hausaradio/BBCHausaTV2020-09-28
More actions
https://youtu.be/18joqqiTdxE transcribed with the help of https://youtubeloop.net/watch?v=18joqqiTdxE
Toh jama'a barka da sake saduwa da ku a cikin shirin, ga taƙaitattun labaran duniyar da wasanni daga nan BBC.
- Za mu ga ɓarnar da cutar Korona ke cigaba da yi a duniya, a daidai lokacin da waɗanda suka mutu, suka haura miliyan guda.
- Shin, ko yaya rayuwa take ga al'ummar da ta dogara da yawon buɗe ido a lokacin da kuma aka dakatar da hakan?
Annobar cutar Korona, na cigaba da yin ɓarna a doran ƙasa, inda cutar ta yi adalin sama da mutane miliyan ɗaya a faɗin duniya. Alamu dai sun nuna cewa cutar na yaɗuwa cikin sauri a Indiya fiye da sauran ƙasashe. Inda a cikin watannan kaɗai, mutane 80,000 ne suka kamu da cutar a kowace rana. An kuma samu ƙaruwar ne saboda gwamnati ta cigaba da sassauta dokar kulle domin bunƙasa tattalin arzikinta. Sai dai kuma, ƙaruwar na nuna ana samun cigaba ta fuskar yin gwaji. Duk da yawan al'ummarta, wadanda suke da mutuwa a Indiyar sanadiyar wannan cuta, ba su da yawa.
Sai da Amurka, ita ce a sahun gaba a duniya da cutar ta fi yin ɓarna. Inda sama da mutum miliyan bakwai suka kamu da ita. Yawanci kuma an samu ƙarun wadanda suka kamu da cutar a kusan rabin jihohin ƙasar. Kuma ƙwararru a fannin lafiya na gargaɗin za a iya samun ƙaruwar a daidai lokacin da ake samun sauyin yanayi da kuma shigowar lokacin hunturu.
(1:40)
Ita kuma Afrika ta Kudu, ita ce tafi jijjiga cikin ƙasashen Afrika. An samu sama da mutum 650,000 da cutar Corona ta kama. Sama da 15,000 sun riga mu gidan gaskiya. A nahiyar Afirkan gabakiɗaya, an samu da sama da 1,390,000 da suka kamu da cutar ta Korona. Wasu kusan 34,000 kuma sun mutu daga watan Janairu kawo yanzu. Wannan adadi dai mai ƙaranci ne idan aka kwatanta da ƙasashen Turai...