Overview
- Lesson Title: The Whirlwind of Politics in 2007
- This editorial discusses the 2007 Nigerian elections and the reactions of the people, as well as national and international bodies.
- Language: Hausa
- Topic: Economics/Politics
- ILR Level: 2+/3
- ACTFL Proficiency: Superior, Advanced-High
- This ACTFL rating is an approximation based on the ILR level
- Modality: Reading
- Learning Objective: Maintenance & Improvement
- Subject Area: Language
- Material Type: LO
- Publication Year: 2007
- ObjectID: HAUS_12119
Transcript
Original | Translation |
---|---|
The Whirlwind of Politics in 2007 Kaxawar guguwar siyasa a 2007 NOTE: ”Q” represents the Hausa hooked ”K” “X” represents the Hausa hooked “D” “V” represents the Hausa hooked “B”
A wannan juyi ne ake tsammanin a Najeriya farar hula zai gudanar da zave ya rantsar da farar hula ya miqa masa mulki. Shi ne irinsa na farko a tarihin siyasar Najeriya. Lokacin da Janar Abdussalami Abubakar ya miqa wa Obasanjo mulki a 1999, jam’iyyu sha xaya ne suka shiga zave. Uku ne suka yi tasiri su ne APP da PDP da AD. Da shekarar zave ta 2003 ta zo, jam’iyyu 20 ne suka shiga zave, amma huxu ne suka taka muhimmiyar rawa ANPP da PDP da AD da APGA. A bana kuwa jam’iyyu 50 ne, waxanda suka yi tasiri su ne PDP, da ANPP da PPA da AC, waxanda suka xan leqo kuma su ne DPP da APGA. Waxannan alamu ne da ke nuna cewa ayyukan jam’iyyun da ‘yan Najeriya suke buqata daga uku ne zuwa shida. Abubuwan al’ajabi a siyasar 2007 sun faru da yawa kuma a kowane vangare na qasar nan. Zavukan da aka yi a ranakun 14 da 21 ga Afrilu, na jihohi da na tarayya, ba a tava samun mummunar sukar yadda aka gudanar da zave ba daga ‘yan cikin gida har waje kamar wannan. An yi kashe-kashe, an saci akwatu, an qi kawo kayan aiki, sannan an yi aringizon quri’u. A wannan zave jam’iyyar PDP ita ce ta xauki kujerar shugaban qasa, xan takararta Umaru Musa ‘Yar Aduwa da mataimakinsa Goodluck Jonathan sune aka bayyana. ‘Yar Aduwa Gwamnan Katsina ne, Musulmi daga Arewa maso Yamma. Jonathan, Gwamnan Jihar Bayelsa ne Kirista daga yankin Kudu maso Kudu. A wannan zave PDP tana da gwamnoni 28, su ne Adamawa da Anambra da Bayelsa da Cross River da Delta da Enugu da Filato da Gombe da Jigawa da Nassarawa da Rivers da Sokoto da Taraba da Kaduna da Katsina da Kebbi da Kwara da Kogi da Ondo da Osun da Ekiti da Ebonyi da Oyo da Niger da Akwa Ibom da Benue da kuma Edo. A wannan zaven jam’iyyun adawa sun sami gwamnoni guda takwas ANPP tana da guda biyar su ne, Kano da Zamfara da Borno da Yobe da Bauchi. PPA tana da jihohi biyu su ne Abiya da Imo, ita kuma AC tana da jiha xaya ita ce Lagos. A jihohi 28 ne aka samu sabbin gwamnoni, a wannan zave. Jihohin Kano kuwa da Kwara da Kogi da Ondo da Ogun da Osun da Borno da Gombe, kome gwamnoninsu suka yi bayan sun samu amincewar jama’arsu. A cikin waxanda suka riqe muqamin mataimakin gwamna tun daga 1999 duk faxin Nijeriya Mahmudu Aliyu Shinkafi shi ne mataimakin da gwamnansa ya ba shi dama ya maye gurbinsa a Jihar Zamfara. A wannan zaven na 2007, ‘yan majalisar dattijai guda goma sha bakwai ne suka shiga takarar gwamna. Guda tara daga jam’iyyar ANPP su ne, Sanata Paul Ohioho Ukepo (Cross River), Sanata Farfesa Daniel Saror (Benue), Sanata Faruk Bello Bunza (Kebbi), Sanata Abu Ibrahim (Katsina), Sanata Muhammad Kirikasamma (Jigawa), Sanata Tokunbo Afikuyomi (Lagos), Sanata Abiola Ajimobi (Oyo), Sanata A.A. Ibrahim (Taraba), da kuma Sanata Mamman Ali (Yobe). A cikinsu guda xaya ne na jihar Yobe ya kai labari. Sanatoci huxu ne PDP ta tsayar, biyu sun ci, biyu sun faxi waxanda suka yi nasara su ne Sanata Farfesa Oserheimen Osunbor (Edo) da Sanata Liyel Imoke (Cross river). Waxanda ba su kai labari ba su ne Sanata Ifeanyi Ararume (Imo) da Sanata Musliu Obanikoro (Lagos). Jam’iyyar DPP ta tsaida sanatoci guda biyu, Sanata Abdullahi Bala Adamu (Taraba) da Sanata Lawali Shu’aibu (Zamfara) babu wanda ya ci. APGA da jam’iyyar Labour Party sun tsaida xai-xai. Su ne Sanata Daniel Gbenga Aluko LP (Ekiti) da Sanata John Wash Pam APGA (Plateau). A wannan zaven, gwamnoni tara ne masu barin gado suka nemi kujerar sanata. Dukkansu sun ci in banda qwaya xaya. Waxanda suka neman su ne; Ahmad Maqarfi PDP (Kaduna), Ahmed Sani Yarima ANPP (Zamfara) da Ahmed Mu’azu (Bauchi) bai ci ba. Adamu Aleiro PDP (Kebbi) da Bukar Abba Ibrahim ANPP (Yobe) da Saminu Turaki PDP (Jigawa ) da George Akume PDP (Benue) da Chimaroke Nnamani PDP (Enugu). Sai tsohon gwamna Kabiru Gaya ANPP (Kano). A wannan zaven waxanda suka sha kashi na ban mamaki su ne Janar Muhammad Buhari na ANPP da Atiku Abubakar na AC a takarar shugabancin qasar nan sai Sanata Ibrahim Mantu da Sanata Arthur Nzeribe da Sanata Jonathan Zwingina. AC ce ta kada Mantu, PPA ta kada Nzeribe. Da Abdul Ningi da Faruq Lawan daga majalisar wakilai sun sha kaye mummuna a hannnun ANPP ta Kano da Bauchi. Sanatoci uku da suka fito daga jihar Oyo, Kamoruddeen Adedibu xan cikin Alhaji Lamidi Adedibu ne, Ubangidan siyasar Ibadan, shi kuma Teslim Kolawole sanata na Oyo ta Tsakiya shi ne PA xin Adedibu, Gbenga Babalola sanatan Oyo ta Arewa shi kuma surukin Adedibu ne duk kuma sun fito daga PDP. Wacce ta ci sanata a Ogun ta tsakiya Iyabo Obasango-Bello ‘yar cikin shugaba Obasanjo ce. Shi kuwa Bukar Abba ya ci sanata, matarasa ta ci ‘yar majalisar tarayya. Matar Uffot Ekaete, shugaban ma’aikata na gwamnatin tarayya ta ci sanata, ita kuma matar Ahmadu Ali, wato Madam Mariam shugaban PDP na qasa ta sha kaye a hannun Accord Party. Gbemi Saraki da ‘yar uwarta Deji duk qannen Bukola Saraki ne, gwamnan Jihar Kwara, ‘ya’yan Olusola Saraki ne mai gidan siyasar Ilorin. Haka ‘ya’yan dattijan ‘yan siyasar suka mamaye lamura. A wannan zave Orji Kalu ya nuna zaqaquranci a PPA, amma Attahiru Xalhatu Bafarawa na DPP ya sha kunya, bai samu shugaban qasa ba, bai samu gwamna ba, bai samu sanata ba, bai samu xan majalisar wakilai ba, kai ko xan majalisar jiha a duk faxin Najeirya bai samu ba. Wannan annobar siyasa haka ta faxa wa Banu Xalhatu a Kano da Jigawa. Shehu Xalhatu bai samu komai ba a PAC, Aminu Xalhatu bai kai gaci ba a AC, Mama Rabi ba ta samu ba a PDP, amma Amina Xalhatu ta kai da qyar a majalisar jihar Kaduna. Sai dai a wannan zave Sanata Mamman Ali shi ya ci Gwamnan Yobe, amma tunda farko kotu ta soke shi, ba a san yadda za su qare da Sanata Albishir ba wanda kwanan nan jam’iyyar ANPP ta kore shi. Shi ma Dokta Ahmed Salik ya samu odar kotu inda tace a ba shi takara a Dala ta Kano mazabar xan majalisar tarayya, shi kuma suna taqaddama da Alhassan Uba Idris wanda jam’iyya ta amince da shi. Haka Yusuf Na Annabi da A.A Sule a Gwale ta Kano. Ranar 29 ga wannan wata za a rantsar da sabbin gwamnoni da shugaban qasa, su kuma majalisu za a rantsar da su ranar 3 ga watan Yuni 2007. Abin da ake jira tun da an samu shugaban qasa da mataimaki shi ne; Bayarbe ne zai zama shugaban majalisar dattijai duk da cewa ana kai gwauro a kai mari, Inyamuri kuma kakakin majalisar wakilai. Wataqila ko xan Taraba, ko Adamawa ko Gombe ya zama sabon magajin Mantu. Mutumin Jos, ko Nassarawa ya zama mataimakin kakakin majaliosar wakilai. Idan da akwai wani abin ta’ajibi da a za a daxe ba a manta da shi ba shi ne zamantowar Umaru ‘Yar Aduwa xan takarar PDP da cinye zaven da ya yi alhali, bai tava nema ba, aka jawo shi aka ba shi kuxi da duk qarfin gwamnati aka xora shi. Bayan haka mutanen Bauchi masu tsarin a kasa, a tsare, a raka, a jira sakamako sun yi juyin waina a Bauchi. Wani kuma abin mamaki shi ne, tsayuwa- tsayin daka na kotunan qasar nan musamman na Abuja. An tsige gwamnoni uku Joshua Dariye da Rasheed Ladoja da Peter Obi saboda qarfin kotuna sun dawo da gwamnonin karagar mulkinsu. Haka kuma kotuna suka baiwa Atiku gaskiya a duk sa’in’sa xin da suka riqa yi da Obasanjo. Majalisar dattijai kuwa da qanwarta ta wakilai kisan mummuqe da suka yi wa “Tazarce” da tankwafe mulkin soja na Tunji Olurin a jihar Ekiti shi ne gagarumin aikin da suka yi wanda ba za a manta da shi ba. Kawai abin da ya yi saura shi ne sauraren yadda ‘yan hamayya da magoya bayansu a qasashen duniya za su yi da sakamakon zaven da suka ce ba su yarda da shi ba. Haka kuma wane shiri za a yi don tunkarar zavukan 2011.Ni kuma ra’ayina shi ne maganin duk wani maguxi a Nijeriya shi ne a wajen fitar da xan takara a kwaikwayi Sakkwato, wajen kare quri’a a kwaikwayi Bauchi da Kano, kuma wajen sanya wakilai a duba Lagos da Abiya. |
The Whirlwind of Politics in 2007 This is the third round of voting in this, the Fifth Republic, and on this occasion all the bad apples have been tossed out of the governorships, the Senate and the House of Representatives, and we’ve even got an elected president. What changes has this wrought? In light of this turn of events, Nigeria was hoping that a civilian government would set up an election, swear in another civilian government, and transfer power to it. It would be the first time that this happened in the political history of Nigeria. When General Abdussalami Abubakar handed over power to Obasanjo in 1999, eleven political parties participated in the election. There were three that made progress: the APP [All People’s Party], the PDP [People’s Democratic Party], and the AD [Alliance for Democracy]. When the 2003 election year arrived, there were 20 political parties that participated in the election, and four played important roles: the ANPP [All Nigeria Peoples Party], the PDP, the AD, and the APGA [All Progressives Grand Alliance]. And this year, there were 50 political parties, the significant ones being the PDP, the ANPP, the PPA [Progressive Peoples Alliance], and the AC [Action Congress], while the DPP [Democratic Peoples Party] and the APGA made a noticeable but smaller impact . These patterns suggest that Nigerians need a political system made up of between three and six political parties. A number of amazing things took place in the political arena of 2007 in every part of this country. There has never been so much criticism of an election like the criticism, from both within and outside Nigeria, of the elections that were held on 14 and 21 April, at the state and national levels. There were killings, thefts of ballot boxes, failures to provide election materials, and shortages of ballots. In this election, it was the PDP that won the presidency with their candidates Umaru Musa ‘Yar Aduwa and his vice president Goodluck Jonathan. ‘Yar Aduwa was the governor of the state of Katsina, and a Muslim from the northwest, while Jonathan had been the governor of Bayelsa State, and a Christian from the southernmost region. The PDP won 28 state governorships in the election; they were in Adamawa, Anambra, Bayelsa, Cross River, Delta, Enugu, Gombe, Jigawa, Nassarawa, Plateau, Rivers, Sokoto, Taraba, Kaduna, Katsina, Kebbi, Kwara, Kogi, Ogun, Ondo, Osun, Ekiti, Ebonyi, Oyo, Niger, Akwa Ibom, Benue and Edo. Opposition parties gained eight governorships in the election: the ANPP got five, namely Kano, Zamfara, Borno, Yobe and Bauchi; the PPA won two states, Abia and Imo; while the AC got only one state, Lagos. New governors were elected in 28 states. Meanwhile, the governors of Kano, Kwara, Kogi, Ondo, Ogun, Osun, Borno and Gombe, having gained the trust of their citizens, were voted back into office. Among those who have held the office of lieutenant governor since 1999, throughout Nigeria, Mahmudu Aliyu Shinkafi is the only lieutenant whose governor has given him the opportunity to take over his position in the State of Zamfara. In the 2007 election, seventeen senators from the National Assembly ran for governor. Nine were from the ANPP: Senator Paul Ohioho Ukepo (Cross River), Senator Professor Daniel Saror (Benue), Senator Faruk Bello Bunza (Kebbi), Senator Abu Ibrahim (Katsina), Senator Muhammad Kirikasamma (Jigawa), Senator Tokunbo Afikuyomi (Lagos), Senator Abiola Ajimobi (Oyo), Senator A.A. Ibrahim (Taraba), and Senator Mamman Ali (Yobe). Of these, only one was victorious, in the State of Yobe. The PDP fielded four senators, two of whom won and two lost: the victorious ones were Senator Oserheimen Osunbor (Edo) and Senator Liyel Imoke (Cross River); those who were defeated were Senator Ifeanyi Ararume (Imo) and Senator Musliu Obanikoro (Lagos). The DPP supported two senators, Senator Abdullahi Bala Adamu (Taraba) and Senator Lawali Shu’aibu (Zamfara), neither of whom succeeded. The APGA and the Labour Party backed one candidate each: the LP Daniel Gbenga Aluko (Ekiti) and the AGPA John Wash Pam (Plateau). Nine departing governors ran for the Senate. All of them won except one. Those who sought senatorial seats were Ahmad Maƙarfi PDP (Kaduna), Ahmed Sani Yarima ANPP (Zamfara) and Ahmed Mu’azu (Bauchi), who didn’t win; in addition to Adamu Aleiro PDP (Kebbi), Bukar Abba Ibrahim ANPP (Yobe), Saminu Turaki PDP (Jigawa), George Akume PDP (Benue), and Chimaroke Nnamani PDP (Enugu); and the former governor Kabiru Gaya ANPP (Kano). Those who were thoroughly and unsurprisingly trounced in the election, , included General Muhammadu Buhari of the ANPP and Atiku Abubakar of the AC, running for president, as well as Senators Ibrahim Mantu, Arthur Nzeribe and Jonathan Zwingina. The AC candidate vanquished Mantu, while the PPA candidate defeated Nzeribe. Both Abdul Ningi and Faruƙ Lawan from the House of Representatives suffered terrible losses at the hands of the ANPP in Bauchi and Kano, respectively. Three senators who came from the State of Oyo Sanatoci were from the PDP: Kamoruddeen Adedibu, son of Alhaji Lamidi Adedibu, the political boss of Ibadan; Teslim Kolawole, senator for Central Oyo and Adedibu’s personal assistant; as well as Gbenga Babalola, senator for Oyo North and Adedibu’s son-in-law.The winner of the senate seat for Central Ogun was Iyabo Obasanjo-Bello, the daughter of President Obasanjo. Also winning a senate seat was (former Yobe governor) Bukar Abba, whose wife won a seat in the House of Representatives. The wife of Uffot Ekaete, head of the federal civil service , won as senator, while Madam Mariam, the wife of national PDP chairman Ahmadu Ali, was soundly defeated at the hands of the Accord Party. Gbemi Saraki and his sister, Deji, are both younger siblings of Bukola Saraki, the governor of the State of Kwara, all of them children of Ilorin’s political strong-man, Olusola Saraki. That’s how the elder statesmen dominated the state’s politics. Orji Kalu of the PPA emerged victorious in the election, but Attahiru Ɗalhatu Bafarawa of the DPP really lost out: he didn’t get the presidency, his candidate didn’t win for governor, he didn’t win a seat in the Senate or House of Representatives, and he didn’t secure a single seat in any state legislature anywhere in Nigeria; . This same political disaster befell Banu Ɗalhatu in Kano and Jigawa. Shehu Ɗalhatu won nothing for the PAC [Progressive Action Congress], Aminu Ɗalhatu didn’t reach his goal [“the opposite river bank”] for the AC, and Mama Rabi didn’t win for the PDP, although Amina Ɗalhatu managed to win her seat in the Kaduna state assembly. Also in this election, Senator Mamman Ali won the gubernatorial race in the State of Yobe, although from the outset the courts had disqualified him, but it was unclear what they would do about Senator Albashir, whom the ANPP had recently expelled. And Dr. Ahmed Salik had received a court order stating that he be allowed to run for the House of Representatives seat for the Kano constituency of Dala. He had been arguing with Alhassan Uba Idris, whom the party approved. Likewise for Yusuf Na Annabi and A. A. Sule from Gwale in Kano. On the 29th of this month [May 2007], the new governors and president will be sworn in, while new legislators will be sworn in on 3 June 2007. What people have been anticipating since electing the president and vice-president is this: it is a Yoruba who will be President of the Senate and, even though they’ve been scurrying about, an Igbo will be Speaker of the House. Perhaps someone from Taraba or Adamawa or Gombe would take over from Mantu (becoming the new senate vice president) ; or someone from Jos or Nassarawa could become Deputy Speaker of the House. If there is one surprising thing that will not be soon forgotten it is how Umaru ‘Yar Aduwa ended up becoming the PDP presidential candidate and winning the election, when in fact he never sought the position: he was pulled into the race, given money and all the clout of the government, and put up to it. Beyond this, the organized people of Bauchi arranged, protected, accompanied their votes and waited for the election results, which produced a shocking effect in Bauchi. Another amazing development was the tough attitude of the country’s courts, especially in Abuja. Three governors, including Joshua Dariye, Rasheed Ladoja and Peter Obi, were impeached, but on account of the strength of the courts, they returned when the courts reinstated their authority. The courts also consistently ruled in favor of Atiku in his legal struggles with his boss, Obasanjo. As for the Senate and the lower House of Representatives, they really dealt a knockout blow to the 3rd term agenda to extend the tenure of the departing government, just as they did in the case of Tunji Olurin’s fooling around with military rule in the State of Ekiti. These are important political landmarks that will not soon be forgotten. The only thing that remains is to be seen is how critics and observers around the world will react to an election result they don’t like. And also, what sort of preparations will be made for the elections of 2011. My own opinion is that the cure for all political fraud in Nigeria would be to emulate Sokoto and the methods adopted by Bauchi and Kano in protecting their votes, while Lagos and Abia stood out in the way they selected their candidates. |
Glossary
Hausa | Hausa Meaning | English Meaning |
---|---|---|
Yaya guguwar ta kada | Yaya a ka yi hidimomin zaɓen | How did the election process occur?(How did the wind blow?) |
Suka taka muhimmiyar rawa | Suka yi aiki mai muhinmanci. | They played a significant role (They did an important dance). |
Ana kai gwauro a kai mari | Yin aiyyuka daban daban a lokaci ɗaya. | Going different ways in doing things; multitasking |
Sun yi juyin waina | Sun sake yadda ya kamata a yi abu ko aiki. | They overturned (the result or the usual process). |
Inyamuri | Mutunen kudacin Nijeriya da ake kira Igbo. | A name used to describe a person from the Igbo tribe in Nigeria.This is used mostly by the Hausa people of Nigeria. |
Kwaikwayi Sakwato | A yi kamar jhar Sokoto. | To do something or a practice exactly as the State of Sokoto does it or did it. |
Note
Hausa | English |
---|---|
Ana yin zaɓe don ya zama wata hanya ta samun kyakyawan canji cikin duniya da ci gaban jama’a. Amma cikin shekarun da suka wuce, mutane na samun rashin biyan buƙata daga shugabanin su waɗanda kuma suka kasance shugabannin siyasa, musanman ma cikin Africa inda ba kulum ba zaɓe ke da kyakyawar sakamako ga jama’a.
|
Elections all over the world are meant to be a tool for positive change, affecting people's socio-economic development. But over the years, voters all around the world are becoming increasingly disappointed with their political leaders turned rulers, especially on the continent of Africa, where the election of political leaders has not necessarily translated into meaningful and effective changes for the populace. http://developmentanalysts.blogspot.com/2007/03/2007-elections-in-africa-nigeria-as.html |
<activity>
<problemset>
<problem correctindex="0">
<choices>
<opt>
<eng-response>This is an editorial by Bello Muhammad that provides a breakdown of what happened in the 2007 election in Nigeria. Muhammad described the election as unprecedented in the history of Nigeria because of the amount of criticism leveled at it by people at both the national and international levels. He concluded with the opinion that the next election in 2011 would be better if Nigeria followed the examples of states like Sokoto, Bauchi, and Kano. These states followed the appropriate procedures in selecting a candidate.</eng-response>
<response>Wannan shafin ra’ayin ne da Bello Muhammad ya bada dalla-dalla bisa sakamakon zaɓen Nijeriya na dubu biyu da bakwai (2007). Ya bayyana cewa zaɓen abu ne da ba’a taɓa yin irinsa ba a Nijeriya saboda mummunar sukar yadda aka gudanar da zaɓe daga ‘yan cikin gida har waje. Ya kamala da ra’ayinsa cewa zaɓen dubu biyu da goma sha ɗaya (2011) na iya zama mai albarka ga jama’a idan an bi misalan wasu jihohi kamar Sakwato, Bauchi da Kano saboda sun bi ƙa’ida wajen zaɓen ‘yan takararsu.</response>
<eng-fdbk>Correct. This editorial discusses the people’s opinions about the 2007 election in Nigeria, and the author concludes with his opinion about how to avoid unfair elections in Nigeria.</eng-fdbk>
<fdbk>Daidai. Wannan rahoton na bayyanin ra’ayin jama’a akan zaɓen 2007 a Nijeriya kuma marubucin ya kamala da ra’ayin shi bisa matakan da ya kamata a ɗauka don guje ma zaɓen da bai kamata.</fdbk>
</opt>
<opt>
<eng-response>This is an editorial explaining the aftermath of the 2007 election in Nigeria. According to the author, this is the first time Nigeria is receiving so much criticism about an election. The criticism relates to murders, theft of ballot boxes, and miscounting of votes. Nigerians were shocked at the candidate who won the presidential elections, the author argues, because it was obvious that he was never interested in the position. The public also blames the Nigerian government for making ‘Yar Adua the winner. The author concludes that the only solution is for Nigeria to follow the good example set by some of its states.</eng-response>
<response>Wannan rahoto ne da ke bayyana sakamakon zaɓen 2007 a Nijeriya. Marubucin ya bayyana cewa wannan ne na farko da Nijeriya ke fuskantar mummunar suka akan kashe-kashe, da sace-sacen ƙuri’a lokacin da ake yin zaɓen. ‘Yan Nijeriya sun yi mamaki sossai akan ɗan takarar da ya ci zaɓen saboda kowa ya sani da cewa bai taɓa yin marmarin matsayin ba. Jama’a sun kuma ba gwamnatin Nijeriya laifin tabbatar da nasarar ‘Yar Adua a matsayin shigaban ƙasa. kuma marubucin ya kamala da cewa mafitar Nijeriya ita ce a bi kyakyawan misalan wasu jihohin ƙasar.</response>
<eng-fdbk>Incorrect. The author did not mention the public’s reaction to the Nigerian government. What did he say about the government’s participation in ‘Yar Adua’s victory as a presidential candidate?</eng-fdbk>
<fdbk>Ba daidai ba ne. Marubucin bai yi bayani ba akan ɗaukar da jama’a ke yi ma gwamnatin Nijeriya ba. Mi ya faɗa akan shigar gwamnati wajen nasarar ‘Yar Adua a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa?</fdbk>
</opt>
<opt>
<eng-response>In this editorial, Bello Muhammad provides a breakdown of the 2007 election in Nigeria, and discusses the reactions of national and international bodies during the process. Some of the activities criticized by these bodies include murder and the mismanagement of the ballot boxes. Since the president and his vice president have been elected, Nigerians expect all the other top positions—majority leader, for example—to be occupied by Yoruba and Ibo representatives. The author concluded that Nigerians are waiting for the political opponent to take action against the whole process.</eng-response>
<response>Cikin wannan rahoto, Bello Muhammad na bada bayyanin zaɓen Nijeriya na 2007 dalla-dalla da kuma sa ra’ayin mutane cikin ƙasa da waje lokacin zaɓen. Mutanen kuma sun yi suka ga abubuwan da suka faru kamar kashe-kashen jama’a da satar akwatunan jefa ƙuru'u. Tun da an zaɓi shugaban ƙasa da mataimakinsa, ‘yan Nijeriya suna zaton cewa za’a ba Yarabawa da Ibo shugabancin sauran manyan maƙaman. Marubucin ya kammala da cewa ‘yan Nijeriya na jiran abun da ‘yan adawa ke da niyar yi akan harakokin zaɓen.</response>
<eng-fdbk>This is incorrect because the editorial is not mainly about the reactions of national and international bodies. What is the author’s main focus in this editorial? What did he say about Yoruba and Ibo representation in the government?</eng-fdbk>
<fdbk>Wannan ba daidai bane saboda rahoton ba yana magana akan ra’ayin jama’a cikin gida da waje kaɗai ba ne. Minene kan maganar marubucin? Mi ya faɗa akan waƙilcin Yarabawa da Ibo cikin gwamanti?</fdbk>
</opt>
</choices>
</problem>
</problemset>
<instr type="eng">INSTRUCTIONS:
Choose the best summary.</instr>
<instr type="target">Umurni:Zaɓi taƙaitawa mafi dacewa.</instr>
<finish>Why do you think some of the states in Nigeria succeeded in following the appropriate procedures during the election process?</finish>
<finishtl>A ganinku mi yasa wasu jihohin Nijeriya suka yi nasarar bin hanyar da ta kamata su bi wajen harakokin zaɓen?</finishtl>
<finish>How do you think the next government could influence the other states to follow the good example set by the few states the author mentions?</finish>
<finishtl>Yaya gwamantin mai zuwa ke iya tasirin tabbatar da jihohi sun bi kyakyawan misalan 'yan jihohin da marubucin ya ambata?</finishtl>
<finish>How do you think the public could avoid violence and ensure the security of the ballot box during elections?</finish>
<finishtl>A ganinku yaya jama'a ke iya kauce ma hayaniya, kuma su tsare akwatunan jefa ƙuri'a lokacin zaɓe?</finishtl>
</activity>