https://gloss.dliflc.edu/products/gloss/hua_soc420/hua_soc420_source.html
Matsalolin Addini a Najeriya | Religious Problems in Nigeria | |
Introduction: Yanzu kuma ga hirar da Nasiru Adamu el-Hikaya ya yi da shugaban ƙungiyar kiristocin Najeriya reshin arewa maso gabas wanda yake aiki da ECWA Bauchi DCC watau Reverend Reverend Shuaibu Byel. Sun zanta ne akan rikicin da ake fama da shi yanzu haka a ƙasar Najeriya da kuma matakin da ƙungiyarsa ta ɗauka cewa Kiristocin Najeriya su kare kansu daga hare-haren da ake kai musu. | Introduction: And now here is Nasiru Adamu el-Hikaya’s chat with the chairman of the north-east region of the Christian Association of Nigeria, who works with ECWA Bauchi DCC, Reverend Shuaibu Byel. They discussed the crisis being faced in Nigeria, and the measures that his organization/association took, that Christians should protect themselves from the attacks being perpetrated against them. | |
Reverend: Eh abinda yake faruwa a cikin Najeriya abin takaici ne, abin ban razana, abin ɓacin zuciya ƙwarai gama abinda yake faruwa a sashin arewa maso gabas, wannan sashi jihohi huɗu yanzu kama daga Maiduguri, Yobe, Gombe, ga shi yanzu Adamawa. Rayuka ana ta kakashe su kawai kamar dabbobi, kuma waɗannan mutane suna fita fili su ce su suka yi. Waɗannan al’amura abubuwa ne na baƙin ciki kuma ya kamata ahhh matakan da shi ka ji a wajen ehh shugaban CAN na ƙasa su ne waɗanda aka gani ya kamata a ɗauke su domin ya zama dole kowane ɗan Adam, ba wai Kirista kawai ba ya zama da cewa yana da bayanin cewa ya san abinda ya shafe shi , ya kuma tsare kada wani abu mai muni ya faru da shi. Ai ba za ka bar garwashin wuta ya faɗa kan cinyanka ka barshi yana ta cinka ba dole ka tura ka yar, ko kuma kana da ruwa sai ka kashe, ruwan. | Reverend: Yes, what is happening in Nigeria is frustrating, terrifying and very heartbreaking because of what is happening in four states in the north-east region. The issues have spread, now in four states, from Maiduguri, Yobe, and Gombe and now Adamawa. People are being killed like animals, and these killers are coming out to say they are responsible. These are sad issues. Some measures, as you heard from the president of CAN, are considered necessary because every human being, not only Christians, should be aware of everything that concerns him and should protect himself from any evil thing happening to him. I bet you would not watch hot embers fall and burn your laps, you must push it off or quench it with water if you have some. | |
Reporter Nasiru Adamu: To wannan mai bishare ya nuna kamar yadda shi Bishop Ayo Oritsejafor ya faɗa cewa daga yanzu mabiya za’a basu umurnin su riƙa kare kansu. Ta wane irin yanayi ne zasu na kare kan nasu? | Reporter Nasiru : Ok preacher, this shows, as Bishop Ayo Oritsejafor mentioned, that henceforth followers will be instructed to protect themselves. In what ways are they going to be protecting themselves? | |
Reverend: Kare kai ina ji ba abu ne sabuwa ba, yana nan cikin kundin tsarin mulkin ƙasar nan da cewa muna da damar abinda ya shafi ‘yancinmu mu kuma tabbatar mun san abinda ‘yancinmu ne mu nemi hakinsa a wajen hukuma. In ta gaza kuma a faɗa mata kamar yadda yanzu ka ji ana faɗa da cewa gwamnoni da sarakunanmu na gargajiya da shugabaninmu na siyasa basu nuna cewa sun nuna damuwa da takaici kan abunda ke faruwa ba don ba matakin da ma suka fara,suka taɓa yi. Muna tsoron kada wani abu ya zama cewa akwai yaƙin basasa a ƙasa nan domin abune mai muni wadda idan za’a ce za’a yi yaƙin basasa, amma gaskiyar kenan shi ne muna da baƙin cikin abinda ke faruwa. Ni mutumin arewa ne, kai mutumen arewa ne,abubuwan da muke yi suna faruwa a wajenmu, ba abubuwan da za su kawo mana ci gaba ba ne a wannan yanki. | Reverend: I don’t think protecting oneself is something new; it is in this country’s constitution that we have rights and to ensure that we know what our rights are and seek our rights from authority. If a situation becomes impossible we should inform this authority. Our governors, traditional chiefs/kings and political leaders show no sign of concern for what is happening as they have not taken any measures nor have they ever taken any measure. We fear that something will happen to cause a civil war. Civil war would be a terrible thing if it were to happen. The truth is that we are very sad about what is happening. I am a northerner, you are a northerner; the things that we do and are happening in our region, are not things that will bring development in this region. | |
Reporter Nasiru: Mai bishara in ka duba yaya kuke ɗaukan wannan al’amari ne a ce wai wani mutun shi guda ɗaya misali ya hida sanarwa ya ce Kiristoci misali su, an ba su ko kwana ukku ko mutanen kudu su koma kudu, bayan kuma ku mabiyannan ma ku ‘yan arewa ne, gidanku ne, iyayenku da kakaninku a nan suke. Yaya kuke ɗaukar wannan labari? Kuna ɗaukansa da wani matsayi mai ƙarfi ? [interruption] | Reporter Nasiru: Preacher, how do you see this issue, that one individual for example gives instruction that Christians for instance have three days, or the southerners should return to the south? When your followers (Christians) are northerners, it is your home, your parents and grandparents that live here. How are you taking this news? Are you taking it seriously? [interruption] | |
Reverend: Fasarar abinda ya zama muna da damuwa ɗin kenan. Yaya za’a yi ta bada kwanaki wa wasu mutane? Waɗansunmu ba mu ‘yan Najeriya ba ne ba? | Reverend: That is the issue that has become a problem for us. How can some people be given days? Are we not all Nigerians? | |
Reporter Nasiru: Ba kwa jin in kun ce wannan saƙo na mabiya su kare kai, watakila wasu za su ɗauka cewa kawai su fita da makamai ne su yi ta faɗa da ‘yan uwansu musulmi? | Reporter Nasiru: Don’t you see that if you ask followers to protect themselves, maybe some will assume that they should arm themselves and fight their Muslim neighbors? | |
Reverend: Eh to yana yiyuwa, abinda ya faɗa ya ce kowa masani ne idan a cikin Christianity ne. idan an ce ka kare kanka, ya nuna cewa idan ka ga wani abu da danja sai ka sanar da wuri don a taimake ka. Idan ka ga ma cewa ga wasu ana kan cutarsu, ka faɗi Magana da wuri. Jami’an tsaro a kullum sukan faɗa mana da cewa idan mun ji abu ƙis, mu faɗa kuma suna ba mu lambobin wayoyinsu don haka wannan mataki na kariya, sai a yi shi. | Reverend: Yes, it is possible. What he said is that everyone is knowledgeable if he is a Christian. If you are asked to protect yourself, it means when you see something suspicious or dangerous, you should notify others early so that they can help you. Also, if you see that some people are being cheated, you should say something right away. Security officials always tell us to tell them when we hear the slightest thing. They also give us their phone numbers, thus this measure of protection should be taken. |