Toggle menu
24.1K
670
183
158.7K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Quran/1/IRIB Hausa Tafsir

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations

Suratul Hamd, Gabatarwa Da Aya Ta 1 (Kashi Na 1)

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da saduwa cikin wani shirin Hannunka Mai Sanda da fatan za ku kasance tare da mu tun daga farkon shirin har zuwa karshensa.

Dukkanin mu mun san cewa a wannan duniya ta mu ta yau da ke cike da ci gaba na masana’antu da sauransu, duk wani abin da wani kamfani ya kera su kan ba wa mai saye takardar da take bayanin dukkanin bangarori na wannan abin, yadda ake amfani da shi da kuma abubuwan da suke cutar da shi, don mai sayen ya san yadda zai yi amfani da shi yadda ya dace don kada ya yi saurin lalacewa.

Ni da ku din nan da kuma dukkanin bil’adama, wata na’ura ce wacce Mahaliccin mu ya halicce mu, sannan kuma sakamakon irin gagarumin rauni na jiki da kwakwalwa da mu ke da shi, mun gaza wajen fahimtar hakikanin kan mu da kuma hanyoyin da za mu sami farin ciki da sa’ada.

A bangare guda kuma shin mu din nan muna kasa da wani firiji ko kuma talabijin ne da wadanda suka samar da su suke ba wa mai saye littafin da ke bayanin yadda za a yi amfani da su, amma kuma Mahaliccin mu ya gagara rubuta wani littafi yadda za mu rayu cikin jin dadi da annashuwa?!!

Ko kuma shin mu din nan bil’adama ba ma bukatar wani littafi mai shiryarwa wanda a cikinsa aka yi karin haske dangane da siffofin da jiki da ruhin mu ya kebanta da su haka nan kuma da irin karfi da damar da muke da shi? Ko kuma hanyar da ta dace wacce za a bi wajen amfani da irin wannan karfi da kwarewa da muke da su ba?

Sama da hakan kuma a yi karin bayani sosai dangane da hatsarin da ke barazana ga jiki da kuma ruhin mutum da kuma haifar masa da matsaloli a cikin wannan dan karamin littafi??

Shin za a iya yarda da cewa Allah Madaukakin Sarki wanda ya halicce mu bisa asasi na ilimi da rahama da so da kauna, zai iya barin mu haka nan kawai ba tare da ya shiryar da mu hanyar sa’ada da samun farin ciki da kwanciyar hankali ba?

Alkur’ani mai girma dai a matsayinsa na Littafi na karshe da Allah Madaukakin Sarki Ya saukar da shi a matsayin littafi mai shiryar da bil’adama, sannan kuma ya nuna masa hanyar samun sa’ada da jin dadi kamar yadda kuma ya nuna masa abubuwan da za su iya halaka shi da haifar masa da matsaloli.

Na’am Alkur’ani mai girma ya yi bayanin ingantacciyar alaka ta iyali da zamantakewa, lamurra na shari’a da kyawawan halaye, bukatu na jiki da ruhi, nauyi na daidaiku da jama’a, ingantattu da kuma sunoni na kuskure da suke cikin al’umma, dokoki na kudi da tattalin arziki da sauran lamurra masu yawa na daban da suke da gagarumar rawa wajen kyautata rayuwar dan’adam ko kuma lalata ta.

Duk da cewa a cikin Alkur'ani mai girma, an kawo labarai da kissoshin yakukuwa da rikice-rikice da kuma yadda yaruwar wadansu maza da mata na al'ummomin da suka gabata ta kasance, to amma Alkur'ani dai ba littafi ne na labari da kissoshi ba, face dai littafi ne na daukan darussa saboda rayuwar al'ummomin wannan zamanin.

A saboda haka ne ma aka sanya wa wannan littafin suna 'Alkur'ani' wato littafin abin karantawa, wato littafin da wajibi ne a karanta shi sai dai ba wai kawai karatu da harshe ba irin yadda ake karantar da yara a makaranta, face dai karatu tare da tunani cikin abubuwan da ake karantawa, duk da cewa an bukace mu din da mu karanta shi din kamar yadda ake karantawar.

'Yan'uwa masu girma cikin wadannan silsila na shirye-shiryen da za mu gabatar muku da su za mu gabatar muku da wasu ma'anoni ne na ayoyin Alkur'ani mai girma da irin sakonnin da ke cikinsu don ku din nan masu karatu da saurare ku sami damar tsara rayuwar ku gwargwadon koyarwar Alkur'ani don sama wa kanku sa'ada, sannan kuma ku amfanar da rayuwar da karatun ayoyin Alkur'ani mai girma.

Kamar yadda muka sani, Alkur'ani yana da surori 114 ne sannan kuma kowace sura tana da wasu ayoyi a cikinta. Alkur'ani dai ya fara ne da surar da ake kiranta da sunan 'Mabudin Littafi' wacce aka fi saninta da Suratul Hamd. Daga cikin muhimmancin da wannan sura wacce take da ayoyi bakwai take da shi, shi ne cewa a kowace rana wajibi ne a karanta alal akalla sau goma yayin salloli biyar na rana, wanda idan ba a karanta ta ba, to salla ta baci.

Wannan sura wacce ita ce mafarin littafin Allah ta fara ne da wata aya wacce duk wani aikin da mutum ya fara da ita to kuwa karshen aikin zai zamanto mai kyau:

A saboda haka sai a gyara zama don sauraren aya ta farko ta wannan surar:

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Tun da jimawa dai ya zamanto wata dabi'a tsakanin mutane cewa su kan fara duk wani aiki mai muhimmanci ne da sunan daya daga cikin manyan mutanen su, don su sami albarkacinsa cikin wannan aiki na su. A matsayin misali masu bautan gumaka, su kan nemi albarka da sunayen gumakan na su, a yau ma a wasu wajajen akan fara wasu bukukuwa da wasu ayyukan ne da sunayen shugabannin kasashe da sauransu.

To amma wanda ya fi dukkanin wasu ma'abota girma, girma da daukaka shi ne Allah Madaukakin Sarki wanda shi ne Mahaliccin dukkanin halittu. Don haka ba wai Alkur'ani kawai ba, dukkanin saukakkun littafa sun faro ne da sunansa.

Baya ga cewa addinin Musulunci ya kiraye mu da mu fara dukkanin ayyukan mu ciki kuwa har da ci da sha, zama da tashi, tafiya, magana da rubutu da sauran ayyukan na rayuwa da sunan Allah wato (Bismillah), sannan kuma matukar ba a yanka wata dabba da sunan Allah ba, to ba ya halalta mu ci namanta.

"Bismillah" dai bai takaita kawai da addinin Musulunci ba, face dai kamar yadda ya zo cikin Alkur'ani jirgin Annabi Nuhu ma da sunan Allah ya fara motsawa, haka nan wasikar da Annabi Sulaiman ya aika wa Bilkisu da shi ma da sunan Allah ya faro ta.

A bisa akidar mu 'Bismillah' wata aya ce cikakkiya kuma wani bangare ne na suratul hamd. Saboda Ahlulbaitin Manzon Allah (s.a.w.a) suna fushi da wadanda suke kin karanta wannan ayar ko kuma suke karanta ta a hankali a lokacin salla, don haka suke karanto ta fili a cikin dukkanin sallolinsu.

Yanzu bari mu yi dubi cikin darussan da suke cikin wannan aya:

"Bismillah" tana sanya wa ayyukan mu abubuwan ado na Ubangiji sannan kuma ta kan tseratar da ayyukan mutum daga bala'i na shirka.

'Bismillah' tana nufin cewa Ya Ubangiji Allah lalle ban mance da kai ba, don haka kai ma kada ka mance da ni. Duk wanda ya ke fadin 'Bismillah' to lalle ya hada kansa da karfi maras karshe da kuma wata rahama maras karewa ta Ubangiji.

Muna fatan kun ji dadin wannan shirin, sannan kuma mun sami damar bayyanar muku da wani bangare na koyarwar Alkur'ani mai girma. Don haka sai ku biyo mu a shiri na gaba inda za mu ci gaba daga inda muka tsaya.

Wassalamu alaikum wa rahamatullah wa barakatuhu.

Suratul Hamd; Aya Ta 2-5 (Kashi Na 2)

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai.

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa cikin wani sabon shirin hannunka mai sanda.

A shirin da ya gabata mun yi muku bayani kan Suratul Hamd inda muka fara da ayar 'Bismillah'. A shirin mu na yau za mu yi dubi ne cikin ayoyi na biyu zuwa na biyar na wannan surar don mu kara fahimtar Ubangijinmu. Don haka sai mu saurari aya ta biyun:

الْحَمْدُ للّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ

"Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin talikai"

Maganar mu ta farko ita ce godiya ga Allah. Ubangijin da halitta da kuma girmar dukkanin duniya suna hannunsa ne, shin duniya ce ta abubuwa marasa rai da tsirrai ko kuma duniyar dabbobi da kuma duniyar sammai da kassai.

Na'am shi ne ya sanar da kudar zuma wacce irin tsirrai ne za ta ci sannan kuma da yadda za ta samar da zuma din. Haka nan kuma shi ne ya sanar da tururuwa yadda za a ta ajiye da kuma tara abin da za ta ci lokacin bazaar. Shi ne wanda ya ke samar da tsirron alkama daga dan tsirron alkama sannan kuma daga dan kwayar tuffah (apple) ya ke samar da wata bishiyar tuffa din da kuma girmar da ita. Shi din ne dai ya samar da wannan sama da irin girman da yake da shi sannan kuma ya sanya wa duk irin wadannan taurari masu tsananin yawa da ake da su a sama hanyar da za su bi.

Shi ne dai Ubangiji wanda ya samar da mu daga wani wulakantaccen ruwa sannan kuma ya girmar da mu a cikin mahaifiyar mu sannan bayan haihuwar mu kuma ya samar mana da hanyoyin da za mu girma. Haka nan kuma ya samar wa jikin mu wani irin yanayi da zai ba mu kariya daga cututtuka ko kuma idan har wani kashi ya karye to ya samar da hanyar da za a hada shi sannan kuma da yadda zai dinga samar da jinni a duk lokacin da ya ke bukatar jinin.

Haka nan kuma ba wai kawai girmar jikinmu ne yake hannunsa ba, face dai shiryarwa da kuma karfafa ruhi da kwakwalanmu ma suna hannunsa ne. Ya sanya mana hankali da ji a jika sannan kuma ya aiko annabawa da saukakkun littafa don su tarbiyantar damu.

A saboda haka a cikin wannan ayar mun koyi cewa:

Bukatar da mu kuma na sauran halittu mu ke da ita ba wai kawai bukata ce ta haliita ba face dai girmar mu ma tana wajensa ne, sannan kuma alakar sa da halittu, wata alaka ce ta har abada. A saboda haka wajibi ne a ko da yaushe mu zamanto masu gode wa ni'imomin da ya yi mana. Ba wai kawai a duniya ba, hatta a lahira maganar 'yan Aljanna ita ce: "Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin talikai"

Yanzu kuma bari mu je ga aya ta gaba, wato aya ta uku da take cewa:

الرَّحْمـنِ الرَّحِيمِ

"Mai rahama, Mai jin kai".

Ubangijin da muka yi imani da shi, mai nuna tausayi da so da kuma jin kauna da yafuwa ne. Muna iya ganin misalan irin rahama da kaunarsa cikin ni'imomi masu da ya yi mana. Furanni masu kyau da kamshi, 'ya'yan itatuwa masu dadi da zaki, abinci masu dadi da kuma kara lafiya, tufafi masu launuka daban-daban, dukkanin wadannan kyauta ce ta Ubangiji a gare mu.

Shi ne wanda ya sanya kauna da tausayin uwa ga 'ya'yanta a cikin zuciyarta, to amma shi din nan ya fi dukkanin uwaye zama mai rahama da tausayawa a gare mu. Azabtarwar da ya ke yi (wa mutanen da suka saba wa umurninsa) yana yin hakan ne a matsayin jan kunne ga bayinsa masu sabo, ba wai yana yin hakan ne saboda gaba da kuma neman daukan fansa ba. A saboda haka idan har muka tuba sannan kuma muka cike gurbin da muka haifar a baya, to ya kan yafe wadannan kura-kurai da zunuban da muka aikata.

Yanzu kuma bari mu yi dubi cikin irin darussan da suke cikin wannan ayar:

Allah Madaukakin Sarki dai ya kasance yana tarbiyantar da halittu ne tare da rahama da nuna kaunarsa, saboda kuwa kafin zamansa 'Ubangijin talikai' da kuma bayan hakan, sai da ya sanar da kansa a matsayin 'Mai Rahama Mai Jin Kai'. Wato ya kasance ne tsakanin wasu rahamomi guda biyu sannan kuma koyarwa da tarbiya su kan faro ne daga mafarin rahama da yafewa sannan kuma daga karshe ma a sami rahama da kuma yafewarsa. A saboda haka malamai da masu tarbiyan cikin al'umma, matukar dai suna son su sami nasara, to wajibi ne su gudanar da ayyukan su bisa asasi da tushe na kauna da kuma tausayawa.

Yanzu kuma bari mu saurari aya ta 4 ta Suratul Hamd din:

مَالِكِ يَوْمِ الدِّينِ

"Mai mulkin Ranar Sakamako"

A nan Allah Madaukakin Sarki ya bayyana kansa ne a matsayin Mamallakin ranar sakamako.

Kalmar 'Din' tana da ma'anar akida da addini haka nan kuma tana da ma'anar sakamako. Abin nufi da 'Ranar Sakamako' shi ne ranar alkiyama wacce rana ce ta hisabi da gurfana a gaban alkali da kuma ba da sakamako (ko dai lada ko kuma azaba).

Ko da yake wajibi ne a lura da wannan lamari na cewa Allah Madaukakin Sarki har ila yau shi ne mamallakin wannan duniyar da kuma lahira, to amma mallakar (iko) tasa a ranar kiyama tana da wata ma'ana ce ta daban. A wancan ranar babu wani mai iko a kan wani abu in ba Allah ba. dukiya da kudi da 'ya'ya duk babu wani amfani da za su yi, haka nan abokai da masoya ba su da wani karfi. Kai hatta ma mutum ba shi da iko a kan gabobinsa, harshe ba shi da karfin neman afuwa ko kuma kwakwalwa ba ta da damar yin tunani, Allah Madaukakin Sarki ne kawai yake da iko da karfi a wannan ranar.

A saboda haka daga wannan ayar za mu iya koyon cewa:

Na farko a daidai lokaci da muke da fata ga rahamar Ubangiji maras karshe, wadda aka yi bayaninta cikin wannan ayar, har ila yau kuma wajibi ne mu tsoraci hisabi da sakamako na ranar tashin kiyama.

Na biyu kuma shi ne cewa ta hanyar imani da ranar tashin kiyama mu dinga jin cewa lalle ayyukan mu na alheri da muka aikata ba za su tafi haka banza ba tare da wata kyauta daga wajen Ubangiji ba.

Darasi na karshe shi ne cewa Allah Madaukakin Sarki yana da masaniya kan dukkanin ayyuka masu kyau da kuma munana da muke aikatawa sannan kuma yana da karfin gurfanar da mu a gaban da kuma ba mu ladar kyawawa da kuma azabtar da mu kan munanan da muka aikata.

To yanzu kuma sai mu saurari aya ta 5:

إِيَّاكَ نَعْبُدُ وإِيَّاكَ نَسْتَعِينُ

"Kai mu ke bauta wa, kuma Kai muke neman taimakonKa"

A cikin wannan aya muna magana ne da Allah Madaukakin Sarki muna cewa: Ya Ubangiji Allah! Kai kadai mu ke bautawa sannan kuma daga gare ka ne kawai muke bukatar taimako.

A cikin ayoyin da suka gabata, mun fahimci wasu siffofin Ubangiji. Mun san cewa shi 'mai rahama' ne sannan kuma 'mai jin kai' ne, haka nan kuma 'Ubangijin talikai' ne sannan kuma 'mai mulkin ranar sakamako' ne, haka nan kuma saboda irin girman halitta da kuma ni'imominsa marasa karshe da ya yi mana shi ya sa mu keg ode masa muna fadin 'Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai".

Gaskiya dai ita ce mu tafi zuwa ga hallararsa sannan kuma mu bayyanar da rauni da kuma gazawar mu da cewa mu din nan bayinsa ne kawai, sannan kuma ba za mu taba yin karen tsaye wa dokokinsa don biyan bukatun wasu ba. Haka nan mu dai ba za mu zamanto bayin abin duniya ba, kamar yadda kuma ba za mu mika wuya da zama bayin tursasawa da kuma karfi na 'yan mulkin mallaka ba.

To amma da ya ke addinin Musulunci, addini ne na daidaiku da kuma al'ummance sannan kuma salla a matsayin mafi girman alama ta bautar Allah ana gudanar da ita ce a jama'ance. A saboda haka mu musulmi, da murya daya mu ke fadin cewa: "Kai mu ke bauta wa, kuma Kai muke neman taimakonKa".

Wato Ya Ubangiji Allah, ba wai ni kadai ba, dukkanin mu gaba daya bayinka ne. Haka nan kuma Ya Ubangiji Allah hatta bautar da muke maka tana karkashin taimakonka ne, idan har ba ka taimaka mana ba, to za mu zamanto bayin wasu.

Yanzu kuma bari mu yi dubi cikin darussan da muka koya cikin wannan ayar:

Darasi na farko da muka koya a cikin wannan ayar shi ne, duk da cewa mun yarda da dokokin da suke mulki da halittu, to amma hakan lamari ne da ke nuni da irin tanadin da Ubangiji ya yi mana sannan kuma dukkanin su suna karkashin ikon sa ne. A saboda haka ne mu ke mika wuya a gare shi sannan kuma ba za mu zamanto bayin dabi'a ba. A wajen Allah Madaukakin Sarki ne kawai mu ke neman taimako hatta cikin lamurra na duniya.

Wani darasin kuma na daban shi ne cewa idan har muka yi salla cikin kula da kuma komawa ga Allah sannan kuma muna jin cewa mu bayinsa ne kawai, to don haka ba za mu fuskanci matsalar jiji da kai da kuma girman kai ba.

Muna fatan kun ji dadin abin da muka gabatar muku a wannan shirin. Kuma da haka ne muka kawo karshen shirin na mu na yau, sai ku tarbe mu a shiri na gaba don jin ci gaban wannan shirin.

A huta lafiya.

Suratul Hamd; Aya Ta 6-7 (Kashi Na 3)

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai.

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa cikin wani sabon shirin hannunka mai sanda. A shiri guda biyun da suka gabata mun yi dubi ne cikin ayoyi na farko zuwa na biyar na Suratul Hamd, inda Allah Madaukakin Sarki ya bayyanar da kansa a matsayin Ubangiji mai rahama mai jin kai, mamallaki sannan kuma mai tarbiyantar da dukkanin halittu wanda kuma ya ke yin hisabi kan ayyukan mu da ba mu lada cikin wadanda muka kyautata su da kuma yin ukuba kan wanda aka saba. Haka nan kuma mun sanar da cewa gare shi ne kawai za mu mika kai sannan kuma a gare shi kawai muka dogara.

Da 'yar wannan gabatarwa ce za mu shiga cikin aya ta 6 ta wannan surar, don haka sai ku biyo mu sannu a hankali.

Aya ta 6 din tana cewa:

اهدِنَــــا الصِّرَاطَ المُستَقِيمَ

"Ka shiryar da mu ga hanya madaidaiciya".

Mun daga hannayenmu sama zuwa ga Allah Madaukakin Sarki sannan muna addu'a da cewa: Ya Allah ka shiryar da mu zuwa ga hanya madaidaiciya.

Akwai hanyoyi daban-daban cikin rayuwar mutum. Hanyar da shi kansa mutum ya samar wa kansa bisa bukatar da ya ke da ita, hanyar da mutane da al'umma suke tafiya a kanta, hanyar da iyaye da magabatanmu suka tsara rayuwarsu bisa kanta, hanyar da dawagitai da sauran azzaluman shugabanni suka tsara wa mutane, hanyar samun jin dadi na duniya ko kuma hanyar kaucewa gefe da nesantar ayyuka na zamantakewa.

To shin a gaban dukkanin irin wadannan hanyoyi daban-daban ashe mutum ba ya bukatar wani mai shiryarwa? Allah Madaukakin Sarki ya aiko annabawa da saukakkun littafa don shiryar da mutum ne , sannan kuma za mu sami wannan shiriyar ce a lokacin da muka zamanto masu bin tafarkin gaskiya ta annabi da tsarkakan Ahlulbaitinsa da kuma Alkur'ani mai girma.

A saboda wannan dalilin ne a kowace sallar da za mu yi mu ke bukatar Allah da ya shiryar da mu zuwa ga madaidaiciyar hanyarsa. Hanyar da a cikinta babu kauce wa hanya sannan kuma mutum zai sami damar isa gare shi.

Hanya madaidaiciya ita ce hanya ta tsaka-tsaki, madaidaiciyar hanya ita ce hanyar daidaito da tsaka-tsaki cikin dukkanin lamurra ba tare da wuce gona da iri ko kuma nuna gazawa ba. Wasu mutane su kan fuskanci matsalar kauce wa hanya a lokacin da suke neman tushe na akida, wasu kuma a cikin aiki da dabi'u ne, wasu kuma suna jingina dukkan komai ne ga Allah Madaukakin Sarki, kai ka ce tamkar shi mutum ba shi da wani zabi na kansa wajen zaban makomarsa, wasu kuma suna ganin kansu ne a matsayin masu iko cikin dukkanin komai, kai ka ce babu ruwan Allah da kuma hannunsa cikin dukkanin ayyuka.

Wasu daga cikin kafirai suna bayyana annabawan Ubangiji tamkar sauran mutane kai a wani lokaci ma kasa da sauran mutane ko kuma ma a matsayin mahaukata, wasu daga cikin wadanda suka yi imani da wadannan annabawan kuma sun kai matsayin da suna ganin wasu annabawan a matsayin misali annabi Isa a matsayin Ubangiji. Irin wadannan tunani da halaye, wata alama ce da take nuni da kaucewa daga madaidaiciyar hanya wadanda annabi da Ahlulbaitinsa su ne abin koyi na aikace na wannan hanya.

Haka nan kuma Alkur'ani mai girma yana kiran mu zuwa ga riko da tsaka-tsaki cikin lamurra na ibada, tattalin arziki da zamantakewa wanda yanzu bari mu yi dubi cikin wasu daga cikin misalan hakan:

A cikin aya ta 31 ta Suratul A'arafi Allah yana fadin cewa:

"ku ci kuma ku sha: kuma kada ku yi barna".

Haka nan a cikin aya ta 110 ta cikin Suratul Isra ya zo cewa:

"Kuma kada ka bayyana ga sallarka, kuma kada ka boye ta. Ka nemi hanya a tsakanin wancan", wato a cikin wannan aya Allah Madaukakin Sarki yana fadin cewa a lokacin da kake salla kada ka daga muryarka sosai wajen karatu haka nan kuma kada ta sassauto da ita, ka zabi hanya matsakaiciya.

Haka nan kuma a cikin aya ta 67 ta cikin Suratul Furkan, muna karanta cewa:

"Kuma wadanda suke, idan sun ciyar, ba su yin barna, kuma ba su yin kwauro, kumar (ciyarwarsu) sai ta kasance a tsakanin wancan da tsakaitawa".

Wato su muminai a lokacin da suke ciyarwa ba sa yin almubazzaranci sannan kuma ba sa yin rowa, face dai suna dauka matsakaiciyar hanya ce. Duk kuwa da cewa Musulunci ya yi ishara da kuma jaddadawa dangane da batun kayutatawa iyaye inda ya ke cewa "Kuma ga iyaye ku kyautata musu", to amma a bangare guda kuma yana cewa "kada ku yi musu biyayya", wato idan har suka kiyaye ku zuwa ga bata, to kada ku yi musu biyayya.

Alkur'ani mai girma dangane da mutanen da ibada kawai suka sa a gaba sannan suka koma gefe ko kuma mutanen da suke ganin yin hidima wa mutane a matsayin ibada sannan kuma suke gabatar da lamarin salla da zakka a tsakaninsu yana fadin cewa: "Ku tsayar da salla sannan kuma ku ba da zakka" wanda daya daga cikin su alaka ce da mahalicci dayan kuma alaka ce tsakaninsu da mutane..

Muminai na hakika su ne mutanen da suke da yanayi na korewa da kuma yanayi na jan hankulan mutane zuwa gare su. A cikin aya ta karshe ta Suratul Fath Allah Madaukakin Sarki yana fadin cewa: "Muhammadu Manzon Allah ne. Kuma wadannan da ke tare da shi masu tsanani ne a kan kafirai, masu rahama ne a tsakaninsu"

Amma dangane da darussan da za mu iya dauka cikin aya ta 6 kuwa, akwai cewa hanyar sa'ada ita ce hanya madaidaiciya saboda:

- Hanya madaidaiciya a tabbata ce take sabanin hanyoyi na bil'adama wadanda a kowace rana suke sauyawa. - A bangare guda kuma mafi gajartar tazara da take tsakanin hanyoyi biyu ita ce madaidaiciyar hanya wacce hanya guda ce wacce kuma babu wani kauce wa hanya a tattare da ita sannan kuma cikin sauki mutum zai iya isa ga wajen da yake son isa gare shi.

Wani sako na gaba shi ne cewa wajibi ne a nemi taimakon Allah wajen zaban wannan hanya da kuma ci gaba da zama a kan wannan hanyar. Don kuwa a koda yaushe mun kasance muna fuskantar matsayar kura-kurai da kuma bacewa daga hanya, bai kamata mu yi zaton cewa tun da ya zuwa yanzu ba su fuskanci wata matsala ta kauce wa hanya da kuma faduwa kasa ba a kan hanyar da muke tafiya, mu yi zaton cewa za mu ci gaba da zama a kan wannan hanyar ba tare da wata matsala ba. Don kuwa akwai mutane masu yawan gaske da suka gudanar da rayuwarsu a bisa tafarkin imani, to amma daga lokacin da suka sami kudi ko kuma suka sami wani mukami, nan take su ke mantawa da Allah.

Bisa la'akari da cewa fahimtar madaidaiciyar hanya wani aiki ne mai wahalar gaske, don haka aya ta gaba take karantar da mu abin da za mu rika a wannan tafarki da kuma sanar da mu wadanda suka kauce wa wannan hanyar. Wannan ayar tana fadin cewa:

Aya ta bakwai:

صِرَاطَ الَّذِينَ أَنعَمتَ عَلَيهِمْ غَيرِ المَغضُوبِ عَلَيهِمْ وَلاَ الضَّالِّينَ

"Hanyar wadanda Ka yi wa ni'ima, ba wadanda aka yi wa fushi ba, kuma ba batattu ba".

Wannan aya mai girma tana fadin cewa ne: Ya Ubangiji Allah, ka shiryar da mu hanyar mutanen da ka sanya su cikin ni'imarka, ba hanyar mutanen da ka yi fushi da su ko kuma wadanda suka kauce wa hanya ba.

Mutane sun kasu kashi uku wajen zabar hanyar da za su gudanar da rayuwarsu. Bangaren farko su ne mutanen da suke zaban tafarkin Allah sannan kuma suna tsara rayuwarsu ta daidaiku da ta jama'a gwargwadon koyarwar da Allah Madaukakin Sarki ya gabatar da ita cikin Littafinsa. Wadannan mutane a ko da yaushe sun kasance ciikin ni'ima da rahama ta musamman ta Ubangiji.

Bangare na biyu na mutanen su ne kishiyar na farko, su ne mutanen da duk da cewa sun fahimci gaskiya to amma duk da haka sun yi watsi da Allah, inda suka kama hanya wasun Allah, sannan kuma suka fifita soyace-soyacen zukatansu da na abokai da dangin su bisa abin da Allah Madaukakin Sarki ya ke so.

Wannan gungun na mutane ayyuka da dabi'unsu a hankali a hankali sukan bayyana musu sannan kuma a sannu-sannu sai su kauce daga 'madaidaiciyar hanya', sannan kuma maimakon su kama hanyar Ubangiji sannan kuma su sami tausayawarsa ta musamman, sai su kama hanyar hasara da rugujewa sannan kuma su zamanto cikin fushin Allah Madaukakin Sarki. Wadannan mutane su ne wannan ayar ta kira su da sunan 'wadanda aka yi fushi da su".

Akwai kuma kungiya ta uku wadanda ba su da wata takamammiyar hanya, suna cikin damuwa da rudu kamar yadda wannan aya ta kira su, su ne batattu wadanda suka rasa hanya.

A kowace salla muna karanta cewa:

"Ka shiryar da mu ga hanya madaidaiciya. Hanyar wadanda Ka yi wa ni'ima, ba wadanda aka yi wa fushi ba, kuma ba batattu ba".

Wato Ya Allah ka shiryar da mu hanyar gaskiya, hanyar da annabawa da waliyai da tsarkakan mutane suke kai, wadanda a ko da yaushe suke cikin tausayawa ta musamman ta Ubangiji. Sannan kuma ka nesantar da mu daga hanyar mutanen da suka yi nisa da 'yan'adamtaka wadanda suke cikin fushinka, haka nan kuma daga hanyar mutane da suka bace wa hanya.

To a nan dai wata tambaya ta kan taso cewa: Su wane ne wadannan mutanen da aka yi fushi da su din wadanda kuma suka kauce wa hanya?

A yayin amsa wannan tambaya wajibi ne mu bayyana cewar, a cikin Alkur'ani mai girma akwai wadansu mutane da kuma kungiyoyi na mutane da yawa da aka bayyana su a matsayin wadanda suka cancanci wannan siffar. A nan bari mu kawo wani fitaccen misali guda:

A cikin Alkur'ani an yi bayanin kissar Bani Isra'ila da yadda rayuwarsu ta kasance karkashin mulkin Fir'auna da yadda Annabi Musa ya 'yanto su daga hannun Fir'aunan. A wani lokaci sun kasance karkashin tausayawa ta Ubangiji sakamakon aiki da suka yi da koyarwar Ubangiji sannan kuma Allah ya fifita su a kan mutanen da suke zaluntarsu, kamar yadda ya zo cikin aya ta 47 ta cikin Suratul Bakara inda Allah Madaukakin Sarki yake cewa: "kuma lalle ne Ni, Na fifita ku a kan talikai", wato na daukaka ku a kan sauran mutane.

To amma wadannan kabilar Bani Isra'ilan dai, sakamakon munanan ayyukansu sai suka fada cikin fushin Ubangiji, wanda Alkur'ani ya ke fadin cewa: "Kuma suka koma da wani fushi daga Allah" saboda "suna gurbata kalmomi", malaman yahudawa suna gurbata dokokin Allah da suka zo cikin Attaura. 'Da kuma cin riba da suke yi" 'yan kasuwansu da masu kudin su suna cin riba da kuma gudanar da kasuwancin da aka haramta.

Mutane dai sun saba da son jin dadi da hutawa sannan kuma ba a shirye suke su kare koyarwa masu tsarki da suke da su ba, don haka ne ma suka gaya wa annabi Musa cewa: "Ka tafi kai da Ubangijinka, ka yi yaki, mu dai muna zaune a nan", wato ka tafi kai ga Ubangijinka ku yi yaki, mu dai ba mu da shirin yin yaki.

Mutanen kirki na cikin al'ummar ma sun yi shiru dangane da wannan kauce wa hanyar, ba su yi wani abu na fada ko kuma nuna damuwa da hakan ba. Daga karshe dai sai suka fado kasa warwas daga wannan matsayi na koli na daukaka zuwa ga kaskanci da wulakanci.

Yanzu kuma bari mu yi dubi cikin darussan da suke cikin aya ta karshe da Suratul Hamd:

A wajen zaban madaidaiciyar hanya, muna da bukatar sanin abin da ya kamata ya rika a matsayin abin koyi wanda Allah Madaukakin Sarki ya yi bayaninsu cikin aya ta 69 ta Suratun Nisa inda ya ke cewa (su ne): annabawa da siddikai da shahidai da salihai wadanda suke da ni'imarsa ta musamman.

Wani darasin kuma na daban shi ne cewa duk wani abin da ya zo daga wajen Allah zuwa ga mutum ni'ima ce, amma fushi da kuma azabar Allah tana samun mu ne sakamakon munanan ayyukanmu. A saboda haka ne ayar da ta yi magana dangane da ni'imar Ubangiji take cewa: "Ka yi wa ni'ima", amma dangane da batun fushi kuwa ba a ci 'ka yi fushi ba'.

To da haka ne dai muka kawo karshen shirin na mu na yau da fatan mun amfana. Sai kuma a tarbe mu a shiri na gaba. Kafin nan ku huta lafiya, wassalamu alaikum wa rahamatullah wa barakatuhu.