https://gloss.dliflc.edu/products/gloss/hua_soc411/hua_soc411_source.html
Hira da Sarkin Noma
Saude: Ran sarki ya daɗe. Maidubu: Amin, tare da naki. Saude: Yaya damina? Maidubu: Damina, an gode Allah Saude: To madalla. Allah ya ba da alheri. Maidubu: Amin, amin. Saude: To sarki mi kukan noma wannan lokacin? Maidubu: To mukan noma gero lokacin damina. Akwai kuma gyaɗa da wake da masara. Mata su kan shuka yakuwa da kuɓewa . Saude: Lalle kuna fama da aiki don samar da cimaka. Lokacin da damina ta wuce mi kuke yi? Maidubu: To ai akwai noman rani. Ga kaka mukan adana albarkatun gona. Kuma mukan fara shirin noman rani. Saude: Cikin gonar da kuke shuka gero kuke noman ranin? Maidubu: A’a akwai lambuna don wannan aiki. Saude: Mi kukan sa a lambunan naku? Maidubu: Mukan noma tumatir, tugande, albasa, kabewa, barkono da sauransu. Saude: Allah ya sa albarka. Maidubu: Amin, muna bukatar ta sosai. Saude: To Allah ya ja zamanin sarki, na gode da wannan hira. Mu huta lafiya Maidubu: Amin, sai an jima. |
A Conversation with a Lead Farmer
Saude: Long life to the chief. Maidubu: Amen, to you as well. Saude: How is the rainy season? Maidubu: Thank God for the rainy season. Saude: Excellent! May God grant us good favor. Maidubu: Amen, amen. Saude: Well, chief, what do you usually grow during this season? Maidubu: Well, we grow millet during the rainy season. And also peanuts, beans and corn. Women sow red sorrel and okra. Saude: You surely work hard to provide food. What do you do after the rainy season has passed? Maidubu: Well, there is dry season farming. We usually store crops at harvest time. Then we start preparing for dry season farming. Saude: Do you do it on the same farm as you grow the millet? Maidubu: No, there are irrigated fields for that type of work. Saude: What do you usually plant in your irrigated fields? Maidubu: We usually grow tomatoes, peppers, onions, pumpkin, chilis and others. Saude: May God bless you. Maidubu: Amen, we very much need it. Saude: Well, may the chief's reign last a long time, thank you for the conversation. Goodbye. Maidubu: Goodbye. |