan ku ga yadda karshen mãsu karyatãwa ya kasance."

Saboda farkar da mutanen da suka shiga barcin gafala kuma basu ganin gaskiya, Alkurani yana kiran su da su yi dubi a cikin tarihin wadanda suka gabata su san sakamakon day a same su domin su farka daga barcinsu. Daya daga cikin muhimman karanta tarihin magabata shi ne ziyartar wuraren da suke da alamun tsofaffin dauloli wadanda suka yi zamani a da, kuma a wannan zamani ana kiran wannan ziyara yawon bude ido ko yawon shakatawa. Sai dai ganin alamun tsofaffin dauloli ba zai wadatar ba sai mutum ya yi tunani da daukar darasi kan yan da suka rayu day an da karshe ya zo. Darusa: 1-Addinin Musulunci yana horo da yin tafiya zuwa wuraren tarihi kuma hakan dama ce ta sanin abinda ya shude da zimmar mutane su dauki hanya ta kwarai a rayuwa. 2-Mutane da dabbobi duka suna kallo kuma suna ganin abubuwa amma abinda yake da muhgimmanci shi ne kula da daukar darasi daga abinda mutum ytake gani.

Sai mu saurari aya ta 12 da ta 13:

قُل لِّمَن مَّا فِي السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ قُل لِلّهِ كَتَبَ عَلَى نَفْسِهِ الرَّحْمَةَ لَيَجْمَعَنَّكُمْ إِلَى يَوْمِ الْقِيَامَةِ لاَ رَيْبَ فِيهِ الَّذِينَ خَسِرُواْ أَنفُسَهُمْ فَهُمْ لاَ يُؤْمِنُونَ{12} وَلَهُ مَا سَكَنَ فِي اللَّيْلِ وَالنَّهَارِ وَهُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ{13}

"Ka ce: 'Shin abin da yake cikin sammai da kasa na wãne ne?' Ka ce: 'Na Allah ne. Yã dora wa kansa yin rahama. Ba shakka kuma zai tattara ku a rãnar alkiyãma, wannan babu kokwanto a cikinsa. Wadanda suka cuci kansu ba sa ba da gaskiya."

"Duk kuma abin da ya nutsu a mazauninsa a cikin dare ko rana nasa ne; kuma Shi Mai ji ne, Masani."

Wannan aya kuma tana bayanin cewa da akwai alaka tsakanin inda mutum ya fito da inda za shi (wato halitta daga Allah da kuma tashin alkiyama). Ubangijin da ku ma ku ka yarda cewa shi ne ya hallici dukan ababen da suke samammu, lallai shi ne ya halicci talikai bias rahamarsa mai yalwa. Bai bar ku a nan duniya kara zube ba, kuma a ranar alkiyama zai tattaraku ya yi muku hisabi, ko dai ku tafi aljanna ko kuma ku tafi wuta, Allah ya kiayye. Daga karshe ayar tana cewa, mutanen da suka yi watsi da dabi’arsu ta asali mai tsabta wacce take son biyayya ga tauhidi, suka kuma karkace zuwa ga bata da abubuwan da zasu jawo hasarar lahira, ba zasu taba yin imani ba.

Wadannna ayoyi suna koyar da mu darusa kamar haka:

1-Tashin alkiyama yana tabbatar da adalci da hikimar Ubangiji, sannan kuma hikimarsa ta sa ya zama wajibi kada rayuwar dan Adam ta takaita da nan duniya ba, zata ci gaba a wata duniyar ta har abada. 2-Ko da yake bamu ganin Allah kuma ba mu jin maganarsa, shi yana ganinmu kuma yana jin maganar da muke yi.

Sai mu saurari aya ta 14:

قُلْ أَغَيْرَ اللّهِ أَتَّخِذُ وَلِيّاً فَاطِرِ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ وَهُوَ يُطْعِمُ وَلاَ يُطْعَمُ قُلْ إِنِّيَ أُمِرْتُ أَنْ أَكُونَ أَوَّلَ مَنْ أَسْلَمَ وَلاَ تَكُونَنَّ مِنَ الْمُشْرِكَينَ{14}

"Ka ce: 'Yanzu wanin Allah zan rika Ubangiji majibinci, (alhãli Allah ne) ya halicci sammai da kasa, Shi ne kuma mai ciyarwa, ba a kuwa ciyar da Shi?" Fada musu cewa: 'Hakika ni an umarce ni da in zama farkon wanda ya ba da gaskiya, kuma (an ce da ni): Lalle kada ka zamanto daga mushrikai."

Wasu mushirikan Makka suna cewa abinda ya sa Annabi yake kira zuwa ga Allah da kuma daawar da yake yi cewa Allah ne ya aiko shi, shi ne yana cikin talauci, saboda haka suka ce ya bar wannan kira zuwa ga tauhidi da addinin Allah su kuma zasu bashi dukiyarsu shi ma ya zama mai arziki. Allah y ace da manzonsa cewa ya fada musu duk abinda suke das hi hatta abincin da suke ci ai daga Allah suka same shi, saboda basu da komai balle Annabi ya bar Ubangijinsa ya bi su. Annabi y ace: Ni ina karkashin njibintar Ubangijinn da ikon sama da kasa duk a hannunsa yake kuma b azan taba yin shakka dangane das hi ba, ina kuma biyayya ga dokokinsa. Darusa: 1-A duk fadin sama da kasa ba bu wata mafaka idan ba Allah ba kuma daga arzikinsa ne suke ci. 2-Addinin Annabinmu shi ne Musulunci, kuma karbar Musulunci yana wajabta mika wuya ga Allah da bin dokokinsa.

      • To a nan zamu dakata a shirin Hannunka mai Sanda sai kuma shiri na gaba da yardar Allah zaku ji bayanai akan wasun ayoyin na surar An’am. Tare da fatar Allah Madaukakin Sarki ya haskaak zukatanmu da hasken Alkurani. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi taaala wa barakatuhu.

Suratul An'am, Aya Ta 15-19 (Kashi Na 190)

Bismillahir Rahmanir Rahim. Assalamu alaikum jamaa masu saurare. Barkan mu da sake saduwa a shirin Hannunka mai Sanda shirin da yake kawo muku sharhi na ayoyin Alkurani mai girma. Zamu ci gaba da bayani ne a cikin Surar An’am, ta fatar Allah ya bamu hasken Alkur’ani mai girma ya kuma taimaka mana wajen aiki da koyarwarsa. Sharhin namu zai fara ne daga aya ta 15 zuwa aya ta 19

To madalla. Da farko bari mu saurari aya ta 15 da ta 16:

قُلْ إِنِّيَ أَخَافُ إِنْ عَصَيْتُ رَبِّي عَذَابَ يَوْمٍ عَظِيمٍ{15} مَّن يُصْرَفْ عَنْهُ يَوْمَئِذٍ فَقَدْ رَحِمَهُ وَذَلِكَ الْفَوْزُ الْمُبِينُ{16}

"Kace: 'Hakika nĩ inã jin tsõron azãbar rana mai girma idan na sabi Ubangijina."

"Wanda duk kuwa aka tunkude wa azaba a wannan rãnar to ba shakka (Allah) ya ji kan sa. Wannan kuwa shi ne rabo mabayyani."

Shawarar da mushirikan Makka suka bauin wa Annabi cewa idan ya bar kira zuwa ga hanyar Allah zasu azurta shi, Allah yana fdada wa annabinsa a wannan aya cewa: Ka ce mjusu kun yi mini alkawarin duniya ama ni ina tsoron hisabin lahira domnin nkujwa duk wani sakaci da na yi wajen bayyana sakonn Allah ko boye wani abu daga ciki ko canya shi yana da azaba mai tsanani wanda kuma b azan iya jure masa ba. Sai dai a fili yake cewa Annabi bai taba saba wa Allah ba kuma ba taba saba masa ba, amma wannan bayani yana nuna wa Musulmi cewa dole su nisanci kwadaitarwar da wasu zasu yi musu da alkawuran biya musu wasu bukatu, su tuna da lahira su ji tsoron azabarta, kuma wannan tsoro ya zame musu linzami. Wanna n aya tana koya mana cewa: 1-A wajen Allah dokokin horo ga masu aikata laifi daya suke ga dukan mutane, kum ako da annabi ne ya yui laifi Allah zai hukunta shi, sai dai kamar yanda muka ji Annabi baya sabon Allah. 2-Tsoron azabar Allah tsoro ne day a dace sabanin tsoron zaluncin azaluman shugabanni da zauran azzalumai. 3-Kowa yana fuskantar hadari, rahamar Allah ce kawai take nisantar da mutum daga aiukata sabo kokuma bayan aikata sabon take bude wa mutum kofar tuba da samun gafara.

Sai mu saurari aya ta 17 da ta 18:

وَإِن يَمْسَسْكَ اللّهُ بِضُرٍّ فَلاَ كَاشِفَ لَهُ إِلاَّ هُوَ وَإِن يَمْسَسْكَ بِخَيْرٍ فَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدُيرٌ{17} وَهُوَ الْقَاهِرُ فَوْقَ عِبَادِهِ وَهُوَ الْحَكِيمُ الْخَبِيرُ{18}

"Idan kuma Allah ya dora maka wani bala'ii to ba mai yaye shi sai Shi, idan kuma ya gana ka da alhẽri to shĩ mai iko ne a bisa kõmai." "Kuma Shĩ ne mai iko a kan bayinsa, kuma Shi gwani ne, masani."

Ayoyin da suka gabata sun bayyana amsa a yanke kan alkawuran bad a abin duniya da mushrikai suka yi wa Annabi, wadanmnan ayoyi kuma suna cewa: Ya kai Annabi ka ce das u komai yana hannun Allah, babu abinda zai faru ko mai dadi ko mai daci idan bad a izininsa ba, kuma idan ya so ya yi wa wani azaba ko kuma sauki da rahama babu wanda zai iya hana wa. Saboda haka alkawuranku bas u da wata kima dom in kuwa idan Allah bai so ba babu sauki d azan samu, kamar haka nan idan ku ka yi mini barazana babu abin da zai same ni sai idan Allah ya so. Wadannan ayoyi suna koya mana: 1-Dukan fata ko tsoro dole ne su kasance daga Allah saboda dukkan alamura daga gareshi suke. 2-Kada mu ji tsoron kowa domin ba wanda yake da iko; mu ji tsoron Allah shi kadai domin ikonsa yana sama da ikon wanda ba shi ba. 3-Karfi yana da kima ne a lokacin da aka gwama shi da hikima. A wadannan ayoyi, an yi bayanin karfin Allah da ikonsa ne tare da iliminsa da hikimarsa.

Sai mu saurari aya ta 19:

قُلْ أَيُّ شَيْءٍ أَكْبَرُ شَهَادةً قُلِ اللّهِ شَهِيدٌ بِيْنِي وَبَيْنَكُمْ وَأُوحِيَ إِلَيَّ هَذَا الْقُرْآنُ لأُنذِرَكُم بِهِ وَمَن بَلَغَ أَئِنَّكُمْ لَتَشْهَدُونَ أَنَّ مَعَ اللّهِ آلِهَةً أُخْرَى قُل لاَّ أَشْهَدُ قُلْ إِنَّمَا هُوَ إِلَـهٌ وَاحِدٌ وَإِنَّنِي بَرِيءٌ مِّمَّا تُشْرِكُونَ{19}

"Ka ce (da su): 'Mene ne ya fi girman shaida?' Ka ce: 'Allah ne shaida a tsakãnina da ku. An kuma saukar mini da wannan Alkur'ãni ne dõmin in yi muku gargadi da shi da kuma duk wanda (wannan gargadi) ya riska. Yanzu kuwa ku din nan kwa shaida cewa akwai wasu iyayen giji tãre da Allah?' Ka ce: 'Ni kam ba zan shaida ba.' Ka ce: 'Hakika Shi Abin bautãwa Guda, kumã hakika ni ba ruwa na da abin da kuke yin shirka da shi."

Wasu mushirakan Makka sun je wajen Annabi suka ce ba wanda yake bad a shaidar cewa kana da gaskiya a kiran da ka ke yi, hatta Yahudawa da Nasara da Ahlul Kitabi ne basu yarda da sakon ka ba, ka nuna mana ko da mutum guda mai bada shedar gaskiyar sakonka. Wannan aya tana cewa: A ganinku wane ne mafificin shaida? Akwai shaidar da ta fi shaidar Allah ne wanda ya saukar da Alkurani yana bad a shaidar manzanci na a ciki? Alkuranin da kuma zai yi wu tunanin dan Adam ya samar da lafazinsa ko maanar da ya kunsa ba. A gaba kuma ayar tana Magana kan manufar sakon da Abnnabi ya kawo, tana cewa, ai Annabi bai zo domin ya sami matsayi ko dukiya ba kuma ba ya neman komai daga gare ku, abin da ya kawo shi shi ne ya yi musu gargadi don su bar bautar gumaka, su bauta wa Allah makadaici. Wani abin lura a wanna aya shi ne shelar sakon Musulunci ga duk duniya da kiran illahirin mutane zuwa ga Musulunci, don kada a dauka sakon Annabi ya kebanta da Larabawa ko wani lokaci ko wuri, ko a dauka ya kebanta da wancan zamani. Kamar yanda Imam Ali (a.s.) yak e bayyana maanar maganar da Allah ya fadi: “Sani dai shi Allah makadaici”, inda y ace ‘Idan da akwai wasu alloli da sun aiko da annabawa amma a duk tsawon tarihi dukkan annabawa sun kawo sako ne daga Allah daya.’ Darussa: 1-Alkurani shi ne mafificin shaida kan gaskiyar sakon Annabin Musulunci. 2-sakon Annabion Musulunci na duk duniya ne kuma na har abada ne, ya zo ne sdaboda shiaryar da dukan mutane na dukkan zamuna. 3-Bayan Annabi muminai da salihai ne suke da nauyin isar da sakon Allah, domin kuwa idan ba a isar da sakon Allah ba to ayyukan da Allah ya wajabta wa mutane ba zasu hau kansu ba. 4-Wajibi ne mutum ya sanar da biyayyarsa ga addini da jagora da Allah ya nada, kuma wajibi ne ya sanar da bara’arsa wato ko rashin goyon bayansa da kuma kiyayya ga shirkar da mashrikai suke yi.

      • To a nan zamu dakata a shirin Hannunka mai Sanda sai kuma shiri na gaba da yardar Allah zaku ji bayanai akan wasun ayoyin na surar An’am. Tare da fatar Allah Madaukakin Sarki ya haskaka zukatanmu da hasken Alkurani. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi taaala wa barakatuhu.

Suratul An'am, Aya Ta 20-24 (Kashi Na 191)

Bismillahir Rahmanir Rahim. Assalamu alaikum jamaa masu saurare. Barkan mu da sake saduwa a shirin Hannunka mai Sanda shirin da yake kawo muku sharhi na ayoyin Alkurani mai girma. Zamu ci gaba da bayani ne a cikin Surar An’am, ta fatar Allah ya bamu hasken Alkur’ani mai girma ya kuma taimaka mana wajen aiki da koyarwarsa.

To madalla. Da farko bari mu saurari aya 20:

الَّذِينَ آتَيْنَاهُمُ الْكِتَابَ يَعْرِفُونَهُ كَمَا يَعْرِفُونَ أَبْنَاءهُمُ الَّذِينَ خَسِرُواْ أَنفُسَهُمْ فَهُمْ لاَ يُؤْمِنُونَ{20}

"Wadanda Muka bai wa Littãfi sun san shi kamar yadda suka san 'ya'yansu, amma wadanda suka cuci kansu, sũ kuma bã sa ba da gaskiya."

Wannan aya mai kama da aya ta 146 a surar Baqara tana ishara da wani batu mai muhimmanci wato mabiya addinin Kiristaci da Yahudanci wadanda suka yi zamani da Annabi Muhammadu (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa) sun san shi kamar yan da suka san 'ya'yan da suka haifa, wato kamar yanda mutum ya ke ganin halayensu daga farkon haifuwarsu har girmansu. Attaura da Linjila sun yi bayanin Annabin Muhamadu dan Abdullahi (Ts.) kuma sun bayyana alamominsa kuma malamann Ahlul Kitabi sun san shi a matsayin annabin da Allah ya yi bisharar zuwansa a nan gaba. Karshen ayar yana cewa wadannan mutanen, da yake basu da niyar karbar gaskiya kuma baza su yi imani ba, kada ku yi zaton zasu cutar da Annabi ko addininsa, kansu suke cuta saboda sun hana kansu kaiwa ga kamala ta fuskar shiriya da hasken zuciya. Darusa: 1-Sanin gaskiya kadai baya sa mutum ya karbeta ya kuma bi abinda ta zo da shi; sau da yawa ana samun mutanen da suka san annabi amma saboda taurin kai da jayayya su ki imani da shi. 2-A mahangar Alkurani, ba a dukiya kadai bane ake samun hasara ko cutuwa ba, ai babbar hasara ita ce wacce ruhi yake samu wanda kuma ta ke hana mutum fahimta da samun kamala ta ruhi wanda ake samu ta hanyar wahayi.

Sai mu saurari aya ta 21:

وَمَنْ أَظْلَمُ مِمَّنِ افْتَرَى عَلَى اللّهِ كَذِباً أَوْ كَذَّبَ بِآيَاتِهِ إِنَّهُ لاَ يُفْلِحُ الظَّالِمُونَ{21}

"Ba wanda ya cuci kansa kamar wanda ya kaga wa Allah karya, ko ya karyata ãyõyinsa. Hakika su dai azzalumai bã zã su tsira ba."

Ayoyin da suka gabata sun yi magana kan akidojin bata na kafirai da mushirikai, wannan aya kuma tana bayyana cewa zaluncin da yafi girma shi ne zaluncin da mutum zai yi ta fuskar tunani ko akida, wato ba tare da dalili ba mutum ya sanya wa Allah abokin tarayya ya kuma karyata ayoyin da Allah ya saukar domin shiryar da bil Adama. Ko da yake zakuncin da ake yi ta fuskar zamantakewa yana da matukar muni, amma idan aka sa lura za a ga cewa wani naui na shirka da kuma kafirci shi ne tushen dukkanin zaluncin zamantakewa, kuma shi yake yin shimfida ga wannan zalunci. Idan mutum yana bauta wa Allah shi kadai yana kuma aiki da koyarwar annabawan Allah ba zai take hakkokin wasu ko ya zaluncesu ba, saboda kiyaya hakkokin mutane yana daga cikin manyan umurce-umurcen da addinan Allah suka zo sa su. Daga karshe ayar tana cewa: amma fa kada azzalumai su yi zaton cewa zasu taba samun sakamako mai kyau da irin wannan tunani da kuma aiki da suke yi. Darusa: 1-Shirka da kafirci sune tushen dukkan zaluncin da ake yi, ko zaluncin da mutum yake yi wa kansa, ya hana kansa samun shiriya da hasken ruhi, ko zaluntar alumma ta hanyar rarraba kan jamaa da hana su hadin kai, ko kuma zaluntar annabawa ta hanayar rashin daukar kokarin da suke yi a matsayin abu mai kima. 2-Yin karya da kuma karyata gaskiya suna hana mutum samun tsira da saada a lahira.

Sai mu saurari aya ta 22:

وَيَوْمَ نَحْشُرُهُمْ جَمِيعاً ثُمَّ نَقُولُ لِلَّذِينَ أَشْرَكُواْ أَيْنَ شُرَكَآؤُكُمُ الَّذِينَ كُنتُمْ تَزْعُمُونَ{22}

"Kuma ka tuna ranar da zamu tattara su gabã daya, sannan Mu ce da wadanda suka yi shirka: 'Inã gumakan na ku wadanda kuka kasance kunã riyãwa (cewa zasu cece ku)?"

Mushirikai basu samun tsira da saada a nan duniya, dadin dadawa kuma a lahira ma ba zasu sami mafaka ba domin kuwa karfi da kuma iko da suke dogara da su a nan duniya suke kuma daukar su tamkar alloli abokan tarayya da Allah, su kansu ma suna bukatar taimako a ranar lahira. Darusa: 1-Kada mu dogara kan wasu mutane ko wasu abubuwan da muka san cewa a ranar lahira ba zasu tsinana mana komai ba. 2-Na biyu shirka ba komai ba ce, kuma a ranar alkiyama za a gane cewa shirka fanko ce ba ta kunshi komai ba.

Sai mu saurari aya ta 23 da ta 24:

ثُمَّ لَمْ تَكُن فِتْنَتُهُمْ إِلاَّ أَن قَالُواْ وَاللّهِ رَبِّنَا مَا كُنَّا مُشْرِكِينَ{23} انظُرْ كَيْفَ كَذَبُواْ عَلَى أَنفُسِهِمْ وَضَلَّ عَنْهُم مَّا كَانُواْ يَفْتَرُونَ{24}

"Sannan ba wani hanzari ta ya fito daga sai cewa suka yi: 'Mun rantse da Allah Ubangijinmu mu ba mu kasance mushrikai ba." "Duba ka ga irin yadda suke karyata kansu da kansu, kuma abin da suke kagen (zai cece su) ya bace musu."

Wadannan ayoyi suna bayyana yanda ranar alkiyama ta ke da kuma yanda mushrikai zasu gurafana a gaban kotun Ubangiji. Suna cewa wadanda suka riki abokan tarayya wa Allah wadanda kuma basu iya tsinana komai, zasu farka daga barcin gafala wanda suke yi a duniya kuma zasu gane gaskiya a ranar alkiyama amma basu da mafita, abin da kawai zasu fada shi ne; “Mu mun rabu da abubuwan da muka yi shirka da su kuma mu ma mun yi imani da Allah makadaici kamar yanda kuka yi.” Mushirikan da suka karyata ayoyi da kuma alamu da Allah ya nuna a duniya, karyatawa da batar da suka kasance suna kanta a duniya amma ina amfani wannan ikirari bayan lokaci ya kure? Darusa: 1-A ranar alkiyama neman uzuri da kuma rantse-rantse ba shi da amfani, haka kuma furuci da akida mai kyau ko karbar gaskiya duk basu da amfani. 2-Ka da mu yi aikin da a ranar alkiyama zamu yi nadama saboda munin aikin. 3-Dukkan madogara da mutum ya dauka a duniya, a ranar alkiyama zasu bace baki daya su bar mutum ba tareda mafaka ba.

      • To a nan zamu dakata a shirin Hannunka mai Sanda sai kuma shiri na gaba da yardar Allah zaku ji bayanai akan wasun ayoyin na surar An'am. Da fatar Allah madaukakin sarki ya haskaka mana zukatanmu da hasken Alkurani mai girma Wassalamau alaikmun wa rahmatullahi taala wa barakatuhu.

Suratul An'am, Aya Ta 25-28 (Kashi Na 192)

Assalamu alaikum jama'a masu saurare. Barkan mu da sake saduwa a shirin Hannunka mai Sanda shirin da yake kawo muku sharhi na ayoyin Alkurani mai girma. A yau sharhin namu zai fara ne daga aya 25 zuwa aya ta 28 ta Surar An'am

To madalla. Da farko bari mu saurari aya ta 25 din da take cewa:

وَمِنْهُم مَّن يَسْتَمِعُ إِلَيْكَ وَجَعَلْنَا عَلَى قُلُوبِهِمْ أَكِنَّةً أَن يَفْقَهُوهُ وَفِي آذَانِهِمْ وَقْراً وَإِن يَرَوْاْ كُلَّ آيَةٍ لاَّ يُؤْمِنُواْ بِهَا حَتَّى إِذَا جَآؤُوكَ يُجَادِلُونَكَ يَقُولُ الَّذِينَ كَفَرُواْ إِنْ هَذَا إِلاَّ أَسَاطِيرُ الأَوَّلِينَ{25}

"Kuma daga cikinsu akwai wadanda suke saurãron ka, Muka kuma sanya marufi a zukãtansu don kada su fahimcẽ shi, a kunnuwansu kuma (Mun sanya) kurumta. Idan kuma da zasu ga kõwace irin ãyã to bã zã su ba da gaskiya da ita ba; har ma idan sun zo maka sunã jãyayya da kai sai wadanda suka kãfirce su rika cẽwa: 'Ai wannan ba komai ba ne sai tãtsũniyõyin mutãnen da."

Wannan aya tana nuni ne da irin yanayi na taurin kai na wasu daga cikin mutane wadanda suka tsaya kyam kan karkatattun tunani da akidojinsu na bata sannan kuma ba a shirye suke su amince da akidoji na gaskiya sakamakon irin taurin kan da suke da shi. Wato a takaice ba ma kawai ba a shirye suke su saurari maganar gaskiya ba ne, face ma dai suna adawa da hakan. haka nan kuma suna ganin wadannan ayoyi na Alkur'ani a matsayin wata tatsuniya da kuma maganganun mutanen da. Duk kuwa da cewa a cikin wannan ayar, an jingina wannan rashin fahimtar gaskiya da kuma karbarta na wadannan mutanen ga Allah Madaukakin Sarki ne, to amma a hakikanin gaskiya hakan ta samo asali ne sakamakon ayyukan su na bin soyace-soyacen zukatansu, a saboda hakan wadannan ayyuka na su suka zamanto musu shamaki da garkuwa cikin fahimtarsu. Yana da kyau a fahimci cewa ba wai Allah ne ya sanya su suka zamanto hakan ba, face dai ayyukansu ne suka sanya su zama hakan.

Allah Madaukakin Sarki dai ya halicci tunanin dan'adam ne tamkar wani madubi wanda yake a tsaftace da babu wata kura a jikinsa don haka yana iya fahimtar gaskiya kamar yadda take, to amma zunubai da taurin kan mutum su ne suka zama tamkar kura a kan zuciya da kuma tunanin nasa don haka, a irin wannan yanayi ba wai ma kawai mutum zai ki amincewa da gaskiya ba ne face ma zai yi adawa da ita ne.

Daga wannan ayar za mu iya daukan darussa kamar haka:

1- Karatu da kuma sauraren ayoyin Alkur'ani suna da wata kima ne a lokacin da hakan ya zamanto mai tasiri cikin zuciya, idan kuwa ba haka ba, to babu wani amfani da hakan yake da shi don kuwa munafukai ma ai suna karanta Alkur'ani. 2- Kafirai dai ba su da wata hujja da ta yi daidai da hankali, a saboda haka suke fakewa da tuhumce-tuhumce da kuma kokarin wulakantar da abu.

Yanzu kuma bari mu saurari aya ta 26:

وَهُمْ يَنْهَوْنَ عَنْهُ وَيَنْأَوْنَ عَنْهُ وَإِن يُهْلِكُونَ إِلاَّ أَنفُسَهُمْ وَمَا يَشْعُرُونَ{26}

"Su kuma sunã hanã mutane jin sa (watau Alkur'ani), su kuma kansu suna nesanta daga gare shi, ba kuwa kowa suke hallakawa ba sai kansu, kuma bã su sansancẽwa."

Wannan ayar ma dai tana ci gaba da bayani ne kan irin taurin kan da mushirikai suke nuna wa Ma'aikin Allah (s.a.w.a) inda take cewa: ba wai kawai suna nesanta kansu daga sauraren Manzon Allah (s.a.w.a) da kuma ayoyin Alkur'ani ba ne, face ma dai suna hana mutane yin hakan ne duk kuwa da cewa ita dai gaskiya ba wata aba ba ce da za a iya boyeta har abada, ko ba dade ba ko jima sai ta yi halinta.

A saboda ko shakka kokarin batar da wasu mutane lamari ne da babu inda zai je sannan kuma abu ne da zai zamanto ummul aba'isin din halakar masu aikata hakan.

Daga cikin wannan ayar za mu iya daukan darussa kamar hakan:

1- Mu yi taka tsantsan da masu fakewa da sunan 'yanci da fadin albarkacin baki wajen yada kafirci, don kuwa ba za su taba barin masu fadin gaskiya su fadi abin da suke da shi cikin 'yancin ba, don kada gaskiya ta bayyana jama'a su yi riko da ita. 2- Jagororin kafirci da shirka, kafin dai su halakar da sauran mutane, suna halakar da kansu ne, ko da kuwa ba su fahimci hakan ba.

Yanzu kuma bari mu saurari aya ta 27 ta cikin wannan sura ta An'am:

وَلَوْ تَرَىَ إِذْ وُقِفُواْ عَلَى النَّارِ فَقَالُواْ يَا لَيْتَنَا نُرَدُّ وَلاَ نُكَذِّبَ بِآيَاتِ رَبِّنَا وَنَكُونَ مِنَ الْمُؤْمِنِينَ{27}

"Kuma dã kanã gani, a lõkacin da aka tsayar da su a kan wuta, sai suka ce: "Yã kaitõnmu! Dã ana mayar da mu, kuma bã zã mu karyata ba daga ãyõyin Ubangijinmu, kuma zã mu kasance Daga mũminai."

A cikin ayar da ta gabata an yi bayanin irin munanan ayyukan wasu mutane wajen tinkarar kira zuwa ga gaskiya da Annabawan Allah suke yi, to ita kuwa wannan ayar tana magana kan mummunar makomar su a ranar lahira, inda take cewa: bai kamata wadannan mutane su yi zaton cewa aikin su zai zamanto ba tare da sakamako ba, lalle za su fuskanci hukumci da kuma ukuba mai girma daga wajen Allah. Wato sakamakon da zai farkar da su daga wannan gafala da suke ciki da kuma gane gaskiya, to amma kuma hakan babu wani amfani da zai musu saboda kuma ba su damar dawowa duniya don aikata aikin kwarai, duk kuwa da cewa suna fadin hakan da kuma fatan ganin an ba su wannan damar, amma ina, alkalami ya riga da ya bushe, sun riga da sun makara.

Darussan da za mu iya dauka daga wannan aya sun hada da:

1- Matukar dai muna raye, to kuwa dama tana nan, wato muna da damar gyara kanmu, to amma daga lokacin da mutuwa ta zo, to babu damar komawa da baya. 2- Ranar lahira rana ce ta nadama da cizon yatsa ga wadanda suka nuna gazawa wajen sauke nauyin da ke wuyansu, don kuwa ba za su sake samun damar yin hakan ba. don haka wajibi ne mu yi kokarin yin ayyukan da suka dace kuma a lokacin da ya dace.

To yanzu kuma bari mu saurari aya ta 28 ta cikin wannan sura ta An'am:

بَلْ بَدَا لَهُم مَّا كَانُواْ يُخْفُونَ مِن قَبْلُ وَلَوْ رُدُّواْ لَعَادُواْ لِمَا نُهُواْ عَنْهُ وَإِنَّهُمْ لَكَاذِبُونَ{28}

"Ã'aha, abin da suka kasance suna bõyẽwa, daga gabãni, ya bayyana a gare su. Kuma dã an mayar da su, lalle dã sun kõma ga abin da aka hana su daga barinsa. Kuma lalle ne sũ, hakĩka, makaryata ne."

Wannan aya dai ta yi ishara ne da daya daga cikin batutuwa masu muhimmanci wajen fahimtar halayen mutum tana cewa: a wani lokaci mutum yana yaudarar hatta kansa ta yadda yake tunanin zai yaudari zuciyarsa da kuma fidirarsa, ta yadda zai aikata mummunan aiki sannan kuma ya san cewa aiki ne mummuna, to amma duk da haka sai yana kokarin nuna wa zuciyarsa cewa bai fahimci hakan ba, alhali kuwa karya yake yi. Alkur'ani mai girma dai cikin ayoyi daban-daban yana bayyana cewar a ranar tashin kiyama za a bayyanar wa masu munanan ayyuka da ayyukansu, a lokacin kan babu wani batun boye-boye.

Wannan ayar tana bayyana cewar dalilin da ya sanya su fatan ganin an dawo da su duniya shi ne saboda sun ga mummunan aikin da suka aikata ne karara sannan kuma sakamakon hakan ma ya bayyana musu don haka suke neman dawowa duniya ko za su iya yin wani abu, to amma babu tabbas din cewa za su iya yi din.

Darussan da suke cikin wannan ayar dai sun hada da:

1- Ana ba da dama ce ga mutanen da ake da fatan cewa za su gyaru, to amma mutanen da dauda ta rufe musu zukatansu kan babu wani amfani a ba su wannan damar, don haka ma ba za a ba su din ba. 2- Abin da muka yi kokarin boye wa zuciyar mu da kuma sauran mutane, to a ranar lahira dai za ta bayyana mana da kuma sauran mutane a fili. Don haka wajibi ne mu nesanci kokarin yaudarar kanmu da kanmu don kuwa babu wani amfani da hakan zai yi mana.

      • To a nan zamu dakata a shirin Hannunka mai Sanda sai kuma shiri na gaba da yardar A... zaku ji bayanai akan wasun ayoyin na surar An'am. Wassalamu alaikum wa rahamatullah.

Suratul An'am, Aya Ta 29-32 (Kashi Na 193)

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shiri na hannunka mai sanda, shirin da a cikinsa muke dubi a ayoyin alkur'ani mai girma domin su kasance mana jagora a rayuwa, sai a biyo mu don jin abin da shirinmu na yau ya kunsa.

A shirinmu na yau zamu fara ne da ambaton aya ta 29 zuwa 30 da suke cikin suratul-An'am kamar haka:-

وَقَالُواْ إِنْ هِيَ إِلاَّ حَيَاتُنَا الدُّنْيَا وَمَا نَحْنُ بِمَبْعُوثِينَ{29} وَلَوْ تَرَى إِذْ وُقِفُواْ عَلَى رَبِّهِمْ قَالَ أَلَيْسَ هَذَا بِالْحَقِّ قَالُواْ بَلَى وَرَبِّنَا قَالَ فَذُوقُواْ العَذَابَ بِمَا كُنتُمْ تَكْفُرُونَ{30}

"Kuma suka ce: "Ba mu da wata rayuwa sai ta wannan duniya, kuma ba za a tashe mu ba {ranar kiyama}" Kuma dã zaka ga lõkacin da aka tsayar da su a gaban Ubangijinsu; Ya ce: "Ashe wannan bai zama gaskiya ba?" sai su ce: "Lalle gaskiya ne muna rantsuwa da Ubangijinmu!" Ya ce: "To ku dandani azaba sabõda abin da kuka kasance kuna kãfirce {masa}."

A cikin ayar da ta gabata alkur'ani ya bayyana akidar mushrikai dangane da Allah da littattafan da aka saukar da kuma Annabawa, inda a cikin wannan ayoyin, alkur'ani ke nuni kan mummunar akidarsu dangane da musun ranar kiyama da cewa: Wadannan mushrikai sun takaita rayuwa ce kawai da duniya wanda da zarar sun mutu, to rayuwarsu ta kawo karshe, amma babu wani dalili da suka gabatar kan kore ranar ta kiyama. Iyaka dai sun takaita ne kawai da cewa; bayan wannan rayuwa ta duniya babu wata rayuwa ta daban.

Aya ta gaba kuma tana ci gaba da magana ne da Annabi da cewa: Wadannan mutane a lokacin da aka tsaida su a ranar kiyama a gaban kotun adalci ta Allah Madaukaki zasu kasance cikin rudu da kaduwa suna rantsuwar cewar lalle kiyama gaskiya ce. Wannan furuci da ikrari da suke yi cikin kaduwa a ranar kiyama wani amfani za su yi musu?, domin furuci ne da ba shi da wani kima, kuma ba zai taba kare su daga gamuwa da azabar Allah ba.

A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-

{1} Mushrikai da kafirai ba su da zurfin tunani, kuma son duniya ta mamaye musu zukata, don haka suke tsammanin ta hanyar musun ranar kiyama da duk wani abu mai kima da ba a gani na gaibu, zasu rusa akidar tsayuwar ranar kiyama da gaibu.

{2} A ranar kiyama Allah da kansa zai kasance babban alkali.

Shirinmu zai ci gaba ne ta hanyar ambaton aya ta 31 da ke cikin suratul-An'am kamar haka:-

قَدْ خَسِرَ الَّذِينَ كَذَّبُواْ بِلِقَاء اللّهِ حَتَّى إِذَا جَاءتْهُمُ السَّاعَةُ بَغْتَةً قَالُواْ يَا حَسْرَتَنَا عَلَى مَا فَرَّطْنَا فِيهَا وَهُمْ يَحْمِلُونَ أَوْزَارَهُمْ عَلَى ظُهُورِهِمْ أَلاَ سَاء مَا يَزِرُونَ{31}

"Lalle ne wadanda suka karyata gamuwa da Allah sun yi hasara, har sai tashin kiyama ta zo musu kwatsam, sai su ce: "Kaitonmu kan irin sakacin da muka yi a cikinta!" Alhãli kuwa suna dauke da laifukansu a bayansu. To ba shakka abin da suke dauke da shi ya mũnana".

A ranar kiyama duk wani abu da ke da alaka da mutum a duniya zai yanke masa, misalin dukiya, matsayi da makusantansa, kuma a lokacin da mutum ya ga lalle an tada matattu, kuma ya yi ido biyu da sakamakon ayyuka na lada da azabar Allah, zai samu tabbacin lalle Allah yana da iko a kan komai. Wannan ayar tana bayyana cewa: karyata ranar kiyama baya zama cutuwa a kan Allah, iyaka dai cutuwa ce a kan masu karyata wannan ranar.

A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-

{1} Duk wanda ke daukar mutuwa a matsayin karshen rayuwa, to hakika ya sayar da kansa ga duniya wanda hakan ba karamar hasara ba ce.

{2} Kiyama rana ce ta hasara da nadama, to wane amfani nadama zata yi a wannan ranar, don haka nadama ce maras amfani.

Yanzu kuma zamu saurari aya ta 32 da ke cikin suratul-An'am kamar haka:-

وَمَا الْحَيَاةُ الدُّنْيَا إِلاَّ لَعِبٌ وَلَهْوٌ وَلَلدَّارُ الآخِرَةُ خَيْرٌ لِّلَّذِينَ يَتَّقُونَ أَفَلاَ تَعْقِلُونَ{32}

"Kuma ba komai ba ce rãyuwar dũniya fãce wãsa da sharholiya, kuma lalle ne Lãhira ce mafi alhẽri ga wadanda suka ji tsoron Allah. Shin ba za ku yi hankali ba?".

A cikin ayoyin da suka gabata mun ambaci irin yadda masu bautan duniya suka takaita karshen rayuwa da duniya ta hanyar musun ranar kiyama, don haka wannan ayar take mayar musu da martani kan mummunan tunaninsu da cewa: Wadannan mutane suna rayuwa ce kawai domin duniya da cimma manufofinta, tun daga yaranta har zuwa girmansu, burinsu shi ne tara dukiya, samun matsayi da mazauni da kuma abin hawa, sun dulmiya cikin sharholiya, amma bayan dan wani lokaci sai su fahimci cewa lalle rayuwarsu ta kare kamar mafarki.

Tabbas rayuwar duniya ba tare da lahira ba; kamar wasa ce, kuma ba ta da wani amfani, amma dole ne mu fahimci cewa; wannan aya da ayoyi makamantanta da suke cikin kur'ani mai girma, ba suna suka da aibanta rayuwar duniya kwata-kwata ba ne, amma suna bayani ne kan rayuwar duniyar da babu tunanin lahira a cikinta inda take kasancewa tamkar ba a matsayin komai ba, kuma a matsayin wasan yara. Amma matukar duniya ta kasance sharar fagen lahira, kuma gona da ake shuka domin girbi a ranar lahira, to zata kasance ta samar da amfani mai yawa, kuma bayin Allah tsarkaka da salihan bayi suna shuka kyakkyawar iri ne a wannan gonar domin su girbi amfani mafi daukaka a ranar lahira.

A gefe guda kuma babban abin bakin ciki, ana samun masu wuce gona da iri sakamakon gurbataccen tunani, inda suke kore duk wata rayuwa ta duniya da al'amuran da suke cikinta, ta hanyar kira zuwa ga kauracewa duniya da katange kansu daga kusantar duk wata rayuwa, ciki har da haramtawa kansu aure sakamakon gafala da suka yi da fadin Allah da ke cewa; ya halicci ni'imomin duniya ne domin dadadawa mutane, kuma rashin kulawa da wadannan ni'imomin yana daga cikin rashin godiya.

A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:- {1} Mu kiyaye kada bukatarmu ga duniya ta mantar da mu lahira, idan har kuma muka gafala da lahira, to mun koma kananan yara bayan girma.

{2} Muminai su kasance cikin zurfin tunani domin kada masu bautan duniya su yaudarar da su, inda a karshe zasu kasance cikin masu gafala.

{3} Tsoron Allah da zurfafa tunani suna tafiya ne kafada da kafada, domin hankalin da ke tare da mutum yana kiransa ne zuwa ga tsarki da gudanar da kyakkyawan aiki, haka nan tsoron Allah yana kare mutum ne ga afkawa cikin bata da gurbatar tunani.

To a nan ne shirin na mu ya zo karshe, sai kuma a gamo na gaba. Wassalamu alaikum warahmatullah.

Suratul An'am, Aya Ta 33-36 (Kashi Na 194)

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shiri na hannunka mai sanda, shirin da a cikinsa muke dubi a ayoyin alkur'ani mai girma domin su kasance mana jagora a rayuwa, sai a biyo mu don jin abin da shirinmu na yau ya kunsa.

A shirinmu na yau zamu fara ne da ambaton aya ta 33 zuwa 34 da suke cikin suratul-An'am kamar haka:-

قَدْ نَعْلَمُ إِنَّهُ لَيَحْزُنُكَ الَّذِي يَقُولُونَ فَإِنَّهُمْ لاَ يُكَذِّبُونَكَ وَلَكِنَّ الظَّالِمِينَ بِآيَاتِ اللّهِ يَجْحَدُونَ{33} وَلَقَدْ كُذِّبَتْ رُسُلٌ مِّن قَبْلِكَ فَصَبَرُواْ عَلَى مَا كُذِّبُواْ وَأُوذُواْ حَتَّى أَتَاهُمْ نَصْرُنَا وَلاَ مُبَدِّلَ لِكَلِمَاتِ اللّهِ وَلَقدْ جَاءكَ مِن نَّبَإِ الْمُرْسَلِينَ{34}

"Hakika muna sane da cewa abin da suke fada yana bãta maka rai. To a hakikanin gaskiya su ba kai suke karyatawa ba , sai dai su azzãlumai suna yin jayayya da ãyõyin Allah ne. "Kuma lalle ne, hakĩka, an karyata manzanni a gabãninka, sai suka yi hakuri a kan abin da aka karyata su, kuma aka cũtar da su, har taimakonMu ya je musu, kuma babu wanda zai iya canza alkawarin Allah. Kuma hakika {wani abu} daga labarin manzanni ya zo maka".

Hakika Manzon Allah ya kasance yana kiran mushrikai zuwa ga gaskiya ta hanyar wa'azi da maganganu na hankali, amma ba kawai sun ki amincewa da kiran ba ne, suna gudanar da jayayya da furta munanan maganganu kansa ta hanyar tuhuma da kaskantashi, wannan bakar dabi'a tasu tana bakanta ran Manzon Allah, don haka sau da dama a cikin kur'ani Allah yake karfafa gwiwar Manzonsa tare da karfafa shi yana cewa: baya ga karyata ka da suke yi kana fushi kan haka, suna kuma karyata Allah da ayoyinsa, kuma ba kai ne farkon Annabin da aka karyata ba domin a tsawon tarihi Annanabawa da suka gabace ka sun fuskanci karyatawa daga masu adawa da su, don haka wannan dabi'a ce ta kafirai, amma sunnar Allah da ke kalubalantar wannan dabi'a ta su ita ce taimakon gaskiya matukar ma'abuta gaskiya suka tsaya a kan dugadugansu na imani da gudanar da ayyuka.

A cikin wannan ayoyi zamu fahimci darussa kamar haka:-

{1} Hakika karyata gaskiya da ayoyin Allah zaluntar kai ne – ba cutuwa ce ga hanyar Allah ba- kuma hakan yana mummunan tasiri a kan mai karyatawar.

{2} Hanyar gaskiya hanya ce mai wahala, don haka isar da sakon Annabawa yake tare da matsaloli.

{3} Jagororin shiriya zuwa ga Allah kada su taba tsammanin da zarar sun gabatar da sakon Allah mutane zasu amsa musu tare da yin biyayya.

Shirinmu zai ci gaba ne ta hanyar ambaton aya ta 35 da ke cikin suratul-An'am kamar haka:-

وَإِن كَانَ كَبُرَ عَلَيْكَ إِعْرَاضُهُمْ فَإِنِ اسْتَطَعْتَ أَن تَبْتَغِيَ نَفَقاً فِي الأَرْضِ أَوْ سُلَّماً فِي السَّمَاء فَتَأْتِيَهُم بِآيَةٍ وَلَوْ شَاء اللّهُ لَجَمَعَهُمْ عَلَى الْهُدَى فَلاَ تَكُونَنَّ مِنَ الْجَاهِلِينَ{35}

"Kuma idan yã kasance cewa bijirewarsu tã yi nauyi a gare ka, to, idan kana iyãwa, ka nemi wani rami a cikin kasa kõ kuma wani tsãni a cikin sama dõmin ka zo musu da wata ãyã { sai ka yi}. Kuma dã Allah Yã so hakĩka dã yã tãttara su a kan shiriya. Sabõda haka kada ka kuskura ka kasance daga jãhilai".

Ayoyin da suka gabata suna magana ne kan hanyoyi daban daban maras kyau da kafirai suke amfani da su wajen musgunawa Annabawan Allah da suke gabatar musu da maganganu na hankali, amma wannan aya tana magana ne da Manzon Allah cewa: kada ka taba tsammanin rashin imaninsu ya samo asali ne daga matsala a salon isar da sakonka ko akwai wani kuskure ne da ka yi a wajen gabatar musu da sakon, lalle matsalar daga gare su take, saboda ba su son karbar gaskiya ce kawai, kuma ba hakkinka ba ne ka tilasta musu karbar gaskiyar, kuma shi kansa Allah baya kaunar tilasta musu, domin da ya so da dukkanin mutane sun yi imani tare da mika wuya, amma Allah ya bai wa mutane damar zaben gaskiya bisa radin kansu. Wannan ayar tana bayani ne kan cewa duk wani rashin jurewa karyatawa alama ce ta rashin fahimtar wannan sunna ta Allah da ta bai wa mutane damar zaben gaskiya da kansu, inda take magana da Manzon Allah da cewa: kada ya kasance cikin masu wannan tunani saboda tuanni ne na jahilai.

A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-

{1} Lalle Allah Madaukaki ya samar da duk wata hanyar shiryar da mutane domin yana son kowa ya shiriya, amma hikimarsa ta hukunta cewa mutane su kasance cikin 'yancin zaben shiriya da kansu.

{2} Gabatar da bukatu marassa tushe kafin amincewa da gaskiya aiki ne na jahilai domin ba a shirye suke su karbi gaskiya ba.

Yanzu kuma zamu saurari aya ta 36 da ke cikin suratul-An'am kamar haka:-

إِنَّمَا يَسْتَجِيبُ الَّذِينَ يَسْمَعُونَ وَالْمَوْتَى يَبْعَثُهُمُ اللّهُ ثُمَّ إِلَيْهِ يُرْجَعُونَ{36}

"Hakika iyaka dai wadanda suke saurare ne suke karbãwa, kuma matattu Allah Yake tãyar da su, sannan kuma gare Shi ne za a komar da su".

Alkur'ani a cikin ayoyi da dama yana bayyana wadanda ba su sauraren gaskiya da rashin tasirantuwa da ita a matsayin matattu. Haka nan wadanda suke dauke da hankali amma ba su tasirantuwa da gaskiya su ma kamar matattu ne da ba su ji ko fahimtar komai. Irin wadannan mutane bayan Allah ya tashe su a ranar kiyama sai su fadaka daga barcin gafalar da suka shiga tare da riya imani, amma wani amfani irin wannan imani zai yi? Lalle imani ne da ba shi da wani kima.

A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-

{1} Kafirai masu jayayya da gaskiya kamar matattu ne, inda mutuwa da hakika zata fadakar da su.

{2} Hakika mutum ya kan kasance mai kima ne a lokacin da yake rayuwa cikin hali na addini da mika kai ga umurni Allah, domin rayuwar duniya ba ta takaita da ci da sha da kuma barci ba, saboda dabbobi ma suna da wadannan halaye a rayuwarsu.

{3} Hakki ne a kanmu isar da sakon gaskiya ga mutane da suke da zuciyar amince da ita, amma kafiran da suka bijire wa gaskiya hisabinsu na wajen Allah, saboda ba mu da hakkin tilasta musu amincewa da gaskiyar.

To a nan ne shirin na mu ya zo karshe, sai kuma a gamo na gaba. Wassalamu alaikum warahmatullah.

Suratul An'am, Aya Ta 37-39 (Kashi Na 195)

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shiri na hannunka mai sanda, shirin da a cikinsa muke dubi a ayoyin alkur'ani mai girma domin su kasance mana jagora a rayuwa, sai a biyo mu don jin abin da shirinmu na yau ya kunsa.

A shirinmu na yau zamu fara ne da ambaton aya ta 37 da ke cikin suratul-An'am kamar haka:-

وَمَا مِن دَآبَّةٍ فِي الأَرْضِ وَلاَ طَائِرٍ يَطِيرُ بِجَنَاحَيْهِ إِلاَّ أُمَمٌ أَمْثَالُكُم مَّا فَرَّطْنَا فِي الكِتَابِ مِن شَيْءٍ ثُمَّ إِلَى رَبِّهِمْ يُحْشَرُونَ{38}

"Kuma suka ce: "Ina ma da an saukar masa da ãyã daga Ubangjinsa?" Ka ce: "Lalle ne Allah Mai ĩko ne a kan saukar da ãyã, amma mafi yawansu ba su san {haka} ba."

Ya zo cikin tarihi cewa: A lokacin da manyan mushrikan kuraishawa suka ga sun gaza a fadar da suke yi da kur'ani, sai suka ce; alkur'ani ba zai yiyu ya kasance mu'ujiza ba, idan kuma har Manzon Allah gaskiya ya ke fadi, to ya gabatar da mu'ujiza irin wanda Annabi Musa da Isa suka zo da ita kafin mu yi imani da shi. A fili yake wannan maganganu da suke gabatarwa ba ta neman gaskiya ba ce, iyaka dai kokari ne na neman gujewa yin imani da kur'ani da Manzon Allah {s.a.w}, domin da Manzon Allah zai zo musu da mu'ujiza irinta Annabawan da suka gabace shi, da sun nemi ya kara gabatar da wata mu'ujizar, saboda ba a shirye suke su karbi gaskiya ba, kuma su kansu mutanen da suka yi zamani da wadancan Annabawan sun bayyana mu'ujizozin da ake je musu da su da cewa sihiri ne da bokanci, sannan suka zargi Annabawan da cewa masu sihiri ne kuma bokaye.

A wani lokaci idan mutum yana barci matukar aka kira shi sau da dama, to zai farka, amma idan da'awar barcin yake yi, to komai kiran da aka masa, ba zai farka ba, saboda dama baya son farkawa. Kamar haka ne mutane suna da fuska biyu wajen karbar gaskiya; wasu da zarar sun ji kiran gaskiya sukan farka daga barcin gafala tare da kama hanya madaidaiciya, amma wasu barcin karya suke yi, ba a shirye suke su karbi gaskiya ba, kuma duk wata hanya da aka bi wajen gabatar musu da gaskiyar, ba zasu shiriya ba.

A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-

{1} Manufar gabatar da mu'ujiza ita ce tabbatar da gaskiyar annabcin mutum da cika hujja kan mutane, ba wai biyan bukatu da son ran masu girman kai ba.

{2} Allah mai iko ne kan komai, amma ikonsa yana gudana ne kan hikima, saboda yana da ikon aiwatar da kowace irin mu'ujiza da mutane ke bukata sai dai bukatar masu babu hikima ciki, kuma tarihi ya tabbatar da cewa duk mu'ujizar da aka gabatar ga masu girman kai ba su shiriya.

Shirinmu zai ci gaba ne ta hanyar ambaton aya ta 38 da ke cikin suratul-An'am kamar haka:-

وَمَا مِن دَآبَّةٍ فِي الأَرْضِ وَلاَ طَائِرٍ يَطِيرُ بِجَنَاحَيْهِ إِلاَّ أُمَمٌ أَمْثَالُكُم مَّا فَرَّطْنَا فِي الكِتَابِ مِن شَيْءٍ ثُمَّ إِلَى رَبِّهِمْ يُحْشَرُونَ{38}

"Kuma bãbu wata dabba da take bayan kasa, kuma bãbu wani tsuntsu da yake tashi da fukafukansa fãce al'umma ne kamarku. Ba mu yi sakacin barin kõmai a cikin Littãfin nan ba, sannan za a tattara su ne zuwa ga Ubangjinsu".

Wannan ayar tana gargadi ne ga mutum da cewa kada ya dauka sauran halittu ba su riskar abubuwa da fahimta, amma ya sani dukkanin halittu shin dabbobi ne da ke tafiya a kan doron kasa da wadanda suke shawagi a sararin samaniya su ma halittu ne kamar mutum da suke da irin nau'in fahimta da riskar abubuwa irin ta su; kamar haka ne kur'ani ke nuni kan furucin tururruwa da huda-huda a cikin labarin Annabi Sulaiman, to sai dai a fili yake cewa fahimta da riskar al'amura suna da matakai, inda riskar al'amura da fahimtar mutum shi ne mafi daukakan matakin fahimta, yayin da fahimtar dabbobi ita ce mafi raunin fahimta. Haka nan mutum yana da karancin fahimta da riskar al'amura misali a lokacin da yaro yake shekarar farko fahimtarsa da riskar al'amuransa yana da rauni, kamar yadda a dabi'ar mutane suke dauka cewa karamin yaro baya da hankali da riskar al'amura.

Baya ga batun fahimta da riskar al'amura na halittu wannan aya ta yi nuni kan tayar da halittu da tattara su a ranar kiyama, inda take bayanin cewa: za a tayar da halittu a ranar kiyama, kamar yadda ya zo cikin aya ta biyar da ke cikin surar Takwir cewa: "Idan kuma namun daji aka tattara su". Ya zo cikin ruwaya da ke nuni kan cewa; za a tayar da dabbobi a ranar kiyama tare da bayyana irin hukuncin da za a yi kan dabbobin da suka yi zalunci a kan junansu, sai dai kasancewar fahimtar dabbobi ba irin na mutane ba ne don haka ba a daura musu hukunce-hukunce ba, amma za a musu hukunci gwargwadon irin fahimtar da suke da ita, misali kamar karamin yaro ne dan shekaru goma sha biyu da ya aikata laifin kisan kai da gangan, a dukkanin dokokin duniya yana da irin hukuncin da za a masa kan wannan laifin da ya aikata daidai da matsayin shekarunsa da fahimtarsa ga al'amura.

A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-

{1} Tsarin zamantakewar rayuwa bai takaita da mutane ba kawai, har dabbobi suna da irin na su tsarin zamantakewar.

{2} Kada mu zame masu zalunci a kan dabbobi ko cutar da su saboda su ma suna da hakkin rayuwa da irin nau'in fahimtarsu da riskarsu ga al'amura.

{3} Dukkanin halittu daga Allah suke kuma gare shi zasu koma, don haka dukkanin halittu suna karkashin kulawan Allah ne kuma shi ne mai rainonsu.

Yanzu kuma zamu saurari aya ta 39 da ke cikin suratul-An'am kamar haka:-

وَالَّذِينَ كَذَّبُواْ بِآيَاتِنَا صُمٌّ وَبُكْمٌ فِي الظُّلُمَاتِ مَن يَشَإِ اللّهُ يُضْلِلْهُ وَمَن يَشَأْ يَجْعَلْهُ عَلَى صِرَاطٍ مُّسْتَقِيمٍ{39}

"Kuma wadanda suka karyata ãyõyinmu, kurãme ne kuma bebãye a cikin duffai. Wanda Allah ya so yanã batar da shi, kuma wanda ya so ya sanya shi a kan hanya madaidaiciya".

Wannan ayar tana bayyana karyata ayoyin Allah a matsayin tawaye da afkawa cikin duhun zalunci, don haka masu karyata ayoyin Allah suna cikin mummunar kangi saboda sun haramta wa kansu fahimtar gaskiya kuma sun kasance suna furuci da hakan. Lalle son ransu da biyewa sha'awace sha'awacen zuciyarsu sun wurga su cikin duhun bata don haka suka katange kansu daga ganin hasken shiriya.

Har ila yau ci gaban ayar tana danganta shiriyar mutane da batarsu ga Allah, to a fili yake cewa: Allah Madaukaki ya mallaka wa mutane hankali tare da aiko musu da Manzanni domin su kasance dalilin shiriyarsu tare da ba su hakkin zaben hanyar da suka dama bisa radin kansu, don haka duk wanda ya yi tawaye ya ki amincewa da hanyar shiriya, to shi da kansa ne ya toshe kafar shiriya wa kansa, wato gudanar da munanan ayyuka da dogewa a kai yana kai mutum ga yin nisa da hanyar gaskiya, kamar yadda gudanar da kyawawan ayyuka kan kai mutum ga karbar gaskiya da yin furuci da ita.

A cikin wannan ayar zamu fahimci darussa kamar haka:-

{1} Kafirci da juya baya ga gaskiya duhu ne kuma zaluntan kai ne da ke kai mutum ga rashin fahimtar hakikanin al'amura.

{2} Azabar karyata ayoyin Allah a duniya ita ce yin nisa ga shiriya da shiga cikin rudun rayuwar duniya.

To a nan ne shirin na mu ya zo karshe, sai kuma a gamo na gaba. Wassalamu alaikum warahmatullah.

Suratul An'am, Aya Ta 40-45 (Kashi Na 196)

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shiri na hannunka mai sanda, shirin da a cikinsa muke dubi a ayoyin alkur'ani mai girma domin su kasance mana jagora a rayuwa, sai a biyo mu don jin abin da shirinmu na yau ya kunsa.

A shirinmu na yau zamu fara ne da ambaton aya ta 40 zuwa 41 da suke cikin suratul-An'am kamar haka:-

قُلْ أَرَأَيْتُكُم إِنْ أَتَاكُمْ عَذَابُ اللّهِ أَوْ أَتَتْكُمُ السَّاعَةُ أَغَيْرَ اللّهِ تَدْعُونَ إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ{40} بَلْ إِيَّاهُ تَدْعُونَ فَيَكْشِفُ مَا تَدْعُونَ إِلَيْهِ إِنْ شَاء وَتَنسَوْنَ مَا تُشْرِكُونَ{41}

"Ka ce: "Ku ba ni labari idan azãbar Allah ta zo muku kõ kuma alkiyama ta zo muku, shin wanin Allah zaku yi kira? idan dai kun kasance mãsu gaskiya?" "Ã'a {Allah} shĩ dai kuke kira, sai ya yaye abin da kuke rokonsa a kai idan ya so, kuma kuke mantã abin da kuke yin shirka da shi."

A shirin da ya gabata mun bayyana cewa tushen kafirci da kin karbar gaskiya sun samo asali ne daga tawaye da bijirewa gaskiya da kafirai suka yi amma babu wata hujjar da suke gabatarwa wajen kore samuwan Allah, kuma ba a shirye suke su karbi dalilan na hankali ba. Amma domin fadakar da irin wadannan mutane wannan aya tana bayyana cewa; da kuke kiran wadansu maimakon Allah kuma kuke riya cewa suna da karfi da iko a kan komai, to a lokacin da masifa da bala'i suka afka muku wane ne kuke kira ya ceceku? Shin a irin wannan lokacin kuna neman ceto ne a wajen wadanda kuka rika ne a matsayin Alloli? Kuma shin wadannan abubuwan zasu iya taimaka muku tare da tseratar da ku daga mutuwa? Idan har ranar kiyama ta tabbata gaskiya, to a lokacin da aka tsayar da ku a ranar ta kiyama, shin kun yi tunanin wane ne zai ceceku?.

Har ila yau wannan aya tana magana da hankalin kafirai da cewa: Hakika a lokacin da kuka shiga cikin halin masifa da bala'i, Allah Madaukakin Sarki kawai kuke kira ya ceto ku daga matsalar da kuka afka, kuma a wannan yana yin ku kan mance da kowa da komai.

A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-

{1} Imani da samuwar Allah Makadaici al'amari ne da ke cikin zuciyar kowane bil-Adama saboda haka mutane suna dauke da akidar samuwar Allah, amma sharholiyar duniya ke gafalar da su daga al'amarin samuwar Allah, kuma wahala da matsala tana taimakawa wajen yaye shamakin gafalar da mutum ya shiga ciki kan akidar samuwan Allah.

{2} A lokacin wahala da matsala zuciya ta kan mance duk wani abu koma bayan Allah, kuma gare shi ake komawa domin biyan bukatu.

Shirinmu zai ci gaba ne ta hanyar ambaton aya ta 42 da ke cikin suratul-An'am kamar haka:-

وَلَقَدْ أَرْسَلنَا إِلَى أُمَمٍ مِّن قَبْلِكَ فَأَخَذْنَاهُمْ بِالْبَأْسَاء وَالضَّرَّاء لَعَلَّهُمْ يَتَضَرَّعُونَ{42}

"Kuma hakika mun aiko {manzanni} zuwa ga al'ummai a gabãninka, sai muka dora musu talauci da cũta, don su kankantar da kai".

Wannan aya tana ci gaba da bayani kan ayoyin da suka gabata ne da cewa: Baya ga aiko Annabawa da Allah Madaukaki ke yi domin shiryar da mutane, kuma yana jaraba mutane a rayuwarsu da wahalhalu da matsaloli da nufin fadakar da su zuwa ga akidar samuwan Allah da karban bayanan Annabawa domin tsarkake mutane daga gurbataccen tunani, zuciyarsu ta kasance mai tsarki da hasken shiriya zai haskakata.

A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-

{1} A wani lokaci dole ne a fagen tarbiyya sai an dauki matakin matsin lamba da fuskantar matsaloli kafin a kai ga fadakar da mutum zuwa ga akidar samuwan Allah da mika masa wuya.

{2} Kankantar da kai da kuka a fadar Allah lamari ne da ke tausasa zuciya, kuma shimfida ne na karbar gaskiya.

Yanzu kuma zamu saurari aya ta 43 da ke cikin suratul-An'am kamar haka:-

فَلَوْلا إِذْ جَاءهُمْ بَأْسُنَا تَضَرَّعُواْ وَلَـكِن قَسَتْ قُلُوبُهُمْ وَزَيَّنَ لَهُمُ الشَّيْطَانُ مَا كَانُواْ يَعْمَلُونَ{43}

"To ina ma a ce, a lõkacin da tsananinMu ya jẽ musu sun kankantar da kai, Kuma amma sai zukatansu suka kẽkashe, kuma shaidan yã kawãta musu abin da suka kasance sunã aikatãwa".

Bayan mun saurari ayar da ta gabata, wannan ayar kuma tana bayyana cewa: Kafirai da masu inkarin gaskiya suna cikin barcin gafala, don haka gargadi baya musu amfani, kuma dalilan gafalarsu abubuwa ne guda biyu kamar haka:- Na farko nutso a cikin tekun laifi yana janyo kekashewar zuciya da daudarta. Na biyu daukan munanan ayyuka a matsayin ado, wanda a duk lokacin da suka aikata laifi suna ganinsa a matsayin ado ne gare su, kuma duk wani sabo suna daukansa a matsayin daidai ne da rayuwarsu.

A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-

{1} Mutanen da ke jayayya da gaskiya ba su jin kira, kuma fadakarwa ba ta musu tasiri, kuma ba a shirye suke su fahimci sakon gaskiya ba ko karbanta.

{2} Mutum a dabi'arsa yana son abu mai kyau, don haka sai shaidan ya yi amfani da sha'awar da ke tare da mutum wajen kawata masa munanan ayyuka.

Yanzu kuma zamu saurari aya ta 44 zuwa 45 da suke cikin suratul-An'am kamar haka:-

فَلَمَّا نَسُواْ مَا ذُكِّرُواْ بِهِ فَتَحْنَا عَلَيْهِمْ أَبْوَابَ كُلِّ شَيْءٍ حَتَّى إِذَا فَرِحُواْ بِمَا أُوتُواْ أَخَذْنَاهُم بَغْتَةً فَإِذَا هُم مُّبْلِسُونَ{44} فَقُطِعَ دَابِرُ الْقَوْمِ الَّذِينَ ظَلَمُواْ وَالْحَمْدُ لِلّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ{45}

"Sannan kuma a lõkacin da suka manta da abin da aka tunãtar da su da shi, sai Muka bũde musu kõfõfin dukkan kõmai {na ni'ima}, har lõkacin da suka yi farin ciki da abin da aka ba su, sai Muka kãmã su, kwatsam, sai gã su sun yanke kauna. Sai aka katse karshen mutãnen da suke azzalumai. Kuma gõdiya tã tabbata ga Allah Ubangijin tãlikai.

Allah Madaukaki yana amfani da hanyoyi da dama wajen shiryar da mutane, don haka yake aiko Annabawa domin su isar da sakon gaskiya a tsakanin mutane, idan hakan bai yi tasiri ba, to yana daukan matakin matsin lamba da wahalarwa a kan masu inkarin gaskiya ko zasu farka daga barcin gafala da suke ciki, idan kuma har hakan bai musu tasiri ba, to sai Allah ya barsu cikin halin da suke tare da wadata su da nau'o'in ni'ima, a cikin tsarin Allah Madaukaki wadannan mutane zasu amfana da wannan ni'imomi na duniya, amma hakan ba zai dauki tsawo lokaci ba, Allah ya yi musu daurin talala ne domin aikin laifinsu da barnar da suke yi su kai tukewa sai Allah ya saukar musu da azabar duniya wadda zata kawar da su daga shafin rayuwa.

Manzon Allah {s.a.w} yana bayyana cewa: "A duk lokacin da kuka ga duniya a hannun mabarnata masu laifi, -to kada ku fitar da rai- hakan wani shimfidi ne na halakarsu". Har ila yau shugaban muminai Imam Ali {a.s} yana bayyana cewa: "Idan har ka ga Allah ya sakan maka ni'imarsa tana ci gaba da gudana a karkashinka - alhalin kana aikata laifi- to ka sani wannan ni'ima karshenta ba zata yi kyau ba".

A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-

{1} Jin dadin duniya zai iya zama ni'ima, kamar yadda zai iya zama azaba, idan yana tafiya ne tare da imani da tsoron Allah, to ni'ima ne, idan kuma yana gudana ne da aikin laifi da fasikanci, to azabar Allah ne, koma dai ya ya lamarin yake, jin dadin rayuwa ba alama ne na rahama ba, domin wani lokaci shimfidi ne na azaba.

{2} Zalunci da cuta ba su tabbata, don haka halakar azzalumai lamari ne da babu makawa.

To a nan ne shirin na mu ya zo karshe, sai kuma a gamo na gaba. Wassalamu alaikum warahmatullah.

Suratul An'am, Aya Ta 46-49 (Kashi Na 197)

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shiri na hannunka mai sanda, shirin da a cikinsa muke dubi a ayoyin alkur'ani mai girma domin su kasance mana jagora a rayuwa, sai a biyo mu don jin abin da shirinmu na yau ya kunsa.

A shirinmu na yau zamu fara ne da ambaton aya ta 46 da ke cikin suratul-An'am kamar haka:-

قُلْ أَرَأَيْتُمْ إِنْ أَخَذَ اللّهُ سَمْعَكُمْ وَأَبْصَارَكُمْ وَخَتَمَ عَلَى قُلُوبِكُم مَّنْ إِلَـهٌ غَيْرُ اللّهِ يَأْتِيكُم بِهِ انظُرْ كَيْفَ نُصَرِّفُ الآيَاتِ ثُمَّ هُمْ يَصْدِفُونَ{46}

"Ka ce: "ku ba ni labari, {yanzu} idan Allah Ya rike jinku, da gannanku, kuma Ya rufe zukãtanku, wani abin bauttãwa ne zai zo muku da shi in ba Allah ba? Ka dũba irin yadda Muke bayyana musu ayoyi, Sannan suke bijirẽwa".

Wannan ayar kamar sauran ayoyin da suka gabace ta; tana umurtar Manzon Allah da ya dauki matakin kiran kafirai zuwa ga zurfafa tunani da yin nazari kan ni'imomin da Allah ya yi musu, kuma ya tambaye su cewa; idan Allah ya karbe jinku da ganinku, shi ke nan ba ku da wata damar fahimtar al'amura- kuma shin wadannan gumaka da kuka rike su abin bauta ko kuma wadanda zuciyarku ta karkata zuwa gare su zasu iya dawo muku da wadannan kafofi masu muhimmanci da fahimtar al'amura? Lalle su kansu wadannan gumaka ba su ji ko gani, kuma ba su da hankali ballantana su dauki matakin azurtaku da wadannan ni'imomi.

Ayar ta ci gaba da bayyana cewa: Alkur'ani yana bayanin dalilan da yake dauke da shi ta hanyoyi daban daban ko watakila wadannan kafirai zasu fadaka su rungumi gaskiya, sai dai matsalar ita ce son kai da jayayya maras tushe sun riga sun galaba a kansu don haka ba su jin kira ballantana su karbi gaskiya.

A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-

{1} Yin tunani kan ni'imomin Allah da tsammanin gushewarsu daya ne daga cikin hanyoyin sanin Allah.

{2} Dukkanin halittu daga Allah suke, haka nan ci gaba da gudanar ni'imomi da wanzuwarsu duk yana wajen Allah ne.

Shirinmu zai ci gaba ne ta hanyar ambaton aya ta 47 da ke cikin suratul-An'am kamar haka:-

قُلْ أَرَأَيْتَكُمْ إِنْ أَتَاكُمْ عَذَابُ اللّهِ بَغْتَةً أَوْ جَهْرَةً هَلْ يُهْلَكُ إِلاَّ الْقَوْمُ الظَّالِمُونَ{47}

"Ka ce: "ku ba ni labari idan azãbar Allah ta zo muku kwatsam, kõ kuma cikin sani, shin wa za a hallakã in ban da mutãne azzãlumai?"

Ayar da ta gabata ta bayyana cewa: Idan Allah ya karbe dukkanin ni'imomin da ya yi muku, babu yadda kuka iya, sannan wannan ayar ke cewa: Idan Allah ya saukar muku da azaba, tabbas ba ku da karfin kare kanku daga gare ta, ko hana saukarta a kanku, kamar yadda ba zaku iya guje mata ba, don haka sai ku sallama lalle gumaka da wadanda kuka rika a zuciya ba Allah ba, ba su da ikon saukar muku da wata ni'ima, kuma ba zasu iya kawar muku da wata cutu ko hatsari ba, to don mene ne zaku rike su maimakon Allah Madaukaki?

Ayar ta ci gaba da bayyana cewa: Ka gargade su da cewa; irin wannan taurin kai da bijirewa gaskiya, nau'i ne na zalunci da ke addabarku da ma al'umma baki daya, kuma yana sanadiyyar saukar azaba a kanku tun daga nan duniya.

A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-

{1} Kada mu yaudaru saboda jinkirin saukar azabar Allah a kanmu, watakila azabar ta sauko mana kwatsam ba shiri.

{2} Hanya mafi dacewa wajen yin kira ga mutanen da suka bijirewa gaskiya ita ce gabatar musu da hakikanin al'amura ta hanyar tambaya da haka zai wurga su cikin tunani da nazari, watakila su fadaka daga gafalar da suka shiga.

Yanzu kuma zamu saurari aya ta 48 zuwa 49 da suke cikin suratul-An'am kamar haka:-

وَمَا نُرْسِلُ الْمُرْسَلِينَ إِلاَّ مُبَشِّرِينَ وَمُنذِرِينَ فَمَنْ آمَنَ وَأَصْلَحَ فَلاَ خَوْفٌ عَلَيْهِمْ وَلاَ هُمْ يَحْزَنُونَ{48} وَالَّذِينَ كَذَّبُواْ بِآيَاتِنَا يَمَسُّهُمُ الْعَذَابُ بِمَا كَانُواْ يَفْسُقُونَ{49}

"Kuma bã Mu aiko da manzãnni sai don su yi bushãra da kuma gargadi. sannan wadanda suka yi ĩmãni kuma suka kyautata aiki, to babu tsõro a gare su, kuma ba za su yi bakin ciki ba. "Kuma wadanda suka karyata ãyõyinMu, azãba tanã shãfarsu sabõda abin da suka kasance sunã aikatawa na fãsikanci".

A cikin ayoyin da suka gabata an umurci Manzon Allah ne da ya gargadi mushrikai tare da fadakar da su dangane da sakamakon mummunar ayyukansu. Yayin da wadannan ayoyin suke bayyana cewa: Manufar aiko Annabawa a tsawon tarihi ita ce gudanar da fadakarwa da gargadi domin katange mutane daga afkawa cikin gurbatacce tunani da gudanar da munanan ayyuka, kuma suna yin kira ga mutane zuwa ga kyawawan ayyuka tare da musu bushara kan kyakkyawar sakamakon da zasu tarar a wajen Allah.

Daga cikin busharar da Annabawa ke yi ga muminai akwai rashin bakin ciki da tsoro irin wadda masu bautan duniya ke yi saboda tsammanin gushewar al'amuransu na duniya, tare da karfafa musu zuciya da tabbatar da dugadugansu a kan tafarkin gaskiya gami da karfin fuskantar duk wani azzalumin shugaba ba tare da nuna wani rauni da gajiyawa a gabansa ba, amma su kuwa kafirai da suke karyata gaskiya suka kuma rungumi ayyukan laifuka da sharholiya, Allah zai dandana musu mummunar azabar duniya ta zahiri da ta boye, sannan a ranar kiyama su fuskanci azaba mai radadi.

A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-

{1} Aikin Annabawa shi ne isar da sako da shiryar da mutane, ba tilasta musu amince da sakon gaskiyar da suka je musu da shi ba, don haka ake samun wasu mutane sun yi imani, wasu kuma sun kafirce.

{2} Dole ne tarbiyya ta ginu a kan tubali biyu tsakanin tsoratarwa da kwadaitarwa, saboda kada mutane su fitar da ran ko yaudaruwa. {3} Imani baya amfani matukar babu aiki, kamar yadda aiki baya da wani kima matukar babu imani.

{4} Tsoro da bakin ciki suna daga cikin manyan matsalolin da suke addabar mutane har a wannan zamani da muke ciki sakamakon nisan da suka yi da Allah da imani.

To a nan ne shirin na mu ya zo karshe, sai kuma a gamo na gaba. Wassalamu alaikum warahmatullah.

Suratul An'am, Aya Ta 50-52 (Kashi Na 198)

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shiri na hannunka mai sanda, shirin da a cikinsa muke dubi a ayoyin alkur'ani mai girma domin su kasance mana jagora a rayuwa, sai a biyo mu don jin abin da shirinmu na yau ya kunsa.

A shirinmu na yau zamu fara ne da ambaton aya ta 50 da ke cikin suratul-An'am kamar haka:-

قُل لاَّ أَقُولُ لَكُمْ عِندِي خَزَآئِنُ اللّهِ وَلا أَعْلَمُ الْغَيْبَ وَلا أَقُولُ لَكُمْ إِنِّي مَلَكٌ إِنْ أَتَّبِعُ إِلاَّ مَا يُوحَى إِلَيَّ قُلْ هَلْ يَسْتَوِي الأَعْمَى وَالْبَصِيرُ أَفَلاَ تَتَفَكَّرُونَ{50}

"Ka ce: "Ba zan ce muku taskõkin Allah suna waje na ba. Kuma ba ni da sanin gaibi, kuma ban ce da ku ni Malã'ika ba ne. Ba abin da nake bi fãce abin da ake yiwo wahayi zuwa gare ni."Ka ce: "Shin makãho da mai gani sunã daidaita? To mene ne ya sanya ba ku yin tunãni?"

Da dama daga cikin mutane suna tsammanin duk wanda yake Annabi ne, to dukkanin al'amuran gudanar da wannan duniya suna hannunsa, kuma dukkanin ayyuka da matsaloli yana da damar warware su ta hanyar gaibu, haka nan duk abin da yake so zai aiwatar, kuma duk wanda ya saba masa zai rushe, don haka wannan ayar take umurtan Manzon Allah kan ya sanar da mutane cewa; aikin Annabi shi ne kiran mutane zuwa ga Allah da isar da sakon Allah gare su, ba aikin Annabi ba ne bada labarin gaibu ga mutane, inda zasu yi tsammanin zai dinga ba su labarin abin da ya faru a baya da abin da zai faru da su a nan gaba, kuma ba Mala'ika ba ne da aka dauke masa duk wata bukatar dan Adam na jiki misalin abinci, aure da sauransu. Sannan mu'ujiza da Annabawa ke gabatarwa suna gudana ne karkashin izinin Allah, ba suna gudanarwa ba ne bisa son ran mutane, don haka a duk lokacin da suke bukata Manzon Allah ya gudanar musu da wani abu na mu'ujiza sai ya aiwatar musu.

A karshe ayar tana kira ga mutane ne da su yi amfani da hankali da zurfafa tunani har su kai ga riskar gaskiya, ba su dogara da gani ko jin abubuwan al'ajabi da na gaibu ba, saboda matukar babu batun sanya hankali da tunani, to mutumin da ke son jayayya duk abin da ya gani zai nuna rashin amincewarsa da shi, sannan abin da bai gani ba kuwa zai yi musunsa.

A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-

{1} Annabawa suna gudanar da ma'amalarsu da mutane ne a kan gaskiya, kuma duk abin da ba za iya ba, to suna sanar da mutane.

{2} Yaki da wuce gona da iri da munanan akidu na shaci fadi yana daga cikin ayyukan Annabawa.

Shirinmu zai ci gaba ne ta hanyar ambaton aya ta 51 da ke cikin suratul-An'am kamar haka:-

وَأَنذِرْ بِهِ الَّذِينَ يَخَافُونَ أَن يُحْشَرُواْ إِلَى رَبِّهِمْ لَيْسَ لَهُم مِّن دُونِهِ وَلِيٌّ وَلاَ شَفِيعٌ لَّعَلَّهُمْ يَتَّقُونَ{51}

"Kuma ka yi gargadi ga wadanda suke jin tsõron a tãra su zuwa ga Ubangijinsu, ba su da wani mataimaki ko kuma mai cẽto baicin shi, {ka yi musu gargadi} ko sa ji tsoron {Allah}".

Ayar da ta gabata ta bayyana cewa: Mai gani da makaho ba su daidaita, don haka mai gani shi ke karbar gaskiya tare da zurfafa tunani, yayin da wannan ayar ke bayyana cewa: duk da kasancewar Manzon Allah yana kiran dukkanin mutane ne zuwa ga gaskiya, tare da musu gargadi kan sakamakon munanan ayyukansu, amma ba dukkan mutane ne ke karban gaskiya ba, sai dai wadanda ake musu gargadi kuma zukatansu suke shirye su karbi gaskiya, akalla za su yi tsammanin akwai hisabi kan ayyukan da suka aikata, don haka dole ne su kasance cikin shirin fuskantar hisabin ayyukansu.

Ayar tana ci gaba da bayyana cewa: Iyaka dai abin dogaron mutum a ranar kiyama shi ne Allah Madaukaki, saboda babu wani abu da zai tseratar da mutane a wannan ranar, wannan ita ce akidar mutanen da yake jin tsoron Allah tare da kauracewa duk wani laifi.

A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-

{1} Samun mai tarbiyya mai tausayi kuma mai dauke da tsarin tarbiyya ingantacciya baya isarwa wajen shiryar da mutane, dole ne sai mutanen sun kasance masu shirin karban gaskiya da nemanta kafin ta kasance ta yi musu tasiri.

{2} Imani da ranar kiyama da tsayiwa a gaban Allah suna daga cikin al'amuran da suke kara karfafa tsoron Allah.

Yanzu kuma zamu saurari aya ta 52 da ke cikin suratul-An'am kamar haka:-

وَلاَ تَطْرُدِ الَّذِينَ يَدْعُونَ رَبَّهُم بِالْغَدَاةِ وَالْعَشِيِّ يُرِيدُونَ وَجْهَهُ مَا عَلَيْكَ مِنْ حِسَابِهِم مِّن شَيْءٍ وَمَا مِنْ حِسَابِكَ عَلَيْهِم مِّن شَيْءٍ فَتَطْرُدَهُمْ فَتَكُونَ مِنَ الظَّالِمِينَ{52}

"Kuma kada ka kõri wadanda suke bauta wa Ubangijinsu sãfe da yamma, sunã masu neman yardarsa, babu wani abu daga hisãbinsu a kanka, kuma babu wani abu daga hisãbinka a kansu, har ka kõre su ka kasance daga azzãlumai".

Ya zo cikin tarihi cewa: Wasu daga cikin masu hannu da shuni a mushrikan Makkah sun gabatar da shawara ga Manzon Allah cewa; ya kori matalauta da suke tare da shi ta hanyar nisantarsu, misalin Ammar dan Yasir da Bilal sannan su kuma su kusance shi tare da yin imani da Musulunci, sai wasu daga cikin musulmai suka ce wa Manzon Allah ya amince da wannan shawara saboda hakan zai magance matsalar talauci da ke addabar musulmi, sai wannan ayar ta sauko tana magana da Manzon Allah cewa: Kada ka kuskura ka nisanci muminai na hakika da kae tare da su saboda janyo wasu kusa da kai domin hakan yana daga cikin nau'in zalunci.

Hakika wannan ayar tana kore duk wani tsarin nuna fifiko da bambanci tsakanin mutane, kuma nuna fifiko tsakanin mutane ya yi hannun riga da ruhin addini da ya yi kira zuwa ga 'yan uwantaka tsakanin mutane tare da jaddada cewa babu wanda ya fi wani daukaka a tsakaninsu saboda dukiya ko matsayi, duk daya suke a wajen Allah, iyaka dai Allah yana daukaka wanda ya fi ilimi da gudanar da aiki mai kyau ne a tsakanin mutane, don haka imani da aiki na gari shi ne ma'aunin daukaka a wajen Allah, ba dukiya da matsayi ba.

A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-

{1} Yin riko da mutumin da yake mai tsarkin zuciya da imani da gudanar da ayyuka na gwarai, koda matalauci ne; shi ya fi muhimmanci a kan janyo masu hannu da shuni da suke kafirai.

{2} Addinin Musulunci yana yaki da duk wani nau'in nuna bambanci da fifita wasu jama'a a kan sauran al'umma, saboda wani dalili na rayuwar duniya misalin dangantaka, dukiya, matsayi, launin fata da sauransu.

{3} Hisabin ayyuakan mutane yana wajen Allah kawai, don haka har Manzon Allah baya da hakkin yin hukunci kan ayyukan mutane, sakamakon haka ba mu da hakkin tantance cewa wannan dan aljanna ne wannan kuma dan wuta.

{4} Gudanar da addu'a da kankantar da kai ga Allah al'amari ne mai kima, matukar mutum ya gudanar da hakan ne da nufin neman kusanci ga Allah da neman yardansa.

To a nan ne shirin na mu ya zo karshe, sai kuma a gamo na gaba. Wassalamu alaikum warahmatullah.

Suratul An'am, Aya Ta 53-56 (Kashi Na 199)

Masu sauraro barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shirin da mu ke kawo mu ku fassarar ayoyin kur'ani mai girma. Da fatan za a kasance a tare da mu domin jin ci gabansa.

To yanzu sai a saurari aya ta 53 a cikin suratu An'ami.

وَكَذَلِكَ فَتَنَّا بَعْضَهُم بِبَعْضٍ لِّيَقُولواْ أَهَـؤُلاء مَنَّ اللّهُ عَلَيْهِم مِّن بَيْنِنَا أَلَيْسَ اللّهُ بِأَعْلَمَ بِالشَّاكِرِينَ{53}

" Da haka ne mu ka jarrabi sashensu saboda su ce shin wadannan ne wadanda Allah ya fifita su a tsakaninmu. Ashe Allah ba shi ne ya fi sanin masu godiya ba? "

A cikin shirin da ya gabata mun bayyana cewa mutane da dama suna zaton cewa annabawa su zama mala'iku ko kuma idan ma ba su zama mala'ikun ba to su yi kama da su a dabi'a, kamar rashin cin abinci da rashin bukatuwa da aure. Suna kuma tsammanin annabawa su zama daidai da bokaye irin na baya da su ke bada labaran abubuwa da su ka gushe da kuma masu zuwa anan gaba. Su zama masu yin wasu ayyuka na ban mamaki da su ka sabawa dabi'a.

To wannan ayar ma tana yin ishara ne da irin wannan tsammanin da mutane su ke da shi wanda ya yi kama da mafarkin tsaye. Tana cewa wasu mutanen suna da maanga ne da abin duniya da matsayi da mukami a cikin al'umma. Idan su ka ga yadda annabawa su ke rayuwa cikin sauki irin ta mutane sai su ka rika mamaki suna cewa shin wadannan su ne mutanen da Ubangiji ya fifita su a kanmu ya saukar da wahayi a gare su? Me zai sa ba a saukar da wahayi ga wadanda ya fi su ba?

Alkur'ani mai girma yana maida musu martani da cewa: Ba dukiya da mukami ko matsayi na duniya ba ne sharadin saukar wahayi akan wani mutum balle ya zamana ku ne za ku yanke hukunci akan wanda ya dace ya sauka. Ubangiji shi ne ya san wanda ya fi dacewa ta fuskar tsarkin niyya da hali wajen saukar da wahayi.

Abubuwan da za mu koya daga wannan ayar.

1-Daya daga cikin dalilan banbance-banbancen da ake da su a tsarin al'umma tsakanin talakawa da masu wadata shi ne jarabawa.

2-Da akwai talakawa masu yawan da su ke samun jin kan ubangiji saboda godiyar da su ke yi wa Allah. Kuma da akwai masu wadata da dama wadanda su ke jiji da kai saboda abinda su ke ganin suna da shi kuma ba su yi wa Allah godiya saboda haka su zama wadanda Allah ya ke la'anta.

Yanzu kuma sai ayoyi na 54 da 55 a cikin wannan sura ta An'am.

وَإِذَا جَاءكَ الَّذِينَ يُؤْمِنُونَ بِآيَاتِنَا فَقُلْ سَلاَمٌ عَلَيْكُمْ كَتَبَ رَبُّكُمْ عَلَى نَفْسِهِ الرَّحْمَةَ أَنَّهُ مَن عَمِلَ مِنكُمْ سُوءاً بِجَهَالَةٍ ثُمَّ تَابَ مِن بَعْدِهِ وَأَصْلَحَ فَأَنَّهُ غَفُورٌ رَّحِيمٌ{54} وَكَذَلِكَ نفَصِّلُ الآيَاتِ وَلِتَسْتَبِينَ سَبِيلُ الْمُجْرِمِينَ{55}

" Idan wadanda su ka bada gaskiya da Allah su ka zo gare ka ka ce musu amincin Allah a gare ku, kuma Ubangijinku ya tsaidawa kansa yin rahama, saboda haka wanda duk ya aikata mummuna daga cikinku bisa jahilci sannan kuma ya tuba ya kuma kyautata aiki, to shi- Ubangiji- mai gafara ne kuma mai rahama. Haka mu ke fayyace ayoyi domin hanyar masu laifi ta bayyana."

Wannan ayar taba bada umarni ne ga ma'aiki akan cewa duk yadda masu imani su ka yi sabo kada ya kore su, ya kuma rungume su da hannu biyu sannan ya yi musu sallama sannan kuma ya basu labarin cewa Allah zai yi musu gafara idan su ka tuba.

A bisa ka'ida a cikin al'ummar musulmi wajibi ne alaka a tsakanin al'umma da kuma jagorori ta zama ta kaunar juna da tausayawa. Wannan ita ce ka'idar da Allah ya sanya ta yin mu'amala da bayinsa hatta masu yin sabo. Yana karbar tubarsu idan sun tuba kuma yana umartar ma'aikinsa ya gaishe su.

Shakka babu kafuwar alaka tsakanin jagora da kuma al'umma bisa tausayawa da jin kai zai kawar da duk wata kiyayya da rike juna a zuci.

Abubuwan da za mu koya daga wadannan ayoyi.

1-Ziyarar annabi- hanya ce ta samun jin kan Allah kuma duk wanda ya ziyarci ma'aiki zai yi masa sallama.

2-Idan sabo ya zama bisa jahilci ne ba ganganci da naciya ba za a iya samun gafara akansa.

3-Tuban da ya ke zama karbabbe shi ne wanda ya kasance a tare da kyautata ayyuka.

4-Ubangiji ya luzumtawa kansa yin rahama sai dai nesantar zunubi da bayi za su yi ne zai sa su same shi.

Yanzu kuma za mu saurari aya ta56 a cikin suratu An'am.

قُلْ إِنِّي نُهِيتُ أَنْ أَعْبُدَ الَّذِينَ تَدْعُونَ مِن دُونِ اللّهِ قُل لاَّ أَتَّبِعُ أَهْوَاءكُمْ قَدْ ضَلَلْتُ إِذاً وَمَا أَنَاْ مِنَ الْمُهْتَدِينَ{56}

" Ka ce ni an hane ni da in bautawa abubuwan da ku ke kira sabanin Allah. Ka ce ba zan biyewa son ciyarku ba, idan na yi hakan na bace kuma ni ban kasance cikin masu shiriya ba."

A daidai lokacin da annabi ya ke yin kira zuwa ga tauhudi da kadaita Allah, mushrikai kuma su ke kiransa zuwa ga akidunsu na bautar gumaka. To a cikin wannan ayar ana fadawa annabi cewa ya fito fili kai tsaye ya shelanta musu cewa ba zai bautawa abinda su ke bautawa ba. Domin kuwa yin hakan yana nufin nesantar shiriya da kuma fadawa cikin bata.

Alkur'ani acikin wannan ayar yana bayyana bautar gumaka a matsayin biyewa son zuciya. Domin kuwa bautar gunki ba ta ginu kan wani dalili na hankali ba. Kuma ba ta tafiya kafada da kafada da hankali. Babu hankali ace mutum yana bautawa abinda shi ne da hannunsa ya kera shi.

Abubuwan da za mu koya daga cikin wannan aya.

1-Wajibi ne a fito fili a maida martani ga makiya akan buktunsu da su ka sabawa hankali, domin a akwar da duk wani shakku akansa.

2-Bai kamata mai isar da sakon addini ya zama yana biyewa son zuciyar mutane ba saboda ya gamsar da su.

Wannan shi ne karshen shirinmu na wannan lokacin sai kuma mun sake haduwa da ku a cikin wani shirin.

Suratul An'am, Aya Ta 57-60 (Kashi Na 200)

Masu sauraro barkahmu da sake saduwa da ku a cikin shirin hannunka mai sanda. Shiri ne dai wanda mu ke kawo mu ku fassarar ayoyin kur’ani mai girma. Muna fatan za a kasance a tare da mu domin jin yadda shirin zai kasance.

Yanzu sai a saurari ayoyi na 57 da 58 acikin wannan sura ta “An’am.

قُلْ إِنِّي عَلَى بَيِّنَةٍ مِّن رَّبِّي وَكَذَّبْتُم بِهِ مَا عِندِي مَا تَسْتَعْجِلُونَ بِهِ إِنِ الْحُكْمُ إِلاَّ لِلّهِ يَقُصُّ الْحَقَّ وَهُوَ خَيْرُ الْفَاصِلِينَ{57} قُل لَّوْ أَنَّ عِندِي مَا تَسْتَعْجِلُونَ بِهِ لَقُضِيَ الأَمْرُ بَيْنِي وَبَيْنَكُمْ وَاللّهُ أَعْلَمُ بِالظَّالِمِينَ{58}

“ Ka ce ni ina kan dalili bayyananne daga Ubangijina wanda ku ka karyata shi. A tare da ni babu abinda ku ke neman zuwansa da gaggawa, domin a hannun Allah ne hukunci ya ke, Allah ne mai hukunta gaskiya, shi ne mafificin masu hukunci. “ “Ka ce idan a ce a tare da ni da akwai abinda ku ke neman zuwansa da gaggawa to da tuni an zartar da hukunci tsakanina da ku. Allah shi ne mafi sani akan wadanda su ke azzalumai.”

Ayar karshe da mu ka karanta a shirin baya tana yin magana ne akan yadda masu bautar gumaka su ke kiran ma’aiki zuwa ga akidarsu da kuma martanin da Ubangiji ya maida musu. Ayar kuma tana ci gaba da kiran ma’aiki da fada musu cewa: Bautar gumaka bat a ginu akan wani dalili na hankali ba. Amma alkuranin da na ke karanta mu ku wanda ya zo ne daga Ubangiji yana fayyace gaskiya da kuma bayayna abinda shi ne bata. Sai dai duk da haka kun ki amincewa da shi kuna karyata shi. Haka nan kuna cewa idan har ni manzon Allah ne to in zo mu ku da azaba, alhali wannan azabar da ku ke son ta sauko mu ku ba a hannuna ta ke ba tana hannun ubangiji ne. Ubangijin da ya ke bayyana mu ku gaskiya ya ke kuma bayyana muku abinda shi ne bata. Idan kuwa da ace a hannuna ne azaba ta ke to da tuni an gama aiki. Jin kai ne na Allah da ya ke bada dama ga kafirai da mushirkai domin su tuba. Shi ya sa baya yin gaggawa wajen saukar da azaba. Darussan da su ke cikin wadannan ayoyin. 1-Kiran da annabawa su ke yi ya ginu ne bisa kwararan dalilai da kuma hujjoji bayyanannu, ba bisa zato da camfe-camfe ba. 2-Ubangiji ya umarci annabawa da su isar da sakonnin addini, ba nauyi ne da ya rataya a wuyansu ba su saukar da azaba akan kafirai da masu sabo. 3-Jinkirin saukar azaba bai kamata ya sa kafirai su kara nutsewa cikin barna da kuma kara girman kai ba, su dauke cewa an kyale su ne ko an mance da su.

Yanzu kuma sai aya ta 59 a cikin wannan sura ta An’am.

وَعِندَهُ مَفَاتِحُ الْغَيْبِ لاَ يَعْلَمُهَا إِلاَّ هُوَ وَيَعْلَمُ مَا فِي الْبَرِّ وَالْبَحْرِ وَمَا تَسْقُطُ مِن وَرَقَةٍ إِلاَّ يَعْلَمُهَا وَلاَ حَبَّةٍ فِي ظُلُمَاتِ الأَرْضِ وَلاَ رَطْبٍ وَلاَ يَابِسٍ إِلاَّ فِي كِتَابٍ مُّبِينٍ{59}

“Mabudan gaibu suna ga Allah babu wanda ya sansu sai shi. Yana sane da abinda ya ke kan doron kasa da abinda ya ke cikin kogi. Babu wani ganye da ya ke faduwa sai cikin saninsa da shi, kuma babu wata kwaya acikin duhun kasa ko danyen abu ko kekasasshe face suna cikin littafi bayyananne.”

Wannan ayar tana ci gaba da maida martani ne ga masu bautar gumaka cewa: duniyar nan da su ke gani bakidayanta tana tafiya ne a karkashin umarnin Allah. Tana kuma cewa abinda ya faku a wurinku a cikin sammai da kassai kuma wanda baku ganin muhimmancinsa kamar faduwar ganye daga jikin bishiya da bacewar kwayar hatsi a cikin kasa to dukkanin wadannan abubuwan a bayyane su ke a wurin Ubangiji, kuma yana sane da su sannan kuma uwa uba a rubuce su ke acikin littafi. Wato dukkanin abubuwan da su ke faruwa a wurin Allah a tsare su ke kuma suna tafiya ne bisa ilimi da hikima. Wannan duniyar da ku ke gani Allah ne ya yi ta cikin ilimi kuma yana sane da duk abinda ya ke faruwa acikinta komai girma da kaskantarsa. Babu kuma wani abu da ya ke faruwa acikinta ba tare da saninsa ba. Darussan da za mu koya daga wannan aya. 1-Ubangiji yana da masaniya akan dukkanin abinda ya ke gudana acikin duniya komai karantarsa. 2-Sanin gaibu Allah ne kadai ya kebanta da shi, babu wanda ya ke sanin gaibu ba tare da nufin Allah ba. 3-Duniya ta ginu ne bisa cikakken tsari da kuma manufa, kuma babu wani abu da ya gunada acikinta sai a karkashin ikon Ubangiji.

Yanzu kuma sai aya ta 60 acikin suratu An’am.

وَهُوَ الَّذِي يَتَوَفَّاكُم بِاللَّيْلِ وَيَعْلَمُ مَا جَرَحْتُم بِالنَّهَارِ ثُمَّ يَبْعَثُكُمْ فِيهِ لِيُقْضَى أَجَلٌ مُّسَمًّى ثُمَّ إِلَيْهِ مَرْجِعُكُمْ ثُمَّ يُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ{60}

“Shi ne wanda ya ke karbar ranku da daddare kuma yana sane da abinda ku ke aikatawa da rana, sannan kuma ya tashe ku a rana don ya hukunta ajali abin ambato. Ya zuwa gare shi ne makomarku sannan ya ba ku labarin abinda ku ka kasance kuna aikatawa.”

Idan ayar da ta gabata tana yin magana ne akan cewa Allah yana da cikakkiyar masaniya akan dukkanin abinda ya ke faruwa a duniya to wannan ayar tana yin magana ne akan cewa Allah yana da sane da rayuwar daidaikun mutane kuma shi ne mai tafiyar da ita. Shi ne wanda ya ke karbar rayukanku a lokacin da ku ke bacci kuma ya ke farkar da ku da rana domin ku amfana da rayuwa. Darussan da za a koya daga wannan aya. 1-Abisa mahangar kur’ani bacci yana nuni ne da mutuwa, farkawa daga bacci kuma yana nuni da rayar da matattu. 2-Mu kasance cikin shiri domin bada jawabi a gobe kiyama kuma mu yi mafani da gajeruwar rayumarsu ta duniya bisa hanya mafi dacewa. Anan mu ka kawo karshen wannan shirin da fatan za ku kasance a tare da mu nan gaba domin ci gaba daga inda mu ka tsaya.

Suratul An'am, Aya Ta 61-65 (Kashi Na 201)

Barkanmu da sake haduwa acikin wannan shirin da mu ke kawo mu ku fassarar ayoyin kur’ani mai girma. A shirin da ya gabata mun tsaya ne akan aya ta 60 a suratu An’am. Da fatan za a kasance tare da mu domin jin ci gaban shirin daga inda mu ka tsaya.

To yanzu sai a saurari aya ta 61 a cikin wannan sura ta An’am.

وَهُوَ الْقَاهِرُ فَوْقَ عِبَادِهِ وَيُرْسِلُ عَلَيْكُم حَفَظَةً حَتَّىَ إِذَا جَاء أَحَدَكُمُ الْمَوْتُ تَوَفَّتْهُ رُسُلُنَا وَهُمْ لاَ يُفَرِّطُونَ{61}

“ Shi ne mai rinjaye wanda ikonsa ya ke saman bayinsa, yana aiko mu ku da mala’iku masu kiyaye ku, har idan mutuwa ta zo wa dayanku sai ‘yan aikenmu su zo su karbi rayinsa, su ba su sakaci.”

A shirin baya mun ce rayuwa da mutuwa a hannun Allah su ke, kuma Allah ya ayyanawa kowane mahaluki lokaci kayyadajje na rayuwa. To a cikin wannan ayar alkur’ani mai girma yana fadin cewa: Allah yana aiko da mala’iku domin su rika kula da tafiyar da lamurranku bisa umarnin Ubangiji. Bisa izinin Allah wani sashe na mala’iku suna kare mutane daga bala’oi da dama yayin da wani sashe na mala’ikun su ke rubuta ayyukan da mutane su ke aikatawa. Idan kuma lokacin mutuwar mutum ya zo Allah zai aiko da wasu mala’ikun da za su karbi rayinsa kuma ba su yin sakaci kamar yadda kur’anin ya ambata. Wato ba su yin gaggawa wajen karbar rayi ko kuma yin jinkiri. Wannan ayar tana sake jaddada cewa Allah yana iko da dukkin rayuwar mutum babu wani sashe nata da ya ke faruwa nesa da ikonsa. Mutum kuwa ba shi da wani iko ko karfin da zai iya bijirewa ko kaucewa zama a karkashin ikon Allah. Shi ne abinda farkon ayar ya ke nufi da cewa: “Allah shi ne mai rinjaye wanda ikonsa ya ke saman bayinsa." Darussan da su ke cikin wannan aya. 1-Allah yana da cikakken iko akanmu, idan ya kyale mu muna aikata abubuwan da ba su dace ba to saboda ya badu dama ne mu tuba. 2-Mala’iku suna a matsayin ma’aikata ne na Allah acikin tsarin halitta da su ke sanya idanu akan ayyukan mutane.

Yanzu kuma sai aya ta 62 a cikin suratu An’am.

ثُمَّ رُدُّواْ إِلَى اللّهِ مَوْلاَهُمُ الْحَقِّ أَلاَ لَهُ الْحُكْمُ وَهُوَ أَسْرَعُ الْحَاسِبِينَ{62}

“Sannan a maida su zuwa ga Allah mamallakinsu na gaskiya. Kuma zartaccen hukunci na gareshi. Shi ne mafi gaggawar lissafi.”

Wannan ayar tana bada labarin karshen ayyukan mutum ne a doron kasa da kuma halartarsa a filin kiyama. Bayan mutuwa, mutane za su koma ne ga Ubangiji domin su ga ayyukan da su ka yi a duniya a tsare a cikin littatafan ayyukansu. Idan har tambaya za ta fadowa mutum cewa ya za a yi a iya kiyaye ayyukan da dukkanin mutane su ka yi a tsawon tarihin rayuwarsu a doron kasa, to jawabinta ya zo da fadin Allah cewa shi ne mafi saurin masu lissafi. Kuma dama ayoyin baya sun yi magana akan cewa dukkanin ayyukan da kowane mutum ya ke yi ana rubuta su daya bayan daya a cikin kowace kyaftawar idanu. Saboda haka kowane mutum zai karbi littafin ayyukansa wanda akanshi ne zai shiga aljanna ko wuta. Ya zo acikin riwayoyi cewa Ubangiji zai yi wa dukkanin mutane hisabi ne a lokaci guda kamar yadda a duniya ya ke baiwa dukkanin halittu arzikinsu a lokaci guda. Abubuwan da za mu koya daga cikin wadannan ayoyi. 1-Ubangiji ne kadai mai yi wa mutum hukunci domin kuwa shi ne mamallakinsa na gaskiya dukkanin halittu kuwa bayinsa ne. 2-Ubangiji ne mamallakin bayi na gaskiya babu wani mahaluki da ya ke a matsayin mamallakin wani mutum, ko ya zama mai jibintar lamarinsa sai iwanda Allah ya dora akan wannan matsayin kamar iyaye maza da mata, kamar annabawa da waliyan Allah.

Yanzu kuma sai mu saurari ayoyi na 63 da kuma 64 a wannan sura ta An’am.

قُلْ مَن يُنَجِّيكُم مِّن ظُلُمَاتِ الْبَرِّ وَالْبَحْرِ تَدْعُونَهُ تَضَرُّعاً وَخُفْيَةً لَّئِنْ أَنجَانَا مِنْ هَـذِهِ لَنَكُونَنَّ مِنَ الشَّاكِرِينَ{63} قُلِ اللّهُ يُنَجِّيكُم مِّنْهَا وَمِن كُلِّ كَرْبٍ ثُمَّ أَنتُمْ تُشْرِكُونَ{64}

“Ka ce wanene zai tseratar da ku daga duhun sarari da na kogi? Ku ke kiranshi a sarari da boye, idan –Ubangiji- ya tseratar da mu daga wannan-duhu- za mu kasance cikin masu yin godiya." " Ka ce Allah ne ya ke tseratar da ku daga gare shi kuma daga kowane irin bakin ciki, amma kuma ku ke yin shirka.”

Kasantuwar mutum mai tsoron duhu ne ya ke kuma shiga cikin tashin hankali saboda shi, kur’ani mai girma acikin wannan ayar ya ke fadin cewa: Alokuta da dama kuna kasantuwa cikin tsoro da razana a cikin sarari ne ko a cikin kogi, wato a lokacin da baku da wani mahaluki mai taimako kuma babu alamar za ku iya samun wata hanyar tsira, abisa fitirarku kuna komawa ga Allah kuna kuma neman taimako daga gare shi. A wani lokacin kuna yin addu’a da fatar baki wani lokacin kuma kuna yi a cikin zuci. Mai makon ace idan bukata ta biya a koma ga Allah da watsi da kafirci, sai a mance da shi a koma kan shirka. Abubuwan da za mu koya daga wadannan ayoyi. 1-Daya daga cikin abubuwan da su ke kusanta mutum ga Allah da nesanta shi daga kafirci shi ne wahala da kuma matsaloli a rayuwa. Kamar kuma yadda jin dadi da hutu ya ke sa mutum ya gafala daga Allah da kuma ni’imominsa. 2-Mutum mai karya alkawalin da ya dauka ga Allah ne wannan kuma shi ne hali mafi muni.

Yanzu kuma sai aya ta 65 acikin wannan sura ta An’am.

قُلْ هُوَ الْقَادِرُ عَلَى أَن يَبْعَثَ عَلَيْكُمْ عَذَاباً مِّن فَوْقِكُمْ أَوْ مِن تَحْتِ أَرْجُلِكُمْ أَوْ يَلْبِسَكُمْ شِيَعاً وَيُذِيقَ بَعْضَكُم بَأْسَ بَعْضٍ انظُرْ كَيْفَ نُصَرِّفُ الآيَاتِ لَعَلَّهُمْ يَفْقَهُونَ{65}

“Ka ce shi mai iko ne akan ya aiko muku da azaba daga samanku ko daga karkashin kafafunku ko ya cudanya ku zuwa kungiya-kungiya ya dandanawa junanaku azabar sashe. Dubi yadda mu ke bayyana ayoyi ko za su fahimta.”

Wannan ayar tana yin bayani ne akan fushin Ubangiji da kuma azabarsa. Tana fadin cewa jin kan Allah yana tare da fushinsa kafada da kafada. Idan mutum ya kusanci Ubangiji zai sami jin kan nashi idan kuwa ya juya wa Ubangiji baya sannan ya rungumi shirka to zai fuskanci fushin Ubangiji da kuma azabarsa. Azaba ce wacce za ta mamaye mutum daga sama da kasa da hagu da dama. Yin nisa daga tauhidi yana tarwatsa hadin kan mutane ya maida su zama kungiya-kungiya su zama masu fada da juna da zubar da jini. Haka nan kuma nesantar yin aiki da umarnin Ubangiji acikin al’umma yana jefa wannan al’ummar fadawa cikin matsala da maida mutane su zama aji-aji na masu mahaukaciyar wadata da kuma masu bakin talauci. Abubuwan da za mu koya daga wannan aya. 1-kada mu gafala daga iko da karfin Ubangiji. Kada iko da karfi da kuma matsayin da mu ke da su, su shagaltar da mu, domin idan fushin Allah ya sauka to ba za mu iya daukarsa ba. 2-Rabuwar kawuna yana daga cikin tasirin shirka wanda ya ke tarwatsa kan al’umma ya kuma share fagen yaki a tsakanin al’umma da zubar da jini. Karshen shirin namu na wannan lokacin kenan da fatan za a kasance a tare da mu a lokaci na gaba domin jin ci gabansa.

Suratul An'am, Aya Ta 66-70 (Kashi Na 202)

Masu sauraro barkanmu da saduwa da ku a cikin wannan shirin na Hannunka Mai Sanda. Shiri ne dai wanda mu ke kawo mu ku fassarar ayoyin kur'ani mai girma. Da fatan za a kasance a tare da mu domin sauraron ci gaban shirin daga inda ya tsaya a baya.

Yanzu za mu saurari ayoyi na 66 da kuma 67 acikin wannan sura ta An'am.

وَكَذَّبَ بِهِ قَوْمُكَ وَهُوَ الْحَقُّ قُل لَّسْتُ عَلَيْكُم بِوَكِيلٍ{66} لِّكُلِّ نَبَإٍ مُّسْتَقَرٌّ وَسَوْفَ تَعْلَمُونَ{67}

"Mutanenka- ya annabi- sun karyata shi-kur'ani-alhali shi gaskiya ne. Ka ce ni ba wakili ba ne a gare ku. Kowane labari yana da lokacinsa. Da sannu za ku sani."

A cikin shirin da ya gabata an yi bayani akan cewa ma'aiki yana gargadin mutane akan hatsarin da ya ke tattare da sabawa umarnin ubangiji. Da kuma mummunan sakamakon da ya ke tattare da shi a ranar kiyama. To wannan ayar tana fadin cewa ya annabi mutanenka wato kuraishawa suna karyata wannan zancen na gaskiya mai tattare da haske, suna kuma karyata alkiyama wacce gaskiya ce kuma a kodayaushe alkur'ani yana yin magana akanta. Ka kuma fada musu cewa aikinka shi ne isar da sakon wahayi amma ba wanda zai tilastawa mutane su karbi imani ba. Mutane ne wadanda za su bada gaskiya da kansu su karbi zancen Ubangiji. Ayar ta ci gaba da cewa: Duk abinda ma'aiki ya bada labari dangane da saukar azaba tabbas zai tabbata idan lokacinsa ya zo, kuma da sannu za ku gani da idanunku. Saboda haka ku daina gaggawa kuma kada ku zaci cewa inkarin gaskiya zai hana azabar Allah sauka akanku. Allah yana baiwa bayinsa dama ce a rayuwa domin su yi nadama su tuba. Abubuwan da za mu koya daga wadannan ayoyin. 1-Wanda duk ya fahimci gaskiyar zancen da ma'aiki ya ke yi sannan kuma ya karyata shi, to ya kwana cikin shirin azaba mai tsanani. 2-Karyata gaskiya da makiya za su yi, ba zai rage kaifin gaskiyar kur'ani ba, komai tsananin inkarinsu.

Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 68 acikin wannan sura ta An'am.

وَإِذَا رَأَيْتَ الَّذِينَ يَخُوضُونَ فِي آيَاتِنَا فَأَعْرِضْ عَنْهُمْ حَتَّى يَخُوضُواْ فِي حَدِيثٍ غَيْرِهِ وَإِمَّا يُنسِيَنَّكَ الشَّيْطَانُ فَلاَ تَقْعُدْ بَعْدَ الذِّكْرَى مَعَ الْقَوْمِ الظَّالِمِينَ{68}

"Idan ka ga wadanda su ke kutsawa cikin ayoyinmu ( suna isgili) to rabu da su har sai idan sun shiga wani zancen na daban. Idan shaidan ya mantar da kai to kada ka zauna da azzaluman mutane bayan tunawa."

Wannan ayar tana yin magana ne da musulmi,kuma mabiya annabi, a cikin sigar yin kira ga ma'aiki cewa: "Idan ka je wata majalisa ka ji ana yin isgili da ayoyin kur'ani da kuma hukunce-hukuncen addini, idan har za ka iya to ka sauya jigon da ake yin magana akansa. Idan kuwa ba za ka iya ba to ka fice daga wannan majalisa kada ka zauna a inda masu inkarin gaskiya za su yi wa addini isgili. Idan kuwa ka mance ka ci gaba da zama to da zarar ka tuna sai ka kakkabe rigarka ka fice daga cikin wannan majalisa. Gabagadi wannan ayar tana hana mu zama a wuraren da masu sabo da shirka su ke. Idan kuma ba ka sani ba kuma baka lura da cewa isgili ake yi wa addini ba a wurin, to da zarar ka farga sai ka yi aiki da hani da munanan ayyuka ka sauya jigon da ake magana akansa. Ko kuma ka fice da salo irin na nuna rashin jin dadi, koda kuwa danginka ne a wurin. Abubuwan da za mu koya daga wannan aya. 1-Mu zama masu kishin addini kada mu bada dama makiya su yi wa abubuwa masu tsarki na addini sigili. 2-Nuna rashin jin dadi acikin majalisun da ake aikata sabo wani salo ne na hani da munanan ayyuka.

Yanzu kuma sai a saurari aya ta 69 acikin wannan sura ta An'am.

وَمَا عَلَى الَّذِينَ يَتَّقُونَ مِنْ حِسَابِهِم مِّن شَيْءٍ وَلَـكِن ذِكْرَى لَعَلَّهُمْ يَتَّقُونَ{69}

"Kuma babu laifi da zai hau kan wadanda su ke tsoron haduwarsu da Allah ( idan sun zauna da su) sai dai kuma abinda ya ke kansu shi ne su yi musu wa'azi don su ji tsoron Allah."

Abinda wannan ayar ta ke nufi shi ne cewa wadanda su ka je wuri irin wannan da zummar yin wa'azi da gargadi to zunubin masu sabon ba zai shafe su ba, domin ba sun ne waurin ne da zummar yin sabo ba. A fili ya ke cewa ba kowane mutum ne zai je wurare irin wadannan da zummar kawo gyara, domin kuwa abu ne mai sauki a gare shi ya narke a ciki. Wanda zai iya zuwa wuri irin wannan da zummar kawo gyara shi ne mutum mai tsoron Allah wanda kuma da wuya a iya sauya masa tunani, shi ne wanda ya cancanci ya halarci wannan wurin. Abubuwan da za mu koya daga wannan aya. 1-Mu nesanci zama da mutane masu yasasshen zance, domin hakan yana a matsayin garkuwa ne ga mutum. 2-Mutanen kwarai masu karfin imani su zama cikin shiri domin gyara masu karkataccen tunani, su kuma rika inda su ke domin shiryar da su. Yanzu kuma sai aya ta 70 acikin wannan sura ta An'am.

وَذَرِ الَّذِينَ اتَّخَذُواْ دِينَهُمْ لَعِباً وَلَهْواً وَغَرَّتْهُمُ الْحَيَاةُ الدُّنْيَا وَذَكِّرْ بِهِ أَن تُبْسَلَ نَفْسٌ بِمَا كَسَبَتْ لَيْسَ لَهَا مِن دُونِ اللّهِ وَلِيٌّ وَلاَ شَفِيعٌ وَإِن تَعْدِلْ كُلَّ عَدْلٍ لاَّ يُؤْخَذْ مِنْهَا أُوْلَـئِكَ الَّذِينَ أُبْسِلُواْ بِمَا كَسَبُواْ لَهُمْ شَرَابٌ مِّنْ حَمِيمٍ وَعَذَابٌ أَلِيمٌ بِمَا كَانُواْ يَكْفُرُونَ{70}

" Ka rabu da wadanda su ka dauki addininsu wasa da sharholiya, rayuwar duniya kuma ta rude su. Ka yi gargadi da shi ( kur'ani) saboda kada a jarrabi rai da abinda ta aikata wanda ba shi da wani mamallaki ko maiceto ban da Allah. Koda kuwa-ran ta bada kowane irin fansa ba za a karba ba daga gare ta. Wadancan su ne wadanda aka kange- domin yi musu azaba- saboda abinda su ka aikata. Suna da abin sha na tafasasshen ruwa da kuma azaba mai radadi saboda abinda su ka zamanto suna kafircewa da shi."

Ayar da ta gabaci wacce aka saurara yanzu ta yi magana ne akan masu karkataccen tunani da sharadin zama da su a majalisa guda. To wannan ayar kuwa tana yin kira ne ga ma'aiki da ya yanke alaka da mutane irin wadanncan ya kuma bayyana kin jininsa da ayyukan da su ke yi da kuma kubuta daga gare su. Sai dai a lokaci guda idan har da dama ayi musu wa'azi da kuma fada musu gaskiya. Idan sun yi taurin kai kuma basu yi nadama ba balle kuma su tuba, to a yi watsi da su. Idan masu addini su na kallon masu bautar duniya a matsayin masu sharholiya, to su kuwa masu bautar duniyar suna yin isgili da addini. Suna isgili da ayoyin ubangiji da wasa da su. Abubuwan da za mu koya daga wannan aya. 1-A cikin al'ummar musulmi wajibi ne a rika ladabtar da wadanda su ke yi wa addini isgili, domin kada su rika watsa tunaninsu a cikin al'umma. 2-Son duniya ne ya ke a rika yi wa addini isgili da kuma inkarin abinda ya ke ginshiki ne na addini. Karshen shirin kenan sai mun sake hadewa da ku a cikin wani shirin.

Suratul An'am, Aya Ta 71-74 (Kashi Na 203)

Masu sauraro barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shirin da mu ke kawo mu ku fassarar ayoyin kur’ani mai girma. Da fatan za ku kasance a tare da mu domin jin ci gabansa daga inda mu ka tsaya a baya.

Yanzu sai a saurari ayoyi na 71 da kuma 72 a cikin wannan sura ta An’am.

قُلْ أَنَدْعُو مِن دُونِ اللّهِ مَا لاَ يَنفَعُنَا وَلاَ يَضُرُّنَا وَنُرَدُّ عَلَى أَعْقَابِنَا بَعْدَ إِذْ هَدَانَا اللّهُ كَالَّذِي اسْتَهْوَتْهُ الشَّيَاطِينُ فِي الأَرْضِ حَيْرَانَ لَهُ أَصْحَابٌ يَدْعُونَهُ إِلَى الْهُدَى ائْتِنَا قُلْ إِنَّ هُدَى اللّهِ هُوَ الْهُدَىَ وَأُمِرْنَا لِنُسْلِمَ لِرَبِّ الْعَالَمِينَ{71} وَأَنْ أَقِيمُواْ الصَّلاةَ وَاتَّقُوهُ وَهُوَ الَّذِيَ إِلَيْهِ تُحْشَرُونَ{72}

“ Ka ce shin za mu rika kiran wani ba Allah ba wanda ba ya amfanarmu kuma baya cutar da mu, ya zaman mun juya da baya, bayan da Allah ya shiryar da mu, tamkar wanda shaidanu su ka batar da shi ya dimance, yana da abokai suna kiransa zuwa shiriya- suna cewa- kazo wurinmu. Ka ce shiriyar da Allah ya ke yi ita ce shiriya, an kumarce mu mu mika wuya ya zuwa ga Ubangijin talikai. “An umarce ku ku tsaida salla kuma ku ji tsoron Allah, shi ne wanda za a tara ku ya zuwa gare shi.”

A cikin shirye-shiryen da su ka gabata mun ambaci cewa mushrikai da masu bautar gumaka suna kokarin jawo hankalin wadanda ba su dade da musulunta ba domin maida su ruwa. Suna kuma yin isgili da annabi da kuma koyarwar kur’ani. To wannan ayar tana bada umarni ne ga ma’aiki da cewa ka maida musu martani kai tsaye da cewa: Su yi wa lamirinsu tambaya ko abinda ya fi dacewa shi ne mai makon bautar Allah shi ne komawa ga wasu abubuwa da wasu mutane da ba su amfanarmu ko cutar da mu. Idan wadanda su ka musulunta su ka ja da baya zuwa ga bautar gumakan da su ka yi bankwana da ita, to zai zama ci baya ne a wurinsu ba ci gaba ba ta fuskar kamala. Larabawan jahiliyya sun yi imani da cewa mutumin da ya ke bacewa a cikin sahara, shaidanu ne su ka yi masa kwantan bauta akan hanya su ke yawo da hankalinsu kuma su ke sa shi yin dimuwa. Wannan ayar ta kur’ani tana kafa musu misali ne da abinda su ka sani kuma su ka yi imani da shi. Yana fada musu cewa, yin ridda daidai ya ke da yin dimuwa da rashin sani alkibla. A karshen ayar tana cewa, hanya guda daya tilo ta samun tsira daga bata da dimuwa shi ne mika kai ga umarnin Ubangiji da hukunce-hukuncensa, domin kuwa Allah shi ne shiryar da mutane kuma samun yardarsa yana da muhimmanci wajen samarwa mutum da sa’ada. Abubuwan da za mu koya daga wannan aya. 1-Gumaka basu da wani amfani ga kawunansu balle kuma ga wasunsu. Saboda haka wane dalili zai sa a rika rokonsu da kiransu? 2-Dukkanin duniya da abinda ke cikinta sun mika kai ga Allah. Wajibi ne a gare mu mika kai ga Allah domin dace da sauran halittun da su ka riga su ka mika kai.

Yanzu kuma sai aya ta 73 a cikin wannan sura ta An’am.

وَهُوَ الَّذِي خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضَ بِالْحَقِّ وَيَوْمَ يَقُولُ كُن فَيَكُونُ قَوْلُهُ الْحَقُّ وَلَهُ الْمُلْكُ يَوْمَ يُنفَخُ فِي الصُّوَرِ عَالِمُ الْغَيْبِ وَالشَّهَادَةِ وَهُوَ الْحَكِيمُ الْخَبِيرُ{73}

“Shi ne wanda ya halicci sammai da kasa bisa gaskiya ranar da ya ke cewa da abu samu, sai ya samu. Maganarsa ce gaskiya mulki na gare shi ranar da ake yin busa acikin kaho, masanin abinda ya ke fake da sarari shi ne mai hikima kuma gwani.”

Ayoyin baya sun yi magana ne akan mika kai ga Allah da kuma aiki da hukunce-hukuncensa. To wannan ayar tana kafa kwakkwaran dalili ne akan cewa Allah shi ne makagin duniya da halitta bakidaya. Shi ne ya kirkiri sammai da kasa kuma zai tashi duniya ya tsaida ranar kiyama. Idan har kun yi imani da hakan to wajibi ne ku mika kai a gare shi. Darussan da su ke cikin wannan aya. 1-Halittar duniya da Allah ya yi tana da manufa kuma ta ginu ne bisa hikima. Ubangiji ya halicci kowane samamme ne bisa maslaha. 2-Hukunce-hukuncen Allah sun kasance ne bisa ilimi da hikima, saboda haka wajibi tafiyar da iko ya kasance bisa hikima.

Yanzu kuma sai aya ta 74 a cikin wannan sura ta An’am.

وَإِذْ قَالَ إِبْرَاهِيمُ لأَبِيهِ آزَرَ أَتَتَّخِذُ أَصْنَاماً آلِهَةً إِنِّي أَرَاكَ وَقَوْمَكَ فِي ضَلاَلٍ مُّبِينٍ{74}

“Ambaci lokacin da Ibrahim ya fadawa babansa Azara cewa: Don me ka ke rikon gumaka a matsayin iyayengiji. Ina ganinka da mutanenka acikin bata bayyananne.”

Wannan ayar tana fadawa ma’aiki ne cewa, kada ka zaci cewa mutanen makka ne kadai su ka yi bautar gumaka a zamanin annabi Ibrahim ma wani sashe na mutane sun bautawa gumaka. Kuma annabi Ibrahim ya fadawa wanda ya ke akarkashinsa, wanda kuma ga dukkanin alamu shi ne jagoran mutanensa, cewa me ya sa ka ke bautar gumaka mai makon ubangiji? Wannan abinda ka ke yi karkace hanya ne. Azara kawu ne ga annabi Ibrahim ba shi ne mahaifinsa ba, saboda shi ne wanda ya riki shi, kur’ani ya kira shi da mahaifinsa. Abubuwan da za mu koya daga wannan aya. 1-Nauyi ne da ya rataya a wuyan ‘Da, ya ki karbar akidojin mahaifinsa da su ke karkatattu, ya kuma yi amfani da kwararan dalilai wajen gamsar da shi akan karkacewar akidojin. 2-Al’adun da akidojin da su ke gurbatattu abin yin watsi da su ne duk da cewa suna da dadewa domin kuwa ma’auni shi ne gaskiya ba dadewa ko yawa ba. Karshen wannan shirin kenan, sai kuma mun sake haduwa da ku a cikin wani shirin. An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa

Search... Shafin Farko RSS Mobile Application Labarai Babban Labari Sharhin Labarai Dangane Da Radiyo Tarihin Radiyo Jadawali Ma'aikatanmu Shirye Shirye Matambayi Hannunka Mai Sanda Iran A Mako Afirka A Mako Dubi A Rayuwar Salihai Kyawawan Dabiu Mitoci Musamman Sauti Breaking News Ganawar Shugaba Buhari Na Najeriya Da XI Jinping Na China Bin Kadun Cin Zarafin Musulmin Turai Ta Hanyar Doka Babban Mai Bayar Da Fatawa A Quds Ya Gargadi Yahudawan Isra'ila Kasashen Kongo Da Burundi Sun Sanar Da Shirin Aiki Tare Don Fada Da 'Yan Tawaye Shugabar Kasar Brazil, Rouseff, Na Fuskantar Barazanar Tsigewa A Majalisar Kasar UNICEF: Ana Samun Karuwar Masu Kunar Bakin Wake Tsakanin Yara A Yammacin Afirka Jagora Ya Ja Kunnen Kasashen Turai Saboda Goyon Bayan Ta'addanci Da Wasunsu Suke Yi Shugaba Ruhani: Akwai Bukatar Aiki Tare Wajen Fada Da Ta'addanci Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Gargadi Kan Bullar Masifar Cuta A Kasar Afrika Ta Tsakiya Amnesty Int. Ta Bukaci Sojoji Su Yi Bayani Kan Kisan Gilla A Zaria


Tuesday, 19 September 2017


whatsapp


Wasikar Jagora Ga Matasan Turai


letter4u



Ziyarar Buhari


Ko Kun San

Ko Kun San Na (348) 12 Ga Watan Esfan Ahekara Ta 1394 Hijira Shamsia 2016-02-28 Yau Laraba 12-Esfand-1394 Hijira Shamsia=22-Jamada-Ula-1437 Hijira Kamria=02=Maris-2016 Miladia. KomKun San Na (347) 11 Ga Watan Esfand -shekara Ta 1394 Hijirta Shamsia. 2016-02-28 Yau Talata 10 ga watan Esfand -Shekara Ta 1394 Hijira Shamsia wacce ta yindai dai da 29-Jamada ula.1437 Hijira Kamaria. … Yemen


Polls

Mene ne Ra'ayinka Kan Katse Shirye-Shiryen Gidajen Talabijin Na Iran Da Kasashen Yammaci Suka Yi

Wani Bangare Ne Na Makircinsu Kan Iran
Wani Kokari Ne Na Rufe Muryar Gaskiya
Saboda Rage Kaifin Tasirin Tashoshin Ne
Kasashen Yammacin Suna Da Hakkin Yin Hakan

Vote Social Networks

facebook Language Selector

عربي English Français Kiswahili Español Other languages Copyright © 2017 hausa. All Rights Reserved. To Top ▲

Suratul An'am, Aya Ta 80-83 (Kashi Na 205)

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da war haka barkammu da sake saduwa cikin shirimmu na hannunka mai sanda shiri wanda yake dubi cikin wasu ayoyin Alkur'ani mai girma don su zama fitila a cikin rayuwarmu. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.

      • .

To bari mu fara shirimmu nay au da sauraron aya ta 80 daga cikin surar An'aam kamar haka.

وَحَآجَّهُ قَوْمُهُ قَالَ أَتُحَاجُّونِّي فِي اللّهِ وَقَدْ هَدَانِ وَلاَ أَخَافُ مَا تُشْرِكُونَ بِهِ إِلاَّ أَن يَشَاءَ رَبِّي شَيْئاً وَسِعَ رَبِّي كُلَّ شَيْءٍ عِلْماً أَفَلاَ تَتَذَكَّرُونَ{80}

80-Kuma mutãnensa suka yi musu da shi. Ya ce: "Shin kunã musu da ni a cikin sha'anin Allah, alhãli kuwa Yã shiryad da ni? Kuma bã ni tsõron abin da kuke yin shirki da shi, fãce idan Ubangijina Yã so wani abu. Ubangijina Ya yalwaci dukkan kõme da ilmi. Shin, ba zã ku yi tunãni ba?"

A cikin shirin da ya gabata mun yi ishara da yadda Annabi Ibrahim (a) ya tafi tare da masu bautan gomaka, rana, taurari, wata, da sauransu akan cewa su ma iyayen gijine ne, amma daga baya ya nuna masu ta hanyar fitira da kuma dabi'ar halittar mutum cewa wadannan ba su isa su zama iyayen giji ba. Basu isa su zama sune suke fayyace makomar dan'adam ba. A sarari ya fito ya bayyana masu cewa ni ubangiji na shi ne wanda ya halicci sammai da kassai. Kuma shi ne yake fayyace makomar dan'adam ni shi ne ke bautatwa. A cikin wannan ayar mun ji yadda mutanensa suka yi ca akansa. Ba wai sun ki amincewa da shi kadai ba, aa suna son su kauda shi daga tafarkin tauhidi, tafrkin bautawa Allah shi kadai. Yana ce masu, ta yaya zai dawo daga bautawa ubangijina bayan ya shiryatar da ni, bayan na gane shi kuma ta ya ya zan bi akidunku wadanda basa da asasi mai karfi?. Ya kara da cewa, kuma yakamata ku sani cewa idan wani abu na cutarwa ya samine a kan yafarkin da nake a kai, kada ku zaci cewa gumakanku ne suka cutar da ni. A'a shi ubangijina ba bu abinda zai faru ba tare da amincewarsa ba. Ya gewaye kome da ilminsa. Don haka a cikin wannan ayar muna iya daukan darussa kamar haka. 1. Mumini wanda yake kan ikidar tauhidi baya jin tsoron cewa shi kadai yake, ko da kuwa dukkan mutane sun taru sun kaurace masa ne. 2. Yana daga cikin cikekken Imani da Allah, rashin jin tsoron waninsa ko menen shi kuwa.

Yanzun kuma mu saurari karatun aya ta 81 cikin surar An'am kamar haka:

وَكَيْفَ أَخَافُ مَا أَشْرَكْتُمْ وَلاَ تَخَافُونَ أَنَّكُمْ أَشْرَكْتُم بِاللّهِ مَا لَمْ يُنَزِّلْ بِهِ عَلَيْكُمْ سُلْطَاناً فَأَيُّ الْفَرِيقَيْنِ أَحَقُّ بِالأَمْنِ إِن كُنتُمْ تَعْلَمُونَ{81}

81-"Kuma yãyã zan ji tsõron abin da kuka yi shirki da shi, kuma ba kwu tsõron cẽwa lalle ne kũ, kun yi shirki da Allah, abin da (Allah) bai saukar da wata hujja ba game da shi? To, wane bangare ne daga sãssan biyu mafi cancanta da aminci, idan kun kasance kunã sani?"

A ciki gaba da basu hujjoji na hankali, Annabi Ibrahim (a) ya ce da su, ta ya ya ku bakwa ji tsron Allah bayan shi ya halicce ku? Sannan kuna son ni na ji tsoron gumakanku?.Ta yaya zaku bautawa gumaka wadanda ubangijin da ya halicceku bai saukar da wata hujja ta bauta masu ba?, Mai hankali yakamta ya san cewa mahaliccin sammai da kassai ne yakamata a ji tsoronsa ba gumaka ba. Muna iya daukan darussa a cikin wannan ayar kamar haka. 1. Asasin ko wace akida ta gaskiya dole ne ya kasance ta hanyar amfani da hankali. Ba bin zace zace ko mafarki da tunanin da babu gaskiya cikinsa ba. 2. A cikin jayayya da mushrikai ko kuma wadanda kuke sabanin cikin akida da su, a ko yauce ku yi amfani da tambaya wajen dawo da hanakalinsa cikin kwatanta gaskiya da kariya. Ya zama shi ne zai bada amsa wa kansa daga karshe.

Yanzun kuma mu saurari karatun aya ta 82 cikin surar An'am kamar haka:

الَّذِينَ آمَنُواْ وَلَمْ يَلْبِسُواْ إِيمَانَهُم بِظُلْمٍ أُوْلَـئِكَ لَهُمُ الأَمْنُ وَهُم مُّهْتَدُونَ{82}

82-"Wadanda suka yi ĩmãni, kuma ba su gurbata ĩmãninsu da zãlunci ba, wadannan sunã da aminci, kuma sũ ne shiryayyu."

Daga karshe a cikin jayayyar Annabi Ibrahim (a) da mutanensa, da kuma tambayoyin da ya jera masu, wadanda suka kasa bada amsarsu. Alkur'ani mai girma ya bayyana cewa, wadanda sukayi imani da Allah anan duniya basu gurbata imaninsu da shirka ba, kuma a cikin ayyukansu basu fada cikin zalunci ba to a ranar lahira su ne suke cikin aminci, babu tsoro a garesu. Don haka muna iya daukan darussa daga cikin wadannan ayoyi kamar haka. 1. Abinda ya fi muhimmanci a cikin rayuwar mumini shi ne kiyaye akidarsa da imaninsa da kuma wanzuwa kan tafarkin gaskiya 2. Aminci na gaskiya shi ne aminci karkashin imani a ranar da babu wanda zai sami aminci sai wanda yake da imani. ranar lahira kenen.

Yanzun kuma mu saurari karatun aya ta 83 daga cikin surar An'am kamar haka.

وَتِلْكَ حُجَّتُنَا آتَيْنَاهَا إِبْرَاهِيمَ عَلَى قَوْمِهِ نَرْفَعُ دَرَجَاتٍ مَّن نَّشَاء إِنَّ رَبَّكَ حَكِيمٌ عَلِيمٌ{83}

83-Kuma wancan ita ce hujjarMu, Mun bayãr da ita ga Ibrãhĩma a kan mutãnensa. Munã daukaka wanda Muka so da darajõji. Lalle ne Ubangijinka Mai hikima ne, Masani.

Daga karshen jayayyar Annabi Ibrahim (a) da mutanensa Allah ya bayyana cewa shi ne ya tsarawa annabinsa Ibrahim (a) wannan jayayyar bisa wahayin da ya yi masa. Sannan mutane masu hankali kuma yakamata su fahinci cewa Allah yana zaben Annabawa ne a cikin wadanda suka fi cancanta daga cikin mutane, don hikimarsa. Don su zama abin koikoyo ga sauran mutane. Kuma a ko yauce mutane suna bukatar wanda zai jagorancesu ya nuna masu hanyar gaskiya da shiriya. Don haka a cikin wannan ayar muna iya daukan darussa kamar haka. 1. Allah yana daukaka darajar mutane ne bisa hikimarsa da kuma ilmin da ya basu. Ba bisa yawan dunkiya da ikon da suke da shi a cikin al-ummar ba. 2. Tafarkin kiran Annabawa ya ginu ne bisa tabbatar da hujja wanda hankali yake iya ganewa ya fahinta. Ba bisa abinda mutane suka gada ba ko al'adunsu ba. Masu sauraro anan kuma zamu dasa aya a cikin shirimmu nay au sai kuma wani shirin idan Allah ya kaimu a huta lafita wassalamu alaikum warahmatullahi wa barakatuhu.

Suratul An'am, Aya Ta 84-90 (Kashi Na 206)

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da war haka barkammu da sake saduwa cikin shirimmu na hannunka mai sanda shiri wanda yake dubi cikin wasu ayoyin Alkur'ani mai girma don su zama darasi a cikin rayuwarmu. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.

      • .

To bari mu fara shirimmu na yau da sauraron aya ta 84 har zuwa ta 87 daga cikin surar An'aam kamar haka.

وَوَهَبْنَا لَهُ إِسْحَاقَ وَيَعْقُوبَ كُلاًّ هَدَيْنَا وَنُوحاً هَدَيْنَا مِن قَبْلُ وَمِن ذُرِّيَّتِهِ دَاوُودَ وَسُلَيْمَانَ وَأَيُّوبَ وَيُوسُفَ وَمُوسَى وَهَارُونَ وَكَذَلِكَ نَجْزِي الْمُحْسِنِينَ{84} وَزَكَرِيَّا وَيَحْيَى وَعِيسَى وَإِلْيَاسَ كُلٌّ مِّنَ الصَّالِحِينَ{85} وَإِسْمَاعِيلَ وَالْيَسَعَ وَيُونُسَ وَلُوطاً وَكُلاًّ فضَّلْنَا عَلَى الْعَالَمِينَ{86} وَمِنْ آبَائِهِمْ وَذُرِّيَّاتِهِمْ وَإِخْوَانِهِمْ وَاجْتَبَيْنَاهُمْ وَهَدَيْنَاهُمْ إِلَى صِرَاطٍ مُّسْتَقِيمٍ{87}

84-Kuma Muka bã shi Is'hãka da Yãkubu, dukkansu Mun shiryar, kuma Nũhu Mun shiryar da shi a gabãni, kuma daga zuriyarsa akwai Dãwũda da Sulaimãnu da Ayyũba, da Yũsufu da Mũsã da Hãrũna, kuma kamar wancan ne Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.

85- Da Zakariyya da Yahaya da Isa da Ilyasu dukkansu daga sãlihai ne.

86- Da Ismã'ila da Ilyasa, da Yũnusa da Ludu, kuma dukkansu Mun fĩfĩtã su a kan tãlikai.

87-Kuma daga ubanninsu, da zũriyarsu, da 'yan'uwansu, Muka zãbe su, kuma Muka shiryar da su zuwa ga hanya madaidaiciya.

A cikin ayoyin da suka gabata a shirimmu na bayan, mun bayyana yadda annabi Ibrahim (a) ya jagoranci kira zuwa ga tauhidi da kuma kadaita Allah. Har'ila yau da nisantar bautar gumaka. Amma wadannan ayoyi suna bayyana yadda ikidar tauhidi da bautar Allah ya yi tasiri a cikin zurriyar Annabi Ibrahim (a). Alla ya bawa annabi Ibrahim (a) yaya wadanda suka kasance masu kadaita Allah, ya shiryatardasu shiryatarwa ta musamman, wanda ya kaiga ya zabi wasu daga cikinsu ya sanyasu Annabawa da manzanni. Hakama a cikin iyayensa akwai wadanda Allah ya zaba. Sannna a cikin zurriyyarsa ya zabi wasu daga cikinsu ya basu darajoji ta annabci da manzanci. A cikin aya ta 81 ya ambaci wasu daga cikin iyaye, yaya da kuma jikokin annabi Ibrahim (a) wadanda suka kai ga wannan matsayin na annabci. Kamar, Nuhu(a), wanda ya zo kafin shi annabi Ibrahim(a),

Sai dai abin lura anan, Allah ya zabesu ne don kasancewarsu masu imani da ayyukan alkhairi. Ba wai don suna matsayin yaya da jikokin annabi Ibrahima (a) ba. Sanna ba dukkan yayan annabawa ne mutanen kirki ba, duk da cewa ayuka da addu'ar iyayensu na da tasiri cikin taimaka masu su zama mutanen kirki masu aikata ayyuka na gari. Muna aya daukan darussa a cikin wadannan ayoyi kamar haka. 1. Ayyukan iyaye da addu'arsu suna da tasiri cikin yayansu da zuriyyarsu. Allah yakan yi baiwa ga zuriyyar bawansa sanadiyyar ayyukan alkhairi wanda iyaye suka aikata. 2. Allah yana yin kyauta ga bayinsa salihai, ya basu yaya wadanda suke na gari.

Yanzun kuma mu saurari karatun aya ta 88 a cikin surar An'am kamar haka.

ذَلِكَ هُدَى اللّهِ يَهْدِي بِهِ مَن يَشَاءُ مِنْ عِبَادِهِ وَلَوْ أَشْرَكُواْ لَحَبِطَ عَنْهُم مَّا كَانُواْ يَعْمَلُونَ{88}

88- Wancan ne shiryarwar Allah, Yanã shiryar da wanda Yake so daga bayinSa. Kuma dã sun yi shirki dã hakĩka abin da suka kasance sunã, aikatãwa yã lãlãce.

Wanna ayar tana nuna yadda Allah yake bada tallafi na musamman ga annabawasa don su tafi a kan tafarkin shiriya, da kuma bayyana gaskiya. Sai dai wannan ba yana nufin wadannan annabawa an tilasta masu aikata ayyukan alkhairi bane. A a, da zabinsu ne, tare da ilmin da Allah ya basu, suka zabi shiriyarsa. Don haka da suma zasu yi shirka da Allah – Allah ya kiyaye- da basu kai ga wannan matsayinba, kuma da basu sami taimakon Allah ba. Muna iya daukan darussa a cikin wannan ayar kamar haka. 1. Shiriya daga wajen Allah yake, hatta Annabawa suna samun shiriya da kamala ne daga wajen Allah sa shi kadai. 2. A cikin sunnar Allah, babu wariya a cikinsa, da annabawa ma zasu kaucewa tafarkin Allah, to da su ma makomarsu daya ce da wadanda ba su ba.

Yanzun kuma mu saurari karatun aya ta 89 a cikin surar An'am kamar haka.

أُوْلَـئِكَ الَّذِينَ آتَيْنَاهُمُ الْكِتَابَ وَالْحُكْمَ وَالنُّبُوَّةَ فَإِن يَكْفُرْ بِهَا هَـؤُلاء فَقَدْ وَكَّلْنَا بِهَا قَوْماً لَّيْسُواْ بِهَا بِكَافِرِينَ{89}

89-Wadancan ne wadanda Muka bai wa Littãfi da hukunci da Annabci. To idan wadannan (mutãne ) sun kãfirta da ita, to, hakĩka, Mun wakkala wasu mutãne gare ta, ba su zama game da ita kãfirai ba.

A ciga daga da bayanin irin taimakon da Allah yake yiwa annabawansa . Wannan ayar tana kara bayani na cewa, bayan saukar masu littafai mun basu daukaka da iko a kan mutane don su tafiyar da dokokin Allah a cikin mutane su aiwatar da hukunce hukluncen Allah a cikinsu. Mun umurce su da su yi alkalanci, su warware sabani tsakanin mutanensu da hukuncin Allah. Amma abinda ya tabbata shi ne cewa mafi yawan wadannan mutane sun kafirce sun ki amincewa da bin wadannan Annabawa. Sannan ayar ta yi kira ga manzon Allah (a) da cewa, kada ka damu idan mutanenka sun kafirce, don mun samar da wasu wadanda zasu tabbata a cikin imani da kai da kuma bin tafarkin Ubangijinka, baza su sako sako da bin hanyar Allah. Muna iya daukan darussa a cikin wannan ayar kamar haka. 1. Jagoranci da kuma alkalanci cikin rayuwar dan'adam hakki ne na annabawa da kuma bayinsa salihai. 2. Karba ko rashin karban mutane sakon Allah, da kuma amincewarsu ko rashin amincewarsu da hukunce hukuncen annabawa Allah da salihai bayi, ba shi ne mizanin gano gaskiya da kariya ba. Don haka kada wannan ya girgiza imanin mai imani.

Yanzun kuma mu saurari karatin aya ta 90 daga cikin surar An'am kamar haka.

أُوْلَـئِكَ الَّذِينَ هَدَى اللّهُ فَبِهُدَاهُمُ اقْتَدِهْ قُل لاَّ أَسْأَلُكُمْ عَلَيْهِ أَجْراً إِنْ هُوَ إِلاَّ ذِكْرَى لِلْعَالَمِينَ{90}

90- Wadancan ne Allah Ya shiryar, sabõda haka ka yi kõyi da shiryarsu. Ka ce: "Ba ni tambayar ku wata lada. Shĩ (Alkur'ãni) bai zama ba fãce tunãtarwa ga tãlikai."

A karshen jerin wadannan ayoyi, Allah yana Magana da manzonsa (s) da cewa, abinda kazo da shi karashe ne na abinda annabawan da suka gabata, ba wani sabon abuba ne daga sakonnin da suka gabata ba. Aikin na kadai shi ne isar da sako da kuma tunatarwa a gareku. Bana neman wata lada ko wata bukata daga gareku. Daga cikin wannan ayar muna iyadaukan darussa kamar haka. 1. Addinan da annabawa suke zuwa da su iri daya ne, babu bambanci a tsakaninsu. Sabon Annabi da sabon sako bai maida addinin baya bata ba. Sai dai bambamcin wasu dokoki. 2. Tafarkin kiran annabawa shi ne tafarkin tunatarwa da yin nisiha. Babu tilastawa a cikin kiransu. 3. Kiran annabawa baya tattare da neman duniya. Tunatarwa ce kawai ga mutane. Da kuma isar da sakon Allah a garesu. Masu sauraro da wannan kuma muka kawo karshen shirmmu na yau sai kuma wani shirin idan Allah ya kaimu a huta lafiya wassalamu alaikum warahmatullahi wa barakatuhu.

Suratul An'am, Aya Ta 91-93 (Kashi Na 207)

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da war haka barkammu da sake saduwa cikin shirimmu na hannunka mai sanda shiri wanda yake dubi cikin wasu ayoyin Alkur'ani mai girma don su zama darasi a cikin rayuwarmu. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.

      • .

To bari mu fara shirimmu na yau da sauraron aya ta 91 daga cikin surar An'aam kamar haka.

وَمَا قَدَرُواْ اللّهَ حَقَّ قَدْرِهِ إِذْ قَالُواْ مَا أَنزَلَ اللّهُ عَلَى بَشَرٍ مِّن شَيْءٍ قُلْ مَنْ أَنزَلَ الْكِتَابَ الَّذِي جَاء بِهِ مُوسَى نُوراً وَهُدًى لِّلنَّاسِ تَجْعَلُونَهُ قَرَاطِيسَ تُبْدُونَهَا وَتُخْفُونَ كَثِيراً وَعُلِّمْتُم مَّا لَمْ تَعْلَمُواْ أَنتُمْ وَلاَ آبَاؤُكُمْ قُلِ اللّهُ ثُمَّ ذَرْهُمْ فِي خَوْضِهِمْ يَلْعَبُونَ{91}

91-Kuma ba su kaddara Allah a kan hakikanin kaddararsa ba, a lõkacin da suka ce: "Allah bai saukar da kõme ba ga wani mutum." Ka ce: "Wãne ne ya saukar da Littãfi wanda Mũsã ya zo da shi, yanã haske da shiriya ga mutãne, kukã maida shi takarda takarda, kũna bayyana wasu, kuma kunã bõye masu yawa daga cikinsu, kuma an sanar da ku abin da ba ku sani ba, ku da ubanninku?" Ka ce: "Allah," sa'an nan ka bar su a cikin sharhõliyarsu sunã wãsã.

Wasu daga cikin yahudawa, wadanda suka yi imani da cewa an saukar da littafin attauna ga annabi Musa (a) amma sai gashi suna fadawa manzon Allah (s) cewa, ai Allah baya saukar da littafi ga mutum, a lokacin ne Alkur'ani mai girma ya basu amsa da cewa , ta yaya kuka amice da cewa an saukar da Attaura ga Annabi Musa (a) amma baza ku amince da cewa an saukar da Alkur'ani ga Annabi Muhammad (s) ba?. Duk abinda kuka sani a cikin Attaura shi ma Alkur'ani yana da shi. Duk da cewa kukan boye wasu hukunce hukuncen Attaura idan basu dace da son zuciyarku ba. Amma duk da haka kun yi imani da cewa daga wajen Allah ne ya sauko. Daga karshe ayar tana kira ga manzon Allah (s) da ya basu amma, sannan ya tsaya daram kan abinda aka saukar masa ya yi watsi da su, ya barsu cikin rudu da sharholiya da suke ciki. Allah ya isar masa.

Muna iya daukan darussa daga cikin wannan ayar kamar haka.

1. Rashin amini da annabawa yana dai dai da rashin sanin ni'imomin da Allah ya yiwa dan adam ne. Sannan annabci rahamar Allah ne ga mutane. Kuma yana zaben Annabawa ne bisa hikimarsa. 2. Wazifar annabawa shi ne gargadi ga mutane da kuma shiryatar da su kan tafarkin gaskiya. Basa tilastawa mutane imani da annabcinsu ko imani da abinda suka zo da shi.

Yanzun kuma mu saurari karatun aya ta 92 daga cikin surar An'am kamar haka.

وَهَـذَا كِتَابٌ أَنزَلْنَاهُ مُبَارَكٌ مُّصَدِّقُ الَّذِي بَيْنَ يَدَيْهِ وَلِتُنذِرَ أُمَّ الْقُرَى وَمَنْ حَوْلَهَا وَالَّذِينَ يُؤْمِنُونَ بِالآخِرَةِ يُؤْمِنُونَ بِهِ وَهُمْ عَلَى صَلاَتِهِمْ يُحَافِظُونَ{92}

92- Kuma wannan Littãfi ne, Mun saukar da shi, mai albarka ne, mai gaskata wanda yake a gabansa ne, kuma dõmin ka yi gargadi ga Uwar Alkaryu (Makka) da wanda yake gefenta. Kuma wadanda suke yin ĩmãni da Lãhira sunã ĩmãni da shi (Alkur'ãni), kuma sũ, a kan sallarsu, sunã tsarẽwa.

Ayar da ta gabata ta bayyana yadda wasu yahudawa suka tunkari manzon Allah (s) suna musanta cewa an saukar masa da wani sako daga Allah. Alhali sun yi imani cewa, an saukarwa annabu Musa (a) littafin Attaura sako daga Allah. Shi ne wannan ayar ta dora a kai tana cewa, idan ku baku yi imani da shi alkur'ani ba, amma shi alkur'ani ya amince da littafan da suka sauka gabaninsa na Attaura da linzili. Kuma alkur'ani ya tabbatar da cewa Allah ne ya saukar da Attaura ga Annabi Musa (a).

Sannan ayar ta ci gaba da kira ga manzon Allah (s), tana cewa, mun saukar maka da wannan Alkur'anin ne don ka kira mutanen makka da farko sannan sauran mutane. Amma fa ka sani ba kowa ne zai yi imani da kai da kuma littafin ka ba. Mutane, wadanda zasu yi imani da kai da kuma littafin da aka saukar maka. to sune wadanda suka sakankance da cewa akwai ranar lahira kuma suna kusantar Allah ta hanyar kiyaye sallolinsu. Muna iya daukan darussa a cikin wannan ayar kamar haka 1. Littafan da suka gabaci alkur'ani daga Allah suka sauko, bambamcinsu da alkur'ani shi ne, an shafe shari'ar da ta zo a cikinsu, sai wadanda alkur'ani ya zartar da su 2. Kiyaya sallah alama ce babban ga imanin masu imani, akwai nakasa babba ga wanda yake wulakantata.

Yanzun kuma mu saurari aya karatun ta 93 cikisurar An'am kamar haka.

وَمَنْ أَظْلَمُ مِمَّنِ افْتَرَى عَلَى اللّهِ كَذِباً أَوْ قَالَ أُوْحِيَ إِلَيَّ وَلَمْ يُوحَ إِلَيْهِ شَيْءٌ وَمَن قَالَ سَأُنزِلُ مِثْلَ مَا أَنَزلَ اللّهُ وَلَوْ تَرَى إِذِ الظَّالِمُونَ فِي غَمَرَاتِ الْمَوْتِ وَالْمَلآئِكَةُ بَاسِطُواْ أَيْدِيهِمْ أَخْرِجُواْ أَنفُسَكُمُ الْيَوْمَ تُجْزَوْنَ عَذَابَ الْهُونِ بِمَا كُنتُمْ تَقُولُونَ عَلَى اللّهِ غَيْرَ الْحَقِّ وَكُنتُمْ عَنْ آيَاتِهِ تَسْتَكْبِرُونَ{93}

93-Kuma wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya kirkira karya ga Allah, kõ kuwa ya ce: "An yi wahayi zuwa gare ni," alhãli kuwa ba a yi wahayin kõme ba zuwa gare shi, da wanda ya ce: "zan saukar da misãlin abin da Allah Ya saukar?" Kuma dã kã ga, a lõkacin da azzãlumai suke cikin mãgegen mutuwa, kuma malã'iku sunã shimfida masu hannuwansu, (sunã ce musu) "Ku fitar da kanku; a yau anã sãka muku da azãbar wulãkanci sabõda abin da kuka kasance kunã fada, ba gaskiya ba, ga Allah kuma kun kasance daga ãyõyinSa kunã yin girman kai."

A cikin tsawon tarihi an sami wasu mutane wadanda suke riya cewa an yi masu wahayi suna gayawa mutane su ma annabawan Allah ne. Ko kuma su ce suna iya samar da irin abinda Allah ya saukar na ayoyi masu shiryatarwa. An sami wasu daga cikin wadannan mutane a cikin zamanin manzon Allah (s). Kuma sun aikewa manzon Allah cewa suma annabawan Allah ne, kuma ana masu wahayi. Daga cikinsu akwai wanda ake kira Ubaid Bin Sa'ad, wanda ya kasance yana rubuta wahayi wa manzon Allah (s) amma saboya ha'incinsa ya kore shi. Daga baya ya tara mutane ya na ce masu, nima zan iya kawo maku ayoyi irin na alkur'ani. Akwai kuma Musailam makaryashi. Amma dukkaninsu ba wanda ya sami amincewar mutane kan abinda suke riyawa. Irin wadannan makaryata a lokacin mutuwa zasu hadu da azaba mai tsanani kafin na lahira. Muna iya daukan darussa a cikin wannan ayar kamar haka. 1. Zalunci mafi girma shi ne batar da mutane daga tarkin addinin gaskiya. Wandan hakan yakan jawo halakar mutane na lokaci mai tsawo. 2. Dole ne mu kula da makaryata musamman wadanda zasu zo da shiffar malanta da kuma addini. Suna yada ikidon kariya suna rufesu da addinin gaskiya. Masu sauraro da wannan kuma muka kawo karshen shirimmu na yau sai kuma wani shirin idan Allah yakaimau. Mu huta lafiya wassalamu alaikum warahmatullahi wa barakatuhu.

Suratul An'am, Aya Ta 94-97 (Kashi Na 208)

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na na hannunka mai sanda shiri wanda yake dubi cikin wasu ayoyin al-kur'ani mai girma don su zama fitila a cikin rayuwarmu. Ta fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.

      • .

To bari mu fara shirimmu da sauraron aya ta 94 da ga cikin sura Anaam kamar haka.

وَلَقَدْ جِئْتُمُونَا فُرَادَى كَمَا خَلَقْنَاكُمْ أَوَّلَ مَرَّةٍ وَتَرَكْتُم مَّا خَوَّلْنَاكُمْ وَرَاء ظُهُورِكُمْ وَمَا نَرَى مَعَكُمْ شُفَعَاءكُمُ الَّذِينَ زَعَمْتُمْ أَنَّهُمْ فِيكُمْ شُرَكَاء لَقَد تَّقَطَّعَ بَيْنَكُمْ وَضَلَّ عَنكُم مَّا كُنتُمْ تَزْعُمُونَ{94}

94- Kuma lalle ne hakĩka, kun zo Mana dai dai, kamar yadda Muka halittã ku a farkon lõkaci. Kuma kun bar abin da Muka mallaka muku a bayan bayan ku, kuma ba Mu gani a tãre da kũ ba, masu cẽto wadanda kuka riya cẽwa lalle ne sũ, a cikinku mãsu tãrayya ne. Lalle ne, hãkĩka,kõme yã yanyanke a tsakãninku, kuma abin da kuka kasance kunã riyãwa ya bace daga gare ku.

A cikin shirimmu da ya gabata mun karanta ayoyi wadanda suke magana kan irin halin da mushrikai suke shiga a lokacin mutuwa. Wannan yara tana dorawa kan abinda ya gabata. Mala'iku zasu cewa kafirai a lokacin da suka mutu, a rayuwarku ta duniya kun tara dukiyoyi masu yawa kun yi ta bin wasu mutane har sai da kuna ganin su masu ceton ku ne a lokacin da kuka shiga tsanani, a yau gashi kun zo mana ku kadai ba tare da kowa ba, a halin yanzu me kuke tunani makomanku zata kasance.

Muna iya daukan darussa daga cikin wannan ayar kamar haka.

1. Tsarin rayuwa a lahita ta daddaiku ne, dangantaka ta iyali da yan uwa duk zasu yanke.

2. A lokacin mutuwa ne, mutum zai tabbatar cewa dukiya da wani daukaka a duniya ba kome bane fashi kamar mafarki.

Yanzun kuma bari mu saurari karatun aya ta 95 daga cikin sura anaam kamar haka.

إِنَّ اللّهَ فَالِقُ الْحَبِّ وَالنَّوَى يُخْرِجُ الْحَيَّ مِنَ الْمَيِّتِ وَمُخْرِجُ الْمَيِّتِ مِنَ الْحَيِّ ذَلِكُمُ اللّهُ فَأَنَّى تُؤْفَكُونَ{95}

95- Lalle ne, Allah ne Mai tsãgewar kwãyar hatsi da kwalfar gurtsu. Yanã fitar da mai rai daga mamaci, kuma (Shi) Mai fitar da mamaci ne daga mai rai, wannan ne Allah. To, yãya ake karkatar da ku?

A ci gaba da bayani dangane da ikon Allah ta'ala a wajen mutuwa da kuma rayawa. Wanna ayar tana bayyana cewa, Allah ne yake fidda matacce daga rayyya ya kuma fidda rayayye daga mattace. Mutum yakan taimaka wajen shuga iri a cikin kasa da kuma gyara kasa domin noma, amma Allah ne ya ke tsaga kwayar hatsi mattace ya fidda tsiro ko kuma itaciya daga cikin ta.

Sannan kamar yadda ya zo cikin ruwayoyi a cikin rayuwar mutane Allah yakan samar da mumini daga mahaifi ko mahaifiya kafirai kamar yadda akasin yaha yake faruwa duk daga gare shi ne.

Muna iya daukan darussa a cin wanna ayar kamar haka.

1. Yin dubi cikin hilittun Allah shi hanya mafi sauki wajen sanin Allah.

2. Ta yaya mutum zai bautawa wanin Allah alhali shi ne yake arzuta shi ta ko ina?.

Yanzu kuma sai aya ta 96:

فَالِقُ الإِصْبَاحِ وَجَعَلَ اللَّيْلَ سَكَناً وَالشَّمْسَ وَالْقَمَرَ حُسْبَاناً ذَلِكَ تَقْدِيرُ الْعَزِيزِ الْعَلِيمِ{96}

96- Mai tsãgẽwar sãfiya, kuma Ya sanya dare mai natsuwa, kuma da rãna da watã a bisa lissãfi. wannan ne kaddarãwar Mabuwãyi Masani.

Banda tsagar kwayar hatsi matattce ya maida ita rayayye alkur'ani ya ci gaba da bayyana ayayoyin Allah. Inda a wannan ayar yana bayyana yaoyinsa da ke cikin jujjuyawar rana da dare.

Banda tasirin da hasken rana yakle da shi wajen raya shuka, tafiyar rana da kuma jujjuyawar wata suna da tasiri mai yawa a cikin rayuwarmu. Muna hutu cikin dare sannan da rana kuma muna neman arziki.

Juyyuyawan rana da wata suna daga cikin manya manyan ayoyin Allah ga wanda yake da tunani.

Muna iya daukan darussa a cikin wanna yara kamar haka.

1. Yin tunani cikin halittun Allah hanya ce ta sanin sa.

2. Ayyukan ubangiji a tsare suke –don haka muma ana bukatar mu tafiyar da rayuwarmu cikin tsari. Idan ba haka ba zamu fada cikin matsaloli da dama.

Yanzun kuma bari mu saurari karatun aya ta 97 daga cikin surar anaam kamar haka.

وَهُوَ الَّذِي جَعَلَ لَكُمُ النُّجُومَ لِتَهْتَدُواْ بِهَا فِي ظُلُمَاتِ الْبَرِّ وَالْبَحْرِ قَدْ فَصَّلْنَا الآيَاتِ لِقَوْمٍ يَعْلَمُونَ{97}

97- Kuma Shi ne Ya sanya muku taurãri dõmin ku shiryu da su a cikin duffan tudu da ruwa. Lalle ne Mun bayyana ãyõyi daki-daki, ga mutãne wadanda suke sani.

Banda rana da wata da kuma tasirin da suke da shi a cikin rayuwar dan adam, taurari ma suna da tasiri mai yawa a cikin rayuwar mutum. Taurari suna daga cikin manya manyan ayoyin Allah. Wadanda suka kasance abin lura ga masu hankali. Har yanzun dan adam ya kasa sanin yawan tauri da suke cikin sararin samaniya don yawansu da kuma girmasu. Muna amfani da taurari wagen gano hanyarmu a cikin take da kuma a cikin duhun dare.

Muna iya daukan darussa daga cikin wannan yar kamar haka.

1. tauraru duk da yawansu suna nan cikin tsari wanda mutum yake amfana da shi musamman wayen gano hanyarsa a lokacinda yake cikin duhun dare ko kuma cikin take inda babu wata alama da zai gane inda yake said a su taurari.

2. Mutum yana samun jagoranci daga halittun Allah a lokacinda babu wani abinda zai fidda shi daga wurin da yake said a wannan jagoranci to me yasa ba zai amince da jagorancin Allah a cikin rayuwarsa ba.

Masu sauraro da wannan kuma muka kawo karshen shirimmu nay au sai kuma wani shirin idan Allah ya kai mu a huta lafiya wassalamu alaikum wa rahamtullahi wa barakatuhu.

Suratul An'am, Aya Ta 98-102 (Kashi Na 209)

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na na hannunka mai sanda shiri wanda yake dubi cikin wasu ayoyin al-kur'ani mai girma don su zama fitila a cikin rayuwarmu. Ta fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.

      • .

To bari mu fara shirimmu da sauraron aya ta 98 da ga cikin sura Anaam kamar haka.

وَهُوَ الَّذِيَ أَنشَأَكُم مِّن نَّفْسٍ وَاحِدَةٍ فَمُسْتَقَرٌّ وَمُسْتَوْدَعٌ قَدْ فَصَّلْنَا الآيَاتِ لِقَوْمٍ يَفْقَهُونَ{98}

98-Kuma Shi ne Ya kãga halittarku daga rai guda, sa'an nan da mai tabbata da wanda ake ajẽwa. Lalle ne Mun bayyanã ãyõyi daki-daki, ga mutãne wadanda suke fahimta.

A ci gaba da kawo jerin ayoyi wadanda suke magana kan ayoyin Allah, wannan ayar tana magana kan halittar shi mutum. Allah ya kagi halittar mutum sannan ya halicce sauran mutane gaba daya daga rai guda watu annabi adama (a).

A cikin mutane akwai wadanda sun zo duniyar har sun tafi wato kamar iyayenku da kakanninki. Sai kuma ku da kuke raye a halin yanzu, akwai kuma wadanda har yanzun basu zo duniyar ba, suna nan tafe a dai dai loakcinda Allaha ya kaddara masu zuwa cikinta.

Don haka mutane gaba dayansu fari da baki da ja kakansu adamu (a).

Muna iya daukan darussa a cikin wannan ayar kamar haka.

1. Dukkan mutane daya suke a wajen Allah, fifiko da ke tsakaninsu a wajen dukiya da kuma halitta baya da tasiri a wajen Allah.

2. Akwai ayar Allah babba cikin halittan dan'adam daga rai guda amma ga masu tunani da kuma hankali.

Yanzun kuma mu saurari karatun aya ta 99 daga cikin surar Anaam kamar haka.

وَهُوَ الَّذِيَ أَنزَلَ مِنَ السَّمَاءِ مَاءً فَأَخْرَجْنَا بِهِ نَبَاتَ كُلِّ شَيْءٍ فَأَخْرَجْنَا مِنْهُ خَضِراً نُّخْرِجُ مِنْهُ حَبّاً مُّتَرَاكِباً وَمِنَ النَّخْلِ مِن طَلْعِهَا قِنْوَانٌ دَانِيَةٌ وَجَنَّاتٍ مِّنْ أَعْنَابٍ وَالزَّيْتُونَ وَالرُّمَّانَ مُشْتَبِهاً وَغَيْرَ مُتَشَابِهٍ انظُرُواْ إِلِى ثَمَرِهِ إِذَا أَثْمَرَ وَيَنْعِهِ إِنَّ فِي ذَلِكُمْ لآيَاتٍ لِّقَوْمٍ يُؤْمِنُونَ{99}

99- Kuma Shi ne Ya saukar da ruwa daga sama, Muka fitar da tsiron dukkan kõme game dã shi, sa'an nan Muka fitar da kõre daga gare shi, Muna fitar da kwãya damfararriya daga gare shi (kõren), kuma daga dabĩno daga hirtsinta akwai dumbuje-dumbuje makusanta, kuma (Muka fitar) da gõnaki na inabõbi da zãitũni da rummãni, mãsu kamã da jũna da wasun mãsu kama da jũna. Ku dũba zuwa 'ya'yan itãcensa, idan ya yi 'ya'yan, da nunarsa. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyõyi ga wadanda suke yin ĩmãni.

Ayan da ta gabata ta yi maganar halittar mutum da kuma ayar Allah take cikin hakan. A cikin wannan ayar alkur'ani mai girma ya bayyana muhimmancin ruwan sama da kuma irin yayan itatuwa nau'I daban daban wanda sanadiyyar ruwan sama suke samuwa. A cikin ayar ya ambaci sunayen wasu yayan itatuwa kamar inabi da dabino da kuma yayan itawa daban daban. Wadanda suk suke samuwa ta hanyar samar da ruwan sama. Shi dan adama anan baya iya yin kome a cikinsa samar da su.

Daga cikin wannan ayar muna iya daukan darussa kamar haka.

1. Dangantakar mutum da wadan nan yayan itatuwa kada ya kasance na kasancewarsu abincin mutum ba, yakamata dan 'adam ya yi tunani cikin halittarsu da kuma yadda Allaha yake samar da su.

2. Tunanin mutum kada ya takaita wajen abinda ya bayyana na halittun Allah, yakamata ya zurfafa tuna cikin halittun Allah don neman saninsa.

Yanzun kuma bari mu saurari karatun aya ta 100 daga cikin sura anaam kamar haka.

وَجَعَلُواْ لِلّهِ شُرَكَاء الْجِنَّ وَخَلَقَهُمْ وَخَرَقُواْ لَهُ بَنِينَ وَبَنَاتٍ بِغَيْرِ عِلْمٍ سُبْحَانَهُ وَتَعَالَى عَمَّا يَصِفُونَ{100}

100- Kuma suka sanya wa Allah abõkan tãrayya, aljannu, alhãli kuwa (Shi) Ya halitta su. Kuma sun kirkira masa diya da 'yã'ya, bã da ilmi ba. TsarkinSa yã tabbata! Kuma Ya daukaka daga abin da suke sifantãwa.

Abin bakinciki shi ne wasu mabiyan wasu addinai da suka zo kafin Musulunci suna daukar wasu bayin Allah a matsayin yayan Allah. Kiristoci suna Dakar Annabi Isa (a) a matsayin dan Allah a yayinda yahudawa suke ganin uzairu dan Allah ne. Hakama a cikin wasu addinan, sun dauki mala'iku a matsayin yayan Allah Allah mata. Sai kuma wasu kabilun larabawa sun dauki aljannu a matsayin masu dangantaka da ubangiji.

Alkur'ani mai girma a cikin wannan ayar tana karyata wannan zancen da kuma tunanin da irin wadannan akidu.

Allah ya tsarkaka ya zama yana da yaya ko mata, banda haka mutum bai isa ya suranta Allah ba. Don shi bai yi kama da kome be kuma shi ya halicce kome. Aljannu da mala'iku su ma halittun Allah kamar yadda kuke halittun na Allah.

Muna iya daukan darussa daga cikin wannan ayar kamar haka.

1. Jahilci ne yake sanya mutane daukar ikidu wadanda ba gaikiya bane. A cikin abinda ya shafi akida dole ne mutum ya gina ikidarsa bisa ilmi da sani.

2. Ubangji bai da mata ko kuma mai kama da shi ballantana ya sami yaya. Ta yaya wasu suke kokarin dangantawa Allah yaya da mata ?

Yanzun kuma mu saurari karatun aya ta 101 da kuma 102 daga cikin sararar Anaam kamar haka.

بَدِيعُ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ أَنَّى يَكُونُ لَهُ وَلَدٌ وَلَمْ تَكُن لَّهُ صَاحِبَةٌ وَخَلَقَ كُلَّ شَيْءٍ وهُوَ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمٌ{101} ذَلِكُمُ اللّهُ رَبُّكُمْ لا إِلَـهَ إِلاَّ هُوَ خَالِقُ كُلِّ شَيْءٍ فَاعْبُدُوهُ وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ وَكِيلٌ{102}

101-Mafarin halittar sammai da kasa. Yãya dã zai zama a gare Shi alhãli kuwa mãta ba ta kasance ba, a gare Shi, kuma Ya halitta dukkan, kõme, kuma Shĩ, game da dukan kõme, Masani ne?

102- Wancan ne Allah Ubangijinku. Bãbu wani abin bautãwa fãce Shĩ, Mahaliccin dukan kõme. Sabõda haka ku bauta Masa kuma Shi ne wakĩli a kan dukkan, kõme

A cikin jerin wadannan ayoyi wadanda suke magana dangane da ayoyin Allah da kuma sifofinsa, wannan ayar tana kara bayanin kadaitakar Allah ta'ala, wanda ya halicci kome daga babu. Shi ne ya kagi halittar mutum ba tare da daukar misali a wani waje ba. Babu wanda ya yi kama da shi, to ta yaya zaku kirkiro masa yaya alhali bai riki mata ba ? Allah bai bukatar taimakon kowa, don haka shi yakamata ku bautawa.

Muna iya daukan darussa a cikin wadanan ayoyi kamar haka

1. Mu kwatanta yadda alkur'ani mai girma yake sifanta Allah da kuma yadda sauran littafin suke daukarsa sannan mu gane bambanci.

2. Ayoyin Allah sune tafarkin da ya kamata mutum ya bi don sanin Allah. Don akwai ayarsa a cikin dukkan halittunsa.

Masu saurare da wannan kuma muka kawo karshen shirimmu na yau sai kuma wani shirin adin Allah ya kaimu a huta lafiya wassalamu alaikum warhamatullahi wa barakatunhu.

Suratul An'am, Aya Ta 103-106 (Kashi Na 210)

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa cikin shirimmu na hannunka mai sanda shiri wanda yake yin dubi a cikin wasu ayoyin Al'qur'ani mai girma don su zama fitila a cikin rayuawrmu. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.

To bari mu fara shirimmu da sauraron aya ta 103 daga cikin surar An'aam kamar haka:

لاَّ تُدْرِكُهُ الأَبْصَارُ وَهُوَ يُدْرِكُ الأَبْصَارَ وَهُوَ اللَّطِيفُ الْخَبِيرُ{103}

103-Gannai bã su iya riskuwarSa, kuma Shĩ Yanã riskuwar gannai, kuma Shĩ ne Mai tausasãwa, Masani.

A cikin shirimmu da ya gabata mun karanta wasu ayoyi dangane da sifofin Allah ta'ala kuma mun yi bayaninsu. Wannan ayar ma tana magana a kan sifofin Allah wadanda suka kebanta gare shi. Anan yana magana ba wai kawai idanu na zahiri ba, a'a hatta kwakwalwan mutum baya ya iya sawwara ubangiji, sai dai ya fahinci samuwarsa ya fahinci sifofinsa. Amma shi yana gani yana jin dunk abinda mutum yake aikawa a boye ko a bayyane, shi babu abinda ya boyu gare shi. Muna iya daukan darussa a cikin wannan ayar kamar haka. 1. Sanin zatin Ubangija bai yuwa ga kowa, amma shi ya riskar kome da kowa. 2. Duk da cewa Ubangaji yana san da zunubbammu da kura kurammu, ammam wannan baya han shi tausaya man.

Yanzun kuma mu saurari karatun aya ta 104 daga cikin surar An'am kamar haka.

قَدْ جَاءكُم بَصَآئِرُ مِن رَّبِّكُمْ فَمَنْ أَبْصَرَ فَلِنَفْسِهِ وَمَنْ عَمِيَ فَعَلَيْهَا وَمَا أَنَاْ عَلَيْكُم بِحَفِيظٍ{104}

104-Lalle ne abũbuwan lũra sun je muku daga Ubangijinku, to, wanda ya kula, to, dõmin kansa, kuma wanda ya makanta, to, laifi yanã a kansa, kuma nĩ, a kanku, bã mai tsaro ba ne.

Bayan ayan da ta gabata ta bayyana sifofin Allah, wadanda suka tabbatar da cewa abubuwan da ake hada shi da su wajen bauta basu cancanci bauta ba. Wannan ayar tana bayyana cewa, duk abinda yakmata mu bayyana mun bayyana, duk abinda ya kamata mu fada mun fada, ya rage wa masu hankali su zabi hanya madai daiciya ko kuma su zabi bata. Allah bai aiko da manzanni don su tilastawa mutane imani ba. Duk abinda mutum ya zaba don kansa ne. Mai kyau ko mara kyau. Daga cikin wannan ayar muna iya fahintar abubuwa kamar haka. 1. Aikimmu shi ne bayyana gaskiya don tabbatar da hujja kan mutane, don ya zama bas a da uzurin da zasu bayar ranar kiyama. Aikimmu ba tilastawa mutane Imani bane. 2. Don wasu mutane sun kafircewa Ubangijinsu, sun ki amsa kiran annabinsa, wannan bai nuna cewa baya kan gaskiya ba. Don abin babu tilastawa cikin sa.

Yanzun kuma mu saurari aya ta 105 kamar haka.

وَكَذَلِكَ نُصَرِّفُ الآيَاتِ وَلِيَقُولُواْ دَرَسْتَ وَلِنُبَيِّنَهُ لِقَوْمٍ يَعْلَمُونَ{105}

105 - Kamar wannan ne Muke sarrafa ãyõyi, kuma dõmin su ce: "Kã karanta!" Kuma dõmin Mu bayyana shi ga mutãne wadanda sunã sani.

Yana daga cikin tuhumar da mushrikam Makka sukewa manzon Allah (s) cewa Alqur'ani da yake cewa an saukar msa din nan, ba daga gareshi bane, ya yi karatunsu a gaban wasu malamai na yahudu ko nasara sun sanar da shi. Ba gaskiya bane wahayi ake masaba. Shi ne wannan ayar ta basu amsa da cewa, kada da damu da wannan tuhumar da suke maka. Wadanda suke da sanka kuma suka gano gaskiya ba za su yi maka wannan tuhumar ba. Sannan masu tuhumar basu gabatar da wani dalili wanda zai tabbatar da abinda suke riyawa ba. Babu wani shaida da ta tabbatar cewa manzon Allah ya yi karatu a gaban wani malami kafin ya bayyana cewa shi manzo ne daga Ubangijinsa. Sannan banda wannan, akwai bambamci tsakanin littafin attaura, wanda ake dangantawa da annabi Musa da kuma Linjila wanda ake dangantawa da aannabi Isa (a) na lokacin saukar Al'qur'ani da shi alqur'anin. Don an sauya abubuwa da dama a cikinsu. Muna iya daukan darussa a cikin wannan ayar kamar haka. 1. Hatta makiya sun tabbatar da zurfin ilmin da ke cikin alkur'ani, amma suna ganin cewa maganganun wasu malamai ne masana suka koya masa. 2. Masana da masu ilmin sun tabbatar da cewa, lallai alkur'ani littafi ne kunshe da ilmi, basa buye wannan. Kuma sun shaida cewa ya cancanci yabo ko da kuwa su basu bi shi ba.

Yanzun kuma mu saurari karatun aya ta 106 daga cikin surar An'am kamar haka.

اتَّبِعْ مَا أُوحِيَ إِلَيْكَ مِن رَّبِّكَ لا إِلَـهَ إِلاَّ هُوَ وَأَعْرِضْ عَنِ الْمُشْرِكِينَ{106}

106-Ka bi abin da aka yi wahayi zuwa gare ka daga Ubangijinka; babu wani abin bautãwa fãce Shi, kuma ka bijire daga mãsu shirki.

Har'yanzun raddi ga wadnad suke cewa alkur'ani ba wahayin Allah bane, wasu masana ne suka ilmantar da manzon Allah (s). Wannan ayar tana gayawa manzon Allah (s) cewa kada ka kula da abinda suke fada. Ka himmatu da kiyaye wahayin da muke maka. Aikimmu kawai shi ne isar da sako, da kuma kafa hujja a kan mutane. Babu tilastawa a cikin sa. Don haka ka kyale su. Don haka daga cikin wannan yar muna iya fahintar abubuw akamar haka. 1. A cikin kira zuwa ga tafarkin Allah akwai matsaloli, dole ne mai kira ya kasance mai istikama, ya zama mai dagaewa da tabbata cikin riko da gaskiya da kuma kira zuwa gareta. 2. Manzon Allah (s) shi ma mai bin umurnin Allah ne, babu ra'ayinsa a cikin dukkan abinda ya zo da shi. Masu sauraro da wannan kuma muka kawo karshen shirimmu na yau sai kuma shiri na gaba idan Allah ya kaimu. Wassalamu alaikum warahmatullahi wa barakatuhu.

Suratul An'am, Aya Ta 107-110 (Kashi Na 211)

Jama'a masu saurare Assalamu alaikum barkarku da sake saduwa da mu a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda ,inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki ,tare da yin bayani gwargwadon iko kan abin da suke koyar da mu ,tare da yi mana hannunka mai sanda a cikin lamurran rayuwa da zamantakewa.Amma kafin mu shiga cikin shirin gadan gadan ga abin da aka yi mana tanadi a kan inji.

Sai a saurari karatun aya ta 107 a cikin suratul An'am:

وَلَوْ شَاء اللّهُ مَا أَشْرَكُواْ وَمَا جَعَلْنَاكَ عَلَيْهِمْ حَفِيظاً وَمَا أَنتَ عَلَيْهِم بِوَكِيلٍ{107}

Kuma dã Allah Yã so, dã ba su yi shirki ba, kuma ba Mu, sanya ka mai tsaro a kansu ba, kuma ba kai ne wakĩli a kansu ba.

A ayoyin da suka gabata a cikin shirin da ya gabata suna magana ne kan shirkar da wasu ke yi da danganta karya ga Allah madaukakin sarki don haka a cikin wannan Ayar Allah tabaraka wa ta'ala ya ke cewa ma'aikinsa kar su yi zaton Allah ba ya da karfi kansu ,idan Allah ya so zai kawar da mushirikai daga doran kasa da shafe su baki daya.Allah ne ya so kuma ya bawa mutum damar zabin abin da zai aikata na alheri ko lala.Hatta kai kanka ma'aikin Allah ba ka da hakkin tilastawa wani aikata abin da bai yi niyar aikatawa ba ko yin imani kuma ba ka jibantar abin da mutane suke aikatawa.Kawai ci gaba da fadakarwa ko za su yi imani.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda biyu akalla:

1- Allah ne ya bawa kowa damar zaba da aikata abin da ya ga dama hatta Mushrikai sun zabi kne don radin kansu.

2-Nauyin Manzonni isar da sakon musulunci fadakar da mutane ba tilasta masu yin imani da addini ba.

Sai a saurari karatun aya ta 108 a cikin suratul An'am:

وَلاَ تَسُبُّواْ الَّذِينَ يَدْعُونَ مِن دُونِ اللّهِ فَيَسُبُّواْ اللّهَ عَدْواً بِغَيْرِ عِلْمٍ كَذَلِكَ زَيَّنَّا لِكُلِّ أُمَّةٍ عَمَلَهُمْ ثُمَّ إِلَى رَبِّهِم مَّرْجِعُهُمْ فَيُنَبِّئُهُم بِمَا كَانُواْ يَعْمَلُونَ{108}

Kuma kada ku zãgi wadanda suke kira, baicin Allah, har su zãgi Allah bisa zãlunci, ba, da ilmi ba. Kamar wannan ne Muka kawãta ga kõwace al'umma aikinsu, sa'an nan zuwa ga Ubangijinsu makõmarsu take, sa'an nan Ya ba su lãbari da abin da suka kasance sunã aikatãwa.

Bayan da Allah ya hana manzo da mumunai tilasta wa Mushrikai yin imani da addini to ita kuwa wannan aya tana yi magana ne kan hakurin da manzo da mumunai suka yi da izgili da cutarwa da takurawar Mushrikan Makka da cewa; kar ku yi magana marar dadi da batanci kan abubuan da Mushrikai ke yi bauta gudun kar su fake da haka su batanci abin da kuke bautawa . Kawai ku ci gaba da kokarin shiryar da su ta hanyar aiki da hankali da salo na addini idan sun so su bi idan sun ki zabinsu ne ba ku da leifi a kai. Imani na zuci shi ne zai banna a lafira da akidar kowa za ta bayyana da shiga makomar da ta yi daidai da imaninsa da aikinsa.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda biyu akalla:

1- A kullum mu yi la'akari da abubuwan da za su je su komo da abin da za amaida mana alheri ko lala.

2- Lamarin la'anta da nisanta da tsinuwa ya sha banban da zagi da maganganu maras kyau da batancin abin da mushrikai ke bautawa.

Sai a saurari karatun aya ta 109 a cikin suratul An'am:

وَأَقْسَمُواْ بِاللّهِ جَهْدَ أَيْمَانِهِمْ لَئِن جَاءتْهُمْ آيَةٌ لَّيُؤْمِنُنَّ بِهَا قُلْ إِنَّمَا الآيَاتُ عِندَ اللّهِ وَمَا يُشْعِرُكُمْ أَنَّهَا إِذَا جَاءتْ لاَ يُؤْمِنُونَ{109}

Kuma suka yi rantsuwa da Allah iyakar rantsuwõyinsu (cẽwa) lalle ne idan wata ãyã ta jẽmusu, hakĩka, sunã yin ĩmãni da ita. Ka ce: "Abin sani kawai, ãyõyi a wurin Allah suke. Kuma mẽne nezai sanya ku ku sansance cẽwa,lalle ne su, idan ãyõyin sun je, ba zã su yi ĩmãni ba?"

Daya daga cikin abin da kafirai da mushrikan makka ke fakewa a lolakcin ma'aikin Allah shi ne suna cewa mai ya sa mu'ujizar da muka bukata ba ka zo mana da ita? Don haka wannan aya take miada masu martani da cewa ma'aikin Allah ka ce masu: Mu'ujizar ba a hannuna take ba balantana in zo maku da ita a duk lokacin da yake so tana hannun mai sama Allah madaukakin sarki don haka a duk lokacin da Allah ya ga dama da maslaha ya zuwa da ita don kafa hujja kan bayunsa ba wai bukatun mutane ne ba kuma bugu da kari dayawa daga cikin bukatun mutane ya sabawa tafarki na gaskiya da hankali kamar yadda wasu ke bukatar ganin Allah da ido abin da ba zai taba yuyuwa ba da sauran bukatu makamantan haka.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda biyu akalla:

1- A kullum mu yi hankali kar mu fada tarkon makiya masu nacewa kan bukatunsu na yaudara.

2-Tushen kafirci ta'assubanci da jayayya duk wata hujja da za a kafa masu ba su amincewa da yin imani.

Sai a saurari karatun aya ta 110 a cikin suratul An'am:

وَنُقَلِّبُ أَفْئِدَتَهُمْ وَأَبْصَارَهُمْ كَمَا لَمْ يُؤْمِنُواْ بِهِ أَوَّلَ مَرَّةٍ وَنَذَرُهُمْ فِي طُغْيَانِهِمْ يَعْمَهُونَ{110}

Kuma Munã jujjũya zukãtansu da ganansu, kamar yadda ba su yi ĩmãni da shi ba a farkon lõkaci kuma Munã barin su a cikin kũtsãwarsu, sunã dĩmuwa.

Kafirci da jayayya yau da gobe ke kai mutum su baro shi da kai wa wani matsayi na kasa ji da fahimtar gaskiya da gaskiya ya maida ta karya, karya ya maida ta gaskiya don haka kur'ani ke cewa; wannan tafarkin haka yake kafirai da masu jayayya da suka kai wannan matsayi za su ci gaba da kutsawa da nucewa cikin batansu da kasancewa cikin dimuwa.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda biyu akalla:

1- imani da Allah da ma'aikinsa ana bukatar tsarkin zucciya,zucciyar da ta gurbata da jayayya da kabilanci ba a shirye take ba ta karbi gaskiya.

2- Nisanta da Allah da hanya madaidaiciya na jawo asara a wannan duniya balantana gobe kiyama.

Da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shirin na yau sai kuma shiri na gaba da yardar Allah kafin lokacin Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram na na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalamu alaikum warahmatullahi wa barkatuhu.

Suratul An'am, Aya Ta 111-114 (Kashi Na 212)

Jama'a masu saurare Assalamu alaikum barkarku da sake saduwa da mu a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda ,inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki ,tare da yin bayani gwargwadon iko kan abin da suke koyar da mu ,tare da yi mana hannunka mai sanda a cikin lamurran rayuwa da zamantakewa.Amma kafin mu shiga cikin shirin gadan gadan ga abin da aka yi mana tanadi a kan inji.

Sai a saurari karatun aya ta 111 a cikin suratul An'am:

وَلَوْ أَنَّنَا نَزَّلْنَا إِلَيْهِمُ الْمَلآئِكَةَ وَكَلَّمَهُمُ الْمَوْتَى وَحَشَرْنَا عَلَيْهِمْ كُلَّ شَيْءٍ قُبُلاً مَّا كَانُواْ لِيُؤْمِنُواْ إِلاَّ أَن يَشَاءَ اللّهُ وَلَـكِنَّ أَكْثَرَهُمْ يَجْهَلُونَ{111}

Kuma dã a ce, lalle Mũ Mun saukar da Malã'iku zuwa gare su, kuma matattu suka yi musu magana, kuma Muka tãra dukkan kõme a kansu, gungu-gungu, ba su kasance sunã iya yin ĩmãni ba, sai fa idan Allah Yã so, Kuma amma mafi yawansu sunã jãhiltar haka.

A cikin shirin da ya gabata mun bayyana cewa tushen kafircin yawancin mutane jayayya da hakan ke hana su karbar gaskiya ba don ba su fahimtar gaskiya ba ne to wannan aya ma na cewa: daya daga cikin bukatar kafirai a sabkar masu da mala'ika su ganshi da idonsu alhali ba su da karfin jurewa hakan bugu da kari kamar yadda wasu ayoyi suka yi bayani mala'kun da za a iya ganinsu cikin siffar mutane sun bayyana a zahiri kamar ga Annabi Ibrahima da Ludu amma duk da haka kafirai suka karyata da ci gaba da kafirci. Wasu sun bukaci tayar da matacce daya daga cikin mu'ujizar Annabi Isa (AS) shin dukan wadanda suka ga wannan mu'ujizar daga Annabi Isa ne suka yi imani? Amsa matukar jayayya da kiyayya a zukatansu ba za su yi imani ba ko da an sabkar masu da mala'ika da ganinsa a zahiri ko tayar da matacce ya yi masu magana da duk wani abu da suka bukata ba za su yi imani ba za su zarge ka da boka mai sihiri don ba a shirye suke su yi imani da bin hanya madaidaiciya.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda biyu akalla:

1-Sani da ilimi kawai ba su wadatar ba don yin imani.

2- Zai yi wuya dukan mutane su yi imani domin Allah ya bawa kowa damar zabin abin da yaga dama.

Sai a saurari karatun aya ta 112 a cikin suratul An'am:

وَكَذَلِكَ جَعَلْنَا لِكُلِّ نِبِيٍّ عَدُوّاً شَيَاطِينَ الإِنسِ وَالْجِنِّ يُوحِي بَعْضُهُمْ إِلَى بَعْضٍ زُخْرُفَ الْقَوْلِ غُرُوراً وَلَوْ شَاء رَبُّكَ مَا فَعَلُوهُ فَذَرْهُمْ وَمَا يَفْتَرُونَ{112}

Kuma kamar wancan ne Muka sanya wa kõwane Annabi makiyi; shaidãnun mutãne da aljannu, sãshensu yanã yin ishãra zuwa sãshe da kawãtaccen zance bisa ga rũdi. Kuma dã Ubangijinka Yã so, dã ba su aikatã shi ba, don haka ka bar su da abin da, suke kirkirãwa.

Kamar ayar da ta gabata wannan ayar ma na cewa: wasu kungu na mutane da aljannu ba a shirye suke su yi aiki da koyarwar Annabawa sai ma a maimakon haka suna kalubalantar hanya madaidaiciya.To abu mai muhimmanci zabin da Allah ya bawa mutum da aljanni kamar yadda shaidan ya zabi bata da tabewa wanda ya fito daga jinsin aljanni wanda ya hallaka saboda kin bin umarnin Allah to haka mutane an ba mu wannan damar ta zabar shiriya don radin kanmu babu tilastawa har zuwa karshen rayuwarmu a wannan duniya. Yawancin mutane suna fadawa ne tarkon shaidan da kin bin tafarkin Annabawa na shiriya da tauhidi kuma shaidan ne ke ingiza su su fada tarkonsa amma duk da haka Annabawa da manzonni da malaman shiriya suna ci gaba da kokarin shiryar da mu da fadakar da mu don samin tsira duniya da lahira amin.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda biyu akalla:

1-A tsawon tarihi akwai gwagwarmaya tsakanin gaskiya da karya ba ta kai bantu da wani lokaci ba wani ba.

2-Mu yi hankali da maganganu da jawabai masu dadi na yaudara da yawancin tafarkin karya da na shaidan wannan ya kumsa.

Sai a saurari karatun aya ta 113 a cikin suratul An'am:

وَلِتَصْغَى إِلَيْهِ أَفْئِدَةُ الَّذِينَ لاَ يُؤْمِنُونَ بِالآخِرَةِ وَلِيَرْضَوْهُ وَلِيَقْتَرِفُواْ مَا هُم مُّقْتَرِفُونَ{113}

Kuma dõmin zukãtan wadanda ba su yi ĩmãni da Lãhira ba su karkata saurãrẽ zuwa gareshi, kuma dõmin su yarda da shi, kuma dõmin su kamfaci abin da suke mãsu kamfata.

Wannan aya tana nuni ne kan masu yada kiyayya kan gaskiya da cewa; ku lura da yin takatsantsan da masu shirya jawabi da maganganun yaudara don batar da ku da za ku ji sun iya tsara bayani da salon magana da isar da ku inda suke so da kai ku su baro. Idan kun fahimci wadanda ke tafarkin shaidan da yi maku jawaban yaudara kar ku kasance tare da su da saurarensu ko zama tare da su.Kuma ku killace kar su kutsa cikinku don batar da ku.

Sai a saurari karatun aya ta 114 a cikin suratul An'am:

أَفَغَيْرَ اللّهِ أَبْتَغِي حَكَماً وَهُوَ الَّذِي أَنَزَلَ إِلَيْكُمُ الْكِتَابَ مُفَصَّلاً وَالَّذِينَ آتَيْنَاهُمُ الْكِتَابَ يَعْلَمُونَ أَنَّهُ مُنَزَّلٌ مِّن رَّبِّكَ بِالْحَقِّ فَلاَ تَكُونَنَّ مِنَ الْمُمْتَرِينَ{114}

Shin fa, wanin Allah nake nẽma ya zama mai hukunci, alhãli kuwa Shĩ ne wanda Ya saukar muku da Littãfi abin rabẽwadaki-daki? Kuma wadanda Muka bai wa Littãfi sunã sanin cẽwa lalleshi (Alkur'ãni) abin saukarwa ne daga Ubangijinka, da gaskiya? Sabõda haka kada ku kasance daga mãsu shakku.

Wannan aya tana magana kan ma'abuta littafi daga yahudawa da kiristoci da cewa: ku da kuka ga ma'aikin Allah ,kun saurari jawabinsa kuma kun sani abin da yake fadi ya yi daidai da wanda Annabin Musa da Isa (AS) suka fadi a cikin littafin Attaura da Injila amma ba a shirye kuke ku yi imani da littafin da ya zo da shi kuma bukatun mu'ujizar da kuke bukata sun yi kama da wadanda Musa da Isa (AS) suka zo da su kawai kuna fakewa ne don haka ci gaban ayar ke yi wa musulmi kashedi da kar su yi shakku kan tafarkin gaskiya.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda biyu akalla:

1-Daya daga cikin gaskiyar Addinin musulunci da manzon Allah ya zo da shi bada labarin annabawa da manzonnin da suka gabata a cikin attaura da injila.

2- kafircin wani ba ya shafar wani ko batar da wani, kowa na girbar abin da ya shibga ne.

Da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shirin na yau sai kuma shiri na gaba da yardar Allah kafin lokacin Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram na na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalamu alaikum warahmatullahi wa barkatuhu.

Suratul An'am, Aya Ta 115-119 (Kashi Na 213)

Jama'a masu saurare Assalamu alaikum barkarku da sake saduwa da mu a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda ,inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki ,tare da yin bayani gwargwadon iko kan abin da suke koyar da mu ,tare da yi mana hannunka mai sanda a cikin lamurran rayuwa da zamantakewa.Amma kafin mu shiga cikin shirin gadan gadan ga abin da aka yi mana tanadi a kan inji.

Sai a saurari karatun aya ta 115 a cikin suratul An'am:

وَتَمَّتْ كَلِمَتُ رَبِّكَ صِدْقاً وَعَدْلاً لاَّ مُبَدِّلِ لِكَلِمَاتِهِ وَهُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ{115}

Kuma kalmar Ubangijinka tã cika, tanã gaskiya da ãdalci. Babu mai musanyãwa ga kalmõminSa, kuma Shi ne Maiji, Masani.

A cikin shirin da ya gabata mun bayyana cewa; wasu masana na yahudawa da nasara suna madina lokacin sabkar kur'ani kuma sunada masaniya kan kasancewar wannan littafi daga Allah ya ke amma saboda wasu dalilai masu yawa mabanbanta ba a shirye suke su yi imani da shi ba don haka wannan aya ke cewa: ma'aikin Allah: Kar ka da mu da kin yin imani da kai domin Allah ya san da gaskiyarka kan abin da ya sabkar a gare ka .Duk wata magana ta gaskiya da hankali ya san abin da kur'ani ya kumsa hukumci ne daga Allah don kafa hujja da adalci a tsakanin al'umma kuma har a bada ba za a samu sauyi ko canji a cikinsa ba kuma zai dawwama sabanin litttafan da suka gabace shi.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda biyu akalla:

1-Kur'ani ne kamilalle kuma cikekken littafin da ya kumshi maganar Allah da sako ga mutane da aljannu saboda haka ma ya zamanto addini na karshe. 2- Dokokin Kur'ani sun ginu da jinjina aiki da gaskiya da adalci bin gaskiya da aiki da ita da kuma yada gaskiya a ko ina.

Sai a saurari karatun aya ta 116 a cikin suratul An'am:

وَإِن تُطِعْ أَكْثَرَ مَن فِي الأَرْضِ يُضِلُّوكَ عَن سَبِيلِ اللّهِ إِن يَتَّبِعُونَ إِلاَّ الظَّنَّ وَإِنْ هُمْ إِلاَّ يَخْرُصُونَ{116}

Kuma idan ka bi mafiya yawan wadanda suke a cikin kasa da dã'a sunã batar da kai daga hanyar Allah. Ba su bin kõme sai fãce kaddari-fadi suke yi.

Ita kuwa wannan aya tana magana ne ga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka da kuma wadanda suka yi da shi cewa:yanzu da aka sabkar maku da maganar gaskiya daga Allah ,kar ku damu da raaayi da abubuwan da wasu ke cewa ko da kuwa adadinsu yana da yawa domin yawan yawan mutane ba shi ne ke nuni da suna kan gaskiya musamman ga al'ummar da ke rayuwa da yawancin mutane ba su kahu kan tafarkin hankali da aiki da gaskiya sai dai kan tafarkin cemfi da bin tafarkin iyaye da kakannunsu kafirai da mushirikai masu rayuwa cikin duhun bata da tabewa.Annabawa suna kokarin shiryar da mutane ne sabanin bukatar yawancin mutane da ke rayuwa cikin Al'umma. Kuma idan yawancin mutane ake la'akari da bin ra'ayinsu da babu wani annabi da manzo da za aiko ko ya yi kira zuwa wani abu da ya sabawa na mushrikai da kafirai. Amma a cikin al'amarin da ya shafi zabar shugaban kasa ana la'akari da yawan kur'un jama'a kuma wannan ba shi ne dalilin shi ne yafi cancantar rike wannan mukami ba saboda haka ra'ayin yawan mutane ba dalili ne na tafarki na gaskiya ko zabi na gari.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda uku akalla:

1-Shiriya ta gaskiya tana tare da mabiya gaskiya da Kur'ani ba wai yawan mutane ba.

2-A cikin lamuran tunani da akida ba a la'akari da yawanci sai a cikin lamura da suka shafi zamantakewa ake amfani da wadanda suka fi yawa don warware wata matsala ba wai gane gaskiya ba.

3- A kullum mu yi aiki da gaskiya da hankali ba son zucciya da son rai ba. Sai a saurari karatun aya ta 117 a cikin suratul An'am:

إِنَّ رَبَّكَ هُوَ أَعْلَمُ مَن يَضِلُّ عَن سَبِيلِهِ وَهُوَ أَعْلَمُ بِالْمُهْتَدِينَ{117}

Lalle ne Ubangijinka Shĩ ne Mafi sani ga wanda yake bacẽwa daga hanyarsa kuma Shi ne mafi sani ga masu shiryuwa.

Kamar yadda ta bayyana mana cewa ra'ayin yawancin mutane ba zai tamtamce mana tafarkin gaskiya ba ,to sai mu fahimci gaskiya da yin riko da ita ta hanyar fadar Allah ko da kuwa wannan gaskiya tana tare da gungun mutane mafi karamci. Fahimtar gaskiya ko bata yana bukatar ilimi da fahimta da tsarkin zucciya.Kan haka duk mutum yana bukatar aiki da hankali da zai taimaka masa wajan fahimtar gaskiya daga cikin karya amma shi ilimi yana iya kai mu ga bata idan muka rungume shi ,shi kadai saboda haka wannan aya ke kiranmu zuwa ga neman taimakon Allah ya bamu ilimi da shiriya daga gare shi duniya da lahira.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda biyu akalla:

1- Komin ilimin mutun da hankalinsa dole ya dogara da ilimi da shiriya daga Allah kamar yadda hankali ke cewa mafi sani shi ne ya cancanci a bi shi.

2- kar mu yi zaton za mu iya yaudarar Allah ta hanyar riya da munafinci kamar yadda muke yaudarar mutane.Allahu shi ne masanin abin da muka boye kuma shi ne mai shiryarwa.

Sai a saurari aya ta 118 da 119 a cikin suratul An'am kamar haka:

فَكُلُواْ مِمَّا ذُكِرَ اسْمُ اللّهِ عَلَيْهِ إِن كُنتُمْ بِآيَاتِهِ مُؤْمِنِينَ{118} وَمَا لَكُمْ أَلاَّ تَأْكُلُواْ مِمَّا ذُكِرَ اسْمُ اللّهِ عَلَيْهِ وَقَدْ فَصَّلَ لَكُم مَّا حَرَّمَ عَلَيْكُمْ إِلاَّ مَا اضْطُرِرْتُمْ إِلَيْهِ وَإِنَّ كَثِيراً لَّيُضِلُّونَ بِأَهْوَائِهِم بِغَيْرِ عِلْمٍ إِنَّ رَبَّكَ هُوَ أَعْلَمُ بِالْمُعْتَدِينَ{119}

Sabõda haka ku ci daga abin da aka ambaci sũnan Allah kansa, idan kun kasance mãsu ĩmãni da ãyõyinSa. Kuma mẽne ne ya sãme ku, bã zã ku ci ba daga abin da aka ambaci sũnan Allah a kansa,alhãli kuwa, hakĩka, Ya rarrabe, muku daki-daki, abin da Ya haramta a kanku, fãce fa abin da aka bukãtar da ku bisa lalũra zuwa gare shi? Kuma lalle ne mãsu yawa sunã batarwa, da son zũciyõyinsu, ba da wani ilmi ba. Lalle ne Ubangijinka Shĩ ne Mafi sani ga mãsu ta'addi.

Wadannan ayoyi na nuni ne da daya daga cikin mafi girman misali na shirka a rayuwar mutane da cewa: Abubuwan da suke aikatawa ya yi nisa da tafarkin Allah. Don sun kaucewa hanya da zurfafawa a cikin duhun kafirci da shirka inda hatta a ci da sha suna wuce gon ada iri da halastawa kansu ko haramta abin da suke so.Sun ganin yanka wasu dabbobi ya haramta da cin namansu.To wannan ba gaskiyaba ne da danganta hakan da Allah.Su sani duk dabbar da Allah ya halitta namanta ta halasta bayan an yanka ta da ambatan sunan Allah.Allah ne mahaliccin ku da dabbobi kuma shi ne ya halitta maku cin namansu kuma idan kuka ambaci sunan Allah wajan yanka dabba ya kara tsarkake maku naman da kara muku lafiyar jiki. Kuma ambaton sunan Allah yana tsakake maku ruhi da kara kamala ta wannan abinci da kuka ci. Ci gaban ayoyin na tabbatar mana da nisantar dabbobin da Allah ya haramta da kusantar wadanda ya halitta amma kafirai da mushrikai sai su haramta abin da suka ga dama don son rai da jahilcinsu kuma wannan wuce gona da iri ne kan tafarkin Allah da hakkokin mutane.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda biyu akalla:

1-Hatta abin da mumini zai ci ya sha ya bi umarnin Allah da tafarkin addini ba son rai da zucciya ba.

2- Dole mutum ya yi aiki da halal da haram da Allah ya yi bayani kansu.

3- Babu laifi cin abin da aka haramta a halin larura domin Addini ne ya yi mana falala da wannan sassuci.

Da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shirin na yau sai kuma shiri na gaba da yardar Allah kafin lokacin Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram na na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalamu alaikum warahmatullahi wa barkatuhu.

Suratul An'am, Aya Ta 120-122 (Kashi Na 214)

Jama'a masu saurare Assalamu alaikum barkarku da sake saduwa da mu a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda ,inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki ,tare da yin bayani gwargwadon iko kan abin da suke koyar da mu ,tare da yi mana hannunka mai sanda a cikin lamurran rayuwa da zamantakewa.Amma kafin mu shiga cikin shirin gadan gadan ga abin da aka yi mana tanadi a kan inji.

Sai a saurari karatun aya ta 120 a cikin suratul An'am:

وَذَرُواْ ظَاهِرَ الإِثْمِ وَبَاطِنَهُ إِنَّ الَّذِينَ يَكْسِبُونَ الإِثْمَ سَيُجْزَوْنَ بِمَا كَانُواْ يَقْتَرِفُونَ{120}

Kuma ku bar bayyanannen zunubi da bõyayyensa. Lalle ne wadanda suke tsiwurwurin zunubi za a sãka musu da abin da suka kasance sunã kamfata.

Wannan ayar tana bayyanawa wadanda suka yi imani da Allah da manzonsa da kaucewa duk wani sabo na zahiri dad a na boye da muke aikatawa a boye duk da cewa kowa ne irin sabo yanada da zahiri dad a muke aikata wa a gaban mutane da kuma badini da ke lalata karfin imini da ruhin mutum tamkar abinci mai guba ne yana da dadi a baki amma sannu a hankali yak e gaurbata gangar jiki da ruhi da kwantar da mutum. Haka cin abin da Allah ya haramta zai yuyu yanada dadi a baki amma yana cutar da zucciya da mutum da kekashewar zucciya tamkar dutse.Ci gaban ayar na shaida mana cewa; wadanda suka kafircewa Allah a wannan duniya ko a lahira za su gamu da aikin da suka aikata,domin kuwa kowa zai ga sakamakon aikin day a aikata.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda biyu akalla:

1- Musulunci yana aiki da tsarki na zahiri da kuma na badini don haka mu nisanci aikata sabo da mummunan zato ga mutane. 2-Duk da cewa shaidan na yi wa mutum wasiwasi kan aikata sabo amma mutum ne ke da zabin aikata abin da yaga dama na sabo.

Sai a saurari karatun aya ta 121 a cikin suratul An'am:

وَلاَ تَأْكُلُواْ مِمَّا لَمْ يُذْكَرِ اسْمُ اللّهِ عَلَيْهِ وَإِنَّهُ لَفِسْقٌ وَإِنَّ الشَّيَاطِينَ لَيُوحُونَ إِلَى أَوْلِيَآئِهِمْ لِيُجَادِلُوكُمْ وَإِنْ أَطَعْتُمُوهُمْ إِنَّكُمْ لَمُشْرِكُونَ{121}

Kada ku ci daga abin da ba a ambaci sũnan Allah ba a kansa . Kuma lalle ne shĩ fãsikanci ne. Kuma lalle ne, shaidãnu, hakĩka, suna yin ishãra zuwa ga masõyansu, dõmin su yi jãyayya da ku. Kuma idan kuka yi musu dã'a, lalle ne kũ, hakĩka, mãsu shirki ne.

Ganin addinan Allah sun zo ne don shiryar da al'umma da sa'adan mutum don haka dokokinsu suka shafi harkokin rayuwar mu a wannna duniya da abin da za mu ci mu sha da sanya kuma musulunci yana lura da abin da za mu ci mu sha da kuma sitirarmu . Idan muka yi la'akari za mu ga wani abu ne da bai taka kara ya karya ba daga cikin ni'imomin Allah na dabi'a ya haramta mana saboda Allah masani ya san lahani da cutarwa da ke tattare da wannan abin ci ko sha ko sitira don haka ya haramta mana. Daya daga cikin abin da Allah ya haramta akwain cin mushe da wasu larabawa masu izgili ke cewa: wane banbanci ke akwai cin naman dabba da ta mutu da wadda aka yanka asali ma dabbar da ta mutu,kisan Allah ne kuma kisan Allah yafi na mutum to irin wannan magana wata yaudara ce ta shaidan .Domin duk dabbar da ta mutu tana dauke da wasu cututtuka kuma cin namanta yana cutar da mutum sabanin dabbar da aka yanka da jinin jikinta ya fita daka ainahin naman dabbar kuma namanta lafiyayye ne uwa uba kafin yanka dabba ana ambaton sunan Allah ga mumuni wanda ya yi imani da Allah kamar yadda yake kollon kibla lokacin salla haka sai dabbar ta kalli kibla lokacin yanka ta.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda biyu akalla:

1- hatta a ci da shayarwa a kiyayye dokokin musulunci.

2- wasiwasin shaidan kan abin da aka hana cinsa alamar mummunan tasiri a ruhinmu ne.

Sai a saurari karatun aya ta 122 a cikin suratul An'am:

أَوَ مَن كَانَ مَيْتاً فَأَحْيَيْنَاهُ وَجَعَلْنَا لَهُ نُوراً يَمْشِي بِهِ فِي النَّاسِ كَمَن مَّثَلُهُ فِي الظُّلُمَاتِ لَيْسَ بِخَارِجٍ مِّنْهَا كَذَلِكَ زُيِّنَ لِلْكَافِرِينَ مَا كَانُواْ يَعْمَلُونَ{122}

Shin, kuma wanda ya kasance matacce sa'an nan Muka rãyar da shi, kuma Muka sanya wani haske dõminsa, yanã tafiya da shi, yanã zama kamar wanda misãlinsa yanã cikin duffai, shĩ kuma ba mai fita ba daga gare su? Kamar wancan ne aka kawãta wa kãfirai abin da suka kasance sunã aikatãwa.

Kamar yadda ya zo a cikin ruwaya a daidai lokacin da Hadarat Hamza baffan ma'aikin Allah zai yi imani da shi da karbar musulunci yana kuma kare ma'aikin Allah daga cuutarwar da kafiri mushriki Abu Jahal ke yi manzon tsira sai wannan ayar ta sabka da jinjina wa Hamza wannan bajinta da aiki mai kyau nasa kamar yadda wata ayar ta sabka kan wani baffansa abu lahafin wanda ya nuna bakar kiyayya da jayayya da cutarwa kan ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda biyu akalla:

1- Shirka da kafirci na kai mutum ga hallaka kamar yadda imani na raya mutum da samar masa da sa'ada don haka rayuwa da mutuwa na hakika su ne imani da kafirci.

2- Imani yana haskaka zucciya da tunani yayin da kafirci ya dashe zucciya da zullimi ,mutum mumuni ba ya da na sani da kasa samin mafita domin hasken Allah zai haskaka masa rayuwa.

Da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shirin na yau sai kuma shiri na gaba da yardar Allah kafin lokacin Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram na na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalamu alaikum warahmatullahi wa barkatuhu.

Suratul An'am, Aya Ta 123-125 (Kashi Na 215)

Jama'a masu saurare Assalamu alaikum barkarku da sake saduwa da mu a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda ,inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki ,tare da yin bayani gwargwadon iko kan abin da suke koyar da mu ,tare da yi mana hannunka mai sanda a cikin lamurran rayuwa da zamantakewa.Amma kafin mu shiga cikin shirin gadan gadan ga abin da aka yi mana tanadi a kan inji.

Sai a saurari karatun aya ta 123 a cikin suratul An'am:

وَكَذَلِكَ جَعَلْنَا فِي كُلِّ قَرْيَةٍ أَكَابِرَ مُجَرِمِيهَا لِيَمْكُرُواْ فِيهَا وَمَا يَمْكُرُونَ إِلاَّ بِأَنفُسِهِمْ وَمَا يَشْعُرُونَ{123}

Kuma kamar wancan ne Mun sanya a cikin kõwace alkarya, shugabanni sũ ne mãsu laifinta dõmin su yi mãkirci a cikinta, alhãli kuwa ba su yin makirci fãce ga rayukansu, kuma ba su fahimta.

A cikin shirin da ya gabata mun bayyana cewa: wasu manyan makka kamar su Abu Jahal suna kulla makirci ga manzon musulunci da sahabbansa don hana yaduwar musulunci saboda haka wannan aya ke cewa: manzon da mumunai irin su Abu Jahil ba wani sabon abu ba ne a tsawon tarihin rayuwar annabawa da manzonni da waliyan Allah akwai irin wadannan mutane masu tashi tukuru wajan ganin sun dakile da rusa addinin Allah da hana Annabawa isar da sakon da suka zo da shi. Kuma duk wani aiki mai kyau ko lala da mutum zai aikata yana karkashin kudurar Allah ne idan ba haka ba ba za mu iya komi ba saboda haka wannan ayar ke cewa; masu banna da neman toshe hasken addini kar su yi zaton Allah bai san abin da suka yi ba,zai iya kawar da su ba su fi karfin kudurar Allah ba.Sunnar Allah ce da damar da Allah ya bamu ta zabar abin da muka ga damar aikatawa a wannan duniya ya sa aka kale su a wannan duniya yayin da a gobe kiyama za su girbe abin da suka aikata.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda uku akalla:

1- Jagororin bata sune ummul aba'isar rushe tattalin arziki da tunanin jama'a da al'umma.

2- Tunanin masu adawa da Annabawa da Manzonni aikata yaudara da yin zagon kasa ba aikata gaskiya da tsarkaka ba.

3- Mu sani duk wanda ya gina ramin mugunta shi ne zai fada ma'ana mai yaudara yana yaudarar kansa ne.

Sai a saurari karatun aya ta 124 a cikin suratul An'am:

وَإِذَا جَاءتْهُمْ آيَةٌ قَالُواْ لَن نُّؤْمِنَ حَتَّى نُؤْتَى مِثْلَ مَا أُوتِيَ رُسُلُ اللّهِ اللّهُ أَعْلَمُ حَيْثُ يَجْعَلُ رِسَالَتَهُ سَيُصِيبُ الَّذِينَ أَجْرَمُواْ صَغَارٌ عِندَ اللّهِ وَعَذَابٌ شَدِيدٌ بِمَا كَانُواْ يَمْكُرُونَ{124}

Kuma idan wata ãyã ta je musu sai su ce: "Ba zã mu yi ĩmãni ba, sai an kãwo mana kamar abin da aka kãwo wa manzannin Allah." Allah Mafi sanin inda Yake sanya manzancinSa. Wani wulakanci a wurin Allah da wata azãba mai tsanani zã su sãmi wadanda suka yi laifi, sabõda abin da suka kasance sunã yi na mãkirci.

Wannan aya ma kamar wadda ta gaba ce ta tana magana ne kan nauyin makirce-makircen masu adawa da manzon rahama da cewa; daya daga cikin abin da mushrikan Makka ke fakewa shi ne cewa sun fi ma'aikin Allah dukiya da kudi da matsayi na zahiri da suna da ke raya cewa ma'aiki ne daga Allah don shiryar da mu. Idan wani ya cancanci Allah ya aiko shi to mu ne ba shi ba . Kuma ko ba komi duk abin da aka yi masa wahayi sai a yi mana mu ma to da haka ba ta samu ba ba za mu yi imani da shi ba ko gaskanta abin da yake cewa ba. To Allah a cikin kur'ani ya masa masu da cewa: Allah ne ya fi sanin wanda ya cancanci ya ba shi wannan matsayi mai girma na isar da sakonsa ga bayunsa kuma kudi da dukiya ba su da wani fifiko ko kusa ,shiriyar da mutane yana bukatar wasu abubuwa ba wannan ba.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda biyu akalla:

1- daga cikin hanyoyin kin amsa kiran Annabawa akwai jin fifiko da jiji da kai da girman kai wajan bin gaskiya.

2- Mu sani Allah ya yi alkawalin kunyatar da masu girman kai tun a wannan duniya domin zama darasi ga saura.

Sai a saurari karatun aya ta 125 a cikin suratul An'am:

فَمَن يُرِدِ اللّهُ أَن يَهْدِيَهُ يَشْرَحْ صَدْرَهُ لِلإِسْلاَمِ وَمَن يُرِدْ أَن يُضِلَّهُ يَجْعَلْ صَدْرَهُ ضَيِّقاً حَرَجاً كَأَنَّمَا يَصَّعَّدُ فِي السَّمَاء كَذَلِكَ يَجْعَلُ اللّهُ الرِّجْسَ عَلَى الَّذِينَ لاَ يُؤْمِنُونَ{125}

Dõmin haka wanda Allah Ya yi nufin ya shiryar da shi sai ya bũda kirjinsa dõmĩn Musulunci, kuma wanda Ya yi nufin Ya batar da shi, sai Ya sanya kirjinsa mai kunci matsattse, kamar dai yanã tãkãwa ne a ckin sama. Kamar wannan ne Allah Yake sanyãwar kazanta a kan wadanda bã su yin ĩmãni.

Wannan aya ta hada sauran ayoyin da suka gabata kan cewa: makoma da tushen kafirci da imani shi ne zucciya da ruhin mutane a daidaikunsu kafirci ko imani. Kuma wani sirri ne na ayyukan da muke aikata ,imani amincewar zucciya ne kan aikata gaskiya da mika wuya ga dokokin Allah tare da mincewar zucciya da ruhi. Yayin da kafirci kin zucciya ne da nuna kiyayya da jayayya da tsayuwar kalubalantar gaskiya don haka kur'ani ke cewa; duk wanda ya samu shiriyar Allah sai ya tsarkake zucciyarsa da ruhinsa to zai karbi gaskiya amma duk wanda ruhinsa ya gurbace ba za iya karbar gaskiya ba da yin imani kamar yadda gangar jikin maras lafiya ba ta jin dadi da dandon abinci mai dadi.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda biyu akalla:

1- Karbar gaskiya tana bukatuwa da tsarkin zucciya da na ruhi da zaran mutum ya karbi gaskiya zai ciyar da ruhinsa gaba kan tafarkin Allah.

2- Batattu suna cikin damuwa da kumci ko da kuwa a zahiri suna nuna sabanin hakan.

Da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shirin na yau sai kuma shiri na gaba da yardar Allah kafin lokacin Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram na na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalamu alaikum warahmatullahi wa barkat

Suratul An'am, Aya Ta 126-130 (Kashi Na 216)

Jama'a masu saurare Assalamu alaikum barkarku da sake saduwa da mu a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda ,inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki, tare da yin bayani gwargwadon iko kan abin da suke koyar da mu ,tare da yi mana hannunka mai sanda a cikin lamurran rayuwa da zamantakewa.Amma kafin mu shiga cikin shirin gadan gadan ga abin da aka yi mana tanadi a kan inji.

Sai a saurari karatun aya ta 126 da kum 127 a cikin suratul An'am:

وَهَـذَا صِرَاطُ رَبِّكَ مُسْتَقِيماً قَدْ فَصَّلْنَا الآيَاتِ لِقَوْمٍ يَذَّكَّرُونَ{126} لَهُمْ دَارُ السَّلاَمِ عِندَ رَبِّهِمْ وَهُوَ وَلِيُّهُمْ بِمَا كَانُواْ يَعْمَلُونَ{127}

Wannan ita ce hanya ta Ubangijinka madaidaiciya. Lalle ne Mun bayyana ãyõyi daki-daki ga mutãne mãsu karbar tunãtarwa.

Sunã da gidan aminci a wurin Ubangjinsu, kuma Shĩ ne Majibincinsu, sabõda abin da suka kasance sunã aikatãwa.

A cikin shirye shiryen da suka gabata mun kawo ayoyi da ke bayani kan fuskantar ayoyin Allah da mumunai da kafirai suka yi da kuma nuni da alamomin Allah kuma a aya ta karshe mun bayyana cewa; karbar musulunci alama ce ta tsarkin zucciya da ruhi n mutum to ita wannan aya na cewa ne: dokokin musulunci ba wani abu ba ne face hanya madaidaiciya da Allah ya shinfida mana domin isa ga kamala da sa'ada ta hanyar aiki da akida irin ta musulunci. Babu wanda zai isa ga kamala sai wanda ya bi hanya madaidaiciya da aiki da hanayr Allah a wannan duniya da kuma a ranar kiyama sai samu aminci daga azaba da kumci da shiga gidan aljanna da matsayi babba.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda biyu akalla:

1-Hanya madaidaiciya ita ce hanayr Allah wadda ba ita ba hanyar bata ce.

2-dauwama kan hanya madaidaiciya yana bukatar fadakarwa a kullum don taimakawa mutum shagaltuwa da fita daga hanya ta gaskiya.

Sai a saurari karatun aya ta 128 da kum 129 a cikin suratul An'am:

وَيَوْمَ يِحْشُرُهُمْ جَمِيعاً يَا مَعْشَرَ الْجِنِّ قَدِ اسْتَكْثَرْتُم مِّنَ الإِنسِ وَقَالَ أَوْلِيَآؤُهُم مِّنَ الإِنسِ رَبَّنَا اسْتَمْتَعَ بَعْضُنَا بِبَعْضٍ وَبَلَغْنَا أَجَلَنَا الَّذِيَ أَجَّلْتَ لَنَا قَالَ النَّارُ مَثْوَاكُمْ خَالِدِينَ فِيهَا إِلاَّ مَا شَاء اللّهُ إِنَّ رَبَّكَ حَكِيمٌ عَليمٌ{128} وَكَذَلِكَ نُوَلِّي بَعْضَ الظَّالِمِينَ بَعْضاً بِمَا كَانُواْ يَكْسِبُونَ{129}

Kuma rãnar da yake tãra su gaba daya (Yanã cẽwa): "Yã jama'ar aljannu! Lalle ne kun yawaita kanku daga mutãne." Kuma majibantansu daga mutãne suka ce: "Yã Ubangjinmu! Sãshenmu ya ji dãdi da sãshe, kuma mun kai ga ajalinmu wanda Ka yanka mana!" (Allah) Ya ce: "Wuta ce mazaunarku, kunã madawwama acikinta, sai abin da Allah Ya so. Lalle ne Ubangijinka Mai hikima ne, Masani."

Kuma kamar wancan ne Muke jibintar da sãshen azzãlumai ga sãshe, sabõda abin da suka kasance sunã tãrãwa.

Wadannan ayoyi na sake yin nuni da halin da tababbu ke ciki a ranar tashin kiyama da halin da suke ciki da farko na cewa; Ko shaidan ne majibincin tabbabbu ko shaidanun mutane dukan hanyoyin biyu ba su da wani amfani ga mutum domin babu wata riba a gare shi saboda babu hanya da damar komawa baya don gyara abin da ya wuce ,shaidan ko aljannu maus sawa mutum wasiwasi ba su iya taimaka masa da komi domin su kansu a wannan rana ta kansu suke, kuma hatta shi kansa babu wani abu da iya na kubutar da kansa daga wannan hali da yake ciki .Mutum mai hankali shi ne wanda ya yi dace da gidan aljanna a wannan rana wanda ya sami kansa cikin jin dadi wanda ba ya karewa. Ci gaban ayoyin na cewa; ku wadanda kuka aika sabo a duniya a yau kun hura wuta da za ta kuna ku da kanku.kuma babu wata hanya ta kubuta daga wannan bala'I sai idan Allah ya so ya yafe muku idan kuma ya so ya azabtar da ku kuma Allah baya abu sai da dadlili da hikima da yi wa wadanda suka kafirta hisabi kuma shi ne mai rahama da jin kai.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa hudu:

1- A kiyama mutum da shaidan duk za a tada su a guri daya da yi wa kowa tambayar aikin da ya aikata,shaidan da mabiyansa su shiga wutar jahannama.

2- Mun rika yin tunani kan karshenmu da aikata alheri don gobe kiyama.

3- Dukan kafirai da tababbu baki daya za a yi masu azaba ne da dawwama a cikin wuta karkashin hikima da ilimin Allah.

4-mabiya shaidan a rayuwa suna shinfida mulkin azzalumai ne kan al'umma da mulkinsu.

Sai a saurari karatun aya ta 130 a cikin suratul An'am:

يَا مَعْشَرَ الْجِنِّ وَالإِنسِ أَلَمْ يَأْتِكُمْ رُسُلٌ مِّنكُمْ يَقُصُّونَ عَلَيْكُمْ آيَاتِي وَيُنذِرُونَكُمْ لِقَاء يَوْمِكُمْ هَـذَا قَالُواْ شَهِدْنَا عَلَى أَنفُسِنَا وَغَرَّتْهُمُ الْحَيَاةُ الدُّنْيَا وَشَهِدُواْ عَلَى أَنفُسِهِمْ أَنَّهُمْ كَانُواْ كَافِرِينَ{130}

Yã jama'ar aljannu da mutãne! Shin, manzanni daga gare ku ba su jẽ muku ba sunã lãbarta ãyõyiNa a kanku, kuma sunã yi muku gargadin haduwa da wannan yini nãku? Suka ce: "Mun yi shaida a kan kãwunanmu." Kuma rãyuwar dũniya tã rũdẽ su. Kuma suka yi shaida a kan kãwunansu cẽwa lalle ne sũ, sun kasance kãfirai.

Wannan ayar ci gaban bayanin ayar da ta gabace ta ce da ke bayin cewa: Allah madaukakin sarki a ranar kiyama kafin ya azabtar da kafirai sai sun tabbatar da leifin da suka aika da kansu da tabbatar da sun fahimci gaskiya amma suka ki binta kuma suna iya karbar shiriya amma suka rungumi bata da tabewa.sun ji sunan kiyama amma suka rayu a duniya tamkar za su dauwama a cikinta da shagaltuwa da lahira da mantawa da Allah da ni'imomin da ya yi masu suna cikin haka sai kwacam suka samu kansu a kiyama da fuskantar abin da suka aikata mummuna.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa uku kamar haka:

1-Mutum da aljani kowa yanada nauyin da ya rataya kansa kuma an aiko masu da annabawa da manzonni.

2- Kiyama ba guri ba ne na boyewa ko musantawa hatta masu banna a doran kasa suna yin shaida abin da suka aikata mummuna don radin kansu.

3- Babban dalilin kifircewa kiran Annabawa da manzonni shi ne rungumar mutane da jin dadin wannan duniya mai karewa.

Da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shirin na yau sai kuma shiri na gaba da yardar Allah kafin lokacin Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram na na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalamu alaikum warahmatullahi wa barkatuhu.

Suratul An'am, Aya Ta 131-136 (Kashi Na 217)

Jama'a masu saurare Assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannuka mai sanda, inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki, tare da yin bayani gwargwadon iko kan abin da suke koyar da mu, tare da yi mana hannuka mai sanda a cikin lamurran rayuwa. Har yanzu muna cikin surat An'am, sai a biyo mu sannu a hankali a cikin shirin.

Aya ta (131) da (132) surat An'am

ذَلِكَ أَن لَّمْ يَكُن رَّبُّكَ مُهْلِكَ الْقُرَى بِظُلْمٍ وَأَهْلُهَا غَافِلُونَ{131} وَلِكُلٍّ دَرَجَاتٌ مِّمَّا عَمِلُواْ وَمَا رَبُّكَ بِغَافِلٍ عَمَّا يَعْمَلُونَ{132}

Wanan kuwa sabõda Ubangijinka bai kasance Mai halaka alkaryõyi sabõda wani zãlunci ba ne, alhãli kuwa mutãnensu sunã jãhilai.

Kuma akwai darajõji ga kõwanne daga abin da suka aikata. Kuma Ubangijinka bai zama mai shagala ba daga abin da suke aikatãwa.

Wannan aya tana nuni da cewa aiko annabawa da Allah ya yi zuwa ga mutane da aljannu yanke hujja ne gare su, domin kuwa Allah ba halakar da mutane da ba su da labarin shiriya, wannan ya saba ma sunnar Allah madaukakin sarki. A cikin tarihi dukkanin al'ummomin da Allah ya halakar ya halakar da su ne saboda musu da ayoyinsa, da bijire wa manzanninsa, kenan mutane da ake halakarwa wadanda manzanni suka je musu ne suka karyata su.

Babbar manufar aikewa da manzannin ita ce, yin wa'azi da shiryawarwa zuwa ga tafarkin Allah, aya ta 15 a cikin surat Isra'i, ta kara tabbatar da wannan magana da cewa, Allah ba ya azabtarwa har sai ya aiko manzo, wato kafirce ma sakonnin da manzannin Allah suka zo da shi n eke jawo azabar Allah a kan al'ummar, da hakan ka iya kai ga halakar da ita, kamar yadda ta faru da wasu al'ummomi da kur'ani mai tsarki ya ba mu labarinsu.

Darussan koyo a nan :

1 – Dukkanin mutanen da suke shiga wuta suna da labari kan addinin Allah, amma kuma suka bijire masa, kodai ta hanyar kin yin imani, ko kuma ta hanyar aikata laifuka na sabo.

2 – Mutanen da ba su da labarin sakonnin Allah, to Allah ne ya san matsayinsu a wurinsa.

Aya ta (133) da (134) surat An'am

وَرَبُّكَ الْغَنِيُّ ذُو الرَّحْمَةِ إِن يَشَأْ يُذْهِبْكُمْ وَيَسْتَخْلِفْ مِن بَعْدِكُم مَّا يَشَاءُ كَمَا أَنشَأَكُم مِّن ذُرِّيَّةِ قَوْمٍ آخَرِينَ{133} إِنَّ مَا تُوعَدُونَ لآتٍ وَمَا أَنتُم بِمُعْجِزِينَ{134}

Kuma Ubangijinka Wadãtacce ne Ma'abũcin rahama. Idan Yã so zai tafi da ku, kuma Ya musanya abin da Yake so daga bayanku, kamar yadda Ya kãga halittarku daga zũriyar wasu mutãne na dabam.

Lalle ne abin da ake yi muku alakawali mai zuwa ne, kuma kuma ku ba masu buwaya ba ne.

Wannan ayar mai albarka tana jan hankalin masu aikata laifuka na sabo, da kada su yi zaton cewa Allah ya kyale su bai safkar musu da wata azaba, hakan ya zama tamkar wani lamuni gare su na sabo, hakika Allah bad a bukatar ayyukansu kamar yadda sabonsu ba zai cutar da shi da komai, kuma shi mai rahma ne da tausayi ga dukaknin talikai, amma da Allah ya ga dama zai iya kawar da dukkanin mutanen da suke bayan kasa ya kawo wasu na daban, hakan ba abu ne dai zai gagari Allah inda ya so hakan, kuma abin da Allah ya yi alkawali na azaba ko rahama daidai da aikin mutane yana zuwa babu kokwanto.

Darussan koyo a nan su ne:

1 – Allah ba ya da bukatuwa zuwa ga ibadarmu, ba ma ibadarmu ba, hatta samuwarmu ba ta amfanar da Allah dakomai a cikin mulkinsa.

2 – Duk da cewa rahamar Allah ba ta da iyaka, amma wasu saboda tsananin sabo har sukan kai matsayin da suke fita daga karkashin wannan rahma ta ubangiji.

Aya ta (135) surat An'am

قُلْ يَا قَوْمِ اعْمَلُواْ عَلَى مَكَانَتِكُمْ إِنِّي عَامِلٌ فَسَوْفَ تَعْلَمُونَ مَن تَكُونُ لَهُ عَاقِبَةُ الدِّارِ إِنَّهُ لاَ يُفْلِحُ الظَّالِمُونَ{135}

Ka ce: "Yã ku mutãnena! Ku yi aiki a kan halinku, lalle ne nĩ mai aiki ne, sa'an nan da sannu zã ku san wanda ãkibar gida zã ta kasance a gare shi. Lalle ne azzãlumai bã zã su ci nasarã ba."

Wannan aya tana magana ne da manzon Allah (SAW) tana gaya masa matsayin da zai dauka dangane da masu musu da ayoyin Allah kuma suka ki karbar gaskiya, cewa manzon Allah ya fada musu cewa su yi duk aabin da suka ga dama, shi ma zai aiki da umurnin Allah, daga karshe za a san wane zai rabauta., domin kuwa duk wanda yake kan bata da zalunci, ba zai yi nasara ba, kuma ba zai samu kyaykyawan sakamako ba.

Darussan koyo a nan su ne: Karshen rayuwar mutum shi ne na sanin matsayinsa, ba abin da yake yi a wani lokaci na musamman a cikin rayuwarsa ba.

2 – Ko da kuwa akasarin mutane ba su yi imani da Allah ko bin sahihin tafarkinsa ba, hakan ba zai iya hana muminai na hakika bin tafarkin Allah ba komai tsanani da wahala da kunci.

Aya ta (136) surat An'am:

وَجَعَلُواْ لِلّهِ مِمِّا ذَرَأَ مِنَ الْحَرْثِ وَالأَنْعَامِ نَصِيباً فَقَالُواْ هَـذَا لِلّهِ بِزَعْمِهِمْ وَهَـذَا لِشُرَكَآئِنَا فَمَا كَانَ لِشُرَكَآئِهِمْ فَلاَ يَصِلُ إِلَى اللّهِ وَمَا كَانَ لِلّهِ فَهُوَ يَصِلُ إِلَى شُرَكَآئِهِمْ سَاء مَا يَحْكُمُونَ{136}

Kuma sun sanya wani rabõ ga Allah daga abin da Ya halitta daga shũka da dabbõbi, sai suka ce: "Wannan na Allah ne," da riyãwarsu "Kuma wannan na abũbuwan shirkinmu ne." Sa'an nan abin da ya kasance na gumakanmu ba zai sadu da Allah ba, abin da kuma ya kasance na Allah to shi ne zai sadu da gumakancu, abin da suke hukuntawa ya munana.

Wannan ayar tana yin nuni da wani lamari da yake da dangantaka da wata al'ada ta surkullen mushrikan Makka, inda suke kagabatar da wani abu daga cikin abin da suka noma, ko wasu daga cikin dabbobin da suka kiwata ga gumakansu da kuma Allah, abin da suke warewa ga gumakansu ana bayar da shi ne ga masu kula da gumukan, ko kuma ga wasu taruka da ake shiryawa a dakin Ka'aba domin girmama wadannan gumaka da tsarkakae su, yayin da kuma abin da suke gabatarwa ga Alah, ana bayar da shi ne ga mabukata da kuma baki.

Idan abin da ake bayarwa ga gumaka ya yi kadan, sai su diba daga abin da ake bayar na rabon Allah, amma idan abin da ake bayarwa ga Allah ne ya yi kadan, ba za su diba daga rabon gumuka ba, suna cewa ai shi Allah ba shi da bukatar wani abun duniya.

Duk da cewa suna raya cewa suna bauta ma gumaka domin su kusantar da su da Allah, to amma kuma a aikace suna fifita gumukan ne a kan Allah madaukakin sarki, wanda ya samar da su kuma ya samar da ita ce ko yambun da suke yin gumakan da su.

Wani abu da wannan ayar take nuni da shi a nan shi ne, abin da mushrikai suke yi na ware wani abu daga kaddarorinsu su bayar a matsayin hakkin Allah, wannan ya samo asali ne daga addinai da annabawa suka zo da su daga Allah, wanda aka sani a cikin addinin muslunci da zakka.

Darussan koyo a nan su ne:

1 – Mushrikan makka ba wai ba su yarda da samuwar Allah ba ne, sai dai sun dauka shi ne dan adam ba zai iya bauta ma Allah kai tsaye ba sai ya bi ta hanayar gumuka, wato tamkar su gumukan su ne kanan Alloli da suke kai mutane zuwa ga Allah.

2 – Annabawan Allah ba ya ga kira zuwa ga tauhidi, sun kuma yi gwagwarmaya domin kawar da surkulle da camfe-camfe a cikin al’umma.

Da wannan ne muka kawo karshen shirin namu na yau, sai idan Allah ya kai mu a shiri na gaba za a ji mu daga inda muka tsaya, kafin lokacin nake yi muku fatan alkhairi, wassalamu alaikum wa rahmatullah.

Suratul An'am, Aya Ta 137-140 (Kashi Na 218)

Jama'a masu saurare Assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannuka mai sanda, inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki, tare da yin bayani gwargawdon iko kan abin da suke koyar da mu, tare da yi mana hannuka mai sanda a cikin lamurran rayuwa. Har yanzu muna cikin surat An'am, sai a biyo mu sannu a hankali a cikin shirin.

Aya ta (137) a cikin surat An'am

وَكَذَلِكَ زَيَّنَ لِكَثِيرٍ مِّنَ الْمُشْرِكِينَ قَتْلَ أَوْلاَدِهِمْ شُرَكَآؤُهُمْ لِيُرْدُوهُمْ وَلِيَلْبِسُواْ عَلَيْهِمْ دِينَهُمْ وَلَوْ شَاء اللّهُ مَا فَعَلُوهُ فَذَرْهُمْ وَمَا يَفْتَرُونَ{137}

Kuma kamar wancan ne abũbuwan shirkinsu suka kãwata wa mãsu yawa daga cikin mushrikai kashe 'ya'yansu dõmin su halaka su, kuma dõmin su rikitar da addininsu a gare su, Kuma dã Allah Yã so dã ba su aikatã shi ba. Sabõda haka ka bar su da abin da suke kirkirãwa.

A cikin shirin da ya gabata an ambaci wasu daga cikin abubuwa na surkulle da da mushrikan makka suka rika a matsayin akida, inda suke fitar da wani bangare na abin da suka noma da kuma abin da suka kiwata a shekara, sai su bayar da su ga gumaka, a cikin kuma sai su fitar da wani bangare da ssuke kira rabon Allah, wanda suke raba ma mabukata da kuma baki.

Wannan ayar mai albarka tana yin ishara da wata akidar da mushrikan makka suke da ita, inda ba kawai bayar da dukiyoyinsu ko abin da suka mallaka ba ne akidar kusanci zuwa ga gumaka ba, a a har ma suka kashe ‘ya’yansu saboda samun kusanci ga gumaka.

Saboda tsananin kaunar gumuka da mushrikan makka suke yi, hakan ya sanya idanunsu sun rufe daga karbar gaskiya da shiriya a hannun manzon Allah, kuma sun gurbata addinin Ibrahim da suke raya cewa sun yarda da shi, domin kuwa daga cikiin abubuwan da annabi Ibrahim ya fara yi na shiryar da mutanensa har da rusa gumuka da suke bauta mawa.

Wannan mummunar tabi’a ta mushrikan makka da kin gaskiya da kafice ma, hakan na bakanta zuciyar manzon Allah, a kan haka Allah ke gaya masa da kada ya damu kansa saboda rashin imanin mushrikai, domin kuwa da Allah ya so da ya shiryar da su, amma saboda su ba a shirye suke su karbi shiriya ba, to Allah ba zai tilasta su yin abin da ba so ba, haka nan kuma ba aikin manzon Allah ne ya tilasta su ba.

Darussan koyo a nan su ne:

1 – Daya daga cikin abin da ke kara nisantar da mutum daga gaskiya shi ne kokarin yi ma karya kwaskwarima tare da kawata ta.

2 – Zuciyar manzon Allah tana kuna ne kan kafirai ba wai kawai domin sun ki yarda da shi ba, a a saboda tausayinsu da yake yi, domin kuwa ya san cewa abin da suke yi bata ne, kuma abin da yake kiransu zuwa gare shi shi ne gaskiya, kuma bin shi shi ne zai kai su ga samun rahamar Allah, kin bin shi kuma zai kai su ga azabar Allah, wadda babu wani mahaluki da zai iya jure mata.

Aya ta (138) cikin surat An’am

وَقَالُواْ هَـذِهِ أَنْعَامٌ وَحَرْثٌ حِجْرٌ لاَّ يَطْعَمُهَا إِلاَّ مَن نّشَاء بِزَعْمِهِمْ وَأَنْعَامٌ حُرِّمَتْ ظُهُورُهَا وَأَنْعَامٌ لاَّ يَذْكُرُونَ اسْمَ اللّهِ عَلَيْهَا افْتِرَاء عَلَيْهِ سَيَجْزِيهِم بِمَا كَانُواْ يَفْتَرُونَ{138}

Kuma sukace: "Wadannan dabbõbi da shũka haramun ne bãbu mai dandanar su fãce wanda muke so ga riyãwarsu. Da wasu dabbõbi an hana hawan bãyayyakinsu, da wasu dabbõbi bã su ambatar sũnan Allah a kansu bisa kirkiren karya gare shi. Zai sãka musu da abin da suka kasance sunã kirkirãwa.

Wannan aya tana yin bayani ne dangane da akidar surkulle ta mushrikan makka, inda suke ware wasu dabbobi su ce wadannan hakkin gumaka ne kawai, hatta Allah ba ya da hakki a cikinsu, ba su bari wani ya yi amfani da wadannan dabbobi, wato hawansu ko kuma dora musu kaya, haka nan kuma ba su bari a yi amfani da namansu ko madararsu, sai dai kawai ga wadanda suke yin hidima ga wadannan gumaka, kuma su kansu mushrikai sun yarda cewa haramun ne gare su su yi amfani da dabbobin da aka ware ga gumaka, sa'annan kuma a lokacin da suke yanka suna kiran sunan gunkin da aka bayar da dabbar ne a gare shi.

Wani abu mafi muni a cikin wannan akida ta surkulle ta mushrikan kuraishawa shi ne, suna yin hakan da sunan cewa Allah ne ya ba su umurnin su yi haka, kuma suna yin e domin umurnin Allah.

Darussan koyo a nan su ne: 1 – Akidar mushrikan makka ta ginu ne surkulle da camfe-camfe, wanda ya yi hannun riga da koyarwar annabawa.

2 – Kirkirar karya a danganta da Allah aiki ne na mutanen da ba su yi iamni da Allah ba.

Aya ta (139) da (140) a cikin surat An'am

وَقَالُواْ مَا فِي بُطُونِ هَـذِهِ الأَنْعَامِ خَالِصَةٌ لِّذُكُورِنَا وَمُحَرَّمٌ عَلَى أَزْوَاجِنَا وَإِن يَكُن مَّيْتَةً فَهُمْ فِيهِ شُرَكَاء سَيَجْزِيهِمْ وَصْفَهُمْ إِنَّهُ حِكِيمٌ عَلِيمٌ{139} قَدْ خَسِرَ الَّذِينَ قَتَلُواْ أَوْلاَدَهُمْ سَفَهاً بِغَيْرِ عِلْمٍ وَحَرَّمُواْ مَا رَزَقَهُمُ اللّهُ افْتِرَاء عَلَى اللّهِ قَدْ ضَلُّواْ وَمَا كَانُواْ مُهْتَدِينَ{140}

Kuma suka ce: "Abin da yake a cikin cikkunan wadannan dabbõbi kẽbantacce ne ga mazanmu, kuma hananne ne a kan mãtan aurenmu. Kuma idan ya kasance mũshe, to a cikinsa sũ abõkan tãrayya ne, zai sãka musu sifantãwarsu. Lalle ne shĩ, Mai hikima ne, Masani."

Lalle ne wadanda suka kashe diyansu sabõda wauta, ba da ilmi ba, sun yi hasãra! Kuma suka haramta abin da Allah Ya azurta su, bisa kirkira karya ga Allah. Lalle ne sun bace, kuma ba su kasance mãsu shiryuwa ba.

Daga cikin akidar mushrian makka har da cewa, dan tayi dake cikin mahaifar dabbar halas ne ga mazaje daga cikinsu, haramun ne ga matayensu, idan kuma dan tayin ya zo duniya matacce, to a lokacin za a raba ne tsakanin maza da mata kowa ya samu nasa rabon.

Aya ta biyu kuma tana yin ishara ne da wata akidar surkulle mai muni ta mushrikan makka wato kisan 'ya'yansu, saboda tsananin wawawanci da jahilci sun haramta ma kansu arzikin Allah, domin kuwa ni'imar da babbar ni'ima ce da Allah yake yi wa mutane a idan duniya.

Darussan koyo a nan su ne:

1 – Mushrikai suna nuna banbanci tsakanin maza da mata, tare da mayar da su tamkar ba mutane ba.

2 – Shigar da surkulle da camfe-camfe a cikin addini na tattare da babban hadari, domin hakan zai cakuda gaskiya da karya a matsayin abu guda cikin addini.

3 – Babbar hasara ita ce jahilci da rashin sanin manufa, ba rasa dukiya da tarkacen duniya ba.

Da wannan ne muka kawo karshen shirin namu na yau, sai idan Allah ya kai mu a shiri na gaba za a ji mu daga inda muka tsaya, kafin lokacin nake yi muku fatan alkhairi, wassalamu alaikum wa rahmatullah.

Suratul An'am, Aya Ta 141-144 (Kashi Na 219)

Jama'a masu saurare Assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannuka mai sanda, inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki, tare da yin bayani gwargawdon iko kan abin da suke koyar da mu, tare da yi mana hannuka mai sanda a cikin lamurran rayuwa. Har yanzu muna cikin surat An'am, sai a biyo mu sannu a hankali a cikin shirin.

Aya ta (141) a cikin surat An'am

وَهُوَ الَّذِي أَنشَأَ جَنَّاتٍ مَّعْرُوشَاتٍ وَغَيْرَ مَعْرُوشَاتٍ وَالنَّخْلَ وَالزَّرْعَ مُخْتَلِفاً أُكُلُهُ وَالزَّيْتُونَ وَالرُّمَّانَ مُتَشَابِهاً وَغَيْرَ مُتَشَابِهٍ كُلُواْ مِن ثَمَرِهِ إِذَا أَثْمَرَ وَآتُواْ حَقَّهُ يَوْمَ حَصَادِهِ وَلاَ تُسْرِفُواْ إِنَّهُ لاَ يُحِبُّ الْمُسْرِفِينَ{141}

Kuma Shĩ ne Wanda Ya kãga halittar gõnaki mãsu rumfuna da wasun mãsu rumfuna da dabĩnai da shũka, mai sãbãwa ga 'yã'yansa na ci, da zaituni da rummãni mai kama da jũna da wani mai kama da jũna. Ku ci daga 'ya'yan itãcensa, idan ya yi 'yã'yan, kuma ku bãyar da hakkinsa a rãnar girbinsa, kuma kada ku yi barna. Lalle ne shĩ, ba ya son mafarauta.

A cikin shirin da ya gabata ayoyin da suka zo kafin wannan sun yi bayani dangane da yadda mushrikan makka suke ware wasu daga cikin dabbobin da suke kiwatawa a shekara, da kuma abubuwan da suke nomawa domin gabatar da su ga gumaka, haka nan kuma suna ware wasu dabbobi su gabatar da su ga Allah. Wannan ayar tana yin bayani dangane da abin da suke warewa domin hakkin Allah wanda suke bayar da shi domin mabukata ko marayu ko matafiya, da cewa Allah yana da hakki hatta a cikin wasu daga cikin kayan da ake shukawa a gonaki ko a lambuna, duk da cewa hatta a cikin mushrikan akwai wadanda suke boye hakkin Allah, amma kuma akwai masu bayar da hadayarsu ga gumaka da kuma abin da suke gabatarwa ga Allah, inda sukan bayar da mafi yawan abin da suka samu a shekara, wanda hakan ko surkullen mushrikai wuce gona da iri ne, domin kuwa a cikin addinin musulunci ma an hana mutum ya wuce gona da iri cikin kowane lamari.

Aya ta 67 a cikin surat Furqan tana yin ishara, da cewa muminai na hakika idan sun ciyar da dukiyarsu, to ba su yin israfi kuma ba su tauye hannu, suna yin komai tsakatsaki.

Darussan da zamu koyo a nan su ne:

1 – Allah shi ne mai samar da dukkanin ababen da mutane suke amfani da su na abinci da sha, saboda haka boye hakkin Allah lamari mai matukar muni hatta a cikin akidar mushrikai.

2 – Musulunci yana umurni da kada a wuce gona da iri a cikin kowane irin lamari, hatta ciyarwa domin Allah kada mutum ya yi yadda zai kwari kansa da iyalansa, haka nan kuma kada ya tauye hannu saboda rowa.

Aya ta (142) surat An’am

وَمِنَ الأَنْعَامِ حَمُولَةً وَفَرْشاً كُلُواْ مِمَّا رَزَقَكُمُ اللّهُ وَلاَ تَتَّبِعُواْ خُطُوَاتِ الشَّيْطَانِ إِنَّهُ لَكُمْ عَدُوٌّ مُّبِينٌ{142}

Kuma daga dabbõbi (Ya kãga halittar) mai daukar kãya da kanãna; Ku ci daga abin da Allah ya azurta ku, kuma kada ku bi hanyoyin shaidan: LalLe ne shi, a gare ku, makiyi ne bayyananne.

Wannan ayar ma tana kara jaddada abin da aka fada a baya ne, cewa Allah shi ne ya halicce komai, da hakan ya hada da dabbobi da itatuwa, tsirrai, duwatsu da duk wani abin halitta, shi ne ya halicci dabbobi da mutane suke amfani da su domin daukar kayansu, kamar rakuma dawaki alfadarai jakuna da sauransu, haka nan kuma ya halicci dabbobi da mutane suke cin namansu kamar tumaki awaki da sauransu, da kuma yin amfani da fatunsu.

Saboda haka mutane suna amfana daga wadannan dabbobi ne da izinin Allah, gumaka ko wasu abubuwa na surkulle da camfae-camfe ba su da hakki a cikin wannan arziki na Allah, bin wadannan abubuwa yana kai mutane zuwa ga bin tafarkin shaidan, sun sani ko ba su sani ba.

Darussan koyo a nan su ne:

1 – Musulunci yana da ka’idoji da ya gindaya wajen cin naman dabbobi, akawai wadanda suka halasta akwai wadanda ba suhalasta ba, saboda haka abin da musulunci ya haramta shi ne haram, abin da kuma ya halasta shi ne halas.

2 – Haramta naman dabbobi da aka halasta, ko halasta naman dabbobin da aka haramta saboda surkulle, bin tafarkin shaidan ne.

Ayoyi na (143) da (144) surat An’am

ثَمَانِيَةَ أَزْوَاجٍ مِّنَ الضَّأْنِ اثْنَيْنِ وَمِنَ الْمَعْزِ اثْنَيْنِ قُلْ آلذَّكَرَيْنِ حَرَّمَ أَمِ الأُنثَيَيْنِ أَمَّا اشْتَمَلَتْ عَلَيْهِ أَرْحَامُ الأُنثَيَيْنِ نَبِّؤُونِي بِعِلْمٍ إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ{143} وَمِنَ الإِبْلِ اثْنَيْنِ وَمِنَ الْبَقَرِ اثْنَيْنِ قُلْ آلذَّكَرَيْنِ حَرَّمَ أَمِ الأُنثَيَيْنِ أَمَّا اشْتَمَلَتْ عَلَيْهِ أَرْحَامُ الأُنثَيَيْنِ أَمْ كُنتُمْ شُهَدَاء إِذْ وَصَّاكُمُ اللّهُ بِهَـذَا فَمَنْ أَظْلَمُ مِمَّنِ افْتَرَى عَلَى اللّهِ كَذِباً لِيُضِلَّ النَّاسَ بِغَيْرِ عِلْمٍ إِنَّ اللّهَ لاَ يَهْدِي الْقَوْمَ الظَّالِمِينَ{144}

Nau'õ'i takwas daga tumãkai biyu, kuma daga awãkai biyu; ka ce: Shin mazan biyu ne Ya haramta ko mãtan biyu, ko abin da mahaifar mãtan biyu suka tattara a kansa? Ku bã ni lãbãri da ilmi, idan kun kasance mãsu gaskiya.

Kuma daga rãkuma akwai nau'i biyu, kuma daga shãnu biyu; ka ce: Shin, mazan biyu ne Ya hana ko mãtan biyu Ya hana, kõ abin da mahaifar mãtan biyu suka tattara a kansa? Kõ kun kasance halarce ne a lõkacin da Allah Ya yi muku wasiyya da wannan? To, wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya kirkira karya ga Allah, dõmin ya batar da mutãne bã da wani ilmi ba? Lalle ne, Allah bã Ya shiryar da mutãne azzãlumai.

Mushrikai suna haramta wasu dabbobi kuma su halasta wasu daidai da abin da suke kudircewa na shirka, wani lokaci su haramta maza daga cikin jinsin dabbobi na tumaki ko awakai ko rakuma da shanu, wasu lokutan kuma su haramta mata daga cikin wannan dabbobi ko abin da ke cikin mahaifarsu, alhali kuwa Allah halasta ma mutane naman dukkanin wadannan na'uoi na dabbobi mazansu da matansu, tare da yin amfani da fatunsu.

Wannan ayar tana yin ishara da cewa abun da mushrikan makka suke yi ba su da wani dalili na ilimi a kansa, kamar yadda ba su da wata hujja daga Allah ko manzanninsa da suka gabata, illa dai kawai shaidan n eke raya musu abin da za su sai su bi shi kan hakan, kuma abu mafi muni shi ne suna ganin abin da suke yi addini ne.

Darussan koyo a nan su ne:

1 – Asalin dukkanin abin ci halas ne, sai dai wanda Allah ya haramta, kuma Allah shi ne mai halastawa ko haramtawa, duk da cewa kur'ani mai tsarki bai ambaci dukkanin abubuwa da Musulunci ya hamta bad a sunayensu daya bayan daya ba, amma a cikin hukunce-hukunce na shari'a an yi bayani filla-filla, bisa dogaro da nassi da shari'a take dogara da shi.

2 – Wajibi da ya rataya kan malaman addinin muslunci su bayyana ma mutane hakikanin koyarwar addini, kuma bayyana abin da yake surkulle ne, domin kada a hada addini da abin da ba ya a cikinsa duk ayi musu hukunci guda.

3 – Abin da mutum zai yi imani da shi har ya gina akidarsa a kansa, dole ne ya kasance a kan ilimi da masani, ba a kan jahilci da surkulle ba, domin kuwa da haka ne shaidan ya halakar da al'ummomin da suka gabata.

Da wannan ne muka kawo karshen shirin namu na yau, sai idan Allah ya kai mu a shiri na gaba za a ji mu daga inda muka tsaya, kafin lokacin nake yi muku fatan alkhairi, wassalamu alaikum wa rahmatullah.

Suratul An'am, Aya Ta 145-149 (Kashi Na 220)

Jama'a masu saurare Assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannuka mai sanda, inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki, tare da yin bayani gwargawdon iko kan abin da suke koyar da mu, tare da yi mana hannuka mai sanda a cikin lamurran rayuwa. Har yanzu muna cikin surat An'am, sai a biyo mu sannu a hankali a cikin shirin.

Aya ta (145) a cikin surat An'am

قُل لاَّ أَجِدُ فِي مَا أُوْحِيَ إِلَيَّ مُحَرَّماً عَلَى طَاعِمٍ يَطْعَمُهُ إِلاَّ أَن يَكُونَ مَيْتَةً أَوْ دَماً مَّسْفُوحاً أَوْ لَحْمَ خِنزِيرٍ فَإِنَّهُ رِجْسٌ أَوْ فِسْقاً أُهِلَّ لِغَيْرِ اللّهِ بِهِ فَمَنِ اضْطُرَّ غَيْرَ بَاغٍ وَلاَ عَادٍ فَإِنَّ رَبَّكَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ{145}

Ka ce: "Bã ni sãmu a cikin abin da aka yõ mani wahayi, abin haramtãwa a kan wani abin ci ga mai cinsa, fãce idan ya kasance mũshe kõ kuwa jini abin zubarwa kõ kuwa nãman alade, to lalle ne shi kazanta ne, kõ kuwa fãsikanci wanda aka kurũrũta shi dõmin wanin Allah." Sa'an nan wanda larũra ta kãmã shi, bã mai fita jama'a ba, kuma bã mai ta'addi ba, to Ubangijinka Mai gãfara ne, Mai jin kai.

A cikin shirin da ya gabata an ji wasu daga cikin abubuwa na surkulle da mushrikan makka suke yi, da kuma wasu abubuwa da suka kirkiro kuma suka danganta su da addinin Annabi Ibrahim (AS) bisa wannan gurbatacciyar akidar ta su auna halsta wasu abubuwa kuma suna haramta wasu.

Wannan aya mai albarka ta umurnin manzon Allah (SAW) ne da ya bayyana wasu daga cikin abubuwan da Allah ya haramta, domin a banbance tsakanin haram da halas na Allah da annabi, da kuma abin da mushrikai suka haramta ko halasta.

A fili yake cewa duk abin da Allah ya haramta, to lallai yana da wani abu na zahiri ko na badini, kamar cin naman matacciyar dabba haramun ne a musulunci, haka nan jini da naman alade, dukkanin wadannan abubuwa suna da babbar illa ga lafiyar mutum, saboda haka musulunci yana haslata abubuwa wadanda a asalinsu ba su dauke da abin da zai cutar da mutum. A cikin suratul baqara aya ta 57 tana cewa; ku ci daga kyawawan abubuwan da muka azurta ku da su.

Haka nan kuma a cikin addinin musulunci an haramta cin abin da aka yanka ba da sunan Allah ba, wanda hakan yana da illa ne ta badini da ke da tasiri kai tsaye ga ruhin mutum, saboda haka ba ya halasta a ci naman dabbar da aka yanka da sunan wani gunki, ko wata itaciya ko wani dodo ko aljani, ko kuma an yanka ba tare da ambatar wani suna ba.

Duk kuwa da cewa akwai wurare da shari’a ta yi rangwame kan cin abubuwan da aka haramta saboda shiga wani hali na larura, wanda kuma haramcin yana tabbata a lokacin da larurar ta kau. Darussan koyo a nan su ne:

1 – Daga cikin abubuwan da musulunci ya haramta, ba saboda cutar da suke dauke da ita ga jiki ba ne kawai, a a akwai abubuwan da musulunci ya haramta saboda cutar da ruhin mutum da suke yi, da kuma haifar da mummunan tasiri a cikin dabi’arsa ba tare da ya ankara ba, kamar misalin da aka bayar na cin naman alade.

2 – Saboda saukin da ke akwai a cikin addinin muslunci, duk da tsanantawa da aka yi kan abubuwa na haram, amma akwai halin larura kamar baraza a kan rayuwar mutum, ko kuma ya shiga wani hali da idan bai ci ko sha abin da aka haramta ba, to zai iya rasa rayuwarsa.

Aya ta (146) da (147) surat An’am:

وَعَلَى الَّذِينَ هَادُواْ حَرَّمْنَا كُلَّ ذِي ظُفُرٍ وَمِنَ الْبَقَرِ وَالْغَنَمِ حَرَّمْنَا عَلَيْهِمْ شُحُومَهُمَا إِلاَّ مَا حَمَلَتْ ظُهُورُهُمَا أَوِ الْحَوَايَا أَوْ مَا اخْتَلَطَ بِعَظْمٍ ذَلِكَ جَزَيْنَاهُم بِبَغْيِهِمْ وِإِنَّا لَصَادِقُونَ{146} فَإِن كَذَّبُوكَ فَقُل رَّبُّكُمْ ذُو رَحْمَةٍ وَاسِعَةٍ وَلاَ يُرَدُّ بَأْسُهُ عَنِ الْقَوْمِ الْمُجْرِمِينَ{147}

Kuma a kan Yahũdu Mun haramta dukan mai akaifa, kuma daga shãnu da bisãshe Mun haramta musu kitsattsansu, fãce abin da bãyansu ya dauka, kõ kuwa kãyan ciki, kõ kuwa abin da ya garwaya da kashĩ wannan ne Muka sãka musu sabõda zãluncinsu, kuma Mu, hakĩka, Mãsu gaskiya ne.

To, idan sun karyatã ka, sai ka ce: "Ubangijinku Ma'abũcin rahama ne Mai yalwa; kuma bã a mayar da azãbarsa daga mutãne mãsu laifi."

A cikin wannan ayar ana bayanin wasu daga cikin abubuwan da aka haramta ma yahudawa ne a cikin addininsu, da hakan ya hada da duk wata dabba mai akaifa, haka nan kuma kitsen shanu ko tukamaki da awaki, sai dai wanda ya hadu da kashi ko ‘yan ciki, wannan sakamako ne na abin da suka kasance suna aikatawa, tare da yin shishigi a kan dokokin Allah, da yin girman kai ga umurnin Allah.

A wasu wuraren an bayyana wasu daga cikin abubuwan da aka haramta musu da suka hada da har da dukkanin na’uoin tsuntsaye da naman rakumi, domin a ladabtar da su kan taurin kai da suke yi ma annabawan Allah. Amma a lokacin annabi Isa (AS) an halasta ma mabiya addininsa, saboda haka wannan aya ta ce ma ma’aiki (SAW) idan Mushrikai ko yahudawa sun karyata sakon da ya zo da shi, to ya gaya musu cewa Allah mai yawan rahama ne ga bayinsa, amma wannan rahma ba ta kawar da sakamakon aiki, amma dai Allah yana bayar da lokaci ga masu barna ko sun farga su dawo kan hanya madaidaiciya.

Darussan koyo a nan su ne:

1 – Wajibi ne mutane su kiyaye su nisanci sabon Allah, domin kuwa sabo ma ya kan hana samun wasu daga cikin ni’imomin Allah a duniya.

2 – Masu aikata munan ayyuka ana yi musu nasiha ne ta hanyar jawo hankali da nuna musu illar abin da suke aikata ga rayuwarsu ta duniya, da kuma babban aibin da hakan yake da shi ga rayuwarsu ta lahira.

Aya ta ( 148) da (149) surat An’am

سَيَقُولُ الَّذِينَ أَشْرَكُواْ لَوْ شَاء اللّهُ مَا أَشْرَكْنَا وَلاَ آبَاؤُنَا وَلاَ حَرَّمْنَا مِن شَيْءٍ كَذَلِكَ كَذَّبَ الَّذِينَ مِن قَبْلِهِم حَتَّى ذَاقُواْ بَأْسَنَا قُلْ هَلْ عِندَكُم مِّنْ عِلْمٍ فَتُخْرِجُوهُ لَنَا إِن تَتَّبِعُونَ إِلاَّ الظَّنَّ وَإِنْ أَنتُمْ إَلاَّ تَخْرُصُونَ{148} قُلْ فَلِلّهِ الْحُجَّةُ الْبَالِغَةُ فَلَوْ شَاء لَهَدَاكُمْ أَجْمَعِينَ{149}

Wadanda suka yi shirki zã su ce: "Dã Allah Yã so dã ba mu yi shirka ba, kuma dã uwayensu maza ba su yi ba, kuma dã ba mu haramta wani abu ba." Kamar wannan ne mutãnen da suke a gabãninsu suka karyata, har suka dandani azãbarmu. Ka ce: "Shin, kunã da wani ilmi a wurinku dõmin ku fito mana da shi? Bã ku bin kõme fãce zato kuma ba ku zama ba fãce masu kirkirar abin da suke fada."

Ka ce: "To Allah ne da hujja isasshiya, sabõda haka: Dã Yã so, dã Yã shiryar da ku gabã daya."

Wadannan ayoyi suna yin bayani ne dangane da yadda mushrikai suke kokarin kare kansu dangane da abubuwan da suke yi na surkulle da bautar gumaka, inda suke cewa idan abin da suke yi ba daidai ba ne ai da Allah bar ba su sun yi shirka ba, da ba su haramta wani abu ba, amma tun da ya bar su a kan hakan, to ya yarda da abin da suke yi kenan, sai Allah ke gaya ma manzonsa (SAW) cewa ai dama haka wadanda suka yi shirka a gabaninsu suka fada, alhali abin da suke fada bai ginu a kan wani ilimi daga Allah ba, kawai suna yin hasashe ne sai kuma su abin da suka yi hasashen a kansa. Allah shi ne ke da hujja a kan talikai, da ya so da ya shiryar da kowa, amma komai nasa yana da tsari, domin kuwa Allah yana shiryar da mai son shiriya ne, wanda kuma ba a shirye yake ya karbi shiriya ba, to Allah ya kan bar shi da abin da ya zaba ma rayuwarsa.

Darussan koyo a nan su ne:

1 – Allah yana son mutane su yi imani su samu kamala da kuma rahamarsa, amma kuma bisa zabinsu ba bisa tilasci ba.

2 – Abin da ya fi aikata sabo muni shi ne wanke kai tare da bayar da hanzari na aikata sabon, abin da ya fi wannan muni kuma shi ne danganta sabon da Allah, wato tamkar umurnin Allah ne ake aikatawa ta hanyar yin sabo.

Da wannan ne muka kawo karshen shirin namu na wannan lokaci, sai idan Allah ya kai mu a shiri na gaba za mu ci gaba daga inda muka tsaya, amma kafin wannan lokacin, a madadin wadanda suka hada mana sautin shirin, nake yi muku fatan alkhairi, sai saduwa ta gaba, wassalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh.

Suratul An'am, Aya Ta 150-152 (Kashi Na 221)

Jama'a masu saurare Assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannuka mai sanda, inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki, tare da yin bayani gwargawdon iko kan abin da suke koyar da mu, tare da yi mana hannuka mai sanda a cikin lamurran rayuwa. Har yanzu muna cikin surat An'am, sai a biyo mu sannu a hankali a cikin shirin.

Aya ta (150) a cikin surat An'am

قُلْ هَلُمَّ شُهَدَاءكُمُ الَّذِينَ يَشْهَدُونَ أَنَّ اللّهَ حَرَّمَ هَـذَا فَإِن شَهِدُواْ فَلاَ تَشْهَدْ مَعَهُمْ وَلاَ تَتَّبِعْ أَهْوَاء الَّذِينَ كَذَّبُواْ بِآيَاتِنَا وَالَّذِينَ لاَ يُؤْمِنُونَ بِالآخِرَةِ وَهُم بِرَبِّهِمْ يَعْدِلُونَ{150}

Ka ce: "Ku kãwo shaidunku, wadanda suke bãyar da shaidar cẽwa Allah ne ya haramta wannan." To idan sun kãwo shaida kada ka yi shaida tãre da su. Kuma kada ka bi son zũciyõyin wadanda suka karyata game da ãyõyinmu, da wadanda bã su yin ĩmãni da Lãhira, alhãli kuwa sũ daga Ubangijinsu suna karkacẽwa.

A cikin shirin da ya gabata an ji cewa mushrikan makka sun haramta kansu wasu abubuwa, haka nan kuma sun halasta kansu wasu abubuwan na daban, kuma duk suna danganta haramci da kuma halacin ga Allah madaukakin sarki, an umurci manzon Allah da ya kalubalanci wannan surkulle na mushrikan makka, ta hanyar neman su kawo dalili kan abin da suke rayawa, duk kuwa da cewa ba su da dalili daga Allah, amma wasunsu za su iya yin gaban kansu wajen kirkirar dalilai na karya su danganta da Allah, saboda haka wannan aya take sheda ma ma’aiki ko hakan ta kasance, to kada ya biye musu, domin kuwa su ba a shirye suke su karbi gaskiya ba, duk ya kawo musu sai sun kalubalance da wani abu na daban.

Darussan da za mu koya a nan su ne:

1 – Addinin musulunci addini ne na hujja da kuma dogaro da ka’idoji na hankali, saboda haka bai daidai da duk warta akida ta surkulle ba.

2 – Baya halasta mutum ya bi wani tunani ko akida da bai ginu a kan akida ta kadaita Allah ba, ko yin shakku dangane da sakon Allah da manzonsa ya zo da shi, domin kuwa duk akidar da ba ta ginu kan imani da Allah da manzonsa ba, to hakika wannan karkatattar akida ce.

Aya ta (151) surat An’am

قُلْ تَعَالَوْاْ أَتْلُ مَا حَرَّمَ رَبُّكُمْ عَلَيْكُمْ أَلاَّ تُشْرِكُواْ بِهِ شَيْئاً وَبِالْوَالِدَيْنِ إِحْسَاناً وَلاَ تَقْتُلُواْ أَوْلاَدَكُم مِّنْ إمْلاَقٍ نَّحْنُ نَرْزُقُكُمْ وَإِيَّاهُمْ وَلاَ تَقْرَبُواْ الْفَوَاحِشَ مَا ظَهَرَ مِنْهَا وَمَا بَطَنَ وَلاَ تَقْتُلُواْ النَّفْسَ الَّتِي حَرَّمَ اللّهُ إِلاَّ بِالْحَقِّ ذَلِكُمْ وَصَّاكُمْ بِهِ لَعَلَّكُمْ تَعْقِلُونَ{151}

Ka ce: "Ku zo in karanta abin da Ubangijinku Ya haramta." wãjibi ne a kanku kada ku hada kõme da shi, kuma ga mahaifa biyu (ku kyautata) kyautatãwa, kuma kada ku kashe diyanku sabõda talauci, Mũ ne Muke azurta ku, kũ da su, kuma kada ku kusanci abũbuwa na alfãsha, abin da ya bayyana daga gare ta da abin da ya bõyu, kada ku kashe rai wanda Allah Ya haramta fãce da hakki. Wannan ne (Allah) Ya yi muku wasiyya da Shi: Tsammãninku, kunã hankalta.

Wannan aya mai albarka tana yin ishara da abin da yake haram a cikin dukkanin addinan Allah da suka gabata, hakan bai takaitu kawai da addinin muslunci ba, babban abin da yake haram na farko a cikin dukaknin addinai da suka zo daga Allah shi ne shirka, wanda kuma mushrikan makka suna cikin wannan babban aiki na haram, kuma suna zaton cewa da hakan ne ma za su bi Allah yadda yake so, ta hanyar bauta ma gumaka da sunan suna bauta masa.

Ba’ada bayan haka kuma suna aikata wani babban sabo mai muni wanda shi ma ayar tana bayyana shi a cikin ayyuka na haram, wato kashe ‘ya’yansu da suke yi saboda tsoron talauci, alhali Allah madaukakin sarki shi ne mai azurta su da ‘ya’yan nasu baki daya. Haka nan kuma suna kirkirar yake-yake domin neman duniya da mulki, inda suke kashe mutane ba gaira ba sabar domin kawai su mamaye musu yankuna, su kwashe arzikinsu, kuma su zubar da jininsu ba hakki ba. Su cutar da mata da tsoffi da kananan yara, wanda hakan aiki na haram a cikin koyarwar dukkanin addinai da suka gabaci musulunci.

Haka nan kuma saba ma iyaye da cutar da su da bakanta musu aiki na haram, dole ne mutum ya kyautata ma mahaifansa, sai dai in sun umurce shi da ya saba Allah ne, to a lokacin ba zai yi biyayya gare su ba. Sa’annan kuma wani babban aiki na haram shi ne, aikata alfasha a zahiri ko a badini, saboda haka ne ma ya zamanto kusantar aikata ayyukan alfasha haram ne, alhali kuwa mushrikan makka ba su tsentseni wajen aikata duk wani aiki na alfasha, bil hasali ma hakan ya zama tamkar wani bangare na al’adarsu.

Duka wadannan abubuwa Allah yana bayyana su ne ga mushrikai da sauran mutane baki daya domin su hankalta, su san abin da yake daidai a wurin Allah da kuma abin da yake sabo ne haram ne.

Darussan koyo a nan su ne:

1 – Shirka da Allah ita ce tushen duk wata barna, shi ya sanya a ko da yaushe shirka ta kanzo a mataki na farko a cikin manyan laifuka na sabon Allah.

2 – Kashe ‘ya’ya saboda tsoron talauci babban sabon Allah ne, kuma yin hakan aiki ne na mushrikai.

3 – Wasu zunubban sabon tsananin hadarin da suke tattare da shi, aka haramta kusantar su, balantana aikata su.

Aya ta (152) surat An’am

وَلاَ تَقْرَبُواْ مَالَ الْيَتِيمِ إِلاَّ بِالَّتِي هِيَ أَحْسَنُ حَتَّى يَبْلُغَ أَشُدَّهُ وَأَوْفُواْ الْكَيْلَ وَالْمِيزَانَ بِالْقِسْطِ لاَ نُكَلِّفُ نَفْساً إِلاَّ وُسْعَهَا وَإِذَا قُلْتُمْ فَاعْدِلُواْ وَلَوْ كَانَ ذَا قُرْبَى وَبِعَهْدِ اللّهِ أَوْفُواْ ذَلِكُمْ وَصَّاكُم بِهِ لَعَلَّكُمْ تَذَكَّرُونَ{152}

Kada ku kusanci dũkiyar marãya fãce da wadda take ita ce mafi kyau, har ya kai ga karfinsa. Kuma ku cika mũdu da sikẽli da ãdalci, bã mu kallafã wa rai fãce iyãwarsa. Kuma idan kun fadi magana, to ku yi ãdalci, kuma ko dã yã kasance ma'abũcin zumunta ne. Kuma ku cika alkawarin Allah. wannan ne ya yi muku wasiyya da shi: Tsammãninku, kunã tunãwa.

A ci gaba da bayanin abubuwan da suke haram wadanda Allah ya hana, kuma suke da tasiri a cikin rayuwar mutane ta zamantakewa, wannan aya mai albarka ita ma tana yin ishara da wasu daga cikinsu, daga ciki har da cin dukiyar marayu, haramun ne a ci dukiyar marayu bisa zalunci ta hanayar da shari’a ta halasta, dole ne kare dukiyar marayu yadda ya kamata har sai sun isa matsayin da za su iya tafiyar da ita sai a damka musu ita kamar yadda Allah ya yi umurni.

Haka nan a cikin mu’amala ta yau da kullum, wajibi ne a kiyaye hakkokin mutane, da hakan ya hada sayen ababen aunawa kan sikeli, tauye ma’uni a cikin mu’ama haram ne, dole a kiyae adlci da gaskiya a cikin harkar kasuwanci da sauran lamurra na zamantakewa, haka nan kuma fadin gaskiya da yin adalci a cikin zantuttuka, wannan ita ce koyarwar addinin musulunci.

Darussan da za mu koya a nan su ne:

1 – Allah madaukakin sarki bai taba kasawa ba wajen kyautata ma bayinsa, saboda haka a hankalce ya kamata su bayinsa su kyautata ta hanyar yin abin da ya umurce su, da kuma hanuwa da abin da ya hane su.

2 – Tsarin tattalin arzikin al’umma dole ne ya kasance bisa asasi na adalci da kuma kiyaye hakkokin mutane, maimakon ya kasance bisa asasi na jari hujja da maslahar kashin kai kawai, ta yadda masu dukiya za su yi ta zama su ne suke danne sauran mutane, su tasiri a cikin dukkanin harkoki har da na siyasar al’umma.

3 – A koda yaushe taklifin ayyuka a cikin addini muslunci daidai yake da abin da mutane za su iya, Allah ba ya dora ma mutane abin da ba za su iya ba.

4 – Kiyaye adalci da gaskiya a cikin magana, na daga cikin muhimman abubuwan da musulunci ya karfafa a kansu.

Da wannan ne muka kawo karshen shirin namu na wannan lokaci, sai idan Allah ya kai mu a shiri na gaba za mu ci gaba daga inda muka tsaya, amma kafin wannan lokacin, a madadin wadanda suka hada mana sautin shirin, nake yi muku fatan alkhairi, sai saduwa ta gaba, wassalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh.

Suratul An'am, Aya Ta 153-157 (Kashi Na 222)

Jama'a masu saurare Assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannuka mai sanda, inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki, tare da yin bayani gwargawdon iko kan abin da suke koyar da mu, tare da yi mana hannuka mai sanda a cikin lamurran rayuwa. Har yanzu muna cikin surat An'am, sai a biyo mu sannu a hankali a cikin shirin.

Aya ta (153) a cikin surat An'am

وَأَنَّ هَـذَا صِرَاطِي مُسْتَقِيماً فَاتَّبِعُوهُ وَلاَ تَتَّبِعُواْ السُّبُلَ فَتَفَرَّقَ بِكُمْ عَن سَبِيلِهِ ذَلِكُمْ وَصَّاكُم بِهِ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ{153}

Kuma lalle wannan ne tafarkĩna madaidaici: Sai ku bĩ shi, kuma kada ku bi wasu hanyõyi, su rarraba ku daga barin hanyãta. Wannan ne Allah ya yi muku wasiyya da shi tsammãninku, kunã yin takawa.

A cikin bayanin ayoyin da suka gabata a baya, ayoyin sun yi mana bayani dangane da wasu daga cikin irin al’adu na mushrikai da kuma akidojinsu, wadanda suka doru kan asasi na surkulle da hasashe, inda suke haramta kansu wasu abubuwa kuma su halasta wasu, kuma suke danganta hakan da Allah, duk kuwa da cewa ba su dogara da wata hujja daga Allah kan abin da suke yi ba.

Wannan ayar mai albarka tana yin ishara da cewa mutane suna da hanyoyi daban-daban da suke bi a matsayin hanya ta rayuwa ko addini ko wata akida, amma abin da manzon Allah ya zo da shi wanda yake kore duk wata akida ta hda bautar Allah da wani abu, tare da kadaita Allah a cikin imani da bauta, wannan shi ne sahihin tafarki mikakke wanda Allah ya ayarda bayinsa su bi.

Mushrikai da suke bauta ma gumaka da suka sassaka da hannusu, suna bin abin da rayukansu suka raya musu ne, domin kuwa manzon Allah (SAW) ya kure su a lokacin da ya bukaci su kawo wata hujja daga Allah da take tabbatar da abin da suke yi shi ne Allah ya yarda da shi, su kawo hujja daga Allah da take tabbatar da cewa abubuwa n da suke haramtawa Allah ne ya haramta su, ko kumaabubuwan da suke halasta ma kansu Allah ya halasta su, kuma suka gagara kawo hujja daga addinan da suka gabata da ke tabbatar da gaskiyarsu kan abin da suke rayawa.

Wasu daga cikin mushrikai da suke bin ruhbaniyawan da ke magana a maimakon gumaka sun dawo sun bi gaskiya bayan suka ga hujjojin manzon Allah sun rinjayi nasu, wasu kuma sun ci gaba da yin taurin kai tare da bijire wa manzon Allah da yi masa izgili, har ma da cutar da shi tsawon shekaru goma sha uku da ya kwashe yana yin kira a garin Makka.

Darussan da za mu iya dauka a nan su ne:

1 – Babban abin da yake hada dukaknin al’ummomi a wuri guda shi ne addini da akida, domin kuwa tushen addinin Allah guda daya ne, yayin da sauaran addinai da ba na Allah ba tushensu hasashe ne kawai na mutum, tare da shifta irin ta shaidan.

2 – A ko da yaushe kur’ani yana fadakar da mutane na kowane zamani, ba sai lokacin ma’aiki ba, umurnin Allah da ke cikinsa wanzajje ne har zuwa tashin kimaya, haka nan haninsa, domin kuwa kur’ani ba a yi masa kwaskwarima, ba ma ba a yi masa kwaskwarima ba ne kawai, a a baya ma karbar kwaskwarimar ne.

Aya ta (154) a cikin surat An'am

ثُمَّ آتَيْنَا مُوسَى الْكِتَابَ تَمَاماً عَلَى الَّذِيَ أَحْسَنَ وَتَفْصِيلاً لِّكُلِّ شَيْءٍ وَهُدًى وَرَحْمَةً لَّعَلَّهُم بِلِقَاء رَبِّهِمْ يُؤْمِنُونَ{154}

Sa'an nan kuma mun bai wa Mũsã Littãfi, cikakke bisa ga wanda ya kyautata, da rarrabẽwa daki-daki ga kõwane abu, da shiriya da rahama, tsammãninsu, sunã yin ĩmãni da haduwa da ubangijinsu.

Sabanin abin da wasu suke yin tunani kan cewa akwai sabani a tsakanin addinai na ubangiji, alhali dukkanin addinai da suka zo daga sama, suna yin kira ne zuwa ga abu guda, wato kadaita Allah a cikin bauta da kuma aiwatar da umurninsa da hanuwa da haninsa, dukkanin annabawa da littafansu suna gasgata annabawa da suka gabace su da kuma littafan da suka zo da su daga Allah, abin da ke cikin littafin Attaura wanda aka baiwa annabi Musa yana gasgata littafan da suka gabace, kamar yadda Ingila da kur'ani suka gasgata attaura da sauran littafan annabawan da suka gabaci annabi Musa (AS)

Darussan koyo a nan su ne:

1 – Dukkanin littafan da Allah ya safkar suna shiryar da mutum ne zuwa tafarkin kamala.

2 – Wadanda suka yi imani kuma suka yi ayyuka na gari suke amfana da sakonnin annabawan Allah, wadanda suka yi musu kuma suna haramta kansu samun wannan babbar falala.

Aya ta (155) da (156) surat An'am

وَهَـذَا كِتَابٌ أَنزَلْنَاهُ مُبَارَكٌ فَاتَّبِعُوهُ وَاتَّقُواْ لَعَلَّكُمْ تُرْحَمُونَ{155} أَن تَقُولُواْ إِنَّمَا أُنزِلَ الْكِتَابُ عَلَى طَآئِفَتَيْنِ مِن قَبْلِنَا وَإِن كُنَّا عَن دِرَاسَتِهِمْ لَغَافِلِينَ{156}

Kuma wannan littãfi ne, Mun saukar da shi mai albarka, sai ku bĩ shi kuma ku yi takawa, tsammãninku, anã jin kanku.

(Dõmin) kada ku ce: "Abin sani kawai, an saukar da littãfi a kan kungiya biyu daga gabãninmu, kuma lalle ne mũ, mun kasance marafkana daga karatunsu."

Wannan aya mai albarka tana yin bayani ne dangane da littafin da aka safkar wa manzon Allah wato kur'ani, da cewa shi littafi mai albarka da ya zo daga Allah, mutane su bi abin da ke cikinsa, idan suka yi haka sun yi aiki da umurnin Allah, kuma za su samu kaiwa ga matsayi na tsoron Allah.

Allah ya safkar da wannan littafi domin katse duk wata hujja da al'ummomin karshen zamani za su iya gabatarwa, ba sai kafiran makka ba kawai, ta yadda ba za su iya cewa an safkar da littafai ga annabawan da suka gabata ba, amma su ba su da littafin da za su bi domin sanin shiriya, domin kuwa kur'ani mai tsarki shi ne cikar shiriya baki daya.

Darussan koyo a nan su ne:

1 – Kur'ani mai tsarki ba littafi ne karatu ba ne kawai, a a littafi ne na aiki a cikin dukkanin rayuwar mutum, yin aiki da shi shi ne hakikanin imani da sako da ke cikinsa.

2 – Sa'adar duniya tat a lahira tana cikin lamurra biyu ne, bin gaskiya da kuma nisata daga bata.

Aya ta (157) surat An'am

أَوْ تَقُولُواْ لَوْ أَنَّا أُنزِلَ عَلَيْنَا الْكِتَابُ لَكُنَّا أَهْدَى مِنْهُمْ فَقَدْ جَاءكُم بَيِّنَةٌ مِّن رَّبِّكُمْ وَهُدًى وَرَحْمَةٌ فَمَنْ أَظْلَمُ مِمَّن كَذَّبَ بِآيَاتِ اللّهِ وَصَدَفَ عَنْهَا سَنَجْزِي الَّذِينَ يَصْدِفُونَ عَنْ آيَاتِنَا سُوءَ الْعَذَابِ بِمَا كَانُواْ يَصْدِفُونَ{157}

Kõ kuwa ku ce: "Dã dai an saukar da Littãfi a kanmu, hakĩka dã mun kasance mafiya shiryuwa daga gare su." To, lalle ne wata hujja bayyananniya daga ubangijinku tã zo muku da shiriya da rahama. To, wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya karyata game da ãyõyin Allah, kuma ya bijire daga barinsu? Zã mu sãka wa wadanda suke bijirewa daga barin ãyõyinmu da mummunar azãba, sabõda abin da suka kasance sunã yi na bijirewa.

Wannan ayar ma tana kara yin bayani dangane da yadda kur'ani mai tsarki ya yanke duk wani hanzari ga masu bautar gumaka, ko wasu abubuwa na daban, ko bin son ransu wajen yin watsi da ayoyin Allah, bayan safkar kur'ani babu sauran wata hujja ga mutane kan cewa ba safkar da littafin da ke bayyana umurnin Allah da hanninsa ba, balanta su samu hujjar saba ma Allah ta hanyar shirka da sauran hanyoyi na barna.

Babban zalunci ne mutum ya karyata ayoyin Allah, duk kuwa da falalar ubangiji maras lisaftuwa a kansa, hakika mutanen da suka juya baya daga bin sakon Allah, za su hadu da sakamakon abin da suka aikata.

Darussan koyo a nan su ne:

1 – Masu raya imani suna yawa, amma ana tantance hakan ne kawai ta hanayar aiki da kuma tsayuwa kyam a lokacin fuskantar jarabawa.

2 – Babban zalunci shi ne mutum ya karyata ayoyin Allah, tare da yin hawan kawara kan dokokinsa madaukakin sarki.

Da wannan ne muka kawo karshen shirin namu na wannan lokaci, sai idan Allah ya kai mu a shiri na gaba za mu ci gaba daga inda muka tsaya, amma kafin wannan lokacin, a madadin wadanda suka hada mana sautin shirin, nake yi muku fatan alkhairi, sai saduwa ta gaba, wassalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh.

Suratul An'am, Aya Ta 158-161 (Kashi Na 223)

Jama'a masu saurare Assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannuka mai sanda, inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki, tare da yin bayani gwargawdon iko kan abin da suke koyar da mu, tare da yi mana hannuka mai sanda a cikin lamurran rayuwa. Har yanzu muna cikin surat An'am, sai a biyo mu sannu a hankali a cikin shirin.

Aya ta (158) a cikin surat An'am

هَلْ يَنظُرُونَ إِلاَّ أَن تَأْتِيهُمُ الْمَلآئِكَةُ أَوْ يَأْتِيَ رَبُّكَ أَوْ يَأْتِيَ بَعْضُ آيَاتِ رَبِّكَ يَوْمَ يَأْتِي بَعْضُ آيَاتِ رَبِّكَ لاَ يَنفَعُ نَفْساً إِيمَانُهَا لَمْ تَكُنْ آمَنَتْ مِن قَبْلُ أَوْ كَسَبَتْ فِي إِيمَانِهَا خَيْراً قُلِ انتَظِرُواْ إِنَّا مُنتَظِرُونَ{158}

Shin, sunã jiran (wani abu), fãce dai malã'iku su zo musu kõ kuwa Ubangijinka Ya zo, kõ kuwa sãshen ãyõyin Ubangijinka. A rãnar da sãshen ãyõyin Ubangijinka ke zuwa, ĩmãnin rai wanda bai kasance yã yi ĩmãnin ba da farko kõ kuwa ya yi tsiwirwirin wani alhẽri ba, bã ya amfãninsa. Ka ce: "Ku yi jira: Lalle ne mũ, mãsu jira ne."

Ayoyin da suka gabata, sun tabbatar mana karara cewa, kur’ani mai tsarki shi ne babbar mu’ujizar manzon Allah (SAW) kuma shi ne littafin dokoki a cikin addinin musulunci, amma mushrikai da kafirai suna yin musun ayoyin Allah, suna kalubalantar manzon Allah da ya tabbatar musu da wata mu’ujizar ta daban, bayan da kur’ani ya kure su, kuma ya gagare su, domin kuwa sun kasa kawo koda aya daya wadda ta yi kama da ayar kur’ani balantana su kawo sura wadda ta yi kama da da surorinsa, suna son su ga m,ala’iku da idanunsu suna safka suna gasgata manzon Allah, ko kuma Allah madaukakin sarki da kansa ya zo su gan shi da idanunsu kuru-kuru, kuma ya tabbatar musu da cewa shine ya aiko manzon Allah (SAW) ko kuma a safkar musu da tsawa mai tsanani daga sama, da dai sauran maganganu da ke tabbatar da musunsu ga ayoyin Allah.

Manzon Allah (SAW) ya ba su amsa da umurnin Allah cewa; a matsayinsu na marassa imani idan aka safkar musu da abin da suke nema to za su halaka, domin kuwa sun mu’ujizozi da suke gasgata sakon Allah amma saboda girman kai da kin gaskiya, suka yi watsi da duk wadannan mu’ujizozi, domin aduuk lokacin da suka wata mu’ujiza sau su ce wannan saddabaru kawai irin na muhammadu, duk kuwa da cewa su ne suka fi kowa sanin gaskiyarsa da amanarsa.

1 – Wadanda suka kafirce ayoyin Allah bayan sun zo musu, ba a shirye suke su amince da duk wata mu’ujiza daga annabawan Allah ba.

2 – Imani da Allah da manzonsa yana tafiya ne tare da aiki na gari, imanin da ba a gwama shi da aiki na gari ba, to ba shi da wata kima.

Aya ta (159) surat An’am

إِنَّ الَّذِينَ فَرَّقُواْ دِينَهُمْ وَكَانُواْ شِيَعاً لَّسْتَ مِنْهُمْ فِي شَيْءٍ إِنَّمَا أَمْرُهُمْ إِلَى اللّهِ ثُمَّ يُنَبِّئُهُم بِمَا كَانُواْ يَفْعَلُونَ{159}

Lalle ne wadanda suka rarraba addininsu, kuma suka kasance kungiyã-kungiyã, kai ba ka zama daga gare su ba a cikin kõme: abin sani kawai al'amarinsu zuwa ga Allah yake. Sa'an nan ya bã su lãbãri game da abin da suka kasance sunã aikatãwa.

Ba wai kawai kafirai da mushrikai za su ne za su gurfana a gaban kotun Allah a ranar kiyama domin bayar da bayani kan shirka da kafircin da suka yi ba, a a hatta ma muminai da suka yi imani da Allah, amma kuma suka kirkiro wasu abubuwa da ba bu su a cikin addini suka mayar da su addini, ko jingina karya ga manzon Allah domin kaiwa ga manufofinsu na duniya, suka rarraba kan musulmi, suka yi ta shirya makida domin ganin cewa ba a bi addinin kamar yadda manzo ya zo da shi ba, to a ranar kiyama za su dauki alhakin hisabi kan hakan, kuma Allah ne da hisabinsu, shi ne ya san yadda zai yi da su.

Daya daga cikin abubuwan da kur’ani ya zargi wasu daga cikin mabiya addinan da aka aka aiko annabawan da suka da su shi ne, canja lafazi da ma’anar littafan annabawansu, amma kur’ani mai tsarki lafazinsa yana nan kamar yadda Allah ya safkar da shi, amma wajen tafsirin ayoyinsa da bayaninsa, wasu za su iya juya ma’anarsa daidai da yadda suke so, ko yadda su suka fahimci addini, wata kila bisa dogaro da ruwayoyi marassa tushe, ko kuma dalilai na siyasa.

Darussan koyo a nan su ne:

1 – Wajibi ne a yi imani da dukkanin hukunce-hukunce na addini, yin imani da wani bangare na hukunce-hukuncen Allah tare da yin watsi da wani bagarensu ya yi hannun riga da koyarwar manzon allah.

2 – Rarraba tsakanin musulmi ba ya nufin cewa akwai canje-canje a cikin kur’ani, hakan yana da dangantaka ne kawai da ra’ayoyin daidaikun muusulmin, amma musulunci addini daya kamar yadda kur’ani littafi ne daya, da kuma manzo daya wanda kuma yin koyi da sahihiyar koyarwarsa shi ne bin su.

Aya ta (160) surat An’am

مَن جَاء بِالْحَسَنَةِ فَلَهُ عَشْرُ أَمْثَالِهَا وَمَن جَاء بِالسَّيِّئَةِ فَلاَ يُجْزَى إِلاَّ مِثْلَهَا وَهُمْ لاَ يُظْلَمُونَ{160}

Wanda ya zo da kyakkyãwan aiki guda, to yanã da gõma makamancinsa. Kuma wanda ya zo da mũgun aiki gũda, to, bã zã a sãka masa ba fãce da misãlinsa. Kuma sũ bã a zãluntar su.

Bin dokokin da Allah ya kafa na sakamako mai kyau a ranar kiyama, kamar yadda hakan yake barin tasiri mai kyau ga rayuwar mutane da daidaiku da ta zamantakewa, haka nan kuma saba dokokin Allah yana sakamako na azaba, hakan nan kuma yakan bar mummunan tasiri a cikin rayuwar mutane ta daidaiku da kuma ta zamantakewa

Wani abu da ke banbanta dokokin Allah da kuma wadanda mutum ya kafa shi ne, idan aka bi dokar Allah akwai sakamako mai kyau, idan kuma aka saba akwai akasin hakan, yayin da dokokin mutane suke kafawa idan aka saba musu ne ake haduwa da sakamako maras, amma idan aka bi su tare da kiyaye su babu wani sakamako da za a baiwa mutum.

A nan za mu iya daukar darussa kamar haka:

1 – Musulunci yana karfafa gwiwar mutane da su yi aiki na gari, domin kuwa sakamakon kyakyawan aiki ana rubanya shi har sau goma, sabanin aikin sabo, wanda ake sakama mutum da sakamako daya na wannan aikin kawai.

2 – Abin da ke raka mutum zuwa lahira alokacin da ya bar gidan duniya aikinsa ne kawai, na alkhairi ko na sharri.

Aya ta (161) suurat An’am

قُلْ إِنَّنِي هَدَانِي رَبِّي إِلَى صِرَاطٍ مُّسْتَقِيمٍ دِيناً قِيَماً مِّلَّةَ إِبْرَاهِيمَ حَنِيفاً وَمَا كَانَ مِنَ الْمُشْرِكِينَ{161}

Ka ce: "Lalle nĩ, Ubangijina Yã shiryar da ni zuwa ga tafarki madaidaici, addĩni mai kima, akĩdar Ibrãhĩm mai karkata zuwa ga gaskiya, kuma bai kasance daga mãsu shirka ba."

Mushrikan makka sun akiran kansu a matsayin mabiya addinin Ibrahim, Allah madaukakin sarki a cikin wannan aya mai albarka yana umurta manzonsa (SAW) da ya sheda ma mushrikai cewa; shi ne a kan tafarkin shiriya, tafarkin annabi Ibrahim (AS) kuma annabi Ibrahim bai taba kasancewa cikin masu hada bautar Allah da wani ba.

Annabi Ibrahim (AS) ya kasance yana yin kira zuwa ga bautar Allah shi kadai, da fadakar da mutane a cikin hikima domin su nisanci bautar gumaka da ma bautar duk wani ba Allah ba, a cikin wasu ayoyin na kur’ani an yi ishara da yadda ya sare gumakan da mutanesa suke bautama wa, da hikimar da ya yi amfani da ita wajen nuna musu cewa wadannan gumaka ba za su iya amfanar da kansu da komai ba, balntana waninsu.

Darussan koyo a nan su ne:

1 – A kowane lokaci manzannin Allah su ne abin koyi ga al’ummomi, domin kuwa su suna samun shiriya ne kai tsaye daga Allah.

2 – Tushen addinai da aka safkar daga sama guda daya ne, shi ne kadaita Allah, kuma addinin musulunci ci gaba ne na addinin annabi Ibrahim (AS)

Da wannan ne muka kawo karshen shirin namu na wannan lokaci, sai idan Allah ya kai mu a shiri na gaba za mu ci gaba daga inda muka tsaya, amma kafin wannan lokacin, a madadin wadanda suka hada mana sautin shirin, nake yi muku fatan alkhairi, sai saduwa ta gaba, wassalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh.

Suratul An'am, Aya Ta 162-165 (Kashi Na 224)

Jama'a masu saurare Assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannuka mai sanda, inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki, tare da yin bayani gwargawdon iko kan abin da suke koyar da mu, tare da yi mana hannuka mai sanda a cikin lamurran rayuwa. Har yanzu muna cikin surat An'am, sai a biyo mu sannu a hankali a cikin shirin.

Aya ta (162) da (163) a cikin surat An'am

قُلْ إِنَّ صَلاَتِي وَنُسُكِي وَمَحْيَايَ وَمَمَاتِي لِلّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ{162} لاَ شَرِيكَ لَهُ وَبِذَلِكَ أُمِرْتُ وَأَنَاْ أَوَّلُ الْمُسْلِمِينَ{163}

Ka ce: "Lalle ne sallãta, da baikõna, da rãyuwãta, da mutuwãta, na Allah ne Ubangijin tãlikai."

"Bãbu abõkin tãrayya a gare Shi. Kuma da wancan aka umurce ni, kuma ni ne farkon mãsu sallamãwa."

A cikin ayoyin da suka gabaci wannan, an yi ishara da cewa mushrikan makka suna tsammanin cewa suna bin tafarkin annabi Ibrahim (AS) alhali annabi Ibrahim ya kasance a kan sahihin tafarki ne na sallamawa ga Allah. Wannan ayar tana yin nuni da cewa, tsarkae rai da mika wuya ga Allah mikawa su ne matakan farko na hawa sahihiyar turba ta addinin Allah, ayar tana umurnin manzon Allah da ya sheda ma mutane cewa rayuwarsa da mutuwarsa da dukkanin ayyukan ibadarsa, da sallarsa duka yana yinsu ne domin Allah kuma a tafarkin Allah.

Manzon Allah shi ne aka dora ma nauyin yin kira zuwa tafarkin kadaita Allah, idan ya kasance mai kiran wasu zuwa ga wannan tafarki, to shi ne farkon wanda ya fara mika wuya ga dukkanin umurnin Allah wajen bin tafarkin bautarsa shi kadai.

Wannan sunna ce ta Allah, dukkanin annabawan da suka gabacin manzon karshe Muhammad dan Abdullahi (SAW) su ne suka fara mika wuya ga Allah kafin al’ummominsu, kuma Allah ya san tsarkinsu kuma ya san cewa za su iya daukar nauyin isar da sakonsa, shi ya sanya ya zabe domin wannan muhimmin aiki.

Darussan koyo a nan su ne:

1 – Mutum ba alokacin da yake cikin salla ko wani aikin ibada ne yake matsayin bawan Allah ba, a dukkanin rayuwar mutum bawan Allah ne.

2 – Rayuwa ko mutuwa ba su ne suke da muhimmanci ba, abin da ke da muhimmanci shi ne su kasance a tafarkin Allah.

Aya ta (164) surat An’am

قُلْ أَغَيْرَ اللّهِ أَبْغِي رَبّاً وَهُوَ رَبُّ كُلِّ شَيْءٍ وَلاَ تَكْسِبُ كُلُّ نَفْسٍ إِلاَّ عَلَيْهَا وَلاَ تَزِرُ وَازِرَةٌ وِزْرَ أُخْرَى ثُمَّ إِلَى رَبِّكُم مَّرْجِعُكُمْ فَيُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمْ فِيهِ تَخْتَلِفُونَ{164}

Ka ce: "Shin wanin Allah nake nema ya zama Ubangiji, alhãli kuwa shi ne Ubangijin dukkan kome? Kuma wani rai ba ya yin tsirfa face domin kansa, kuma mai daukar nauyi, bã ya daukar nauyin wani, sa'an nan kuma komawarku zuwa ga Ubangijinku take; Sa'an nan ya ba ku labari ga abin da kuka kasance a cikinsa, kuna sabawa juna."

Manzon Allah (SAW) yana tambayar mushrikan makka cewa; shin yanzu sai bar Allah ubangijina in bi gumankanku, alhali shi ne ubangijin dukkanin komai? Shin akwai wani abu da gumanka za su iya yi ne wanda zai gagari Allah? Me ya sanya kuke kira na zuwa ga gumakanku da ba su iya amfanar da kansu balanta su iya amfar da ku?

Manzon Allah (SAW) ya sheda ma mushrikai gaba-da gaba cewa; dukkanin abin da suke aikatawa na shirka da Allah, to kansu ne suke yi wi hasara, domin kuwa kowane rai abin da ya tsuwuwuri a gidan duniya shi ne zai iske, wani rai ba zai dauki laifi wani rai ba, kuma makomar kowa ga Allah ubangijin dukkanin talikai take, kuma zai fayyace wa mutane wane ne ya kasance kan gaskiya a gidan duniya, wane ne kuma ya kasance kan bata.

Darussan koyo a nan su ne:

1 – Kafirci ko imani, kyautatawa ko munanawa wajen aiki, dukkan wadannan abubuwa ba su amfanar da Allah da komai kuma cutar da shi da komai, amfani ko cutarwar hakan na komawa ne zuwa ga shi mutum kansa.

2 – A ranar kiyama Allah shi ne babban alkali mai hukunci na karshe a tsakanin bayinsa, kan abin da suka kasance suna aikatawa a rayuwarsu ta duniya.

Aya ta (165) surat An’am

وَهُوَ الَّذِي جَعَلَكُمْ خَلاَئِفَ الأَرْضِ وَرَفَعَ بَعْضَكُمْ فَوْقَ بَعْضٍ دَرَجَاتٍ لِّيَبْلُوَكُمْ فِي مَا آتَاكُمْ إِنَّ رَبَّكَ سَرِيعُ الْعِقَابِ وَإِنَّهُ لَغَفُورٌ رَّحِيمٌ{165}

"Kuma Shi ne wanda ya sanya ku masu maye wa juna a bayan kasa. Kuma ya daukaka sashenku bisa ga sashe da darajoji; domin ya jarraba ku a cikin abin da ya ba ku." Lalle ne, Ubangijinka mai gaggãwar ukkũba ne, kuma lalle ne shi mai gãfara ne, mai jin kai.

Wannan aya ta karshe a cikin surat An’am, tana yin ishara ne da rayuwar mutum a bayan kasa, da kuma yadda yake yin amfani da dukkanin ni’imomin Allah da ya hore masa a cikin wannan rayuwa, kuma Allah ya sanya rayuwar duniya ta zama jarabawa ga mutum, domin kuwa kafin wannan al’umma ta karshe, an yi al’ummomi da yawa da suka gabata, kuma Allah ya sanya wannan al’umma ta karshe zamani ta zama mai maye gurbin sauran al’ummomi, kuma kamar yadda wadancan al’ummomin suka rayu suka tafi, haka ita wannan al’umma ta karshen zamani za ta yi rayuwarta ta koma ga Allah.

A cikin rayuwar duniya Allah ya daukaka wasu a kan wasu, kuma hakan duk matakai ne na jarabawar ubangiji ga talikai,domin ya ga abin da za su aikta. Saboda haka mutane masu hankali su ne wadanda suke yin amfani da damar da suke da ita ta rayuwar duniya wajen aikata alkhairi, domin su samu yardar Allah, kuma su samu kubuta daga fushinsa da azabarsa ranar da za su hadu da shi. Darussan koyo a nan su ne:

1 – Bambancin ta fuskacin tsakanin mutane ta fuskacin mallakar dukiya ko matsayi a duniya ba shi ne ma'auni wajen gane matsayin mutum a wajen Allah ba, domin kuwa mallakar dukiya da samun matsayi na duniya da kuma talauci, dukkkaninsu hanyoyi ne da Allah ya sanya domin ya jarraba mutane da su. Shi mai dukiya idan ya yi amfani da ita kamar yadda Allah ya umurce shi to ya ci wannan jarabawa, haka nan kuma maras galihu idan ya yi hakuri tare da kiyaye dokokin Allah a duk yanayin day a samu knsa a ciki, to a lokacin ya ci jarabawar ubangiji. Haka nan mai iko ko wani matsayi a cikin al'umma, idan ya yi amfani da matsayinsa domin tsaida adalci da gaskiya da kiyaye dokokin Allah da hakkokin jama'a da suke karkashinsa, to a lokacin ya ci jarabawar ubangiji.

2 – Allah madaukakin sarki sarki mai gaggawar hisabi ne ga wadanda suka ci jarabawarsa da ma wadanda suka fadi, a lokaci guda kuma shi mai tausayi ne da rahama ga bayinsa.

3 – Duk abin da muka mallaka da mu kanmu duka mallakin Allah ne, idan muka fahimci haka, to a lokacin za mu ciyarwa a tafarkin Allah cikin sauki, za mu iya taimaka ma marassa galihu ba tare da jin abin da muka mallaka ya ragu ba.

Da wannan ne muka kawo karshen wannan sura ta An'am, kuma muka kawo karshe shirin namu na wannan lokaci, sai idan Allah ya kai mu a shiri na gaba za mu ci gaba daga farkon surat A'araf, amma kafin wannan lokacin, a madadin wadanda suka hada mana sautin shirin, nake yi muku fatan alkhairi, sai saduwa ta gaba, wassalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh.

Contents