Toggle menu
24.9K
759
183
164.9K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

hausaradio/2022-05-28

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations

BBC Safe 2022-05-28 Saturday at 5:23 AM

BBC Safe 2022-05-28 Saturday at 5.23 AM.mp3 for hausaradio/2022-05-28

https://www.bbc.com/hausa/bbc_hausa_radio/programmes/p030s4n1

  1. Ukraine ta ce dole ne sojojinta su ja da baya daga sansanoninsu na ƙarshe (Luhansk) da ke gabashin ƙasar matsauri. Su na son kaucewa faɗawa hannun Rasha.
  2. MDD ta yi gargadin cewa kasashe a gabashin Africa na fama da matsanancin fari sakamakon ƙarancin ruwan sama.
  3. A Nigeria, yau ne babbar jam'iyyar hamayya ta PDP za ta zaɓi wanda zai mata takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023.
    "Kowanne yanzu yana jira ya ga da wane ɓangare ne zai ɗauki wannan tikitin. Idan kudu ne suka ɗauka, to kuma wannan ne zai haskawa ita kuma jam'iyyar hamayya da kuma sauran ma jam'iyyu ɗin."
  4. Hukumar Zaɓen Ƙasar (INEC), ta yi ƙarin bayani ne akan matakinta na tsawaita wa'adin gudanar da zaɓen da ta sake yi a jiya.
    "Ta sake duba wannan buƙatar nasun ne... toh ta ga amincewa da tsawaita wannan wa'adin, ba zai kawo cikas da wani abu da ya ke cikin wannan jadawali da aka tsara ba."

VOA Safe 2022-05-28 Saturday at 6:13 AM

https://www.voahausa.com/a/6570867.html

  1. Mai gabatarwa (Intro, labaran duniya, A Bari Ya Huce): Muhammad Hafiz Baballe
  2. Labaran Duniya (mai karantawa Baba Yakubu Makeri)
    1. Zantawar jami'an sojan Amurka da Ukraine a kan buƙatar Keiv ta samar mata da sabbin kayan yaƙi na zamani da za su taimaka wajen takawa Rasha birki a galabar da take samu a yankin Donbass. Amma ba su bayyana lokacin da za a kai wadannan kayayyakin ba.
    2. Shugaban sashin kare lafiyar jama'a na jihar Texas ya faɗa a jiya Juma'a cewa, 'yan sandan da suka bayar da martani game da harbin da aka yi a wata makarantar firamare a Texas sun yanke shawarar ƙin shiga ajujuwa inda maharin yake saboda sun yi imanin cewa ɗaliban ba su cikin haɗari.
    3. Ƙungiyar Taliban mai mulkin Afghanistan, ta yi watsi da kiran da MDD ta yi mata da ta ɗage dokokin da ke take hakkokin mata a kasar.
    4. Kafafen yada labarai da kungiyoyin kare hakkin bil Adama sun ce an tsare aƙalla wasu 'yan jarida 12 a cikin wani kame-kame da aka yi a Habasha.
    5. Sojojin ruwan Iran, sun kwace wasu jiragen mai guda 2 na kasar Girka a tekun Gulf.