hausaradio/BBCHausaTV 2019-08-28
From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
More actions
Full 10 minute version on BBCHausa.com
- Yau ta kasance wata rana mai ɗaukar hankali a siyasar Burtaniya. An amince za'a rufe majalisan dokoki tsawon makwanni yayin da wa'adin ficewar ƙasar daga ƙungiyar EU ke ƙara matsowa. Bayan zaman da za su yi a farkon watan gobe, majalisar ba za ta sake zama ba har sai ranar sha huɗu ga watan Oktoba. Wato makonni biyu kafin wa'adin. Ga rahoton Buhari Muhammad Fagge:
Haka dai majalisar dokoki za ta kasance a kusan tsawon makwanni biyar a cikin Satumba zuwa Oktoba, yayin da wa'adin ficewar ƙasar daga ƙungiyar EU ya ƙarato. 'Yan majalisa ba za su zauna a zauran majalisar ba. An dakatar da ita. Yau sarauniyar Burtaniya Elizabeth ta amince da shirin firam minista Boris Johnson na rufe zaman majalisar na yanzu.
Related links