Toggle menu
24.9K
762
183
165K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

hausaradio/BBCHausaSafe2025-08-11

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations

[1] [2]

00:00:10,179 --> 00:00:22,079 [BBC Hausa's Umaymah Sani Abdulmumin]

Masu saurare da fatan an wayi gari lafiya a cikin shirinmu na 6:30 agogon Najeriya, 5:30 kenan agogon GMT.

00:00:22,079 --> 00:00:57,020 [BBC Hausa's Umaymah Sani Abdulmumin]

To a cikin shirin za a ji cewa ƙungiyoyin 'yan jarida da Majalisar Dinki Duniya sun shiga yanayi na kaɗuwa kan kisan da Isra'ila ta yi wa fitaccen ɗan jaridan Al Jazeera, Anas al-Sharif, tare da abokan aikinsa huɗu a Gaza. Australia ta shiga cikin jerin ƙasashen duniya da ke shirin amincewa da kafuwar ƙasar Falisɗinu, a babban taron Majalisar Dinki Duniya na watan Satumba. Gwamnatin Jihar Katsina da ke arewacin Najeriya ta yi tsokaci kan irin matakan da take ɗauka bayan wani rahoton MSF ya nuna ana samun ƙananan yara da ke ci gaba da mutuwa a jiharsa sakamakon tamowa.

00:00:57,020 --> 00:01:11,299 [Speaker 1]

Mun san cewa tamowa yana ɗaya daga cikin matsalolin da jihar Katsina take da shi kamar sauran jihohi na Northwest kuma mai girma gwamnan da kanshi ya gani ma idon shi abin da ke faruwa aka ba da miliyan 500 domin a yi adressing wannan issue ɗin.

00:01:11,299 --> 00:01:21,360 [BBC Hausa's Umaymah Sani Abdulmumin]

A Jamhuriyyar Niger kuma ra'ayoyi ne suka banbanta kan matakin gwamnati na rusa ƙungiyar ƙwadago na ma'aikatan shari'a.

00:01:21,360 --> 00:01:29,739 [Speaker 2]

Duk inda aka ce kalmar ƙungiya. Ana nufin jama'a. Ana nufin gabakiɗaya a taru a duba hanya guda. Lallai in ko wannan ya kauce, ya zama ba ƙungiya ba ya zama wani abu daban.

00:01:29,739 --> 00:01:41,040 [Speaker 3]

Illa ce babba kuma koma baya ce babba tun da ai kasar Niger ya sama dokoki dayawa na ƙasa da ƙasa hannu.

00:01:41,040 --> 00:01:53,499 [BBC Hausa's Umaymah Sani Abdulmumin]

A Cameroon, ana nuna shakku kan 'yan addawa su iya taka rawar gani wajen kada jam'iyyar mai mulki ta Paul Biya. Toh amma kafin mu je, ga rahotanni, sai na gabatar da labaran duniya. Sunana Umaymah Sani Abdulmumin.