hausaradio/BBCHausaTV 2019-08-29
From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
More actions
Full 10 minute version on BBCHausa.com
- Gwamnati a nan Burtaniya ta haƙiƙance cewa 'yan majalisar dokoki za su sami lokacin da za su yi muhawarar ficewar Burtaniya daga Tarayyar Turai. Duk kuwa da shirye-shiryen dakatar da majalisar na makonni biyar. A jiya ne dai sarauniya ta amince da buƙatar firam minista Boris Johnson na rufe majalisar har sai ranar sha huɗu ga Oktoba. Ƙasa da makonni uku kenan kafin Burtaniya ta fice daga Tarayyar Turai. Wannan batu dai ya janyo zanga-zanga a faɗin ƙasar.
Ga rahoton Buhari Muhammad Fagge:
Washe garin wata turka-turka a Westminster taƙaddamar ta cigaba sakamakon shawarar firam minista ta dakatar da majalisa. An dai samu ɓacin rai da rashin jin daɗi tare da zanga-zanga da ke iƙirarin gwamnati na amfani da ikonta ba bisa ƙa'ida ba. Masu adawa da ficewar Burtaniya daga ƙungiyar Tarayyar Turai sun ce ana neman saka musu takunkumi.
"There's going to be lots of... Za'a samu lokaci ne mai yawa na yin muhawara kafin ranar 31 ga watan Oktoba. Majalisa za ta zauna lokacin kuma za ta samu damar samun kowane ƙuduri ta ke so. Ina ji ɓacin ran na bogi ne. Mutanen da ba su son mu bar ƙungiyar Tarayyar Turai ne suka ƙirƙire shi. Kuma suna ƙoƙarin matuƙa su sauya sakamakon ƙuri'ar raba gardamar. Ba su kuma son mu samu alfanun da barin ƙungiyar EU ke da."
Tuni dai lokaci ya ƙure wa waɗanda a nan, suke son su dakatar da ficewar ba tare da wata yarjejeniya ba. Jam'iyyar adawa ta Labor da sauransu sun ce, dole su yi wani abu cikin gaggawa a yanzu domin ƙoƙarin cimma burinsu.
"It is about preventing... Wani ƙoƙari ne na hana ikon majalisa. Kuma domin dakatar da su, za mu ƙirƙiri wata muhawara ta gaggawa."
A yau, shugabar jam'iyyar Conservative a yankin Scotland ta fice. Ta ce, bisa dalilan kanta, ba na siyasa ba. Dama, ba mai goyon bayan firam ministan Boris ba ce. Toh amma ta fice tare da gargaɗi da 'yan majalisar su goya masa baya.
"Na tambaye sa kai tsaye: Ina son sanin kana son samun wata yarjejeniya ko kuwa? Ya tabbatar min ƙararar cewa ba ya yi. Ya yi amannar ƙoƙarinsa a taron G7. Ya taimaka ga samar da wata 'yar dama. Abinda zai ƙara taimakawa shi ne mutane waɗanda ke son a kauwace wa samun yarjejeniya. Su fito su ce, idan an sake kawo wata yarjejeniya a majalisa, toh za su goya mata baya."
An sake soma kururuwa a London. Yayin da hutun bazara na majalisa ke kusa da ƙarewa. A lokacin da 'yan majalisa za su komo a cikin mako mai zuwa, toh a sa ran rugugin ya ƙara zafafa. - Masu bincike, sun gano ƙoƙan kan ɗan Adam wanda ya kai kusan shekaru miliyan uku da dubu ɗari takwas (3.8 million years) a ƙasar Ethiopia. Sharhin da aka yi akan ƙoƙan wanda kuma aka wallafa a wata mujalla, ya ƙalubalanci ra'ayoyin da ake da su game da yadda ɗan Adam ya samu asali daga goggon biri.
Ga rahoton Haruna Shehu Tangaza:
Tsawon shekaru gwammai, masana kimiyya sun yi imani da cewa halittar da ke da waɗannan ƙasusuwan da suka kira Lucy, ita ce ta haifi bil Adama na farko. Toh amma, yayin tonan ƙasa mai zurfin gaske da aka yi a yankin Afar na Ethiopia, aka tono wannan abin da ya nuna ra'ayin na masana kimiyya ba daidai yake ba. Lokacin da aka kakkaɓe shi, aka goge, sai aka ga ƙashin kare na wata halittar da ta gabaci Lucy da ake kira anamensis. Kuma, har ake jin Lucy ɗin zuri'arta ce. Masu binciken, sun yi amfanin da na'urar kwamfuta wajen kwatanta yadda fuskar anamensis ta kasance.
"Abinda muka yi shi ne, zana fuska da gangar jikin halittar da ba mu san komai game da ita ba. Kuma muka san wani ɗan ƙalilan game da ita. Wannan na nufin za mu iya soma kwatanta su da wasu halittun. Kuma za mu iya fahimtar idan suna da dangantaka."
A halin yanzu dai, abinda aka sani game da anamensis, kaɗan ne ainun.
"Waɗannan ƙasusuwa ne da aka ƙera domin kwatanta yadda ƙasusuwan jikin anamensis suka kasance. Akwai ƙashin haɓa da na hannu da kuma na ƙafa. A halin yanzu, wannan shi ne iya abinda aka sani game da wannan halittar. Amma dai samun ƙashin ƙoƙuwar ke cikakkiya, ya ƙara mana fahimta game da ita. Sai dai, wani sharhi da aka wallafa a mujallar The Nature, ya nuna cewa anamensis, ba shi ne kakan Lucy ba. Balma, na [unintelligible] halittun biyu, sauraye a doron ƙasa tare da juna aƙalla shekara dubu ɗari. Wannan na nuna yiyuwar kasancewar Lucy da anamensis sun fito ne daga tsatso ɗaya. Kuma idan har hakanne, toh suma sauran halittu masu kama da gwaggon biri, da masana kimiyya ke da'awar cewa daga gare su ne 'yan Adam suka fito, suna da nasu kakannin na daban. Masu bincike sun ce yanzu, an ƙara samun [unintelligible] wasu halittun da kowace ka iya zama na bani Adam na farko da suka rayu a doron ƙasa.- 'All bets now off' on which ape was humanity's ancestor --Dated: 28 August 2019
- An gano kwarangwal mai 'shekara miliyan uku' a Afirka Ta Kudu --Dated: 6 Disamba 2017
- Ko ka san dalilan da suka sa dan adam ke tafiya da kafa biyu? --Dated: 25 Janairu 2017
- Yau, masu fama da cutar [unintelligible: measles?] da ya ƙaru zuwa matakin [unintelligible] a cikin shekaru sha shida. Hukumar lafiya ta duniya WHO ta dangantaka wannan da rashin kayan aikin kiwon lafiya masu kyau. Da kuma kuskuren da wasu ke yi na cewa allurar riga-kafi na da cutarwa. Duk kuwa da hujjar da aka samu na cewa wato saɓanin haka.
- Gwamnatin Yemen ta zargi haɗaɗiyar daular Larabawa da gaddamar da hare-haren sama akan dakarunta a garin Aden na kudancin ƙasar. Ƙunguyoyin agaji sun ba da rahoton mummunar faɗa a babbar birnin ƙasar. Kuma jami'ar gwamnati sun ce haɗaɗiyar daular Larabawar ta kashe sojojin gwamnati kusan talatin.
- Yemen war: Government forces re-enter key city of Aden --Dated: 28 August 2019
- Al-Farouq Aminu, wani shahararren ɗan wasan ƙwallon kwando ne na NBA. Wanda kuma yake yin wasan ƙwallon kwandon a Amurka. Babu shakka, ya kuma yi suna a Najeriya inda yake yi wa tawagar wasan ƙwallon kwandon ta ƙasa da aka sani da D'Tigers wasa. BBC ta samu tattaunawa da shi a Lagos game da usulinsa.
Duk da an haifi shi a Atlanta mai nesan mil dubu biyar daga Najeriya, toh amma hakan ba zai hanawa Al-Farooq Aminu kiran Najeriya gida ba. Daga wasan ƙwallon kwando na NBA da kulob-kulob kamar na LA Clippers da Portland Trailblazers, yanzu kuma Orlando Magic, tarihinsa da nasarar sa ta kasance a Najeriya.
Matambayi: Barka da zuwa gida Al-Farooq. Mun yi farin cikin kasancewarka tare da mu. Kana wasan ƙwallon kwando ne na NBA a Amurka. Muna da wani shiri mai ban-sha'awa a gare ka. Ana kiransa Najeria a Jikka.
Al-Farook: Eh, na zaƙu matuƙa.
Matambayi: Abu ne mai sauƙi...
Al-Farooq: Ah, wannan yana tuna min sarauta ne. Na tuna, da ina tasowa, na ga hoton kaka na da wannan. Kuma kaka na sarki ne a Ibadan. Kuma sukan bayar da wannan ga sarki ko kuma wani shugaba ne.
Matambayi: Yanzu kuma ga wannan. Abu mai fice matuƙa.
Al-Farooq: Ƙwarai! Wannan abinci ne, wannan amala ce. Toh amma galibi teba na ke ci lokacin da na ke tasowa.
Matambayi: Haka ya sa ka ke da tsawo?
Al-Farooq: Eh, da kuma ƙarfi ba.
Matambayi: Wannan almara ce. Kulob ɗin D'Tigers a gasar cin kofin duniya, tamkar dai mafarki ne yadda wannan tawagar wasan ƙwallon kwando ta Najeriya ta soma. Kuma, ka san D'Tigers na ta kafa tarihi ɗaya bayan ɗaya.
Al-Farooq: Gaskiya! Abin alfahari ne. A shekara ta 2012, mun je wasan Olympics a karon farko, a matsayin wata tawagar kwando. Daga nan, mun tafi gasar Afro Basket ta cin kofin Afrika. Kuma mun ɗakko kofin a karon farko. A yanzu, za mu je gasar cin kofin duniya. Muna kuma fatan mu samu lambar yabo ta yadda za mu iya sake samun wani abu a karon farko.