1
- Godiya ta tabbata ga ALLAH wanda ya saukar da littafi a kan bawanSa kuma bai sanya karkata ba a gare shi.
- Madaidaicin (littafi) domin Ya yi gargadi game da azaba mai radadi daga wurinSa, kuma Ya yi bishara ga muminai wadanda suke aikata ayyuka na qwarai, da cewa suna da lada mai karimci.
- Suna masu zama a cikinta na har abada.
- Kuma Ya yi gargadi ga wadanda suka ce, “ALLAH Ya haifi da!”
- Ba su da wani ilmi game da wannan furcin, kuma iyayensu ba su da shi. Abin da ke fita daga bakinsu yin sabo ne! Abin da suke furtawa babban qarya ne.
- Za ka kusan ka zargi kanka dangane da gurabbansu na wannan hadisin, da bijirewa da shi; za ka kusan baqin ciki.
- Mun qawaita kome a qasa, domin mu jarrabe su, sa’annan ya bambanta a cikinsu wadanda suke ayyuka na qwarai.
- Kuma lalle ne, za mu shafe kome da ke kanta, ta rage cikakken bakarare.
- To, mene ne kuwa ka ke tsamanin abin da yasa muke gaya maka game da as’hab el kahf, da lambobin da ke alaqa da su? Suna cikin mu’ijizanMu na ban mamaki.
- Sa’ad da samarin suka yi hijira a cikin ‘kahf’ (kogo), sai suka ce, “Ubangijinmu, ka bamu rahamah daga gare Ka, kuma Ka sa mana albarkacinKa a kan al’amarinmu da shiriyarKa.”
- Sai muka rufe kunnuwarsu a cikin kogo na qudirin lambobin shekaru.
- Sa’annan muka tayar da su, domin mu ga kowane dayan gungiyoyin biyu zai iya lissafin adadin lokacin da suka tsaya a wurin.
- Mu ne ke baka wannan labarin, da gaskiya. Lalle ne, su wasu samari ne wanda suka yi imani da Ubangijinsu, kuma muka qara masu shiriya.
- Kuma muka qarfafa masu zukatansu sa’ad da suka yi tsayin daka suka ce: “Ubangijinmu kadai Shi ne Ubangijin sammai da qasa. Ba za mu bautawa wani baicinSa ba. Idan muka yi haka, za mu bata.
- Ga mutanenmu suna sanya wasu abin bautawa baicinSa. Idan da ma za su bada wani hujja bayyananna a kan dalilin abin da suke bautawa! To, wane ne mafi zalunci da wanda ya qaga qarya ya dangana su ga ALLAH?
- “Tun da kuna nufin ku nisance su, su da abin da suke bautawa baicin ALLAH,* bari mu fake a cikin kogo. Ubangijinku Ya sanya maku rahamarSa kuma Ya nuna maku madaidaicin shawararku.”
- Kuma (da kuna wurin) za ku ga rana idan ta fito tana karkata daga kogonsu ta hannun dama, kuma idan ta fadi, tana haska masu daga hagu, da suke ta yin barcinsu a fili. Wannan abu yana daya daga cikin mu’ijizan ALLAH. Wanda ALLAH Ya shiriyar shi ne shiriyayyen gaskiya, kuma wanda Ya batar, to, ba za ka samar masa wani majibinci mai shiryarwa ba.
- Kuma (da kun kasance wurin) za ku zaton su farkakku ne, alhali kuwa su masu barci ne. muna juya su zuwa dama da ta hagu, kuma karensu yana miqan qafafuwansa a tsakaninsu. Da kun kallesu, da za ku sheqa a guje daga gare su, saboda tsoro.
2
[18:19] Kuma ta haka ne muka tayar da su, domin su tambayi junansu,
“Wani mai magana daga cikinsu ya ce, “Tun yaushe ne kuke nan?” Suka ce,
“Muna nan na yini daya ko sahen yini,” suka amsa. “Ubangijinku ne mafi
sani ga tun yaushe muke nan, to, bari mu aiki dayanku da wannan azurfarku
zuwa cikin gari. Bari ya je ya nemo mana mafi tsakin abin dafawa, ya saya
mana. Amma sai ya yi a hankali, kada ya ja hankali game da ku ga wani.
[18:20] “Idan suka kama ku, za su jefe ku, ko kuwa su tilasta ku, domin ku
koma zuwa addininsu, sa’annan ba za ku ci nasara ba.”
Alaqa Da Qarshen Duniya*
[18:21] Sai muka yi sanadin a gano su, domin mu bari kowa ya san cewa
wa’adin ALLAH gaskiya ne, kuma mu cire shakka game da qarshen duniya.*
Sa’annan mutane suka yi jayayya a tsakanin junansu game da su. Wadansu
suka ce, “Bari mu yi gini a wurinsu.” Ubangijinsu ne mafi sani game da su.
Wadanda suka rinjaya suka ce, “Za mu gina masallaci wurinsu.”
*18:21 Kamar yadda dalla dallan bayani yake a cikin shafi 25, wannan
tarihin ya taimaka wurin gano bakin alura dangane da qarshen duniya.
[18:22] Wadansu za su ce, “Da su uku ne; karensu ne na hudunsu,” alhali
kuwa wasu za su ce su, “Biyar ne; karensu ne na shida,” da suke ta cinci.
Wadansu suna cewa, “Bakwai ne, da na takwas dinsu karensu. Ka ce,
“Ubangijina ne mafi sani adadin lambarsu.” Kadan ne kawai suka san adadin
lambarsu daidai. Saboda haka, kada ka yi jayayya da su; ku yarda da su
kawai. Kuma kada ka yi fatawa ga kowa game da wannan.
Ambatar Allah
A Kowane Daman Da Muka Samu
[18:23] Kada ka ce za ka aikata wani abu nan gaba,
[18:24] ba tare da ka ce, “Insha ALLAH.” Idan ka manta baka ce hakan ba,
sai ka tuna Ubangijinka nan da nan kuma ka ce, “Ubangijina Ya shiriyar da
ni domin in gyara wani sa’a.”
*18:24 Wannan muhimmiyar umurni ce da ke bamu daman tunawa da Allah
ala kullu yaumin.
[18:25] Sun tsaya a cikin kogonsu shekaru dari uku, aka qara da tara.*
*18:25 Bambancin shekaru 300 qidayan watan rana, da shekaru 300 na
watan muhammadiya, shekaru tara ne. ta haka ne, madaukakin sarki Ya
qaddara gano qarshen duniya ya faru a cikin AD 1980 (1400 AH), shekaru
300 (309 shekarun watan muhamamdiya) gabanin qarshen duniya (dubi
72:27 da shafi 25).
[18:26] Ka ce, “ALLAH ne mafi sanin adadin lokutan da suka tsaya a
wurin.” Shi ne da sanin gaibun sammai da qasa. Da izininSa za ka iya gani;
da izininSa za ka iya ji. Babu wani majibinci baicinSa, kuma ba Ya tarayya
da kowa a cikin hukuncinSa.
[18:27] Ka karanta abin da aka yi wahayi zuwa gare ka na littafin
Ubangijinka. Babu wani abu mai kau da kalmominSa, kuma ba za ka sami
wata madogara ba baicin shi.
Karatun Alqurani Tare
[18:28] Ka yi haqurin tilasta kanka da zama tare da wadanda ke kiran
Ubangijinsu safe da maraice, suna neman yardanSa. Kuma kada idanunka
su juya ga barinsu, kana neman wuqiniyan rayuwar duniya. Kumar kada ka
bi wanda muka shagaltar da zuciyarsa daga hukuncinMu; wanda yake bin
son zuciyarsa, kuma wanda ya rikitad da al’amarinsa.
Cikakken ‘Yanci Ga Addini
[18:29] Ka zayyana: “Wannan shi ne gaskiya daga Ubangijinku,” saboda
haka wanda ya so, to, ya yi imani, kuma wanda ya so, to, ya kafirta. Mun
shirya wa azzalumai wuta, wanda shamakunta zai kewaye su. Idan suka yi
kukan neman taimako, za ba su wani abu na ruwa-ruwa, kamar dabzar mai
na acid mai qona fuskoki. Tir da abin shansu na zullumi! Kuma tir da
makoman zullumi!
[18:30] Amma ga wadanda suka yi imani kuma suka aikata ayyuka na
qwarai, ba rasa baiwa lada ga wadanda suka kyautata ayyukan qwarai.
[18:31] Wadannan sun cancanci gidajen Aljannah wurin da qoramu suke
gudana daga qarqashinsu. Za qawaita masu a wurin da suluwan zinariya,
kuma za su sa tufafin siliki da karammiski masu ruwan kore, kuma za su
huta a kan karagu suna holewa. Sambarika da sakamakonsu; kuma
sambarika da qasaitacen wurin mahuta!
Muhalli A Matsayin Abin Shirka
[18:32] Kuma ka buga masu misali da wasu mutane biyu: mun baiwa
dayansu gonaki biyu na inabobi, kuma muka kewaye su da itacen dabinai,
kuma muka sanya wasu shuke-shuke a tsakanin gonakin.
*18:32-42 Alqurani ya buga misalai da dama na abubuwan shirka dabam
dabam wanda mutane suke bauta baicin Allah; wanda suka hada da yara
[7:190], shugabanin addinai da shehunai [9:31], muhalli [18:42], matattun
waliyai da annabawa [16:20-21, 35:14, da 46:5-6], da kuma son kai
[25:43, 45:23].
[18:33] Kowace gona daga biyun, ta bayar da amfaninta a cikin lokaci, da
kariminci, saboda mun sanya qorami ta gudana a tsakaninsu.
[18:34] Wata rana, bayan girbi, ya yi alfaharin gayawa abokinsa cewa: “Ni
ne mafificin wadata a kanka, kuma ni ne mafi mutunci daga wurin mutane.”
[18:35] Kuma sa’ad da ya shiga gonansa, sai ya zalunci kansa da cewa, “Ba
ni zaton wannan zai taba qarewa ba.
[18:36] Kumar ba ni zaton sa’a (Alqiyamah) mai tsayuwa ce. Kuma ko da an
mayar da ni ne ga Ubangijina, zan ( koma samun dabara) in mallaki abin da
ya dara wannan a can.”
[18:37] Abokinsa ya ce masa, sa’ad da yake muhawara da shi, “Shin ka
kafirta ne ga wanda Ya halitta ka daga turbaya, sa’annan daga digon maniyi,
sa’annan Ya daidaita ka, ka zama mutum?
[18:38] “Ni kam, ALLAH ne Ubangijina, kuma ba zan yi shirka da kowane
abu ba da Ubangijina.
Muhimmin Umurni
[18:39] “Sa’ad da ka shiga gonarka, da ya kamata ka ce, Ma Sha ALLAH. La
Quwwata Illa Bi’ALLAH. Za ka ga cewa ni ba ni da dukiya da yara kamar ka.
[18:40] To, amma Ubangijina zai iya ya bani gona fiye da naka. Kuma zai
iya ya aika da goguwar iskan hadari daga sama wanda za ta shafe gonarka,
ta bar shi bakarare.
[18:41] “Ko kuma, ruwanta ta nutsad da zurufi, inda ba za ka iya kaiwa ba.”
[18:42] Kuma haka ne, an shafe gonarsa, sai ya yai gari yana nadama, yana
koke saboda abin da ya kashe a banza a cikinta, sa’ad da aka bari gonansa
bakarare. Daga qarshe sai ya ce, “Kaitona, da ma ban yi shirkanta gona na
da Ubangijina ba.”
[18:43] kuma da babu wani mai tallafa masa ga ALLAH, kuma ba wanda ya
iya ya basi wani taimako.
[18:44] Dalili shi ne taimakon gaskiya da jibinta daga ALLAH yake; Yana ba
da mafificin lada, kuma da mafificin aqiba.
[18:45] Ka buga masu misalin rayuwar duniya, kamar ruwa ne wanda muka
sakar daga sama domin ya fito da tsiro a qasa, sa’annan suka koma baro
wanda tafi da hurin iska. Kuma ALLAH Ya kasance mai yawan ikon yi a kan
dukan kome.
Yin Gyara Ga Al’amrarmu
[18:46] Kudi da yara su ne qawar rayuwar duniya, amma ayyuka na qwarai
sun fi zama alheri daga Ubangijinka ga lada, kuma mafi alheri ga buri.
[18:47] Akwai ranar da za mu shafe tsaunika, kuma za ku ga qasa
bakarareya. Sa,annan mu tara su duka, ba za mu bar ko dayansu ba.
[18:48] Za gufanad da su a gaban Ubangijinka a cikin sahu guda. Kun zo
mana yasu-yasunku, kamar yadda muka halicce ku farkon lokaci. Lalle ne,
da abin da kuka riya cewan ba zai taba faruwa ba kenan.
[18:49] Za gabatar da littafin ayyuka, kuma za ka ga mai laifi yana fargaban
abin da ya qumsa. Za su ce, “Kaitonmu. Yahya aka yi wannan littafin bai bar
kome ba, qarami ko babba, ba tare da ya qidaya shi ba?” Za su tarad da
kome da suka aikata an gabatar da shi. Ubangijinka ba ya zaluntar kowa.
Nau’in Halittan Allah
[18:50] Sa’ad da muka ce wa mala’iku, “Ku yi sujadah ga Adam.” Sai suka
yi sujadah, ban da Iblis. Sai ya kasance aljanni, saboda ya finjire bin
umurnin Ubangijinsa.* To, shin, za ku zabe shi, shi da zuriyarsa a matsayin
majibinta baicin Ni, duk da cewan su maqiyanku ne? Wannan shi ne musaya
da azzalumai na zullumi!
*18:50 A lokacin da aka yi tarna mai girma a cikin duniyar sama [38:69], an
yi nau’in dukan halittu cikin mala’iku, aljannu da mutane (shafi ta 7).
[18:51] Ban bari su shaida game da halittar sammai da qasa ba, ko kuma
halittar kansu. Kuma bana bari mugu ya yi aiki a cikin masarautaNa.
*18:51 Allah ne mafi sani Iblis da masu taya shi aiki, watau aljannu da
mutane, cewa za su yanke shawarin da bai dace ba. Dalili kenan da ya sa
aka kange su daga shaidan dabarun halitta.
[18:52] Akwai ranar da zai ce, “Ku kira abokan tarayyaTa, wanda kuke riya
su ne baicin Ni,” za su kira su, amma ba za su amsa masu ba. Shamakin
‘maubiqa’ zai rabe su daga junansu.
[18:53] Masu laifi za su ga wuta, kuma za su tabbatar cewa za su fada ne a
cikinta. Ba za su sami kubucewa ba daga gare ta.
Kafirai Sun Qi Su Amince
Da Cikan Alqurani
[18:54] Mun bada kowane irin misali a cikin wannan Alqurani ga mutane,
amma mutum ya kasance halitta mafi yawan jayayya.
[18:55] Babu abin da ya hana mutum daga yin imani, sa’ad da shiriya ya je
masu, kuma daga neman gafara daga Ubangijinsu, sai dai cewa sun nemi su
ga (irin mu’ijizai) kamar na mutanen da, ko kuwa su ga azaba tukuna.
18:56] Mu kan aika da manzanni ne kawai domin su ba da bushara, kuma
da gargadi. Wadanda suka kafirta suna jayayya da qarya daomin su kayar
da gaskiya, kuma suna daukan ayoyiNa da gargadiNa a banza.
Aikin Matsakancin Ikon Alllah
[18:57] Wane ne mafi zalunci da wanda aka tunatar game da ayoyin
Ubangijinsa, sai ya bijire da barinsu, ba tare da sanin abin da suke yi ba.
Saboda haka, muka sanya abubuwan rufi a kan zukatansu domin kada su
fahimce shi (Alqur’ani), kuma a cikin kunnuwansu. Ta haka ne, duk kome da
za ka yi, ka shiriyad da su, ba za su shiryu ba, har abada.
[18:58] Duk da haka, Ubangijinka mai gafara ne, mai yawan rahamah. Idan
da zai kama su saboda abin da suka aikata, da ya shafe su nan da nan.
Amma a maimakon haka, sai Ya jinkirta masu sai qayyadadden lokaci, sa’an
da aka qaddarta; sa’annan ba za su kubuta ba.
[18:59] Alqaryu masu yawa wanda muka halaka saboda zaluncinsu, sai da
muka sanya qayyadadden lokaci na halaka su.
Darussa Masu Amfani Daga Musa Da Malaminsa
[18:60] A lokacin da Musa ya ce wa bawansa, “Ba zan huta ba sai na isa
wurin da rafi biyu suka game, kome nisan shi.”
[18:61] A lokacin da suka kai dam da wurin da magamar tsakaninsu, sai
suka manta da kifinsu, sai ta kama hanyan komawa zuwa rafi, a labe.
18:62] A lokacin da suka wuce wurin, sai ya ce wa bawansa, “Ka kawo mana
kalacinmu. Tafiyar nan ta gajiyar da mu matuqa.”
[18:63] Ya ce, “Ka tuna sa’ad da muka zauna kusa da wani dutse bayan
can? Ban ba da hankali ga kifin ba. Iblis ne ya sa na manta da ita, sai ta
kama hanyanta komawa zuwa ruwa, ta garibi.”
[18:64] (Musa) ya ce, “To, daidan wurin da muke nema kenan.” Sai suka
koma bin sawun qafansu baya.
[18:65] Sai suka sami daya daga bayinMu, wanda muka bashi wata
rahamah daga wurinMu, kuma muka koya masa wani ilmi daga wurinMu.
[18:66] Musa ya ce masa, “Ko in bi ka, domin ka koya mani daga abin da
aka koya maka na shiriya?”
[18:67] Ya ce, “Ba za ka iya yin juriya tare da ni ba.”
[18:68] Ta yaya za ka iya juriya ga abin da baka sani ba?”
[18:69] Ya ce, “Insha ALLAH, za ka ga cewa ni mai haquri ne. Ba zan qi bin
umurnin da ka yi mani ba.”
[18:70] Ya ce, “Idan ka bi ni, to, kada ka tambaye ni game da kome, sai
idan na ga daman in gaya maka game da shi.”
[18:71] Sai suka tafi. A lokacin da suka hau cikin girgi, sai ya huda ta. Ya
ce, “Ka huda ta ne domin ta nutsar da mutanenta? Lalle, ka aikata
mumunan abu.”
[18:72] Ya ce, “Ashe, ban ce ba za ka iya juriya tare da ni ba?”
[18:73] Ya ce, “Ka yi haquri. Kada ka hukunta ni bisa ga mantuwana; kuma
kada ka kallafa mini tsanani ga al’amarina.”
[18:74] Sai suka tafi. Da suka hadu da yaro qarami, sai ya kashe shi. Ya ce,
“Don me ka kashe irin wannan mutum mara laifi? Lalle, ka aikata qazamin
aiki.”
[18:75] Ya ce, “Ashe ban gaya maka ba cewa ba za ka iya juriya tare da ni
ba?”
[18:76] Ya ce, “Idan na sake tambayar ka wani abu kuma, to, kada ka bar
ni tare da kai. Ka ga yawan uzuri daga gare ni.”
[18:77] Sai suka tafi. Har da suka kai ga mutanen wata alqarya, suka nemi
mtanenta da su basu abinci, sai suka qi su yi masu liyafa. Jim kadan, sai
suka ga wani bango a cikinta ta kusan ta fadi, sai ya gyara ta. Ya ce, “Ai da
ka nemi su biya ka ujiri a kansa!”
Kome Yana da Dalilinsa.
[18:78] Ya ce, “Yanzu ya wajabta mu rabu. Amma zan byyana maka kome
da baka iya yin juriya ba a kansa.
[18:79] Amma bisa ga girgin, ta kasance na wadansu matalauta ne masu
kamun kifi, kuma na so in aibanta ta. Saboda akwai wani sarki a gaba zuwa
gare su, wanda yana qwatar kowane girgi, da qarfi.
[18:80] “Kuma yaron, iyayensa muminai ne na qwarai, kuma mun ga cewa
zai kallafa masu da bijirewa da kafirci.*
*18:80 Adolf Hitler da can kyakkyawa ne kuma ana ganin shi mara laifi. Da
ya mutu yana yaro, da mutane masu yawa sun yi baqin ciki, kuma da wasu
masu yawa ma sun jahilci hikimar Allah. An sanar da mu daga wadannan
darussa da cewa kome da ya faru yana da dalilinsa
[18:81] “Sai muka yi nufin cewa Ubangijinsu, Ya musanya masu wani da
mafi alheri da shi; wanda ya fi kirki da tausayi.
[18:82] Amma dangane da banon, ya kasance na wadansu yara biyu ne,
marayu a cikin birnin. Qarqashinta, akwai dukiya wanda na su ne. kuma
babansu ya kasance salihin mutum ne, saboda haka Ubangijinka Ya nufe su,
su yi girma kuma su kai ga iyakn qarfinsu, sa’annan, su cire dukiyarsu.
Saboda wannan rahamah ne daga Ubangijinka. Ban aikata kowanensu bisa
son ra’ayin kaina ba. To, bayanin abin da baka iya ka haqura a kansa ba
kenan.”
Wani Mai Qaho Biyu Ko Kuma Mai Zamani Biyu
[18:83] Kuma suna tambayar ka game da Zul-Qarnain. Ka ce, “Zan karanta
maku wasu labarunsa.”
[18:84] Lalle ne, Mun ba shi mulki a cikin qasa, kuma muka ba shi hanyoyin
abubuwa dabam dabam.
[18:85] Sa’annan, ya bi hanya guda.
[18:86] Sa’ad da ya kai nesa da yamma, sai ya ga rana na fadiwa a cikin
qaton teku, kuma ya sami mutane daga wurin. Muka ce, “Ya Zul-Qqrnain,
(ka yi mulki yadda kake so); imma za ka azabtar, ko ka kyautata zuwa gare
su.”
[18:87] Ya ce, “Bisa ga wadanda suke zalunci, za mu azabta su, sa’annan,
idan suka koma ga Ubangijinsu, sai kuma Ya qara masu azaba mai muni.
[18:88] “Amma ga wadanda suka yi imani kuma suka aikata ayyuka na
qwarai, suna samun kyakkyawan lada; za mu kyautata masu.”
[18:89] Sa’annan kuma ya bi wani hanya.
[18:90] Sa’ad da ya kai nesa da gabas, ya ga inda rana ke fitowa a kan
mutane wanda ba su da abin da za su tsare kansu daga ita.
[18:91] Tun asali, mu ne mafi sani ga kome da ya gani.
[18:92] Sa’annan ya bi wani hanya.
[18:93] Sa’ad da ya kai ga kwari tsakanin kawarai, sai ya tarad da mutanen
da daqyar ake fahimtar yarensu.
Ya’juj Da Ma’juj*
[18:94] Suka ce, “Ya Zul-Qarnain, lalle ne, Ya’juj da Ma’juj masu barna ne a
cikin qasa. To, ko mu biya ka domin ka sanya shingen danni tsakaninmu da
su?”
*18:94-98 Daya daga cikin ayyukan manzon Allah na Wa’adi shi ne ya
ayyane cewa Ya’ajuja da Ma’ajuja, alamar qarshe kafin qarshen duniya, za
su sake fitowa cikin shekara 2270 AD (1700 AH), ya rage shekaru 10 kawai
kafin qarshe. A lura cewa Ya’ajuja da Ma’ajuja sun auku a cikin Surah 18 da
21, watau ayoyi 17 daidai kafin qarshen kowane surah, a madadin shekarun
qirgan watan Muhammadiya (dubi 72:27 da shafi 25).
[18:95] Ya ce, “Ubangijina Ya mallaka mini karimci mai yawa. Idan kuka
bani hadin kai, zan gina datsiya tsakaninku da su.
[18:96] “Ku kawo mini qarafuna masu yawa.” Sa’alin da ya cike gurbin
tsakanin kawaran biyu, ya ce, “Ku hura.” Da ya yi jan zafi, ya ce, “Ku taya ni
kwarara kwalta a kansa.”
[18:97] Ta haka ne, ba za su iya hawanta ba, kuma ba za su iya huda
ramuka a cikinta ba.
[18:98] Ya ce, “Wannan wata rahamah ce daga Ubangijina. Sai idan wa’adin
Ubangijina ya zo, zai sa datsiyan ta marmashe. Kuma wa’adin Ubangijina
gaskiya ne.”
[18:99] A lokacin ne, za mu bari su yi shigan farmakin juna, sa’anna a busa
qaho, kuma mu tara su duka gaba daya.
[18:100] Kuma mu gabatar da Jahannama, a ranar, ga kafirai gittawa.
[18:101] Wadanda idanunsu suka kasance a rufe da tunawa da Ni. Kuma
sun kasance ba su iya saurarawa ba.
[18:102] Shin, wadanda suka kafirta suna zoton za su tsira ne da sanya
bayiNa majibinta baici Na? lalle, mun shirya Jahannama ta zama liyafa ga
kafirai wurin zama na dindin.
Ka Binciki Kanka
[18:103] Ka ce, Ko in gaya maku game da mafifita hasara ga ayyuka?”
[18:104] Su ne wadanda ayyukansu a cikin wannan rayuwar duniya suke
kan bata, amma suna zaton suna kyautata ayyukan qwarai.”
[18:105] Wadannan su ne suka kafirta da ayoyin Ubangijinsu kuma da
haduwa da Shi. Saboda haka, ayyukansu duk abanza ne; kuma a Ranar
Alqiyamah, awonsu ba za su yi nauyi ba.
[18:106] Sakamakonsu shi ne Jahannama, saboda kafircinsu, kuma saboda
sun mayar da ayoyiNa da manzanniNa abin yin ba’a.
[18:107] Amma ga wadanda suka yi imani kuma suka aikata ayyuka na
qwarai, to, sun cancanci Aljannar Firdausi ta zama liyafa a gare su.
[18:108] Suna madauwama a cikinta; ba za su bukaci wani musayanta ba.
Alqur’an: Kome Ne Da Muke Bukata
[18:109] Ka ce, “Idan da ruwan teku tawada ce ga (abin rubutun) kalmomin
Ubangijina, da tekun ta qare, kalmomin Ubangijina basu qare ba, kuma ko
da mun ninka misalin tawadar ne.”
[18:110] Ka ce, “Ni mutum ne kawai kamarku, ana yin wahayi zuwa gare ni
cewa: Abin bautawarku Daya ne. Saboda haka, wadanda suke fatan su hadu
da Ubangijinsu, to sai su aikata ayyuka na qwarai, kuma kada su hada kowa
ga bauta ga UbangijinSa.”