https://gloss.dliflc.edu/products/gloss/hua_soc424/hua_soc424_source.html
Manyan Gobe | Leaders of Tomorrow | |
Sanarwa | Announcement | |
Ga wata sanrawa. Gidan rediyon Imani na sanar da cewa an kafa sabuwar ƙungiya. Ana kiranta ƙungiyar Manyan Gobe. An kafa wannan ƙungiya tare da haɗin kai daga kamfanoni da ƙungiyoyi daban-daban. Wannan ƙungiya za ta yi ayyuka waɗanda suka shafe makarantu a ƙauyuka. Ƙungiyar za ta fara aiki a wasu ƙauyuka guda ɗari a jihohin Kano da Sakwato. Daga baya kuma za a ƙara garuruwa a jihohi daban-daban na arewacin Nijeriya. | Here is an announcement. Radio Imani is announcing the establishment of a new organization. The organization is called Leaders of Tomorrow. This organization was established with cooperation from various companies and organizations. This organization will create projects that relate to rural schools. The organization will begin work in a hundred villages in the states of Kano and Sokoto. After that, they will add towns in various states of Northern Nigeria. | |
Ayyukan da ƙungiyar za ta yi suna dayawa. Za a bada horo ga malamain makarantu. Za a samar da litattafai ga makarantu. Za a yi gyare-gyare a gidajen makaranta. Haka kuma za a samar da na’urorin zamani ga makarantu. A wasu garuruwa kuma za a gina sabbin gidajen makaranta. Duk waɗannan ayyuka za a yi kyauta. Za mu tabbata da cewa kowane ɗan makaranta ya samu ilimin da ya kamata. | The organization will conduct many projects. They will train teachers. They will provide books for schools. They will repair school buildings. Also, they will provide current technology to schools. Additionally, in some towns, they will build new school buildings. All of these projects will be free. We are going to make sure that every student receives the education that he should. | |
Gidan rediyon Imani za ta taimaka ta hanyar bada sanarwa game da shirye-shiyen ƙungiyar Manyan Gobe. Ƙungiyar UNICEF za ta bada taimakon kuɗi. Haka kuma UNICEF za ta aika wasu masanan harkar ilimi zuwa nan. Masanan za su horas da malaman makaranta. Bayan haka kamfanoni daban-daban za su bada taimakon kuɗi. Hakazalika, muna yin kira ga dukkan masu sauraronmu da ku goyi bayan wannan aiki mai muhimmanci. | Radio Imani will help by making announcements about the programs of Leaders of Tomorrow. UNICEF will give financial assistance. Also, UNICEF will send education experts here. These experts will train teachers. Additionally, various companies will give financial assistance. Furthermore, we are calling on all of our listeners to support this important work. | |
Aiki Na Shidda | Activity Six | |
Idan ana son bada taimakon kudi, sai a je shafin duniyar gizonmu inda za a biya kuɗi ta hanyar intanet. Aikin da wannan ƙungiyan ke yi na da amfani ga yara da matasan ƙasarmu. Mu tuna da cewa ‘yan makaranta sun ne manyan gobe. Saboda haka, ya kamata mu haɗa kanmu. | If you want to give financial help, go to our website where you can give money via the Internet. The work that this organization is doing is useful for the young people of our country. Remember that the students are the leaders of tomorrow. Because of that, we should work together. |