https://gloss.dliflc.edu/products/gloss/hua_soc418/hua_soc418_source.html
Sabon Shirinmu | Our Newest Program | |
Masu sauraro albishirinku! Muna gabatar da wani sabon shirin da muke kira Koyarwa a Yau. Cikin wannan shiri za mu duba harkar ilimi a ƙasar Hausa. Za mu yi hira da ma’aikata daga gwamnati da ƙungiyoyi. Za mu yi masu tambayoyi a kan irin nasarori da suke samu da kuma shirye-shiryen da sukan kafa. Za mu kuma tattauna da malaman makaranta a kan irin kalubalen da sukan fuskanci a kowace rana. Haka kuma za mu yi magana da ɗalibai game da karatun da suke yi. | Listeners, here’s some good news! We are introducing a new program called Teaching Today. In this program, we will look at the business of education in Hausaland. We'll talk with officials from governments and organizations. We'll ask them about their successes and the programs they have established. We will also talk with teachers about their everyday challenges. Also, we will talk with students about their studies. | |
Za mu kewaya duniya mu yi hira da ma’aikata da malamai da ɗalibai daga ƙasashe daban daban. Daga ɗaliban jami’a a Amurka zuwa ‘yan makaranta a wani makarantar firamare a kasar Afghanistan. Muna magana da su don mu gane yadda suke bambanta. | We will circle the globe and chat with officials, teachers, and students from various countries, from American university students to students at a primary school in Afghanistan. We will talk to them to see how they differ. | |
Ku zo ku ji bayyanai da ra’ayoyi a kan halin da aikin bada ilimi ke ciki a ƙasashenmu. | Join us and listen for information and opinions on the state of education in our countries. | |
A kowace sati za mu duba wani shirin da wata makaranta ke yi a ƙasar Hausa. Haka kuma za mu nemi ra’ayoyi daga mutane a ƙasar Hausa. | Each week, we will look at a program that a school is undertaking in Hausaland. We will also ask the opinions of people in Hausaland. | |
Za mu fara gobe da wata hira da muka yi da farfesa Amadu Lawal na Kano. Ya yi mana bayanai a kan wata sabuwar makarantar firamare da aka buɗe a Kano. | We are starting tomorrow with an interview we had with Professor Amadu Lawal of Kano. He talks about a new primary school that has opened in Kano. | |
Muna fatan za ku sauraremu kowace ranar Laraba a ƙarfe takwas na marece. Koyarwa a Yau. Sabon shirin na sashen Hausa. Zo ku saurara. | We hope you will listen to us each Wednesday at eight in the evening. Teaching Today - the new program from Hausa Service. Join us and listen. |