- LANGUAGE: Hausa
- TOPIC: Economics/Politics
- SKILL: Listening
- LEVEL: ILR Level 2+/3 - ACTFL Superior
- CONTENT SOURCE: Interviewer (Jummai Ali) and analyst Professor Abba (2005 September 9). U.N. Security Council.Washington, D.C.: Voice of America, Hausa Service.
- Objective: Demonstrate your core comprehension.
- Content description: This interview addresses Nigeria's controversial bid for a seat on the United Nations Security Council, from an analyst's point of view.
- Lesson Title: U.N. Security Council-This interview addresses Nigeria's controversial bid for a seat on the United Nations Security Council, from an analyst's point of view.
- Language: Hausa
- Topic: Economics/Politics
- ILR Level: 2+/3
- ACTFL Proficiency: Superior, Advanced-High
- This ACTFL rating is an approximation based on the ILR level
- Modality: Listening
- Learning Objective: Maintenance & Improvement
- Subject Area: Language
- Material Type: LO
- Publication Year: 2007
- ObjectID: HAUS_11719
Transcript
Original | Translation |
---|---|
U.N. Security Council A: Ai… a gaskiya ba na ganin ah… zai ɗan samu dai … nasara a waɗansu ƙudurorin da ya … ya bayyana. Amma … ah … magana da shi ya kawo na … yanda za a … za a daɗa ƙarfafa shi kwamitin sulhu … ah … da kuma a daɗa ba wa … ah … kwamitin da yake kula da hakkin bil’Adam. Ah … ƙarfi fiye da yanda yake da shi da ... ah ... ga yanda ni na ga waɗansu watau ... ah … wakilan shugaba a ƙasashe. Ah … yanda suke magana akai gaskiya kamar abun ba zai yiwu ba. Ah … ina ganin … ah … daga abin da tsokacin wakilin kamar {Egypt [English]} … ah … ya nuna cewa su gaskiya ba sa tunanin a daɗa ƙarfafa wannan … ah … kwamitin … na … hakkin ɗan Adam … ah … a ba shi ƙarfi, zai yi wahala. -- B: A saboda ha- -- A: -- To, maganarku -- ... na'am? B: -- ai, a saboda haka kake ganin zai samu cikas a wannan fannin? A: Eee, ina ganin. Lalle, zai samu cikas. Kuma … ah … maganar wai a ƙara ƙarfafa kwamitin sulhu, shi ma daga … tadda wannan ƙudurin ƙasashe da yawa, kowane sun fara … watau … faɗa albarkacin bakinsu. Ah … kuma kama yanda ni nake gani, da wuya a ce za a samu wani kyakkyawan … yarjejeniya akan … watau … yaya za a ƙara su waye za su shiga, saboda kowa yana … ah … yana so shi ma ya zama, yana daga cikin wannan ... kwamitin sulhu ɗin. B: Eee, to wannan batun na ... batun kwamitin sulhu da ka yi, ka san Nijeriya ita ma, tana neman a ba ta wakilci. A: Ee, ƙwarai da gaskiya, na -- B: -- Kuma -- A: -- Nijeriya -- B: -- mmm, ai -- A: -- da {South Africa [English]} -- B: -- ai, to, kuma, ka san -- A: -- ah … da {Egypt [English]} … ai -- B: -- to, kuma, ka san cewa … tun ba yau ba … kotu ta musamman da Majalisar ta kafa domin … shari’a laifuffukan yaƙi ta bukace a miƙa … tsohon shugaban Liberiya Charles Taylor, wanda yanzu haka yana can Nijeriya inda aka ba shi mafakar siyasa. A: To … B: To, yaya kake ganin batun dangantakan neman wakilcin Nijeriya ɗin a kwamitin sulhu, da kuma batun miƙa shi tsohon shugaban Liberiya, ɗin? A: Eee, to … ah … a gaskiya, ni ina ganin abun da Nijeriya ta yi, in kar- … in kika duba … ah … an yi ne don … ah … a kashe wutar … watau … rigingimu da ake a Liberiya. Kuma, ina ganin Nijeriya ta … ta nuna shugabanci da ta yadda da Charles Taylor ya shigo. Ah … kuma, ta ba da … ah … ta turfa, ta ce ba za ta ba da Charles Taylor zuwa wannan … kwa- … kwamitin … ah … majan- -- B: Kotun -- A: -- Kotun, Kotun … ah … Duniya. Bai kamata a matsa wa Nijeriya, a ce wannan abun da ta yi, saboda dama, in za a yi … ah … za a kwantar da … tashin hankali, yawanci akan yi waɗansu alƙawarori don kowa dai ya zamanto kome ya zauna lafiya. B: Ba ka ganin -- A: Bai … B: -- ba ka ganin ko ƙila … tun da Majalisar Ɗinkin Duniya ne ta bukaci Nijeriya ɗin ta yi miƙa Charles Taylor a mishi shari’a, ba ka ganin ko ƙila a yi ma Nijeriya ɗin ci da ceto? A: Eee, za a iya yi, amma ni ina ganin … ah … kamar tun da Nijeriya … ta … tana son ta shiga wannan kwamitin sulhu, ko sabida tana ganin ƙasashen Afrika, za su goya mata baya. Kuma ni ina ganin ƙasashen Afrika nan za su fahimci matsayin Nijeriya akan wannan matsalar … ah … ita Liberiya. Ah ... duk da cewa sauran ƙasashe za su ga kamar … ah … Nijeriya ta yi wa wannan kotu … ah … kunan uwa shegu a game da abin da take so ta yi. Ah … ina gani za a iya samun a dai sauran ƙasashen Afrika wanda sune in suka ce, ai mun yadda Nijeriya, ta zama wakiliyarmu daga … ah … sashen Afrika. Ah … ina ganin sauran ƙasashe ma kuma za su biyo baya. Ah {so [English]} … kin fa gaskiya ne cewa zai iya zama matsala, amma ni ina ganin … ah … da wuya ya zama cikas. |
U.N. Security Council A: Well … I really don’t see ah … that he would get any … success in those decisions that he … he put forth. But … ah … what he said about … giving more weight to the Security Council … ah … and giving more to … ah … the Human Rights Commission. Ah … more power than it already has, and … ah … here’s how I see these, you know … ah … representatives, a leader for the countries. Ah … as they have said repeatedly, it really would not be possible. Ah … I think … ah … from looking at a representative like Egypt … ah … he points out that they really didn’t think much about increasing the power of this … ah … Commission … for … Human Rights … ah … if it’s given power, it would have trouble. -- B: Because of -- A: -- OK, what you’re saying -- … Yes? B: -- Well, because of this, do you think that it would create problems in the organization? A: Yes, I think so. Indeed, it would cause problems. And … ah … the discussion about further strengthening the Security Council, and by … overtaking the decision of several countries, everyone began to … that is … put their own perspective on the matter. Ah … as I see it, it’s difficult to say whether we would get a really good … agreement on … that is … how to increase them and who would join, because everyone … ah … wants to become a member within the … Security Council. B: Yes, so this matter of … the Security Council that you refer to, you know that Nigeria herself is seeking membership on the council. A: Yes, exactly, I -- B: -- And -- A: -- Nigeria -- B: -- mmm, so -- A: -- as well as South Africa -- B: -- and also you know -- A: -- ah … and Egypt … so -- B: -- so you also know that … for some time now … the U.N. high court, established a special court to … try … former Liberian president Charles Taylor, who is now there in Nigeria, where he’s been granted political asylum. A: OK … B: So, how do you see the relationship between Nigeria’s request for representation on the Security Council and the issue of handing over the former Liberian president? A: Yes, well … ah … really, I think what Nigeria did, if you … if you really look at it … ah … it was done … ah to bring about the resolution of the crisis … in Liberia. And I think that Nigeria showed leadership by allowing Charles Taylor to seek refuge. Ah … it also gave him … ah … a cover, and said it would not hand over Charles Taylor to that … comm- … committee … ah … of the Coun- -- B: Court -- A: -- Court … ah … World Court. It’s not necessary to put pressure on Nigeria, or to say that this was done out of opportunity, when it was done … ah … to relieve … tensions, most of them made promises to everyone that everything would turn out peacefully. B: Don’t you think -- A: It didn’t … B: -- don’t you think that perhaps … since the U.N. has ordered Nigeria to hand over Charles Taylor to face the law, don’t you think that perhaps Nigeria is helping to get him off his punishment? A: Yes, that could be done, but I think … ah … that since Nigeria … wants to join the Security Council, and because it understands the countries of Africa, they will support her. And I think that these African countries will understand Nigeria’s position on this matter of … ah … Liberia. Ah … which is to say, the other countries will see that … ah … Nigeria has … ah … turned a deaf ear to the court regarding what she wants to do. Ah … I think it’s possible that there are other African countries that will say, yes we agree that Nigeria should become our representative from … ah … the African group. Ah … I think other countries would follow behind them. Ah, so … you’re correct that it may become an issue, but I think … ah … it would be difficult to go wrong. |
Glossary
Hausa | Hausa Meaning | English Meaning |
---|---|---|
A kashe wuta. | A tsaida rikici ko faɗa. A sassanta mutane lokacin da suna cikin wata rigima. | This is an expression meaning to stop a dispute. |
Ta turfa ta ce... | Ta tsaya kan maganarta. A nan mai maganar yana nufin Nijeriya ta nanata ƙudirinta na mafakar da ta ba Charles Taylor. | She stood by her words. In this case, the speaker means that Nigeria is firm on its decision about the asylum given to Charles Taylor. |
Ci da ceto. | A yi jan rai, ko a kawo hujjoji domin kada a ba mutum abin da ya ke nema. | To delay giving something to somebody in order to take revenge, or to take advantage of a situation in order to retaliate. |
Yin kunan uwa shegu. | Wannan karin magana ne da ke nufin: yin kamar ba a ji abin da ake faɗi ba domin ba a so a son maganar. | This is a proverb in Hausa which means to not pay attention to what is being said. |
A kwantar da tashin hankali. | A tsaida rigima, ko faɗa. A sasanta masu faɗa. | This expression means to calm down the parties in a fight or conflict. |
Hakkin bil’Adam. | Wannan na nufin haƙin dan Adam ko haƙin mutane. | This describes human rights and it is written in two ways in Hausa, as explained in the target language definition. |
XML
<activity>
<problemset>
<problem correctindex="1">
<choices>
<opt>
<eng-response>In this interview, Professor Abba, an analyst, comments on the United Nations Security Council, its motions for reform, and Africa’s membership in the Council, with Nigeria as a front runner. Looking at the reaction of some countries, he expresses doubt about a possible consensus on the motions presented. Regarding Nigeria’s candidacy for a seat on the Security Council, he thinks the chances are good, despite the asylum granted by Nigeria to former Liberian President Charles Taylor, which he sees as a responsible and peaceful move on the part of the country. He expects that Nigeria’s refusal to hand Taylor over to the Court will be an obstacle for the Security Council, but feels that other African countries will understand Nigeria’s position and support its representation of the continent.</eng-response>
<response>Wani shehun malami kuma manazarci, Abba, yana bayyani cikin wannan tattaunawar, bisa ƙudurorin ƙarfafa Kwamitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya, da kuma takarar Nijeriya a matsayin waƙiliyar Afrika cikin kwamitin. Yana nuna shakka bisa jituwar ƙasashen wajen maganar ƙarfafawar domin wasu ƙasashen sun nuna rashin goyon bayansu. Yana kwatamta yarda shi ga niyya Nijeriya ko da shike ƙasar ta kawo wa kanta matsala da kotu ta Majalisar Ɗinkin Duniya saboda mafakar siyasa da ta ba tsohon Shugaban ƙasar Liberiya, Charles Taylor, kuma da shi Abba yake gani kamar abin kirki ne don ƙarfafa salama.Yana ganin Majalisar za ta kawo matsala ga Nijeriya saboda harakar Taylor. Yana kuma ganin wasu ƙasahen Afrika sun fahimci matsayinta kuma su goya mata baya domin ta waƙilce su gaban kwamitin.</response>
<eng-fdbk>Incorrect. This is not the best option. The summary does not indicate Nigeria's interest in representing Africa in the Council, as mentioned in the interview, in spite of its importance in the organization. What comment shows that interest?</eng-fdbk>
<fdbk>Ba daidai ba ne.Wannan zaɓe ba mafi kyau ba ne. Taƙaitarwar ba ta nuna sha'awar Nijeriya ba ga wakilcin Afirka a kwamitin duk da yake da muhimmanci ga hirar. Wace magana take nuna sha'awar Nigeria?</fdbk>
</opt>
<opt>
<eng-response>This interview gives an analyst’s point of view on the situation at the United Nations. This includes information about the plan to expand the Security Council and reinforce human rights, and the possibility of Nigeria winning the seat to represent Africa in the Council. Although he describes Nigeria’s offer of political asylum to Charles Taylor, former President of Liberia, as a noble attempt to settle the Liberian conflict, he does not rule out a reprisal from the United Nations for Nigeria’s refusal to hand over the President to the International Court. Professor Abba, the analyst, assumes that some African countries will potentially understand Nigeria’s position, as well as the country’s interest in the seat, and support the nomination despite the Taylor issue. He also expresses skepticism about the expansion of the Council because some countries are not in favor of it.</eng-response>
<response>Wannan tattaunawar tana bada ra'ayin wani manazarci bisa ga halin da ake ciki na ƙara ƙarfin Kwamitin Sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya da na Haƙƙin Dan Adam, da kuma irin ƙaddara da ke ga Nijeriya ta cin nassara ga samun wakilcin Afirka cikin kwamitin. A ganin shi Nijeriya ta yi tattalin salama ga rikicin Liberiya lokacin da ta ba tsohon shugaban ƙasar Taylor mafaka amma, bai hidda tsamanin Majalisar Ɗinkin Duniya ta kawo gardama ga takarar ba domin rashin bada Taylor ga kotu duniya. Abba ya ɗauka cewa wasu mahimman ƙasahen Afirka za su gane matsayin Nijeriya, da abin da take so, kuma su kama mata ta ci nasara duk da harakar Taylor. Ya kuma nuna kushe ga daɗa ƙarfin Kwamitin Sulhu saboda wasu ƙasashe ba su amince da wannan ba.</response>
<eng-fdbk>Correct. This is the best choice as it accurately reflects the content of the interview, as well as the speaker's view on how issues regarding countries are being treated at the Security Council.</eng-fdbk>
<fdbk>Daidai ne. Wannan amsa ta fi domin tana bada mahimman ra'ayoyin da tattaunawar ta ƙunsa, da kuma tunanin mai maganar bisa al'amuran da suke faruwa a Kwamitin Sulhu da ƙasashe duniya.</fdbk>
</opt>
<opt>
<eng-response>In this interview, Professor Abba, an analyst, speaks about the reform plan at the United Nations Security Council, and Nigeria as a potential, albeit problematic, candidate for membership on the Council. Abba mentions the obstacle that some countries present to the realization of the reform. He favors Nigeria as a candidate, suggesting that the world should look at Nigeria’s handling of former Liberian President Charles Taylor’s case as an example of a peaceful solution to a conflict. Nigeria may have a problem with the United Nations for protecting Taylor, but that should not be a hindrance. The rest of the African countries will back Nigeria to get the African seat on the Security Council, he adds, since the country has shown its interest and hope for the seat.</eng-response>
<response>Wani manazarci, Abba, yana magana bisa shirin jaddada da ake yi na Kwamitin Sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya, da kuma bisa girma da matsalar takarar Nijeriya ta wakilci a kwamitin, cikin wannan tattaunawar. Abba ya ce wasu ƙasashe suna kawo cikas ga jaddadar. Yana aminci da takarar Nijeriya, inda yake nuna wajibi ne ga duniya, ta ga yadda Nijeriya ta ɗauki harakar tsohon Shugaban Liberiya akan aikin sulhu ne ta yi bisa rikicin ƙasar. Ya ce
kuma ko da shike Nijeriya tana da laifin kare Taylor ga idon Majalisar Ɗinkin Duniya, wannan ba zai iya zama cikas ba; yana gani sauran ƙasashen Afirka sun goyi bayan ta domin ta nuna tana so kuma tana fatan ta wakilci Afirka ga Kwamitin Sulhun.</response>
<fdbk>Ba daidai ba. Wannan taƙaitarwa ba ta bada issashen bayyani bisa kan maganar tattaunawar wanda ya shafi musamman Kwamitin Sulhun. Ku ƙara saurara farkon hirar. Minene mai maganar ya faɗa bisan gyara a kwamitin?</fdbk>
<eng-fdbk>Incorrect. This choice is wrong because it does not fully reflect the topic of the interview, which specifically concerns the Security Council. Please listen to the beginning of the interview. What statements by the interviewee relate to reform at the Council?</eng-fdbk>
</opt>
</choices>
</problem>
</problemset>
<instr type="eng">INSTRUCTIONS:
Choose the best summary.</instr>
<instr type="target">Umurni:Zaɓi taƙaitawa mafi dacewa.</instr>
<finishtl>A ganinku, waɗɗane irin hujjoji Nijeriya take iya kawowa domin ta samu matsayin wakilci a Kwamiti Sulhu?</finishtl>
<finish>What arguments do you think Nigeria can make in favor of its getting the seat on the Security Council?</finish>
<finishtl>Yaya kuke gani Majalisar Ɗinkin Duniya za ta ɗauki takarar Nijeriya bayan ta ba Charles Taylor mafakar siyasa?</finishtl>
<finish>How do you think the United Nations views Nigeria' s candidacy after Charles Taylor's political asylum?</finish>
<finishtl>Waɗɗane hujjoji kuke gani zasu ba Afirka 'yancin zama mamba na Kwamitin Sulhun?</finishtl>
<finish>What reasons support making Africa eligible for a seat on the Security Council?</finish>
</activity>