https://gloss.dliflc.edu/products/gloss/hua_soc419/hua_soc419_source.html
A Tura Yara Zuwa Makaranta | Send Your Children to School | |
Masu sauraro sallama alaikum. Ni ne farfesa Abdou Moumouni. Ina kira ga uwaye a duk faɗin ƙasarmu da su tura ‘ya’yansu zuwa makaranta. Zuwan makaranta dole ne ga kowane yaro daga shekara bakwai da haifuwa zuwa shekara goma sha biyar da haifuwa. Haka kuma zuwan makaranta yana da amfani. | Greetings, listeners. I am Professor Abdou Moumouni. I am calling on parents across our country to send their children to school. Attending school is required for all children between the ages of seven and fifteen. Furthermore, going to school is useful. | |
A lokacin da nike da shekara bakwai da haifuwa an gina makaranta a garinmu. Uwaye dayawa suke hana ‘ya’yansu su tafiyan makaranta. Amma uwayena sun ce dole ne in yi makaranta. Na tafi makaranta kowace rana. Saboda wannan damar da uwayena suka ba ni, na samu damar yin dogon ilimi a jami’a. Yanzu ni farfesa ne a Jami’a. Kuma ina aiki domin ci gaban ƙasarmu. Duka wannan na samu saboda uwayena sun tura ni makaranta. | When I was seven years old, a school was built in our village. Many parents kept their children from going to the school. But, my parents told me that I had to go to school. I went to school every day. Because of this opportunity that my parents gave me, I was able to pursue a higher education. Now, I am a university professor, and I am working to help our country develop. All of this is because my parents sent me to school. | |
Duniya tana canzawa. Saboda haka yaranmu suna bukata ilimi na fannoni daban-daban don su samu aiki mai kyau su samu ci-gaba. Muna bukata mutane da za su kula da makomar ƙasarmu. Saboda haka ya kamata kowane yaro ya tafi makaranta. | The world is changing. Because of that, our children need an education in various subject areas in order to find good work and success. Our country needs people who will look after its future. That is why every child should go to school. | |
A tuna fa ya kamata a tura ‘yan mata zuwa makaranta daidai da maza. Su ma dole su yi makaranta. Su ma suna bukata ilimi. Karatu da rubutu na da amfani ga kowa da kowa. Daga shugaban ƙasa zuwa uwar gida, kowa na bukatan ilimi. | Remember that girls should be sent to school just like boys. They are also required to attend school. They also need an education. Reading and writing are important for everyone. From the president of the country to the housewife, eveyone needs an education. | |
Yaranmu su ne manyan gobe. Saboda haka ya kamata mu ba su damar samun ilimi. Ta haka ne ƙasarmu za ta ci gaba. Allah ya bada alheri. Allah kuma ya kiyaye kasarmu. | Our children are the leaders of tomorrow. So, we should give them the opportunity to gain an education. That is how our country will move forward. May God bless you, and may God protect our country. |