Toggle menu
24.1K
670
183
158.6K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Quran/2/IRIB Hausa Tafsir

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations

Suratul Bakara; Aya Ta 1-2 (Kashi Na 4)

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai.

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa cikin wani sabon shirin hannunka mai sanda. Muna fatan za ku kasance tare da mu tun daga farkon shirin har zuwa karshensa.

Sura ta biyu ta cikin Alkur'ani mai girma wacce kuma ita ce sura mafi girma a cikin Alkur'anin ita ce suratul Bakara (wato saniya). An sanya mata wannan sura ne dai saboda kissar saniyar Bani Isra'ila wadda ta zo cikin surar.

Wannan surar dai ta fara ne da wasu haruffa na musamman masu janyo hankula. Don haka sai a saurare wannan ayar:

Aya ta 1:

الم

ALM (Alif Lam Mim)

A mafi yawan lokuta kalma guda ta kumshi wasu haruffa ne wadanda idan aka hada su suke tayar da wannan kalmar da kuma bat a ma'ana. Amma Allah Madaukakin Sarki ya faro wasu surori 29 cikin surori 114 da Alkur'ani mai girma ne da wasu haruffa wadanda kowane guda daga cikin su ana karanto shi ne shi kadai dinsa. Misalin hakan ita ce wannan aya ta farko ta cikin Suratul Bakara wanda muke karanta wa A L M ba wai Alam ba kamar yadda ya kamata su kasance. Irin wadannan haruffa wadanda larabawa ma ba su saba da su ba masana Alkur'ani suna kiran su da sunan 'huruf al-Mukadda'a' wato haruffa da suke rarrabe da junansu wadanda kuma a rarraben ake karanta su.

A mafi yawan lokuta bayan wadannan haruffan, akan gabatar da aya ta gaba ne wacce za ta yi nuni da girmar Alkur'ani da kuma kasantuwarsa a matsayin wata mu'ujiza, kamar yadda ya zo cikin Suratush Shura 'Ha mim Ain Sin Kaf daga nan sai ya ci gaba da cewa: "Haka nan kuma sai ya yi maka wahayi da kuma wadanda suka zo a gabaninka, lalle Allah mai girma ne kuma mai hikima".

Tamkar Allah Madaukakin Sarki yana son ya ce ne ni dai na samar da wannan littafi na wa ne wanda kuma yake a matsayin mu'ujiza daga wadannan haruffa da kuka riga da kuka san su ne, ba wai daga kalmomin da ku din nan ba ku san su ba ne ko kuma ba za ku iya fahimtar su ba.

Akwai wadansu mutane da suke da'awar cewa Alkur'ani dai ba mu'ujiza ba ne, to idan har abin da suke fadi gaskiya ne, to shi kenan su rubuta wani litttafi da irin wadannan haruffa kamar yadda ya zo cikin Alkur'ani sannan kuma a fagen jumloli ya zamanto maras tamka haka nan kuma a bangaren abubuwan da ya kumsa.

Lalle wannan yana daga cikin fasahar Ubangiji wanda ya samar da wani littafi daga wadannan haruffa da muka saba ganinsu ta yadda dan'adam zai gaza hatta wajen samar da wata sura ko da guda ce, kamar yadda hakan ta faru a duniya ta dabi'a inda Allah Madaukakin Sarki ya ke samar da nau'oi daban-daban na tsirrai da 'ya'yan itatuwa daga wata kasa macacciya maras rai.

A cikin wannan surar kamar Suratush Shura bayan wadannan haruffa sai kuma ya ci gaba da cewa:

Aya ta 2:

ذَلِكَ الْكِتَابُ لاَ رَيْبَ فِيهِ هُدًى لِّلْمُتَّقِينَ

"Wancan ne Littafi, babu shakka a cikinsa, shiriya ne ga masu takawa".

Wato wannan littafi mai girma wanda babu wata shakka cikin gaskiyarsa, kuma ya kasance jagora ne ga masu tsoron Allah.

Wannan littafi mai girma wanda wani gado ne na mutanen da suka gabata har zuwa ga mutanen wannan zamanin sannan kuma wanda ya sami damar isar da sakonni da kuma manyan ma'anoni da ilmummuka ga dukkanin bil'adama.

Duk kuwa da cewa ba wai an saukar da Alkur'ani ne daga sama a lokacin guda ban e, to amma sakamakon kariya ta Ubangiji da wannan littafi ya ke da shi ba a sami komai kashin wani sauyi ko gurbata a cikinsa ba. Manzon Allah (s) ya kasance yana karanta wa wasu daga cikin sahabbansa abin da aka saukar masa su kuma suna rubutawa sannan wasu kuma daga cikinsu suna haddacewa.

A lokacin da mutum ya karanci wannan littafi na Ubangiji da kyau, ko shakka babu zai fahimci cewa lalle wannan littafi daga wajen Allah ya ke, don kuwa irin bayanai da masaniyar da ke cikinsa wani lamari ne da ba ma za a yi tunanin ganinsa daga wajen wani mutum, shi din ma mutumin wancan lokaci da ilimi da masaniya suka yi karanci.

Kamar yadda muka fadi a shiri na farko a matsayin gabatarwa mun fadi cewa Alkur'ani littafi ne na shiriya da jan bil'adama zuwa ga sa'ada da farin ciki. Duk wanda ya kasance mai neman sa'ada, to ba shi da wata hanya da ta wuce ya koma ga wannan littafi da Allah Mahalacci ya aiko masa, sannan kuma ya yi amfani da hanyoyi da kayan aiki da ya ke da su wajen nesantar abubuwan da suke barazana ga ruhi da kuma jikinsa.

Allah Madaukakin Sarki cikin aya ta 185 ta cikin Suratul Bakaran yana cewa: "Watan Ramalana ne wanda aka saukar da Alkur'ani a cikinsa yana shiriya ga mutane" wato an saukar da Alkur'ani ne don shiryar da dukkanin mutane.

To amma a fili ya ke cewa mutanen da za su amfana daga wannan littafi na Ubangiji su ne mutanen da suke neman gaskiya sannan kuma a shirye suke su karbe ta. Don kuwa mutane masu taurin kai da tsaurin ra'ayi da bautar son zuciyarsu, wadanda ba wai ma kawai ba a shirye suke su nemi gaskiya ba, face ma dai a shirye su ke su dushe haske gaskiya a duk inda ta kunno kai, lalle irin wadannan mutanen kan ba za su taba amfanuwa da Alkur'ani din ba.

A saboda haka tun a farko akwai bukatar tsoron Allah na fidira da kuma daga cikin zuciyar mutum wadanda su ke a matsayin share fage karbar wannan shiriya. A saboda haka ne wannan aya take cewa: "shiriya ne ga masu takawa", wato Alkur'ani shi ne tushen shiriyar masu tsoron Allah.

Yanzu kuma bari mu yi dubi cikin darussan da suke cikin wannan ayar:

1- Sahabban annabi sun kasance masu ba da muhimmanci ga hadda da kuma rubuta Alkur'ani. A saboda haka ne aka mai da ayoyin da aka saukar da su suka zamanto Littafi har ya iso hannayenmu. A saboda haka wajibi ne mu ma mu kiyaye da kuma girmama tsarkin wannan littafi na Ubangiji mai tsarki. 2- Abubuwan da ke cikin wannan littafi abubuwa ne masu tsarki sannan kuma tsayayyu, saboda kuwa Allah Madaukakin Sarki ne ya saukar da su. 3- Alkur'ani littafi ne na shiriya bil'adama, ba wai wani littafi ne da ya kebanci wasu gungun mutane ba. 4- Za mu iya samun hasken Alkur'ani cikin zukatan mu ne a lokacin da muka zamanto muna da ruhin karbar gaskiya a duk lokacin da ta iso gare mu.

Da fatan Allah Madaukakin Sarki ya haskaka mana zukatan mu da haske Alkur'ani mai girma. Da hakan ne kuma muka kawo karshen shirin na mu na wannan makon sai kuma a mako na gaba inda za mu ci gaba daga inda muka tsara. Kafin nan na ke cewa ku zama lafiya.

Wassalamu alaikum wa rahamatullah wa barakatuhu.

Suratul Bakara; Aya Ta 3-4 (Kashi Na 5)

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai.

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa cikin wani sabon shirin hannunka mai sanda. A shirin da ya gabata mun yi muku karin haske kan ayoyin farko na Suratul Bakara inda muka bayyana cewar aya ta biyu ta cikin wannan surar ta yi magana kan shiryarwa ta Alkur'ani. To a yau za mu yi dubi ne cikin ayoyi na gaba da kuma siffofin da suka kebanta da su. Don haka sai ku saurari aya ta 3 ta cikin Suratul Bakaran da take cewa:

الَّذِينَ يُؤْمِنُونَ بِالْغَيْبِ وَيُقِيمُونَ الصَّلاةَ وَمِمَّا رَزَقْنَاهُمْ يُنفِقُونَ

"Wadanda suke yin imani game da gaibi, kuma suna tsayar da salla, kuma daga abin da Muka arzuta su suna ciyarwa".

Alkur'ani mai girma ya raba duniya zuwa biyu, na farko ita ce duniyar gaibi wacce ta buya daga fahimtar mu, ta biyu kuma ita ce duniyar da muke ganinta, ta dabi'a wacce aka saba da ita.

Wasu mutanen suna amincewa ne kawai da abin da suke iya gani da kuma ji sannan kuma suke iya jinsa a jikinsu, suna masu nuna cewa abin da kawai za su iya amincewa da shi shi ne duk wani abin da gabobinsu suke iya jinsu, alhali kuwa wadannan ababen ji da muke da su ba komai suke iya fahimta ba. Akwai abubuwa da yawa da ba za mu iya jin su a jiki ba face dai abin da za mu iya fahimta da kuma ji shi ne sakamakonsu.

Wasu mutane kuma suna son su ga Allah ne da idanuwansu kafin su yi imani da shi kamar yadda Bani Isra'ila suka gaya wa annabi Musa (a.s) inda suke cewa: "Ba za mu imani da kai ba, har sai mun ga Allah a fili (ido da ido)", alhali kuwa Allah ba jiki ba ne ballantana a gan shi, to amma muna iya ganin alamar girma da daukakarsa cikin halittu, don haka muka yi imani da shi.

Mutane masu tsoron Allah da neman gaskiya, ba sa takaita masaniyarsu da wannan duniya da ake ganinta, face dai sun yi imani da duniyar gaibi, wato samuwar Allah Madaukakin Sarki, mala'iku da kuma lahira wadanda suka buya daga gani da kuma jin mu.

Tabbas imani wani mataki ne da ya ke sama da ilimi da masaniya, wani mataki ne da zuciyar mutum za ta yi imani da wata samuwa, ta kulla alaka da ita da kuma nuna kauna da soyayya gare ta. Ko shakka babu irin wannan imani da akida za su zamanto tare da ayyuka na kwarai. Saboda a bisa koyarwar Musulunci imani ba tare da aiki ba haka nan kuma akida ita kadai kawai ba abu ne da za su shiryar da mutum da kai shi ga kamala ba.

Wannan aya tana cewa ne mutane masu tsoron Allah, suna imani da gaibi, haka nan kuma masu tsayar da salla da kuma ciyarwa ne. Ta hanyar salla wacce tuna Allah ne suna lamunce bukatunsu na ruhi sannan da kuma samun kwanciyar hankali, sannan kuma ta hanyar ciyar da wani bangare na abin da suka mallaka ga mabukata suna lamunce bukatar da al'umma suke da ita, don sauran mutane ma su zamanto cikin jin dadi da kwanciyar hankali.

Ko da yake salla kawai ba ta wadatarwa, face dai akwai bukatar mutum ya yi salla sannan kuma ya kirayi sauran mutane zuwa ga sallar. Ya yi sallar a farkon lokaci, haka nan kuma a masallaci tare da sauran jama'a, a irin wannan lokaci mutum ya kan sami wata lada ta musamman da kuma samun wani matsayi shi ma na musamman.

Haka nan a bangaren ciyar ma dai, ba wai kawai Musulunci yana maganar ba da taimakon kudi ba ne, face dai kamar yadda Alkur'ani ya bayyana 'daga cikin abin da muka arzurta ku", wato daga cikin abubuwan da muka ba ku ku ciyar, wanda hakan ya hada da dukiya, mulki, ilimi da dukkanin dama da ni'ima da Allah Madaukakin Sarki ya ba mu.

Yanzu kuma bari mu je ga darussan da suke cikin wannan magana ta Ubangiji:

1- Duniyar halitta ba ta takaita kawai da wannan duniya da muke ganinta ba, face dai akwai wadansu abubuwa da suka buya daga idanuwanmu to amma hankali da zuciyar mu suna sane da samuwarsu. A saboda haka wajibi ne mu yi imani da samuwarsu. 2- Imani da aiki tare suke ba za su rabu ba, sannan kuma mumini ma'abocin aiki ne, sai dai kuma aiki da koyarwar Allah Madaukakin Sarki. 3- Ita ita ce tushen ayyukan mutane masu imani. 4- Dukkanin abin da muke da shi daga wajen Allah ne, a saboda haka wajibi ne mu ba da wani bangare na wannan abin saboda Allah, wanda kuma Allah Madaukakin Sarki a duniya da lahira zai saka mana. 5- Addinin Musulunci addini ne na dukkanin al'umma sannan kuma ya zo don gudanar da rayuwar al'umma. Ya kasance mai kira zuwa ga mika wuya ga Ubangiji haka nan kuma yana kira zuwa ga kyautata alaka da mutane da kuma kula da bukatun mutane.

Yanzu kuma bari mu ji wasu siffofin na muminai daga bakin Alkur'ani mai girma. Don haka sai mu gyara zama don sauraren aya ta 4 ta cikin suratul Bakaran da take cewa:

والَّذِينَ يُؤْمِنُونَ بِمَا أُنزِلَ إِلَيْكَ وَمَا أُنزِلَ مِن قَبْلِكَ وَبِالآخِرَةِ هُمْ يُوقِنُونَ

"Kuma wadanda suke yin imani da abin da aka saukar zuwa gare ka, da abin da aka saukar daga gabaninka, kuma game da Lahira suna yin yakini".

Wahayi dai daya ne daga cikin hanyoyin samun masaniya wadanda muminai suka yi imani da ita. kamar yadda muka fadi a ayar da ta gabata, hanyoyin masaniyar mutum ba su takaita kawai da abubuwa da ya ke iya ji ko ganinsu ba, akwai wata duniyar wacce ba wannan duniyar da muke iya ganinsa wanda lalle hankali ya san da zamanta. Duk da cewa shi kansa hankali ya gaza wajen saninta masaniya ta hakika. A irin wannan yanayi ne ya sanya Allah Madaukakin Sarki ya aiko da wahayi don ya cika mana wannan masaniay da muke da ita.

Hankali yana fadin cewa lalle akwai Allah, shi kuwa wahayi yana mana bayanin siffofin wannan Ubangiji ne. Hankali yana fadin cewa wajibi ne a samar da wata kotu ta duniya don yin hukumci da kuma fitar da sakamako, wahayi kuma yana gaya mana cewa lalle akwai ranar kiyama wacce ita ma take da irin wadannan siffofi. A saboda haka hankali da wahayi masu cika junansu ne, sannan kuma mutane muminai suna amfani da dukkanin wadannan hanyoyin.

Wahayi dai ba lamari ne da ya takaita kawai da Manzon Allah (s.a.w.a) ba, face dai dukkanin annabawa sun kasance suna karbar wahayin Ubangiji. A saboda haka ne mutane masu tsoron Allah sun yi imani da dukkanin annabawan Ubangiji ba wai kawai Manzon Allah (s.a.w.a) ba, sannan kuma sun yi imani da kuma yarda da dukkanin abin da suka zo da shi.

Lahira dai tana daga cikin lamurra na gaibi wacce ta hanyar wahayi ne kawai za a iya fahimtarta fahimta ta hakika. A bisa wannan asasin ne ya sanya muminai suka yi imani da ita da kuma samun yakini sannan kuma ba sa ganin mutuwa a matsayin karshensu.

Yanzu kuma bari mu yi dubi cikin darussan da suke cikin wannan ayar:

1- Dukkanin annabawa suna da manufa guda ne, a saboda haka imani da dukkanin saukakkun littafa ya zama wajibi. 2- Al'ummar musulmi sun gaji saukakkun littafan da suka gabace su, a saboda haka wajibi ne su yi dukkanin abin da za su iya wajen kiyaye su. 3- Samun yakini da kuma imani da kiyama yana da tasiri mai girma, ya kan kaskantar da duniya a mahangar dan'adam da kuma kare shi daga fadawa tarkon sabo da kuma shiryar da shi zuwa ga ayyukan da suka kamata.

A nan ne za mu kawo karshen shirin na mu na yau, sai kuma a shiri na gaba inda da yardar Allah za mu ci gaba daga inda muka tsara. Sai a biyo. Wassalamu alaikum wa rahamatullah wa barakatuhu.

Suratul Bakara; Aya Ta 5-7 (Kashi Na 6)

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai.

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa cikin wani sabon shirin hannunka mai sanda. Idan dai ana iya tunawa a cikin ayoyin da muka yi nazari kansu a shirye-shiryen da suka gabata mun yi bayani kan siffofin muminai. To yanzu kuma sai a gyara zama don sauraren aya ta biyar ta Suratul Bakara:

Aya ta 5:

إِنَّ الَّذِينَ كَفَرُواْ سَوَاءٌ عَلَيْهِمْ أَأَنذَرْتَهُمْ أَمْ لَمْ تُنذِرْهُمْ لاَ يُؤْمِنُونَ

"Wadannan suna kan shiriya, daga Ubangijinsu, kuma wadannan su ne masu cin nasara".

Wannan ayar tana bayyana masu tsarkin zuciya a matsayin wadanda suke samun nasara da kuma rabauta ta Ubangiji sannan kuma suna kan tafarkin samun shiriya ta Ubangiji. Su ne wadanda suka 'yantu daga soyace-soyacen zuciya da kuma lizimtar kyawawan halaye. Samun nasara da rabauta shi ne mafi koli matakin kamalar mutum don kuwa kamar yadda ayoyin Alkur'ani suka bayyana, an saukar da Alkur'ani ne saboda dan'adam shi kuwa dan'adam an halicce shi don ibada, ita kuwa ibada ana yinta saboda a samu damar isa ga samun takawa, ita kuwa wannan ayar tana bayyana cewar masu tsoron Allah ne suke samun nasara da kuma rabauta.

Wannan aya tana karantar da mu abubuwa ne kamar haka:

1- Hanyar isa ga sa'ada da samun farin ciki ita ce yarda da shiriya ta Ubangiji. 2- Ba za a taba samun rabauta ba tare da kokari ba. Rabautar tana bukatar ilimi da imani, haka nan kuma da ayyuka na kwarai.

Yanzu kuma bari mu saurari aya ta 6 ta cikin Suratul Bakaran inda take cewa:

إِنَّ الَّذِينَ كَفَرُواْ سَوَاءٌ عَلَيْهِمْ أَأَنذَرْتَهُمْ أَمْ لَمْ تُنذِرْهُمْ لاَ يُؤْمِنُونَ

"Lalle ne, wadanda suka kafirta daidai ne a kansu, shin ka yi musu gardadi ko ba ka yi musu gargadi ba, ba za su yi imani ba".

Wato wadanda su ka kafirta kan, shin Ya kai Manzo ka tsoratar da su da azabar Ubangiji ko kuma ba ka yi musu hakan ba, babu wani bambanci a wajensu, lalle ba za su taba yin imani ba.

To bayan bayyanar da masu tsoron Allah da kuma tsarkin zuciya, wadannan ayoyi sun yi bayanin ko su wane ne kafirai wadanda suke da irin wannan taurin kan da maganar gaskiya ba ta yin wani tasiri a cikin zuciyarsu, sannan kuma ba za sa yin imani.

A harshen larabci 'kufr' wato kafirci yana nufin rufe abu da kuma rufe ido kan wani abu. A matsayin misali a kan ce wane ya kafirce wa ni'ima, wato ya ido rufe kan ni'imar da aka yi masa da kuma nuna rashin godiya. Don haka kafiri yana nufin mutumin da ya ke boye gaskiya da kuma rufe ido kanta.

Idan da Allah Madaukakin Sarki ya so yana iya tilasta wa dukkanin mutane su yi imani da shi, to amma dukkanin imanin da aka tilasta wa mutum shi ba shi da wata kima sannan kuma shi Allah Madaukakin Sarki yana son ne shi kansa mutum da kansa ya yi imanin. A saboda haka bai kamata mu yi zaton cewa dukkanin mutane za su yi imani su zamanto masu tsoron Allah ba.

Yanzu bari mu yi dubi cikin darussan da suke cikin wannan ayar:

1- Kafirci da tsaurin ra'ayi su kan sanya mutum ya zamanto mai daskararren tunani da babu wani lamari na ci gaba cikin tunaninsa ta yadda ya kan zama tamkar wani dutse ko kuma itace a tsaye yake babu ruwansa da wani abu na ci gaba. 2- Idan mutane suka zamanto marasa yarda da gaskiya, to kuwa ko da'awa da kira ta annabawa ma ba za ta yi musu wani tasiri ba. Alhali kuwa sakonnin annabawa tamkar ruwan sama ne wanda idan ya zuba a kasar da take rayayyiya nan take za ka ga tsirrai suna fitowa, amma idan kuwa a kan macacciyar kasa ya zuba, to babu wani abin da zai kara mata in ba bushewa da fari ba. 3- Ko da a ce mun san cewa kafirai ba za su yi imani ba, to amma wajibi ne mu yi kokarin sauke nauyin da ke wuyanmu wajen jan kunnensu.

Yanzu kuma bari mu je ga aya ta 7 ta cikin wannan sura ta Bakarar wacce take cewa:

خَتَمَ اللّهُ عَلَى قُلُوبِهمْ وَعَلَى سَمْعِهِمْ وَعَلَى أَبْصَارِهِمْ غِشَاوَةٌ وَلَهُمْ عَذَابٌ عظِيمٌ

"Allah Ya sa hatimi a kan zukatansu, da a kan jinsu, kuma a kan ganin su akwai wata yana; kuma suna da wata azaba mai girma".

Wato Allah Madaukakin Sarki ya rufe zukata da kunnuwansu sannan kuma ya sanya musu labule a kan idanuwansu (ba sa gani) sannan kuma azaba mai tsanani tana jiransu.

Kafirai dai suna da hankali da idanuwa da kuma kunnuwa, to amma munanan ayyukansu da kuma taurin kan da suke da shi ya sanya musu labule a kan wadannan abubuwa da kuma rufe ta yadda suka rasa karfi na fahimta da ji da kuma gani, hakan kuwa shi ne mummunan sakamakon da Allah ya yi musu a duniya, sannan a lahira kuma azaba mai girma da radadi tana jiransu.

A nan dai wannan tambayar ta kan bayyanar da kanta cewa idan har Allah Madaukakin Sarki ya rufe zukata, idanuwa da kuma kunnuwan kafirai, to ai ba su da wani laifi cikin wannan kafirci na su, don kuwa an tilasta musu zama kafiran ne?

To Alkur'ani mai girma dai ya yi bayanin wannan amsa. A cikin aya ta 35 ta cikin Suratul Ghafir Allah yana fadin cewa: "kamar haka Allah ya ke yin rufi a kan zuciyar dukkan makangari, mai tilastawa" ko kuma kamar yadda ya zo cikin aya ta 155 ta cikin Suratun Nisa'i inda Allah ya ke cewa: "A'a, Allah ne Ya rufe a kansu saboda kafircinsu", wato Allah Madaukakin Sarki ya rufe musu zukatansu ne saboda kafircinsu.

A hakikanin gaskiya wannan aya tana bayani ne kan sunnar Ubangiji dangane da dan'adam, wato a duk lokacin da ya zamanto mai girman kai, ya zamanto mai takadaranci a kan gaskiya, to kuwa hanyoyin fahimtarsa za su tashi a aiki, ba zai taba ganin gaskiya da kyau ba, sannan kuma zai zamanto mai mummunan makoma a duniya da lahira.

Yanzu kuma bari mu yi dubi cikin darussan da suke cikin wannan ayar:

1- Mutumin da ya fahimci gaskiya, to amma sai ya juya mata baya da kuma kokarin rufe ta, to Allah Madaukakin Sarki zai zai rufe idanuwa da kuma zukatansa. Wannan shi ne sakamako na Ubangiji. 2- Fifikon da mutum ya ke da shi a kan dabbobi shi ne hankali da fahimtar gaskiya da kuma madaidaiciyar hanya, to amma kafirci ya kan sanya shi rasa wannan siffa ta fifiko.

Masu saurare yau ma dai a nan ne za mu yi ban kwana da ku sai kuma a shiri na gaba inda za mu dora daga inda muka tsaya. Kafin nan na ke cewa ku zama lafiya. Wassalamu alaikum wa rahamatullah wa barakatuhu.

Suratul Bakara; Aya Ta 8-10 (Kashi Na 7)

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai.

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa cikin wani sabon shirin hannunka mai sanda. Za mu fara shirin na mu ne da sura ta 8 ta Suratul Bakaran wacce take cewa:

وَمِنَ النَّاسِ مَن يَقُولُ آمَنَّا بِاللّهِ وَبِالْيَوْمِ الآخِرِ وَمَا هُم بِمُؤْمِنِينَ

"Kuma akwai daga mutane wanda ya ke cewa: Mun yi imani da Allah kuma da Yinin Lahira, alhali kuwa su ba muminai ba ne".

Alkur'ani dai wanda littafi ne na shiriya ya yi mana bayani dangane da siffofin muminai, kafirai da kuma munafukai don mu san a cikin wacce kungiyar muke sannan kuma mu san sauran mutane kuma a ina suke don mu san irin alakar da ta dace da su.

Tun daga farkon Suratul Bakara ya zuwa wannan wajen, ayoyi hudu sun yi mana bayani dangane da muminai sannan wasu biyu kuma sun yi mana karin haske kan kafirai. Wannan ayar kuma da ayoyin da za su biyo bayanta za su yi mana bayani kan kungiya ta uku ta mutanen wadanda ba su da hasken da kungiya ta farko suke da shi sannan kuma ba su da jaruntaka da kuma fitowa fili irn na kungiya ta uku. Wato su dai ba su da imani a cikin zuciyarsu sannan kuma ba za su iya bayyanar da kafircinsu a fili da bakinsu ba. Su ne dai munafukai masu tsoro wadanda suke boye kafircin da ke cikin zuciyarsu, suna masu bayyanar da Musulunci a zahiri.

Bayan da Manzon Allah (s.a.w.a) ya yi hijira daga Makka zuwa Madina sannan kuma ya samu nasarori a kan mushirikai masu tsananin adawa da musulmi, wasu daga cikin mutanen Makka da Madinan, duk kuwa da cewa a cikin zuciyar su ba su yi imani da Musulunci ba, to amma saboda kiyaye rayuka da kuma dukiyarsu ko kuma saboda samun wani mukami a tsakanin musulmi, sai suka dinga bayyanar da Musulunci na karya a fili, suna nuna cewa su ma suna tare da musulmi. A fili yake cewa su din nan dai mutane matsorata, ba su da irin wannan jaruntaka da karfin gwuiwa, tamkar sauran kafirai su fito fili su bayyana cewar su kafirai ne wadanda ba su yi imani da addinin da musulmi suka rika ba.

Ala kulli hal, munafunci da bayyanar da fuska biyu wani lamari ne da dukkanin juyi da kuma yunkuri na sauyi na zamantakewa suka fuskanta, don haka bai kamata a yi zaton cewa dukkanin mutanen da a zahiri suke nuna imani da kasancewa tare da su ya zamana haka lamarin ya ke ba. Akwai irin wadannan mutane da yawa wadanda a zahiri suke nuna cewa suna tare da Musulunci amma kuma a badini suke cutar da shi gagarumar cutarwa.

Darasin da za mu iya dauka daga cikin wannan aya suna hada da cewa:

Imani dai wani lamari ne na zuciya ba wai na harshe ba. A saboda haka wajen fahimtar mutane, bai kamata a takaita kawai da abubuwan da suke furtawa da bakinsu ba.

Yanzu kuma bari mu saurari aya ta 9 ta cikin wannan sura ta Bakara:

يُخَادِعُونَ اللّهَ وَالَّذِينَ آمَنُوا وَمَا يَخْدَعُونَ إِلاَّ أَنفُسَهُم وَمَا يَشْعُرُونَ

"Suna yaudarayya da Allah da wadanda suka yi imani, alhali ba su yaudarar kowa face kansu, kuma ba su sakankancewa".

Wato su din nan suna zaton cewa suna yaudarar Allah da kuma muminai ne alhali ba su san cewa ba sa yaudarar kowa face kansu.

Munafukai dai suna zaton cewa su din nan mutane ne masu wayo suna zaton cewa ta hanyar bayyanar da imani za su yaudari Allah da kuma muminai don su sami kauna da kuma wajen zama a cikin zukatan musulmi. Suna son su yaudari annabi da kuma muminai, to amma a duk lokacin da suka ga ya dace sai su cutar da Musulunci da kuma yi masa bugun mummuke. Alhali kuwa Allah Madaukakin Sarki yana da masaniya dangane da wannan kafirci na badini da suke da shi, ya san wannan munafunci da suke da shi cikin zuciyarsu. Ya kan yi hakuri ne sai an kai wani matsayi da zai kunyata su da bayyanar da su ga muminai don su fahimce su da kyau.

A matsayin misali mara lafiyan da ya je wajen wani likita don gabatar masa da cutar da take damunsa, sannan kuma likitan ya ba shi magungunan da ya kamata ya yi amfani da su don samun sauki. To amma sai ya ki amfani da maganin, a bangare guda kuma ya tafi wajen likitan ya ce masa ai ina nan ina amfani da magungunan nan kamar yadda ka ce in yi amfani da su. To a nan a zatonsa ya yaudari likitan ne, alhali kuwa babu wanda ya yaudara in ba kansa ba, don kuwa babu wani abin da zai shafi shi wannan likitan. Don haka su ma wadannan mutane da suke zaton suna yaudarar Allah ne, ba kowa suke yaudara ba in ba kansu ba.

Yanzu kuma bari mu je ga darussan da za mu iya dauka daga cikin wannan ayar:

1- Manufukai dai mayaudara ne. A saboda haka wajibi ne mu yi taka tsantsan wajen ganin ba mu fada tarkon yaudararsu ba. 2- Mu ma bai kamata mu kama hanyar yaudarar wasu mutane na daban ba, don kuwa mu san cewa shika tana komawa kan mashekiya ne. 3- Musulunci yana mu'amala da munafukai ne gwargwadon yadda su ma suka yi mu'amala da shi. A zahiri suna bayyanar da kansu a matsayin musulmi, don haka shi ma Musulunci a zahiri yana kallonsu a matsayin musulmin ne. A zuci kuwa ba su yi imani da Allah da kuma Musulunci ba, don haka a ranar tashin kiyama Allah Madaukakin Sarki zai yi musu hukumci ne irin na kafirai. 4- Munafukai suna daukan kansu ne a matsayin masu yawo alhali kuwa babu wawaye kamar su, don kuwa ba su fahimci cewa wanda suke kokarin yaudarar Allah Madaukakin Sarki ne ba, wanda kuma ya ke masani kan dukkanin komai.

To yanzu kuma bari mu saurari aya ta 10 ta cikin Suratul Bakaran wacce take cewa:

فِي قُلُوبِهِم مَّرَضٌ فَزَادَهُمُ اللّهُ مَرَضاً وَلَهُم عَذَابٌ أَلِيمٌ بِمَا كَانُوا يَكْذِبُونَ

"A cikin zukatansu akwai wata cuta; sai Allah Ya kara musu wata cuta, kuma suna da azaba mai radadi saboda abin da suka kasance suna yi na karya".

A mahangar Alkur'ani mai girma ruhin mutum tamkar jikijnsa a wasu lokuta ya kan fuskanci matsalar cuta wanda idan har ba a yi masa magani ba, to a kowace rana zai ci gaba da yaduwa ne da kuma girma ta yadda zai kai matsayin da dan'adamtakar mutum za ta kawu gaba daya.

To munafunci dai yana daga cikin mafiya hatsarin cuta ta ruhi da take barazana ga ruhi da kuma zuciyar mu. Lafiyayyen mutum dai ba shi da wata fuska idan ba guda daya ba, sannan kuma akwai hadin kai da fahimtar juna tsakanin jiki da ruhinsa. Zarshensa na fadin dukkanin abin da ke cikin zuciyarsa ne sannan kuma mu'amalarsa tana yin daidai da tunaninsa. Amma a lokacin da lamarin ya zamanto sabanin haka, to kuwa ruhinsa ya samu matsala da kuma kamuwa da cuta wanda hakan zai yi sanadiyar kaucewarsa daga hanya.

Cutar munafunci, tana share fagen bullar wasu cututtuka na ruhi na daban irin su rowa, hassada da kuma kwadayi sannan kuma tamkar wata cutar kansa a kowace rana tana ci gaba da yaduwa ne da bakanta zuciya. Alkur'ani mai girma dai ya bayyana karya a matsayin tushe da kuma ummul aba'isin din cutar munafunci. Ko da yake karya dai ba ta takaita kawai da harshe ba, face dai a aikace ma mutum ya kan yi ta, a matsayin misali ta hanyar aikata wani abin da ya saba wa abin da ya yi imani da shi ba tare da wani dalili da shari'a ta yarda ya aikata hakan ba.

A matsayin misali gawar da ta fada cikin ruwa da kuma rubewa za ta ci gaba da warin gaske, ko da kuwa ruwan sama ya zo ya buge ta maimakon ya wanke ta da kawar da wannan wari sai ma dai ya kara warin ne sosai. To munafunci tamkar wannan gawar ce wanda idan har ya ci gaba da zama cikin ruhi da kuma zuciyar mutum, to duk wani hukumci da zai sauko daga wajen Allah Madaukakin Sarki, duk kuwa da cewa hakan rahama ce ga dan'adam, to amma shi munafuki maimakon ya mika wuya da amincewa da shi, to babu abin da zai yi face nuna cewa a zahiri ya amince da hakan amma a boye kan karya yake yi, don haka babu abin da hakan zai kara masa in banda kara wa wannan cuta tasa girma.

Munafunci dai yana fadaddiyar ma'ana ta yadda duk wani baki biyu cikin magana da aiki da zahiri da badini (wato abin da mutum ya ke fadi daban sannan kuma abin da ya ke aikatawa daban) hakan ya kan shiga cikin ma'anar munafunci, wanda mai yiyuwa ne a sami irin wannan ma'ana a tattare da wasu muminan ma. Wato mai yiyuwa ne su bayyanar da kansu da yin riya a lokacin ibada wato ya zamana suna ibadan ne saboda wanin Allah, to shi ma hakan wani nau'ii ne munafunci.

Manzon Allah (s.a.w.a) yana fadin cewa: Akwai wadansu siffofi guda uku wadanda idan aka same su tattare da wani mutum to ya zama munafuki ko da kuwa yana azumi yana salla sannan kuma yana ganin kansa a matsayin musulmi. (Wadannan abubuwa su ne) Mutumin da ya ke cin amana, mutumin da ya ke fadin karya a lokacin da ya ke magana sai kuma mutumin da ya ke saba alkawarin da ya yi.

Yanzu kuma bari mu yi dubi cikin darasin da za mu iya dauka cikin wannan aya:

1- Munafunci dai wata cuta ce ta ruhi, haka nan kuma munafuki tamkar sauran mutanen da suke fama da wata cuta, shi din ba mai lafiya ba ne sannan kuma shi ba macacce ba ne, haka kuma shi ba musulmi ban e sannan kuma ba kafiri ba ne. 2- Munafunci yana girma irin na cutar kansa cikin sauri da kuma game ko ina, don haka matukar ba a yi maganinsa ba, to kuwa zai kama dukkanin jikin mutum. 3- Tushen munafunci shi ne karya, sannan kuma fadin karya wata alama ce da take a fili ta munafukai.

Masu saurare da haka ne kuma za mu kawo karshen shirin na mu na yau, sai kuma a shiri na gaba inda za mu sake kasancewa tare da ku. Kafin nan na ke cewa ku zama lafiya.

Wassalamu alaikum wa rahamatullah wa barakatuhu.

Suratul Bakara; Aya Ta 11-13 (Kashi Na 8)

Da sunan Allah Mai rahma Mai Jin kai Assalamu alaikum jama’a masu saurare, barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda, yanzu za mu saurarin karatun ayoyin kur’ani mai tsarki, ayoyi na 11 da 12 a cikin suratul Baqara Ayoyin ( 11 ) – (12 )

وَإِذَا قِيلَ لَهُمْ لاَ تُفْسِدُواْ فِي الأَرْضِ قَالُواْ إِنَّمَا نَحْنُ مُصْلِحُونَ{11} أَلا إِنَّهُمْ هُمُ الْمُفْسِدُونَ وَلَـكِن لاَّ يَشْعُرُونَ{12}

Tarjama: Kuma idan aka ce da su su "kada ku yi barna a bayan kasa sai su ce Ai mu masu gyara ne. (12) Ka gane cewa su su ne mabarnata , sai dai ba sa ganewa.

    • Munafunci wata rashin lafiya ce da ke cutar da dan adam a cikin dukkanin lamurransa na rayuwarsa ta zamnatakewa, wanda idan ma’abocinsa bai iya shawo kan wannan matsalar ba, a cikin kankanin lokaci zai cutar da dukaknin sauran mutanen da yake rayuwa tare da su. Daga cikin abubuwan da munafunci ke haifarwa har da riya da nuna fuskoki daban-daban a cikin al’umma, tare da yaduwa fasadi da barna.

Munafuki ya san cewa baya aiki da koyarwar addini da umurninsa, haka nan kuma yan ason hana dukkanin mumunai yin aiki da koyi da addini a cikin lamurransu na rayuwa, a kan haka ne yake yin izgigili ga umurnin Allah, haka nan kuma baya bayar da muhimmanci ga duk wani aikin addini. Kur’ani mai ttsarki ya yi nuni zuwa ga wasu daga cikin soffofin munafukai a cikin suratul munafikin, da kuma surat tauba, irin yadda suke gudu a lokacin yaki da makiya addnin muslunci, domin su karya gwiwar muminai su sanya su su yi rauni, ko kuma a lokacin da ake bayar da gudunmwa wajne taimakon addinin Allah, sai su rika yin izgili ga masu bayar da kudade, duna cewa wadannan ‘yan kudin ba su da wata kima, domin kawai su hana musulmi yin aikin ibada. Munafunci shi ne tushen duk wata barna a cikin al’umma, ammam mai irin wannan dabi’a idanunsa makance suke ba ya ganin gaskiya balantan aya bi ta, kuma a lokaci guda baya ganin barnan da yake kuma yake watsawa cikin mutane. A maimakon haka ma munafukai suna ganin su ne kan sahihin tafarki, inda suke ganin cewa kawo cikas ga aikin jihadi wani kokari ne na hana zubar da jini, duk kuwa da cewa rashin yin hakan shi ne zai karfafa makiya da kafirai wajen yin dirar mikiya kan addini da mabiyansa. Sakonnin da ke cikin wadannan ayoyi da kuma darussan da muka koya daga aikin munafunci su ne: 1- Tasirin munafuncibai takaitu ga mutumin da yake munafuki ba, hakan yana rusa al’umma ga baki daya. 2- Daga cikin alamun munafunci, jiji da kai da ganin fifiko a kan sauran mutane, har munafukai sukan ce, mu ne kawai muka cancanta ba waninmu ba. 3- Idan munafunci ya samu wurin zama a cikin zuciyuar mutum, ya kan han shi gane a bin da yake daidai da wanda ba daidai ba, ya sanya ma’abucinsa ya zama ba a shirye yake ya saurari gaskiya ba. 4- Dole ne muminai su zama a farke domin kada su fada cikin tarkon munafukai. 5- Duk wata dubara da wayau da ba ya cikin abin da zai amfanar da al’umma, ba shi da amfani. Aya ta ( 13 ) Bakara:

وَإِذَا قِيلَ لَهُمْ آمِنُواْ كَمَا آمَنَ النَّاسُ قَالُواْ أَنُؤْمِنُ كَمَا آمَنَ السُّفَهَاء أَلا إِنَّهُمْ هُمُ السُّفَهَاء وَلَـكِن لاَّ يَعْلَمُونَ


Tarjama: " Kuma idan aka ce da su: Ku ba da gaskiya kamar yadda mutane suka ba da gaskiya, (sai0 su ce: Yanzu kuwa ma ba da gaskiya kamar yadda wawaye suak ba da gaskiya? Ka gane, hakika su (wadannan mutane su ne wawaye, sai dai kuma ba su san (haka ba)".


Daga cikin alamun munafunci akwai girman kai da jiji da kai da kuma ganin fifiko a kn sauran mutane, tare da raina kowa, munafiukai suna ganin su kadai ne masu hankali, su kadai ne masu wayau, suna kallon muminai mutane masu saukin yarda marassa wayau. A duk lokacin da aka ce musu me ya sanya kuke fitar da kanku daga cikin sahun sauran muminai, sai su koma suna izgili, suna fadin maganganu masu kaushi da rashin kunya ga sauran muminai, kuma ga raki a duk lokacin da wata musiba ta same su, wanda hakan ke nuna raunin imaninsu da Allah madaukakin sarki, da kuma yadda shedan ya yi tasiri a cikin hankalinsu da zukatansu. Kur’ani mai tsarki yana ba su amsa da cewa ku ne kuke zargin muminai da wawanci, alhali ke wawaye na hakika, amma babbar matasalar ita ce ku ba ku da labarrin cewa ku wawaye ne, abu mafi muni shi ne mutum batacce ya kasa fahimtar cewa shi batacce ne, kuma lokaci guda yana kallon wasu a matsayin batattu.

Abubuwan da za a koya daga wannan aya: 1- Wulakanta muminai na daga cikin siffofin munafukai, ta yadda suke ganin su ne birbishin kowa. 2- Dole ne a yi wa mai girman kai girman kai kamar yadda yake yi wa mutane muminai, domin a wulaknata shi cikin al'umma, ta yadda zai kwashi kaskanci. 3- Yin izgili da wulaknta wasu aiki ne na wawanci, mai hankali shi ne wanda yake yin magana da hankali, wawa kuma da izgili da wulakanci. 4- Allah madaukakin sarki yana tozarta fusakun munafukai tun a rayuwar duniya.

Suratul Bakara; Aya Ta 14-16 (Kashi Na 8)

Da sunan Allah Mai rahma Mai Jin kai Assalamu alaikum jama’a masu saurare, barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda, yanzu za mu saurarin karatun ayar kur’ani mai tsarki, ayat a 14 a cikin suratul Baqakara: Aya ta (14 ) Bakara:

وَإِذَا لَقُواْ الَّذِينَ آمَنُواْ قَالُواْ آمَنَّا وَإِذَا خَلَوْاْ إِلَى شَيَاطِينِهِمْ قَالُواْ إِنَّا مَعَكْمْ إِنَّمَا نَحْنُ مُسْتَهْزِئُونَ


Kuma idan suka hadu da wadanda suka ba da gaskiya sau su ce: Mun ba da gaskiya idan suka su da shaidanunsu sai su ce muna tare da ku, ai mu da ma izgili muke yi (wa Musilmi).

      • Daga cikin alamomin munafucn shi ne, munafuki ba shi da wata lama ko kuma wani matsayi takamaimai, a duk inda ya samu kansa to zai kokari ya saje da yanayin wurin, shi ne ya nuna kansa kamar mutanen wurin, a lokacin da yake tare muminai sai ya nuna cewa shi ma mai imani ne, a lokacin da kuma yake tare da makiya addini makiya al'umma sai ya nuna shi ma makiyin Musulunci, har ma sai ya rika yin izgili ga muminai.

Wannan aya na numa cewa, dole ne ma zama cikin fadaka kada mu fada cikin tarkon munafukai masu yaudarar musulmi da yi musu izgili. A dul lolacin da wani ya zo ya bayyana imani kada a amince masa kai tsaye, dole ne a duba a gas u wane ne yake yin mu'amala da su, su wane ne abokansa, mutum ba zai taba zama cikakken mumini ba,a lokacin yake dasawa da makiya addinin Musulunci, domin kuwa imani da son addini ba za su taba tafiya tare da son makiyin Allah da makiya addininsa ba. Abubuwan da za a koya acikin wadannan ayoyi: 1- Shaidain ba wai kawai shadanin aljani ba ne, a 'a mutanen da suke yin sanadiyar bacewar wasu ma shaidanu ne, dole ne a yi nesa da su. 2- Gudanar da zaman tattaunawa na kulla makirci a kan addini da tsarin Musulunci da gaskiya, hakan ya nuna rashin jaruntakar akidar munafunci, domin kuwa munafukai da suke yi muminai izgili suna yin hakan ne a cikin tsoro kuma gaba da gaba ba. 3- Munafukai su ne abin dogara ga makiya Musulunci, domin kuwa aduk lokacin da suke tare da su za su gaya musu cewa muna tare da ku, ba tare muke da muminai ba.

Aya ta (15) Bakara

اللّهُ يَسْتَهْزِئُ بِهِمْ وَيَمُدُّهُمْ فِي طُغْيَانِهِمْ يَعْمَهُونَ Tarjama: Allah yana saka masu (da irin izgilinsu yana kuma kara tsunduma su a cikin shsshiginsu su yi ta faganniya.

    • Imam Ali dan Musa Rida (AS) daga cikin limaman ahlul bait yana cewa: Allah madaukakin sarki ba ahalin makirci da yaudara da izgili ba ne, amma yana saka wa makiya da sakamakon makirci da izgili.

Hakika yin nsa a cikin duhu da rashin shiriya da bacewar zuciya da tunani da rashin basira da munafukai suke ciki, ya sanya sun rasa alkibla da rashin sanin ina suka dosa. Sunnar Allah ita ce yakan baiwa kafirai da batattu dama da lokaci isassshe, domin rahmarsa da tausayinsa gare su, domin ko sun samu damar yin tunani su tuba su dawo daga abin da suke yi, amma yin watsi da wannan damar da Allah madaukakin sarki yake baiwa mutum domin ya yi tunani kana bin yake yi, shi n eke kai mutum ga halaka acikin duhun bata. Abubuwan koyo a cikin wannan aya: 1- Yadda Allah yake sakawa masu aikata laifi da abin da ya dace da su daga cikin mutane. 2- Jinkirin da Allah yake wa masu aikata laifi domin su dawo su tuba saboda rahmarsa. 3- Allah shi ne mai kare muminai, idan munafukai da kafirai suna yi wa masu imani izgili to Allah ne da kansa yake rama musu a kan kafirai da munafukai.

Aya ta ( 16 ) Bakara:

أُوْلَـئِكَ الَّذِينَ اشْتَرُوُاْ الضَّلاَلَةَ بِالْهُدَى فَمَا رَبِحَت تِّجَارَتُهُمْ وَمَا كَانُواْ مُهْتَدِينَ Tarjama: Wadancan (su ne) wadanda suka sayi bata (suka biya) da shiriya, to cinikinsu bai yi riba ba, ba su kuwa kasance shiryayyu ba.

    • Duniyar da muke rayuwa a cikinta, tamkar wata kasuwa ce, mu kuma tamkar wasu 'yan kasuwa ne dole ne mu saka dukiyoyinmu a matsayin jarukanmu na kasuwanci, mu saye da sayarwa, jarin namu kuwa shi ne rayuwa da samartaka, hankali da tunani, ilimi da iko da dukkanin daar da muke da ita wadda Allah ya ba mu a cikin rayuwa.

A cikin wannan kasuwa wasu suna cin riba, kuma suna kaiwa ga sa'ada ta duniya da lahira, yayin da kuma wasu suke samun karaya acikin harkarsu ta kasuwanci, kamar mai sayar da kankara ne, idan bai sayar da ita ba to za ta zama ruwa, kuma zai rasa jarinsa. A cikin wurare da dama a cikin kur'ani mai tsarki, an yi nuni da hakan, inda a cikin surat Saf aya ta 9 aka siffanta imani da jihadi a matsayin tijara, inda ayar ke nuna cewa Allah madaukakin sarki yan akira ga muminai cewa ba zai shiryar da su zuwa ga wani kasuwanci ba da zai tseratar da su daga azabar wuta, ya ce su yi imani da Allah da manzonsa kuma su yi jihadi a taarkin Allah da dukiyoyinsu da kawukansu. A cikin wannan ayar za a fahimci cewa munafukai sanannun 'yan kasuwa ne, wadanda suka sayar da imaninsu na fitira da tunani, sun saba da aikata zunubi da munafunci, domin kuwa munafukai ba a mabota shiriya ba ne, sun sayar da shiriya suka karbi bata, to irin wadannan 'yan kasuwa ne suka yi asarar kasuwancincu, suka rasa abin kasuwanci da kuma hannayen jarukansu. Abubuwan koyo a cikin wannan aya: 1 – Ka da kawai mu yi ta tunanin samun riba da dukiya a cikin harkar kasuwanci, a a mu yi tunani kan wane ne za mu sayarawa zukatanmu da rayukanmu, kuma me za mu samu da hakan, ka da abin da za mu samu ya zama azaba ce da tabewa a rayuwar duniya da lahira. 2 – Shiriya da bata dukkaninsu abubuwa ne biyu da suke a matsayin abin da ake samu ta hanyar irin wannan kasuwanci, bawai kawai haka ne Allah ya so ko ya kaddara ba ko ya tilasta, a a tare da son ranmu lamarin yake kasancewa.

Suratul Bakara; Aya Ta 17-19 (Kashi Na 10)

Da sunan Allah Mai rahma Mai Jin kai Assalamu alaikum jama’a masu saurare, barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda, yanzu za mu saurarin karatun ayar kur’ani mai tsarki, ayat a 17 a cikin suratul Baqara:

Aya ta ( 17 ) Bakara

مَثَلُهُمْ كَمَثَلِ الَّذِي اسْتَوْقَدَ نَاراً فَلَمَّا أَضَاءتْ مَا حَوْلَهُ ذَهَبَ اللّهُ بِنُورِهِمْ وَتَرَكَهُمْ فِي ظُلُمَاتٍ لاَّ يُبْصِرُونَ Tarjama: Misalinsu kamar misalin wani da ya hura wuta ne, sannan yayin da ta haskaka abin da yake kewaye da shi, sai Allah ya gusar da haskensu kuma Ya bar su (dindin) a cikin duffai, ba sa gani. Ayar da ta gabata ta yi mana karin haske ne kan alamomin munafukai, da kuma irin salon mganarsu, kwatankwacinsu kamar hasken wuta a cikin duhu, bayan an tafi da kaskn zukatansu, kuma hasken wuta ba mai dawwama ba ne, saboda haka bayan lokaci kadan za tabbata a cikin duhu, wato tamkar wuta ce take cin zukatansu saboda rashin sahihin imani da Allah madaukakin sarki. Da sannu hijabi zai yaye kowa ya gansu a cikin duhun bata da jahilci da zalunci, domin kuwa su ne suka zalunci kansu, sakamakon yin musu da ayoyin Allah da cutar da masu imani. Za a iya kiran munafukai a matsayin ahalin kafirci kuma ahalin wuta kamar dai yadda ayoyi da dama suka ishara da hakan, a ranar lahira munafukai za su tashi bas u da rabo daga rahmar ubangiji da sa'adarsa, muminai da suke fuskantar izgili da ba'a daga munafukai su ne cikin ni'ima da gafara daga ubangijinsu madaukakin sarki. Abubuwann koyo daga wannan aya: 1- Hasken munafuki hasken wuta ne mai rauni, wanda ba ya tabbata. 2- Kasantuwar munafuki a cikin al'umma na kara ruruwar wutar fitina ne. 3- Munafuki yana yin amfani da wuta domin isa ga haske, inda yake konewa a cikin zafi hayaki. 4- Allah madaukakin sarki yana raba unafuki da hasken imani, kuma yana hana shi hatta hase na zahiri. 5- Makomar munafuki tana cikin duhu, ba ya da wani sa rain a tsira daga fushin ubangiji. 6- Munafunci da yaudara a wurin Allah ba dubara ba ce, hakan alama ce ta halka da zalunci. Aya ta (18) Bakara

صُمٌّ بُكْمٌ عُمْيٌ فَهُمْ لاَ يَرْجِعُونَ Tarjama: "(Su) kurame ne (daga jin gaskiya) bebaye ne (daga fadar gaskiya) makafi ne (daga ganin hanyar shiriya) sannan kuma ba sa komowa (zuwa shiriya)".

Ko da yake mutum munafuki yana da harshe da idanu da kunnuwa kamar sauran mutane, amma kuma kunnuwansa da idanunsa ha harshensa ba a shirye suke su karbi gaskiya ba, ta hanyar saurare ko gani ko fada ba. Saboda haka ne ma kur'ani mai tsarki ya bayyana munafukai da cewa mutane wadanda ba su da shu'uri, ba sad a masaniya, ba sa idon basira, suna cikin dimowa. Suna rufe idanunsu daga bin gaskiya, tare da karkata zuwa ga kafirci , da kuma kasa banbamce tsakanin gaskiya da karya a cikin lamurra, suna bin bata ido rufe wannan ne ya sanya ko sun ga gaskiya da idanunsu biyu ba za su bita ba, ko sun ji gaskiya da kunnuwansu ba su yi aiki da ita, harshensu kullum yana fadin abin da shi ne cikin zukatansu ba, wanda ya karar da rayuwarsa acikin wannan yanayi, yana daga cikin masu hasara a rayuwar duniya.

Aya ta ( 19 ) Bakara

أَوْ كَصَيِّبٍ مِّنَ السَّمَاءِ فِيهِ ظُلُمَاتٌ وَرَعْدٌ وَبَرْقٌ يَجْعَلُونَ أَصْابِعَهُمْ فِي آذَانِهِم مِّنَ الصَّوَاعِقِ حَذَرَ الْمَوْتِ واللّهُ مُحِيطٌ بِالْكافِرِينَ Tarjama: "Ko kuma (halinsu) kamar ruwan sama ne mai zuba da karfi, a cikinsa ga tsananin duhu da tsawa da walkiya har ta kai) suna sanya yatsunsu a cikin kunnuwansu don tsananin tsawarwaki saboda tsoron mutuwa, alhali kuwa (ilimin) Allah yana kewaye da kafirai".

A cikin aya ta goma sha bakawai Allah madaukakin sarki ya kamanta munafukai da haske da ke tafiya sakai, haka nan kuma munafukai tamkar masu tafiya ne a cikin duhun dare da suke tafiya acikin cabin laka, suna cikin tsoro da figita a duk lokacin da suka tsawa ko ganin walkiya, sakamakon rashin natsuwar zuciya, da rashin imani na gaskiya. Abubuwan da za akoya daga wannan aya:

1- Munafukai sun nutse a cikin matsaloli da damuwa da rashin natsuwa. 2- Suna cikin firgici da tsoron mutuwa akowane lokaci, ba su da natsuwar zuciya a cikin rayuwarsu. 3- Allah yana sane da dukkanin abin da munufukai suke ciki. 4- Daga karshe dai kafirci yana karewa zuwa ga kafirci, saboda fadinsa cewa Allah yana mai kewayewa da munafukai. 5- Rabon munafuki dag aruwan sama shi ne tsawa da walkiya da tsoron mutuwa, duk kuwa da cewa ruwan sama rahmar ubangiji ce, amma ga munafukai ta kan zama wani nau'in azaba.

Daga karshe muna kira ga masu saurare, da su yi la'akari da irin abubuwan da wadannan ayoyi suke dauke da sun a darussa da kuma yin hannuka mai sanda ga dukkain mutane masu imani, domin kauce wa fadawa cikin wani yanayin da Allah bai yarda da shi ba, Allah ya kare mu.

Suratul Bakara; Aya Ta 20-22 (Kashi Na 11)

Da sunan Allah Mai rahma Mai Jin kai Assalamu alaikum jama’a masu saurare, barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda, yanzu za mu saurarin karatun ayar kur’ani mai tsarki, aya ta 20 a cikin suratul Baqara: Aya ta ( 20 ) Bakara:

يَكَادُ الْبَرْقُ يَخْطَفُ أَبْصَارَهُمْ كُلَّمَا أَضَاء لَهُم مَّشَوْاْ فِيهِ وَإِذَا أَظْلَمَ عَلَيْهِمْ قَامُواْ وَلَوْ شَاء اللّهُ لَذَهَبَ بِسَمْعِهِمْ وَأَبْصَارِهِمْ إِنَّ اللَّه عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِير Tarjama: Walkiyar tana kusan fauce ganansu, duk sanda (haskenta) ya haskaka musu sai sukan tafi cikinsa, kuma idan wurin ya yi duhu a gare su (sai ) su tsaya ( a dimauce); da kuwa Allah ya so da sai ya tafiyar da jinsu da ganinsu. Hakika Allah Mai iko ne a bisa komai.

Tsawa da walkiya a sararin samaniya alama ce ta safkar ruwan sama da rahma da jin dadi da kuma fitar tsirrai a bayan kasa, amma hakan ba ga kowa yake ba, sai dai ga wadanda dama a suna jiran wannan rahmar ubangiji ne, amma ga mutumin da yake kan hanaya matafiyi ya lamarin yake? Hasken wuta mai rauni da kuma walkiya da ke tafe da hadari ba za su iya haskaka wa munafuki ba, wanda ba ashirye yake ya karbi gaskiya daga ubangiji ba, saboda haka irin wadannan tsawa da walikiya da ruwan sama ba rahma ce a gare su ba, domin su kansu wani bangare ne na musiba acikin rayuwar al’umma. Munafukai ba su cikin tarbar duk wata albarka da Allah madaukakin sarki yake safkar ma bayinsa, domin kuwa a kowane lokaci suna zaton rahmar Allah azaba ce gare su saboda munanan ayyukan da suke aikatawa, domin kuwa ba su kan shirya da ubangiji ya aiko wa bayinsa ta hanyar manzonsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka. Kur’ani mia tsarki ya yi bayani filla-filla dangane da matsayin irin wadannan munafukai a cikin rayuwar al’umma, inda sukan rufe idanunsu gaba daya daga duk wani haske na shiriya saboda girman kai da kuma izgili ga mumunai da kin gaskiya. Ko da yake Allah ya mayar musu da martani kan izgilin da suke yi wa bayinsa masu imani na gaskiya da sakon Allah madaukakin sarki, wannan ne ya sanya akullum suna cikin dimuwa da rashin sanin matsayinsu a rayuwar duniya, balantana lahira da su yi mata tanadi ba.

Abubuwan koyo daga wannan aya; 1- Munafuki ba ya da damar ganin hasken ubangiji, walkiyar hadari da ke safkar da ruwan sama tana tsorata su da girgiza zukatansu. 2- Munafuki shi a kansa ba shi da haske balanta ya haskaka wani, saboda haka yana samun albarkacin hasken muminai. 3- Munafuki yana yin aiki domin cimma manufarsa amma ba ya kaiwa ga sakamakon da yake bukata. 4- Saboda ayyukan da yake aikatawa, a kowane lokaci zai iya fadawa cikin fushin ubangiji mai tsanani. 5- Ba zai iya yaudarar Allah ba, a kowane lokaci ubangiji ya ga dama zai iya kama shi.

Ayat ( 21 ) Bakara:

يَا أَيُّهَا النَّاسُ اعْبُدُواْ رَبَّكُمُ الَّذِي خَلَقَكُمْ وَالَّذِينَ مِن قَبْلِكُمْ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ Tarjama: Ya ku mutane, ku bauta wa Ubangijinku wanda ya halicce ku, ku da wadanda suka gabace ku don ko kwa tsoraci (Allah).

A cikin ayoyin ashirin da suka gabata Allah madaukakin sarki ya yi bayani kan siffofi uku na gungun mutane, masu imani da takawa, muminai da kuma munafukai, idan muka duba dukkanin bangarorin uku za mu ga irin yadda kowanne ya kebanta da wasu abubuwa na musamman a cikin ayyukansa da da kuma abin da ya kudurce a cikin ransa, wanda ya yarda da shi a matsayin hanya ta rayuwa. Domin kasancewac acikin bangare na farko akwai bukatar tsarkake rai daga da kuma mayar da komai ga Allah, tare da tsarkake aiki ga Allah madaukakin sarki. Da dama daga cikin mutane sun amince da Allah a matsayin ubangiji, sun san cewa shi ne mahaliccinsu kuma maliccin komai da ke cikin duniyar nan, amma kuma a lokaci ba su aiki da umurninsa acikin sauran harkokinsu na rayuwa. Wannan aya ta nuna cewa Allah shi ne wanda ya yi halitta kuma yake da iko a kanta, kuma bai bar halittarsa hakan nan ba har sai ta ya tsara mata hanyar rayuwa, saboda haka bin tafarkin rayuwa da Allah ya tsara ma dukkanin halittunsa kama daga mutane da aljannu da mala’iku da sauransu, shi ne cikamakon imanin da shi, domin imani ba tare da aiki ba, yana da tawaya. Saboda haka yin imani da Allah shi kadai ba tare da yin aiki da umarninsa acikin sauran lamurra na rayuwa ba, ba zai kusantar mutum zuwa ga Allah ba har ya samu kaiwa ga matsayi na takawa da wannan aya ta yi ishara a kansa.

Abubuwan koyo daga wannan aya: 1- Kiran manzon Allah ga dukkanin mutane ne da suke rayuwa abayan kasa, bai kebance wasu gungun mutane a duniya ba yace wannan kira bai shafe su ba. 2- Daya daga cikin hikimar ibada ga Allah madaukakin sarki ita ce yin godiya ga ni’imarsa ga talikai, wadda ba ta da karshe, shi yasa yakan ce ya ku mutane ku bauta ma ubangijinku wanda ya halicce ku. 3- Ni’imar halitta ita ce babbar ni’ima ta farko ga mutane, saboda haka bauta ma Allah madaukakin sarki wani bangare na godiya ga wannan ni’ima. 4- Ibada tana kai mu zuwa ga tsoron Allah, idan muna ibada da bata kai mu ga tsoron Allah ba to ba ibada muke yi ba. 5- Mu yi hattara ka da mu gwama bautar Allah da ta waninsa, kada mu son ransu domin yin hakan ya yi daidai bin waniumurni wanda ba na Allah ba, domin kuwa ba a bin wani abin halitta a sabi Allah, mutum ne ko zuciya. 6- Allah madaukakin sarki ba ya da bukatuwa zuwa ga ibdarmu, domin kuwa Allah ya daukaka tare da wadatuwa daga gare mu da ayyukanmu baki daya, haka nan kuma rashin ibadarmu ba zai rage shi da komai a cikin mulkinsa madawwami ba. 7- Ka da mu rudu da ibadarmu, domin kuwa jiji da kai yana hana mutum kaiwa zuwa ga matsayi na takawa da tsoron Allah.

Aya ta (22) Bakara:

الَّذِي جَعَلَ لَكُمُ الأَرْضَ فِرَاشاً وَالسَّمَاء بِنَاء وَأَنزَلَ مِنَ السَّمَاءِ مَاءً فَأَخْرَجَ بِهِ مِنَ الثَّمَرَاتِ رِزْقاً لَّكُمْ فَلاَ تَجْعَلُواْ لِلّهِ أَندَاداً وَأَنتُمْ تَعْلَمُونَ Tarjama: Wanda ya sanya muku kasa (ta zama) shimfida, kuma (ya sanya muku) sama (ta zama) rufi, kuma ya saukar da ruwa daga sama, sannan ya fitar da 'ya'yan itatuwa da shi don amfaninku. To kada ku sanya kishiyoyi ga Allah (wurin bauta) alhali kuwa ku kuna sane (da wannan).


A cikin wannan aya mai albarka Allah madaukakin sarki ya nuna mana ni’imominsa ta suke zagaye da mu, inda kasa ta zama daya daga cikin wadannan ni’imomi, inda yakan safkar da ruwan sama ya raya ta, ya fitar da tsirrao\i daga cikinta, ya fitar mana da abinci da arziki mai yawa, da ya hada da ma’adanai da sauransu, domin kawai mu amfana da su, domin kuwa ya wada tu daga wannan baki daya. Dangantakar da ke akwai tsakanin sama da kasa ta hanyar samar da ruwan sama, tana haifar da mafani da ke komawa zuwa ga dan adam, haka nan kuma Allah ya sanya abin da ke bayan kasa baki daya ya zama karkashin dan adam, kuma yasana wasu abubuwa masu baiwa kasa kariya kamar duwatsu da suka kafe ta.

Abubuwan koyo daga wannan aya: 1- Babbar kulawa ga ni’imar ubangiji ita ce saninsa tare da bauta masa. 2- Samun dangantaka tsakanin sama da kasa da suke samar da ruwa ya tabbatar da samur ubangijinsu da abin da ke tsakaninsu. 3- Abubuwan da Allah ya safkar na arziki a bayan kasa domin amfanin dan adam ne kafin duk wata halitta. 4- Tsarin da ke akwai a cikin duniya ya tabbatar da cewa mahaliccin duniya da abin da ke cikin ta daya ne. 5- Sanin Allah da kuma bauta masa abubuwa ne guda biyu da suke tare da halittar dan adam da kuma fitirarsa. 6- Ruwa da kasa wasu hanyoyi ne na samar da abinci ga dan adam, amma safkar da su da fitar da tsirrai da amfanin gona duka aiki ne na Allah.

Suratul Bakara; Aya Ta 23-24 (Kashi Na 12)

Assalamu alaikum jama’a masu saurare, barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda, inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur’ani mai tsarki, domin daukar darussan da suke koyar da mu. Har yanzu muna cikin suratul Bakara, inda yanzu za a saurarin karatun aya ta 23 a cikin suratul Bakara:

Allah madaukakin sarki yana cewa:

وَإِن كُنتُمْ فِي رَيْبٍ مِّمَّا نَزَّلْنَا عَلَى عَبْدِنَا فَأْتُواْ بِسُورَةٍ مِّن مِّثْلِهِ وَادْعُواْ شُهَدَاءكُم مِّن دُونِ اللّهِ إِنْ كُنْتُمْ صَادِقِينَ

"Kuma idan kun kasance cikin kokwanto a kan (wani abu) daga abin da Muka saukar bisa bawanmu, to ku zo da sura daga irinsa(surar Alkur'ani) ku kuma kirawo shaidunku wadanda za su taimaka muku ba Allah ba, idan kun kasance ku masu gaskiya ne".

Kowane manzon Allah da Allah madaukakin sarki ya aiko yana da wata mu’ujiza da yake nuna wa mutanensa domin gajiyar da su kan sakon Allah, amma mu’ujizar manzon karshe tsira da amincin su tabbata a gare shi da iyalan gidansa ita ce kur’ani mai tsarki. Allah ya kirayi masu musun muslunci da kur’ani da su kawo wani littafi da ya yi kama da kur’ani sai a kwatanta a gani, ba za su iya kawo wani makamncinsa ba, koda kuwa aya daya ce da ta yi kama da ayar kur’ani mai tsarki, domin kuwa lafazin kur’ani ba lafazi ne na mutum ba, bai ma yi kama da lafazin abin halitta ba. Dukkanin masana na duniya sun tafi kan cewa kur’ani babbar mu’ujiza ce manzon Allah ya zo da ita, domin kuwa kur’ani mai tsarki ya bayar da bayanai dangane da annabawa da suka gabata, da abubuwan da suka faru tun daga lokacin halittar annabi Adamu da sauran annabawa, har zuwa lokacin da manzo ya bayyana da sakon Allah madaukakin sarki a hijaz. Kamar yadda muka fada kowane annabi daga cikin annabawan Allah ya kan zo da mu’ujiza da za ta tabbatar da cewa abin da ya zo da shi ba daga gare shi yake ba, sako ne daga Allah mahaliccin kowa da komai, kuma mun bayyana cewa sakon kur’ani daga Allah shi ne mu’ujizar manzon Allah Muhammad dan Abdullah (SAW) Za mu kawo abubuwa kamar hudu dangane da hakan: Na farko annabawa da dama da suka gabata suna zuwa da mu’ujiza kuma su yi ma matane bayani cewa wannan mu’ujiza ce ta sakon Allah madaukakin sarki, amma kur’ani ba ya bukatar wani bayani kan cewa mu’ujiza ce da ke tabbatar da shi a matsayin sako da ba na mutum ba ko wani abun halitta. Na biyu, mu’ujizar da annabawa suke zuwa da ita ta takaitu ne da zamanin da aka aiko su, amma mu’ujizar kur’ani ta zo ne domin ta dawwama har zuwa karshen duniya, kuma ita ce mu’ujiza mafi girma daga cikin wadanda suka gabace ta daga cikin mu’ujizozin annabawan Allah madaukakin sarki. Na uku, Kur’ani mai tsarki bai takaitu da wata al’umma ba kamar a ce larabawa ko al’ummomin da ke yankinsu ba, domin kuwa littafi ne da ke magana a kan al’ummomin da suka gabata da kuma wadanda suke rayuwa a lokacinsa, hakan nan kuma tsarin rayuwa da ke cikinsa ya yi daidai da dukkanin al’umomin lokacinsa da kuma masu zuwa. Na hudu, sakon da ke cikin kur’ani mai tsarki yana ratsa zuciyar dan adam, domin kuwa shi mu’ujiza ce ta lafazi da ma’ana,

Abubuwan da za a iya koyo daga wannan aya: 1- Daya daga cikin fitattun siffofin annabawan Allah ita ce bayin Allah, inda ya kan ambace su da bayinsa, wasu wuraren yakan ce mun safkar a kan bawanmu wane, wanda hakan ke nuna matsayin annabawa na bauta ga Allah madaukakin sarki. 2- Kur’ani mai tsarki littafi ne kafa dalili, shi hanya ce ta kawar da shakku kan sakon Allah madaukakin sarki da ya safkar wa manzonsa. 3- Kur’ani mu’ujiza ce madawwamiya daga Allah, wadda ta yi daidai da dukkanin zamuna a lokacin safkarsa da kuma sauran zamuna har karshen duniya. 4- Addinin musulunci addini ne na duniya baki daya, domin kuwa mu’ujizar kur’ani dawwamammiya ce tare da addinin msulunci. 5- Ba ya halasta mu ba zuciyarmu dama ta yi shakku kan sakon Allah da tushen addini, da zaran mun yi wani shakku mu gaggauta kawar da shi. 6- Babban alkali shi ne samuwarmu, domin kuwa a lokacin da muke da samuwa ne za mu iya gane daidai da abin da ba daidai ba, ta hanyar yin amfani da hankali. 7- Kur’ani ya tabbatar da cewa shi fadar Allah ne ba ta mutum ba, domin kuwa ya kalubalanci kafirai da suke shakku a kansa kan su kawo ko da sura daya da ta yi daidai da kur’ani, amma ba su iya ba.

Yanzu kuma sai a saurari karatun aya ta ( 24 ) daga suratul Bakara Allah madaukakin sarki yana cewa:

فَإِن لَّمْ تَفْعَلُواْ وَلَن تَفْعَلُواْ فَاتَّقُواْ النَّارَ الَّتِي وَقُودُهَا النَّاسُ وَالْحِجَارَةُ أُعِدَّتْ لِلْكَافِرِينَ

"To idan kuwa ba ku aikata (haka ba), hakika ba kuwa za ku iya aikatawa ba, to ku ji tsoron wutar nan wadda makamashinta mutane ne da duwatsu, wadda aka tanada don kafirai".

Wannan aya tana nuni da cewa lallai masu musu kan kur’ani ba za su iya kawo wani abu makamancin kur’ani ba, domin kuwa a baya ba su yi ba, kuma a gaba ma ba za su iya yin hakan ba, saboda haka wannan aya mai albarka ta kiraye su da su ji tsoron wutar da Allah madaukakin sarki, wadda ya yi tanadinta ga masu kafirce wa ayoyinsa, kuma abubuwan da ake hura ta da su mutane da kuma duwatsu, su ne matsayin makamashinsa. A nan kur’ani yana yin barazana da jan hankali ga masu yin musu da ayoyin Allah, domin kuwa a lokacin da ya misilta wuta da cewa makamashinta mutane da kuma duwatsu, hakan na nuni da irin tsananin zafin da ke tattare da ita da kuma yadda take kone abun da aka saka cikinta, domin kuwa dutse ba abun da wuta take konewa ba ne, amma lokacin da wuta take kone dutse kurmus, ya mutum zai kasance a cikinta. wanda hakan jan hankali ne da kuma baraza ga masu yin musu da jayayya akan ayoyin Allah madaukakin sarki. Kamar yadda ya yi ishara kan hakan a cikin aya ta 98 a cikin suratul anbiya da ke cewa: ku da abin da abin da kuke bauta mawa ba wani abu ba ne illa makamshin jahannama.

Abubuwan koyo a cikin wannan aya: 1- Dangane da addinin gaskiya dole ne a tabbatar wa masu musu da gaske cewa addinin Allah shi ne addini na sakankancewa, domin kuwa ayar tana cewa idan ba ku iya kawo makamancinsa ba to kuwa ba zu taba iyawa ba. 2- Saboda kafirce wa ayoyin Allah mutum zai iya kaiwa ga wani matsayi da zuciyarsa za ta zama tamkar dutse, saboda tsananin kekashewa, ta yadda zai zama garwashin wuta a ranar kiyama. 3- Zuciyar da ta zama tamkar dutse saboda kekashewa babu abin da zai huda ta, hakan nan ma kur’ani mai tsarki ba zai samu wurin zama a cikinta ba, a kan haka za a tayar da ita tamkar dutse a ranar kiyama. 4- Mu’ujizar kur’ani ba ta takaitu da lokacin manzon Allah ba kawai, domin kuwa kamar a lokacin manzo wani bai iya kawo abin da ya yi kama da kur’ani, haka nan ma a bayansa babu wani wanda zai iya kawo wani abu makamancin kur’ani mai tsarki. 5- Wutar jahannama tana da tsananin zafi da kuna, ta yadda take kone dutse tamkar karmami.

Suratul Bakara; Aya Ta 25-26 (Kashi Na 13)

Da sunan Allah Mai rahma Mai Jin kai Assalamu alaikum jama’a masu saurare, barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda, yanzu za mu saurarin karatun ayar kur’ani mai tsarki, aya ta 25 a cikin suratul Bakara: Aya ta ( 25 ) Bakara

وَبَشِّرِ الَّذِين آمَنُواْ وَعَمِلُواْ الصَّالِحَاتِ أَنَّ لَهُمْ جَنَّاتٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الأَنْهَارُ كُلَّمَا رُزِقُواْ مِنْهَا مِن ثَمَرَةٍ رِّزْقاً قَالُواْ هَـذَا الَّذِي رُزِقْنَا مِن قَبْلُ وَأُتُواْ بِهِ مُتَشَابِهاً وَلَهُمْ فِيهَا أَزْوَاجٌ مُّطَهَّرَةٌ وَهُمْ فِيهَا خَالِدُونَ Tarjama: "Kuma ka bãyar da bishãra ga wadanda suka yi ĩmãni. kuma suka aikata ayyuka na kwarai, cẽwa lallene, suna da gidãjen Aljanna, kõramu na gudãna daga karkashinsu. Ko da yaushe aka azurta su da abinci daga wasu 'ya'yan itãce daga gare su, sai su ce: "Wannan shi ne aka azurta mu da shi daga gabãnin haka," Kuma a je musu da shi yana mai kama da juna, Kuma sunã da, a cikin su, mãtan aure mãsu tsarki, kuma su, cikin su madawwama ne". Wannan ayar sabanin wadda ta gabace ta, da take yi wa kafirai barazana da azabar ubangiji mai radi, ita kuma wannan ayar tana yi muminai bushara ne da aljanna da kuma sakamako mai kyau daga Allah madaukakin sarki, sakamakon imaninsu da kuma ayyuka na gari da suka aikata a rayuwar duniya. A kowane lokaci imani da Allah yana tafiya tare da aiki na gari, ba imani kawai babu aiki na gari ba, ko kuma ana yin aikin amma babu imani, dole ne biyu su tafi tare a kowane lokaci, domin kowannensu yana matsayin cikamako ne ga dayansa. Imani tamkar wani rehsn itaciya ne, aikin na gari shi ne ‘ya’yan marmari da yake fitarwa, a lokacin da itaciya ta zama mai kyau to ya kamata ta fitar da ‘ya’ya masu kyau da dadi. Matsayin ma’abota imani a ranar kiyama da kuma sakamakonsu shi ne aljanna, a lokacin da suka ga tanadin da Allah madaukakin sarki ya yi musu na sakamon aljanna sai su ce wanna shi ne abin da Allah ya yi mana alkawali, mun kuma samu alkawalin Allah gaskiya ne. Masu imani da ayyuka na gari a ranar kiyama suna cikin farin ciki da murna d akuma annashawa, sabanin yanayin da wadanda suka kafirce wa ayoyin Allah suke ciki. Muminai suna cikin aljanna suna cin kayan marmari, koramu suna gudana akarshinsu, ga kamshi da ababen ci masu dadi da ababen kallo masu dada rai. A wasu wurare kur’ani ya yi nuni da irin ni’imomin da ke cikin aljanna, na manyan gidaje da benaye da kuma mata da lambuna da kayan marmari, a wani wurin kumaya yi nuni da abubuwan jin dadi na ma’ana, wato yardar Allah madaukakin sarki, inda yake bayyana hakan da cewa ita yardar Allah tafi komai daga dukkanin abubuwan jin dadi dake cikin aljanna. A wasu wuraren kuma yana bayyana ‘yan aljanna da cewa sun yarda da Allah shi kumaya yarda da su. Daga cikin abin da Allah zai yi wa sauran mutane shi ne su kasance tare da bayinsa na gari a cikin aljanna, ga annabawa da mazanni da waliyyai da salihai da kuma sauran bayi na gari, wanda hakan babbar falala ce ga sauran bayinsa da suka yi imanin da sakonninsa da annabawa suka zo da su. Abubuwan koyo a cikin wannan aya: 1- A lokacin tarbiya dole ne a tsawatar kuma kuma a karfafa gwiwa, ana tsawatar da kafirai kan rashin imani, ana kuma karfafa muminai kan su gaba da abin da suke yi na bin tafarkin ubangiji. 2- Alamar imani na cikin aiki na gari, saboda haka kur’ani a kowane lokaci yake gwaman imani da aiki na gari. 3- A kowane lokaci aiki na gari yana samo asali ne daga niyyar bautar Allah da tsarkake niyyar aiki saboda Allah. Saboda haka a aiki na gari shi ne aikin da aka nufi Allah da shi, aka tsarkake niyya wajen aikata shi. 4- Abubuwan da aka haramta mummini su da kuma wadanda aka halasta masa su ya kiyae su kamar yadda ubangiji ya yi umurni, a ranar kiyama Allah zai saka masa da lada mai yawa. 5- Ni’imar duniya mai gushewa ce komai yawanta, kuma ni’imar duniya sau daya tana tare da wahala da bacin rai da bakin ciki a wasu lokuta, amma ni’imar lahira ba ta gushewa, kuma tana sa’ada da farin ciki da dada rai ga wadanda suka same ta. 6- Tsakakan mata su ne wadanda suke da tsarki na rashin sabo, a ranar lahira Allah zai huwace ma ‘yan aljanna mata da ba su taba saba masa ba, tsarkaka masu kyawun halitta, sakamakon ayyuka na gari da mumunai suka aikata.

Aya ta ( 26 ) Bakarah:

إِنَّ اللَّهَ لاَ يَسْتَحْيِي أَن يَضْرِبَ مَثَلاً مَّا بَعُوضَةً فَمَا فَوْقَهَا فَأَمَّا الَّذِينَ آمَنُواْ فَيَعْلَمُونَ أَنَّهُ الْحَقُّ مِن رَّبِّهِمْ وَأَمَّا الَّذِينَ كَفَرُواْ فَيَقُولُونَ مَاذَا أَرَادَ اللَّهُ بِهَـذَا مَثَلاً يُضِلُّ بِهِ كَثِيراً وَيَهْدِي بِهِ كَثِيراً وَمَا يُضِلُّ بِهِ إِلاَّ الْفَاسِقِينَ Tarjama:

Lalle ne, Allah bã Ya jin kunyar Ya bayyana wani misãli, kõwane iri ne, sauro da abin da yake bisa gare shi. To, amma wadanda suka yi ĩmãni, sai su san cewa lalle shi ne gaskiya daga Ubangijin su, kuma amma wadanda suka kãfirta, sai su ce: "Mẽne ne Allah Ya yi nufi da wannan ya zama misãli?" yana batar da wasu mãsu yawa da shi, kuma Yana shiryar da wasu mãsu yawa da shi, kuma bã Ya batarwa da shi fãce fasikai".

Wadanda suke musu da addinin musluncici suna dag acikin dalilansu na kin amincewa da kur'ani har da yadda ake buga misali da wasu kananan abubuwa, kamar gizo-gizo da kuda da dai sauransu, inda suke ganin cewa mummunan abu ga Allah ya buga misali da kanan abubuwa irin wadanna, har ma suna cewa wannan magana ce ta mutum da ake fakewa da ita domin a dangantata da Allah a matsayin mu'ujizar tabbatar da annabcin manzon Allah da gaskiyar kur'ani, a kan haka Allah madaukakin sarki yake gaya musu cewa bay a shayin ya buga misali da karamin abu komai kankancinsa, ko da kuwa sauro ko abin da ya yi kama da hakan. Masu musu da ayoyin Allah da ma can ba su yi imani ba, saboda haka ba su da cancantar gane maganar da Allah da wadda bat a Allah ba, domin kuwa ba su san maganarsa ba, balantana salonta, kuma ga alama manufarsu ta yin hakan ita ce kokarin saka shakku cikin zuciyar manzon Allah da sauran muminai da suke tare da shi. Kuma bayan haka ma kur'ani ya buga misalai da abubuwa da dama, da cikin kuwa har da masu girma daga cikinsu, bil hasali ma dukkanin misalan da kur'ani ke bugawa suna zuwa ne daidai da abin da ya faru, wanda ake buga misali kansa, amma kafirai da sauran masu musu da ayoyin Allah ba su hankaltar hakan. Inda Allah yake buga misali da kusa, uana mai cewa wadanda kuke bauta mawa ba su iya halittar koda kuda ne, kuma da zai fada cikin wani yanayi ba za su iya tseratar da shi ba. Wannan misali ne da ke nuna ma kafirai matukar rauninsu, da ma rashin basirarsu, inda suke bauta ma wani abu dab a zai iya amfanar da kansa, ko tseratar da wani abu mai rauni daga mawuyacin hali ba. Abubuwan da za a koya a cikin wannan aya; 1- Kunya a cikin koyon lamurran addini baa bin amincewa ban e, ana yin kunya ne a cikin lamurra da suka dangaci lamurra dab a na koyon addni ko sanin shari da dokokinsa ba. 2- Dole ne a yi bayanin lamurra masu mihimmanci da salon magana mai sauki, ta kowa zai iya fahimtar abin da ake nufi. 3- Dukkanin misalan da kur'ani yake bugawa suna zuwa ne kan abubuwa masu samuwa, ba abubuwa na almara ko sake-sake ba. 4- Aikata laifukan zunubi da barna, suna hana mutum sanin hakikanin lamurra na gaskiya, suna batar da mutum daga shiriya. 5- Duk abin da ya zo daga Allah to yana bayani ne kan lamurra na gaskiya, yin riko da shi shi ne kama tafarki na gaskiya, yin watsi da shi, shi ne hakikanin bata.

Suratul Bakara; Aya Ta 27-28 (Kashi Na 14)

Da sunan Allah Mai rahma Mai Jin kai.

Assalamu alaikum jama’a masu saurare, barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda, yanzu za mu saurarin karatun ayar kur’ani mai tsarki, aya ta 27 a cikin suratul Bakara: Aya ta (27) Bakarah

الَّذِينَ يَنقُضُونَ عَهْدَ اللَّهِ مِن بَعْدِ مِيثَاقِهِ وَيَقْطَعُونَ مَا أَمَرَ اللَّهُ بِهِ أَن يُوصَلَ وَيُفْسِدُونَ فِي الأَرْضِ أُولَـئِكَ هُمُ الْخَاسِرُونَ

"Wadanda suke warware alkawarin Allah bãyan kulla shi, kuma su yanke abin da Allah ya yi umurni da shi a sãdar, kuma suna barna a cikin kasa, wadannan sũ ne mãsu hasãra".

Wannan aya mai albarka tana bayyana wasu daga cikin siffofin munafukai da suke bayyana fuska biyu a cikin lamurransu, inda suke nuna ma muminai cewa su masu imani ne, yayin da suke bayyana akasin hakan idan sun hadu da makiya muslunci. Ayar tana yin ishara ga wasu abubuwa uku dangane da munafukai. Na farko suna take alkawalinsu tsakaninsu da ubagiji, suna bin abubuwan da zukatansu suka sawwala musu. Ma’anar alkawali tsakanisu da ubangiji yana nufin alkawali dake tsakanin Allah da dukkanin talikai, domin kuwa Allah yana da alkawali tare da dukkanin talikai, wanda kuma fitira, wato tunani da hankalin dan adam a ko da yaushe suna riskar abubuwa tare da fayyace masu kyau da marassa kyau daga cikinsu, a kan haka mutum yana da dukkanin abubuwan da dukkanin abubuwan da yake buakata na gane gaskiya, da kuma karbar sakon Allah. Na biyu suna yanke duk wata dangantaka tsakaninsu da sakon Allah da ke tattare da umurninsa da haninsa, da hakan ya hada da yanke dangantaka da sakonnin manzannin Allah suka zo da su, da kuma lamurran na zamantakewa da sauran muminai. Suna yada fasadi da barna abayan kasa, domin kuwa aikin barna yana shafar rayuwar al’umma kai tsaye, ko da kuwa mai aikata hakan yana aikata barnar ne shi a kashin kansa, amma tasirin hakan zai koma ga al’umma ne, zai gurbata rayuwar zamantakewarta. A fili yake cewa Allah ba ya tilasta mutum a kan yin wani aiki, ya bar zabi ga mutum ya aikata abin ya zaba, duk kuwada cewa Allah ya bayyana ma dan adam abin da ya kamata ya yi da wanda bai kamata ba, ta hanyar aiko annabawa, amma duk da haka mutum yan ada zabi domin bin da yake so, sai dai kawai sakamakon ayyukan ne ke da banbamci a ranar kiyama, inda yake samun sakamako na aljanna da rahma daga Allah idan ya aikata kyakkyawa aduniya, kamar yadda yake samun sakamako sabanin hakan idan ya aikata mummuna a rayuwar duniya. Abubuwan koyoo daga wannan aya: 1- Addini da saba alkawali a lokaci guda ba su tafiya tare a lokaci guda, ko da kuwa wadanda aka yi alkawali da su kafirai ne. 2- Yin watsi da abin da ya kamata mutum ya yi, hakan ya kan shi zuwa ga aikata abin da bai kamata ma na sabon Allah, da fasadi a bayan kasa. 3- Babbar hasarar duniya ita ce yin fatali da umurnin Allah tare da aikata son rai. 4- Saba ma shugabanci na mazannin Allah da wadanda suka yi wasici da su saba ma Allah ne kai tsaye. 5- Addinin muslunci a koda yaushe yana shiryarwa zuwa ga kyakkyawa, yana umurnin da sada zumunci, tare da yin hani daga yanke zumunta. 6- Musulunci ya yi hani daga kaurace wa jama’a, a kan haka ne ma yake karfafa abubuwa na haduwar jama’a musulmi domin raya sha’anin addini kamar sallar juma’a da sauran tarukan addini.

A cikin addinin muslunci akwai ruwayoyi da dama kan sada zumunci tsakanin mabiya addinin muslunci da muhimmancin da ke tattare da hakan. A cikin wasu ruwayoyin ya zo cewa sada zumunci, wato ziyarar ‘yan uwa da dangi yana kawar da talauci, yana kara yawan arziki, yana kara tsawon rai, yana kara albarka a cikin rayuwa. Wasu ruwayoyin na cewa: ku sada zumunci ko da kuwa daya bangaren bai da mu da sha’aninku ba, ko da kuwa wadanda kuke sada zumunci da su ba mutanen kwarai ne ba. A wata ruwayar ku sada zumunci ko da kuwa za ku yi tafiya ta shekara guda ne kafin isa wurin sada zumuncin. A wata ruwayar mai sada zumunci mutuwa da hisabi za su zo masa da sauki, sai samu matsayi na musamman a cikin aljanna saboda wannan aiki da Allah ke so.

Yanzu kuma ga aya ta 28 daga suratul Baqarah:

كَيْفَ تَكْفُرُونَ بِاللَّهِ وَكُنتُمْ أَمْوَاتاً فَأَحْيَاكُمْ ثُمَّ يُمِيتُكُمْ ثُمَّ يُحْيِيكُمْ ثُمَّ إِلَيْهِ تُرْجَعُونَ

Yaya kuke kãfirta da Allah, alhãli kuwa kun kasance matattu sa'an nan Ya rãyar da ku, sa'nnan kuma Ya matar da ku, sa'an nan kuma Ya rãya ku, sa'an nan zuwa gare Shi ake mayar da ku?

Mafificiyar hanayar sanin Allah ita ce yin tunani kan halittunsa da kuma duniya da abin da ke cikinta, da yadda Allah ya ahalicci abubuwan da ke cikinta da kuma yadda yake tafiyarda su cikin tsari, ba tare da taimakon wani ba, yin tunani a kan mutuwa da rayuwa, da yadda Allah ya samar da rayuwa ga halittunsa da suka hada da mutane da dabbobi da sauransu, alhali kafin nan ba su da samuwa. Babbar ni’imar da Allah madaukakin sarki ya yi mana a mtasyinmu na ‘yan adam ita ce rayuwa, domin kuwa a cikinta ne muke saninsa mu bauta masa, ta hanyar rarrabe abubuwa da hankalin da ya yi mana baiwa da shi a cikin rayuwar, a matsayin jagora gare mu, , wanda zai kai mu ga yin tunain ayoyin ubangiji da suke kewaye da mu da mu a cikin rayuwar ta duniya baki daya. Rayuwa da mutuwar mutum duk suna hannun Allah, amma kuma a lokaci guda ya ba mu zabi a cikin wannan rayuwa kamar dai yadda muka yi bayani a baya, rayuwar duniya ita ce mafarin rayuwar lahira, domin kuwa ita rayuwar duniya takaitatta ce, ita kuwa rayuwar lahira ta har abada ce, kuma daga duniya ne mutum zai dora tubalin rayuwarsa ta lahira. Ga muhimamn abubuwan da za mu koya daga wannan aya mai albarka:

1- Alkur’ani mai tsarki yana yi mana ishara da cewa yin amfani da hankali da tunai shi ne mabudin kofar gane ubangiji, ta yadda mai yin amfani da su ba zai yi musun sakon ubangiji ba. 2- Rayuwa tana tabbatar da samuwar ubangiji, mutuwa kuma dalili ce na cewa lallai akwai wata rayuwa bayan rayuwar duniya. 3- Mutum ya san kansa shi fahimci shi wane ne, shi ne matakin farki na sanin mahalicci, idan ya san hakika ya karbe to zai san ubangiji kuma ya karbi sakonsa, domin Allah shi ne hakika ta gaskiya. 4- Karshen duk wata kamala ta mutum ita ce komawa zuwa ga Allah, komawa zuwa ga asalin rayuwa wadda ita ce aka halicci mutum domin kaiwa zuwa gare ta ita ce karshen kamala, ita ce kuma rayuwa ga muminai. 5- Mutuwa ba ita ce karshen rayuwa ba, a ‘a hakan farkon wata rayuwar ce bayan rayuwar duniya. 6- Wadanda suka kafirce ba su da wani dalili na kore kiyama, illa dai kawai tambayar da suke yi kan lahira ba ta ginu a kan komai ba illa shakku da taraddudi, alhali kur’ani mai tsarki ya masa tambayoyinsu a wurare daban-daban.

Suratul Bakara; Aya Ta 29-30 (Kashi Na 15)

Jama'a masu saurare barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hanunnka mai sanda ,shirin da a cikinsa muke yin bayani da dubi a cikin ayoyin alkur'ani mai girma da domin ya zama jagora a rayuwar ta dukkan bangarori. Kuma babu wani littafi da hanyar da tafi yin riko da alkur'ani da kuma tafarkin ma'aikin Allah tsira da aminci ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka kuma ko shakka babu duk wanda ya yi riko da wadannan abubuwa biyu zai samu tsira da dacewa duniya da lahira bugu da kari ya samu sauki da walwala a rayuwarsa ta wannan duniya da samin hisabi mai sauki a ranar da tsanani da kunci da damuwa ya lullube zukata da tunanin kowa. Da fatar Allah ya lullube mu da rahama da lutifinsa duniya da lahira amin. To madallah yanzu kuma za mu shiga cikin shirin gadan-gadan da sauraren aya ta 29 a cikin suratun bakara kamar haka:

هُوَ الَّذِي خَلَقَ لَكُم مَّا فِي الأَرْضِ جَمِيعاً ثُمَّ اسْتَوَى إِلَى السَّمَاء فَسَوَّاهُنَّ سَبْعَ سَمَاوَاتٍ وَهُوَ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمٌ

"(Allah) Shi ne wanda ya halicci dukkan abin da ke cikin kasa saboda ku, sannan Ya nufi (halittar) sammai bakwai, (Ubangiji) kuwa Shi ne Masanin komi".

Allah madaukakin sarki da ya halicce mutane sai ya samara mana da abubuwan jin dadin rayuwarmu abubuwan da ke kassai da samma ya mallaka mana kuma ya fifita mutum kan sauran halittu kuma dukan sauran halitta kama daga tsirre da itatuwa da duwatsu dabbabi da samma da kassai ya sa suna yi mana khidima da mallaka mana su kamar yadda ayar kur'ani ke cewa an haliccin duka abin da ke doran kasa saboda mu kamar yadda dayar ayar ke cewa dukan abin da ke samma na yin khidima a gare mu. Wannan wani dalili ne daga cikin dalilai na tauhidi domin kuwa Allah ya halicce mu don yi masa bauta da kadaita shi da bauta kuma ya halicci dukan wadannan ni'imomi don mu don ga duk wani mai hankali babu wani abi day a dace face yin godiya ga Maliccinsa da ya halicci mutum da sauran halittu a kan doran kasa da cikin sammai.Giram halittun Allah na nuni da azamar wanda ya halicce su kawai sammai guda bakwai ne Allah ya halitta bayan wannan sama ta daya da muke gani akwai wasu shidda na daban.

A cikin wannan aya ta 29 a cikin suratul ta Bakara za mu iya ilmantuwa da abubuwa biyu kamar haka:

Na farko: Shi Mutum Allah ya bashi fifiko sama da sauran halittu da ke sammai da kassai kuma wannan shi ne dalilin halittarsa domin ya bautawa Allah.

Na biyu:Allah Madaukakin sarki ya bam u zabi da falala mai girma saboda haka sai mu bautawa Allah shi kadai ba tare da mun yi masa abokinn tarayya. To madalla to za mu ci gaba da shirin na yau da sauraren aya ta 30 a cikin wannan sura ta Bakara kamar:

وَإِذْ قَالَ رَبُّكَ لِلْمَلاَئِكَةِ إِنِّي جَاعِلٌ فِي الأَرْضِ خَلِيفَةً قَالُواْ أَتَجْعَلُ فِيهَا مَن يُفْسِدُ فِيهَا وَيَسْفِكُ الدِّمَاء وَنَحْنُ نُسَبِّحُ بِحَمْدِكَ وَنُقَدِّسُ لَكَ قَالَ إِنِّي أَعْلَمُ مَا لاَ تَعْلَمُونَ

"Ka tuna) yayin da Ubangijinka Ya ce da mala'iku: Kakika Ni zan sanya halifa a cikin kasa, suka ce: " shin kuwa ka sanya mata wanda zai yi barna a cikinta kuma ya zubar da jini, alhali kuwa mu muna tasbihi don gode maka kuma muna tsarkake ka? (Sai) ya ce (da su): hakika NI Na San abin da ba ku sani ba."

A cikin ayoyin da suka gabata a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda mun yi bayani ne kan ni'imomin da Allah ya halitta masu yawa da sun fi a kilga su kuma ya halicce sun e domin yalwar falalarsa a gare mu to wannan aya tana bayani ne kan matsayi da dokarakar mutum da hassashen da mala'iku ke yi dangane da mutum. Lokacin da Allah ya halicci mutum sai ya gabatar da shi a gurin mala'iku da bayyana masu daraja da daukakarsa na zama khalifarsa a doran kasa amma mala'iku sun nuna damuwa kan hakan da dora ayar tambaya cewa: tayaya wanda zuriyarsa za ta aikata zabo da fasadi da zubar da jini a doran kasa za la ba shi matsayin khalifarka a doran kasa.Tunanin mala'iku a nan shi ne idan Allah zai ayyana wani da zama khalifarsa a doran kasa dole ya nisantu daga duk wani nauyi na sabo da fasadi kawai ya kasance mai yin biyayya tsantsa ga Allah saboda haka suka yi mamaki kan wannan lamari kuma mi yasa Allah bai bas u wannan matsayi ba ganin su masu biyayya da da'a da ibada ne ga Allah bas u kaucewa umarni da haninsa. Allah ya amsa masu da cewa ku kuna kollon dayan bangare na raunin mutum ne kawai. Ba ku da masaniya da dayan bangare na alherinsa da darajarsa kuma ni nasan abin dab a ku sani ba.Idan ku mala'iku saboda kuna yin tasbihi da ibadodi shi ne dalilin da kuke fifita kanku kan mutum da ganin kun cancanci matsayin khlifana a doran kasa to ku sani a tsakanin mutane akwai wasu salihan bayu masu daraja da suka fiku cancantar wannan matsayi na khalifana a doransa. Kuma su suna bauta mani ne karkashin zabinsu da sanin na cancanci a yi mani bauta kuma suna bauta mani ne b adon kwadayin aljanna ko tsoran azabar wutar jahannama ba.

A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu kuma sune :

Na farko: Allah n eke da iko da hakkin zabar Khalifansa a doran kasa kuma wannan wani hakki ne nasa ba waninsa ba.

Na biyu: Shi Khalifan Allah a doran kasa dole ya kasance mai adalci ba mai fasadi ba dalili da yasa mala'iku suka yi ishara kan mutum kar ya zamo mai banna a doran kasa. Da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin na yau. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barkatuhu.

Suratul Bakara; Aya Ta 31-33 (Kashi Na 16)

Jama'a masu saurare barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hanunnka mai sanda, shirin da a cikinsa muke yin bayani da dubi a cikin ayoyin alkur'ani mai girma da domin ya zama jagora a rayuwar ta dukkan bangarori .Kuma babu wani littafi da hanyar da tafi yin riko da alkur'ani da kuma tafarkin ma'aikin Allah tsira da aminci ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka kuma ko shakka babu duk wanda ya yi riko da wadannan abubuwa biyu zai samu tsira da dacewa duniya da lahira bugu da kari ya samu sauki da walwala a rayuwarsa ta wannan duniya da samin hisabi mai sauki a ranar da tsanani da kunci da damuwa ya lullube zukata da tunanin kowa. Da fatar Allah ya lullube mud a rahama da lutifinsa duniya da lahira amin.

To madallah yanzu kuma za mu shiga cikin shirin gadan-gadan da sauraren aya ta 31 da 32 a cikin wannan sura ta Bakara kamar haka:

وَعَلَّمَ آدَمَ الأَسْمَاء كُلَّهَا ثُمَّ عَرَضَهُمْ عَلَى الْمَلاَئِكَةِ فَقَالَ أَنبِئُونِي بِأَسْمَاء هَـؤُلاء إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ{31} قَالُواْ سُبْحَانَكَ لاَ عِلْمَ لَنَا إِلاَّ مَا عَلَّمْتَنَا إِنَّكَ أَنتَ الْعَلِيمُ الْحَكِيمُ{32}

"Kuma (Allah) Ya sanar da (Annabi) Adamu dukkanin sunaye sannan ya kawo su gaban mala'iku ya ce: Ku ba Ni labarin sanayen wadannan abubuwa in kun kasance masu gaskiya (cikin abin da ku ka fada). (Mala'iku) suka ce; Tsarki ya tabbata a gare Ka, ba mu san komai ba sai abin da Ka sanar da mu, Hakika Kai ne Masani Mai Hikima."

Domin Allah ya tabbatarwa da Mala'iku matsayi da darajar mutum da kuma ba shi wannan matsayi na Khalifar Allah a doran kasa sai ya jarraba kowa ne bangare daga cikin bangarorin biyu ta hanyar ilimi.Da farko ya tambayi mala'iku da su ba Shi labarin da sunayen wasu abubuwa na ilimi sai suka kasa saboda bas u sani ba.Duk da cewa Kur'ani bai bayyana sunaye da wadannan abubuwa na ilimi amma yawancin masu fassara da malamai sun cewa;duniya da dabi'a da wasu halittu day a ilmantar da shi mutum da sunayansu karkashin karfi da ikon fahimta da Allah ya bashi.Idan kuna ganin kunfi mutum saboda ibadodi to sai ku ba ni labarin sunayen wadannan abubuwa kuma idan abin da kuke rayawa gaskiya ne sai ku bani labarin wadannan abubuwa da na sanar da ku.Nan mala'iku suka fahimci abin da suke rayawa ba gaskiya ne ba ibadda da tsbihi kadai bay a zama dalili na fifiko kuma Khalifan Allah a doran kasa dole ya zama yanada matsayi da daraja ta ilimi da sani na hakika da amsa cewa: Allah kai ne mai hikima kuma mun yi imani da yakini kan halittar mutum na cikin hikima da daukaka.Kuma tambayar mu a gare ka tana kan kuskure da rashin sani. A cikin wannan aya ta 31 da 32 a cikin suratul hudu za mu iya ilmantuwa da abubuwa uku kamar haka:

Na farko: Allah ne farkon malamin day a koyar da mutum da ya ba shi karfin fahimta da karfin sani da hankali da hazaka.

Na biyu: Mutum yana da karfi da ikon fahimtar duk kowane irin ilimi da kuma koyar da shi da kuma Allah ne ya bashiwannan falala da albakatarsa da haka.

To madalla to za mu ci gaba da shirin na yau da sauraren aya ta 33 a cikin suratul bakara :

قَالَ يَا آدَمُ أَنبِئْهُم بِأَسْمَآئِهِمْ فَلَمَّا أَنبَأَهُمْ بِأَسْمَآئِهِمْ قَالَ أَلَمْ أَقُل لَّكُمْ إِنِّي أَعْلَمُ غَيْبَ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ وَأَعْلَمُ مَا تُبْدُونَ وَمَا كُنتُمْ تَكْتُمُونَ

"(Allah) Ya ce: Ya kai Adamu, ba su labarin sunayensu, Sannan lokacin da ya ba su labarin sunayensu (Sai Allah) Ya ce; Ashe ban gaya muku ba ( tuni) cewa Ni Na san abin da yake boye a sammai da kassai, kuma Na san abin da ku ke bayyanawa da kuma abin da ku ke kasancewa kuna boyewa.

Wannan aya tana bayani kan nasara da daukakar da mutum ya sami karkashin ilimin da Allah ya sanar da shi da sanin abubuwa na badini day a sanar da mala'iku abin dab a su sani bad a samin ilimi ta hanyar mutum da kuma Allah ne ya bawa mutum karfin fahimta sabanin mala'iku.Bayan wannan jarabawa sai Allah madaukakin sarki ya cewa mala'iku: Kuna zaton kufi sauran halittun da Allah ya halitta daukaka da daraja da bauye hakan a cikin zukatanku da kasa bayyana hakan a karara to ku sani Allah masanin abubuwan da ke boye da sarari ne .kuma abin da ke cikin zukatanku ina sane da shi kuma ina sane da abin da ke boye a cikin zukatan dukan halittu babu abin da yake boyuwa a gare ni. Wannan aya tana jaddada mana cewa; Allah masanin abubuwan da ke boye da sarari ne sabanin mutane da mala'iku masu aiki da kawai abubuwan da ke sarari ko wanda Allah ya ilmantar da su karkashin lutifi da hikimarsa.

A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu kuma sune :

Na farko: Mutum ya zarta mala'ika ta fuskar karfin fahimta da kaifin ilimi saboda haka ne ma abubuwa da mala'iku bas u sani ba Annabi adam ne yak e bas u labarinsu da ilmantar da su.

Na biyu:A duk lokacin da ake son sani karfin sani da fahimtar mutum ko wani abu ana jarraba shi da kwada shi dalilin day a sa Allah ya tambayi mala'iku da suka kasa amsawa sai ya tambayi Adam sai ya amsa. Da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin na yau kafin wani mako wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barkatuhu.

Suratul Bakara; Aya Ta 34-35 (Kashi Na 17)

Jama'a masu saurare barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hanunnka mai sanda ,shirin da a cikinsa muke yin bayani da dubi a cikin ayoyin alkur'ani mai girma da domin ya zama jagora a rayuwar ta dukkan bangarori. Kuma babu wani littafi da hanyar da tafi yin riko da alkur'ani da kuma tafarkin ma'aikin Allah tsira da aminci ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka kuma ko shakka babu duk wanda ya yi riko da wadannan abubuwa biyu zai samu tsira da dacewa duniya da lahira bugu da kari ya samu sauki da walwala a rayuwarsa ta wannan duniya da samin hisabi mai sauki a ranar da tsanani da kunci da damuwa ya lullube zukata da tunanin kowa. Da fatar Allah ya lullube mu da rahama da lutifinsa duniya da lahira amin.

To madallah yanzu kuma za mu shiga cikin shirin gadan-gadan da sauraren aya ta 34 a cikin suratul Bakara kamar haka:

وَإِذْ قُلْنَا لِلْمَلاَئِكَةِ اسْجُدُواْ لآدَمَ فَسَجَدُواْ إِلاَّ إِبْلِيسَ أَبَى وَاسْتَكْبَرَ وَكَانَ مِنَ الْكَافِرِينَ Kuma (ka tuna ya Muhammadu)lokacin da Muka ce da Mala'iku: Ku yi sujjada ga Adamu, sai ku ka sujjada in ban da Iblis da ya ki, ya kuma yi girman kai kuma ya kasance a cikin kafirai.

A cikin shirin da ya gabata mun kawo ayoyin da ke bayani kan ni'imomin na zahiri da jin dadin wannan duniya da Allah ya huwacewa bayunsa mutane a doran kasa da kuma ayoyin da suka yi bayani kan yadda Allah ya aina adam a matsayin khalifansa a doran kasa da hakan yak e nuni da karamcin da Allah ya yi masa to wannan aya kuma tana bayani ne kan wata karama da girmamawa da Allah tabaraka wata'ala ya bawa bawonsa kakanmu Adam inda ya umarci mala'iku da su yi masa sajada ta girmamawa kamar yadda ayoyi da dama suka yi bayani kan wannan matsayi da karamci da Allah ya bawa kakanmu Adam da sauran karamomi makamantan haka kuma wannan umarni shi ke nuni da matsayinsa Adam na khalifan Allah a doran kasa da yadda mala'iku suka bi wannan umarni suka yi wa Adam sajada ta girmamawa da kuma yadda Shaidan ya ki bin wannan umarni da nuna girman kai da dagawa da hakan ya kai shi ga hallaka duniya da lahira. A ayoyin da suka gabata suna Magana da bayani kan ni'imomin mada da na ma'anawiya da Allah madaukakin sarki ya wadatar da mutum da kuma ba shi matsayin khalifarsa a doran kasa amma ita wannan aya tana bayani ne kan wani matsayin ga Adam da Allah ya ba shi wanda mala'iku suka yi masa sajada ta girmamawa. Kamar yadda aya a cikin Hijir da Sad suka yi bayani kuma suka yi masa sajda ta girmamawa yayin da a cikin aya ta hamsin a cikin suratul Kahaf Iblis wanda yake cikin jinsin Aljannu ya ki yin sujadar ma'ana ya bijirewa umarnin Allah day a halicce shi da jiji da kai da nuna hassda ga Adam. Kuma wannan shi ne dalilin tabewar Iblis wanda ya share shekaru yana bautawa Allah amma kin yin sujada ga Adam da Allah ya umarce shi ya sa ya tabe duniya da lahira.

A cikin wannan aya ta 34 a cikin suratul Bakara za mu iya ilmantuwa da abubuwa uku kamar haka:

Na farko: ibada ta gaskiya it ace da mutum yake yi karkashin umarnin Allah da hanin Allah ba wai son zucciya da ra'ayinsa.Iblisa ya yi shekaru yana yin ibada ga Allah rashin yin sujjada da kin bin umarnin Allah ya rusa komi saboda son zucciya.

Na biyu:Girman kai da jiji da kai da kin bin gaskiya da fahimtar yana kai mutum da aljani zuwa ga hallaka da kaucewa daga kan hanyar addini da gaskiya.

To madalla to za mu ci gaba da shirin na yau da sauraren aya ta 35 a cikin wannan sura ta Bakara :

وَقُلْنَا يَا آدَمُ اسْكُنْ أَنتَ وَزَوْجُكَ الْجَنَّةَ وَكُلاَ مِنْهَا رَغَداً حَيْثُ شِئْتُمَا وَلاَ تَقْرَبَا هَـذِهِ الشَّجَرَةَ فَتَكُونَا مِنَ الْظَّالِمِينَ

Kuma Muka ce: Ya kai Adamu ka zauna (cikin) Aljanna kai da matarka kuma ku ci (komi) mai dadi daga gare ta a duk inda kuke so kada kuma ku kusanci wannan bishiyar (idan kuka kusance ta) sai , ku kasance daga cikin azzalumai.

Allah madaukakin sarki da ya halicci adam daga turba da kasa domin ya zama khalifarsa a doran kasa kuma domin ya wadata shi da ni'imomin rayuwa ya halicci matarsa Hawa daga shi kansa Adam don zame masa abukkiyar zama da samara da zuriya mai yawa da zama cikin aljanna da za su ci da sha a cikinta.Ta haka Allah ya cika ni'imominsa ga Adam da matarsa.Kuma wannan ba yana nufin duk wani abu na cid a sha yana yin amfani ga jikin dan adam dalilin day a sa ken an Allah ya hana adam da matarsa kusantar wannan itaciya da kuma ci daga wannan itaciyar saboda idan suka ci wannan itaciya za su cutar da kansu ne da kuma zai yi sanadiyar fitarsu daga cikin wannan aljanna ta ni'ima kuma wannan na bayyana cewa aljannar da aka fitar da Adam da matarsa ba it ace aljannar da aka yi mana tanadi a gobe kiyama dalili na farko ita Aljannar Lahira sakamakon aiki ne har yanzu babu wani aiki da Adam ya yi balantana a saka masa da gidan aljanna kamar yadda aya ta 142 a cikin suratul Ali Imrana na biyu ita aljannar Lahira duk wanda ya shige ta baya fita kamar yadda aya ta 48 a cikin suratul hijir ke yin bayani. Na uku a cikin aljannar lahira babu wata itaciya da aka hana ci saima komi a cikinta halaliya ne duk wanda mutum yaga dama sai ya ci.A wani bangare hatta guri mai ni'ima da tsanwa shar a wannan duniya Allah yana kiransa da Aljanna saboda haka wannan kalma bat a kadaita da aljannar da aka yi mana tanadi ba.

A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu kuma sune :

Na farko: Mata, muhalli,abinci da ruwa da sauransu ni'imomi ne da Allah ya huwacewa mutum domin ya ji dadin rayuwarsa da jin dad a doran kasa da sammai da kuma hakan zai kara masa karfin guiwar bautawa Allah.

Na biyu: Aikata sabon da Allah ya hana ,cutarwa tana komawa ne ga mutum saboda haka ne Allah ya hana Adam kusantar itaciya a maimakon ya ce kar ku ci wannan itaciya.

Da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin nay au kafin wani mako da yardarm Allah mai ikon linfashin taliakai, ni tidjani malam Lawali damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barkatuhu.

Suratul Bakara; Aya Ta 36-37 (Kashi Na 18)

Jama'a masu saurare barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hanunnka mai sanda ,shirin da a cikinsa muke yin bayani da dubi a cikin ayoyin alkur'ani mai girma da domin ya zama jagora a rayuwar ta dukkan bangarori. Kuma babu wani littafi da hanyar da tafi yin riko da alkur'ani da kuma tafarkin ma'aikin Allah tsira da aminci ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka kuma ko shakka babu duk wanda ya yi riko da wadannan abubuwa biyu zai samu tsira da dacewa duniya da lahira bugu da kari ya samu sauki da walwala a rayuwarsa ta wannan duniya da samin hisabi mai sauki a ranar da tsanani da kunci da damuwa ya lullube zukata da tunanin kowa. Da fatar Allah ya lullube mud a rahama da lutifinsa duniya da lahira amin.

To madallah yanzu kuma za mu shiga cikin shirin gadan-gadan da sauraren aya ta 36 a cikin suratul Bakara kamar haka: فَأَزَلَّهُمَا الشَّيْطَانُ عَنْهَا فَأَخْرَجَهُمَا مِمَّا كَانَا فِيهِ وَقُلْنَا اهْبِطُواْ بَعْضُكُمْ لِبَعْضٍ عَدُوٌّ وَلَكُمْ فِي الأَرْضِ مُسْتَقَرٌّ وَمَتَاعٌ إِلَى حِينٍ

Sai Shaidan ya juyar da su suka bar ta ta hanyar sa masu waswasi sannan ya fitar da su daga abin da suka kasance a cikinsa (Aljanna) kuma sai Muka ce (da Adamu da Hawwa'u): Ku sauka (daga cikinta) sashinku suna masu gaba da sashi, kuna da gurin zama a cikin kasa da kuma abin jin dadi na zuwa wani dan lokaci.(kayyadajje).

A cikin shirye-shiryen da suka gabata mun yi bayani ne kan halitta da khalifancin Adam a doran kasa da kuma yadda shi adam da matarsa Allah ya ni'imce su da yayan marmari da itatuwa na ni'ima da wadatar da su da komi na wadata face itaciya guda day a hana su ci saboda cin wannan itaciya za su cutar da kansu da zaluntar kansu.Amma Shaidan da ya bijirewa umarnin Allah na yin sijadar girmamawa ga Adam aka kore shi da la'antarsa yana neman hanyar cutar da Adam sai ya dauki niya da bin hanyoyi da salon ganin ya yi sanadiyar fitar da Adam da matarsa daga wannan aljanna ta kwanciyar hankali da nucuwa,saboda haka ya yi ta sanya wasiwasi da siffanta wannan itaciya da cewa adam da matarsa Hawa cewa cin wannan itaciya nada amfani mai yawa a gare su.Adam da hawa sun ci wannan itaciya neb a da nufin bijirewa umarnin Allah ne ba tamakra yaron da bai saba da karya ba da yaudara yana kollon kowa tamkarsa masu gaskiya kuma lokacin da Shaidan ya rantse masu da cewa alherin da ya gaya masu kan wannan itaciya gaskiya ne sai suka yarda.Cin wannan itaciya ked a wuya sai aka fitar da su daga wannan aljanna da nisanta da kusancin Allah kuma ba don sun aikata sabo ba sai dai saboda sun cutar da kansu kuma kiyayya a tsakanin mutum da shaidan za ta ci gaba har ranar tashin kiyama. Kuma tun farko an halicci adam ne domin rayuwa a doran kasa kuma da farko yana bukatar wani guri da zai rayuwa da sabawa da matsaloli da hakan zai ba shi damar rayuwa a doran kasa da sanin makiyinsa na hakika shaidan. A cikin wannan aya ta 36 a cikin suratul Bakara za mu iya ilmantuwa da abubuwa uku kamar haka:

Na farko: Yin biyayya ga Shaidan bayan yana nisantar da mutum daga kusanci da Allah da samin matsayi a gurinsa yana kuma rusa masa jin dadi da kwanciyar hankali da samara masa da matsaloli masu yawa .

Na biyu: wannan duniya da rayuwa a cikinta na wani gajeran lokaci ne saboda haka mutum mai hankali da hangen nesa sai ya yi wa makomarsa ta har abada tanadi da guzuri na alheri. To madalla to za mu ci gaba da shirin na yau da sauraren aya ta 37 a cikin wannan sura ta Bakara:

فَتَلَقَّى آدَمُ مِن رَّبِّهِ كَلِمَاتٍ فَتَابَ عَلَيْهِ إِنَّهُ هُوَ التَّوَّابُ الرَّحِيمُ

Sai Adamu ya samo kalmomi daga Ubangijinsa (wadanda ya nemi gafara da su) sai Allah ya karbi tabarsa, hakika shi (Ubangiji) Mai yawan karbar tuba ne, Mai yawan jin kai.

Bayan fitar da Adam da matarsa daga aljannar ni'ima da samin kansa a doran kasa gidan wahala da matsaloli,sai Adam ya fahimci kuransa da kuma yaudarar da Shaidan ya yi masa saboda haka yayi nadama kan aikinsa da tunanin hanyar tuba to amma ta yaya ne zai tuba Allah ya karbi tubarsa da samin kusanci da Mahaliccinsa? Allah mai rahama da lutifi bai bar Adam shi kadai bay a ilmantar da shi kalmomi da na neman tuba da rahamar Allah ya yi amfani da su kamar yadda ya zo a cikin suratul A'araf aya ta 23 cewa sai suka ce Ubangijinmu mun zalumci kanmu kuma idan ba ka yafe mana bad a rahamshe mu lalle za mu kasance daga cikin tababbu.Irin wadannan kalamomi ba wai kawai Adam ne ya yi anfani da sub a hatta Annani Yunus da Annabi Musa (AS) sun yi amfani da irin wadannan kalmomi.A cikin tafsirin Siyuti a littafin tafsirinsa na Durrul mansur jildi na daya shafi na satti ya kawo cewa ruwayoyi da dama sun bayyana cewa Adam y agama Allah ne da darajar Annabi Muhammadu da zuriyarsa kafin a yafe masa kuma akwai ruwayoyi da dama da suka yi bayani kan hakan.

A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu kuma sune :

Na farko:Idan mutum da gaske yake a lokacin da yake furta kalmomin tuba to Allah yana karbar tubarsa da yafe masa kurakuran day a aikata.

Na biyu: Karbar tubar mutum daga Allah tana tare da rahama da falalar Allah da kuma kauna kuma yana karbar tubarmu a kullum saboda lutifinsa da rahamarsa.

Da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin nay au kafin wani mako da yardar Allah mai ikon linfashin taliakai ,ni tidjani malam Lawali damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barkatuhu.

Suratul Bakara; Aya Ta 38-39 (Kashi Na 19)

Jama'a masu saurare barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hanunnka mai sanda ,shirin da a cikinsa muke yin bayani da dubi a cikin ayoyin alkur'ani mai girma da domin ya zama jagora a rayuwar ta dukkan bangarori .Kuma babu wani littafi da hanyar da tafi yin riko da alkur'ani da kuma tafarkin ma'aikin Allah tsira da aminci ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka kuma ko shakka babu duk wanda ya yi riko da wadannan abubuwa biyu zai samu tsira da dacewa duniya da lahira bugu da kari ya samu sauki da walwala a rayuwarsa ta wannan duniya da samin hisabi mai sauki a ranar da tsanani da kunci da damuwa ya lullube zukata da tunanin kowa. Da fatar Allah ya lullube mud a rahama da lutifinsa duniya da lahira amin.

To madallah yanzu kuma za mu shiga cikin shirin gadan-gadan da sauraren aya ta 38 a cikin suratul Bakara kamar haka:

قُلْنَا اهْبِطُواْ مِنْهَا جَمِيعاً فَإِمَّا يَأْتِيَنَّكُم مِّنِّي هُدًى فَمَن تَبِعَ هُدَايَ فَلاَ خَوْفٌ عَلَيْهِمْ وَلاَ هُمْ يَحْزَنُونَ

Mu ka ce;Ku sauka daga cikinta ( Aljannar) gaba daya, sannan idan lalle shiriya ta zo muku daga gare Ni wadanda suke bin shiriyata. babu tsoro a gare su kuma ba za su yi bakin ciki ba.

Duk da cewa an karbi tubarsa Adam amma sai aka fitar da shi daga doran kasa kuma babu shi babu komawa a cikin wannan aljanna ta itatuwa da ilmantar da mutum cewa yafewa da karbar tuba ba yana nunfin asar na liafin da karbar tuba akawai dangantaka ta kud da kud ma'ana fitar da Adam daga Aljanna na yin bayani da cewa asar na halin day a ke ciki sakamakon cin wannan itaciya da aka hana shi tuba ba ta canja shi saboda haka ta kowa ne hali Adam da matarsa sai sun fita daga cikin wannan aljanna da rayuwa a doran kasa da babu irin wannan ni'ima.Kuma fitar da shi daga aljanna yana nufin shi da zuriyarsa domin neman shiriya ta hanayr aiko da annabawa da manzonni da littafi duk wanda ya bi su zai samu shiriya wannan kuma ya ki zai tabe saboda haka mutane kashi biyu ne mutanan kirki shiryyayu wadanda suka amsa kiran Annabawa da littafin Allah sai kuma kaso na biyu wannan ya bijirewa kiransu.

A cikin wannan aya ta 38 a cikin suratul Bakara za mu iya ilmantuwa da abubuwa uku kamar haka: Na farko: wani lokaci kuskure daya yana shafar dukan zurriya da sauran al'ummomi kamar yadda Adam kusantar itaciya da yayi ta shafi zuriyarsa na fitar da su daga cikin Aljanna.

Na biyu:Rahama da lutifin Allah a kullum yana tare dad an adama ba ya nisa da shi kuma yana samara masa da hanyar fita da hanyar tuba daga kurakuran day a aikata .

To madalla to za mu ci gaba da shirin na yau da sauraren aya ta 39 a cikin wannan sura ta Bakara:

وَالَّذِينَ كَفَرواْ وَكَذَّبُواْ بِآيَاتِنَا أُولَـئِكَ أَصْحَابُ النَّارِ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ

Kuma wadanda suka kafirta suka karyata ayoyinmu,wadannan su ne 'yan wuta suna masu dawwama a cikinta.

Wannan aya tana bayani ne kan dayan bangare ko gungu bayan wadanda suka karbi shiriya daga Allah madaukakin sarki karkashin yarda da zabinsu da alheri ke riskarsu akwai dayan gungun na mutane wanda ya kafirce da bjirewa ayyoyin Allah da yin jayayya da karyata ayoyin Allah ido rufe.Dalilan shiriya da bayanai masu gamsarwa a cikin ayoyin allah a fili karara su ke amam wadana ya rungumi kafirci da kin gaskiya bayan yaki bin gaskiya da shiriya yana kuma karyatawa da musamnta danganta hakan da Allah to irin wannan mutane kafire makomarsu wuta ce a ranar tashin kiyama domin itace makomar masu jayayya da nuna kiyayya ido rufe da kuma za su dauwama a cikinta kuma nan ne makomarsu.

A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu kuma sune :

Na farko:Hatta Kafirai Allah yana samara masu da hanyar shiriya da samin tsira amma sune suke kin bin hanyar shiriya da hallakar da kansu da kansa.

Na biyu:Rahamar Allah tana shafar kowa da kowa ne mumuni da kuma kafiri a wannan duniya.

Da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin nay au kafin wani mako da yardarm Allah mai ikon linfashin taliakai ,ni tidjani malam Lawali damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barkatuhu.

Suratul Bakara; Aya Ta 40-43 (Kashi Na 20)

Jama'a masu saurare barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hanunnka mai sanda ,shirin da a cikinsa muke yin bayani da dubi a cikin ayoyin Alkur'ani mai girma da domin ya zama jagora a rayuwar ta dukkan bangarori .Kuma babu wani littafi da hanyar da tafi yin riko da alkur'ani da kuma tafarkin ma'aikin Allah tsira da aminci ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka kuma ko shakka babu duk wanda ya yi riko da wadannan abubuwa biyu zai samu tsira da dacewa duniya da lahira bugu da kari ya samu sauki da walwala a rayuwarsa ta wannan duniya da samin hisabi mai sauki a ranar da tsanani da kunci da damuwa ya lullube zukata da tunanin kowa. Da fatar Allah ya lullube mud a rahama da lutifinsa duniya da lahira amin. To madallah yanzu kuma za mu shiga cikin shirin gadan-gadan da sauraren aya ta 40 da 41 a cikin suratul Bakara kamar haka:

يَا بَنِي إِسْرَائِيلَ اذْكُرُواْ نِعْمَتِيَ الَّتِي أَنْعَمْتُ عَلَيْكُمْ وَأَوْفُواْ بِعَهْدِي أُوفِ بِعَهْدِكُمْ وَإِيَّايَ فَارْهَبُونِ{40} وَآمِنُواْ بِمَا أَنزَلْتُ مُصَدِّقاً لِّمَا مَعَكُمْ وَلاَ تَكُونُواْ أَوَّلَ كَافِرٍ بِهِ وَلاَ تَشْتَرُواْ بِآيَاتِي ثَمَناً قَلِيلاً وَإِيَّايَ فَاتَّقُونِ{41}

40-Ya ku 'ya'yan Isra'ila ( wato 'yayan Yakubu), ku tuna ni'imata wadda Na ni'imta ku da ita, kuma ku cika alkawarinku, kuma Ni kadai za ku ji tsorona. 41- Kuma ku ba da gaskiya da abin da Na saukar (Alkur'ani), mai gaskanta abin da yake tare da ku, kada kuwa ku kasance farkon masu kafircewaa da shi (Alkur'ani), kar kuma ku sayar da ayoyina da 'yan kudi kadan, kuma Ni kadai za ku kiyaye ( ku ji tsoro na Ni kadai Kawai).

Bayan ayoyin da suka yi bayani da kawo kissar Annabi adam da yadda mala'iku suka yi masa sajada da kuma yadda Iblisa ya ki yi masa sajada da kuma yadda ya yaudare su har aka fitar da Adam da Matarsa Hauwa daga alajanna da kuma sauran ni'imomi da darajoji da Allah yaw a Adam to wadannan ayoyi kuwa na bayani ne kan kissar bani Isra'ila da suma kissarsu ta yi kama da ta Adam domin kuwa Allah ya yi masu ni'imomi masu yawa amma suna mantawa da kin godewa Allah kuma su bani Israila yaya ne daga cikin yayan Adam (AS) kuma sun samo wannan suna ne daga Annabi Yakub (AS) domin kuwa bani Israila yayan Annabi Yakub (AS) ne ake yiwa lakabi da hakan kuma ayoyi da dama sun yi Magana da bayani kan wannan suriya kuma a cikin wadannan ayoyi Allah yana tunatar da sun e da ni'imomin day a yi masu da yadda ya nuna masu kauna da kuma ya kamata ko wajibi su gode masa amma sun gagara yin haka.

A cikin wannan aya ta 40 da 41 a cikin suratul Bakara za mu iya ilmantuwa da abubuwa uku kamar haka:

Na farko: Ni'imomin da Allah ya huwace mana mud a iyalanmu da al'ummarmu sai mu rika bayyanawa domin wannan ma wata hanya ce ta godewa Allah da fadakar dam u da kuma sauran mutane kan ni'imomin day a yi mana.

Na biyu: Kar mu ji tsoro da kumyar wani kowa ne shi idan lamarin ya shafi sauke nauyi da takalifin da Allah ya umarce mu da shi kuma kar dukiya da kudi da kuma makami su sa mu kafircewa Allah.

To madalla to za mu ci gaba da shirin na yau da sauraren aya ta 42 da kuma 43 a cikin wannan sura ta Bakara :

وَلاَ تَلْبِسُواْ الْحَقَّ بِالْبَاطِلِ وَتَكْتُمُواْ الْحَقَّ وَأَنتُمْ تَعْلَمُونَ{42} وَأَقِيمُواْ الصَّلاَةَ وَآتُواْ الزَّكَاةَ وَارْكَعُواْ مَعَ الرَّاكِعِينَ{43}

42-Kuma kada ku cudanya gaskiya da karya, (kada) kuma ku boye gaskiya, alhali kuwa ku kun san (wannan yana cikijn littafinku). 43- Kuma ku tsada salla kuma ku ba da zakka kuma ku yi ruku'u tare da masu yin ruku'i (watau ku yi salla tare da masu salla).

Wannan aya tana ilmantar da mu da kuma fadakar dam u muni da kuma girman laifi a cikin al'umma kan yadda masana da malamai da kuma shugabanni za su boye gaskiya da adalci a maimaikon sun gayawa al'umma da sauran mutane gaskiya da kuma sa su kan hanyar gaskiya da shiriya a'a sai su rike batar da su da umurtar su kan aikata bata da sabo a doran kasa to wannan wani babban liafi ne da kr da girman gasket domin kuwa sauran Al'umma za su fada cikin batan da ba su ne sanadinsa ba kuma kan jahilci alhali magabata da shugabanninsu da malamai sun san da hakan.Kuma ya kamata malamai da shugabanni da sauran jagororin al'umma su gaya wa sauran mutane gaskiya da ba su damar zabar hanya ta gaskiya ba su boye masu gaskiya da bayyana masu bata ba,to wannan zalunci ne a fili karara.

A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu kuma sune :

Da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin na yau kafin wani mako da yardar Allah mai ikon linfashin taliakai, ni tidjani malam Lawali damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barkatuhu.

Suratul Bakara; Aya Ta 44-47 (Kashi Na 21)

Jama'a masu saurare barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hanunnka mai sanda ,shirin da a cikinsa muke yin bayani da dubi a cikin ayoyin alkur'ani mai girma da domin ya zama jagora a rayuwar ta dukkan bangarori. Kuma babu wani littafi da hanyar da tafi yin riko da alkur'ani da kuma tafarkin ma'aikin Allah tsira da aminci ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka kuma ko shakka babu duk wanda ya yi riko da wadannan abubuwa biyu zai samu tsira da dacewa duniya da lahira bugu da kari ya samu sauki da walwala a rayuwarsa ta wannan duniya da samin hisabi mai sauki a ranar da tsanani da kunci da damuwa ya lullube zukata da tunanin kowa. Da fatar Allah ya lullube mu da rahama da lutifinsa duniya da lahira amin.

To madallah yanzu kuma za mu shiga cikin shirin gadan-gadan da sauraren aya ta 44 zuwa 45 a cikin suratul Bakara kamar haka:

أَتَأْمُرُونَ النَّاسَ بِالْبِرِّ وَتَنسَوْنَ أَنفُسَكُمْ وَأَنتُمْ تَتْلُونَ الْكِتَابَ أَفَلاَ تَعْقِلُونَ{44} وَاسْتَعِينُواْ بِالصَّبْرِ وَالصَّلاَةِ وَإِنَّهَا لَكَبِيرَةٌ إِلاَّ عَلَى الْخَاشِعِينَ{45}

44-Yanzu kwa rika umartar mutane da kyawawan ayyuka kuna kuma mantawa da kanku, alhali kuwa ku kuna karanta littaiun (Attaura). Yanzu ba za ku hankalta ba? 45-Kuma ku nemi taimako (a kan gyra kanku)ta hanyar hakuri da kuma salla. Hakika kuwa ita (salla) ba sahkka aba ce mai wuya, sai dai ga masu tsoron (Allah).

A cikin ayoyin da suka gabata a shirin da ya gabata suna bayani ne kan yadda Allah yak e Magana dam asana daga cikin Yahudawa da cewa: mene ne ya sa kuke boye gaskiya ba ku shaidawa mutane kuma ba ku bawa mutane damar sanin gaskiya da zabin bin abin day a kwanta masu a zucciya to wadannan ayoyin ma sun ci gaba da yin bayani da kalubalantar masanan da cewa: ku da kuka kasance kuna yi wa mutane bushara da bayyanar Annabi Muhammadu kafin bayyanarsa kuma kuna kiransu da su yi imani da shi to me ya sa ku ba ku yin imani da shi alhali kuna da ilimi da masaniya kan abubuwan da ke cikin Attaura.Duk da cewa zahirin wannan aya tana Magana ne kai tsaye da bani Isra'ila dam asana ko malamai daga cikinsu to amma a gaskiya tana Magana ne ga duk wani malami da mai yadda addini a musulunci ne ko yahudanci da kiristanci da sauran addinai.Imam Ja'afar Sadik (AS) daya daga cikin malamai shiriya na gidan Manzon Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi dangane da haka yana cewa: ku kira yi mutane zuwa gare ku ta hanyar aikin alhaeri bat a hanyar Magana ba aikatawa ba. Amirul muminina Imam Ali (AS) yana cewa: Yak u mutane ku sani na rantse da Allan day a halicce ni babu wani abu day a shafi da'a da na ke kiranku da aiaktawa da gwadaitar da ku face na aikata hakan kafin in bukace ku da aikatawa kuma babu wani sabo da na ke kiranku da kaucewa aikata shi face na hana kaina aikatawa.

To madalla to za mu ci gaba da shirin na yau da sauraren aya ta 46 da kuma 47 a cikin wannan sura ta Bakara:

الَّذِينَ يَظُنُّونَ أَنَّهُم مُّلاَقُوا رَبِّهِمْ وَأَنَّهُمْ إِلَيْهِ رَاجِعُونَ{46} يَا بَنِي إِسْرَائِيلَ اذْكُرُواْ نِعْمَتِيَ الَّتِي أَنْعَمْتُ عَلَيْكُمْ وَأَنِّي فَضَّلْتُكُمْ عَلَى الْعَالَمِينَ{47}

46-(Su ne) wadanda sukasakankace cewa su za su sadu da Ubangijinsu kuma lalle su wurinsa za su koma. 47-(Allah yana cewa): Ya ku 'ya'yan Isra'ila, ku tuna ni'imantawadanda Na ni'imanta ku da ita, hakika kuwa Na fifita ku a kan sauran halittu (na zamaninku).

Wadannan ayoyi na magana da bayani ne kan matsayin sallayi da hakuri da kuma duk da cewa abubuwa masu nauyi da tsanani amma hakan alheri babba da kuma matsayi mai girma ga masu tsoran Allah.Sai kuma aya ta biyo baya ta arabayi da 46 da muka saurara da ke Magana da bayani kan masu tsoran Allah da suka tsoran ranar gamuwa da Allah a wannan rana mai girama wadanda suka yi imani da Allah da kuma ranar tashin kiyama masu kaskantar da kai da takawa da jin suna da nauyi a aknsu masu tanadin amsoshin da za su bayar a wannan rana da kowa zai amsa aikin day a aikata a wannan duniya.Sai kuma aya ta 47 da take Magana har ila yau kan bani Isra'ila da tunatar da su ni'imomin da Allaha ya yi masu da kuma yadda ya fifita su da ni'imomi kan sauran da hakan ke a matsayin babbar hanya ta jarraba su da kuma gwaji kansu matukar ba su yi aiki da wadannan ni'imomi to za su hallaka duniya da lahira da kuma tabewa da yin nadama ta karshe. Da fatar Allah ya kiyashe mud a yin nadama duniya da lahira amin.

A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu kuma sune :

Na farko:Hanya mafi kyau ta kiran sauran mutane zuwa ga aikata aikin Alheri ita ce aikata aikin alheri ba wai fadi da baki ba babu aikatawa mana mu fadi amma bamu aikatawa.

Na biyu: domin yin nasara kan matsalolinmu akwai abubuwa biyu na farko: samin galaba a zucciya ta hanyar hakuri da tsayin daka na biyu: yin salla da samin kusanci da Allah.

Da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin na yau kafin wani mako da yardar Allah mai ikon linfashin taliakai, ni tidjani malam Lawali damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barkatuhu.

Suratul Bakara; Aya Ta 48-52 (Kashi Na 22)

Assalamu alaikum masu saurare a cikin shirimmu na hannunka mai sanda zamu dubu ayoyi 48 zuwa karshen aya ta 52 na surar bakara. Yanzu bari mu saurari karatun aya ta 48 na cikin surar bakara.

وَاتَّقُواْ يَوْماً لاَّ تَجْزِي نَفْسٌ عَن نَّفْسٍ شَيْئاً وَلاَ يُقْبَلُ مِنْهَا شَفَاعَةٌ وَلاَ يُؤْخَذُ مِنْهَا عَدْلٌ وَلاَ هُمْ يُنصَرُونَ

" Ku tsoraci ranar da wani rai ba zai amfana wa wani rai komai ba, kuma ba za a karbi ceto daga gares hi ba, kuma ba za a karbi fansa daga gare shi ba, su kuma ba za a taimaka musu ba".

Wannan ayar tana Magana kan abubuwa guda 4 dangane da mummunar akidar mutane kan ranar kiyama. Ayar tana musanta akidar yahudawa ta cewa iyayensu da manya manyansu zasu iya tunkude masu azaba a ranar kiyama . Ko kuma abokai da kudi suna iya fansarsu daga azabar Allah a rannar. A jawabin da alkur’ani ya bawa wadan nan mutane ya zo cewa. A rannan babu wani ko wani abu da zai iya fansar wani mai sabo daga azabar Allah. Kuma a rannan ko wace rai tana ta kanta ne. Don haka kada ku dogara sai kan imanin da ayyuka na gari. Amma duk da haka Allah da rahamar sa bai toshe kofar tuba ba, kofar tuba da dawowa a bude take haka ma akwai kofar sheto ga masu sabo a ranar kiyama. Sai dai abin lura anan shi ne cewa tuba da sheto suna da sharudda, sharudda wadanda suke toshe hanyoyin kara sabo da kuma nisanta mai sabo daga sabo. Don haka wannan ayar bata amince da tuba da kuma ceto wadanda basa da kaidi ko sharadi kamar yadda wadan nan yahudawa suke zato ba. Haka ma ayrar ta yi watsi da akidar nasara na cewa annabi Isa علیه السام ya zubar da jininsa don ceton zunuban mabiyansa. Yanzu kuma mu saurari karatun aya ta 49:

وَإِذْ نَجَّيْنَاكُم مِّنْ آلِ فِرْعَوْنَ يَسُومُونَكُمْ سُوَءَ الْعَذَابِ يُذَبِّحُونَ أَبْنَاءكُمْ وَيَسْتَحْيُونَ نِسَاءكُمْ وَفِي ذَلِكُم بَلاءٌ مِّن رَّبِّكُمْ عَظِيمٌ

"Kuma (ku tuna) lokacin da Muka kubutar da ku daga mutanen Fir'auna da suke dandana muku mummunar azaba, suna yanka 'yayanku (maza) suna kuma barin matanku (watau 'ya'yanku mata) a cikin wannan abu akwai bala'i mai girma daga Ubangijinku".

Fir’auna ya dauki matakai da dama don kare mulkinsa, daga cikinsu yakan kasha mazaje da matasan bani Isra’ila sannan ya maida matansu bayinsa. Ya dauki wadannan matakai don kada su sami karfi kalubalantarsa. Alkur’ani mai girma ya na ganin wahalhalu da musibu a bangare guda da kuma rayuwa mai sauki da nishadi hanyoyi ne na jarrabawa ga mutum wadanda suke kai shi ga sanin kansa da kuma shiryatar das hi zuwa ga kamala. Aya ta gaba ta kara bayanin wasu ni’momin da Allah ya yi wa bani Isra’ila. Kafin mu yi bayani. Bari mu saurari karatun aya ta 50 daga cikin sura ta bakara.

وَإِذْ فَرَقْنَا بِكُمُ الْبَحْرَ فَأَنجَيْنَاكُمْ وَأَغْرَقْنَا آلَ فِرْعَوْنَ وَأَنتُمْ تَنظُرُونَ

"Kuma (ku tuna) lokacin da Muka raba muku kogi (Muka sa ya dare kashi biyu), Muka tserar da ku, muka nutsar da mutanen Fir'auna, alhali ku kuna kallo".

Wannan ayar ta yi ishara kan yadda Allah ya tsamar da bani Isra’ila daga hannu Fir’auna. Wanda hakan yana nuni ne ga wata mu’jiza ta ubangiji. Ubangiji ya umurci Annabi Musa (a.s) ya jagoranci mutanensa su fita daga kasar Masar. Amma a dai dai lokacinda suka isa kusa da kogin Nilu sai suka fahinci cewa Fir’auna da rundunarsa suna binsu. Dagan an suka suka tsorata suka dimauce suna ganin halaka ta riskesu inda basu mafita. Ubangiji ya umurci annabi Musa (a.s) ya daki kogin Nilu da sandarsa wanda yin hakan ya samar da hanyoyi masu yawa cikin kogin don ketarewa zuwa dayan gabar kogin. Amma a lokacinda Fir’auna da rundunarsa suka isa tsakiyar kogin a kokarinsu na bin Musa ( a) da mutanensa sai rowan kogin ya hade ya halakasu gaba daya. Bani Isra’ila suna gani da idanunsu yadda Allah ya kubutar da su daga azaba, sannan ya halaka makiyinsu cikin lamari wanda yake nuna rahama da kuma mujizar Ubangiji a garesu wanda babu abinda ake iya kwatantawa da shi. A halin yanzu bari mu saurari aya ta 51 na cikin surar bakara wacce take bayanin mummunan halayen Bani Isra’ila a lokacinda annabi Musa (a ) ya je ganawa da Ubangijinsa.

وَإِذْ وَاعَدْنَا مُوسَى أَرْبَعِينَ لَيْلَةً ثُمَّ اتَّخَذْتُمُ الْعِجْلَ مِن بَعْدِهِ وَأَنتُمْ ظَالِمُونَ

"Kuma (ku tuna dai) lokacin da Muka yi wa Musa wa'adi na dare arba'in sannan kuka riki dan maraki (kuka bauta masa) bayan (tafiyar Annabi Musa), alhali kuwa ku kuna masu zaluntar kanku".

Bayan kubutar da Bani Isra’ila daga Fir’auna. Ubangji ya umurci Annabi Musa (a) nisanci mutanensa na tsawon kwanaki 40 don ya tanadi kansa wajen karbar ayoyin Littafin shiriya na Attaura. Amma a cikin dan karamin lokacinda Musa ( a) ya je kan tsaunukan Tur don karban sakon Attaura. Allah ya jarrabi mutanensa da wata jarrabawa mai girma da tsananin gaske. Wani mutum daga cikinsu masanin aikin hannu mai suna Samiri ya tattara golagolai da azurfansu ya gina wata dabba mai kama da dam maraki wanda yake bada sauti irin da dan maraki. Wannan ya jawo hankalin mafi yawan mutane. Dagan an Samiri ya fara kiransu zuwa ga bautar wannan dan marakin, inda mafi yawan mutane suka bi shi. Da wannan kuma mutanen Bani Isra’ila sun zalunci kansu da bautar dan maraki mai makon Ubangiji. Sannan sun zalunci annabi Musa (a ) wanda ya sha wahala mai yawa wajen kubutar da su daga azabtarwa fir’auna. Amma bayan dawowar annabi Musa (a ) daga tsaunin Tur sun fahinci girman barna da zunubin da suka fada. Sannan Allah da rahamarsa ya gafarta masu zunubin shirka da suka fada cikinsa. Ayar da zo gaba wato aya ta 52 ta yi Karin bayani cikin wannan batun. Mu saurari karatunta.

ثُمَّ عَفَوْنَا عَنكُمِ مِّن بَعْدِ ذَلِكَ لَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ

"Sannan Muka yafe muku bayan wancan, ko watakila kwa gode".

Daya daga cikin tausayawar Ubangiji ga bayinsa shi ne cewa baya gaggauta saukar masu da azaba bayan sun saba masa. Yakan bada tazara na lokaci mai yuwa su yi nadama su tuba su dawo bisa shiriya. A wannan karom ma Ubangiji ya tanadarwa bani Isra’ila hanyar tuba daga shirkan da suka yi masa albarkacin jagorancin annabi Musa (a ). A karshen wannan shirin namu, muna iya ambaton wasu darussan da zamu iya dauka daga cikin wadan nan ayoyin da muka karanta kamar haka. 1) A cikin rayuwarmu ta duniya, a ko yaushe mu rika tunanin ranar kiyama. Kada mu yarda mu fada cikin sabon Allah don neman mukami dunkiya ko wata daukaka a cikin ta. Don a wancan ranar matsayi da dunkiya ko wani kusance ga wani mutum ba zai amfanemu ba. 2) Matasa sune shuwagabnnin azzalumai sune amfani da su dafarko don cimma manufofinsu. Ko a cikin zamanimmu na yau manya manyan kasashen duniya suna iya kokari don ganin sun kasha ruhi da lafiyan jikin matasa ta hanyar yada fasadi da amfani da muggan kwayoyi don lalata rayuwarsu. Mata kuma su jawosu ta hanyar kawata masu kayan sawa takalma jakar hannu da sauran abin kawar mata, don jawosu cikin fasadi. 3) Kubuta daga zaluncin shuwagabanni azzalumai na daga cikin manya manyan ni’imomin ubangiji ga bayinsa. Don haka ya zama wajibi ga mumini ya yi kokarin neman taimakon Allah a wannan fagen. 4) Shuwagabannin da Allah ke aikowa suna da tasiri mai yawa wajen shiryatar da mutane. Idon kwanaki 40 kacal ya wadatar ga shaidanu su jawo hankalin jahilan mutane ga bautawa dan maraki, to zai kasance idan Allah bai aiko da wani don shiryatar damutane ba a duk tsawon zamani?. A karshen shirin namu muna rokon Allah ta’ala da ya tabbatar da duga dugammu kan tafarkin shiriya ya kuma kare mu daga musibun zamanimmu da muke ciki.

Suratul Bakara; Aya Ta 53-56 (Kashi Na 23)

Assalamu alaikum manu sauraren barkammu da saduwa cikin shirimmu na hannunka mai sanda shirin na 23, inda da yar dar Allah zamu karanta ayoyi 53 zuwa 56 na suratul Bakara. Yanzu bari mu saurari aya ta 53 kamar haka.

وَإِذْ آتَيْنَا مُوسَى الْكِتَابَ وَالْفُرْقَانَ لَعَلَّكُمْ تَهْتَدُونَ

Kuma (har yau dai ku tuna) lokacin da Muka bai wa Musa littafin nan mai raba (karya da gaskiya) don watakila kwa shiriya (idan kun bi shi).

Kalmar ((فرقان)) a cikin wannan ayar tana nufin abinda yake rarrabe tsakanin gaskiya da kariya. Kasancewar littatafan sama da kuma mujizojin da ke aukuwa a hannun annabawan Allah ta’ala suna fayyace tsakanin gaskiya da kariya shi ya sa ake kiransu ((فرقان)). Don shiryatar da mutane Ubangiji yakan aiko saukar da littatafai har’ila yau da manzannin a matsayin jagorori. Haka kuma yakan bayyana ayoyi da mujizoji don bawa mutane dammar fayyace tsakanin mai gaskiya da makaryaci. Da haka kuma Allah yake kafa hujjarsa kan mutane.

Yanzu kuma bari mu saurari aya ta 54 ta surar bakara.:

وَإِذْ قَالَ مُوسَى لِقَوْمِهِ يَا قَوْمِ إِنَّكُمْ ظَلَمْتُمْ أَنفُسَكُمْ بِاتِّخَاذِكُمُ الْعِجْلَ فَتُوبُواْ إِلَى بَارِئِكُمْ فَاقْتُلُواْ أَنفُسَكُمْ ذَلِكُمْ خَيْرٌ لَّكُمْ عِندَ بَارِئِكُمْ فَتَابَ عَلَيْكُمْ إِنَّهُ هُوَ التَّوَّابُ الرَّحِيمُ

Kuma (ku dai tuna) lokacin da Musa ya ce da mutanensa: Ya ku mutanena, hakika ku kun zalunci kawunanku saboda rikarku danmaraki (kamar Ubangiji), ku tuba ga Wanda ya halicce ku, ku kashe kanku ( da kanku), wannan shi ne ya fi muku alheri a wurin Mahaliccinku, sai Ya yafe maku. Hakika kam Shi ne Mai yawan gafara Mai yawan Jin kai.

A lokacin da annabi Musa (a ) ya dawo daga tafayarsa na kwanaki 40 zuwa kan tsaunukan Tur, ya ga yadda mutanensa suke bautawa dan maraki, sai ya tunatar da su abu biyu. Na frako shi ne cewa kun zalunci kanku da kuka bautawa dan maraki maimakon Allah, sannan kun yada mutunci ga girman da Allah ya yiwa dan adam. Na biyu kuma kun fi kafirai bata, don kun sanda gaskiya kun fahince kun yi imani das hi, sannan kuka barshi kuka kafirce kuka yi ridda. Hukuncin wanda yayi ridda kuma shi ne kisa. Duk da cewa Ubangiji mai rahama ne mai jinkai, amma a matsayinsa na mai bada tarbiyya da kuma reno. Wani lokacin yakan yi ukuba da azaba mai tsanani ga masu laifi don hakan ya zama darasi ga wasu don kada su yi awasa da addini. Sannan da hakan yakan shafe gurbin mummunan ayyuka a cikin mutane. Batun bautawa gumaka ko dan maraki ba abune mai sauki ba wanda tare da tubar baka za’a manta da shi ba. Musamman ga mutanen da suka ga ayoyi da mujizojin Allah masu yawa.

A halin yanzu mu saurari aya ta 55 wanda yake kara bayyana muhimmancin lamarin.

وَإِذْ قُلْتُمْ يَا مُوسَى لَن نُّؤْمِنَ لَكَ حَتَّى نَرَى اللَّهَ جَهْرَةً فَأَخَذَتْكُمُ الصَّاعِقَةُ وَأَنتُمْ تَنظُرُونَ

Kuma (ku tuna) yayin da kuka ce da Musa: Ba za mu ba da gaskiya da kai ba har sai mun ga Allah a sarari, sai tsawa ta fado muku, ( saboda wannan muguwar maganar da kuka yi), alhali ku kuwa kuna kallo.

Wannan ayar ma tana bayyana wani sabon da bani isra’ila suka yi. Da farko sun bautawa dan maraki, sai ga shi a wannan karon sun gabatar da wata bukata wacce bata cancanci matsayinsu ba. Sun bukaci ganin Allah da idanunsu kafin su amince ko kuma su yi imani da annabi Musa. Ubangiji a wannan karon don ya nuna masu cewa raunin idanunsu ya kai ga ba zasu iya ganin wasu halittun sa ba ma, ballantana zatinsa mai tsarki, sai nan take ya saukar masu da aradu da walkiya masu ban tsoro. Wadanda nan take suka fadi matattu. Karashen labarin yana cikin aya ta gaba. Aya ta 56 kamar yadda zamu ji:

ثُمَّ بَعَثْنَاكُم مِّن بَعْدِ مَوْتِكُمْ لَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ

Sannan Muka tashe ku (da rai) bayan kun mutu, don ko kwa gode.

Bayan mutuwar zababbun manya manyan mutane guda 70 cikin bani isra’ila, sai annabi Musa (a ) ya roki Allah ya tada su. Nan take kuwa Allah ya amsa addu’ar annabi Musa ( a) ya tada su don su da mutanensu su gano ikon Allah da kudurassa su yi imani da shi. Daga karshe muna iya ambaton wasu darussa da muke iya dauka daga cikin wadan nan ayoyi da muka karanta kamar haka: 1) Mai sabo yana zaluntar kansa ne ba Allah ba. Asalin mutum ruhinsa ne ba jikinsa ba. Sabo yakan gurbata ya kuma kashe ruhin mutum, ya maida shi kamar dabba wacce bata da wata kima. 2) Ko wani zunubi da irin tuban da ta tace da shi. Tuba daga sabo na bautar dan maraki mai makon Allah madaukaki, ba takaita da kuka da kuma tubar baki ba. A’a sai dai yana bukatar rai da kuma kisa ne. Zubar da hawaye bai wadatar ba, wani lokaci abin yana bukatar zubar da jini. 3) Wadanda suke cewa sai sun ga Allah kafin su yi imani da shi, imma jahilai ne ko kuma dai suna neman wani dililin kaucewa gaskiya ne. Don shi Allah ba’a iya ganinsa sai dai ayoyinsa alamun samuwarsa suna nan tare da mutum kansa ko kuma sauran halittunsa da ke ko ina. 4) Tada matattu ba abu ne da ba zai yu ba. Sau da dama Ubangiji ya tada matattu. Kamar yadda ya faru da shuwagabannin Bani Isra’ila 70 wadanda suka mutu sanadiyyar aradu da walkiya mai ban tsoro da suka fada masu, amma Allah ya rayadda su albarkacin addu’ar annabi Musa(a ). Daga karshe zamu kawo karshen shirimmu da wannan addu’ar, Ya Ubangiji kada ka sanya mu cikin mutanen suka zalunci kansu bayan imani, kada ka sanya mu cikin wadanda suka kaficewa ni’imarka suka yi mummunan karshe.

Suratul Bakara; Aya Ta 57-60 (Kashi Na 24)

Shirin Hannunka mai sanda na 24 daga aya ta 57 zuwa 60 cikin suratul Bakara Assalamu alaikum amsu saurare zamu fara shirimmu na 24 tare da sauraren aya ta 57 cikin surar Bakara.

وَظَلَّلْنَا عَلَيْكُمُ الْغَمَامَ وَأَنزَلْنَا عَلَيْكُمُ الْمَنَّ وَالسَّلْوَى كُلُواْ مِن طَيِّبَاتِ مَا رَزَقْنَاكُمْ وَمَا ظَلَمُونَا وَلَـكِن كَانُواْ أَنفُسَهُمْ يَظْلِمُونَ

" Kuma (ku tuna ni'imomin Allah a gare ku lokacin da) Muka yi muku inuwa da girgije muka saukar muku da darba da 'yanshila (soyayyu), ku ci daga dadadan abin da Muka azurta ku:

Bayan da Ubangiji ya kubutar da Bani Isra’ila daga azzabatarwan fir’auna sai ya ce masu su rayu a kasar Palasdinu mai tsarki. Amma kasancewar shuwagabanni azzalumai ne suke da iko a kasar basu amince da hakan ba. Daga nan sai fushin Allah ya hau kansu, ya kyalesu a hamadar Sina na tsawon shekaru 40 suna rayuwa cikin dimaucewa da wahala. A cikin wannan lokaci mai tsawo wasu daga cikinsu sun yi nadamar aikinsu na kin zuwa kasar Palasdinu kamar yadda aka umurcesu. Don haka rahamar Allah ta sake sauka a garesu kamar yadda wani sashe na wannan ayar yake bayani. Banda inuwar da giragizai suke masu a cikin wannan busashiyar hamada Ubangiji yana saukar masu da abinci nau’i biyu. Daya daga ciksu yana nan kamar zuma wanda ake kira “Manna”. Dayan kuma tsuntsye ne masu kama da tattabaru, wadanda Alkur’ani ya ambata da suna “Salwa”.

Aya ta 58 tana dauke da ci gaban abinda ya faru, kamar yadda zamu ji.

وَإِذْ قُلْنَا ادْخُلُواْ هَـذِهِ الْقَرْيَةَ فَكُلُواْ مِنْهَا حَيْثُ شِئْتُمْ رَغَداً وَادْخُلُواْ الْبَابَ سُجَّداً وَقُولُواْ حِطَّةٌ نَّغْفِرْ لَكُمْ خَطَايَاكُمْ وَسَنَزِيدُ الْمُحْسِنِينَ

"Kuma (ku tuna) lokacin da muka ce: Ku shiga wannan alkarya (wato Kudus) sannan ku ci abin da kuka ga dama, a wadace a cikinta kuma ku shiga kofar kuna masu yin sujjada ( wato a sunkuye) ku ce: (Allah) ka kankare mana kurakuranmu, za Mu yafe muku kurakuranku, da sannu kuma za mu kara wa masu kyakkyawan (aiki daukaka da rahama).

Bayan wahala da dimaucewa na shekaru 40 a hamadar Sinaa, ubangiji ya umurcesu da su shiga Baitul Mukaddasi, su shiga masallaci suna masu masu istafari suna fada “khiddatun”. Ma’anar wannan kalmar shi ne ya Ubangijimmu ka gafarta mana zunubamu ka yi mana afwa. Ubangiji ya yi alkawarin cewa idan suka fadi wannan kalmar a lokacinda suke shigar baitul mukaddasi suna masu gasgatata to zai gafarta masu zunubansu. Har yanzun akwai wata kofa a masallaci Qudus wacce sunanta “kofar khitta”. Wannan ayar tana nuna mana cewa yakamata a girmama wurare masu tsarki a lokacin shigarsu. Har’ila yau tana karantar da mu ladubban addu’a da kuma Ubangiji ne yake sanarda mu hanyar neman gafararsa.

Aya ta gaba tana bayyana mana irin yadda wadan nan bayin suka sabawa umurnin Ubangiji. Da farko mu saurari ayar, wato aya ta 59:

فَبَدَّلَ الَّذِينَ ظَلَمُواْ قَوْلاً غَيْرَ الَّذِي قِيلَ لَهُمْ فَأَنزَلْنَا عَلَى الَّذِينَ ظَلَمُواْ رِجْزاً مِّنَ السَّمَاء بِمَا كَانُواْ يَفْسُقُونَ

"Sannan wadanda suka yi zalunci suka musanya wata magana ba maganar ba aka fada musu ba, sai Muka saukar da azaba daga sama a kan wadanda suka yi zalunci saboda abin da suka kasance suna aikatawa na fasikanci".

Wasu daga cikin Bani Isra’ila don isgila da rani sai suka sabawa umurnin Ubangiji na kalmar da yakamata su fada a lokacinda zasu shiga masallacin Qudus, maimakon kalamar “Khitta” wacce take nufin “Ya ubangiji ga gafarta mana zunubammu” sai suna fadin “khinda” wacce take nufin “alkama”. To annan ma Allah bai saurara masu ba, inda ya saukarwa azzaluman da suka sabawa umurninsa daga cikinsu azaba daga sama. Yin wasa da umurnin Allah ya sanya cutar annoba ta sankarau ya bulla daga cikinsu. Amma kamar yadda ayar ta bayyana cutar ta sami azzalumai daga cikinsu ne kadai. Cutar bata shafi kowa da kowa ba. Wannan ayar har’ila yau tana nuna cewa, a duk lokacinda kaucewa gaskiya da zalunci suka yadu cikin al-umma to kuwa ubar Allah tana kusa ko kuwa a nan duniya ne.

A halin yanzu mu saurare aya ta 60 cikin surar ta Bakara, kamar haka.

وَإِذِ اسْتَسْقَى مُوسَى لِقَوْمِهِ فَقُلْنَا اضْرِب بِّعَصَاكَ الْحَجَرَ فَانفَجَرَتْ مِنْهُ اثْنَتَا عَشْرَةَ عَيْناً قَدْ عَلِمَ كُلُّ أُنَاسٍ مَّشْرَبَهُمْ كُلُواْ وَاشْرَبُواْ مِن رِّزْقِ اللَّهِ وَلاَ تَعْثَوْاْ فِي الأَرْضِ مُفْسِدِينَ

"Kuma (ku tuna) lokacin da Musa ya nemi a shayar da mutanensa, sai Muka ce: Ka bugi dutse da sandarka, sai idanuwan ruwa goma sha biyu suka bubbugo, Hakika kowadanne mutane (watau ko wacce kabila) sun san mashayarsu, (muka ce da su): Ku ci kuma ku sha daga arzikin Allah kuma kada ku yi tafiya a bayan kasa kuna masu barna.

Duk da cewa Annabi Musa (a ) da sauran shuwagabannin daga bangaren Ubangiji aikinsu shi ne isar da sakon Allah ga mutane, amma wannan bai hana su nemawwa mutanensu saukin rayuwa a duniya ba. Don haka ne annabi Musa (a ) ya roki Allah ya samarwa mutanensa ruwan sha ba tare da sun sha wahala ba. Ubangiji ya amsa addu’ar annabi Musa (a ) ya samarwa mutanensa ruwan sha. Inda ya bada umurni ga Musa (a ) ya daki dutse da sandanda wanda ya daki kogi nilo ya sandare ya samarda hanya ga mutanebsa, wanda hakan ya samarda idanun ruwa masu yawa wadanda suka wadatar da mutanensa da ruwan sha. Wannan ma ya zama wata aya ga Bani Isra’ila su san cewa Ubangijin annabi Musa (a) yana da iko kan lome. Bani Isra’ila sun rabu zuwa gidaje 12 ne. Kuma tare da ikon Allah dutsen ya samarda idanun ruwa adadin gidajensu ko kabilunsu. Ko wace kabila ta kebantu da mashaya guda ba tare da takurawa wata kabilar ba. Duk wadan nan mujizoji duk sun zo ne don nisantardasu daga sabon Allah. A cikin shirimmu na yau muna iya daukan darussa kamar haka: 1) Allah ya samarwa mutun duk abinda yake bukata na ci da sha, amma mu ba kamar dabbobi ne ba da zamu rika tunanin abinci da sha kadai ba. Ko kuma abincin da abin shan ya zama duk abinda ya zo hannummu sai mu yi amfani da shi ba. Mu mutane ne dole ne mu zabi abinda zamu ci. Don haka ne aya ta 57 take cewa ((کَلوا من الطیبات ما رزقناکم . 2) Ubangiji mai gafartawa ne, amma tuba tana da sharudda. Tuba tana bukatar kaskantar da kai cikin zuciya da kuma furuci da baki wanda yake tabbatar da zunuban da mutum ya yi da kuma bukatar afwa a wajen Allah. Kamar yadda aya ta 58 ta nuna (أدخلوا الباب سجداً و قولوا خطةٌ) . 3) Bautar Allah dole ne ya kasance da umurnin Allah kamar yadda ya umurta. Yin sabanin umurnin sa ba bautar sa bane. Wasa ne da addini. 4) Zababbun shuwagabannin daga Allah ta’ala banda aikin isar da sakon Allah suna nemawwa mutanen su sauki a rayuwa, kuma suna rabon arziki tsakanin mutanensu da adalci. Kamar yadda aya ta 60 ta bayyana. (قد علم کل اناس مشربهم ) . A karshen wannan shirin muna rokon Allah ta’ala da ya sanya mu masu godewa ni’imominsa da basa kidayuwa a garemu. Da kuma amfani da wadan nan nimomi don anfani da kuma kawo ci gaban dan adam gaba daya.

Suratul Bakara; Aya Ta 61-64 (Kashi Na 25)

Assalamu alaikum masu saurare ina maku maraba cikin shirimmu na hannunka mai sanda na 25 inda zamu dubi ayoyi 61 zuwa 64 na sarra Bakara. Yanzu bari mu fara sauraron aya ta 61 kamar haka:

وَإِذْ قُلْتُمْ يَا مُوسَى لَن نَّصْبِرَ عَلَىَ طَعَامٍ وَاحِدٍ فَادْعُ لَنَا رَبَّكَ يُخْرِجْ لَنَا مِمَّا تُنبِتُ الأَرْضُ مِن بَقْلِهَا وَقِثَّآئِهَا وَفُومِهَا وَعَدَسِهَا وَبَصَلِهَا قَالَ أَتَسْتَبْدِلُونَ الَّذِي هُوَ أَدْنَى بِالَّذِي هُوَ خَيْرٌ اهْبِطُواْ مِصْراً فَإِنَّ لَكُم مَّا سَأَلْتُمْ وَضُرِبَتْ عَلَيْهِمُ الذِّلَّةُ وَالْمَسْكَنَةُ وَبَآؤُوْاْ بِغَضَبٍ مِّنَ اللَّهِ ذَلِكَ بِأَنَّهُمْ كَانُواْ يَكْفُرُونَ بِآيَاتِ اللَّهِ وَيَقْتُلُونَ النَّبِيِّينَ بِغَيْرِ الْحَقِّ ذَلِكَ بِمَا عَصَواْ وَّكَانُواْ يَعْتَدُونَ

"Kuma (ku tuna) lokacin da kuka ce; Ya Musa ba za mu iya hakuri da abinci daya ba, sai ka rokar mana Ubangijinka ya fito mana da (wani abinci) daga (abubuwan da) kasa take tsirarwa na daga mabunkusanta da kulubuntunta da alkamarta da wakenta da albasarta, (Annabi Musa ya ba su amsa) ya ce; Yanzu kwa nemi musanya abin da yake shi ne kaskantacce da abin da yake shi ne mafifici? (To idan haka ne ku tafi cikin gari sannan, hakika an tanadar muku da abin da kuka tambaya. Saboda haka aka saukar musu da kaskanci da talauci, suka kuma wayi gari da fushin Allah. Wannan kuwa saboda hakika sun kasance suna kafurcewa da ayoyin Allah, suna kuma kashe annabawa ba da hakkin komai ba. (Har yau) wancan saboda sabonsu da kuma shisshigi da suke wa (Allah)".

Duk da cewa Ubangiji ya dauki nauyin wadatar da mutanen Bani Isra’ila da abinci da kuma abin sha a wannan busashiyar hamada. Amma jahilci da kuma rashin godiyarsu sun kaisu ga rokon annabi Musa (a ) wani nau’in abinci Annabi Musa (a ) ya basu amsa da cewa, shin ta yaya zasu masanya abinda da ake saukar maku daga sama na abinci da abin sha, da wadanda yake bayan kasa, wanda kuma bai kai shi kyau da daraja ba.?. Sannan idan kuna sun samun irin wannan abincin da kuka tambaya to dole fa ko yaki makiyanku ku shiga gari don kaiwa ga irin wannan abincin. Da farko ba a shirye kuke ku shiga yaki da jihadi ba, sannan akwai bukatar ku yi tanadin rayuwa cikin birni. Wanda ya fi wahala bisa halin da kuke ciki. Son jin dadinku zai jawo mako kaskanci da wahala. Banda haka Allah zai yi fushi da ku. Irin wannan bukatar ku wanda bai dace ba, da kuma rashin mutunta ayoyin Allah da kuka gani zai kai ku ga kashe annabawan Allah don cimma bukatunku na ciki cikunanku rayuwa mai sauki. Wannan ayar tana bayyana inda bautawa ci da kuma kodayin hutu da sauki yakan saukar da mutuncin mutum ya lalata rayuwarsa.

A halin yanzu mu saurari aya ta 62 na surar bakara kamar haka.

إِنَّ الَّذِينَ آمَنُواْ وَالَّذِينَ هَادُواْ وَالنَّصَارَى وَالصَّابِئِينَ مَنْ آمَنَ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الآخِرِ وَعَمِلَ صَالِحاً فَلَهُمْ أَجْرُهُمْ عِندَ رَبِّهِمْ وَلاَ خَوْفٌ عَلَيْهِمْ وَلاَ هُمْ يَحْزَنُونَ

"Hakika wadanda suka ba da gaskiya (da annabawan da suka gabata) da wadanda suke Yahudawa da Annasara da Sabi'awa (duk ), wanda ya ba da gaskiya da Allah da ranar lahira ya yi kuma aiki na gari, to suna da ladarsu a wurin Ubangijinsu, babu kuwa tsoro a gare su kuma su ba za su yi bakin ciki ba".

A cikin dukkan addinan sama mizanin samun ladar Allah sune imani da ayyuka na gari. Imani da Allah da ranar kiyama tare da aiwatar da umurnin Allah, a cikin dokokin Allah basu bambanci tsakanin muslmi, yahudu ko kirista ko kuma sauran mabiya sauran addinin sama. Sai dai abinda zamu lura a nan shi ne cewa Alkur’ani ya yi kira ga yahudawa da kiristoci da su shiga addinin musulunci. Kamar yadda ya zo cikin surar Ali-Imran aya ta 85 inda yake cewa “Wanda ya riki wanin musulunci addinin to ba za’a karba daga wajensa ba”. Don haka mabiya saurana addinin sama, duk wanda ya yi imani da manzo da kuma littafin zamaninsa ya aikata ayyuka na gari zai sami ladar ubangijinsa. Amma bayan bayyanar musulunci babu wani karbebben addini banda shi. Dayana daga cikin addinan da wannan ayar ta ambata shi ne (صائبین) wadanda wasu mabiyan addinan annabi Nuhu ko Annabi Ibrahim ko kuma Annabi Yahya ne. Wadanda kuma suka shigar da akidu da wasu lamura sabbi cikin wadannan addinai. Suna ganin taurari na da tasiri cikin rayuwar mutum. Sannan ayar tana nuni da cewa addinan sama gaba daya sun yi musharaka cikin imani da Allah da ranar lahira. Da kuma cewa tsira kadai yana samuwa ne ta hanyar imani da aiki na gari, ba da fata da kuma burace burace ba. Yanzu kuma mu saurari karatun aya ya 63 kamar haka.

وَإِذْ أَخَذْنَا مِيثَاقَكُمْ وَرَفَعْنَا فَوْقَكُمُ الطُّورَ خُذُواْ مَا آتَيْنَاكُم بِقُوَّةٍ وَاذْكُرُواْ مَا فِيهِ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ

"Kuma (ku tuna) lokacin da Muka dauki alkawari daga wurinku, Muka kuma daukaka dutse (na Sina) a bisanku (Muka ce da ku); Ku karbi abin da Muka ba ku da karfi (watau Attaura) kuma ku tuna abin da yake cikinta (na shiriya) don ko kwa tsoraci (Allah).

Bayan da Allah ya bawa Annabi Musa (a ) littafin Attaura ya bukaci Bani Isra’ila su yi aiki da shi. Kada su saba masa ko su nemi yin watsi da shi. Anan Allah ya sake nunawa Bani Isra’ila wata mujizar inda ya daga dutsen Tur sama ya na reto a kansu. Wannan don su kiyaye alkawarinsu na biyayya gareshi da kuma rashin sabawa umurnin Ubangiji. Har’ila yau ayar tana nuni da cewa ma’abuta addini yakamata su kiyaye imaninsu su kuma yi riko da addininsu ba tare da wargi ko wasa da shi ba.

Amma aya ta gaba tana bayyana yadda yahudawan suka yi watsi da umurnin Allah. Sai kafi mu ci gaba mu saurari karatun aya ta 64 kamar haka.

ثُمَّ تَوَلَّيْتُم مِّن بَعْدِ ذَلِكَ فَلَوْلاَ فَضْلُ اللَّهِ عَلَيْكُمْ وَرَحْمَتُهُ لَكُنتُم مِّنَ الْخَاسِرِينَ

"Sannan kuka ba da baya bayan wancan (alkawarin) . To da ba don falalar Allah ba a gare ku, da rahamarsa, da kun kasance cikin tababbu.

Duk da cewa Ubangiji ya gargadi yahudawan Bani Isra’ila gargadi mai tsanani kan kiyaye alkawarin biyayya ga umurninsa. Amma wadan nan mutane sun yi kunnen uwar shegu da gargadinsa. Sai dai Ubangiji kuma don tsananin rahama da jinkansa ya sake tausaya masu bai saukar masu da azaba ba. A halin yanzu muna iya daukar darussa a cikin wadannan ayoyi kamar haka. 1) Kaucewa umurnin Allah da kuma neman hutu da saukin rayuwa sukan jawo mutane su rasa daukaka da karaman da suke da shi, yakan kaisu ga kaskanci da wulakanci. Kai ya kai ga su take dokokin Ubangiji don kaiwa da bukatunsu na duniya. 2) Sabo da kaucewa gaskiya kadan da kadan suna iya kai mutum ga kafici da rashin Imani. Sannan ya karfafa kekacewar zuciya wacce zata kai mutum ga rashin yarda da gaskiya kwatkwata. 3) Nutsuwa ta gaskiya ita ce ta Imani da Allah da ranar lahira. Wadanda suke yin bushara ga muminai. 4) Ubangiji ya dau alkawali daga mutane ta fidirarsu wato hankulansu da kuma ta wahayin da yakewa annabawansa . Ta wadannan hanyoyi ya dau alkawari daga mutane kan imani da aiki na gari da kuma nisantar mummunan ayyuka. Daga karshen shirimmu wannan muna rokon Allah da ya kiyayemu daga sabawa alkawuransa da kuma tallafa mana kan kiyaye imani da aiki na gari.

Suratul Bakara; Aya Ta 65-69 (Kashi Na 26)

Hannunka mai sanda shiri na 26 cikin surar Bakara daga aya ta 65 zuwa 69. Yanzu bari mu fara sauraron ayoyi na 65 da 66. Kamar haka.

وَلَقَدْ عَلِمْتُمُ الَّذِينَ اعْتَدَواْ مِنكُمْ فِي السَّبْتِ فَقُلْنَا لَهُمْ كُونُواْ قِرَدَةً خَاسِئِينَ{65} فَجَعَلْنَاهَا نَكَالاً لِّمَا بَيْنَ يَدَيْهَا وَمَا خَلْفَهَا وَمَوْعِظَةً لِّلْمُتَّقِينَ{66}

"Hakika kuma (ku Bani-Isra'aila) kun san wadanda suka ketare haddi daga cikinku a (a ranar) Asabar, sai Muka ce da su: Ku zama birrai wulakantattu.

Sai Muka sanya ta izna ga wadanda suke zamaninsu da kuma wadanda za su biyo bayansu ( na zamani mai zuwa) kuma (don ya zama) wa'azi ga masu tsoron (Allah). Wannan na daga cikin labaran Bani Isra’ila inda Allah ya haramta masu aiki a ranar asabar. Amma wasu daga cikinsu wadanda suke rayuwa kusa da kogi suna kamun kifi da wata dubara irin ta su. Sun samar da matattaran a hade da kogi ta yadda idon kifaye sun shiga cikin matattaran sai su tushe hanyar fitar kifiyar sannan a ranar lahadi su zo su kama kifayen da suka tsare tun ran asabar. Da haka suka sabawa umurnin Allah na hutu daga a ranar asabar. Sakamakon sabawa umurnin Ubangiji da kuma yin wargi da sabawa dokokinsa ya shafe fuskokinsu daga fuskar mutum zuwa fuskar birrai. Wannan shi ne sakamako a garesu kuma darasi ga sauran mutane. Amma wannan bai nuna cewa ubangiji baya son dabbobi ba, sai dai saukar da mutum daga siffir dan adam zuwa siffar dabba ya nuna korarsa daga kofar samun rahamar ubangji, da nisantarsa daga jinkansa.

Yanzu kuma mu saurari aya ta 67 kamar haka.

وَإِذْ قَالَ مُوسَى لِقَوْمِهِ إِنَّ اللّهَ يَأْمُرُكُمْ أَنْ تَذْبَحُواْ بَقَرَةً قَالُواْ أَتَتَّخِذُنَا هُزُواً قَالَ أَعُوذُ بِاللّهِ أَنْ أَكُونَ مِنَ الْجَاهِلِينَ

"Kuma (ku tuna) lokacin da Musa ya fada wa mutanensa (a lokacin da aka kashe musu wani mutum): Hakika Allah yana umartar ku da ku yanka saniya. suka ce; Yanzu ka rika yi mana izgili? (Sai annabi Musa) ya ce: Allah ya kiyashe ni da zama cikin jahilai (watau cikin wawaye)."

Labarin saniyar Bani Isra’ila labari wanda daga gareshi ne wannan sura wato surar bakara ta dauki sunanta. Kuma daga aya ta 67 har zuwa aya ya 73 na wannan surar suna bayanin wannan batun. Daga cikin Bani Isra’ila an kashe wani mutum wanda ba’a san wanda ya kashe shi ba. Da haka jayayya ta kunno kai tsakanin kabilinsu. Ko wace kabila tana dora kisan kan wata kabilar. Daga karshe sun kai kara gaban Annabi Musa (a ). Amma warware wannan matsalar bata da sauki. Don haka ne annabi Musa (a ) ya yi amfani da mujiza don warwareta. Ya ce masu, Ubangiji ya umurceku da ku yanka saniya sannan ku dauki wani bangarenta ku daki gawar mamacin zai tashi ya fadi wanda ya kashe shi. Amma bayan sun ji umurnin annabi Musa (a ) sai suka ce: Shin wannan kam wasa ka ke yi da mu? Sai ya basu amsa da cewa : ai jahilai ne suke wasa annabawan Allah basa yin haka. Idan da gaske kuna neman wanda ya aikata kisan ne to ku aikata abinda aka umurceku. Wannan ayar tana nuna mana cewa idon bamu fahinci hikimar da ke cikin wata doka ko wani umurnin Allah ba to kada mu yi inkarinta Ko mu wulakantata mu yi mata rikon sakainar kashi. Duk da cewa Ubangiji yana iya sanar da annabi Musa (a ) wanda ya aikata kisar ta hanyar wahayi. Amma sai ya umurcesu da yanka saniya don fitar da sauran daraja da tsarkakan da wasunsu ke yi wa saniya, wanda ya kaisu ga bauta mata a lokutan baya.

Yanzun mu saurari aya ta 68 kamar haka.

قَالُواْ ادْعُ لَنَا رَبَّكَ يُبَيِّن لّنَا مَا هِيَ قَالَ إِنَّهُ يَقُولُ إِنَّهَا بَقَرَةٌ لاَّ فَارِضٌ وَلاَ بِكْرٌ عَوَانٌ بَيْنَ ذَلِكَ فَافْعَلُواْ مَا تُؤْمَرونَ

"(Sai mutanen Annabu Musa) suka ce: (To in haka ne) ka roka mana Ubangiji ya bayyana mana wacce ce (saniyar ? sai Annabi Musa) ya ce; Hakika Shi (Ubangiji) Yana cewa ita saniya ce ba tsohuwa ba,ba kuma budurwa ba; tana tsakankanin wadancan (biyu) sai ku aikataabin da aka umarce ku.

Amma a lokacinda suka fahinci cewa yankar saniya don warware wannan matsalar da gaske ne. Sai suka cika kuma neman wasu bayanai marasa amfani a garesu. Suka ce masa ka tambayi Ubangijinka wace irin saniya zamu yanka? . A zahiri tambayace ta neman bayani. Amma ganin yadda suka tsara tambayar zaka gane cewa suna kaucewa umurnin ne. Sannan babu ladabi cikin tambayar. Kalmar “ka roki Ubangijinka” tana nuni ne da cewa Ubangijinsu da Ubangijin Musa (a ) ba daya bane.

Yanzu kuma mu saurai aya ta 69 kamar haka.

قَالُواْ ادْعُ لَنَا رَبَّكَ يُبَيِّن لَّنَا مَا لَوْنُهَا قَالَ إِنَّهُ يَقُولُ إِنّهَا بَقَرَةٌ صَفْرَاء فَاقِـعٌ لَّوْنُهَا تَسُرُّ النَّاظِرِينَ

"Sai suka ce: (To sai) ka roka mana Ubangijinka ya bayyana mana mene ne launita? (Sai Annabi Musa) ya ce: Hakika (Ubangiji) Yana cewa ita dai saniya ce mai launin ruwan goro launinta mai tsananin cizawa ne, (sannan kuma) tana farannta wa masu ganinta rai.

Duk da cewa wani umurnin ya sake zuwa daga Ubangiji, ammam suka sake yin wata tambaya don basa son bin umurnin. Suke ce menen launinta? Alhali inda akwai bukatar sanin launinta tun farko da Allah ya fade shi cikin umunin farko. Amma Ubangiji ya ambaci launin kore ne don ya kafa hujja a kansu. Kuma don rashin ladabi da suna nuna ya kara kuntata masu. Ya bukaci su yanka saniya mai kyawun gani koriya wacce ta ke tsaka tsakin shekarun shanu. Muna iya daukan darussa daga cikin wadan nan ayoyi kamar haka. 1) Kada mu yi kokarin kaucewa umurnin Ubangiji da dabarbaru wadanda ba zasu ficcemu ba. Bamu san hikimar da Allah ya sanya cikin hukunce hukuncensa ba. Sannan kokarin kaucewa umurnin Ubangiji da wasu dabar baru suna dai dai da shafe addinin nr gaba daya. 2) Sakamakon mummunan ayyukan mutane ba sai an je lahira kadai ba. Wasu sabon Ubangiji yankan gaggauta saukarwa masu shi azaba a duniya don ya zama darasi ga sauran mutane na zamaninsu ko ga alummu masu zuwa. 3) Kada mu yi wasa da umurnin Allah. Don duk abinda ya umurcemu alkhairi ne a garemu ga kuma sauran mutane. Dukar gawar mutum da sashen gawar saniya ya sake rayar da gawar mutum. Wannan wata aya ce daga cikin ayoyin Allah da suka tabbata da cewa yana da iko kan yin kome. A wani bangaren kuma zai fitarda ikidar girmama saniya wanda yake kunce a cikin zakatan wasu.

Suratul Bakara; Aya Ta 70-74 (Kashi Na 27)

Assalamu alaikum masu saurare a cikin shirimmu na yau zamu dubi aya ta 70 zuwa ta 74 a cikin sarar bakara. Yanzu bira mu saurari aya ta 70 da 71 kamar haka.

قَالُواْ ادْعُ لَنَا رَبَّكَ يُبَيِّن لَّنَا مَا هِيَ إِنَّ البَقَرَ تَشَابَهَ عَلَيْنَا وَإِنَّا إِن شَاء اللَّهُ لَمُهْتَدُونَ{70} قَالَ إِنَّهُ يَقُولُ إِنَّهَا بَقَرَةٌ لاَّ ذَلُولٌ تُثِيرُ الأَرْضَ وَلاَ تَسْقِي الْحَرْثَ مُسَلَّمَةٌ لاَّ شِيَةَ فِيهَا قَالُواْ الآنَ جِئْتَ بِالْحَقِّ فَذَبَحُوهَا وَمَا كَادُواْ يَفْعَلُونَ{71}

"Suka ce: (To ai) sai ka roka mana Ubangijinka Ya bayyana mana wacce iri ce (wannan saniyar)? Hakika saniyar ta rikitar da mu, kuma ba shakka mu idan Allah ya so za mu shiriya. (Sai Annabi Musa) ya ce: Hakika (Ubangiji) Yana cewa ita saniya ce (wadda) ba horarriya ba ce da take noman kasa, kuma ba ta ban ruwan shuka. Lafiyayya ce babu dabbare-dabbare a jikinta. (sai) suka ce: To yanzu ka zo da gaskiya, sai suka yanka ta, amma (a gaskiya da) kamar ba za su aikata ba".

A cikin ayoyin da suka gabata Ubangiji ya bayyana irin saniyar da Bani Isra’ila zasu yanka dan raya mamacinsu ya fadi wanda ya kashe shi. Amma sai suka yi ta tambayoyi kan launi da shekarun saniyar. A cikin wannan ayar ma sun ci gaba da neman karin bayani. Amma a lokacinda Annabi Musa (a ) ya kara karban wani umurnin daga Ubangiji, a wannan karon umurnin ya kara takura masu har ya kai ga sun kusan debe kaunar samun irin saniyar da suka bukata don rayar da mamacinsu. Sannan suka gani sanayar ami dukkan sifofin da suke bukata amma da tsadar kaske. A cikin wannan ayar zamu fahinci cewa son zuciya da kaucewa umurnin Allah zai kai mutum zuwa ga sai abinda shi yake ganin shi ne dai dai a wajensa zai amince da shi. Don zancensu ga Annabi Musa (a ) cewa “الآن جئت بالحق ) wato - yanzu ne ka zo da gaskiya - ya nuna cewa kafin haka ba gaskiya ne yake fadi ba. Wanda hakan rashin imani ne da annabcin annabi Musa (a ).

Yanzu kuma mu saurari aya ta 72 da 73 kamar haka.

وَإِذْ قَتَلْتُمْ نَفْساً فَادَّارَأْتُمْ فِيهَا وَاللّهُ مُخْرِجٌ مَّا كُنتُمْ تَكْتُمُونَ{72} فَقُلْنَا اضْرِبُوهُ بِبَعْضِهَا كَذَلِكَ يُحْيِي اللّهُ الْمَوْتَى وَيُرِيكُمْ آيَاتِهِ لَعَلَّكُمْ تَعْقِلُونَ{73}

"Kuma (ku tuna) lokacin da kuka kashe mutum kuka rika lankaya wa juna laifin kisan, alhali kuwa Allah Mai bayyana abin da kuke boyewa ne. Sai Muka ce: Ku buge shi (gawar) da shashinta (saniyar), kamar haka Allah yake raya matattu, Yana kuma nuna muku ayoyinsa don ko kwa hankalta".

A yoyin da suka gabata sun ambaci tambayoyi da amsoci tsakanin Annabi Musa (a ) da su Bani Isra’ila. A cikin wadan nan ayoyi guda biyu, an takaita labarin gaba daya sannan da bayanin yadda Ubangiji ya tada mamacin nasu. Ya bayyana wanda ko wadanda suka yi kisan daga cikinsu amma suka yi ta boye kansu.

Yanzu kuma mu saurari aya ta 74 kamar haka:

ثُمَّ قَسَتْ قُلُوبُكُم مِّن بَعْدِ ذَلِكَ فَهِيَ كَالْحِجَارَةِ أَوْ أَشَدُّ قَسْوَةً وَإِنَّ مِنَ الْحِجَارَةِ لَمَا يَتَفَجَّرُ مِنْهُ الأَنْهَارُ وَإِنَّ مِنْهَا لَمَا يَشَّقَّقُ فَيَخْرُجُ مِنْهُ الْمَاء وَإِنَّ مِنْهَا لَمَا يَهْبِطُ مِنْ خَشْيَةِ اللّهِ وَمَا اللّهُ بِغَافِلٍ عَمَّا تَعْمَلُونَ

"Sannan zuciyoyinku suka kekashe bayan haka (watau aukuwar wadancan abubuwan), suka zama kamar dutse ko kuma fiye (da dutsen) kekashewa. Hakika akwai daga duwatsu wadanda koramu suke bubbuguwa daga gare su; hakaika kuma cikinsu akwai wadanda suke daddarewa ruwa ya rika fitowa daga gare su; hakika kuma cikinsu akwai wanda yake gangarowa don tsoron Allah, Allah kuwa ba marafkani ba ne da abin da kuke aikatawa".

Daga aya ta 49 zuwa wannan ayar Ubangiji ya yi bayanin da dama daga cikin mujizoji da ludufin sa ga Bani Isra’ila wadanda suka hada da tseratar da su wa azzabtarwan Firauna, tsagewar kogi, karbantubar wadanda suka bautawa dan maraki, tada zababbunsu daga mutuwa bayan saukar tsawa a kansu, saukar amsu da abinci daga sama, daga dutse Tur kan kawukansu, yi masu inuwa da giragizai har zuwa na karshensu gano makashi daga cikinsu tare da tada gawar wanda aka kashen kuma ya fadi wanda ya kashe shi. Amma wadan nan mutane duk da irin wadan nan ayoyi da suka gani da idanunsu bai sa suka mika kai ga umurnin Ubangiji da kuma dokokinsa sa. Sai Allah ya kwatanta bushewar zuciyarsu kamar ta dutse ko ma fiye da haka. Wannan ayar tana nuna yadda mutum yake da taurin kai duk da cewa Ubangiji ya daga shi bisa dabba da kwakwalwan da yi masa, amma sai ya maida kansa kamar dabba, wacce bata da wannan baiwar. Kai fiye ma da haka, har dutse wanda bai da rai ma yana tsagewa ya bawa ruwa hanyan kwarara. A halin yanzu muna iya daukan darussa a cikin wadannan ayayi kamar haka. 1) Kada mu yawaita tambayoyin da basu dace ba dangane da umurnin Ybangiji. Don wani lokacin yawaita tambayoyi kamar kaucewa aiwatar da umurninsa ne. 2) Dabbobin da muke yankawa don neman kusanci ga Ubangiji dole ne su kasance masu lafiya wadanda basa da aibi ko kadan. Kamar dai yadda ake bukatar mahajjata su yanka dabbobi wadanda basa da wani aibi a aikin hajji. 3) Ubangiji ya sanda abinda muke aikatawa a boye ko a bayyane. Don haka kada mu sabamasa a gabansa. Don idan yana so zai kunyata mu ya bayyana asirammu. Kuma idan muka aikata sabo to kada mu dora shi kan wasu. 4) Ubangiji ya nuna mana ikonsa na raya matattu a duniya don mu tabbatar mu kuma yi tunani kan ranar kiyama. 5) Dukkan halittu suna karkashin ikon Allah, hatta wadanda basa da rai basa saba masa. Don haka idan mutum ya sabawa Ubangiji to matsayinsa a wajen Ubangiji zai fadi ya yi kasa da dabba ko ma kasa da dutse.

Suratul Bakara; Aya Ta 75-79 (Kashi Na 28)

Assalamu alaikum masu saurare, barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa cikin shirimmu na hannunka mai sanda. Shiri wanda yake dubi cikin wasu ayoyin al-qur’ani mai girma don su zama darasi a cikin rayuwammu. Da fatan masu saurare zasu kasance tare da mu a cikin wannan shirin.

A cikin shirimmu na yau zamu dubi ayoyi 75 zuwa aya ta79 cikin surar bakara. Kafin mu shiga bayani bari mu fara sauraron karatun aya ta 75 kamar.

أَفَتَطْمَعُونَ أَن يُؤْمِنُواْ لَكُمْ وَقَدْ كَانَ فَرِيقٌ مِّنْهُمْ يَسْمَعُونَ كَلاَمَ اللّهِ ثُمَّ يُحَرِّفُونَهُ مِن بَعْدِ مَا عَقَلُوهُ وَهُمْ يَعْلَمُونَ

"Shin kuna tsammãnin zã su yi imãni sabõda ku ne, alhãli wata kungiya daga cikinsu sun kasance suna jin maganar Allah, sa'an nan su karkatar da ita bãyan sun fahince ta, suna sane?

A cikin wannan ayar, bayan da Ubangiji ya kawo karshen kissar rayuwar bani Isra’ila, ya na son ya fahintar da musulmi dangane da su bani Isra’ila da kuma zurriyarsu da ke rayuwa kusa da musulmi a kasashen larabawa a lokacin musamman yahudawan da ke rayuwa a madina. Yana gargadin musulmi da cewa kada ku zaci cewa wadannan jikokin bani’isra’ila wadanda muka baku labarin kakanninsu za su yi imana da ku don abinda suka sani na sifofin manzon Allah Muhammad (s ) cikin littafansu. Ai suma kamar iyayensu suke, wasu daga cikinsu suna sauraron ayoyin Allah, suna fahintar ma’anarsu, amma wannan ba ya hanasu sauya manar ayoyin, da kuma ma’anar gaskiyar da suka ji ba, su ba jahilai bane, suna sane da abinda suke yi. A farkon musulunci musulmi suna zaton cewa ahlul-kitaba musamman yahuwan da suke rayuwa a kasashen larabawa, musamman kuma yahudawan bani Quraiza, banu Qainuka, da banu Nazir zasu shiga musulunci, don irin ilmin da suke da shi dangane da manzon Allah (s) da kuma addinin musulunci. Don haka wannan ayar tana tunanar da manzon Allah(s) da sauran musulmi cewa, wadannan yahudawa fa, jikokin kakanninsu ne. Kamar yadda kakanninsu suka yi jayayya ga gaskiya haka suma suke, ba don sun jahilce ku ba. Sai dai don boye gaskiya. Bazasu amince da ku ba. Don haka kada da damu da su. A cikin aya ta gaba al-qur’ani ya kara bayyana halayen su.

Yanzun bari mu saurari ayoyi na 76 da kuma 77 cikin surar bakara kamar haka.

وَإِذَا لَقُواْ الَّذِينَ آمَنُواْ قَالُواْ آمَنَّا وَإِذَا خَلاَ بَعْضُهُمْ إِلَىَ بَعْضٍ قَالُواْ أَتُحَدِّثُونَهُم بِمَا فَتَحَ اللّهُ عَلَيْكُمْ لِيُحَآجُّوكُم بِهِ عِندَ رَبِّكُمْ أَفَلاَ تَعْقِلُونَ{76} أَوَلاَ يَعْلَمُونَ أَنَّ اللّهَ يَعْلَمُ مَا يُسِرُّونَ وَمَا يُعْلِنُونَ{77}

76- "Kuma idan sun hadu da wadanda suka yi ĩmãni sukan ce: "Mun yi ĩmãni," kuma idan sãshensu ya kebantu da wani sãshe, sukan ce: "Shin, kuna fada masu abin da Allah Ya buka muku ne dõmin su maida shi hujja a kanku a wurin Ubangijinku?" wai, ba ku da hankalta ne?

77 -Shin, bã su sanin cẽwa lalle Allah Yana sane da abin da suke bõyẽwa da abin da suke bayyanãwa ba?

Wadannan ayoyi sun ci gaba da bayani ne kan yahudawan da suka rayu da musulmin farko. Wadandam idan sun hadu da musulmi sai su ce da su “ai mun yi imani manzancin manzon Allah Muhammad (s ). Don abinda muka sani dangane da shi a cikin littafin attauara. Amma idan kuma suka hadu da wasu yahudawa yan uwansu, sai su aibata su suna ce da su, me yasa kuke fadawa musulmi abinda kuka sani dangane da sifofin annan Muhammad (s). Ai yin haka zai basu damar hujjaceku da su a ranar kiyama a gaban Allah. Sai kuma a cikin aya ta 77 Allah yana tunarada su wadannan yahudawan cewa, sun manta ne, Allah yana sane da abinda suke boyewa cikin zukantansu da kuma abinda suka bayyana a maganganinsu masu sabawa juna?. Sakamakon boye gaskiya wanda malaman yahudawa a farkon musulunci suka yi, yana daga cikin manya manyan dalilan da ya sa a halin yanzu, a zamanimmu kawai, biliyoyin mutane, kiristoci da yahudawa da ma wadanda basu ba suna bin bata. Wannan duk natijar boye gaskiya wanda malaman yahudawa da kiristoci na farkon musulunci suka yi wa mabiyansu ne. Sun boyewa mabiyansu wadanda suka dogara da su don sanin gaskiyar sifofin manzon Allah (s ) dake cikin littafansu.

Yanzu kuma mu saurari aya ta 78 cikin surar ta bakara kamar haka.

وَمِنْهُمْ أُمِّيُّونَ لاَ يَعْلَمُونَ الْكِتَابَ إِلاَّ أَمَانِيَّ وَإِنْ هُمْ إِلاَّ يَظُنُّونَ

"Kuma daga cikinsu akwai jahilai, bã su da sanin Littãfi, fãce tãtsuniyoyi, kuma sũ bã kõme suke yi ba in banda zato.

Ayar da ta zo kafin wacce muaka karanta yanzu ta yi magana ne dangane da bangaren farko na yahudawa a lokacin bayyanar musulunci. Wato masana malamai daga cikinsu. Wadanda suke boye gaskiya kwatakwata ko kuma suke karkatar da ma’anar ayoyin Allah. Sai dai akwai wani bangare na yahudawa, wadanda jahilan littafin attaura ne. basa da wata masaniya ta gaskiyar abinda ke cikin littafansu. Wadan nan jahilai sun dauki cewa, karyayyaki da suka yi ta ji na cewa, yahudawa kabila ce mafi daukaka kuma zababbu ne a wajen Allah. A ranar kiyama bazasu shiga wuta ba. Sanna ko da sun shiga wuta ma na yan kwanaki ne kawai. Suna tsammanin duk wadannan suna cikin littafin attaura. Amma gaskiyan lamarin ba haka yake ba, babu wani addinin sama, addinin da Allah ya saukarwa annabawansa da ke dauke da irin wadannan abubuwan. Mai yuwa irin wannan tunanin ya kasance tare da mabiyan wasu addinan sama ma ba yahudawa kadai ba. Amma dai gaskiyar lamarin shi ne jahilci ne ya kaisu ga wannan tunanin.

Yanzu kuma sai mu saurari karatun aya ta karshe a wannan shirin wato aya ta 79 cikin surar bakara kamar haka.

فَوَيْلٌ لِّلَّذِينَ يَكْتُبُونَ الْكِتَابَ بِأَيْدِيهِمْ ثُمَّ يَقُولُونَ هَـذَا مِنْ عِندِ اللّهِ لِيَشْتَرُواْ بِهِ ثَمَناً قَلِيلاً فَوَيْلٌ لَّهُم مِّمَّا كَتَبَتْ أَيْدِيهِمْ وَوَيْلٌ لَّهُمْ مِّمَّا يَكْسِبُونَ

"Bone ya tabbata ga wadanda suke rubũta littãfi da hannuwansu sa'an nan su ce wannan daga wurin Allah yake, dõmin su sami kudi kadan da shi, san nan bone ya tabbata a gare su kan abin da hannayensu ke rubũtu, kuma bone ya tabbata a gare su daga abin da suke aikatawa".

A duk tsawon zamani sai ka sami cewa akwai wani bangare na malaman addini wadanda suke daukar addini a matsayin hanyar samun duniya. Suna kasuwanci da addini. Wasu malaman suna saida addini don su tara dukiya a rayuwarsu ta duniya. Kirkirar wani abu da kuma danganta shi da addini, wato abinda ake kira bidi’a, imma don neman yardar wasu mutane, ko don neman matsayi a wajen wani mai iko , Ko kuma don kiyaye maslahar wani ko wasu mutane, duk suna daga cikin abinda wannan ayar take nufi. Kalmar (ویل) da ta zo cikin wannan ayar har sau ukku yana nuna irin girman zunubin irin wadannan malamai masu saida addinin don neman duniya. Daga karshe muna iya daukan darussa daga cikin wadannan ayaoyi kamar haka. 1) Mu yi fatar mutane gaba daya su yi imani da addinin gaskiya abu ne mai kyau, amma yakamata mu san cewa mafi yawan mutane ba a shirye suke su yi imani da gaskiya ba. Don haka kada kafircinsu, ga kaucewar gaskiyar da suke yi, ya girgiza imanimmu da gaskiya gaskiya ce. 2) Mafi girman ha’inci shi ne boye gaskiya, boye addinin gaskiya, sauyawa addini fuska. Ha’inci wanda zai batarda al-ummu wadanda suke raye da kuma masu zuwa daga baya. Boye gaskiyar ya hanasu fahintar gaskiya ya jefasu cikin bata na duk tsawon rayuwarsu. 3) Nisantar al-qur’ani mai girma da kuma addinin musulunci da wasu mabiyan addinai sama – wadanda ake kira ahlul-katab - suka yi, ya zo ne saboda jahilcinsu da abinda yake cikin littafansu dangane da addinin musulunci. Suna dauke da tunani dangane da addinansu wadanda kuma ba gaskiya bane. 4) Daga karshe, saida addini da abin duniya ya zama dabi’ar wasu malamai masu bata sunan malanta ko kuma bara gurbi. Hatsarinsu ya kai matuka a cikin al-umma. Don haka masu son gaskiya dole su yi hattara da irin wadannan malaman. Ba duk abinda malamai sanya kayan malanata suka fada ne zai zama gaskiaya ba, ko kuma zamu amince da su ba. A karshen shirimmu na yau masu saurare, muna rokon Allah da ya sanar da mu addininsa don mu tsira daga fadawa hannun mummunan mutane wadanda zasu karkatar da mu daga gaskiya. Kafin shiri na gaba tahir Amin yake sallama da ku. Wassalumu alaikum

Suratul Bakara; Aya Ta 80-84 (Kashi Na 29)

Dasu nan Allah mai rahama mai jin kai. Jama'a masu saurare Assalamu Alaikum barkanku da warhaka da kuma sake saduwa damu a cikin shiri kashi na 29 na hannunka mai sanda wanda a cikinsa muke kawo muku bayanai game da ayoyin alkur'ani mai girma da irin darussan da za mu dauka domin samun dacewa duniya da lahaira, inda a yau za mu kawo muku fassarar waya ta 80 a cikin suratul bakara kana daga bisani mu yi bayani a kai. Sai a biyo mu sannu a hankali domin jin yadda shirin yake amma kafin nan bari mu saurari wannan.

              • ******** ******

To yanzu kuma bari mu fara yaye labulan shirin da sauraran aya ta 80 a cikin suratul Bakara.

وَقَالُواْ لَن تَمَسَّنَا النَّارُ إِلاَّ أَيَّاماً مَّعْدُودَةً قُلْ أَتَّخَذْتُمْ عِندَ اللّهِ عَهْداً فَلَن يُخْلِفَ اللّهُ عَهْدَهُ أَمْ تَقُولُونَ عَلَى اللّهِ مَا لاَ تَعْلَمُونَ

"Kuma suka ce wuta ba za ta shafe mu ba sai yan kwanaki ababan kirgawa, kace, kun dauki alkawari ne a wajen Allah, Allah ba zai saba alkawarinsa ba, ko kuwa kuna kirkirar abin da baku sani ba ne game da Allah".

Kamar yadda muka fadi a shirinmu daya gabata Amawan yahudawa ko kuma jahilainsu da basu da cikakkiyar masaniya game da littafin da aka saukar musu daga sama suna da wannan mummunan tunani, dake nuna cewa su ne suka fi kowa kusanci da Ubangiji, kuma yahudawa su ne jinsin da sukafi fifiko a kan kowa. Don haka wannan ayar tana magana ne game da wannan mummunan tunani da suke da shi, suna cewa bisa misali idan suka aikata zunubi, to sakamakonsu zai fi sauki akan na wasunsu kuma za su kasance cikin azaba na yan kwanakin ne kawai, Saboda haka ne wannan aya ta sanya alama akan wannan tunani na bata, kuma take cewa wannan akida ce ta masu magana ta rashin tunani wato danganta kai da Ubangiji, alhali kuwa Allah Ya halicci dukkan mutane baki daya ne dai dai wa dai da. Ba tare da nuna wani bambanci tsakaninsu ba wajen sakamako. Bisa asasi ma batun nuna bambanci saboda jinsi ko bangarenci ya sabama duk wani ingantancen tunani, domin kuwa jin tsoron All.. da kyawawan halaye su ne kawai ke bambanta tsakanin mutane, wanda shi ne abin da ake la'akari da shi wajen bada lada ko kuma yin sakamakon a ranar kiyama.

Yanzu kuma bari mau saurari aya ta 81 zuwa 82 acikin wannan sura mai alfarma ta bakra kamar haka.

بَلَى مَن كَسَبَ سَيِّئَةً وَأَحَاطَتْ بِهِ خَطِيـئَتُهُ فَأُوْلَـئِكَ أَصْحَابُ النَّارِ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ{81} وَالَّذِينَ آمَنُواْ وَعَمِلُواْ الصَّالِحَاتِ أُولَـئِكَ أَصْحَابُ الْجَنَّةِ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ

A'a ba haka bane ! wanda ya tsuwurwuci mummunan aiki kuma kurakuransa suka kewaye shi, to wadancan su ne yan wuta suna madawwama a cikinta. Wadanda kuwa suka bada gaskiya suka kuma yi aiki na gari to wadancan su ne yan Aljannah su na madawwama a cikinta".

A cikin ayoyin da suka gabata mun yi bayani game da tunanin da yahudawa suke da shi da ya nuna cewa sun kagi karye ne ga Allah madaukakin sarki, amma wadannan ayoyin guda biyu suna bayani ne game da mizani na sakamako da bada lada a wajen ubangiji a gobe kiyama, duk wanda ya bi hanyar sabo da gangan to gwargwadon yadda ya yi nisa acikin sabon gwargwadon yadda zai shiga cikin wuta, kuma ba shi da wata hanyar tserewa, kuma anan babu wani bambanci wajen hukumci tsakanin yahudawa da sauran mutane, to da yake sharadin shiga aljanna shi ne Imani tare da gwama shi da aikin kwarai ya nuna kenan Imani shi kadai baya wadatarwa, hakazalikaa shi ma aiki shi kadai baya wadatarwa, dole sia an gwamansu, to ka ga wannan amsa ce ga wadanda suke ganin za su shiga Aljannah ne bisa asasin wani tunani na daban.

To yanzu kuma bari mu saurari aya ta 83 a cikin suratul Bakara mai tsarki.

وَإِذْ أَخَذْنَا مِيثَاقَ بَنِي إِسْرَائِيلَ لاَ تَعْبُدُونَ إِلاَّ اللّهَ وَبِالْوَالِدَيْنِ إِحْسَاناً وَذِي الْقُرْبَى وَالْيَتَامَى وَالْمَسَاكِينِ وَقُولُواْ لِلنَّاسِ حُسْناً وَأَقِيمُواْ الصَّلاَةَ وَآتُواْ الزَّكَاةَ ثُمَّ تَوَلَّيْتُمْ إِلاَّ قَلِيلاً مِّنكُمْ وَأَنتُم مِّعْرِضُونَ

"Kuma ku tuna lokacin da muka daura alkawari da bani isra'il kan kada ku bauta wa kowa sai All. Kuma ku kyautatawa mahaifa da makusanta da marayu da miskinai, kuma ku rika yi wa mutane kyakkyawar Magana, ku tsai da sallah. Ku bada zakka sannan kuka bada baya sai kadan daga cikinku alhali kuwa ku kuna bijirewa" .

A ayar da ta gabata mun kawo bayani game da alkawarin da bani isara'ila suka dauka sai dai mun kawo suna ne kawai, amma ba mu yi bayani game da alkawarin ba, don haka wannan aya da wadda ke bi mata za mu yi bayani game da wannan alkawarin, wanda saboda karya alkawarin da suka yi sun fuskanci tsananin wulakanci, alkawauran Ubangiji da Annabawa suka isarwa mutane ya yi daidai da hanakali da fidirar dan adam, kuma Ubangiji ya sanya kimar wannan addinin a cikin jinisin dukkan dan Adama. Tauhidi da bautawa All. Shi kadai shi ne ke ke gaban allon makarantar dukkan Annabawa , wato yana nufin duk wani aiki da ake neman dacewa da shi dole ne ya zama akwai All.. Acikinsa kuma bisa ma'aunin tauhidi

Umarnin na biyu da ubangiji ya bayar bayan bauta masa shi ne yin biyayya ga iyaye, da kuma kyautata musu saboda su ne sillar halittarmu kuma duk wani ludufi tahanyar su yazo garemu, hakika bayanai sun zo game da muhimmancin biyan bukatun marasa galihu acikin alumma musamman makusanta bai kamata mutum ya takaita da kansa da iyalansa ba kawai, yana da kyau ya kalli alummar dake rayuwa a cikinta, haka zalika bayan yi wa alumma hidima an yi ishara game da bautama ubangiji musamman tsayar da sallah da yake nuna bukatuwar mutum na samun alaka ta dindindin da mahaliccinsa a kowane lokaci, ba wai aiki ba kwai dole ne maganganun bawan All.. su kasance gaskiya ne. tare kuma da nuna hali nagari ga kowa ba wai ga makusantansa ba a'a ga mutane Musulmi ne ko Kafiri.

To madalla yanzu kuma sai mu saurari aya ta 84 in da Allah yake cewa

وَإِذْ أَخَذْنَا مِيثَاقَكُمْ لاَ تَسْفِكُونَ دِمَاءكُمْ وَلاَ تُخْرِجُونَ أَنفُسَكُم مِّن دِيَارِكُمْ ثُمَّ أَقْرَرْتُمْ وَأَنتُمْ تَشْهَدُونَ

Kuma ku tuna lokacin da muka dauki alkawari daga gareku kan kada ku zubar da jinin junanku ,kuma kada ku fitar da junanku daga gidajenku sannan kuka yi ikirarin yin aiki da alakawarin alhali kuwa ku kuna masu shaidar haka".

Wannan ayar tana son yin bayani ne kamar yadda ta gabaceta da ta kawo abubuwa guda 6 da ubangiji ya yi umarni akansu, da kuma abubuwa guda 2 da suka shafi hurumin ran dan adam, da wurin zama da kuma kasarsu, Yana daga cikin muhimman abubuwa na farko da al'umma take bukata shi ne samar da tsaro, haka zalika ma an kawo batun kare rayuka da kasa a cikin dukkan addinan ubangiji . To da yake hakkin rayuwa shi ne hakkin farko ga duk wani dan Adam kuma ko daga wacce alumma ko jinsi ya fito, don haka aka sanya kisan kai a matsayin babban zunubi, kuma hukumcin wanda ya aikata haka tun a duniya shi ne zartar da haddi akansa, a lahira kuwa zai dawwama cikin wutar jahannama. Son kasa wani abu ne dake cikin fidirar dan adam, kuma addini yana girmamashi don haka ne ma babu wanda yake da hakkin kwacema wani wannan hakkin. To yanzu bari mu duba irin darussan da za mu iya dauka a cikin wadannan ayoyi. Na farko shi ne an hana nuna banbamci ko kuma nuna wariya, domin dukkan mutane daya suke a wajen All.. babu wata kabila ko wani jinsi da yafi wani a wajensa Na biyu . mizani zartar da hukumci ko bada sakamako a wajen ubangiji shi ne Imani da ayyukan kawarai, domin zato da fata ba tare da aiki ba, ba shi da wata kima. Na Uku shi ne a wani lokaci aikata sabo yana yin tsatsa a zuciyar mutum yadda zai kai ya rufe zuciya da ruhinsa wanda babu wani abu da zai fito daga gareshi banda mummunan ayyuka da kalamai marasa kyau, Na Hudu: babban muhimman alkawuran da All.. madaukakin sarki ya rika ga mutane wanda idan suka yi aiki da su za su kai ga samun sa'ada ta har abada. Su ne 1 – tauhidi da bautawa All. Shi kadai. 2- kyautatawa Iyaye . 3 taimakawa marasa galihu da makusanta da marayu da masakai. 4- fadin kyakyawar magana ga mutane. 5- tsayar da sallah 6 bayar da zakka 7 nisantar kisa da zubda jini, 8 nisantar wuce gona da iri akan gidaje da kasashen mutane. to kuma da wannan ne za mu kawo karshen shirin ganin lokacin da aka dibar mana ya kawo jiki da fatan All.. madaukakin sarki zai samu cikin masu yi masa biyayya da cika alkawari tare kuma da kare mu daga bin son zuciya da gurace gurace da basu da amfani, sai Allah ya sake hadamu a wani karon za ku ji mu dauke da ci gaban shirin amma kafin wannan lokacin ni da na kasance tare da ku nake cewa wasall..

Suratul Bakara; Aya Ta 85-88 (Kashi Na 30)

Bismillahir rahamanir rahim. Jama'a masu saurare Assalamu alaikum barka da warahaka da kuma sake saduwa da mu a cikin wani sabon shiri na hannunaka mai sanda wanda a cikinsa muke yi muku bayani game da ayyoyin alkura'ani mai tsarki domin ya zama wa'azo garemu baki daya, sai a biyo mu sannu a hankali domin jin cikakken shirin sai dai kafin nan bari mu saurari wannan.

                    • *******

To yanzu kuma bari musa saurari aya ta 85 acikin suratul Bakara kamar haka.

ثُمَّ أَنتُمْ هَـؤُلاء تَقْتُلُونَ أَنفُسَكُمْ وَتُخْرِجُونَ فَرِيقاً مِّنكُم مِّن دِيَارِهِمْ تَظَاهَرُونَ عَلَيْهِم بِالإِثْمِ وَالْعُدْوَانِ وَإِن يَأتُوكُمْ أُسَارَى تُفَادُوهُمْ وَهُوَ مُحَرَّمٌ عَلَيْكُمْ إِخْرَاجُهُمْ أَفَتُؤْمِنُونَ بِبَعْضِ الْكِتَابِ وَتَكْفُرُونَ بِبَعْضٍ فَمَا جَزَاء مَن يَفْعَلُ ذَلِكَ مِنكُمْ إِلاَّ خِزْيٌ فِي الْحَيَاةِ الدُّنْيَا وَيَوْمَ الْقِيَامَةِ يُرَدُّونَ إِلَى أَشَدِّ الْعَذَابِ وَمَا اللّهُ بِغَافِلٍ عَمَّا تَعْمَلُونَ

"Sannan ku ne wadannan bayan wadannan abubuwan da suka gabata kuke kashe junanku kuke fitar da wasu jama'a daga gidajenku kuma kuna taimakawa makiyansu akansu da cuta da shishshigi , idan kuma suka zo muku suna kamammun yaki sai ku fanshesu alhali kuwa shi fitar dasu haramun ne a gareku, to yanzu kwa rika bada gaskiya da sashin littafi kuma ku rika kafircewa da wani sashi, ba ko mai ne sakamakon mai aikata wannan ba face kaskanci a rayuwar duniya , sannan a ranar kiyama za'a juyar da su zuwa azaba mai tsanani, kuma Allah ba mai rafkana bane daga abubuwan da kuke aikatawa".

Wannan aya tana jan hanakali bani isra'ila ne cewa ku duk da alkawarin da kuka yi wa ubangiji amma kuna kashe kawukanku, kuma kuna fitar da kawukanku daga gidajnesu, amma abin mamaki kamar yadda hukumcin yazo a cikin attaura idan aka kama ribataccen yaki ana sakinsa ne idan aka bada fansa, amma sai gashi a shirye kuke ku kashe junanku, amma ba ashirye kuke ku kasance ribatattun yaki ga junanku ba. Idan zama ribataccen yaki cin zarafi ne to ai kisa da korar mutane daga gidajensu yafi muni, haka zalika idan har bada fansa da sakin ribatattun yaki, umurnin ne na Attaura to shi ma nisantar kisa da korar mutane daga gidansu shi ma umarni ne na Attaura, don haka ya bayyana a fili cewa kuna bin son zuciyarku ne kawai ba wai littafin da aka saukar daga sama ba, domin kuna amincewa da umarnin ubangiji ne idan yayi daidai da ra'yinku da son zuciyarku, amma duk inda yake sabanin haka to bakwa amincewa da shi, kuma ma kuna taimakawa junanku wajen aikata zunubi. Anan wannan ayar tana bayyana aiki a matsayin wata alama ta mutum mai imani na hakika, amma fa aikin da ya dace da umarnin ubangiji ba wanda ya dace da sabo da ra'ayi da son ciyar mutum ba, wanda idan ya kasance haka to daidai yake da bautama son zuciya ba bautama ubangiji ba. Anan yana da kyau a gane cewa ba wai aikita laifi ne kawai haramun ba taimako wajen aikata laifi shi ma haramun ne, Imam musa alkazim (AS) daya daga cikin limaman shiriya na iyalan gidan manzon Allah ya fadama wani daga cikin musulmi cewa: ba yar da hayar rakumi ga fadawan khlaifa haruna Rashid haramun ne, ko da kuwa za'aje aikin hajji ne da su, domin kana so su dawo lafiya daga tafiyar domin su biyaka kudinka, kuma amincewa da ci gaba da wanzuwar Azzalumi shi ma kanshi zunubi ne.

To yanzu kuma bari mu saurari aya ta 86 a cikin suratul bakara kamar haka.

أُولَـئِكَ الَّذِينَ اشْتَرَوُاْ الْحَيَاةَ الدُّنْيَا بِالآَخِرَةِ فَلاَ يُخَفَّفُ عَنْهُمُ الْعَذَابُ وَلاَ هُمْ يُنصَرُونَ

"Wadannan su ne wadanda suka musanya rayuwar duniya da ta lahira ba za'a saukaka musu azaba ba, kuma ba za a taimakesu ba ta ko wane hali".

Wannan ayar tana bayani ne game da asasin karya alkawarin da suka yi ne da suka dauka ma ubangiji , da kuma kashe rai da korar mutane daga gidajensu, inda ya bayyana cewa kuna son rayuwar duniya ne kawai, domin kuna aiki da umarnin ubangiji ne idan zai kare maslaharku kuma babu ruwanku da abin da ya shafi lahira. hakama duk da bautama duniya da laifuffukan da suke aikatawa amma yahudawa suna ikirarin cewa basa son wuta ta shafesu, don haka wannan ayar tana bayyana cewa: sabanin fata da gurin da suke da shi domin kuwa za a sanya su a cikin azaba gwargwadon laifuffukan da suka aikata kamar sauran mujrimai, kuma babu wanda zai taimakesu.

Yanzu kuma bari mu ji abin da aya ta gaba wato ta 87 acikin suratul Bakara take cewa.

وَلَقَدْ آتَيْنَا مُوسَى الْكِتَابَ وَقَفَّيْنَا مِن بَعْدِهِ بِالرُّسُلِ وَآتَيْنَا عِيسَى ابْنَ مَرْيَمَ الْبَيِّنَاتِ وَأَيَّدْنَاهُ بِرُوحِ الْقُدُسِ أَفَكُلَّمَا جَاءكُمْ رَسُولٌ بِمَا لاَ تَهْوَى أَنفُسُكُمُ اسْتَكْبَرْتُمْ فَفَرِيقاً كَذَّبْتُمْ وَفَرِيقاً تَقْتُلُونَ

Hakika kuma mun baiwa Musa littafi kuma muka biyar da manzanni a bayansa, kuma muka baiwa isa dan Maryam ayoyi muka karfafashi da Ruhul kudus, wato mala'ika Jibrilu , yanzu ashe ko da yaushe manzanni suka zo muku da abin da rayukanku ba sa so sai ku yi girman kai, wasu jama'ar ku karyata su wasu jama'ar kuma ku karkashesu?.

Wannan ayar cikin yardar All. Za ta ci gaba da ishara ne game da shiriyar ubangiji, tana cewa bayan Annabi Musa akwai Annabawa dama da Allah madaukakin sarki ya aiko ga bani Isra'ila cikinsu har da Annabi Isa ( As) amma son zuciya da son duniya ya sa sun karyata Annabawan da aka aiko musu, kuma suka kashe wasu daga cikinsu, saboda Annabawan sun ki amince da son zuciyarsu da ya sabama dokoki.

To yanzu kuma bari mu saurari aya ta 88 a cikin suratul Bakara.

وَقَالُواْ قُلُوبُنَا غُلْفٌ بَل لَّعَنَهُمُ اللَّه بِكُفْرِهِمْ فَقَلِيلاً مَّا يُؤْمِنُونَ

"Kuma suka ce zukatanmu a rufe suke a'a ba haka ba ne All. dai ya la'ance su ne saboda butulcewarsu, kadan ne kawai suke ba da gaskiya".

Mutanen da suka kau da kai daga amsa kiran Annabawa sun ba da wannan amsar cikin isgili inda suke cewa mu ba ma fahimtar kalamansu, don haka ba za mu yarda da abin da ba ma fahimta ba. To sai dai Alkur'ani ya ba su amsa da cewa: ba haka bane cewa mutane ba sa iya fahimtar maganganun da Annabawa suke musu, a'a jayayya da gaskiya ne yasa wasu daga cikinku ba sa iya fahimtar gaskiya, kuma kadan daga cikinku ne suka bada gaskiya. Tun asali ma bin son zuciya yana sa wani labule mai kauri ya lullube zuciya, da tunanin mutum yadda zai kasance yana kallon gaskiya ne kawai da idanuwansu na zahiri, kuma sakamakon haka sai ya karyata abubuwa na ilimi da aka saukar daga sama. To yanzu bari mu kawo muku irin darussan da zamu koya a cikin wadannan ayoyi kamar haka, Na farko shi ne yana koyar da mu mika wuya ga dukkan umarnin Ubangiji , ba wai sai abin da yayi daidai da abin da ranmu yake so ne za mu iya karaba ba, kuma duk abin da bamu amince dashi ba sai mu barshi, to anan mun bi son ran mu ne ba wai umarnin ubangiji muka yiwa da'a ba. Na biyu mu sani cewa All. Yana kallon dukkan ayyukan da muke aikatawa, kuma mu sani cewa idan mun gafala daga ubangiji, to shi baya gafala akan bayinsa kuma yana kallon dukkan abin da muke aikatawa. Na Uku : dukkan mutane daya suke game da dokokin ubangiji, don haka abin da wasu suke tunani cewa wata alumma tafi wata fifiko a wajen ubangiji tunani ne batacce, kuma wannan bataccen fata din ba zai sawwaka azabar wadanda suka aikata laifuka ba. Na hudu Allah madaukakin sarki ya aiko Annabawa da dama domin su shiryar da Alumma, sai dai maimakon su girmama abin da aka yi musu sai suka koma suna karyatasu harma suna kashe wasu daga cikin su, Na biyar: Sa'ada da tabewa dukka suna hanun mutum ne, idan har Allah ya la'anci wasu mutane ko ya yi fushi da su sakamakon kafirci da taurin kansu ne, domin ubangiji ya samar da dukkan hanyoyin shiriya ga mutane. To da yake lokacin da aka dibarma shirin ya kawo jiki ya zama wajibi in dasa aya ana sai a wani mako za ku ji mu dauke da ci gaban shirin amma daga karshe muna fatan All. Ya sanya mu cikin wadanda za su rika aiki da dukkan umarninsa, da kuma nisantar bin son zuciya amin. anan nake cewa wassalam.

Suratul Bakara; Aya Ta 89-93 (Kashi Na 31)

Bismilll.......... Masu saurare Assalamu Alaikum barkanmu da sake saduwa daku acikin wani sabon shiri na hannunka mai sanda wanda acikinsa muke kawo muku bayanai game da ayoyin alkura'ani mai girma domin su zama wa'azi garemu baki daya, to sai dai kafin mu shiga cikin shirin bari mu saurari abin da aka yi mana tanadi a bisa fai-fai.

                  • ****

To madalla yanzu kuma bari mu saurari aya ta 89 a cikin suratul bakara kamar haka:

وَلَمَّا جَاءهُمْ كِتَابٌ مِّنْ عِندِ اللّهِ مُصَدِّقٌ لِّمَا مَعَهُمْ وَكَانُواْ مِن قَبْلُ يَسْتَفْتِحُونَ عَلَى الَّذِينَ كَفَرُواْ فَلَمَّا جَاءهُم مَّا عَرَفُواْ كَفَرُواْ بِهِ فَلَعْنَةُ اللَّه عَلَى الْكَافِرِينَ

"Kuma lokacin da littafi yazo muku daga wajen Allah wanda yake gasgata abin da yake tare da su ada can sun kasance suna neman nasara akan wadanda suka kafirce, lokacin da abin da suka sani yazo musu sai suka kafirce da shi to tsinuwar Allah ta tabbata akan kafirai".

A shirinmu da ya gabata mun yi bayani game da kafirci da taurinkan bani isra'ila ga Annabi Musa (AS) da kuma umarnin da suka zo acikin Attaura. Wannan ayar tana Magana ne game da yahudawan da suke tun lokacin bayyanar Musulunci, kamar yadda alamomin manzon musulunci suka zo acikin attaura sun kasance suna jiran bayyanarsa shi ya sa suka bar gidajensu da garuruwansu suka yi hijira zuwa hijaz. Yahudawan dake zaune a Madina da kewayenta sun kasance suna fadawa mushrikan Madina cewa: da sannu za'a tayar da wani Annabi mai suna Mohammad wanda za mu bada gaskiya da shi, kuma zai yi nasara akan makiyansa, amma lokacin da Annabi ya yi hijira zuwa Madina sai gashi mushrikan Madina sun yi imani da shi, amma yahudawa suka karyata shi saboda bangarenci da bin son zuciyarsu. A fili dai sun karyata abin da yazo acikin Attaura. Wannnan yana nuna cewa ilimi shi kadai baya wadatarwa dole ne a gwama shi da ruhin karbar gaskiya da kuma mika wuya gareta. wanda duk da ilimin da yahudawa suke da shi game da Annabin rahma musamman malamansu, amma ba a shirye suke su karbi gaskiya su mika wuya gareta ba.

Yanzu kuma bari mu saurari aya ta 90 a cikin suratul bakra kamar haka

بِئْسَمَا اشْتَرَوْاْ بِهِ أَنفُسَهُمْ أَن يَكْفُرُواْ بِمَا أنَزَلَ اللّهُ بَغْياً أَن يُنَزِّلُ اللّهُ مِن فَضْلِهِ عَلَى مَن يَشَاءُ مِنْ عِبَادِهِ فَبَآؤُواْ بِغَضَبٍ عَلَى غَضَبٍ وَلِلْكَافِرِينَ عَذَابٌ مُّهِينٌ

Allah Wadaran abin suka sayi kawukansu da shi suka kafirce da abin da Allah Ya saukar musu don hassadar ganin Allah Ya saukar da falalarsa ga wanda yaso daga bayinsa sai suka dawo da fushi zuwa fushi, Azaba ta wulakanci kuma ta tabbata ga kafirai".

Yahudawa sun yi tsammanin cewa Annabi musulunci daga cikin bani Isra'ila zai fito kuma za su yi imani da shi, amma da suka ga sabanin haka saboda hasada da nuna bangaranci,ba su yi imani da Musulunci ba, har ima inkirani All.. suka yi game da abin da ya aikata. Hakika yahudawa sun kawo abubuwa masu cutarwa sosai da wananan aiki da suka yi domin sun jurewa tafiya cikin wahala kuma suka zauna acikin Madina domin su yi imani da Annabin musulunci har ma suna kiran kansu daga cikin masu da'awar Musulunci, amma saboda hasada da taurin kai suka kafirce masa suka siyar da kawukansu saboda hasada kuma hakarsu bata cimma ruwa ba.

Yanzu kuma sai mu sake gyara zama tare da sauraron aya ta 91 acikin suratul bakara.

وَإِذَا قِيلَ لَهُمْ آمِنُواْ بِمَا أَنزَلَ اللّهُ قَالُواْ نُؤْمِنُ بِمَا أُنزِلَ عَلَيْنَا وَيَكْفُرونَ بِمَا وَرَاءهُ وَهُوَ الْحَقُّ مُصَدِّقاً لِّمَا مَعَهُمْ قُلْ فَلِمَ تَقْتُلُونَ أَنبِيَاءَ اللّهِ مِن قَبْلُ إِن كُنتُم مُّؤْمِنِينَ

Idan kuma aka ce da su,: ku bada gaskiya da abin da Allah ya saukar sai su ce mun bada gaskiya da abin da aka saukar mana , kuma suna kafircewa a bin da yake bayansa, alhali kuwa shi ne gaskiya mai gasganta abin da yake tare da su wato Attaura, kace da su to don me kuke kashe Annabawan Allah a da can idan kun kasance mu'aminai".

Wannan Magana kai tsaye ana yenta ne ga yahudawa idan kun ki yin imani da Annabi Mohammad (Saww) saboda bai fito daga cikinku ba to me yasa kuka karyata tare kashe wasu Annabawan da aka aiko muku da suka fito daga cikinku? Ashe ku kuna adawa ne da gaskiya kuma bakwa banbamcewa shin gaskiyar nan daga bakin Annabinku ne ta fito ko kuma daga Annabin musulunci, a cikin littafinku Atttaura ne ta zo ko kuma acikin alkura'ani mai girma, asali ma dukkan abin da yazo acikin litattafan da aka saukar daga sama daga wajen Ubangiji daya ne, kuma ga dukkan mutane baki daya. Kuma bai takaita da wata alumma ko wani jisin mutane ba, balle wani yace ni zan yi imani ne kawai da abin da aka saukarwa Annabinmu amma ba zan amince da waninsa ba. Domin dukkan bayanan da suka zo acikin litattafan da aka saukar daga sama daga wajen ubangiji daya ne, kuma sun yi daidai da juna, kuma babu sabani a tsakaninsu, kamar yadda dukkan bayanan da suka zo a littafin darasin daliban jami'a dai dai yake da na wadanda suke acikin na daliban sakandire sai dai yafi fadi yafi kuma zama kammalalle.

Yanzu kuma bari mu ji abin da aya ta 92 a cikin suratul Bakara take cewa:

وَلَقَدْ جَاءكُم مُّوسَى بِالْبَيِّنَاتِ ثُمَّ اتَّخَذْتُمُ الْعِجْلَ مِن بَعْدِهِ وَأَنتُمْ ظَالِمُونَ

Kuma hakika Musa yazo muku da ayoyi bayyanannu sannan kuka bautawa dan Maraki bayansa wato bayan tafiyarsa duri sina'a alhali kuwa ku kuna masu zaluntar kanku".

Daya daga cikin dalilan da yake nuna cewa yahudawa sun fake ne kawai da cewa manzon Musulunci ya fito daga larabawa ne yasa suka ki yin imanin da shi shi ne, Annabi musa ya fito ne daga jinsinsu, kuma ya kawo musu mu'ajizozi bayyanannu amma lokacin da ya tafi dusten dur Sina sai bani isra'il suka koma bautar dan Maraki duk wahalar da Musa ya yi na kiransu zuwa ga gaskiya yabi iska kuma hakika sun zalunci jagoransu da kuma kawukansu.

To yanzu kuma bari mu saurari aya ta 93 a cikin suratul bakara mai alfarma.

وَإِذْ أَخَذْنَا مِيثَاقَكُمْ وَرَفَعْنَا فَوْقَكُمُ الطُّورَ خُذُواْ مَا آتَيْنَاكُم بِقُوَّةٍ وَاسْمَعُواْ قَالُواْ سَمِعْنَا وَعَصَيْنَا وَأُشْرِبُواْ فِي قُلُوبِهِمُ الْعِجْلَ بِكُفْرِهِمْ قُلْ بِئْسَمَا يَأْمُرُكُمْ بِهِ إِيمَانُكُمْ إِن كُنتُمْ مُّؤْمِنِينَ

"Kuma ku tuna har yau lokacin da muka karbi alkawari daga gareku muka kuma daga dutse a samanku muka umarceku da cewa ku riki abin da muka baku wato Attaura da karfi, ku ji abin da yake cikinta, suka amsa suke ce mun ji sai dai kuma mun ki, sai son bautar dan Maraki ya cudu da zuciyoyinsu don kafircinsu, ka gaya musu Ya Mohammad Allah Wadaran abin da imaninku yake umurtarku da shi idan kun kasance mu'aminai".

Idan masu saurare za su iya tunawa mun bayyana cewa daya daga cikin dalilan da yasa yahudawa suka ki yin imani da manzon musulunci shi ne kasancewar shi bai fito daga bani isara'ila ba, kuma za su yi imani ne da Annabin da ya fito daga jinsinsu ne kawai, kuma da littafin Attaura da Musa yazo da shi ne kawai za mu yi aiki, A ayoyin da suka gabata al'kur'ani ya kawo misalai da ke nuna cewa hattama annabin da aka aiko musu din da ya fito daga jinsinsu wato Musa ba su yi imani da shi ba, hakama littafin attaura da yazo da shi ba su yi aiki da shi ba , haka zalika wannan ayar ma ta kawo wasu bayanai da ya shafi wannan batun, All.. madaukakin sarki ya dauki alkawari ga bani isra'ila kan wasu alamura a dutsen dur, Kuma ya bukaci su rike alkawarin da suka dauka, amma sai suka juya baya akan abin da suka ji, saboda shirka da son duniya wanda misalinsu shi ne nuna kauna ga dan marakin Samiri, wannan ya yi musu tsananin tasiri acikin zuciyarsu da ya kai babu sauran wurin da ya rage na yin tunanai ko imani, sai dai babban abin mamaki shi ne duk da rashin bin umarnin da suka yi amma suna da'awar cewa sun yi imani. Al'kur'ani ya basu amsa ta hanyar gabatar da tambaya garesu in da yace shin Imaninku ne ya umurceku ku karya alkawarin ubanjigi? Ku koma bautar dan Maraki kuma ku kashe annabawan All..? Idan haka ne imaninku to ya baku mummunan umarni. To anan akwai darussa da dama da za mu iya koya acikin wadannan ayoyi kamar haka: Na farko idan muka lura a yau zamu ga cewa yahudawa da kiristoci basu yi imani da musulunci ba, kada mu yi shakka game da gaskiyar musulunci, kai mafiyawancinsu ma sun fahimci gaskiya amma saboda dalilai na kashinkansu ba a'a shirye suke su amince da ita ba, domin yahudawa sun san madinar manzon musulunci amma ba su yi imani da shi ba, Na biyu : Hasada tana haifar da kafirci da inkarin gaskiya, bani isra'ila tun da sun ga manzon Musulunci bai fito daga jinsinsu ba don haka suka karyatashi tare da kafricemasa saboda hasada. Na uku : so da kauna da ta wuce gona da iri ga wani Allah ko yaya take tana da hadari sosai domin tana makantar da mutum game da ganin gaskiya. Lokacin da mumbutumin dan Maraki na zinari ya samu wurin zama a cikin zukatan bani isra'il sai umarnin ubangiji da Musa da attauara da aka saukar musu suka rasa kima a idonsu kuma maimakon haka suka karfafa shirka da bautama gunki. To masu saurare dafatan kun amfana daga abubuwan da kuka ji acikin wadannan ayoyi daga karshe muna rokon Allah ya kare zukatanmu daga hasada da nuna wariyar jinsi da son duniya da kyale-kyalen dake cikinta ya cikata da kaunarsa da neman kusanci gareshi, to kuma da haka shirin ya kammala sai a wata saduwar zaku ji mu dauke da ci gaban shirin amma kafi nan nake cewa wassalamu Alikum warahamaullahi ta'ala wabarakatuhu

Suratul Bakara; Aya Ta 94-98 (Kashi Na 32)

Bismillahir rahamanir rahim Jama'a masu saurare Assalamu Alaikum. Barkanku da sake saduwa damu acikin wani sabon shiri na hannunka mai sanda wanda a wannnan karon za mu ci gaba da bayanan da muke yi a kan ayoyin alkur'ani mai girma acikin sura ta bakra sai a biyo mu sannu a hankali domin jin cikakke shirin amma bayan an saurari abin da aka yi mana tanadi a bisa fai-fai.

To Madalla kafinmu shiga cikin kwarayar shirin barin mu sarauri aya ta 94 zuwa ta 95 a cikin Suratul Bakara kamar haka.

قُلْ إِن كَانَتْ لَكُمُ الدَّارُ الآَخِرَةُ عِندَ اللّهِ خَالِصَةً مِّن دُونِ النَّاسِ فَتَمَنَّوُاْ الْمَوْتَ إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ{94} وَلَن يَتَمَنَّوْهُ أَبَداً بِمَا قَدَّمَتْ أَيْدِيهِمْ وَاللّهُ عَلِيمٌ بِالظَّالِمينَ

"Kace musu ya Mohammad idan gidan lahira ya kasance kebantacce ne dominku a wurin Allah banda sauran mutane to sai kuyi burin mutuwa idan kun kasance masu gaskiya. Ba za su yi burinta ba har abada saboda abin da hannayensu suka gabatar Allah kuwa yana sane da Azzalumai".

A tsawon tarihi yahudawa an sansu da nuna wariya kuma sun yi imani cewa aljanna an halicceta ne domin su, don haka wuta ba za ta shafesu ba,. Kuma su 'ya'ya da abokan Ubangiji ne. Wannan mummunar akida tasa a hannu daya suna jin yanci aikata duk wani zalunci da ta'adanci da sabo da wuce gona da iri, a gafe guda kuma suna nuna dagawa da jiji da kai da daukar kansu a matsayin wadanda suke da fifiko akan kowa. Wannan ayar tana kira ga lamirinsu da ya yanke hukumci akansu, yana cewa idan haka ne cewa lallai kuna ikirarin Aljannah an yi ta ne saboda ku, to me yasa bakwa fatan mutuwa? domin ku gaggauta shiga aljannar? Me ya sa kuke tsoron mutuwa kuke guduwa daga gareta? kuna tsoron mutuwa kamar yadda direba yake tsoron yin tafiya, domin matuki yana storo ne ko don bai san hanya ba ko kuma ba shi da isashshen mai, ko kuma ya karya dokoki , ko kuma yana dauke da kayan da aka haramta daukarsu, kuma kuma bashi da inda zai sauka a inda yake son zuwa. Alhali kuwa shi mu'amini na hakika ya san hanya, kuma yana tadanar da mai ne ta hanyar kyawawan aiki, kuma ya goge laifin da ya aikata da tuba, kuma ba ya dauke da kayan da aka hana wato bai yi zalunci da sabo ba , kuma yana da wajen zama a gobe kiyama wadda itace aljannah. Mafiyawancin mutanen da ke tsoron mutuwa yana samo asali ne saboda wasu abubuwa guda 2. ko dai yana ganin mutuwar bata da samuwa ko kuma ana saryar da ita, kamar yadda muka sani ne cewa bisa dabi'a duk wani abu me rai yana tsoro da nuna damuwa akan duk abin da zai yi sanadiyar kawo karshensa. Ko kuma ya yi imani da ranar kiyama amma saboda munanan aiyukan da ya aikata yake tsoron mutuwa domin yasan cewa mutuwa tana nufin fara hukumci da hisabin ayyukan da ya aikata, don haka yafi karkata akan jinkirta masa mutuwa zuwa lokaci mai tsawo. Amma annbawa da waliyan Allah a lokaci guda basa ganin mutuwa a a matsayin wani abu da bashi da samuwa, suna ganinta a matsayin fara wata rayuwace ta daban, a daya hannun kuma basa ganin wani abu dake fitowa daga garesu face tunani da aiki mai kyau, don haka ba wai basa tsoron mutuwa ba ne kawai suna ma begen ta ne . ` Kamar yadda Amirul mu'aminina Ali (as) yake cewa game da kansa: tsananin kaunar mutuwa da dan abi talib yake yi yafe kaunar da jariri yakewa mama da yake sha a jikin mahaifiyarsa.

Yanzu kuma lokaci ya yi da za mu sake gyara zama domin sauraren aya ta 96 a cikin wannan sura ta Bakara.

وَلَتَجِدَنَّهُمْ أَحْرَصَ النَّاسِ عَلَى حَيَاةٍ وَمِنَ الَّذِينَ أَشْرَكُواْ يَوَدُّ أَحَدُهُمْ لَوْ يُعَمَّرُ أَلْفَ سَنَةٍ وَمَا هُوَ بِمُزَحْزِحِهِ مِنَ الْعَذَابِ أَن يُعَمَّرَ وَاللّهُ بَصِيرٌ بِمَا يَعْمَلُونَ

"Hakika za ka samesu sun fi sauran mutane kwadayi kan rayuwa fi ye ma da wadanda suka yi shirka, kowanne dayansu yana burin da za'a raya shi har shekaru dubu, alhali kuwa rayashi rayuwa mai tsawo bai zai gusar da shi daga azaba ba, Allah Kuma yana ganin abin da suke aikatawa".

Wannan aya tana Magana ne da manzon (saw) cewa yahudawan da suke riya cewa aljanna tasu ce su kadai, ba kawai basa fatan mutuwa ba ne domin su gaggauta shiga aljannar , a'a sun fi kwadayin dawwama a duniya fiye da sauran mushrikai ma da basu yarda da ranar lahira ba, kuma suke ganin mutuwa a matsayin karshen rayuwarsu . Sun kasance sun danfaru da rayuwar duniya suna son su rayu shekaru dubbai acikin duniyan nan, ko da kuwa za su yi mafi kaskacin rayuwa ne , koda a wane irin hali za su kasance domin kawai su kara nisanta kansu daga hukumcin ubangiji, da kuma yadda za su iya tara dukiya da kyalkyale-kyalkyalen duniya, amma Allah yana fadin cewa misali idan da za'a basu dama su rayu tsawon shekaru dubbai hakan ba zai kubutar dasu daga hukumcin ubangiji ba, domin dukkan ayyukansu yana karkashin kulawar ubangiji ne don haka wannan gurin na su na yarinta ba zai amfanar da su da komai ba.

Yanzu kuma bari muj i abinda aya ta 97 da kuma 98 suke cewa:

قُلْ مَن كَانَ عَدُوّاً لِّجِبْرِيلَ فَإِنَّهُ نَزَّلَهُ عَلَى قَلْبِكَ بِإِذْنِ اللّهِ مُصَدِّقاً لِّمَا بَيْنَ يَدَيْهِ وَهُدًى وَبُشْرَى لِلْمُؤْمِنِينَ{97} مَن كَانَ عَدُوّاً لِّلّهِ وَمَلآئِكَتِهِ وَرُسُلِهِ وَجِبْرِيلَ وَمِيكَالَ فَإِنَّ اللّهَ عَدُوٌّ لِّلْكَافِرِينَ

"Gaya musu wanda ya kasance makiyi ne ga mala'ika jibiril hakika shi ne ya saukar da shi wato manzanci a zuciyarka da izinin Ubangiji, mai gasgata abin da ya rigaye shi na littafi kuma shiriyane da bushara ga mu'aminai".

Wanda ya kasance makiyin All. da malaikunsa da manzanninsa da jibrila da mika'ila , hakika Allah mai kin kafirai ne. Lokacin da Annabin musulunci yaje madina, wani gungun yahudawa tare da malamansu sun je wajen manzon Allahkuma suka tambayeshi daga cikin tambayar shi ne manene sunan mala'ikan da yake zo maka da wahayi? Lokacin da manzo yace musu jabara'il sai sukace idan da mika'il ne sai mu yi imani da kai, domin jabara'ilu makiyinmu ne, shi ne ya zuwa da hukumce-hukumce masu wahala kamar jihadi. lokacin da mutum baya son gaskiya sai ya rika neman uzuri da mafaka, har ma a shirye yake ya tsannanta wajen yin tuhuma bara toshe ga daya daga cikin mala'ikun Allah. domin ya samu hanyar gujema karbar gaskiya, kamar dalibi ne mai son wasa yana ganin malamin da ke koyar da lissafi ba shi da kyau amma wanda yake koyar da wasanni shi ne mai kyau. A bisa asasi dukkan mala'ikun ubangiji Jabra'ilu ne ko Mika'il ba sa kawo wani abu daga ubangijinsu dake tabbatar da abin da ya shafi abota ko kiyayya su basa yin komai sai dai isar da umarnin ubangiji, su tsani ne kawia na isar da wahayi tsakanin Allah. da annabawansa. Don haka kalaman da yahudawa suka yi ba wani abu ba ne face neman dalilin kin yin imani da musulunci . To bari mu duba irin darussan da zamu ko ya daga cikin wadannan ayoyi. Na farko yakamata mutum ya rayu ne yana cikin shirin mutuwa a kowane lokaci ya yi aiki da nauyin da ya rataya a wuyansa kamar yadda ya dace kuma ya kankare zunubansa da yin tuba, yadda babu wani dalili kuma da zai sa yaji tsoron mutuwa . 2 Tsawon rayuwa bashi ne muhimmi ba, albarka rayuwa da kusanci da ubangiji shi ne ke da kima. kamar yadda Imam sajjad (as) yake fadi a cikin addu'arsa cewa ya ubangiji idan rayuwata za ta kasance wani tsani ne a hanyar yi maka biyayya to ka stawaita ta, idan kuma zai zama mazaunin shedan ne to ka yanketa. Na uku : Addini ua kunshi wasu abubuwa da dole ne ayi imani da su baki daya, domin ba zai yi yu mutum yace ya yi imani da ubangiji ba amma yace yana adawa da wannan mala'ikan ko kuma ban yi imani da wannan Annabin ba, mua'mini na hakika shi ne wanda ya yi imani da Allah da dukkan annabawa da mala'kunsa. To a karshen shirin namu muna rokon All. Madaukakin sarki ya sanya rayuwarmu ta tafi a hanyar yi masa da'a da kuma yi wa bayinsa hidima kuma ya nisantar da mu daga mummuna fata da guri mara amfani kuma anan shirin namu ya kammala sai awata saduwa inda mai duka ya kaimu amma kafin nan ni dana jagoranci shirin nake cewa ku zama lafiya wassalamu Alikum warahamatullah

Suratul Bakara; Aya Ta 99-102 (Kashi Na 33)

BISMILLAHIR RAHMANIR Masu saurare Assalamu Alaikum barka da warhaka da kuma sake saduwa da mu a cikin wani sabon shirin na hannunka mai sanda wanda muke yi muku bayani kan ayoyin al'kura'ani mai girma domin mu waztu dasu domin samun sa'ada ta har abada, sai a biyo mu sannu a hankali domin jin cikakken shirin amma kafin nan bari mu saurari abin da aka yi mana tanadi a bisa fai-fai.

                    • **********

To madalla yanzu kuma kafin mu shiga cikin kwarayar shirin bari mu saurari aya ta 99 a cikin suratul bakara kamar haka:

وَلَقَدْ أَنزَلْنَا إِلَيْكَ آيَاتٍ بَيِّنَاتٍ وَمَا يَكْفُرُ بِهَا إِلاَّ الْفَاسِقُونَ

Hakika kuma mun saukar maka da ayoyi mabayyana , ba kuma mai kafircewa da su sai fasikai.

Idan masu saurare za su iya tunawa a shirinmu da ya gabata mun fadi cewa yahudawan Madina sun fake da abubuwa da dama da yasa suka ki yin imani da Musulunci ciki har da cewa tun da mala'ika Jibiril shi ne ya saukar maka da wahayi don haka ba za mu yi imani da kai ba, hakazalika wannan ayar ma tana bayani ne game da wata hanyar da suka bullo da ita domin su fake da ita wajen kare ra'ayinsu, sun kasance suna cewa mu bama fahimtar komai a cikin wannan littafi don haka mu ba za mu yi imani da kai ba, kuma ba mu ganin alkur'ani a matsayin mu'ajizarka wajen tabbatar da da'awarka to sai dai suna fadin wannan maganar ce alhali idan muka yi nazari tare da zurfafa tunani a cikin ayoyin alkur'ani cikin sauki zamu iya tabbatar da gaskiyar Annabcin Annabin Musulunci Wato Annbi mohammad tsira da aminci su tabbata gareshi da iyalan gidansa tsarkaka, kuma za mu iya fahimtar girman alkura'ani mai tsarki. ko shakka babu wadanda zuciyarsu ba ta yi baki saboda tsananin sabo ba ne za su iya riskar wannan hakikar kuam suek da shimfidar amincewa da ita. saboda aikata sabo yana yin shimfida ne zuwa ga kafirci, kuma ta hanyar bin son zuciya ne mutum yake karkata zuwa ga kafirci da kuma rufe gaskiya, domin idan har ya karbi wannan hakikar to zai yi wahala gare shi ya iya aikata sabo cikin sauki.

To yanzu kuma bari mu saurari aya ta 100 a acikin suratul Bakara kamar haka.

أَوَكُلَّمَا عَاهَدُواْ عَهْداً نَّبَذَهُ فَرِيقٌ مِّنْهُم بَلْ أَكْثَرُهُمْ لاَ يُؤْمِنُونَ

"Yanzu a ce ko da yaushe suka dauki alkawari sai wasu daga cikinsu su warware shi, a a ba haka bane mafi yawancinsu ba su yi imani ba".

Wannan ayar tana jan hanakalin Annabi ne da cewa kada ya damu game da rashin imani da shi da yahudawa suka yi domin su mutane ne da hattama ga Annabin da aka aiko musu basu rike shi da amana ba, duk lokacin da suka kulla wani alkawari da Musa sai su karya shi, sun yi kaurin suna a cikin tarihi akan taurinkai da neman abin da za su fake da shi a matsayin hujja domin cimma muradinsu, yahudawa sun kulla alkawari da manzon Allah a lokacin da ya shigo Madina na cewa akalla kada su taimakawa makiyansa amma kafin aje ko ina suka karya wannan alkawarin kuma suka shiga cikin yakin Ahzab tare da mushurikan Makka domin yakar musulmai, A yau ma Haramtacciyar kasar Isra'ila bata aiki da duk wani kudurin ko wata yarjejeniya ta kasa da kasa idan ma har su sanya hannu kan wata yarjejeniya to kafin aje ko ina sai kaga sun karyata domin su mutane ne masu nuna wariya da son nuna fifiko akan kowa.

Yanzu kuma bari mu ji abin da aya ta 101 a cikin wannan sura ta Bakara take cewa.

وَلَمَّا جَاءهُمْ رَسُولٌ مِّنْ عِندِ اللّهِ مُصَدِّقٌ لِّمَا مَعَهُمْ نَبَذَ فَرِيقٌ مِّنَ الَّذِينَ أُوتُواْ الْكِتَابَ كِتَابَ اللّهِ وَرَاء ظُهُورِهِمْ كَأَنَّهُمْ لاَ يَعْلَمُونَ

Lokacin da manzon ya zo musu daga wajen Allah mai gasgata abin da yake tare da su wato Attaura sai wasu jama'a wadanda aka bai wa littafi suka yi jifa da littafin All. A can bayan bayansu kai kace basu san littafin ba.

Kafin bayyanar Annabin Musulunci manyan malaman yahudawa sun yi wa mutane bushara game da bayyanarsa, kuma suna bayyana alamominsa kamar yadda ya zo a cikin Attaura amma lokacin da suka ganshi sai suka yi inkarinsa kai kace ma basu san komai ba game da shi. Haka ne yana barazana barazana ga matsayin dukkan mutane musamman ma malamansu, don haka lokacin da suka fahimci cewa idan suka yi ikirari da gaskiyar manzon Musulunci za su rasa mukaminsu na duniya sai suka yi inkarin Annabcinsa. babu kokwanto cewa alkur'ani yana bayani kan tarihi ne bisa adalci hattama mutane kirki da masu tsarki a cikin yahudawa yana kiyayewa, yana fadin cewa mafi yawancinsu sun kafirta, wato ke nan wani gungu daga cikinsu ya amince da gaskiya, koda kuwa kadan ne daga cikinsu.

To yanzu kuma bari mu ji abin da aya ta 102 a cikin suratul Bakara take cewa.

وَاتَّبَعُواْ مَا تَتْلُواْ الشَّيَاطِينُ عَلَى مُلْكِ سُلَيْمَانَ وَمَا كَفَرَ سُلَيْمَانُ وَلَـكِنَّ الشَّيْاطِينَ كَفَرُواْ يُعَلِّمُونَ النَّاسَ السِّحْرَ وَمَا أُنزِلَ عَلَى الْمَلَكَيْنِ بِبَابِلَ هَارُوتَ وَمَارُوتَ وَمَا يُعَلِّمَانِ مِنْ أَحَدٍ حَتَّى يَقُولاَ إِنَّمَا نَحْنُ فِتْنَةٌ فَلاَ تَكْفُرْ فَيَتَعَلَّمُونَ مِنْهُمَا مَا يُفَرِّقُونَ بِهِ بَيْنَ الْمَرْءِ وَزَوْجِهِ وَمَا هُم بِضَآرِّينَ بِهِ مِنْ أَحَدٍ إِلاَّ بِإِذْنِ اللّهِ وَيَتَعَلَّمُونَ مَا يَضُرُّهُمْ وَلاَ يَنفَعُهُمْ وَلَقَدْ عَلِمُواْ لَمَنِ اشْتَرَاهُ مَا لَهُ فِي الآخِرَةِ مِنْ خَلاَقٍ وَلَبِئْسَ مَا شَرَوْاْ بِهِ أَنفُسَهُمْ لَوْ كَانُواْ يَعْلَمُونَ

"Bayan haka suka bi abin da shaidanunsu suke karantawa akan mulkin suleman, shi suleman bai kafirta ba sai dai shaidanu ne suka kafirta suna koya wa mutane tsafi da abin da aka saukar ga mala'ikun nan guda biyu su ne Haruta da Maruta, basa sanar da kowa sai sun ce da shi mu fa hakika fitina ce kada ka kafirta , sai mutane suka rika koyon abin da za su rika raba tsakanin mutum da matarsa, to ba abin da za su cuci kowa da shi sai da izinin Allah suna koyon abin da zai cucesu ba zai amfane su ba hakika sun sani duk wanda ya zabe shi (tsafin) bashi da wani rabo a lahira, Allah wadaran abin da suka saya wa kawunansu da sun kasance sun sani. (da basu koya ba)".

A zamanin Annabin Suleman kasuwar bokaye da masu sihiri ta samu habaka sosai, wannan yasa Annabi suleman ya bada dama a tattara dukkan takardun masu sihiri a boye su, amma bayan sa wasu gungun mutane sun yi amfani da wadannan rubutun da aka tara wajen koyar da sihiri da yada shi, wannan ayar tana cewa wasu daga cikin bani Isra'ila mai makon su kasance masu bin Attaura sai suka koma bin littafan sihiri da bokanci, domin su wanke ayyukan da suke yi sai suka ce wadannan littafan suna da alaka da Annabi Suleman kuma shi mai kwararren mai sihiri ne. Alkur'ani ya bada amsa da cewa Suleman bai taba kasancewa ma'abocin sihir ko bokanci ba, shi dai Annabin Allah ne kuma dukkan ayyukansa mu'jiza ce, ku dai kuna bin shaidanu ne da suke karfafa irin wadannan aiyuka, babu shakka akwai wata hanya ta daban da yahudawa suka bi wajen samun sihiri, wato batun da ake yi na mala'ikun Allah din nan guda biyu wato Haruta da Maruta da suke bayyana a siffar mutane suna koyawa mutanen babul hanyoyi da za su bi wajen bata sihiri. Duk da yake cewa wadannan mala'ikun guda 2 sun gagardi mutane da kada su yi amfani da ilimi ta hanya mara kyau, sai dai sun yi kunnen kashi domin kuwa sun rika yin amfani da ilimin ta hanyar da bata dace ba domin cimma manufofinsu na duniya ko kuma na jinsi kuma suna kawo rabuwa tsakanin maza da mata A takaice dai yahudawa sun samu ilimin sihiri ne ta wadannan hanyoyi guda biyu, kuma suna amfani da shi wajen biyan bukatunsu da basu dace ba, duk da yake cewa sun san cewa yin sihiri yana cikin layin kafirci, kuma zai jawo cutarwa ga iyalai da ma alumma, don haka wannan ayar tana nuna cewa sihiri da bokanci suna da samuwa, kuma yana tasiri a rayuwar dan adam, to amma da yake komai yana hannun ubangiji ne za mu iya neman mafaka ga Allah tare da dogaro garashi ta hanyar yin sadaka da addu'a na neman tsari daga sharrinsu. hakazalika a fili yake cewa ba kowanne lokaci ne koyawan wannan ilimin yake da amafani ba sai dai idan mai koyan bai kasance salihi ba to maimakon ya yi amfani da wannan wajen yi wa mutane hidima sai ya jawo fasadi da lalacewar alumma, yanzu kuma bari mu yi dubi game da irin darussan da za mu koya a cikin wadannan ayoyi. Na farko: Idan muka lura za mu ga cewa mafiyawancin mutane a yanzu ba'a shirye suke su yi imani ba, to kada mu yi shakka game da gaskiyar addinan ubangiji, sai dai ya kamata mu sani cewa sabo da aikata zunubi yana tasiri sosai a ruhin mutum yadda zai hana shi amincewa da gaskiya. Na Biyu: Ilimin shi kadai baya wadatarwa ba tare da amincewa da gaskiya ba. malaman yahudawa suna da ilimi game da gaskiyar annabin musulunci bisa abin da yazo a cikin attaura, amma ba wai sun ki yin imani da shi ba ne harma sun taimaka ne wajen kange wasu daga yin imani da shi. Na uku: Ba kowane lokaci ba ne ilimi yake da amfani domin shi kamar wukar fida ce wanda idan ta shiga hannun likitan fida, to zai tseratar da mara lafiya daga mutuwa, amma idan ta shiga hannun mai kashe mutane, yana iya haddasa kashe mutum mai lafiya. Na hudu: shaidanu suna kokarin haifar da rabuwa tsakanin miji da mata ne da kuma sabani tsakanin iyalai, amma mala'iku suna kokarin kawo gyara da sulhu tsakanin miji da mata ne, mutane sun kasu kashi biyu bangaren daya suna kan hanyar shedan, daya bangaren kuma akan hanyar mala'iku. To da fatan masu saurare sun amfana da wadannan bayanai da aka ji, kuma ya bamu tsarkin zuciya kafin ya bamu ilimi yadda zamu yi amfani da abin da muka samu ta hanyar gyara da samar da sulhu tsakanin alumma. Kuma anan shirin na mu ya kammala sai a wata saduwa za ku ji mu dauke da wani sabon shirin amma kafin nan nake cewa wasallamu alaikum warahmatullahi ta'ala wa barakatuhu.

Suratul Bakara; Aya Ta 103-107 (Kashi Na 34)

BISMILLAHAHIR RAHAMNIR RAHIM.

Jama'a masu saurare Assalamu Alaikum barkanku da warhaka da sake saduwa damu acikin wani sabon shiri na hannunka mai sanda wanda a cikinsa muke kawo muku bayanai game da ayoyin alkur'ani mai tsarki dominya zama darasi ga rayuwarmu baki daya da fatan masu saurare za su biyo mu sannu a hanakali domin jin cikakken shirin bayan an saurari a bin da aka yi mana tanadi a bisa fai-fai.

                  • *****

To madalla yanzu kuma bari mu saurari aya ta 103 daga cikin suratul Bakara kamar haka.

وَلَوْ أَنَّهُمْ آمَنُواْ واتَّقَوْا لَمَثُوبَةٌ مِّنْ عِندِ اللَّه خَيْرٌ لَّوْ كَانُواْ يَعْلَمُونَ

Hakika da dai sun bada gaskiya sun ji tsoron Allah da ladan da za su samu daga wajen Allah yafi musu da ace sun kasance sun sani".

A shirin mu da ya gabata mun bayyana cewa yahudawa mai makon su yi riko da Attaura da sauran litattafan da aka saukar daga sama sai suka koma suna bin litafin sihiri da bokanci, domin su wanke wannan aiki da suke yi sai suka jingina asalin ilimin da Annabi sulaiman (as) amma alkur'ani ya kare annabi Suleman game da wannan batu. Wannan ayar tana fadi cewa idan yahudawa za su yi imani na gaskiya kuma suka nisantar da kawukansu game da irin wadannan ayyuka da basu dace ba, da yafi zama alkhairi garesu, domin imani ba zai wadatar ba ba tare da gwamashi da imani da tsarkake zuciya ba. Tsoron All. ko kuma takawa ba yana nufin nisanta ko barin aikata mummunan aiki ba ne a'a wani hali ne da karfi dake cikin zuciya da yake hana mutum aikata mummunan aiki kamar karya, da kuma ingiza shi wajen aikata kyakkyawan aiki kamar sallah, da sauransu.

To yanzu kuma bari mu saurari aya ta 104 a cikin suratul Bakara kamar haka.

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُواْ لاَ تَقُولُواْ رَاعِنَا وَقُولُواْ انظُرْنَا وَاسْمَعُوا ْوَلِلكَافِرِينَ عَذَابٌ أَلِيمٌ

Ya ku wadanda kuka bada gaskiya kada ku fadi kalmar Ra'ina, saboda tana da wata ma'ana mara kyau ku ce unzurna wato ku saurara hakika kafirai suna da sakamakon azaba mai radadi.

A lokacin bayyanar Musulunci musulamai sun kasance idan Manzon ya shagaltu da wa'azi ko kuma karanta musu ayoyin alkur'ani, domin su fahimci bayanan da manzo yake yi sukan bukaci ya yi musu magana sannu-sannu tare da yin la'akari da halin da suke ciki, to sun kasance suna yin amfani da wannan kalma wajen bayyana bukatarsu wato kalmar (Ra'ina) wanda a larabce ana nufin ka kula da mu, amma wannan kalmar a harshen yahudawanci wato (Ibri) tana nufin wawanci , ko kuma abin da aka gundura da shi, sai yahudawa suka rika yi wa musulmi isgili suna cewa kuna neman Annabin ku ya rika muku wawanci, don haka ne aka saukar da wannan ayar aka nuna cewa maimakon yin amfani da kalmar (Ra'in) to ayi amfani da kalmar (Unzurna) don kada makiya su yi mummunar amfani da ita, wajen yi muku izgili da Annabinku, bisa asasi ma ya kamata a nisanci aikata duk wani aiki ko wata magana da za'a iya bawa makiya kafa su yi amfani da ita. Har ila yau wannan aya ta na nuna mana cewa musulunci yana kira da a rika zabar kalmar da ta dace cikin ladabi da girmamawa idan za'a yi magana da na gaba ko malamai, kuma musulmi ya guji yin furci ko aikata wani aiki da zai bada kafa ga makiya su yi amfani da ita wajen tozarta abin girmamawa na addini.

Yanzu kuma bari mu ci gaba da sauraran aya ta 105 a cikin suratul Bakara.

مَّا يَوَدُّ الَّذِينَ كَفَرُواْ مِنْ أَهْلِ الْكِتَابِ وَلاَ الْمُشْرِكِينَ أَن يُنَزَّلَ عَلَيْكُم مِّنْ خَيْرٍ مِّن رَّبِّكُمْ وَاللّهُ يَخْتَصُّ بِرَحْمَتِهِ مَن يَشَاءُ وَاللّهُ ذُو الْفَضْلِ الْعَظِيمِ

Wadanda suka kafirta daga ma'abota littafi da mushurikai, basa kaunar a saukar muku da wani wahayi daga ubangiji, Allah Kuwa yana kebance wanda yaga dama da rahamarsa. Allah kuma ma'abocin falala ne da girma.

Wannan ayar tana bayani game da kololuwar bakin ciki da hasada da makiya da kafirai da mushurikai suke da shi ne akan mu'aminai, wanda saboda tsananin hasada da bakinciki ba sa so su ga musulmai sun zama ma'abota littafi da Annabinsu mai yanci, domin su yi fada da karkatattun tunani da soki burustu da ma'abota littafi suke kawo wa. A cikin wannan Ayar All. madaukakin sarki yana cewa, bisa asasin tausayi da rahamarsa ne yasa kowa akan maslahar da ya sani kuma yake so, kuma yake isarwa ga Annabi, ba tare da la'akari da abin da wannan ko wancan ya karkata akai ba, ko kuma daga wannan jinsin ko wancan jinsin ko kuma daga wannan kabila ko wanncan kabila ba.

Yanzu kuma bari mu saurari aya ta 106 a cikin suratul Bakara kamar haka.

مَا نَنسَخْ مِنْ آيَةٍ أَوْ نُنسِهَا نَأْتِ بِخَيْرٍ مِّنْهَا أَوْ مِثْلِهَا أَلَمْ تَعْلَمْ أَنَّ اللّهَ عَلَىَ كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ

"Ba wata aya da za mu shafeta ko mu jirkinta ta sai mun zo da wadda ta fita ko kuwa misalinta. Yanzu baka sani ba cewa hakika Allah mai iko ne a kan komai?

Farkon alkiblar musulmi shi ne baitul mukaddas amma tun da yahudawa suna fakewa da wannan suna yi wa musulmu gori cewa ku baku da Addinin mai cin gashin kai ya sa kuke kallon alkiblarmu sai All. ya bada umarni a canza alkiblar daga baitul mukaddas zuwa makka, wato a riki kallon dakin ka'aba maimakon masallacin Kudus, duk da haka a wannan karon ma sai da yahudawa suka bijiro da wani laifin, suke cewa idan har alkiblar da kuke kallo ta farko dai dai ce me yasa kuka canza ta , kuma idan alkibla ta biyu da kuka canza daidai ce to ke nan dukkan ayyukan da kuka yi a lokacin da kuke kallon ta farko sun baci ke nan. To sai dai kur'ani ya basu amsa game da wannan furuci nasu, inda yake cewa mu bama goge wani hukumci ko kuma mu jirkinta shi face mun zo da wanda ya fishi ko kuma kwatankwacinsa, ko kuma makwafinsa, don haka canza alkibla da kuma jinkirta sanar da dakin ka'aba a matsayin alkiblar musulmi kowannensa yana da dalilai na daban amma ku baku sani ba. To anan zamu iya kara fahimtar cewa hukumce-hukumcen Addini suna bin hikima ne da maslaha ne , don haka canza zamani ko wuri ko sharadi yana iya canza maslahar alamura kuma ya goge hukumcin baya kuma a maye gurbinsa da wani, ko shakka babu dukkan hukumce-hukumcen ubangiji tabbatattu ne basa canzawa, amma cikin rabe-rabensu musamman a alamuran da suka shafi gwamnati lamarin ne da suke iya karbar canji, don haka wannan ayar tana nuna mana cewa musulunci ba shi da abin da ake kira tura ta kai bango ko kuma ruwa ya karema kifi, domin shi addini ne na duniya kuma na har abada, kuma muna iya canza wasu tababatattun hukumce-hukumcen gwargwadon yadda maslahar musulunci take.

Yanzu kuma bari mu saurari aya ta 107 a cikin suratul Bakara kamar haka.

أَلَمْ تَعْلَمْ أَنَّ اللّهَ لَهُ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ وَمَا لَكُم مِّن دُونِ اللّهِ مِن وَلِيٍّ وَلاَ نَصِيرٍ

Ba ka sani ba cewa hakika Allah shi ne mahaliccin sammai da kassai, baku da wani bayan Allah wanda zai jibinci ala'amarinku ko wanda zai taimakeku?

Game da batun ayar da ta gabata da take magana game da batun goge wani sashin hukumcin ubangiji wannan ayar tana cewa ne wadanda suke inkarin canza wasu umarnin ubangiji, kai kace basa lura da yadda ikon sa ya keywaye dukkan komai, a she basu sani ba cewa Allah shi ne ke da iko akan dukkan abin da ke da samuwa ciki har da mutane kuma yana da hakkin ya canza duk abin da yake so dai dai hikimarsa dake tattare da dokokin da hukumce-hukumcen da ya sanya. Sai dai abin takaici bani isra'ila suna da gurbataccen tunani game da ikon ubangiji suna ganin ikon ubangiji kamar bai kewaye dukkan bayinsa ba alhali kuwa Allah madaukakin sarki yana da cikakken iko wajen canza alamari a cikin halitarsa ne ko kuma wajen sanya dokoki da hukumce-hukumce. To yanzu kuma bari mu yi dubi game da darussan da zamu iya dauka a cikin wadannan ayoyi. Na farko : Imani shi kadai baya wadatarwa sai an gwama shi da takawa da kiyayewa ta musamman domin kare bishiyar imani daga duk wani hadari ko lalacewa. Na biyu: Shi ne : dukkan motsi da furucin da muke yi makiya suna kula da su, don haka dole ne nu nisanci yin duk wani aiki ko furucin da zai bawa makiya dama, kamar yadda suka yi amfani da ita akan Annabi suleman (as), Na uku: makiya musulunci suna so a har kullum duk wani ci gaba da bunkasa ya takaita da su ne kawai, kuma basa son albarka da alheri ya sami musulmai, don haka kada mu karkata zuwa garesu ko mu so su a zuciya , ga Allah kawai ya kamata mu dogara. Na Hudu: sanya hukumci ko jinkirta shi yana hannun All. madaukakin sarki ne, kuma bisa asasin tabbatatun bukatu da masu canzawa ga mutum ne da suka dace da hikimarsa da maslaha yake sanya hukumci ko kuma yake canza shi. To masu saurare daga karshe muna rokon Allah ya bamu sani da imani da yakini yadda zamu mika wuya kai tsaye ga dukkan dokoki da hukumce-hukumcensa. To kuma anan shirin namu na yau zai kammala sai a wani sabon jikon zaku ji mu dauke da wani sabon shirin amma kafin wannan saduwa ni dana kasance tare da ku nake cewa wassalamu Alaikum warahamatullahi ta'ala wa barakatuhu.

Suratul Bakara; Aya Ta 108-112 (Kashi Na 35)

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai.

Masu sauraro barkanmu da sake saduwa da ku acikin wannan shirin na tafsrin kur’ani acikin hanya mafi sauki wanda shi ne bangare na 35. Kuma zai fara ne daga aya ta 108 zuwa ta 112 a cikin suratul bakara.

Aya ta 108 tana fara da cewa:

أَمْ تُرِيدُونَ أَن تَسْأَلُواْ رَسُولَكُمْ كَمَا سُئِلَ مُوسَى مِن قَبْلُ وَمَن يَتَبَدَّلِ الْكُفْرَ بِالإِيمَانِ فَقَدْ ضَلَّ سَوَاء السَّبِيلِ

“Shin kuna son ku yi wa annabinku tambaya ne, daidai da irin tambayar da aka yi wa annabi Musa a baya. Wanda duk ya yi musayar imani da kafirci to ya karkace hanya madaidaiciya.”

Wani sashe na musulmi masu raunin imani sun son su rika tambayar annabi da ya rika nuna musu mu’ujiza acikin kowane abu. Ga misali suna yin kira ga annabi da ya bukaci Ubangiji ya aiko musu da wasika, kamar yadda Banu Isra’ila su ka bukaci aannabi Musa da ya roki Allah ya nuna musu kansa a fili domin su ganshi da idanunsu sai su yi imani da shi. A bisa tushe, mu’ujiza tana bayyana ne domin tabbatar da gaskiyar annabta da kuma yanke hujja. Baya nufin cewa a kodayaushe annabi ya rika zuwa da mu’ujiza saboda wasu suna son ya zo da ita bisa zabin kansu, kamar yadda injiniyan gini ya ke yin taswirorin gidaje domin ya tabbatar da cewa ya san abinda ya ke yi. Ko kuma ya ginawa mutane gidaje bisa yadda su ke sha’awa.

Yanzu kuma za mu shiga cikin aya ta 109.

وَدَّ كَثِيرٌ مِّنْ أَهْلِ الْكِتَابِ لَوْ يَرُدُّونَكُم مِّن بَعْدِ إِيمَانِكُمْ كُفَّاراً حَسَداً مِّنْ عِندِ أَنفُسِهِم مِّن بَعْدِ مَا تَبَيَّنَ لَهُمُ الْحَقُّ فَاعْفُواْ وَاصْفَحُواْ حَتَّى يَأْتِيَ اللّهُ بِأَمْرِهِ إِنَّ اللّهَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ

“Da dama daga cikin ma’abota littafi suna son su juyar da ku zuwa kafirai bayan imaninmu saboda hassadar da su ke da ita bayan gaskiya ta bayyana a gare su. To ku yi afuwa ku yi rangwame har zuwa lokacin da Allah zai zo da al’amarinsa. Allah mai iko ne akan kowane abu.”

Yahudawa mazuna madina a kodayaushe suna kokarin ganin sun karkatar da musulmi daga kan addininsu, ko kuma a kalla su raunana musu imani. To kur’ani yana fadawa musulmi cewa kada ku zaci cewa suna yin haka ne saboda suna daukar cewa su, suna kan gaskiya ne, sun fahimci gaskiyar da take tattare da musulunci da kuma kur’ani, saboda haka hassada da gaba ne su ke sa su yin abinda su ke yi. Saboda a wancan lokacin karfin da musulmi su ke da shi kadan ne sai Ubangiji ya ba su umarni da su yi amfani da hakuri da yafiya a matsayin makami, su dukufa su maida hankali wajen gina kawunansu, har zuwa lokacin da umarnin Ubangiji na yin jihadi akan kafirai ya sauka. Wannan ayar tana nuni da cewa yin amfani da karfi akan makiya a matakin farko ba ya cikin tsarin aiki. Halayyar musulunci ta tanadi cewa a yi amfani da afuwa da kuma yafiya a matsayin hanyar isar da sako da za ta sa su shiriya. Idan kuwa har ba su shiriya ba to sai a kalubalance su.

Yanzu kuma za mu shiga aya ta 110 acikin suratul Bakara.

وَأَقِيمُواْ الصَّلاَةَ وَآتُواْ الزَّكَاةَ وَمَا تُقَدِّمُواْ لأَنفُسِكُم مِّنْ خَيْرٍ تَجِدُوهُ عِندَ اللّهِ إِنَّ اللّهَ بِمَا تَعْمَلُونَ بَصِيرٌ

“Ku tsaida salla kuma ku bada zakka, duk wani alheri da ku ka gabatar domin kanku na alheri za ku same shi a wurin Allah. Allah yana ganin abinda ku ke aikatawa.”

A matsayin kalubalantar manufar makiya ta raunana imanin musulmi, Ubangiji yana kare imaninsu ta hanyar Umarnin da ya bayar na karfafa alaka tsakaninsu da Ubangijin nasu ta hanyar yin salla da kuma karfafa musulmi musamman ma dai raunana ta hanyar basu zakka. A bisa al’ada, yin umarni da salla yana zuwa ne tare da umarni da bada zakka. Watakila saboda bautar Ubangiji kadai ba tare da yi wa mutane hidima ba, ba ta wadatar ba. A daya gefen kuma idan har ya zamana ana taimakawa marasa galihu kadai ba tare da an hada shi da bautar Ubangiji ba to girman kai da kuma gori za su shigo ciki. Daya daga cikin abubuwan da su ke damun mutum shi ne yadda mutane ba su ganin fadi tashi da kuma hidimomin da ya ke yi, idan kuma sun gani to ba su jinjinawa, saboda haka sai mutane su zama masu rauni wajen aikata alheri. To wannan ayar tana fadin cewa kada ku damu domin kuwa Ubangiji yana ganin duk abinda ku ke yi, kuma sakamakon aikinmu yana wurin Allah.

Yanzu kuma sai aya ta 111 da 112 a suratul Bakara.

وَقَالُواْ لَن يَدْخُلَ الْجَنَّةَ إِلاَّ مَن كَانَ هُوداً أَوْ نَصَارَى تِلْكَ أَمَانِيُّهُمْ قُلْ هَاتُواْ بُرْهَانَكُمْ إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ{111} بَلَى مَنْ أَسْلَمَ وَجْهَهُ لِلّهِ وَهُوَ مُحْسِنٌ فَلَهُ أَجْرُهُ عِندَ رَبِّهِ وَلاَ خَوْفٌ عَلَيْهِمْ وَلاَ هُمْ يَحْزَنُونَ{112}

“Sun fadi cewa babu wanda zai shiga aljanna sai wanda ya ke bayahude ko banasare, wannan su ne abinda su ke fata. Ka ce ku zo da dalilanku idan da gaske ku ke yi. Na’am wanda duk ya mika kansa ga Allah yana mai kyautatawa to ladansa yana wurin Ubangijinsa kuma babu tsoro ko bakin ciki a tare da su.”

Wani salo da ma’abota littafi su ke amfani da shi domin raunana imanin musulmi shi ne suna fada musu cewa babu wanda zai shiga aljanna sai mu kadai, saboda haka idan kuna son ku shiga aljanna to shiga addinin yahudanci ko kuma kiristanci. Kur’ani ya maida musu martani da cewa: Wannan maganar da ku ke yi bata wuce mafarkin tsaye ba da fata wanda ba ku da dalili akansa. Domin kuwa aljanna ba ta kebanta da wasu kabilu ko wata zuriya su kadai ba, da akwai ka’idojin da duk mutumin da ya cika su zai shiga aljanna. Makullin shiga aljanna shi ne mika wuya ga Ubangji da mutum zai yi , ya kuma rika yin ayyukan kwarai akan tafarkinsa. Saboda haka babu tafiya kafada kafada tsakanin nuna wariya da tsinci daidai a tsakanin hukunce-hukuncen Ubangiji da kuma mika wuya gare shi. A bisa tushe ba a yi wa hukunce-hukuncen Ubangiji tsinci dai-dai bisa son zuciya wanda hakan ya ke cin karo da ma’anar mika kai ga Ubangiji da riko da dukkanin umarninsa. Wadanda su ka fahimci gaskiyar da ta ke tattare da musulunci amma a lokaci guda ba a shirye su ke su yi imani ba saboda bakin kishi na kabilanci ko wani ra’ayi, to ba za su shiga aljanna ba ko da kuwa su ma’abota littafi ne. A karshe wannan ayar tana cewa. Wanda duk ya mika kansa dari bisa dari ga Ubangiji to ba zai shiga cikin tsoro da bakin ciki ba, domin a kodayaushe yana jin cewa Allah yana a tare da shi. Yanzu kuma sai mu yi la’akari da darussan da su ka zo a cikin wadannan ayoyin. 1- Wani sashe na tsammanin da mutane su ke da shi daga jagororin addini zai iya zama mai share fagen kai wa ga kafirci. Domin kuwa ba za su tasirantu da wadannan abubuwan da su ke bukatuwa da su ba wadanda ba su dace ba. A karshe kuwa sakamako shi ne yin raunin imanin mutum da girgizarsa. 2- Yin afuwa da lallashi shi ne ya ke zuwa kafin amfani da karfi wajen yin hulda da kafirai da mushrikai. Kuma nuna afuwar ba alama ce ta rauni ba, yana a matsayin share fage ne domin makiya su gyaru su karbi gaskiya. 3- Mu yi wa mutane hidima koda kuwa ba su da masaniya kuma ba su yi godiya akai ba. Ubangiji yana gani kuma sakamakon wannan aikin kwarai din yana a jiye a wurinsa har zuwa ranar kiyama da zai bada lada akansa. 4- Kada mu za ci cewa aljanna ta kebanta ne da wasu kabilu ko wata zuriya, ko mu rika sawwara cewa tunda dai mu musulmi ne a suna shikenan aljanna tamu ce mu kadai, domin kuwa ayyukan kwarai ne ma’auni ba sunan musulmi ba kadai. 5- Cikakkiyar nutsuwa ta hakika a duniya da lahira tana a karkashin imani da kyakkyawar niyya da aikin kwarai. Mutumin da ya mika kai ga Ubangiji ya kuma yi tawakkali da shi, to ba shi da tsoron kowa kowanene shi. A karshen wannan shirin muna rokon Ubangiji da ya nesanta mu da yin tsammani da fata da basu dace ba, saboda kada mu fada cikin girman kai da jiji da kai dangane da addininmu, mu kuma rika yin alfahari ga wasu.

Suratul Bakara; Aya Ta 113-117 (Kashi Na 36)

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai.

Masu sauraro barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shirin karo na talati da shida wanda mu ke gabatar da tafsirin ayoyin Kur’ani cikin sauki.

A yau za mu ci gaba ne daga kan aya ta 113 a cikin suratu bakara.

وَقَالَتِ الْيَهُودُ لَيْسَتِ النَّصَارَى عَلَىَ شَيْءٍ وَقَالَتِ النَّصَارَى لَيْسَتِ الْيَهُودُ عَلَى شَيْءٍ وَهُمْ يَتْلُونَ الْكِتَابَ كَذَلِكَ قَالَ الَّذِينَ لاَ يَعْلَمُونَ مِثْلَ قَوْلِهِمْ فَاللّهُ يَحْكُمُ بَيْنَهُمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ فِيمَا كَانُواْ فِيهِ يَخْتَلِفُونَ

“Sai yahudawa su ka ce nasara ba su a bakin komai, suma nasara su ka ce yahudawa basu a bakin komai, alhali suna karanta littafi. Wancanenka shi ne kwatankwacinsu marasa masaniya su ka fada. Allah zai yi hukunci a tsakaninsu a ranar kiyama akan abinda su ke da sabani a cikinsa.”

A shirin baya mun bayyana cewa kowane daga cikin yahudawa da nasara suna jin cewa aljanna tasu ce, basu daukar cewa waninsu yana da wannan hakkin. To wannan ayar tana bayyana tunanin a matsayin kuskure daga tushensa, tana fadin cewa: Bakin kishi wanda bai dace ba ne ya ke sa mutum ya ji cewa shi kadai ya ke da wani hakki amma banda waninsa. Wani abu mai jan hankali anan shi ne cewa mushrkai da masu bautar gumaka wadanda su ba ma’abota littafi ba ne, suma irin maganar da su ke yi kenan akansu. Domin kuwa bakin kishi na ido rufe da daukar gaskiya a matsayin mallakin wani shi kadai, yana rufe idanun mutum ya hana shi ganin gaskiya ta yadda zai rika ganin cewa shi kadai ne akan gaskiya sauran kuma suna kan bata. Wannan ayar ta fito fili tana bayyana cewa acikin yanayin da bakin kishi ya cika shi, jahili da malami suna zama daiidai. Ma’abota littafi wadanda su ke da masaniya da attaura da linjila suna yin magana daidai da ta mushrikai jahilai su ke yi. Kowanensu yana daukar dan’uwansa a matsayin batacce ba tare da dalili ba.

Yanzu kuma za mu shiaga aya ta 114 a cikin suratul Bakara:

وَمَنْ أَظْلَمُ مِمَّن مَّنَعَ مَسَاجِدَ اللّهِ أَن يُذْكَرَ فِيهَا اسْمُهُ وَسَعَى فِي خَرَابِهَا أُوْلَـئِكَ مَا كَانَ لَهُمْ أَن يَدْخُلُوهَا إِلاَّ خَآئِفِينَ لهُمْ فِي الدُّنْيَا خِزْيٌ وَلَهُمْ فِي الآخِرَةِ عَذَابٌ عَظِيمٌ

“Wanene ya fi yin zalunci daga wanda ya hana a ambaci sunan Allah a cikin masallatan Allah sannan kuma ya yi kokarin rusa su? Wadannan ba su da hakkin shigarta sai a cikin tsoro. Tabewa ta tabbata a gare su a duniya kuma a lahira suna cikin azaba mai girma.”

A tsawon tarihi masallatai sun rika fuskantar barazanar rufewa ko kuma rushewa. Domin kuwa masallatai da wuraren ibada suna a matsayin cibiyoyi na hukumar addinin Allah, kuma nan ne wurin yin taruka na mabiyansu. Saboda haka ne azzaluman shugabanni da masu karkataccen tunani su ke kokarin rusa ginin masallaci na zahiri da kuma rawar da su ke takawa ta fuskar addini. Kamar kuma yadda mushrikan makka su ka dauki shekaru masu tsawo suna hana musulmi shiga masallacin harami. A wannan lokacin ma makiya suna kokarin rusa masallacin kudus. Makiyan kuma sun rusa tsohon masallaci mai tarihi na Babri da ya ke a indiya. Yada fina-finan Bidiyo da silma yana daga cikin hanyoyi gurbata kyawawan al’adu da makiya su ke amfani da su domin maida samari a cikin kasashen musulmi wadanda ba su da masaniya da masallaci da kuma wuraren tarukan addini.

Yanzu kuma sai aya ta 115 acikin suratul Bakara.

وَلِلّهِ الْمَشْرِقُ وَالْمَغْرِبُ فَأَيْنَمَا تُوَلُّواْ فَثَمَّ وَجْهُ اللّهِ إِنَّ اللّهَ وَاسِعٌ عَلِيمٌ

“Gabas da yamma na Allah ne, duk inda ku ka juya fuskokinku Allah yana nan. Allah mai wadata ne da sani.”

Bayan da musulmi suka sauya alkibla daga masallacin kudus zuwa makka bisa umarnin Allah, yahudawa sun bijiro da wani batu na rikitarwa wanda mu ka yi maganarsa a cikin shirin da ya gabata. Wannan kuwa shi ne cewa, idan har alkiblar farko da musulmi su ke kallo ita ce daidai to me ya sa za su sauya alkibla, idan kuma ba daidai ba ce to menene matsayin ayyukansu na ibada da su ka yi a wancan lokacin? Wannan ayar ta zo ne a matsayin maida martani ga wancan batu na haddasa rudani, da a ciki ta ke bayanin wata hakika guda tabbatacciya na cewa Ubangiji ba shi da wani wuri na musamman, gabas da yamma da duk inda mutum ya duba ubangiji yana nan. Idan an sanya masallacin kudus ko ka’aba a matsayin alkibla to saboda salla da ibadar da aka yi acikin jam’i su kasance dalilan hadin kai a tsakanin musulmi. A tsawon lokacin da yahudawa ba su yi wa musulmi batunci saboda kallon baitul mukaddas da su ke yi a matsayin alkibla,sun ci gaba da fuskantarta a lokacin salla, amma daga lokacin hakan ya zama abin yi wa musulmi batunci da raunana su, Ubangiji ya sanya ka’aba wacce abin tunawa ce da annabi Ibrahim a matsayin alkibla.

Ayoyi na 116 da 117 a cikin suratul Bakara.

وَقَالُواْ اتَّخَذَ اللّهُ وَلَداً سُبْحَانَهُ بَل لَّهُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ كُلٌّ لَّهُ قَانِتُونَ{116} بَدِيعُ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ وَإِذَا قَضَى أَمْراً فَإِنَّمَا يَقُولُ لَهُ كُن فَيَكُونُ{117}

“Sun ce Allah ya riki Da, tsarki ya tabbata a gare shi, sammai da kasa nashi ne, dukkaninsu masu kaskantar da kai ne a gare shi. Makagin samma da kassai idan ya nufi wani abu zai ce masa kasance sai ya kasance.”

Wato yahudawa da nasara ne su ke fadin cewa Ubangiji yana da Da, wanda haka yana daga cikin akidunsu ma’abota littafi na bata. Kowanensu yana cewa annabawansu diya ne ga Allah, wa iyazu billahi. Yahudawa suna fadin cewa Uzairu dan Allah ne, kiristoci kuma suna cewa Isa dan Allah ne. wani abu mai jan hankali anan shi ne cewa su kansu mushrikan makka abinda su ke fada kenan na cewa mala’iku ‘ya’yan Allah ne-wa’iyazu billahi. Wannan ayar ta zo ne a matsayin maida martani ga wannan karkataccen tunanin da ake watsawa a tsakanin mutane.Ubangiji maaukaki ya tsarkaka daga rikon Da. Ya fadi cewa: “ Ubangiji wanda shi ne mahaliccin sammai da kassai kuma mai iko da su, ba shi da bukatuwa da ya riki Da. Yanzu kuma sai darussan da su ke a cikin ayoyin da mu ka karanta. 1- Bakin kishiya da makancewa akan wani abu yana ingiza mutum ya ya yi ayyuka da kuma maganganu irin na jahilai. Ya rika daukar kansa a matsayin mai gaskiya shi kadai kuma ba a shirye ya ke ya baiwa wasu hakki ba. 2- Masallatai suna a matsayin ciboyoyi ne na fada da kafirci da kuma shirka wanda shi ne abinda ya sa makiya su ke kokarin rusa gininsu na zahiri da kuma lalata rawar da su ke takawa a addinance. Saboda haka wajibi ne mu yi kokarin ganin cewa masallatai sun ci gaba da bunkasa da daukaka da kuma cika ta yadda makiya za su ji tsoron yin tasiri aciki. 3- Iyaye da kuma masu tarbiyya kada su hana ‘ya’yansu zuwa masallaci, su rika tafiya a tare da su domin su karfafa musu guiwa. 4- Ubangiji ba shi da wuri na musamma, duk inda mu ka fuskanta Ubangiji yana nan. Amma hikimar da ta ke tattare da fuskantar alkibla shi ne a samu hadin kai a cikin ayyukan ibada, wanda zai kasance ana fuskantar cibiyar tauhidi ta farko wato ka’aba. 5- Ubangiji ba mutum ba ne balle ya bukaci Da da mata. Shi ne mahaliccin mutum kuma mahaliccin Da da mata, kamar kuma yadda shi ne mahaliccin dukkanin samuwa. Yadda mu ke sawwara Ubangiji acikin kwakwale daga gare mu ba haka ya ke ba. A karshen wannan shirin muna yin fatan samun dace a gare ku masu sauraro. Muna kuma rokon Allah da ya kare mu daga bakin kishi na ido rufe da jahilci.

Sai kuma mun hade a wani shirin.

Suratul Bakara; Aya Ta 118-123 (Kashi Na 37)

Da sunan Allah mai Rahama Mai Jin Kai. Masu sauraro barkanmu da saduwa da ku acikin wannan shirin. Za kuma mu ci gaba ne daga inda mu ka tsaya a baya.

A yau masomin shirin namu shi ne ayoyi na 118 da 119 na suratul Bakara.

وَقَالَ الَّذِينَ لاَ يَعْلَمُونَ لَوْلاَ يُكَلِّمُنَا اللّهُ أَوْ تَأْتِينَا آيَةٌ كَذَلِكَ قَالَ الَّذِينَ مِن قَبْلِهِم مِّثْلَ قَوْلِهِمْ تَشَابَهَتْ قُلُوبُهُمْ قَدْ بَيَّنَّا الآيَاتِ لِقَوْمٍ يُوقِنُونَ{118} إِنَّا أَرْسَلْنَاكَ بِالْحَقِّ بَشِيراً وَنَذِيراً وَلاَ تُسْأَلُ عَنْ أَصْحَابِ الْجَحِيمِ{119}

"Wadanda ba su sani ba suna fadin cewa ina ma ace Allah ya yi magana da mu ko kuma wata aya ta zo mana. To kwatankwacin zancensu ne wadanda su ka gabace su su ka fada. Zukatansu sun yi kama. Mun kuma yi bayani ga mutanen da ba su da sakankancewa."

"Mun aiko ka da gaskiya mai bushara da gargadi. Ba za a tambaye ka ba akan ma'abota wuta." Daga cikin tambayoyin da jahilai su ke yi wa annabin musulunci da akwai cewa me ya sa Ubangiji zai aiko da ku annabawa su zama masu isar da sakonsa ga mutane? Me ya sa ba zai yi magana da mu kai tsaye ba ko kuma ya nuna mana ayoyinsa? Ya zamana mun ji zancen ubangiji da kunnuwanmu. Al'kura'ni mai girma yana maida martani ga zance irin wannan wanda ba shi da wani tushe. Yana kuma kwantarwa da annabi da kuma musulmi hankali da cewa wannan irin zancen ba sabo ba ne. Kafin kafiran zamanin annabi muhammadu su yi magana irin wannan, acan baya sun yi kwatankwacinta. Saboda haka zukatan wadannan mutanen da wadancan na zamunan baya kamanninsu guda ta fuskar rashin lafiya da kuma kin gaskiya. Mutanen da ba su da tsarkin da sakon sakon Ubangiji zai sauka akansu kai tsaye. A bisa kirdado ma idan ayoyin ubangiji su ka sauka gare su ba za su yi imani da su ba, domin kuwa tun da fari ma sun kawo waccan maganar ne domin kaucewa gaskiya ba domin su karbe ta ba. Idan har mutum zai karbi gaskiya to idan ta fito daga waninsa zai karbe ta. Ma'aunin gaskiya ba ya nufin cewa sai abinda ni na fada, ko abinda na fahimta. Idan mu ka ce sai idan ayoyin ubangiji sun sauka a kaina ne zan karbe su, to afili ya ke cewa, son kai shi ne mai muhimmanci a wurin mutum. Wato ni ne mai mai muhimmanci ba ita kanta gaskiyar ba. A fili ya ke cewa aikin annabawa shi ne isar da sakon ayoyin ubangiji da kuma yi wa mutane wa'azi da fadakar da su. Aikinsu shi ne isar da sako ba su tabbatar da cewa an ga sakamako ba. Saboda haka ba su yi wa mutane tilascin sai sun yi imani da gaskiya. A dalilin haka duk mutumin da ya karkace hanya sannan ya shiga wuta to bisa zabin kansa ne ba nauyi ne da ya hau wuyan annbawa ba.

Yanzu kuma sai aya ta 120 a cikin suratul Bakara.

وَلَن تَرْضَى عَنكَ الْيَهُودُ وَلاَ النَّصَارَى حَتَّى تَتَّبِعَ مِلَّتَهُمْ قُلْ إِنَّ هُدَى اللّهِ هُوَ الْهُدَى وَلَئِنِ اتَّبَعْتَ أَهْوَاءهُم بَعْدَ الَّذِي جَاءكَ مِنَ الْعِلْمِ مَا لَكَ مِنَ اللّهِ مِن وَلِيٍّ وَلاَ نَصِيرٍ

"Yahudu da nasara ba za su taba yarda da kai ba har sai ka bi tafarkinsu. Ka ce shiriyar Allah ita ce shirya. Idan ka biye wa son zuciyarsu bayan abinda ya zo maka na ilimi to ba ka da majibincin lamari da mataimaki daga Allah."

Bayan abinda ya faru na sauya alkibla haushin musulmi da yahudawa su ke ji ya kara yawa. Wani sashe na musulmi kuma son so a ce an ci gaba da fuskantar Baitul-mukaddas a matsayin alkibla, saboda ya zama sun sami madogara ta zaman lafiya da yahudawa. Sun gafala da cewa yahudawa sun fake da batun sauya alkibla ne domin su ci gaba da nuna adawarsu ga musulmi. Ba ya ga kasantuwarsu wadanda ba a shirye su ke ba su karbi musulunci suna son su karkatar da musulmin ne daga kan addininsu su maida su yahudawa. Muhimmin sakon da ya ke cikin wannan ayar shi ne gwargwadon yadda musulmi za su ja da baya daga kan akidarsu to makiya ma za su kara samun karfin guiwa su kara nutsewa cikin kafrici da baya. Saboda haka babu maganar ja da baya a cikin riko da addini.

Yanzu kuma sai aya ta 121 a cikin suratul Bakara.

الَّذِينَ آتَيْنَاهُمُ الْكِتَابَ يَتْلُونَهُ حَقَّ تِلاَوَتِهِ أُوْلَـئِكَ يُؤْمِنُونَ بِهِ وَمن يَكْفُرْ بِهِ فَأُوْلَـئِكَ هُمُ الْخَاسِرُونَ

'Wadanda mu ka baiwa littafi suna karanta shi tare da bashi hakkinsa, wadannan su ne wadanda su ka yi imani da shi. Wanda ya kafrice da shi to su ne tababbu."

A ko da yaushe kur'ani yana yin adalci hatta ga wadanda su ke adawa da shi. Saboda haka ne a cikin wannan ayar ya ke cewa tare da cewa mafi yawancin ma'abota littafi ba a shirye su ke su karbi musulunci ba, amma a tsakaninsu da akwai wadanda su ka karanta saukakken littafi da mahanga ta neman gaskiya su ka kuma yi imani da annabi da kuma littafi. A fili ya ke cewa wannan ayar tana yin bayani ne dangane cewa yin karatun lafuzzan kur'ani wanda abu ne mai kyau, amma bai wadatar ba. Abinda ya ke sa mutum ya sami shiriya shi ne yin tunani mai zurfi da daukar izina daga cikin ayoyin kur'ani wanda shi ne ma'anar bada hakkin karatu.

Yanzu kuma sai ayoyi na 122 da 123 a cikin suratul Bakara.

يَا بَنِي إِسْرَائِيلَ اذْكُرُواْ نِعْمَتِيَ الَّتِي أَنْعَمْتُ عَلَيْكُمْ وَأَنِّي فَضَّلْتُكُمْ عَلَى الْعَالَمِينَ{122} وَاتَّقُواْ يَوْماً لاَّ تَجْزِي نَفْسٌ عَن نَّفْسٍ شَيْئاً وَلاَ يُقْبَلُ مِنْهَا عَدْلٌ وَلاَ تَنفَعُهَا شَفَاعَةٌ وَلاَ هُمْ يُنصَرُونَ{123}

"Ya ku Bani Isra'ila ku tuna da ni'imomin da na yi muku baiwa da su kuma na fifita ku akan mutanen duniya." "Ku ji tsoron ranar da wani rai ba zai fanshewa wani rayin daga wani abu ba, kuma ba za a karbi muyasa daga gare ta ba kuma ceto ba zai amfaneta ba ba kuma za a taimake su ba."

Idan mai sauraro zai iya tunowa a cikin ayoyi na 47 da 48 da mu ka karanta a baya a cikin wannan sura din sun yi magana ne akan wannan jigon da mu ka yi bayaninsa. Kuma saboda karancin lokacin da mu ke da shi ba za mu maimaita ba. Yanzu kuma sai magana akan darussan da su ke cikin ayoyin da mu ka karanta. 1-mu karbi gaskiya koda kuwa daga wani ne ta fito. Kada mu rika daukar cewa sai abin da na fada ne ko wana jam'iyyata ko kungiyata ta ke fada ya ke zama gaskiya, kuma duk abinda wani wanda ba ni ma ya fada bata ne. Ya zamana mun sanya mutane su zama su ne ma'aunin gaskiya. Ko kadan ba haka ba ne, mutane ba su ne ma' aunin gakiya ba a wurinmu. 2-Annabawan Allah sun zo ne saboda su yi wa'azi da fadakarwa da yin bushara da gargadi. Ba su zo domin su tilastawa mutane karbar imani ba. Saboda haka wadanda su ka kaucewa gaskiya sune ke da alhakin ayyukansu da su ka zabi hanyar bata isa zabinsu. 3-Saboda kiran wasu zuwa ga addini bai kamata ya sa yi watsi da riko da abubuwan da su ke na tushe ba, Wajibi ne a gare mu mu zama masu son shriyar da mutane ba biye wa son zuciyar su ba. 4-Yin adalci hatta ga wadanda ake da sabani da su. Saboda ayar da ta ke yin suka akan Bani isra'ila tana amfani da kalmomi irin su " Mafi yawanci" ko "wani sashe" ko "Wata kungiya" saboda kada a danne hakkin nakwarai daga cikinsu. Za mu rufe wannan shirin da yin addu'a akan cewa Allah ya bamu dacewa mu zama masu shiriyar da batattu. Kuma mu yi mu'amala da su a cikin adalci ba tare da mun ja da baya ba daga kan manufofi.

Sai kuma wani shirin na gaba.

Suratul Bakara; Aya Ta 124-127 (Kashi Na 38)

Da sunan Allah mai Rahama mai Jinkai.

Salamu Alaikum Masu sauraro. Barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shirin karo ta 38 wanda mu ke gabatar muku da tafsirin ayoyin kur’ani mai tsarki cikin hanya mafi sauki. To a yau shrin namu zai ci gaba ne daga inda mu ka tsaya. Wato daga kan aya ta 124 zuwa ta 127.

Yanzu za mu fara daga aya ta 124 da ta ke cewa:

وَإِذِ ابْتَلَى إِبْرَاهِيمَ رَبُّهُ بِكَلِمَاتٍ فَأَتَمَّهُنَّ قَالَ إِنِّي جَاعِلُكَ لِلنَّاسِ إِمَاماً قَالَ وَمِن ذُرِّيَّتِي قَالَ لاَ يَنَالُ عَهْدِي الظَّالِمِينَ

“Yayinda da Ubangijin Ibrahim ya jarrabe shi da kalmomi sai ya bada su cikakku. Ubangijinka ya ce hakika ni zan sanya ka abin koyi ga mutane. Sai ( Ibrahim) ya ce: Kuma ka sanya limaman nan daga zuciyata. Sai ( Ubangiji) ya ce alkawalina baya samun azzalumai.”

Annabi Ibrahim yana da matsayi na musamman a tsakanin annabawan Allah. Sau 69 ne ambaton sunansa ya zo a cikin kur’ani kuma a cikin surori 25. Tamkar annabin musulunci shi ma ana ambatonsa a matsayin abin koyi ne. Acikin wannan sura din daga kan wannan ayar har zuwa ayoyi goma sha takwas da su ka biyo baya ana magana ne akan wannan annabin na Ubangiji mai girma a matsayin gwarzo na tauhidi wanda kuma ya gina ka’aba. Ya kai ga samun mukamai a wurin Allah ta hanyar cin jarabawa mai yawa. Jarabawa tana daga cikin tabbatacciyar sunnar Allah akan mutane. Sai dai shakka babu jarabawar Allah ba irin ta mutum ba ce. Ta mutum ana so a san ko ya wan wani abu ne, shi kuwa Allah masanin komai ne. Wannan irin jaraabwa tana zuwa ne saboda halin mutane na kwarai da akasinsa ya fito fili, ya kuma bayyana hanyar da mutum zai zabarwa kansa domin ya sami sakamakon da ya dace da shi. “Kalmomi” da su ka zo a cikin wannan aya suna nufin wasu ayyuka masu nauyi wadanda Unagiji da dora wa annabi Ibrahim aikatawa shi kuma ya aiwatar da su, za kuma mu yi ishara da wasu daga cikinsu. Annabi Ibrahim ne kadai mai kadaita ubangiji a tsakanin mutanensa, sai ya zama mai fada da shirka da kuma gumaka. Shi kaidai ya shiga cikin dakin gumaka ya karairaya su. Tare da cewa masu bautar gumaka sun dauki mataki akansa saboda abinda ya aikata su ka jefa shi cikin wuta, ya shiga cikin wutar yana mai cikakken imani da tawakkali ga Allah, bisa umarnin Allah wuta ta zama mai sanyi mai aminci. Tare da cewa ya yi rayuwa mai tsawo ba tare da haihuwa ba, Ubangiji ya azurta shi da Da a lokacin tsufa, sai dai kuma a lokacin da umarnin Ubangiji ya zo masa ya dauki dansa Isma’il zuwa inda zai sadaukar da shi. Ibrahim ya roki Allah ya baiwa ‘ya’yanza da zuriyarsa mukamin imamanci, sai dai Ubangji madaukaki ya bashi jawabi da cewa: “Wannan ba mukami ne na gado ba ana samunsa ne ta hanyar dacewa da cancanta. Matsayin imamanci yana sama da na manzanci. Manzo ana umartarsa ne da ya isar da sakon hukunce-hukuncen Allah ya yi bushara da kuma gargadi ga mutane, shi kuma Imam aikinsa ne ya zartar da wadannan hukunce-hukuncen da kuma aiwatar da adalci a tsakanin mutane. Wannan ayar tana yin bayani ne a fili cewa imamanci alkawali ne da kuma amana daga Allah da baya dora su akan azzalumai da masu sabo. A bisa wannan ka’idar ne shi’a su ka yi imani da cewa, shi ma imami kamar annabi dole ne ya zama ma’asumi, wanda duk ya taba yin shirka ko aikata sabo ba zai zama imami ba.

Yanzu kuma sai aya ta 125 da ta ke cewa:

وَإِذْ جَعَلْنَا الْبَيْتَ مَثَابَةً لِّلنَّاسِ وَأَمْناً وَاتَّخِذُواْ مِن مَّقَامِ إِبْرَاهِيمَ مُصَلًّى وَعَهِدْنَا إِلَى إِبْرَاهِيمَ وَإِسْمَاعِيلَ أَن طَهِّرَا بَيْتِيَ لِلطَّائِفِينَ وَالْعَاكِفِينَ وَالرُّكَّعِ السُّجُودِ

“Yayinda mu ka sanya ka’aba a matsayin waurin gamuwar mutane da kuma aminci. Ku riki mukami Ibrahim a matsayin wurin salla. Mun umarci Ibrahim da Isma’ila da ku tsarkake dankina dom masu yin dawafi da masu yin iitikafi da masu yin ruku’u da masu sujjada.”

Ayar da ta gabata ta yi ishara ne da matsayi mai girma na annabi Ibrahim da kuma imamancinsa. Wannan ayar kuwa tana magana ne akan aikin da annabi Ibrahim ya bari wanda ake tunawa da shi wanda shi ne ka’aba. Ubangiji yana fadin cewa wannan dakin, daki ne na haduwar mutane, wurin da masu tauhidi su ke taruwa. Wuri ne na aminci kuma mai tsarki da ake yin dawafi da kuma salla acikinsa. Alhazai da su ke zuwa makka idan sun gama dawafi to dole ne su yi salla raka’a biyu. Saboda jinjinawa annabi Ibrahim akan wahalar da ya sha, ubangiji ya sanya dutsen da annabi Ibrahim ya rika takawa alokacin da ya ke gina bangayen ka’aba ya zama waurin da mahajjata za su rika yin salla. Baya ga ginin ka’aba da annabi Ibrahim da Isma’ila su ka yi, sun kuma zama masu yin hidima gare ta. Sun tsarkake masallacin harami daga duk wani datti saboda masu yin ibada da salla. A bisa ka’ida masu yin hidima ga dakin Allah wajibi ne su zama waliyyan Allah masu tsarki, haka nan duk wanda nauyin kula da wannan sallaci yah au wuyansa.

Yanzu kuma za mu karanta aya ta 126.

وَإِذْ قَالَ إِبْرَاهِيمُ رَبِّ اجْعَلْ هَـَذَا بَلَداً آمِناً وَارْزُقْ أَهْلَهُ مِنَ الثَّمَرَاتِ مَنْ آمَنَ مِنْهُم بِاللّهِ وَالْيَوْمِ الآخِرِ قَالَ وَمَن كَفَرَ فَأُمَتِّعُهُ قَلِيلاً ثُمَّ أَضْطَرُّهُ إِلَى عَذَابِ النَّارِ وَبِئْسَ الْمَصِيرُ

“Yayinda Ibrahim ya fadi cewa,Ubangiji ka sa wannan gari ya zama amintacce ka kuma azurta mutanesa da su ka yi imani da Allah da ranar kiyama da nauoin itatuwa. Sai (Ubangiji) ya ce zan azurta wanda ya kafirta ma, in jiyar da shi dadi muddar rayuwarsa sannan in saka masa da azabar wuta. Tir da makoma”.

Annabi Ibrahim wanda ya gina ka’aba sannan kuma ya gyara shi domin masu yin ibada, ya roki Allah da ya baiwa mazauna garin makka abubuwa guda biyu: Na farko shi ne aminci da zaman lafiya na biyu kuwa shi ne ni’ima da wadata da jin dadin rayuwa. Tabbas annabi Ibrahim ga muminai kadai ya yi addu’a, amma Ubangiji da ya bashi jawabi ya fada masa cewa, zan azurta kowa da kowa da abin duniya, mumini da kafiri. B azan haramtawa kafirai arziki a duniya ba saboda kafircinsu, amma a kiyama sakamakonsu shi ne wutar jahannama. Wannan ayar tana yin bayani ne akan abubuwa guda biyu. Na farko shi ne jin dadin muninai daga abin duniya da rayuwa cikin ni’ima, saboda haka ne annabi Ibrahim ya roka musu. Na biyu shi ne wadatuwar da kafirai su ke da ita a rayuwar duniya baya nufin cewa suna kan gaskiya, yana nuni ne akan rashin kimar jin dadin duniya a wurin Ubangiji.

Yanzu kuma sai aya ta 127.

وَإِذْ يَرْفَعُ إِبْرَاهِيمُ الْقَوَاعِدَ مِنَ الْبَيْتِ وَإِسْمَاعِيلُ رَبَّنَا تَقَبَّلْ مِنَّا إِنَّكَ أَنتَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ

“A yayin da Ibrahim da kuma Isma’ila ya ke daukaka jigajigan ka’aba, yana cewa, Ubangijina ka karba daga gare mu, kai mai ji ne, masani.”

Tun a lokacin annabi Adamu ne dankin ka’aba ya kasance, amma annabi Ibrahim ya sake gina shi, dalilin hakan kuwa shi ne cewa annabi Ibrahim ya zabi makka a matsayin wurin da matarsa da kuma dansa za su zauna inda ya ke fadin cewa: “Ubangji, na zaunar da iyalina a wurin da ba shi da tsiro a kuma da dakinka mai alfarma.” Saboda haka a lokacin da annabi Ibrahim ya shiga makka dankin Allah wato ka’aba tana nan. Bugu da kari a cikin aya ta 96 a suratu ali-Imran, an bayyana ka’aba a matsayin dakin farko da aka gina ga mutane. Wannan ayar tana nufin cewa idan wani aiki an yi she saboda Allah, to gini da kwadago suna a matsayin ibada ne. A bisa tushe nau’in aiki ba shi da muhimmanci, karbuwar aikin da Allah zai yi ne mai muhimmanci. Idan da za mu gina ka’aba sannan kuma ya zama Allah abi karbi wannan aikin ba to ba shi da wata kima. Yanzu kuma za mu duba darussan da su ke cikin wannan ayoyin. 1-Ubangiji yana bada matsayi da daukaka ne bisa dacewar daidaikun mutane, yana kuma yi wa mutane jarabawa da abubuwa da dama domin dacewar wadannan mutanen ta fito fili. 2-Imamanci, matsayi ne daga Allah ba matsayi ne na abin duniya ba, saboda haka dole ne ya zama yana da sharudda na musamman. Adalilin haka ba kowane mutum ba ne zai iya zama jagoran al’ummar musulmi, wajibi ne ya zama Ubangiji ne ya nada shi. 3-Masallatai dakunan Allah ne saboda haka suna da hurumi na musamman da tsarki, kuma mutanen da su ke da tsarki ne za su zama masu kula da su, ba mutanen da ba su dace ba. 4-Makka yana a matsayin birnin musulunci abin koyi kuma wuri ne na ibada, sannan cibiya ce ta aminci da bautar Ubangiji a karkashin aminci da tsaro domin kuwa ibada tana yiyuwa ne idan akwai tsaro. Addini ba nesa ya ke da duniya ba. A karshen wannan shirin muna rokon Allah da ya azurta mu da ziyartar dabkinsa bisa sani da kuma kauna. Ya kuma sa mu zama masu koyi da annabi Ibrahim da kuma cin jarrabawa. Muna ban kwana da ku anan har zuwa lokacin shiri na gaba.

Suratul Bakara; Aya Ta 128-133 (Kashi Na 39)

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai.

Masu sauraro barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shirin karo na talatin da tara. Kuma zamu ci gaba ne daga inda mu ka tsaya a baya a tafsirin ayoyin kur’ani mai girma cikin hanya mafi sauki.

Yanzu za mu karanta aya ta 128 da ta ke cewa:

رَبَّنَا وَاجْعَلْنَا مُسْلِمَيْنِ لَكَ وَمِن ذُرِّيَّتِنَا أُمَّةً مُّسْلِمَةً لَّكَ وَأَرِنَا مَنَاسِكَنَا وَتُبْ عَلَيْنَا إِنَّكَ أَنتَ التَّوَّابُ الرَّحِيمُ

“Ubangijinmu ka sanya mu masu mika kai gare ka da kuma zuriyarmu, ka kuma nuna mana hanyoyin da za mu bauta maka, ka yi mana gafara, kai mai karbar tuba ne kuma mai rahama.”

Sirrin samun nasarar annabi Ibrahim acikin dukkanin abinda ya ke yi shi ne mika wuya ga Allah da umarninsa,wannan siffar ta kai koli a cikin yadda ya zama cikin shiri domin ya yanka dansa Isma’il. Wannan shi ne ya sa annabi Ibrahim ya kori Allah ya sa shi da dansa da kuma zuriyarsa su zama masu biyayya da mika kai ga umarnin ubangiji, domin kuwa kamala baki dayanta tana tattara da bautar Allah makadaicin sarki. Sai dai wajibi ne bautar ubangiji ta kasance acikin wata siga ta musamman domin a kaucewa yin bidi’a da soki-burutsu. Wannan ne sa annabi Ibrahim ya roki Ubangiji da ya nuna masa hanyar da zai bauta masa ta kasance daidai da yadda ya yarda da ita.

Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 129.

رَبَّنَا وَابْعَثْ فِيهِمْ رَسُولاً مِّنْهُمْ يَتْلُو عَلَيْهِمْ آيَاتِكَ وَيُعَلِّمُهُمُ الْكِتَابَ وَالْحِكْمَةَ وَيُزَكِّيهِمْ إِنَّكَ أَنتَ العَزِيزُ الحَكِيمُ

“Ubangijinmu ka aiko manzo acikinsu daga cikinsu wanda zai rika karanta ayoyinka a gare su, ya sanar da su littafi da hikima ya kuma tsarkake su. Kai ne mai rinjaye, gwani.”

Damuwa da zuriya mai zuwa a gefe daya da kuma damuwa da makomarsu shi ne abinda ya sa annabi Ibrahim yin addu’a domin shiriyar masu zuwa kafin ya roki wani abu saboda kansa a wurin ubangiji. Saboda sa’adar mutum ba tare da shiriyar ubangiji ba, ba karbabben abu ne ba, shi ne ya sa annabi Ibrahim ya roki Allah da ya aiko da annabi ga mutane wanda zai rika ilmantar da su da yi musu tarbiyya.

Yanzu kuma za mu karanta aya ta 130 zuwa ta 131.

وَمَن يَرْغَبُ عَن مِّلَّةِ إِبْرَاهِيمَ إِلاَّ مَن سَفِهَ نَفْسَهُ وَلَقَدِ اصْطَفَيْنَاهُ فِي الدُّنْيَا وَإِنَّهُ فِي الآخِرَةِ لَمِنَ الصَّالِحِينَ{130} إِذْ قَالَ لَهُ رَبُّهُ أَسْلِمْ قَالَ أَسْلَمْتُ لِرَبِّ الْعَالَمِينَ{131}

“Babu wanda zai kyamaci tafarkin Ibrahim sai wanda ya wawautar da kansa. Hakika mun zabe shi a duniya, kuma tabbas shi a lahira yana cikin salihai.” “ Yayin da Ubangijinsa ya ce masa ka mika wuya, sai ya ce na mika wuya ga ubangijin talikai.”

Wannan ayar tana bayyana annabi Ibrahim a matsayin mutum abin koyi kuma zababben Ubangiji wanda tafarkin Allah da ya ke tafiya akansa ya ke a matsayin abin koyi ga dukkanin mutanen duniya. Ashe ba wauta ba ce ace wani mutum ya yi watsi da wannan tafarkin wanda ya ke cike da tsarki, ya bi tafarkin shirka da kafirci? Tafarki ne wanda ya dace da fitra ta mutum kuma hankalin mutum ya ke karbarsa. Tafarkin annabi Ibrahim yana da kimar da ta kai ga annabin musulunci yana yin alfahari da bin wannan tafarkin na annabi Ibrahim. Shi mutum ne wanda ya ke yin galaba akan kafrai ta hanyar kafa dalilai na mandiki da kuma jarunta ya ke karairaya gumaka da gatari shi kadai. Saboda mika kai ga Ubangiji ne ya ajiye matarsa da dansa acikin saharar makka mai zafin kuna, kuma ya yi azamar sadaukar da matashin dansa, saboda ya tabbatar da cewa zuciyarsa ta damfaru ne da ubangiji ba da mata da ‘ya’ya ba. Afili ya ke cewa Ubangiji ya zabi mutum irin wannan ne a matsayin annabi kuma imami sannan ya sanya shi abin koyi ga mutane saboda abubuwan da ya kebanta da su. Babu wanda zai kyamaci wannan tafarkin sai wawa da kuma rashin aiki da hankali.

Yanzu zamu karanta aya ta 132 a cikin suratul Bakara.

وَوَصَّى بِهَا إِبْرَاهِيمُ بَنِيهِ وَيَعْقُوبُ يَا بَنِيَّ إِنَّ اللّهَ اصْطَفَى لَكُمُ الدِّينَ فَلاَ تَمُوتُنَّ إَلاَّ وَأَنتُم مُّسْلِمُونَ

“Ibrahim ya wasici ‘ya’yansa da ya’akub da addinisa ya ce: yak u ‘ya’yana Allah ya zaba mu ku addini kada ku mutum sai kuna masu mika wuya.”

Mahaifi mai tausayi kuma mai kirki aikinsa dangane da ‘ya’yansa bai tsaya acikin kokarin samar musu da abin duniya ba, yana kuma kiyaye lafiyar tunaninsu da akidarsu da hana su karkacewa da bacewa, wadannan ne abubuwan da ya ke baiwa muhimmaci fiye da komai. Akodayaushe waliyan Allah suna kiran ‘ya’yansu ne zuwa ga Allah. Kuma a lokacin mutuwarsu suna yi musu wasiyya ne da tauhidi da ibada ba rabon dukiya da abin duniyar da za su bari ba.

Yanzu kuma za mu saurari aya ta 133.

أَمْ كُنتُمْ شُهَدَاء إِذْ حَضَرَ يَعْقُوبَ الْمَوْتُ إِذْ قَالَ لِبَنِيهِ مَا تَعْبُدُونَ مِن بَعْدِي قَالُواْ نَعْبُدُ إِلَـهَكَ وَإِلَـهَ آبَائِكَ إِبْرَاهِيمَ وَإِسْمَاعِيلَ وَإِسْحَاقَ إِلَـهاً وَاحِداً وَنَحْنُ لَهُ مُسْلِمُونَ

“Shin ku ( yahudawa) kuna nan ne a lokacin da mutuwa ta bijirowa yaa’kub, yayin da ya fadawa ‘ya’yansa cewa me za ku bautawa bayana? Sun ce za mu bautawa ubangijinka, ubangijin mahaifanka Ibrahim da Isma’ila da Ishaka wanda shi ne Ubangiji guda daya, mu masu mika wuya ne gare shi.”

Wani sashe na yahudawa sun riya cewa alokacin da annabi Ya’kub zai yi wafati ya kirayi ‘ya’yansa da su yi riko da addinin yahudanci da su ke yi, akan haka ne Ubangiji ne ya ke fadin cewa: “Shin kuna nan ne a lokacin da mutuwa ta zo wa annabi ya’akub balle ku fadi cewa ya kirayi ‘ya’yansa da su bi addinin yahudanci? Ya kirayi ‘ya’yansa ne da su mika wuya ga ubangiji makadaici, kuma ‘ya’yan nashi sun yi alkawalin yin biyayya ga Ubangiji makadaici. Kuma kamar yadda a ayar da ta gabata mu ka bayyana cewa wajibi ne ga iyaye su zama masu jin nauyi a wuyansu dangane da tunani da akidar ‘ya’yansu, kuma aduk lokacin da dama ta samu da kuma lokuta masu hatsari su rika kula da ayyukansu. Daya daga cikin dalilan tauhidi shi ne cewa dukkanin annabawan da su ka zo suna bada labarin Ubangiji guda daya ne, wanda shi ne ubangijin Ibrahim da Isma’ila da Ishak. Da kuwa da akwai wani Ubangiji baya ga allah madaici to da shi ma ya yi aike kuma sanar da kanshi ga mutane. Yanzu kuma sai darussan da su ke cikin wadannan ayoyin. 1-Mu mika kai ga Allah shi kadai, domin kuwa sirrin samun dace yana acikin mika kai gare shi da kuma bin umarninsa. 2-Ayayin addu’oi kada mu takaita rokon abin duniya kadai, mu kuma rika yin addu’a akan sa’adar ‘ya’yanmu da zuriya mai zuwa. 3-Ba wanda ya rasa hankalinsa ne kadai wawa ba, wawa shi ne wanda cikin hankalinsa da saninsa ya ke zabar bin karkatacciyar hanya wacce zai bace. 4-Kyakkyawan karshe da dawwama acikin imani har zuwa mutuwa yana da matukar muhimmanci. Da dama ana samun musulmin da ya ke mutuwa ba musulmi ba. Saboda haka mu zama masu yin tunani akan yadda za mu kare imaninmu da kuma na ‘ya’yanmu, kada kuma mu gamsu da kasantuwarmu musulmi a halin da mu ke ciki kadai. A karshen wannan shirin muna rokon Allah da ya sa mu zama masu mika wuya ga umarninsa kamar annabi Ibrahim, ya kuma kiyaye mana imaninmu daga karkacewa.

Suratul Bakara; Aya Ta 134-138 (Kashi Na 40)

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai. Masu sauraro barkanmu da saduwa da ku a cikin wannan shirin wanda mu ke yin tafsirin ayoyin kur’ani cikin sauki. A yau ma za mu ci gaba ne daga inda mu ka tsaya acikin suratul Bakara wato daga kan aya ta 134 zuwa ta 138.

Za mu karanta aya ta 134 daga suratul bakara.

تِلْكَ أُمَّةٌ قَدْ خَلَتْ لَهَا مَا كَسَبَتْ وَلَكُم مَّا كَسَبْتُمْ وَلاَ تُسْأَلُونَ عَمَّا كَانُوا يَعْمَلُونَ

“Wadancanenka al’umma ce da ta riga ta gushe, abinda da su ka aikata yana gare su, kuma abinda ku ka aikata yana gare ku. Ba za a tambaye ku akan abinda su ka kasance suna aikatawa ba.”

Banu Isra’ila sun kasance mutane masu yawan alfahari da magabatansu, kuma suna daukar cewa koda sun aikata laifuka marasa kyau to za su sami rahama saboda ayyukan kwarai da magabatansu su ka yi. Sai ya zama maimakon su rika yin ayyukan kwarai sai su ka buge da ambaton ayyukan magabatansu. Wannan ayar tana yin gargadi ne a gare su da kuma musulmi akan cewa kowane mutum shi ne mai daukar alhakin ayyukansa, kuma a ranar kiyama alaka tsakanin Dad a mahaifinsa da danginsa ba ta da matsayi, saboda haka kada aikin magabatanku ya sa ku rika jin dadi. Amirul-muminina ( A.s.) a cikin wata gajeruwar jumla yana fadin cewa: “ Ana samun daukaka ne ta hanyar himma ba ta dogaro da rubabbun kasusuwan magabata ba.”

Yanzu kuma za mu saurari aya ta 135.

وَقَالُواْ كُونُواْ هُوداً أَوْ نَصَارَى تَهْتَدُواْ قُلْ بَلْ مِلَّةَ إِبْرَاهِيمَ حَنِيفاً وَمَا كَانَ مِنَ الْمُشْرِكِينَ

“Sai su ka ce ku zama yahudawa ko nasaru sai ku shiriya. Ka ce da su, tafarkin Ibrahim dai na gaskiya, shi bai kasance acikin masu shirka ba.”

Yahudawa suna daukar kansu a matsayin wanda su ke kan gaskiya, masu bin addinin kiristanci kuma akan bata. Su ma mabiya addinin kiristanci suna daukar kansu a matsayin masu bin gaskiya yahudawa kuma wadanda su ke kan bata. Saboda haka ne kowane daya daga cikinsu ya ke kiran dan’uwansa zuwa ga akidarsa. Suna fadin cewa idan kuna son zama shiryayyu to ku karbi akidarmu. Kur’ani da ya ke maida martani ga wannan irin halin na kebance kai da bin gaskiya wanda babu dalili akansa, yana fadin cewa, hanyar shiriya, ita ce bin gaskiya ba bin wata kungiya ba. Kuma a wurin annabi Ibrahim ne za ku koyi wannan irin bin gaskiyar wanda bai taba yin shirka ba. Abinda wannan ayar ta ke koya mana shi ne cewa suna ba shi ne mai muhimmanci ba, imani da aiki su ne masu muhimmanci. Zama bayahude ko banasare sunaye ne kadai, abinda ya ke da kima shi ne tauhidi da kadaita Allah.

Yanzu kuma za mu karanta aya ta 136 a suratul Bakara.

قُولُواْ آمَنَّا بِاللّهِ وَمَا أُنزِلَ إِلَيْنَا وَمَا أُنزِلَ إِلَى إِبْرَاهِيمَ وَإِسْمَاعِيلَ وَإِسْحَاقَ وَيَعْقُوبَ وَالأسْبَاطِ وَمَا أُوتِيَ مُوسَى وَعِيسَى وَمَا أُوتِيَ النَّبِيُّونَ مِن رَّبِّهِمْ لاَ نُفَرِّقُ بَيْنَ أَحَدٍ مِّنْهُمْ وَنَحْنُ لَهُ مُسْلِمُونَ

“Su ka ce mun yi imani da Allah da abinda aka saukar a gare mu da abinda aka saukar ga Ibrahim da Isma’ila da Ishak da Ya’akub da annabawa daga zuriyarsa da abinda aka baiwa Musa da Isa da abinda aka baiwa annabawa daga Ubangijinsu, ba mu banbanta tsakanin daya daga cikinsu, mun mika wuya a gare shi.”

Dangane da ci gaban bayani akan jayayyar da ke tsakanin yahudawa da mabiya addinin kiristanci, wannan ayar tana yin magana da su da kuma mabiya sauran addinai da cewa kada ku rika banbanta tsakanin annabawan Allah. Babu wani banbanci a tsakaninsu domin kuwa dukkaninsu daga Allah su ke zo, kuma ku yi imani da dukkanin abinda su ka zo da shi. Ba wai ku yi imani da abinda annabin da aka aiko muku shi kadai ba, ku ki yin imani da littatafan da aka aikowa wasu annabawan ba. Annabawan Allah tamkar malaman makaranta ne da kowane daya daga cikinsu ya ke yi wa wani sashe na mutane tarbiyya a wani zango na zamani, kuma daidai da yadda ci gaban tunanin bil’adama ya ke a cikin wannan zamani a tsawon tarihi. Ubangiji ya sauko da littatafai da tsarin ibada domin shiriyar da bil’adama.

Yanzu za mu karanta aya ta 137.

فَإِنْ آمَنُواْ بِمِثْلِ مَا آمَنتُم بِهِ فَقَدِ اهْتَدَواْ وَّإِن تَوَلَّوْاْ فَإِنَّمَا هُمْ فِي شِقَاقٍ فَسَيَكْفِيكَهُمُ اللّهُ وَهُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ

“Idan su ka yi imani da abinda ku ka yi imani da shi, to sun shiriya, idan kuwa su ka juya da barin bada gaskiya da shi to suna cikin sabani ne. Da sannu Ubangiji zai kiyaye ka daga gare su, domin kuwa shi mai ji ne kuma masani.”

Ubangiji yana magana ne da musulmi da fadin cewa, idan ma’abota littafi su ka yi watsi da kebance kai da gaskiya da jin fifiko sannan su ka yi imani irin yadda ku ka yi imani, to sun shiriya. Idan kuwa su ka ci gaba da jin cewa su ne masu gaskiya kuma masu bin wani addini da sauran annabawa karkatattu ne, to wannan yana nuni ne da kin gaskiya da kuma yin nisa daga masu neman gaskiya. Karshen wannan aya kuwa yana kwantarwa da musulmi hankali ne akan cewa Ubangiji ya isar musu wajen kare su daga makircin makiya addini domin kuwa shi mai ji ne kuma masani.

Yanzu kuma sai aya ta 138 a cikin suratul Bakara.

صِبْغَةَ اللّهِ وَمَنْ أَحْسَنُ مِنَ اللّهِ صِبْغَةً وَنَحْنُ لَهُ عَابِدونَ

“Runin Allah, wanene ya fi Allah kyan rini? Mu masu yin bauta ne gare shi.”

Ubangiji madaukaki shi ne karshen fasahar zane a duniya, ya kagi halittar mutum sannan kuma ya runa shi fidira mai tsarki acikin ruhinsa. Sai dai mutane sun dushe wannan runin na Allah ta biye wa sha’awace-sha’awacen zuciyarsa da zuciyarsa. Bakin kishi na bangaranci da son kai da kungiya suna a matsayin launoni ne su ke haddasa sabani da rarraba mutane alhali kamata ya yi dukkanin launuka sun bace saboda runin da Allah ya yi wa mutum ya fito fili. Kowane irin launi yana dushewa saboda gushewar zamani, runin Allah ne kadai ya ke dawwama kuma shi ne tabbatacce. Dukkanin launi yana haddasa sabani da rarraba in bada runin Allah wanda shi ne ginshikin hadin kai da ‘yan’uwantaka shi ma a karkashin ibadar Allah makadaici. A bisa al’ada, mutum mai sajewa ne da launin da ya shiga ciki. Idan ya shiga cikin wata jama’a zai saje da ita saboda ya sami karbuwa, alhali kiran addini ba shi ne rashin sajewa ba, shi ne nesantar daukar wani launi. Rashin daukar launukan daban-daban- masu sunaye mabanbanta na shekaru ko ilimi ko dukiya ko mukami- shi ne abinda ya ke fito da runin Ubangiji. Yanzu kuma za mu ji darussan da su ke cikin wadannan ayoyin. 1-maimakon ace mun dogara da ayyukan magabata da yin alfahari da su, mu zama masu yin tunani akan aikin da za mu yi, kowa ya kasance mai yin aiki nashi na kanshi. Kada ya zamana wasu suna yin aiki saboda lahirarsu mu kuma mu zama masu yin alfahari da danginmu. 2-Mu zama masu goyon bayan gaskiya, ba masu bangaranci ba. Biyayya ga gaskiya ne ya ke budewa mutum idanuwa da kunnuwa domin fahimtar gaskiya, amma bangaranci yana makantar da mutum ya zama wanda baya ganin gaskiya. 3-Idan akwai imani acikin zuciya to yana bukatar ya kasance a tare da mika kai ga ayyuka. Babu yadda za a yi mutum ya riya cewa yana da imani a zuci amma maimakon mu mika kai ga umarnin Ubangiji sai mu biyewa son zuciya. 4-launi mafi fifiko shi ne runin fidira da Allah ya yi a tare da kowane mutum. Launi ne da ya ke dawwamamme wanda kuma shi ne ginshikin hadin kai da tsarki. A karshen wannan shirin muna rokon Allah da ya sake sanar da mu hakikanin kur’ani ya kuma ba mu dacewa mu yi aiki da kur’ani.

Suratul Bakara; Aya Ta 139-142 (Kashi Na 41)

Da sunan Allah mai Raham Mai jinkai. Masu sauraro barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shirin kaso na 41 da ya ke fassarar ayoyin al-kur'ani mai girma cikin hanya mafi sauki. Za kuma mu fara ne daga kan aya ta 139 zuwa ta 142 acikin suratul Bakara.

Da fari za mu saurari aya ta 139:

قُلْ أَتُحَآجُّونَنَا فِي اللّهِ وَهُوَ رَبُّنَا وَرَبُّكُمْ وَلَنَا أَعْمَالُنَا وَلَكُمْ أَعْمَالُكُمْ وَنَحْنُ لَهُ مُخْلِصُونَ

"Ka ce shin dangane da Allah ne ku ke yin jayayya da mu alhali shi ne ubangijinmu kuma ubangijinku, kuma ayyukanmu namu ne, kuma ayyukanku naku ne, mu muna masu tsarkake niyya a gare shi."

Abin takaici ne cewa wasu mabiya addinan da ba su da cikakkiyar masaniya akan koyarwar addini, suna zaton cewa suna da matsayi na musamman a wurin Ubangji, kuma da su kadai ne Ubangiji ya damu, kuma saboda su kadai ne ya aiko annabawa, saboda haka ba a shirye su ke ba su yi imani da wasu annabawa kuma ba su cikin masu yi musu biyayya. Allah madaukakin sarki ba shi da dangantaka da wata kabila ko da wasu iyalai domin kuwa a wurin kowa da kowa daidai wa daida su ke. Abu guda daya wanda ya ke sa mutane su kusance shi ko su yi nisa da shi shi ne aikin da su ke yi, kuma kowane mutum aiki da ya yi ne yake bibiyyarsa. Shakka babu aikin da ya ke zama karbabbe shi ne wanda aka yi da tsarkin niyya saboda Allah, domin kuwa wannan irin aikin yana nuni ne da imani na hakika da kuma nesantar duk wani nau'i na shirka. Wannan ayar tana yin nuni ne da cewa halin mutum na son ya mallaki kowai ya kai shi ga nuna cewa Ubangiji ma yana tare da shi ne shi kadai, ba waninsa ba. Yana daukar cewa Ubangiji nashi ne shi kadai ba na waninsa ba, alhali kuwa shi Ubangiji bai kebanta mabiyan wani addini ne ko wata zuriya ko wata kabila ba, Ubangiji na dukkanin talikai ne.

Yanzu kuma za mu saurari aya ta 140 a cikin suratul Bakara.

أَمْ تَقُولُونَ إِنَّ إِبْرَاهِيمَ وَإِسْمَاعِيلَ وَإِسْحَاقَ وَيَعْقُوبَ وَالأسْبَاطَ كَانُواْ هُوداً أَوْ نَصَارَى قُلْ أَأَنتُمْ أَعْلَمُ أَمِ اللّهُ وَمَنْ أَظْلَمُ مِمَّن كَتَمَ شَهَادَةً عِندَهُ مِنَ اللّهِ وَمَا اللّهُ بِغَافِلٍ عَمَّا تَعْمَلُونَ

" Ko kuna cewa ne Ibrahim da Isma'ila da Ishak da ya'akub da zuriyars, sun kasance yahudawa ne ko nasara, ka ce shin ku ne mafi sani ko kuma Allah. Wanene ya fi zalunci daga wanda ya boye sheda a wurin Allah. Allah ba mai gafala ba ne daga abinda su ke aikatawa."

Wasu daga cikin mabiyan annabi Musa da annabi Isa da su ke son tabbatar da cewa addininsu ne kadai gaskiya da kuma rusa sauran addinai. Abinda su ke riyawa kenan har ta kai suna cewa annabi Ibrahim da kuma sauran annabawan da su ka zo bayansa suna kan addininsu ne. Ga shi kuwa ta fuskar tarihi annabi Musa da annabi Isa sun zu ne bayan wadancan annabawan, saboda haka abinda wadannan mutanen su ke riyawa ba komai ba ne sai bakin kishi mara dalili da kuma nuna wariya, idan ba wannan ba ba su da wani dalilin da za su iya dogaro da shi. Al'kur'ani yana bayyana gurbata gaskiya ko boye ta a matsayin zalunci mai girma, musamman ma dai idan ya kai ga karkacewar akida da kuma tunanin zuriyar da ta biyo baya da kuma zamunna mabanbanta, ya kuma hana al'adun bil'adama su bunkasa su kai ga kamala.

Yanzu kuma za mu saurari aya ta 141:

تِلْكَ أُمَّةٌ قَدْ خَلَتْ لَهَا مَا كَسَبَتْ وَلَكُم مَّا كَسَبْتُمْ وَلاَ تُسْأَلُونَ عَمَّا كَانُواْ يَعْمَلُونَ

"Wancanenka al'umma ce da ta gushe, abinda ta aikata nata ne kuma abinda ku ka aikata naku ne, ba kuma za a tambaye ku akan abinda su ka rika aikatawa ba."

Wannan ayar tazo ne domin maida martani ga abinda wasu yahudawa da nasara su ke riyawa mara tushe wanda ambatonsa ya zo a cikin ayar da ta gabata, yana fadin cewa me ya sa ku ke tunanin jawo abinda ya faru tarihinku na baya zuwa yanzu. Al'ummar da ta ke rayayya dole ne ta zama wacce ta ke dogaro da ayyukanta, ba da tarihin magabatanta annabawa da kabilarta ba. Dukkaninsu sun gushe kuma ayyukan da su ka yi yana damfare ne da su, kamar kuma yadda ayyukanku su ke damfare da ku. Daukaka wani abu ne da wanda daidaikun mutane da kungiyoyi su ke samu ta hanyar aiki, ba abu ne da ake gado ba wanda 'ya'ya za su gada daga iyaye.

Yanzu kuma za mu saurari aya ta 142 a cikin suratul Bakara.

سَيَقُولُ السُّفَهَاء مِنَ النَّاسِ مَا وَلاَّهُمْ عَن قِبْلَتِهِمُ الَّتِي كَانُواْ عَلَيْهَا قُل لِّلّهِ الْمَشْرِقُ وَالْمَغْرِبُ يَهْدِي مَن يَشَاءُ إِلَى صِرَاطٍ مُّسْتَقِيم

" Da sannu wawaye daga cikin mutane za su ce me ya juyad da su daga alkiblar da su ka kasance a kanta. Kace gabas da yamma duk na Allah ne yana shiryar da wanda ya so zuwa ga tafarki madaidaici."

A cikin shirin da ya gabata, mun yi ishara da cewa daya daga cikin abubuwan da yahudawa su ke sukar musulmi da shi, shi ne batun sauya alkibla daga Baitul Mukaddas zuwa makka. Wannan ayar da kuma ayoyin da su ka zo bayanta suna yin magana ne a fili dangane da wannan batun sannan kuma ta ke maida martani akan hakan. Bayan aike, manzon Allah ya dauki shekaru goma sha uku a makko ya rika fuskantar Baitul Mukaddas yana yin salla. Domin kuwa albibla ce wacce dukkanin masu bautar Allah su ke girmamawa, wuri ne kuma da dukkanin addinai su ke girmamawa. Na biyu shi ne cewa, mushrikan makka sun maida ka'aba ta zama wurin bautar gumaka, idan ma'aiki ya tsaya a masallacin harami yana fuskantar ka'aba to a hakikanin gaskiya yana fuskantar gumakan da su ke cikin ka'abar ne. Bayan yin hijira zuwa madina an dauki wasu watanni musulmi suna fuskantar Baitul mkaddas suna yin salla har zuwa lokacin da yahudawa su ka maida batun ya zama na suka suna fadin cewa, mu ku ke yi wa biyayya, ba ku cin gashin kanku, domin kuwa ba ku da alkibla taku ta kanku. Wannan cin zarafin ya fusata ma'aiki da kuma musulmi. Umarni ya zo daga Ubangiji akan sauya alkibla, a yayin da manzon Allah ya ke cikin yin sallar azahar a cikin masallaci. Mala'ika Jibra'ilu ya zo da umarni ga annabi da ya juya alkibla zuwa ga Ka'aba. saboda haka ne ake kiran wannan masallacin da sunan "masallacin alkibloli biyu". Sai dai yahuawa wadanda aikinsu shi ne yin suka, sun sake yin wata sukar su ka fadawa musulmi cewa, idan alkiblarku ta baya daidai ce to me ya sa ku ka sauya ta? Idan kuwa wannan sabuwar alkiblar ce daidai to ya me ya sa tun da farko ku ka rika fuskantar Baitul Mukaddas. Kur'ani da ya ke maida martani yana fadin cewa, alkibla ba ta nufin cewa Ubangiji yana da muhalli ko wani wuri balle mu rika yin jayayya ko a gabas ya ke ko kuma a yamma. Gabas da yamma da dukkanin jihohi da dukkanin duniya mallakinsa ne. Babu wani wuri wanda ya ke da wata martaba tashi ta kashin kanshi, yana samun matsayi ne daga umarnin ubangiji da tsarkinsa da kuma martabarsa. Muhimmin al'amari shi ne mika kai ga umarninsa da fuskantar duk inda ya bada umarni, ka'aba ce ko kuma Baitul mukaddas. Wadanda su ke kan mikakken tafarki na shiriyar Allah, su ke mika kai ga umarninsa, suna yin aiki da duk umarnin da ya bayar ba tare da sun nemi jin dalili ba, ba wai sai abinda ya dace da son zuciyarsu ba, ya zama suna nemin dalili acikin abinda ya sabwa wannan. Yanzu kuma za su yi dubi akan darussan da su ke cikin wadannan ayoyin. 1-Ubangiji, ubangiji ne na dukkanin halittu. Ba mallakin wani addini ne guda daya ba, babu wani mutum ko wata kungiya wacce ta ke da matsayi na musamman a wurinsa. Aikin da mutane za su ne ya ke kusanta su da shi ko ya nisanta su. 2-Gurbata hakikanin addini ko kuma abubuwan da su ka faru na tarihi, zalunci ne ga al'adu da kuma zuriya mai zuwa ta bl'adama, shi ne kuma abinda kur'ani ya ke dauka a matsayin zalunci mafi girma. 3-Mu zama masu yin tunani akan ayyukan da mu ke yi, ba mu zama masu yin alfahari da ayyukan magabatanmu ba ya zamana muna bugun kirji da shi. Babu wani sakamako na ayyukan kwaransu da zai iso gare mu, kuma munanan ayyukansu ba za su zama ukuba akanmu ba. 4-Alkibla tana nufin nahiyar da Ubangiji ya bada umarni mu dube ta, ba ya nufin cewa anan ne Ubangiji ya ke. Saboda haka babu wani banbanci a kan cewa muna kallon Baitul mukaddas ne ko kuma muna kallon ka'aba, domin kuwa umarnin Allah ne ba nufinmu ba ne. Akarshen wannan shirin muna rokon Allah ya ba mu dacewar fahimtar koyarwar kur'ani, ya kuma kiyaye mu daga bin son zuciya kowane iri ne.

Sai kuma wani shirin na gaba.

Suratul Bakara; Aya Ta 143-147 (Kashi Na 42)

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa cikin wani sabon shirin Hannunka Mai Sanda da ke mana dubi da kuma sharhi cikin wasu ayoyi na Alkur’ani mai girma. A yau za mu yi dubi ne cikin aya ta 143 zuwa ta 147 na cikin Suratul Bakaran. Don haka sai a biyo mu sannu a hankali.


Bari mu saurari abin da aya ta 143 take fadi kana daga baya kuma mu yi sharhi kanta:

وَكَذَلِكَ جَعَلْنَاكُمْ أُمَّةً وَسَطاً لِّتَكُونُواْ شُهَدَاء عَلَى النَّاسِ وَيَكُونَ الرَّسُولُ عَلَيْكُمْ شَهِيداً وَمَا جَعَلْنَا الْقِبْلَةَ الَّتِي كُنتَ عَلَيْهَا إِلاَّ لِنَعْلَمَ مَن يَتَّبِعُ الرَّسُولَ مِمَّن يَنقَلِبُ عَلَى عَقِبَيْهِ وَإِن كَانَتْ لَكَبِيرَةً إِلاَّ عَلَى الَّذِينَ هَدَى اللّهُ وَمَا كَانَ اللّهُ لِيُضِيعَ إِيمَانَكُمْ إِنَّ اللّهَ بِالنَّاسِ لَرَؤُوفٌ رَّحِيمٌ

“Kuma kamar wancan, Muka sanya ku al’umma matsakaiciya domin ku kasance masu biyar da shaida a kan mutane. Kuma Manzo ya kasance mai shaida a kanku. Kuma ba mu sanya alkibla wadda ka kasance a kanta ba, face domin Mu san wanda yake biyar Manzo daga wanda yake juyawa a kan duga-dugansa. Kuma lalle ne, ta kasance, hakika, mai girma, sai a kan wadanda Allah Ya shiryar. Kuma ba ya yiyuwa ga Allah Ya tozartar da imaninku. Lalle ne, Allah, ga mutane, hakika, Mai tausayi ne, Mai jin kai.

A cikin shirin da ya gabata mun yi bayani ne dangane abubuwan da Bani Isra’ila suke fakewa da shi dangane da batun sauya alkibla – inda mu ka zo wajen da Allah Madaukakin Sarki ya ke mayar musu da martani inda ya ke ce musu gabashi da yammaci mallaka ce ta Ubangiji sannan kuma shiriya ta hakika tana ga mutanen da suka riki madaidaicin tafarki na Ubangiji ne. Bai kamata mu yi zaton cewa Allah Madaukakin Sarki yana ga gabas ko kuma yamma ne kawai ba don haka wannan wajen ne kawai za mu kalla. Wannan ayar ta bayyana al’ummar musulmi a matsayin al’umma matsakaiciya wacce ta yi nesa da duk wani irin wuce gona da iri ko kuma gazawa, wacce kuma a dukkanin fagage na rayuwa – shin a fage ne na abin duniya ko kuma na lahira, ko kuma fage na akida ko kuma fagen tattalin arziki – ba ta kasance mai fita daga kan iyakan daidaito da tsaka-tsaki ba, sannan kuma ta kasance abar koyi ga dukkanin bil’adama.

A fili yake cewa ba wai dukkanin al’ummar musulmi ne suka kasance haka ba, da dama daga cikinsu cikin tunani da kuma aiki sun kasance masu fuskantar matsalar wuce gona da iri ko kuma nuna gazawa. A saboda haka to mai wannan ayar take nuni?

Abin da take nufi shi ne cewa Musulunci dai yana kiran musulmi ne zuwa ga daidaito da kuma tsaka-tsaki, sannan kuma mutanen da suka yi aiki da dukkanin wannan koyarwa ta Musulunci ba wai wani bangare nasa ba ne za su isa ga matsayin da Allah Madaukakin Sarki zai sanya su a matsayin hujjarsa a kan mutane.

Kamar yadda Ahlulbaitin Manzon Allah (s.a.w.a) wadanda su ne masu aiki da wadannan koyarwa na Ubangiji na farko sannan kuma alamar wannan al’umma ta musulmi da aka yi magana, suna fadin cewa: mu din nan mu ne wannan matsakaiciyar al’umma wacce Allah Madaukakin Sarki ya sanya mu a matsayin hujjarsa a kan al’umma.

Haka nan kuma wannan ayar ta yi ishara da wannan batu mai muhimmanci na cewa umurnin sauya alkibla tamkar sauaran umurni na Ubangiji wata jarrabawa ce ta Ubangiji wacce ta ke bambance sahun masu mika wuya ga Allah da na masu taurin kai. Saboda kuwa amincewa da wannan umurni a wajen mutanen da ba su sami shiriya ta musamman ta Ubangiji ba lamari ne mai wahalar gaske don haka ne suke ta magana da neman dalili da hanyoyin da za su guje mata.

Yanzu kuma bari mu saurari aya ta 144 ta cikin Suratul Bakara inda Allah Madaukakin Sarki yake cewa:

قَدْ نَرَى تَقَلُّبَ وَجْهِكَ فِي السَّمَاء فَلَنُوَلِّيَنَّكَ قِبْلَةً تَرْضَاهَا فَوَلِّ وَجْهَكَ شَطْرَ الْمَسْجِدِ الْحَرَامِ وَحَيْثُ مَا كُنتُمْ فَوَلُّواْ وُجُوِهَكُمْ شَطْرَهُ وَإِنَّ الَّذِينَ أُوْتُواْ الْكِتَابَ لَيَعْلَمُونَ أَنَّهُ الْحَقُّ مِن رَّبِّهِمْ وَمَا اللّهُ بِغَافِلٍ عَمَّا يَعْمَلُونَ

“Lalle ne, Muna ganin jujjuyawar fuskarka a cikin sama. To, lalle ne, Mu juyar da kai ga alkibla wadda kake yarda da ita. Sai ka juyar da fuskarka wajen Masallaci Tsararre, kuma inda duk kuka kasance, to, ku juyar da fuskokinku jiharsa. Kuma lalle ne wadanda aka bai wa Littafi, hakika, su, suna sanin lalle ne, shi ne gaskiya daga Ubangijinka. Kuma Allah bai zama Mai gafala ba daga abin da suke aikatawa”.

A ci gaba da magana kan isgilin da yahudawa suke yi wa musulmi na cewa su din nan ba su da wata takamammiyar alkibla ta su ta kansu, Manzon Allah (s.a.w.a) ya kasance yana jiran umurni ne daga wajen Allah Madaukakin Sarki na ya sauya alkiblar, inda a tsakanin sallar azahar aka saukar da wannan wahayin wa Manzon Allah (s.a.w.a), inda nan take Manzon Allah (s.a.w.a) ya juya daga Baitul Mukaddas zuwa ga Makka sannan kuma musulmin da suke binsa salla ma a lokacin su ma suka juya zuwa ga Ka’aba. Abin ban mamakin shi ne cewa a cikin saukakkun littafan da suka gabata ya zo cewa daya daga cikin alamun annabin Musulunci shi ne cewa shi din nan zai yi salla yana mai kallon alkibla guda biyu. A saboda haka wannan ayar tana jan kunnen ma’abota littafi ne cewa ku din nan da kuka san da wannan umurnin sannan kuma hakan gaskiya ce, don me ya sa kuke nuna rashin amincewarku?

Yanzu kuma bari mu saurari aya ta 145 ta cikin Suratul Bakaran wacce take cewa:

وَلَئِنْ أَتَيْتَ الَّذِينَ أُوْتُواْ الْكِتَابَ بِكُلِّ آيَةٍ مَّا تَبِعُواْ قِبْلَتَكَ وَمَا أَنتَ بِتَابِعٍ قِبْلَتَهُمْ وَمَا بَعْضُهُم بِتَابِعٍ قِبْلَةَ بَعْضٍ وَلَئِنِ اتَّبَعْتَ أَهْوَاءهُم مِّن بَعْدِ مَا جَاءكَ مِنَ الْعِلْمِ إِنَّكَ إِذَاً لَّمِنَ الظَّالِمِينَ

“Kuma hakika, idan ka je wa wadanda aka bai wa Littafi da dukan aya, ba za su bi Alkiblarka ba, kuma kai ba ka zama mai bin Alkiblarsu ba, kuma sashensu ba mai bin Alkiblar sashe ba ne. Kuma hakika, idan ka bi son zuciyoyinsu daga bayan abin da ya zo maka daga ilimi, lalle ne kai, sa’an nan, hakika, azzalumi kake”.

Wannan ayar tana kwantar wa Manzon Allah (s.a.w.a) da zuciya ne tana gaya masa cewa idan har Ahlulkitabi (ma’abota littafi) suka ki amincewa da alkiblarka kada ka damu da kuma yin fushi don kuwa irin taurin kansu ba zai bar su, su karbi abin da ya ke shi ne gaskiya ba, a saboda haka duk wani dalilin da ka gabatar musu, ba za su taba amincewa da shi ba. to amma rashin amincewar su bai kamata ya zamanto abin da zai sanya ka yin sako-sako da wannan alkibla taka ba, face dai da dukkan karfinka ka sanar da cewa mu dai ba za mu mika wuya ga irin wadannan maganganu na ku da kuma sauya matsayar mu ba. A wajen Musulunci doka daidai take a kan kowa, a saboda haka Allah Madaukakin Sarki yake jan kunnen Manzonsa cewa idan har kai ma saboda ka janyo hankalinsu ka yi watsi da wannan alkibla taka, to lalle ka yi gagarumin zalunci ga al’ummar ka.

To yanzu kuma bari mu saurari aya ta 146 da 147 na cikin wannan sura ta Bakara:

الَّذِينَ آتَيْنَاهُمُ الْكِتَابَ يَعْرِفُونَهُ كَمَا يَعْرِفُونَ أَبْنَاءهُمْ وَإِنَّ فَرِيقاً مِّنْهُمْ لَيَكْتُمُونَ الْحَقَّ وَهُمْ يَعْلَمُونَ{146} الْحَقُّ مِن رَّبِّكَ فَلاَ تَكُونَنَّ مِنَ الْمُمْتَرِينَ{147}

“Wadanda Muka ba su Littafi, suna saninsa kamar yadda suke sanin diyansu. Kuma lalle ne wani bangare daga gare su, hakika, suna boye gaskiya alhali kuwa su, suna sane. Gaskiya daga Ubangijinka take, saboda haka: lalle kada ka kasance daga masu shakka”.

A cikin Attaura da Linjila an yi bayanin alamu da siffofin Manzon Allah (s.a.w.a), a saboda haka Ma’abota littafi sun san Manzon Allah (s.a.w.a) to amma taurin kan su ne ya sanya wasu daga cikin su boye wannan gaskiya ga sauran mutane. ko da ya ke wasu daga cikin Ma’abota littafin daga lokacinda suka ga wadannan siffofi na Annabi sun yi imani da shi don kuwa irin wadannan siffofi na jiki da ruhi da Manzon Allah (s.a.w.a) yake da su an yi bayaninsu a cikin Littafinsu, sannan kuma sun san su kamar yadda Alkur’ani ya fadi cewa sun san su kamar yadda suka san ‘ya’yansu.

Aya ta karshe ta cikin wannan shirin ta yi ishara da wannan batu mai muhimmanci na cewa abin da Allah ya saukar shi ne kawai gaskiya, sannan kuma bai kamata abin da mutane suka rika ko da kuwa suna da yawa bai kamata ya zamanto abin da zai kawar da mutum daga gaskiyar wahayin Ubangiji ba.

Yanzu bari mu yi dubi cikin darussan da suke cikin wadannan ayoyi:

1- Alkibla alama ce ta ‘yanci daga dukkanin wata koyarwa da abubuwan da aka tilasta wa muslunci da kuma mika wuya ga dukkanin koyarwa da umurni na Ubangiji. 2- Musulunci addini ne na daidaito da kuma tsaka-tsaki, haka nan kuma idan har musulmi suka riki madaidaicin tafarkin Ubangiji, za su iya zama abin koyi ga sauran al’ummomi sannan kuma hujja a gare su. 3- Taurin kai da tsaurin ra’ayi lamari ne da ke hana duk wani nau'i na tunani da amfani da hankali da ganin gaskiya. A saboda haka ne suke fada da addini da irin wannan yanayi na girman kai. 4- Idan har aka rasa ruhin neman gaskiya a tattare da mutum, to ilimi shi kadai din sa bai wadatar ba, don kuwa son zuciyar mutum a wasu lokuta ya kan rufe ilimi da kuma gurbata shi.

Daga karshe muna rokon Allah Madaukakin Sarki da ya sanya mu cikin masu yarda da umurninsa da kuma aiki da shi.

Sai a shiri na gaba za mu dora daga inda muka tsaya. Wassalamu alaikum wa rahamatullah wa barakatuhu.

Suratul Bakara; Aya Ta 148-152 (Kashi Na 43)

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa cikin wani sabon shirin Hannunka Mai Sanda da ke mana dubi da kuma sharhi cikin wasu ayoyi na Alkur’ani mai girma. Da fatan za ku kasance tare da mu tun daga farkon shirin har zuwa karshensa.


A yau za mu fara shirin na mu da aya ta 148 na cikin Suratul Bakara, don haka sai ku saurari abin da ayar take fadi:

وَلِكُلٍّ وِجْهَةٌ هُوَ مُوَلِّيهَا فَاسْتَبِقُواْ الْخَيْرَاتِ أَيْنَ مَا تَكُونُواْ يَأْتِ بِكُمُ اللّهُ جَمِيعاً إِنَّ اللّهَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ

“Kuma kowane bangare yana da alkibla wadda yake shi mai fuskantar ta ne. Sai ku yi tsere zuwa ga ayyukan alheri, inda kuka kasance duka, Allah zai zo da ku gaba daya. Lalle ne Allah, a kan kome, Mai ikon yi ne”.

Kamar yadda muka bayyana a shirye-shiryen da suka gabata cewa bangaren da alkibla take ba shi ne yake da muhimmanci ba don kuwa a tsawon tarihi addinai daban-daban sun kasance masu alkibloli daban-daban ne, abin da ya ke da muhimmanci shi ne mika wuya ga umurnin Ubangiji. A saboda haka bai kamata a damu kai da lamarin da ba shi daga cikin tushe da kuma asasi na addini ba. mizani a wajen Allah Madaukakin Sarki shi ne aiki na gari wanda shi ne ya zama wajibi mutum ya ba shi muhimmanci da kuma damuwa da shi sannan kuma maimako surutu da maganganu kamata ya yi mutum ya fada fagen aiki. Abin da Alkur’ani mai girma ya ke fadi da kuma kiran mu zuwa gare shi duk wani abin da zai zamanto alheri da kuma taimako ga al’umma, a bangare guda kuma ya zamana an sanya koyarwar Ubangiji a matsayin mizanin auna wannan aiki da kuma ya zamanto don Allah a ke yi da kuma tunanin ranar lahira don kuwa lada ta hakika ta Ubangiji a can za a same ta.

Yanzu kuma bari mu saurari aya ta 149 da 150 na cikin wannan sura ta Bakara da suke cewa:

وَمِنْ حَيْثُ خَرَجْتَ فَوَلِّ وَجْهَكَ شَطْرَ الْمَسْجِدِ الْحَرَامِ وَإِنَّهُ لَلْحَقُّ مِن رَّبِّكَ وَمَا اللّهُ بِغَافِلٍ عَمَّا تَعْمَلُونَ{149} وَمِنْ حَيْثُ خَرَجْتَ فَوَلِّ وَجْهَكَ شَطْرَ الْمَسْجِدِ الْحَرَامِ وَحَيْثُ مَا كُنتُمْ فَوَلُّواْ وُجُوهَكُمْ شَطْرَهُ لِئَلاَّ يَكُونَ لِلنَّاسِ عَلَيْكُمْ حُجَّةٌ إِلاَّ الَّذِينَ ظَلَمُواْ مِنْهُمْ فَلاَ تَخْشَوْهُمْ وَاخْشَوْنِي وَلأُتِمَّ نِعْمَتِي عَلَيْكُمْ وَلَعَلَّكُمْ تَهْتَدُونَ

“Kuma daga inda ka fita, to, sai ka juyar da fuskarka a wajen Masallaci Tsararre, kuma lalle, tabbas, shi ne gaskiya daga Ubangijinka. Kuma Allah bai zama Mai gafala ba daga abin da kuke aikatawa. Kuma daga inda ka fita, to, ka juyar da fuskarka a wajen Masallaci Tsararre, kuma inda kuke duka, to, ku juyar da fuskokinku a wajensa, domin kada wata hujja ta kasance ga mutane a kanku, face wadanda suka yi zalunci daga gare su. Saboda haka kada ku ji tsoronsu, kuma ku ji tsoronNa, kuma domin In cika ni’imata a kanku, kuma tsammaninku za ku shiryu”.

Abu na biyu shi ne cewa Ma’abota littafi sun karanta a cikin littafansu cewa Manzon Allah (s.a.w.a) zai yi salla ta hanyar fuskantar alkibloli guda biyu. To idan har hakan ba ta faru ba ne za su iya cewa ai hakan ba ta tabbata ba ga annabi (s.a.w.a.) don haka ba shi da wadannan siffofi da aka fadi cikin saukakkun littafa. Na uku shi ne cewa ayoyin da suka gabata suna magana ne kan salla a lokacin da mutum ya ke gida sannan wannan ayar kuma tana magana dangane da salla a lokacin da ake tafiya wanda wajibi ne a yi ta alhali ana kallon Masjid al-Haram (Ka’aba). Ala kulli hal ‘yancin da al’ummar musulmi suke da shi daya ne daga cikin manyan ni’imomin Ubangiji wanda wajibi ne a kiyaye su.

To yanzu kuma bari mu saurari aya ta 151 na Suratul Bakaran da take cewa:

كَمَا أَرْسَلْنَا فِيكُمْ رَسُولاً مِّنكُمْ يَتْلُو عَلَيْكُمْ آيَاتِنَا وَيُزَكِّيكُمْ وَيُعَلِّمُكُمُ الْكِتَابَ وَالْحِكْمَةَ وَيُعَلِّمُكُم مَّا لَمْ تَكُونُواْ تَعْلَمُونَ

“Kamar yadda Muka aika Manzo a cikinku, daga gare ku, yana karanta ayoyinMu a gare ku kuma yana tsarkake ku, kuma yana sanar da ku Littafi da hikima, kuma yana sanar da ku abin da ba ku kasance kuna sani ba”.

A cikin ayar da ta gabata, Allah Madaukakin Sarki ya bayyana cewar daya daga cikin dalilan sauya alkibla shi ne cika ni’imarsa a kan musulmi da kuma shiryar da su. Ita kuwa wannan ayar tana cewa ne akwai wata ni’imar kuma mai girma ga mutane wanda mafi muhimmancinsu shi ne samuwar Annabi (s.a.w.a.), manzon da ya kasance mai koyar da mutane da sanar da su dokoki da hukumce-hukumcen Ubangiji haka nan kuma a matsayin wani mai tarbiyya wanda ya ke ba da dukkanin lokaci da tunaninsa wajen kyautata rayuwarsu da kuma shiryar da su. Haka nan kuma karanta Alkur’ani yana share fagen tsarkake ruhi da zuciyar mutum sannan kuma koyon hukumce-hukumce da ingantattun hikimomi su ne mafi muhimmancin ayyukan annabawan Allah wajen shiryar da bil’adama. Sai dai kuma yana da kyau a san cewa annabawan Allah ba wai kawai shugabanni ne na kyawawan halaye da kyautata akidar mutane kawai ba ne, face dai a bangaren tunani da karfafa ilimi da masaniyar mutane ma dai suna nan. Haka nan kuma sun kasance kwadaitar da yaduwar ilimi wanda ya ke karkashin inuwar imani da Allah ba wai a nesance shi ko kuma a tsaya kyam wajen tinkararsa ba.

Yanzu kuma bari mu saurari aya ta 152 na Suratul Bakaran:

فَاذْكُرُونِي أَذْكُرْكُمْ وَاشْكُرُواْ لِي وَلاَ تَكْفُرُونِ

“Saboda haka ku tuna Ni, in tuna ku, kuma ku yi godiya gare Ni, kuma kada ku butulce Mini”.

To da ya ke Allah Madaukakin Sarki ya ba mu wannan gagarumar ni’ima, to hankali dai yana hukumta cewa wajibi ne mu girmama wanda ya ba mu wannan ni’ima sannan kuma mu dauka cewa dukkanin abin da muke da shi daga wajensa ne sannan kuma mu yi amfani da wannan ni’imar a wajen da yake so da kuma yarda da shi. idan har mutum ya mance da Allah, to kuwa ya mance da dukkanin ababe masu kyau, to a dabi’ance dai Allah Madaukakin Sarki zai mance da shi.

Abin nufin da tuna Allah, ba shi ne kawai ambatonsa a baki ba ne face dai ambato da kuma tuna shi na hakika. A matsayin misali a duk lokacin da mutum ya ke son aikata wani sabon Allah, to amma saboda tuna Allah sai ya yi watsi da wannan zunubin. Kamar yadda ma’anar godiyar Allah ba ita ce godiya ta fatar baki kawai ba ne, face dai godiya ta hakika ita ce mutum ya yi aiki da duk wata ni’ima da ya samu daga wajen Ubangiji a bisa tafarkin abin da Ubangiji din ya ke so da kuma kauna.

To yanzu kuma bari mu yi dubi cikin darussan da suke cikin wadannan ayoyi:

1- Maimakon mu damu da gabatar da wasu abubuwa ‘yan kanana wadanda aka gabatar da su a cikin addinai wanda yin hakan ba shi da wata fa’ida, kamata ya yi mu ba da himma wajen yada ababe masu amfani da kuma kyawawan halaye, sannan kuma mu zamanto mun gabaci sauran mutane a wannan fagen. 2- Wajibi ne musulmi su nesanci duk wani aiki da zai ba wa makiya wata dama ta fakewa da shi, sannan kuma kada su bari makiya su sami wata hujja a kansu. 3- Sauya alkibla ta zamanto abin da zai tabbatar da hadin kai tsakanin musulmi sannan kuma wata alama ce ta ‘yancin da suke da shi a gaban ‘yan mulkin mallaka da sauransu. 4- Annabawa malamai da masu tarbiyya ne ga mutane wadanda suke koyar da su da kuma tsarkake su.

Daga karshe dai muna rokon Allah Madaukakin Sarki da ya arzurta mu da karfin fahimta da kuma girmama ni’imomin da ya yi mana da kuma shiryar da mu da ya yi.

Kuma da hakan ne muka kawo karshen shirin na mu na yau, sai kuma a shiri na gaba inda za mu sake kasance tare da ku. Kafin nan na ke cewa ku zama lafiya. Wassalamu alaikum wa rahamatullah wa barakatuhu.

Suratul Bakara; Aya Ta 153-157 (Kashi Na 44)

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa cikin wani sabon shirin Hannunka Mai Sanda da ke mana dubi da kuma sharhi cikin wasu ayoyi na Alkur’ani mai girma. A yau ma ga mu da wani sabon shirin na Hannunka Mai Sanda sai ku biyo mu don jin abin da muke dauke da shi.


A yau za mu fara shirin na mu ne da aya ta 153 ta cikin Suratul Bakara. Sai ku saurari ayar:

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُواْ اسْتَعِينُواْ بِالصَّبْرِ وَالصَّلاَةِ إِنَّ اللّهَ مَعَ الصَّابِرِينَ

“Ya ku wadanda suka yi imani! Ku nemi taimako da hakuri game da salla. Lalle ne, Allah na tare da masu hakuri”.

Dan'adam dai a tsawon rayuwarsa ya kan fuskanci matsaloli da wahalhalu da dama ta yadda matukar dai ba shi da karfin da ake bukata wajen fada da wadannan matsaloli, to kuwa hakan ya kan tilasta masa yarda da ya sha kashi. To amma su muminai kan su kan dogara ne da wadansu abubuwa guda biyu wajen fada da wannan bala'in. Na farko shi ne hakuri da tsayin daka, na biyu kuma shi ne yin salla da neman kusaci da Ubangijin Madaukakin Sarki yana mai dogaro da irin karfi maras iyaka na Ubangiji da kuma dan karfin da ya ke da shi. To shi ma Allah Madaukakin Sarki ya yi alkawarin taimakawa masu salla da suke da hakuri sannan kuma zai kasance tare da su a kowane irin yanayi, wannan taimako da kasantuwa tare da su da Ubangiji zai yi shi ne mafi girma da karfin garkuwa ta fada da wadannan matsaloli da wahalhalu da ake fuskanta.

Yanzu kuma bari mu saurari sura ta 154 ta cikin Suratul Bakaran:

وَلاَ تَقُولُواْ لِمَنْ يُقْتَلُ فِي سَبيلِ اللّهِ أَمْوَاتٌ بَلْ أَحْيَاء وَلَكِن لاَّ تَشْعُرُونَ

"Kada ku ce ga wadanda ake kashewa a cikin hanyar Allah: Matattu ne, a'a, rayayyu ne, kuma amma ba ku sansancewa".

A cikin wannan aya wacce ta kasance kafin wannan wacce take magana kan hakuri da tsayin daka, ita kuwa wannan ayar tana magana ne kan batun jihadi da kuma shahada a tafarkin Allah wanda yake tattare da matsaloli daban-daban na dukiya da rai wanda kuma ya ke bukatar tsayin daka da sadaukarwa.

Wasu daga cikin mutane jahilai ko kuma wadanda suke da wata manufa, ba wai kawai ba sa fita yaki da shiga fagen gwagwarmaya ba ne, face dai ma suna ta kokarin kashe gwuiwan muminai ne da bayyana musu cewa lalle babu wani sakamakon da za su samu a wannan yaki da suke yi. A zahiri suna nuna tausayawarsu ne ga wadannan mutane da suke yaki a tafarkin Allah suna cewa lalle abin tausayi ne a ce mutum ya je ya sadaukar da ransa a banza haka kawai. Wadannan mutane kuwa suna magana ne da mutanen da aka kashe a yakin Badar sannan kuma suka yi shahada, don haka sai aka saukar da wannan aya inda ta hane su daga wannan mummunan aiki, saboda kuwa shahidan da suka yi shahadan dai rayayyu ne suna nan suna wata irin rayuwa wacce mu din nan ba za mu iya fahimtarta ba.

Yanzu kuma bari mu saurari aya ta 155 ta cikin wannan sura ta Bakara:

وَلَنَبْلُوَنَّكُمْ بِشَيْءٍ مِّنَ الْخَوفْ وَالْجُوعِ وَنَقْصٍ مِّنَ الأَمَوَالِ وَالأنفُسِ وَالثَّمَرَاتِ وَبَشِّرِ الصَّابِرِينَ

"Kuma lalle ne, Muna jarrabar ku da wani abu daga tsoro da yunwa da nakasa daga dukiya da rayuka da 'ya'yan itace. Kuma ka yi bishara ga masu hakuri".

Jarrabawa daya ne daga cikin sunnoni na Ubangiji da yake jarraba dukkanin bayinsa da ita, to sai dai kuma irin wannan jarrabawar ba ta zamanto guda ba ga dukkanin bil'adama, face dai kowa da irin yadda tasa take kasancewa gwargwadon irin karfi da damar da yake da ita ne ake masa irin wannan jarrabawar. Wasu daga cikin mutanen akan jarrabe su ne da matsala ta dukiya da kudi don a ga yadda za su yi, wasu kuwa ta hanyar rai ne a fagen yaki ake jarraba su don ganin irin shirin da suke da shi.

Ko da yake yana da kyau a fahimci cewa Allah Madaukakin Sarki yana jarraba bayinsa ne ba wai don ya fahimce su ba, a'a, saboda shi dai ya ma fi mu sanin kanmu, face dai don mu san kanmu da kanmu da kuma fahimtar irin shiri da kwarewar da muke da ita da kuma share fagen samun lada ta Ubangiji ko kuma azabarsa (Allah ya kiyaye), saboda kuma a mafi yawan lokuta a lokacin da matsaloli suka bayyana mana ne ruhin mu ya ke dada samun karfi da kuma zama cikin shiri.

Yanzu kuma bari mu saurari aya ta 156 ta cikin Suratul Bakara:

الَّذِينَ إِذَا أَصَابَتْهُم مُّصِيبَةٌ قَالُواْ إِنَّا لِلّهِ وَإِنَّـا إِلَيْهِ رَاجِعونَ

"Wadanda suke idan wata masifa ta same su, sai su ce: Lalle ne mu ga Allah muke, kuma lalle ne mu, zuwa gare Shi, masu komawa ne".

A cikin gaban wannan aya da ta gabata wacce take bishara ga masu hakuri, wannan ayar kuma ta yi bayanin su wane ne masu hakurin inda take cewa: Mai hakuri na hakika shi ne wanda a lokacin da ya fuskanci wata matsala maiamikon yanke kauna da fata sai ma hakan ta kara masa kyakkyawan fata da Allah Madaukakin Sarki.

Mutumin da ya ke ganin mafari da kuma karshensa duk suna hannun Allah Madaukakin Sarki ne, shi din ma Ubangijin da ya ke gudanar da lamurran mutane bisa asasi na rahama da hikima, to a wajen sa dukkanin komai na hannunSa ne, ba ya ganin duniya a bakin komai yana jin cewa duniya lalle ba wajen dawwama b ace, sannan kuma ba waje ne na hutu da sharholiya ba ballanta mutum ya sake jiki da mike kafafu. A'a, duniya waje ne na jarrabawa da kuma fuskantar matsaloli, don haka sai ya dauke ta a matsayin hanya ta yunkuri da kokari.

To sai dai mutane sun kasu kashi daban-daban wajen fuskantar matsaloli da musibu da suke kunno kai. Akwai wata jama'a mai karancin hakuri wacce babu abin da ta sa a gaba in banda kuka da nuna damuwa. Sai kuma wata jama'ar wacce ta ke yin hakurin a duk lokacin da wata musiba ta same ta, wacce maimakon ta dinga fadin wasu maganganu na kafirci, sai ta koma ga Allah da neman mafaka a wajensa. Akwai wata jama'ar kuma wacce baya ga hakurin, har ila yau kuma ta kasance mai godiya, don kuwa hakan lamari ne da ke kara karfafa mata ruhinta.

Yanzu kuma bari mu saurari aya ta 157 ta Suratul Bakaran:

أُولَـئِكَ عَلَيْهِمْ صَلَوَاتٌ مِّن رَّبِّهِمْ وَرَحْمَةٌ وَأُولَـئِكَ هُمُ الْمُهْتَدُونَ

"Wadannan akwai albarku a kansu daga Ubangijinsu da wata rahama. Kuma wadannan su ne shiryayyu".

Wannan ayar ta bayyana lada mai g irma da masu hakuri za su samu ne da cewa ita ce saukar musu da albarkoki da nitsuwa da sallama ta Ubangiji, wanda hakan lamari ne da zai kiyaye su daga dukkanini kaucewa hanya, sannan kuma su sami shiriya ta hakika.

Na'am duk kuwa da cewa dukkanin halittar Ubangiji tana shiga cikin tausayi da rahamarSa, to amma wannan salama da rahama ta musamman tana sauka ne a kan masu hakuri wadanda kuma ko shakka babu za su sami shiriya ta Ubangiji.

To yanzu kuma bari mu rufe shirin na mu da darussan da muka koya daga wadannan ayoyi:

1- Salla dai ba wani nauyi ba ne face dai wata hanya ce ta samun hakuri a gaban musibun da za su kunno kai wa mutum, a saboda haka ne a lokacin da Allah yake magana kan hakuri ya kirayi mutane wajen riko da salla wacce wata hanya ce ta hada dan'adam da karfi mara iyaka na Ubangiji. 2- Duk da cewa dukkanin mutane bayan mutuwa suna da wata rayuwa ta barzahu wanda alal hakika wata rayuwa ce ta ruhi, to amma su shahidai suna da wata rayuwa ce ta musamman wacce ta bambanta da ta sauran mutane. 3- A yayin jarrabawa ta Ubangiji, to masu hakuri ne kawai za su yi nasara, sauran mutane kuma ba su da wata hanya ta tsira. 4- Tushen hakuri shi ne imani da Allah da ranar tashin alkiyama, wadanda suke saukaka wa mutum jurewa matsalolin da yake fuskanta. 5- Hakuri da tsayin daka lamurra ne da suke samar wa mutum da sa'ada a wannan duniya, sannan kuma ga lada mai yawa a lahira.

Daga karshe dai muna rokon Allah Madaukakin Sarki da ya sanya mu cikin masu hakuri na hakika wadanda za su sami nasara a jarrabawar da aka jarraba su da ita. Sai kuma a shiri na gaba. Wassalamu alaikum wa rahamatullah wa barakatuhu.

Suratul Bakara; Aya Ta 158-162 (Kashi Na 45)

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa cikin wani sabon shirin Hannunka Mai Sanda da ke mana dubi da kuma sharhi cikin wasu ayoyi na Alkur’ani mai girma. A yau ma ga mu da wani sabon shirin na Hannunka Mai Sanda sai ku biyo mu don jin abin da muke dauke da shi.


A yau za mu fara shirin na mu ne da aya ta 158 ta cikin Suratul Bakara. Sai ku saurari ayar:

إِنَّ الصَّفَا وَالْمَرْوَةَ مِن شَعَآئِرِ اللّهِ فَمَنْ حَجَّ الْبَيْتَ أَوِ اعْتَمَرَ فَلاَ جُنَاحَ عَلَيْهِ أَن يَطَّوَّفَ بِهِمَا وَمَن تَطَوَّعَ خَيْراً فَإِنَّ اللّهَ شَاكِرٌ عَلِيم

"Lalle ne Safa da Marwa suna daga wuraren ibadar Allah, to, wanda ya yi hajin Daki ko kuwa ya yi Umra, to, babu laifi a kansa ga ya yi dawafi gare su, su biyu. Kuma wanda ya kara yin wani aikin alheri, to, lalle ne Allah Mai godiya ne, Masani".

Wannan ayar tana magana ne dangane da wani bangare na aikin hajji. Aikin hajji dai wanda ya samo asali daga lokacin annabi Ibrahim (a.s), duk kuwa da cewa tsawon zamani din an samu wasu daga cikin jahilan mutane da kuma masu bautar gumaka sun shigo da wasu abubuwa marasa tushe cikinsa, to amma Musulunci dai ya sake tabbatar da shi da kuma yi masa gyara da mai she shi yadda yake.

Sa'ayi wato sassarfa tsakanin duwatsun Safa da Marwa da suke kusa da Masjid al-Haram yana daga cikin abubuwan da ake gudanarwa a yayin aikin hajjin. A wancan zamanin dai masu bautan gumaka sun sanya wasu gumakansu a saman wadannan duwatsun, ta yadda a lokacin da suke yin sa'ayin suka kewaya wadannan gumakan a matsayin dawafi. To a lokacin da musulmi suka zo da nufin yin aikin hajji, sakamakon sanya wadannan gumaka da mushirikan suka yi sai ya zamanto musulmi suna jin kyamar yin sa'ayi a wannan wajen, suna masu zaton cewa bai kamata su yi sa'ayi a wannan wajen ba saboda wannan batu na sanya gumaka a saman wajen. To amma sai Allah Madaukakin Sarki ya saukar da wannan ayar yana tunatar da su cewa wadannan duwatsu guda biyu wasu alamomi ne na karfin Ubangiji sannan kuma suna tunatarwa ne dangane da wannan ya samar da aikin hajji wato annabi Ibrahim (a.s). Don haka ko da wasu mutane jahilai sun gurbata wajen da abubuwa na shirka, to bai kamata ku din nan musulmi ku sake wannan gagarumin aiki ba, face dai ku kawo karshen wannan bata ta hanyar kasantuwarku a wajen.

A lokacin da annabi Ibrahim, tare da mai dakinsa da dansa Isma'il, ya zo garin Makka don sauke wani nauyi na Ubangiji, ya tafi ya bar su a wannan busasshen waje a hannun Allah Madaukakin Sarki. Lokacin da yanayin rashin ruwan ya tsananta, mahaifiyar Isma'il ta fara neman mafita ta hanyar tafiya tsakanin wadannan duwatsu biyu ko za ta sami wani wajen da yake da ruwa. A irin wannan yanayi ne Allah Madaukakin Sarki ya samar da idon ruwa a inda ta bar wannan jariri, wanda ake kiransa da Zam-zam. A saboda haka ne tun daga wancan lokaci duk wani mutumin da ya tafi Makka da nufin ziyarar dakin Allah sai ya tuna da wannan yunkuri na Hajara mahaifiyar annabi Isma'il na tafiya tsakanin wadannan duwatsu guda biyu don girmama irin sadaukarwar da wannan baiwar Allah da mijinta da danta suka yi. Gudanar da wannan aikin, wata alama ce ta nuna godiyar Ubangiji ga wannan kokari da ke cike da tsarkin zuciya wanda wadannan bayin Allah suka yi da kuma tunatar da mu cewa bai kamata mu yi kasa a gwuiwa wajen aikata komai kashin aiki na kwarai da kuma bin umurnin Ubangiji ba don kuwa Allah Madaukakin Sarki yana ganin dukkanin abubuwan da muka aikata komai kashinsu ne kuwa.

To yanzu kuma bari mu saurari aya ta 159 ta cikin Suratul Bakaran:

إِنَّ الَّذِينَ يَكْتُمُونَ مَا أَنزَلْنَا مِنَ الْبَيِّنَاتِ وَالْهُدَى مِن بَعْدِ مَا بَيَّنَّاهُ لِلنَّاسِ فِي الْكِتَابِ أُولَـئِكَ يَلعَنُهُمُ اللّهُ وَيَلْعَنُهُمُ اللَّاعِنُونَ

"Lalle ne wadanda suke boyewar abin da Allah Ya saukar daga hujjoji bayyananmu da shiriya, daga bayan Mun bayyana shi ga mutane, a cikin Littafi (Alkur'ani), wadannan Allah Yana la'anarsu, kuma masu la'ana ma suna la'anar su".

Wannan aya dai tana magana ne dangane da malaman yahudu da nasara wadanda suna sane da alamun bayyanar annabi (s.a.w.a) wanda aka yi bayaninsa cikin littafansu to amma sai suka kasance suna boye hakan daga mutane da hana mutane fahimtar gaskiya da kuma samun shiriya. Ko shakka babu boye gaskiya wani lamari ne abin kyama. Idan har hakan ya fito ne daga wajen wasu mutane marasa sani wato jahilai, to ukubar hakan tana da sauki idan aka kwatanta irin wadda za ta samu masu aikata hakan idan har suka kasance malamai ne. Don kuwa aikata hakan daga wajen malamai lalle mafi girman zalunci ne a kan al'umma, su kan su annabawan da kuma Allah Madaukakin Sarki. A saboda haka ne a ko da yaushe suke cikin la'ana ta Ubangiji da ta sauran bayi.

Ko da yake a cikin aya ta gaba Allah Madaukakin Sarki ya kebance wasu daga cikinsu inda ya ce:

إِلاَّ الَّذِينَ تَابُواْ وَأَصْلَحُواْ وَبَيَّنُواْ فَأُوْلَـئِكَ أَتُوبُ عَلَيْهِمْ وَأَنَا التَّوَّابُ الرَّحِيمُ

"Sai wadanda suka tuba, kuma suka gyara, kuma suka bayyana, to wadannan Ina karbar tubarsu, kuma Ni ne Mai karbar tuba, Mai jin kai".

Addinin Musulunci dai bai toshe kofa ga bayin Allah gaba daya ba, face dai yana tabbatar mana da cewa kofar rahama da jin kan Ubangiji a ko da yaushe a bude take, ta yadda hatta mutumin da ya fi sauran mutane aikata laifi da zunubi bai kamata ya yanke kauna da jin cewa shi kan tasa ta kare ba, a'a kofar tuba ta Ubangiji a bude take. Sai dai yana da kyau a san cewa ana iya shiga wannan kofa ta tuba din ne ta hanyar yin watsi da wannan mummunan aikin da kuma cike gibin da aka haifar. A matsayin misali mutumin da ya zamanto mai boye gaskiya hanyar tubarsa ita ce barin wannan mummunan aikin da kuma komawa ga bayyanar da gaskiyar da ya sani din ga mutane don kada mutane su ci gaba da zama cikin bata ba tare da sun sami wannan shiriyar ba.

To yanzu kuma bari mu saurari ayoyi na 161 zuwa 162 na cikin Suratul Bakaran:

إِنَّ الَّذِينَ كَفَرُوا وَمَاتُوا وَهُمْ كُفَّارٌ أُولَئِكَ عَلَيْهِمْ لَعْنَةُ اللّهِ وَالْمَلآئِكَةِ وَالنَّاسِ أَجْمَعِينَ{161} خَالِدِينَ فِيهَا لاَ يُخَفَّفُ عَنْهُمُ الْعَذَابُ وَلاَ هُمْ يُنظَرُونَ{162}

"Lalle ne, wadanda suka kafirta, kuma suka mutu, alhali kuwa suna kafirai, wadannan akwai, a kansu, la'anar Allah da mala'iku da mutane gaba daya. Suna dawwama a cikinta, ba a saukaka azaba daga barinsu, kuma ba su zama ana jinkirta musu ba".

A cikin ayar da ta gabaci wadannan mun ji cewa matukar dai masu boye gaskiya, suka dawo suka ci gaba da bayyana wa mutane gaskiyar, to kuwa za su sami rahamar Allah da kuma yafuwarsa. To amma wadannan ayoyi suna jan kunnen masu boye gaskiya din ne cewa matukar dai ba su yi hakan ba, wato ba su koma ga bayyanar da gaskiyar da suke boyewa din ba, to kuwa la'anar Allah da mala'ikunsa da sauran mutane za ta ci gaba da yawo a kansu.

Wani abin da ya ke da muhimmanci a fahimta a nan shi ne cewa ita dai tuba ana yinta ne a lokacin da mutum yake da sauran karfi da sannan kuma alamun ci gaba da rayuwa suka kasance tare da shi, to amma daga lokacin da alamun mutuwa suka fara bayyana wa mutum, to a irin wannan lokaci kan tuba ba ta da wata fa'aida a gare shi kamar yadda ya faru da Fir'auna a lokacin da ya yi kokarin tuba bayan da ya tabbatar cewa zai nutse cikin ruwa da kuma halaka.

A saboda haka ne daya daga cikin addu'oin annabawa da waliyan Allah ita ce cewa Allah ya sanya su su zamanto musulmi a lokacin mutuwarsu, don kuwa mutuwa cikin kafirci wata cuta ce wacce ba ta da magani baya ga haka kuma tana tare da fushin Ubangiji da kuma na bayinsa. Don haka boye gaskiya yana daga cikin manyan zunubai da mai aikata hakan, matukar dai bai tuba ba, ba zai iya tsira daga ukubar Ubangiji ba.

To yanzu kuma bari mu karkare shirin na mu da darussan da muka koya daga wadannan ayoyi:

1- Bai kamata a kaurace wa masallatai da wajajen ibadan da wadansu jahilai suka gurbata su da abubuwa na jahilici ba, face dai wajibi ne mu kasance a wajen don mu sami damar tsarkake su da kuma dawo musu da irin girma da kimar da suke da su. 2- Wajibi ne wajajen da suke bayyanar da rahama da kuma karfin kudura ta Ubangiji irin su Safa da Marwa su zamanto ababen girmamawarmu. 3- Boye gaskiya yana daga cikin zunubai masu girma da hatta lamirin mai aikata hakan yana la'antarsa baya ga la'ana ta Ubangiji da mala'iku da suka sauran mutane. 4- Allah Madaukakin Sarki, a bangare guda ya samar da hanyoyin tuba ga masu aikata zunubi, sannan kuma a bangare guda kuma ya yi alkawarin karbar tubar ta su don kuwa ya bayyana kansa a matsayin mai karbar tuba. 5- Karshen komai shi ne ya ke da muhimmanci ga mutum, wato shin mutum zai mutu a matsayin musulmi ne ko kuma kafiri (wal iyazu billahi)

Daga karshe muna rokon Allah Madaukakin Sarki da ya mu yi kyakkyawan karshe sannan ya sanya mu daga cikin wadanda za su sami rahamar da jin kansa duniya da lahira. Wassalamu alaikum wa rahamatullah wa barakatuhu.

Suratul Bakara; Aya Ta 163-166 (Kashi Na 46)

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa cikin wani sabon shirin Hannunka Mai Sanda da ke mana dubi da kuma sharhi cikin wasu ayoyi na Alkur’ani mai girma. A yau ma ga mu da wani sabon shirin na Hannunka Mai Sanda sai ku biyo mu don jin abin da muke dauke da shi.


A yau za mu fara shirin na mu ne da aya ta 163-164 ta cikin Suratul Bakara. Sai ku saurari ayar:

وَإِلَـهُكُمْ إِلَهٌ وَاحِدٌ لاَّ إِلَهَ إِلاَّ هُوَ الرَّحْمَنُ الرَّحِيمُ{163} إِنَّ فِي خَلْقِ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ وَاخْتِلاَفِ اللَّيْلِ وَالنَّهَارِ وَالْفُلْكِ الَّتِي تَجْرِي فِي الْبَحْرِ بِمَا يَنفَعُ النَّاسَ وَمَا أَنزَلَ اللّهُ مِنَ السَّمَاءِ مِن مَّاء فَأَحْيَا بِهِ الأرْضَ بَعْدَ مَوْتِهَا وَبَثَّ فِيهَا مِن كُلِّ دَآبَّةٍ وَتَصْرِيفِ الرِّيَاحِ وَالسَّحَابِ الْمُسَخِّرِ بَيْنَ السَّمَاء وَالأَرْضِ لآيَاتٍ لِّقَوْمٍ يَعْقِلُونَ

"Kuma Ubangijinku Ubangiji Guda ne. Babu wani Ubangiji face Shi, Mai rahama, Mai jin kai. Lalle ne, a cikin halittar sammai da kasa, da sabawar dare da yini, da jirage wadanda suke gudana a cikin teku (dauke) da (abin) da yake amfanin mutane da abin da Allah Ya saukar daga sama daga ruwa, sai Ya rayar da kasa da shi a bayan mutuwarta, kuma Ya watsa, a cikinta, daga dukkan dabba, kuma da juyawar iskoki da girgije horarre a tsakanin sama da kasa; hakika, akwai ayoyi ga mutane masu hankali".

Daga wannan ayar za mu iya fahimtar cewa daya daga cikin dalilai masu karfi da suke nuni da kadaitakar Ubangiji shi ne daidaiton da ake samu tsakanin abubuwa na dabi'a irin su girgije da iska da ruwan sama da kuma kasa a tsakaninsu wadanda daga suke samar da kasar da za ta iya samar da rayuwa da ci gaba da girman nau'oi daban-daban na tsirrai da halittu.

A bangare guda wannan daidaito dai lamari ne da ke nuni da kadaitaka ta Ubangijin talikai, a bangare guda kuma lamari ne da ke tabbatar da ilimi da kudurarsa maras iyaka. Wadannan ayoyi suna jaddada kadaitakar Ubangiji ne ta hanyar wasu alamu guda shida na daukaka ta Ubangiji cikin abubuwan da ya halitta. Na farko dai shi ne asalin tushen halitta wato sammai da kassai. Ita dai wannan kasar da muke rayuwa a kanta duk da irin girman da take da shi, amma kawai tamkar wani bangare ne na duniyoyin da Allah Madaukakin Sarki ya halitta.

Na biyu kasa tana juyawa da zagaya duniyar rana ce wanda hakan ne ya ke sanya bayyanar dare da rana da kuma lokutan yanayi na shekara da ake da su da suke sassauyawa daga zafi zuwa sanyi da sauransu.

Na uku shi ne cewa jiragen ruwan da suke daukan 'yan'adam da kayansu, duk kuwa da irin girma da nauyin da yake da shi, to amma haka yake yawo a saman ruwa da kuma yin tafiya mai nesan gaske.

Na hudu ruwan saman da Allah Madaukakin Sarki ya ke sauko da shi daga sama wanda ya ke sanadiyyar sake rayar da kasa da kuma fitowar tsirrai daban-daban sannan kuma dabbobi su sami abinci da kuma iska mai kadawa wacce take kyautata yanayi.

Na biyar iskar da take kadawa wacce ba wai kawai tana taimakawa wajen tafiyar jirgin ruwan ba ne, face ma dai tana taimakawa wajen fitowar tsirrai da kuma tafiyar girgije da iska mai sanyi da zafi sannan kuma da maye gurbin iskar da ta gurbace da wata iska mai lafiya.

Na shida girgije wanda duk da nauyin da ruwan sama yake da shi, to amma duk da hakan ya kan rike ruwa din da kai shi wajaje daban-daban don sauke shi kasa.

Wadannan wasu abubuwa ne da za a iya fahimtar cikin wannan aya wadanda kuma suke nuni da irin karfi da kudura ta Ubangiji Madaukakin Sarki.

Yanzu kuma bari mu saurari aya ta 165 ta cikin Suratul Bakaran:

وَمِنَ النَّاسِ مَن يَتَّخِذُ مِن دُونِ اللّهِ أَندَاداً يُحِبُّونَهُمْ كَحُبِّ اللّهِ وَالَّذِينَ آمَنُواْ أَشَدُّ حُبّاً لِّلّهِ وَلَوْ يَرَى الَّذِينَ ظَلَمُواْ إِذْ يَرَوْنَ الْعَذَابَ أَنَّ الْقُوَّةَ لِلّهِ جَمِيعاً وَأَنَّ اللّهَ شَدِيدُ الْعَذَابِ

"Kuma akwai daga mutane wanda yake rikon kinaye baicin Allah, suna son su kamar son Allah, kuma wadanda suka yi imani ne mafiya tsananin so ga Allah. Kuma da wadanda suka yi zalunci, suna ganin lokacin da za su ga azaba da cewa lalle ne karfi ga Allah yake duka da cewa lalle ne Allah Mai tsananin azaba ne".

Duk da cewa dukkanin alamu na samuwa, a cikin sama da kasa da ruwa, da suka hada da dabbobi da tsirrai da sauran su duk suna nuni ne da kadaitakar Ubangiji, to amma wadanda ba sa yin tunani cikin wadannan alamu, abin da kawai suke ba shi muhimmanci shi ne abubuwa na zahiri wadanda suka sanya su abin bauta maimakon Allah. A wasu lokuta su na bautan taurari, wasu kuma suna ba wa wasu dabbobin girma da daukaka ta musamman don haka sai suka sanya su a matsayin allolinsu, dabbobi irin su saniya da sauransu, wasu kuma su da hannunsu suke sassaka ko kuma gina wasu gumaka daga itatuwa da duwatsu sannan kuma su dinga rusuna musu da bauta musu da kuma nuna musu kauna.

Irin wadannan so da kauna da ake nuna wa wasun Allah da ware musu wani matsayi cikin zukata, lamari ne da ke sanya a wasu lokuta a dinga bauta wa wadannan abubuwa, alhali kuwa wajibcin imani da Allah shi ne cewa dukkanin so da kaunar da mutum zai nuna wa wani abu ya zamanto saboda Allah ne sannan kuma a bisa tafarkin Allah. Irin wannan so da kauna kuwa tana tasowa bisa asasin masaniyar Ubangiji ba wai irin kaunar da mushirikai suke yi wa abubuwan da suke bauta musu ba.

Dukkanin irin wadannan so da kauna da suke nuna wa wani Allah sun samo asali ne sakamakon jahilci da camfe-camfe da koyi da iyaye da magabata da kuma son zuciya, duk kuwa da cewa a ranar tashin alkiyama za su fahimci cewa dukkanin karfi yana wajen Allah Madaukakin Sarki ne, kuskure suka yi suka kama wadannan abubuwa don samun karfi da daukaka.

Yanzu kuma bari mu saurari aya ta 166 ta cikin Suratul Bakaran:

إِذْ تَبَرَّأَ الَّذِينَ اتُّبِعُواْ مِنَ الَّذِينَ اتَّبَعُواْ وَرَأَوُاْ الْعَذَابَ وَتَقَطَّعَتْ بِهِمُ الأَسْبَابُ

"A lokadcin da wadanda aka bi suka barranta daga wadanda suka bi, kuma suka ga azaba, kuma sabubba suka yanke da su".

Wannan ayar dai tana jan kunnen 'yan 'adam ne tana gaya musu cewa Ya kai mutum lalle ka dawo cikin hayacinsa ya san wane ne shugabansa. Waye zai bi sannan kuma wa yake so a cikin zuciyarsa.

Kamata ya yi mu nuna so da kaunar mu ne ga mutumin dai ba wai yana son cimma wata manufa tasa ta duniya b ace sannan kuma aranar tashin alkiyama ya yi watsi da mu yana mai nuna cewa shi dai babu ruwansa da mu ba. A saboda haka yana da kyau mu tsaya sosai mu yi dubi da kyau a lokacin da muke son zaban wani mutum wanda zai zamanto mana jagora sannan kuma abin koyi, don kuwa makomarmu a ranar kiyama tana da alaka da shi ne don kuwa kowane mutum ana tayar da shi ne da wanda ya ke so.

Yanzu kuma bari mu yi dubi cikin darussan da suke cikin wadannan ayoyi:

1- Fahimtar dabi'a daya ne daga cikin hanyoyin fahimtar Ubangiji, don kuwa dabi'a wani waje ne na bayyanar ilimi, kudura da kuma hikima ta Ubangiji. 2- Barin kaunar wanin Allah ta sami wajen zama cikin zuciyar mutum dam aye gurbin kaunar Allah Madaukakin Sarki, hakan wata alama ce ta shirka da kuma nesantar Ubangiji. 3- Alamar imani ita ce nuna so da kauna sosai ga Allah Madaukakin Sarki wadda take bayyana cikin biyayya ga umurni da haninsa. 4- A ranar kiyama, dukkanin so da kauna da suka ginu bisa tushe na karya da son zuciya, za su koma su zamanto abin kyama da kuma guje musu. 5- Shugabanni na zalunci wadanda suka yi watsi da koyarwar Ubangiji, a ranar tashin kiyama ba wai kawai ba su da wani karfi ba ne, face ma dai ba su zamanto masu cika alkawari da sadaukarwa ga wadanda suka bi su saboda yadda za su nesance su a ranar tashin kiyama da nuna tamkar ma ba su sansu ba.

Da haka ne kuma muka kawo karshen shirin na mu na yau sai kuma a biyo mu a shiri na gaba inda za mu sake kasancewa tare da ku, kafin nan muna rokon Allah Madaukakin Sarki da ya ba mu damar fahimtarsa fahimta ta asali da kuma nuna so da kauna a gare shi da kuma nesantar duk wani abu sabanin Shi. Wassalamu alaikum wa rahamatullah wa barakatuhu.

Suratul Bakara; Aya Ta 167-171 (Kashi Na 47)

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa cikin wani sabon shirin Hannunka Mai Sanda da ke mana dubi da kuma sharhi cikin wasu ayoyi na Alkur’ani mai girma. A yau ma ga mu da wani sabon shirin na Hannunka Mai Sanda sai ku biyo mu don jin abin da muke dauke da shi.


A yau za mu fara shirin na mu ne da aya ta 167 ta cikin Suratul Bakara. Sai ku saurari ayar:

وَقَالَ الَّذِينَ اتَّبَعُواْ لَوْ أَنَّ لَنَا كَرَّةً فَنَتَبَرَّأَ مِنْهُمْ كَمَا تَبَرَّؤُواْ مِنَّا كَذَلِكَ يُرِيهِمُ اللّهُ أَعْمَالَهُمْ حَسَرَاتٍ عَلَيْهِمْ وَمَا هُم بِخَارِجِينَ مِنَ النَّارِ

"Kuma wadanda suka bi, suka ce: Da lalle ne muna da wata (dama) ta komawa (duniya) da mu barranta daga gare su kamar yadda suka barranta daga gare mu. Kamar wancan ne Allah ke nuna musu ayyukansu, suna da nadamomi a kansu, kuma ba su zama masu fita daga wutar ba".

A shirin da ya gabata mun bayyana cewar a lokacin da masu laifi suka ga ukubar Ubangiji nan take suke barranta daga mabiyansu da nuna cewa su ba su ma san da zamansu saboda kuwa daman so da kaunar da take tsakaninsu ta ginu ne bisa asasi na son zuciya, don haka sai ta koma ta zama gaba da kiyayya. A saboda haka ne wannan ayar take cewa: su wadannan mabiya na su za su yi fatan da ma za su sami damar komawa duniya su barranta da wadannan shugabanni na su da kuma nesantar su don kuwa sun ga cewa babu wani abin da suka samu sakamakon wannan biyayya in ba hasara da nadama ba, sannan kuma ga shi wadannan shugabanni sun nuna cewa ma ba su san su. To amma ina sun makara. Don kuwa ba su da wata hanya ta komawa da baya da cike gurbin da suka haifar wa kansu. Wannan ayar tana jan kunnen mutane ne da su san wanda za su rika a matsayin shugaba a duniya tun da wuri don kuwa idan aka tafi kiyama kan to babu wani abin da za su iya.

To yanzu kuma bari mu saurari aya ta 168 ta cikin wannan sura ta Bakara.

يَا أَيُّهَا النَّاسُ كُلُواْ مِمَّا فِي الأَرْضِ حَلاَلاً طَيِّباً وَلاَ تَتَّبِعُواْ خُطُوَاتِ الشَّيْطَانِ إِنَّهُ لَكُمْ عَدُوٌّ مُّبِينٌ

"Ya ku mutane! Ku ci daga abin da ya ke a cikin kasa, wanda yake halal, mai dadi. Kuma kada ku bi hanyoyin Shaidan. Lalle ne shi, a gare ku, makiyi ne bayyananne".

Ko shakka babu ci da sha daya ne daga cikin lamurra da kuma bukata ta dan'adam ne, don kuwa abinci da abin sha daya ne daga cikin bukatu na asasi na dukkanin bil'adama, to sai dai tamkar sauran abubuwa, su ma a cikinsu akwai yanayi na wuce gona da iri da kuma nuna gazawa. Saboda akwai wadansu mutane wadanda duk wani abin da zuciyarsu take so, to za su yi kokarin ci ko sha ba tare da la'akari da wasu dokoki da ka'idoji na shari'a ko kuma na hankali da suke tattare da wadannan abubuwa ba. abin da kawai suka sa a gaba shi ne yadda za su cika cikinsu da kuma biyan bukatar son zuciyarsu.

A bangare guda kuma akwai wadansu mutanen wadanda ba tare da wani dalili ba suke nesantar cin wasu abubuwa din ko da kuwa shari'a da hankali sun halalta cinsu, suna zaton cewa su din nan suna fada ne da son zuciyar su.

To addinin Musulunci dai a matsayinsa na addinin da ya hada ko ina, yana da dokoki da ka'idoji dangane da abin ci da abin sha da kuma yadda za a yi amfani da su. Ya kan halalta abubuwa masu amfani ga jiki da kuma haramta abubuwan da suke cutar da jiki da kuma ruhin mutum.

Wannan ayar tana fadin cewa ne: Allah Madaukakin Sarki ya samar da abubuwan da suke kan kasa ne saboda ku, don haka sai ku yi amfani da abubuwan da suke halal sannan kuma masu tsarki wadanda suka yi daidai da dabi'ar ku. Bai kamata haka kawai ku halalta ko kuma haramta wani abu ba, wannan wani shiri ne na Shaidan a kokarin da yake yi na batar da ku, kamar yadda ya yaudari Adamu da Hawwa'u wajen cin bishiyar da aka hana su cinta.

Yanzu kuma bari mu saurari aya ta 169 ta cikin Suratul Bakaran:

إِنَّمَا يَأْمُرُكُمْ بِالسُّوءِ وَالْفَحْشَاء وَأَن تَقُولُواْ عَلَى اللّهِ مَا لاَ تَعْلَمُونَ

"Yana umurnin ku ne kawai da mugun aiki da alfasha, kuma da ku fadi abin da ba ku sani ba ga Allah".

Ayar da ta gabaci wannan tana cewa ne: Shaidan dai makiyinku ne, ita kuwa wannan ayar tana cewa ne: alamar kiyayyar shaidan a gare ku ita ce cewa a ko da yaushe ya kasance yana kiranku zuwa ga munanan abubuwa wadanda babu wani abu tattare da su in ban da hasara da fadawa cikin fushi na Ubangiji. Ko da yake shi kansa Shaidan ba shi da iko a kanmu ta yadda zai tilasta mana yi masa biyayya, to sai dai yana bin wasu hanyoyi ne da suka hada da sanya mana waswasi da kirkiro mana abubuwan da za su raunana mana imaninmu ta haka ne sai ya ja mu zuwa ga aikata zunubin da kuma gabatar mana da wasu hanyoyi da za mu fake da su wajen halalta wadannan munanan ayyuka da muka yi. Allah Ya shiga tsakaninmu da bin son zuciyar mu.

To yanzu kuma bari mu saurari aya ta 170 ta cikin Suratul Bakaran:

وَإِذَا قِيلَ لَهُمُ اتَّبِعُوا مَا أَنزَلَ اللّهُ قَالُواْ بَلْ نَتَّبِعُ مَا أَلْفَيْنَا عَلَيْهِ آبَاءنَا أَوَلَوْ كَانَ آبَاؤُهُمْ لاَ يَعْقِلُونَ شَيْئاً وَلاَ يَهْتَدُونَ

"Kuma idan aka ce musu: Ku bi abin da Allah Ya saukar, sai su ce: A'a, muna bin abin da muka iske ubanninmu a kansa. Shin, kuma ko da ubanninsu ba su hankaltar kome, kuma ba su shiryuwa?

Kiyaye al'adu da ladubba na magabata wani lamari ne mai kyau matukar dai suka zamanto sun yi daidai da shari'a da kuma hankali, ba wai kawai riko da wasu camfe-camfe da wasu akidu na magabata din wadanda suka ginu bisa akida ta kabilanci da sauran su. To daya daga cikin hanyoyin da Shaidan yake bi wajen samun kutsawa cikin mutane da sanya riko da al'adu da dabi'un iyaye da kakaninsu ido rufe, ta yadda maimakon aiki da umurnin Ubangiji, sai suka koma suna riko da al'adun magabatansu da suke cike da kura-kurai ba tare da neman karin bayani ko dalilin hakan ba, a takaice dai ido rufe suke yin hakan ba tare da wani dalili na shari'a ko na hankali ba. A wasu lokuta ma su da kansu sun san cewa hakan kuskure ne sannan kuma addini ma yana hana su aikata hakan, to amma kuma duk hakan suke aikatawa.

Yanzu kuma bari mu saurari aya ta 171 ta cikin Suratul Bakara:

وَمَثَلُ الَّذِينَ كَفَرُواْ كَمَثَلِ الَّذِي يَنْعِقُ بِمَا لاَ يَسْمَعُ إِلاَّ دُعَاء وَنِدَاء صُمٌّ بُكْمٌ عُمْيٌ فَهُمْ لاَ يَعْقِلُونَ

"Kuma misalin wadanda suka kafirta, kamar misalin wanda ke yin me! me! ga abin da ba ya ji ne, face kira da kara, kurame, bebaye, makafi, saboda haka ba su hankalta".

Ayar da ta gabata tana fadin cewa ne: su kafirai suna bin iyaye da kakanninsu ne ido rufe, alhali kuwa su wadancan iyaye da kakannin na su ba su gina wadannan akidu da al'adu na su bisa shari'a ta Ubangiji ba. ita kuwa wannan ayar tana cewa ne: kafirai su kan su ba sa tunani ballantana ma su fahimta gaskiya da hakika, sun rufe idanuwa da kunnuwansu a gaban gaskiya don kada ma su ga wani abu ko kuma su ji wani abu. Su dai tamkar wata tinkiya ce wacce ba sa iya jin wani abu da kuma kokarin da makiyayi ya yi na kawar da su daga wani hatsari in ban da kawai ihu. Su din nan tamkar dabbobi ne wadanda suna da kunnuwa da idanuwa da harsuna, to amma duk da haka ba sa amfani da hankali, a saboda haka ba sa fahimtar gaskiya sai dai suka kama ala'adu da hanyoyi na iyaye da kakaninsu. Su na riko da dukkanin abubuwan da suka gaya musu da kuma aiki da shi ba tare da neman wani dalili cikin hakan ba.

Yanzu kuma bari mu karkare shirin na mu da darussan da za mu iya dauka cikin wadannan ayoyi:

1- Mutum dai ba dabba ba ce wacce abin da zai sa a cikinsa ne kawai ya dame shi ba, face dai wajibi ne ya samar da abin da yake bukata na abinci net a hanyoyin da shari'a ta tanadar sannan kuma ya ci abubuwan da shari'ar ta halalta masa ci. 2- Duk wani da ya ke kiran mutu zuwa ga munanan ayyuka da zunubai, to Shaidan ne shi, ko da kuwa yana da siffa ta mutane ne. 3- Ana iya biyayya da kuma riko da al'adu da dabi'un iyaye da kakanni ne a lokacin da suka ginu bisa asasi na ilimi da hankali, idan kuwa ba haka ba to irin wadannan riko da akidun iyaye da kakanni babu wani abin da zai haifar wa mutum in banda koma baya. 4- Kimar da mutum yake da ita tana cikin hankali da tunanin da ya ke yi ne, idan kuwa ba haka ba, to dabbobi ma suna da idanuwa da kunnuwa da kuma harsuna tamkar mutanen.

Muna rokon Allah Madaukakin Sarki da ya taimaka mana wajen fada da waswasi na Shaidan sannan kuma mu zamanto masu amfani da hankali da tunaninmu wajen zaban tafarkin da za mu rika.

Wassalamu alaikum wa rahamatullah wa barakatuhu.

Suratul Bakara; Aya Ta 177-179 (Kashi Na 49)

Assalamu alaikum jama’a masu saurare, barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda, a yau shirin namu zai yi dubi ne a cikin ayoyi masu albarka, a cikin suratul Baqarah, aya ta 177 zuwa 179.

Aya ta ( 177 ) Bakara:

لَّيْسَ الْبِرَّ أَن تُوَلُّواْ وُجُوهَكُمْ قِبَلَ الْمَشْرِقِ وَالْمَغْرِبِ وَلَـكِنَّ الْبِرَّ مَنْ آمَنَ بِاللّهِ وَالْيَوْمِ الآخِرِ وَالْمَلآئِكَةِ وَالْكِتَابِ وَالنَّبِيِّينَ وَآتَى الْمَالَ عَلَى حُبِّهِ ذَوِي الْقُرْبَى وَالْيَتَامَى وَالْمَسَاكِينَ وَابْنَ السَّبِيلِ وَالسَّآئِلِينَ وَفِي الرِّقَابِ وَأَقَامَ الصَّلاةَ وَآتَى الزَّكَاةَ وَالْمُوفُونَ بِعَهْدِهِمْ إِذَا عَاهَدُواْ وَالصَّابِرِينَ فِي الْبَأْسَاء والضَّرَّاء وَحِينَ الْبَأْسِ أُولَـئِكَ الَّذِينَ صَدَقُوا وَأُولَـئِكَ هُمُ الْمُتَّقُونَ

Tarjama: Bai zama addini ba dõmin kun jũyar da fuskõkinku wajen gabas da yamma, kuma amma addini shi ne ga wanda ya yi ĩmãni da Allah da rãnar Lãhira da malã'iku da littattafan sama da Annabãwa, kuma ya bãyar da dũkiya, a kan yana sonta, ga mai zumunta da marãyu da matalauta da matafiyi da mãsu tambaya, kuma a cikin fansar wuyaye, kuma ya tsayar da salla ya bãyar da zakka, da mãsu cika alkawari idan sun kulla alkawarin, da mãsu hakuri a cikin tsanani da cũta da lõkacin yãki. Wadannan su ne suka yi gaskiya. Kuma wadannan su ne mãsu takawa.

Wannan aya mai albarka tana daga cikin ayoyin kur'ani mai tsarki da suka yi bayani filla-filla a kan asalin kyawawan dabi'u da akidar musulunci ta koyar da dan adam, an ruwaito daga manzon Allah (SAW) cewa duk wanda ya yi aiki da wannan aya lallai imaninsa ya kammala. Haka nan dangane da ayar canja alkibla, an ambaci cewa yahudawa sun nemi su kawo rikici kan lamarin, amma wannan aya mai labarka ta ba su amsa, inda ta bayyana musu kada ku yi tsammanin cewa addinin Allah shi ne kawai kallon alkibla, bin addinin Allah da aiki na gari na tattare da abubuwa uku, daya yana da dangantaka da akida ta imani da Allah madaukakin sarki, wato dole mutum ya yi imani da Allah da mala'ikunsa, da littafan da aka safkar daga sama da kuma annabawan Allah. A zahiri lamri yake cewa irin wannan imani na bukatar a gan shi a aikace a cikin ayyukan ibada, kamar su salla, kyautata ma masu rauni da taimakon mubukata, ciyarwa saboda Allah, bayar da zakka da dai sauran ayyuka makamantan hakan. Samun kusanci da Allah ba shi ne abin da ake bukata ba kawai, babban abin da ake bukata shi ne samun kusanci tare da kiyaye shi, wato ba aikata aikin da zai kusantar da mutum zuwa ga Allah ba, a wani lokaci kuma mutum ya aikata abin da zai nisantar da shi daga Allah, tare da rusa ayyuaknsa na alkhairi. Samun tabbatuwa kan kusanci ga Allah yana kasancewa ne ta hanyar kiyaye kyawawan dabi'u, hakuri, cika alkawali, kiyaye hanin Allah, da aikata umurninsa, da sauran abubuwa makamantan hakan, su ne suke taimaka ma mutum wajen tabbatuwa kan kusanci ga Allah madaukakin sarki a kowane lokaci. Wannan ayar tana nuna mana cewa mumini shi ne wanda yake bayar da hakkin Allah daga duniyarsa wanda ya wajabta masa wato zakka, da kuma abin da ma ba a wajabta masa na daga ciyarwa daga dukiyarsa domin Allah.

Aya ta ( 178 ) Bakara:

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُواْ كُتِبَ عَلَيْكُمُ الْقِصَاصُ فِي الْقَتْلَى الْحُرُّ بِالْحُرِّ وَالْعَبْدُ بِالْعَبْدِ وَالأُنثَى بِالأُنثَى فَمَنْ عُفِيَ لَهُ مِنْ أَخِيهِ شَيْءٌ فَاتِّبَاعٌ بِالْمَعْرُوفِ وَأَدَاء إِلَيْهِ بِإِحْسَانٍ ذَلِكَ تَخْفِيفٌ مِّن رَّبِّكُمْ وَرَحْمَةٌ فَمَنِ اعْتَدَى بَعْدَ ذَلِكَ فَلَهُ عَذَابٌ أَلِيم

Tarjama: Yã kũ wadanda suka yi ĩmãni! An wajabta, a kanku, yin kisãsi a cikin kasassu. da da da kuma bãwa da bãwa, kuma mace da mace, to, wanda aka yi rangwamen wani abu gare shi daga dan'uwansa to a bi da alhẽri da biya zuwa gare shi da kyautatãwa. Wancan saukakewa ne daga Ubangijinku, kuma rahama ce. To wanda ya yi zãlunci a bãyan wancan, yana da azãba mai radadi.

Musulunci addini ne da ya dora ka'idoji da suka dace da dabi'a ta dan adam, a matsayi na daidaiku da kuma a mataki nazamantakewarsa, irin wadannan ka'idoji sun hada da shari'a da hukunce-hukuncen da suke cikinta, ta yadda bin irin wanan sahihin tsari na addini muslunci shi ne kubutar mutum da kuma al'ummarsa, ta fuskar tsaronsa, rayuwarsa ta duniya da lahira, da ma samun natsuwar zuci, ta yadda rashin bin dokokin Allah kan sanya mutane su shiga fagamniyya da rashin natsuwa, ta jiki da ta ruhi. Misali, yin kisan kai a cikin al'umma, idan mutun ya san cewa ga hukuncin da zai hau kansa idan ya kashe mutum daidai da shari'a ta addinin muslunci, zai yi shayin yin hakan ko da ba don tsoron Allah ba, domin tunain abin da zai je ya dawo kan rayuwarsa, to lokacin da mutane suke jin haka, za a samu karancin kasashe-kashe a cikin al'umma, kenan ta nan musulunci ya tababbatar da tsaro ta hanyar shari'arsa da tsarinasa a cikin rayuwar jama'a ta zamnatakewa. Idan kuma har wani ya yi hakan, to jinin wanda aka zalunta ba zai tafi wofi ba. A bisa tsari na addinin muslunci, a lokacin aiwatar da kisasi dole ne a kiyaye adalci, a kan haka ne ma wurin aiwatar da irin wannan hukunci babu fifiko ga wani a kan wani, in banda wasu wurare kawai da aka kebance, wanda bahasinsu yana cikin ilimin shari'a da hukunce-hulkuncenta.

Aya ta ( 179 ) Bakara:

وَلَكُمْ فِي الْقِصَاصِ حَيَاةٌ يَاْ أُولِيْ الأَلْبَابِ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ

Tarjama: Kuma kuna da rãyuwa a cikin kisãsi, yã ma'abuta hankula; tsammãninku, zã ku yi takawa.

Abun ban takaici ne yadda wasu masu kallon kansu a matsayin masana a cikin duniya suke kawo wasu bayanai na rikitarwa dangane da sha'anin kisasi, inda suke bayyana cewa babu hikima a ckin irin wannan hukunci, domin kuwa a ganinsu idan wani ya kashe wani, shi kuma aka kashe shi, to mutum biyu aka rasa, kuma wadanda suka kasashe shi su ma sun yi kisan kai. Kuma a cikinsu akwai masu ganin idan aka kashe wanda ya yi kisa, shin wanda aka kashe da farko zai dawo a raye ne? idan har ba zai dawo ba, to a ganinsu babu amfanin a kasha wanda ya kasha shi. Irin wadannan mutane masu irin wannan karkatattar mahanga, kur'ani ya ba su amsa, inda ya ce rayuwar aminci da salama tana nan cikin kisasi, zartar da hukuncin kisa kan wanda ya yi kisan yana haifar da salama a cikin rayuwar al'umma baki daya. Wata kila masu irin wannan mahanga suna ganin cewa kisasi tamkar wani aiki ne na daukar fansa ba wai kawai hukunci ne na shari'a ba, alhali idan suka duba a rayuwar duniyar yau, su ka tambayi kansu ina ne inda akafi aikata muggan laifuka na kisa da abin da ya yi kama da haka, za su ga cewa kasashen da ba su yi imani da irin wannan hukuncin ba ne aka fi aikata laifukan kisan kai, domin kuwa mai a'aikata irin wannan laifin ya san cewa wata kila zai iya kubuta a kotu, ko kuma hukuncin da zai fuskanta mafi tsanani shi ne a daure shi rai da rai, ko kuma wasu shekaru kamar yadda muke gani yanzu a kasashen da ke da'awar ci gaba.

Muhimman abubuwan da za mu iya koyo daga wadannan ayoyi masu albarka: 1- Imani da ubangiji ba tare da taimakon raunana ba, ba tare da girmama mutane da hakkokinsu ba, ba zai zama imani kammalalle ba. 2- Bayar da dukiya da ciyar da ita saboda Allah, alama ce ta cikar imani da Allah da kuma gasgata sakonsa. 3- Imani na bukatar hakuri da juriya a kan musibu, jurewa talauci da tsanani na rayuwa da kuma lokacin yaki, kamar yadda jin dadi da wadata ba za su iya raunana imanin mumini na gaskiya ba. 4- Saboda wasu dalilai musulunci yana karbar afuwa da diyya a lokacin kisasi, idan ma'abota jini suka yafe.

Suratul Bakara; Aya Ta 180-182 (Kashi Na 50)

Assalamu alaikum jama’a masu saurare, barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda, a yau shirin namu zai yi dubi ne a cikin wadannan ayoyi masu albarka, a cikin suratul Baqarah, aya ta 180 zuwa ta 182. Ya zo a cikin wani hadisin ma'aiki tsira da aminicin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa cewa: Madallah da alkur'ani a tsakaninku, ku sanya shi a gaba kuma jagora.

Aya ta (180 ) Bakara

كُتِبَ عَلَيْكُمْ إِذَا حَضَرَ أَحَدَكُمُ الْمَوْتُ إِن تَرَكَ خَيْراً الْوَصِيَّةُ لِلْوَالِدَيْنِ وَالأقْرَبِينَ بِالْمَعْرُوفِ حَقّاً عَلَى الْمُتَّقِينَ

Kuma an wajabta a kanku idan mutuwa ta halarci dayanku, idan ya bar wata dũkiya, yin wasiyya dõmin mahaifa da dangi bisa ga abin da aka sani wajabce a kan mãsu takawa.

Kowane daya daga cikin mutane ya zo duniya ne a wata rana, kuma wata ranar tana zuwa da zai bar duniya, mun zo duniya ba tare da komai ba na tarkacen dukiya, kuma haka za mu koma zuwa ga mahaliccin talikai baki daya. Dukkanin abubuwan da muka mallaka na duniya da tarkacen duniya dole ne za a bar su a gidan duniya. Bisa ka'ida ta addinin muslunci, idan mutuwa ta halarto ma mutum, ya dauki wani bangare da bai wuce haddin da shari'a ta kayyade ba, ya raba wa mahaifansa 'ya'yansa da matansa da 'yan uwansa, wannan ba a lissfa shi a cikin gado bayan rasuwarsa, kuma ba ya da bukatar rubuta wasiyya a kansa a lokacin da ya damka wa kowannensu abin da ya ba shi kafin rasuwarsa. Ko da yake dole ne wasiyya ta yi daidai da abin da hankali zai karba, kada ta zama so da kauna sun shiga cikinta har ta kai ga bayar da abin da zai cutar da wani bangare daga iyalansa da magadansa bayan rasuwarsa, ta yadda hakan zai iya haifar da rikici a cikin iyalansa. Iyaye suna daga cikin wadanda ake yi wa wasiyya da wani bangare na dukiya, bisa la'akari da matsayinsu da Allah ya ba su a cikin addini a kan 'ya'yansu, dole ne a kiyaye hakkinsu.

Aya ta ( 181 ) Bakara

فَمَن بَدَّلَهُ بَعْدَ مَا سَمِعَهُ فَإِنَّمَا إِثْمُهُ عَلَى الَّذِينَ يُبَدِّلُونَهُ إِنَّ اللّهَ سَمِيعٌ عَلِيمٌ

To, wanda ya musanya masa a bãyan ya ji shi, to, kawai laifinsa yana a kan wadanda suke musanya shi. Lalle ne, Allah Mai ji ne, Masani.

Wasu lokuta 'ya'ya ko dangi duk da sun ji wasiyya kamar yadda mamaci ya yi ta kafin rasuwarsa, amma sukan canja ta saboda wasu dalilai, misali mai wasici ya yi wasiyya da a baiwa wani mabukaci wani abu daga cikin dukiyarsa, kudi ko abin da ya yi kamada haka, sai su baiwa wani na daban. Wannan aya tana nuni da cewa a lokacin da aka samu wani ya canja wasiyya, wato ya yi abin da ba shi aka nufa da ita ba, kamar misalin da aka bayar, to a lokacin shi wanda ya karbi abin da aka ce a bayar ba shi da laifi, shi wanda ya canja wasiyar ya bayar da ita ba inda aka ce ba, shi ne ke da laifi. A cikin wannan aya mai albarka za mu iya koyon cewa, wajibi ne a yi aiki da wasiyya kamar yadda aka bayar da ita, kuma canja wani abu daga cikinta aikin ha’inci ne, wanda har Allah ya bayyana shi da aikin zunubi, saboda haka wajibi ne musulmi su kiyaye lamarin wasiyya kamar yadda addinin muslunci ya yi umurni, domin kaucewa fadawa cikin fushin ubangiji.

Aya ta ( 182 ) Baqarah:

فَمَنْ خَافَ مِن مُّوصٍ جَنَفاً أَوْ إِثْماً فَأَصْلَحَ بَيْنَهُمْ فَلاَ إِثْمَ عَلَيْهِ إِنَّ اللّهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ

To, wanda ya ji tsõron karkata ko kuwa wani zunubi daga mai wasiyyar, sai ya yi sulhu a tsakãninsu to bãbu laifi a kansa. Lalle ne Allah, Mai gãfara ne,Mai jin kai.

A cikin aya mai albarka da ta gabaci wannan an bayyana cewa, canja wasiyya aiki ne na laifi, to amma kuma wasu lokuta wata wasiyyar za ta iya jawo wata babbar matsala ko rikici a tsakanin dangi, idan aka aiwatar da ita kamar yadda mamaci ya bayar da ita kafin rasuwarsa, saboda wata kila sonsa da wani bangare a cikin ‘ya’yansa ko matansa ko ‘yan uwansa, sai ya fifita wasu a kan wasu a cikin wasiyarsa, ko kuma ya yi wasiya da a aikakata wani abu na sabon Allah bayan rasuwarsa, to a lokacin za a duba maslaha idan lamarin ya shafi magada, idan kuma wasiyyar tasa ta sabon Allah ce, to haramun ne ma a aiwatar da ita. Wannan ayar tana yi mana hannunka mai sanda kan cewa, addinin muslunci addini ne na adalci da ‘yanci, addini ne da baya zalunci, ba ya umurni da tauye hakkoki, addini ne na zaman lafiya da sulhu da fahimtar juna, addini ne na daidaita tsakanin masu husuma, addini ne da ke girmama dan adam da kare hakkinsa a lokacin rayuwarsa da ma bayan ransa, addini ne da baya umurni da fitina ko abin da zai kawo fitina a cikin al’umma.

Suratul Bakara; Aya Ta 183-186 (Kashi Na 51)

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai.

Assalamu alaikum jama’a masu saurare, barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda, a yau shirin namu zai yi dubi ne a cikin wannan aya mai albarka, a cikin suratul Baqarah, aya ta 183.

Aya ta ( 183 ) Baqarah

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُواْ كُتِبَ عَلَيْكُمُ الصِّيَامُ كَمَا كُتِبَ عَلَى الَّذِينَ مِن قَبْلِكُمْ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ

Yã ku wadanda suka yi ĩmãni! An wajabta azumi a kanku kamar yadda aka wajabta shi a kan wadanda suke daga gabãninku, tsammãninku, zã ku yi takawa,

Daya daga cikin abubuwan da Allah madaukakin sarki ya yi umurni da su kuma ya wajabta su a kan muminai shi ne azumi, wanda kuma wannan aikin ibada bai takaitu da al’ummar manzon Allah Muhammad (SAW) ba, a ‘a har ma sauran annabawa da suka gabata da al’ummominsu suna yin wannan ibada. Ibadar azumi ba aiki ba ne wanda ake gani kamar yin sallah ko aikin hajji, ita ibada ce ta kamewa daga barin wasu abubuwa a wani kayyaden lokaci a cikin wata daya, wato ramadan mai alfarma, inda mutum zai kame daga ci ko sha tun daga fitowar alfijin har zuwa bayan faduwar rana, kamar yadda wajibi ya kame daga dukkanin sha’wace-shawacensa, da kame bakinsa daga furta abubuwa na sabon Allah. Azumi yan asirri a cikin rayuwar mutum ta addini da kuma ta ‘yan adamtaka, inda yakan natsar da ruhin mutum, da ba shi wani wani sabon yanayi na kusanci da Allah, a bangare guda kuma ya kan ladabtar da mutum ta hanyar dandana yunwa kishi, wanda hakan kan sanya mutum tunani kan marassa galihu da kuma halin da suke samun kansu a ciki, tare da tausaya musu da kuma taimaka musu, wanda a nan azumi ya zama wata hanya ta raya ruhin tausayi da kumanjin taimako a tsaknain mutane. Daga wannan aya za mu koyi cewa: 1- Yin azumi na daga cikin alamun imani da Allah, , wanda kuma yinsa yana karfafa ruhin mutum wurin samun takawa (tsoron Allah) 2- Yin aiki da umurnin Allah madaukakin sarki amfanin hakan na komawa ne zuwa gare mu ‘yan adam, domin kuwa Allah ba ya da bukata zuwa ga ibadarmu, kamar yadda sabonmu ba ya cutar da shi.

Aya ta ( 184 ) Baqarah

أَيَّاماً مَّعْدُودَاتٍ فَمَن كَانَ مِنكُم مَّرِيضاً أَوْ عَلَى سَفَرٍ فَعِدَّةٌ مِّنْ أَيَّامٍ أُخَرَ وَعَلَى الَّذِينَ يُطِيقُونَهُ فِدْيَةٌ طَعَامُ مِسْكِينٍ فَمَن تَطَوَّعَ خَيْراً فَهُوَ خَيْرٌ لَّهُ وَأَن تَصُومُواْ خَيْرٌ لَّكُمْ إِن كُنتُمْ تَعْلَمُونَ

Kwanuka kidãyayyu. To, wanda ya kasance daga gare ku majinyaci ko kuwa yana a kan tafiya, sai (ya biya) adadi daga wasu kwanuka na dabam. Kuma a kan wadanda suke yin sa da wahala akwai fansa; ciyar da matalauci, sai dai wanda ya dãra alhẽri to, shi ne mafi alhẽri a gare shi. Kuma ku yi azumi (da wahalar) ne mafi alhẽri a gare ku idan kun kasance kuna sani.

A kowane lokaci Allah madaukakin sarki ba tsanantawa ba ne kan bayinsa, domin kuwa kowane mutum yana aikata umurnin Allah ne daidai iyawarsa da ikon da Allah ya ba shi kan yin hakan. Azumina wajibi a cikin addinin muslunci shi ne na wata guda, wato ramadana mai alfarma, wanda shi ma Allah ya kawo sauki ga marassa lafiya ko matafiya, ko kuma tsoffi. Inda matafiya za su rama abin suka sha na kawanakin watan ramadan a wasu lokutan na daban a cikin wasu watannin, kamar yadda su ma marassa lafiya idan sun samu sauki, da za su iya rama azumi, to za su yi daidai ne da hukuncin matafiya, yayin da tsoffi da ba za su iya ba, ko marassa lafiya da ba su samu saukin da za su iya ramawa ba, to za su bayan ciyar da wani mikidari na abinci.

A cikin wannan ayar mai albarka za mu koyi cewa, musulunci addini ne da ya yi daidai da kowane aji na mutane, da kuma yana ka’idoji da dokoki da suka yi daidai da yanayin da suka samu kansu, wannan kuwa har da zumi, inda musulunci ya yi la’akari da yanayin mutane kuma saka ka’idoji da hukunce-hukuncensa bisa hakan.

Aya ta ( 185 )

شَهْرُ رَمَضَانَ الَّذِيَ أُنزِلَ فِيهِ الْقُرْآنُ هُدًى لِّلنَّاسِ وَبَيِّنَاتٍ مِّنَ الْهُدَى وَالْفُرْقَانِ فَمَن شَهِدَ مِنكُمُ الشَّهْرَ فَلْيَصُمْهُ وَمَن كَانَ مَرِيضاً أَوْ عَلَى سَفَرٍ فَعِدَّةٌ مِّنْ أَيَّامٍ أُخَرَ يُرِيدُ اللّهُ بِكُمُ الْيُسْرَ وَلاَ يُرِيدُ بِكُمُ الْعُسْرَ وَلِتُكْمِلُواْ الْعِدَّةَ وَلِتُكَبِّرُواْ اللّهَ عَلَى مَا هَدَاكُمْ وَلَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ

Watan Ramalãna ne wanda aka saukar da Alkur'ãni a cikinsa yana shiriya ga mutãne da hujjõji bayyanannu daga shiriya da rarrabẽwa. To, wanda ya halarta daga gare ku a watan, sai ya azumce shi, kuma wanda ya kasance majinyaci ko kuwa a kan tafiya, sai ya biya adadi daga wasu kwanuka na dabam. Allah Yana nufin sauki gare ku, kuma ba Ya nufin tsanani gare ku, kuma dõmin ku cika adadin, kuma dõmin ku girmama Allah a kan Yã shiryar da ku, kuma tsammãninku, zã ku gõde.

Ayar da ta gabaci wannan ta yi bayani ne kan wajabcin azumi, da kuma wasu daga cikin hukunce-hukuncensa, yayin da ita kuma wannan aya mai albarka take yin bayani kan lokacin gudanar da wannan aikin ibada na azumi, wato watan ramadana mai lafarma. Kafin watan ramadan ya zama watan azumi na wajibi a kan musulmi, ya kasance shi ne watan da aka safkar da kur’ani mai tsarki a cikinsa, a cikinsa ne dare mafi daraja da albarka yake, wato daren laitul qadr, wanda shi ne daren safkar kur’ani mai tsarki, A cikin kur’ani mai tsarkin sunan watan ramadan ne kawai aka ambata da sunansa,

Musulunci addini ne mai sauki wanda ba ya san tsanantawa a kan mabiyansa, a kan haka ne aka yi sauki ga wadanda suke cikin tafiya ko rashin lafiya da su sha azumi, sai su rama a wasu lokuta na daban, yayin da wadanda ba za su iya yi ba sam-sam sai su bayar da kaffara. A wannan aya za mu koyi cewa: Watan ramadan wata ne na samun tsarki da kusanci da Allah, wata mai albarka da aka safkar da kur’ani a cikinsa, saboda haka mayar da hankali wajen karatun kur’ani da samun falalar hakan yafi yawa a cikin watan azumi fiye da sauran watannin shekara.

Aya ta ( 186 )

وَإِذَا سَأَلَكَ عِبَادِي عَنِّي فَإِنِّي قَرِيبٌ أُجِيبُ دَعْوَةَ الدَّاعِ إِذَا دَعَانِ فَلْيَسْتَجِيبُواْ لِي وَلْيُؤْمِنُواْ بِي لَعَلَّهُمْ يَرْشُدُونَ

Kuma idan bãyiNa suka tambaye ka daga gare Ni, to, lalle Ni Makusanci ne. Ina karba kiran mai kira idan ya kirã Ni. Sabõda haka su nẽmi karbawaTa, kuma su yi ĩmãni da Ni: tsammãninsu, su shiryu.

Wani mutum ya tambayi manzon Allah (SAW) cewa: shin Allah yana kusa da mu ne domin in kira shi a hankali, ko kuwa yana nesa ne domin in daga muryata a lokacin da nake kiransa? Sai wannan aya mai albarka ta dafka, inda take bayyana cewa Allah madaukakin sarki a koda yaushe yana kusa da bayinsa, wata ayar ma dake cikin surat Qaf tana ishara da cewa, shi ne ya fi kusa da bayanisa fiye da jijiyoyin wuyayensu. Addu’a ba ta da wani wuri ko lokaci wanda za a ce dole sai nan kawai za a yi ta, a duk inda mutum ya samu kansa zai iya rokon Allah madaukakin sarki, Allah yana tare da shi kuma yana saurarensa, amma shi watan ramadan yana da wani matsayi na musamman, domin kuwa addu’ar mai azumi karbabba ce, saboda muhimmancin yin addu’a ne ma wannan aya ta kasance tsakanin ayoyin da ke yin magana kan azumi da matsayin watan ramadana mai alfarma. A cikin wannan aya zamu koyi wadannan abubuwa: Allah madaukakin sarki a koda yaushe yana tare da bayinsa, kuma yana sauraren addu’arsu, kuma yana karba musu idan sun roke shi, , a kan haka kada mu yi saku-saku da addu’a, a kowane lokaci. Bayan haka kuma za mu fahimci cewa shi Allah ne yake kiran bayinsa da su roke shi saboda yawan rahamarsa da tausayinsa, da kuma yadda a koda yaushe yake son bayinsa da alkhairi, kuma karba wannan kira na Allah wato rokonsa da yin addu’a, yin hakan yana tattare da shiryar ubangiji.

Suratul Bakara; Aya Ta 187-189 (Kashi Na 52)

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai.

Assalamu alaikum jama’a masu saurare, barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda, a yau shirin namu zai fara ne da yin dubi a cikin wannan aya mai albarka, a cikin suratul Baqarah, aya ta ta 187.

Aya ta ( 187 ) Baqarah

أُحِلَّ لَكُمْ لَيْلَةَ الصِّيَامِ الرَّفَثُ إِلَى نِسَآئِكُمْ هُنَّ لِبَاسٌ لَّكُمْ وَأَنتُمْ لِبَاسٌ لَّهُنَّ عَلِمَ اللّهُ أَنَّكُمْ كُنتُمْ تَخْتانُونَ أَنفُسَكُمْ فَتَابَ عَلَيْكُمْ وَعَفَا عَنكُمْ فَالآنَ بَاشِرُوهُنَّ وَابْتَغُواْ مَا كَتَبَ اللّهُ لَكُمْ وَكُلُواْ وَاشْرَبُواْ حَتَّى يَتَبَيَّنَ لَكُمُ الْخَيْطُ الأَبْيَضُ مِنَ الْخَيْطِ الأَسْوَدِ مِنَ الْفَجْرِ ثُمَّ أَتِمُّواْ الصِّيَامَ إِلَى الَّليْلِ وَلاَ تُبَاشِرُوهُنَّ وَأَنتُمْ عَاكِفُونَ فِي الْمَسَاجِدِ تِلْكَ حُدُودُ اللّهِ فَلاَ تَقْرَبُوهَا كَذَلِكَ يُبَيِّنُ اللّهُ آيَاتِهِ لِلنَّاسِ لَعَلَّهُمْ يَتَّقُونَ

An halatta a gare ku, a daren azumi, yin jima'i zuwa ga matanku sũ tufa ne a gare ku, kuma kũ tufa ne a gare su, Allah Yã sani lalle ne ku kun kasance kuna yaudarar kanku. Sabõda haka Yã karbi tũbarku, kuma Yã yãfe muku. To, yanzu ku rungume su kuma ku nẽmi abin da Allah yã rubũta muku. Kuma ku ci kuma ku sha har sĩlĩli fari ya bayyana a gare ku daga sĩlĩli baki daga alfijiri, sa'an nan kuma ku cika azumi zuwa ga dare. Kuma kada ku rungume su alhãli kuna mãsu itikãfi a cikin masallãtai. Wadancan iyãkokin Allah ne: don haka kada ku kusancesu kamar haka ne Allah Yake bayyana ãyõyinSa ga mutãne: tsammãninsu, zã su yi takawa.

Daga cikin ka’idoji da dokoki na azumi addinin muslunci ya gindaya wa musulmi a cikin watan ramadan, a lokacin azumi haramun ne su kusanci matayensu, kamar yadda haramun ne su ci abinci ko abin sha, har sai bayan shan ruwa, amma kafin safkar wannan ayar kusantar mataye ya kasance cikin abubuwan da aka hana a cikin watan ramadan baki daya har ma cikin dararensa, lamarin da ya yi wa wasu daga cikin musulmi matukar wahala, inda suka fadi wannan jarabawa ta ubangiji, amma daga bisani Allah ya safkar da wannan aya kuma ya yi musu afuwa kan hakan, kuma ka halasta musu kusantar mataye a daga bayan shan ruwa har zuwa kafin fitowar alfijir, koda yake wannan hukunci ya takaitu ne ga wadanda ba suna cikin i’itikafi ne ba ne a masallaci, domin su hakan bai halasta gare su ba. Wannan aya mai albarka ta siffanta mata a matsayin tufa ga maza, kamar yadda mazaje suke a matsayin tufa ga matayensu, tofa bisa ga al’ada tana rufe tsiraici da aibi, tana kuma kawata wanda ya saka ta. A kan haka ne kur’ani ya bayar da wannan misali, domin kuwa ma’aurata suna matsayin tufa ne ga junansu, kowanne dayansu yana taimaka dayan ne, yana yi masa nasiha, yana nuna masa gaskiya, ya shiryear da shi zuwa ga abin da Allah ke so domin ya aikata, da nusar da shi abin da Allah ba ya so domin kaurace masa, sakamakon kaunar juna da tusayi da ke tsakaninsu. Abubuwan da za mu iya koyo daga wannan aya mai labarka: 1- Daga cikin abubuwan da musulmunci ya kebanta da su shi ne saukakawa, a duk lokacin da wani hukunci ya zama da wahala to Allah madaukakin sarki ya kan saukaka ma muminai. 2- Saba ma umurnin Allah da aikata zunubi da yin ha’inci da zalunci yana cutar da mu ne kai tsaye, ba Allah madaukakin sarki ba. 3- Addinin muslunci bai hana mabiyansa jin dadi ba, amma dai ya saka tsari a cikin dukkanin komai, ta yadda mabiyansa ba za su fita daga dokokin ubangiji ba. 4- Mutum ba shi da hujjar aikata sabon ubangiji alhali Allah ya hore masa hanyoyin da zai bi domin samun sa’ada ta duniya da lahira. 5- Kusantar sabo na gab da ya zama aikata shi, domin kuwa sai mutum ya kusanci sabo ne zuciyarsa tare da zugar shedan zai kai ga aikata sabon, shi ya sanya a wasu wurare kur’ani ke yin hani da kusantar sabo domin kada mu fada cikin laifin aikata shi. 6- Dukkanin abubuwan da aka shata na ka’idoji da doki na azumin watan ramadan, babbar manufar hakan ita ce samun tsarkakar ruhi da taqawa, da kuma nisantar sabon ubangiji.

Aya ta ( 188 )

وَلاَ تَأْكُلُواْ أَمْوَالَكُم بَيْنَكُم بِالْبَاطِلِ وَتُدْلُواْ بِهَا إِلَى الْحُكَّامِ لِتَأْكُلُواْ فَرِيقاً مِّنْ أَمْوَالِ النَّاسِ بِالإِثْمِ وَأَنتُمْ تَعْلَمُونَ

Kada ku ci dukiyõyinku a tsakãninku da barna, kuma ku sãdu da ita zuwa ga mahukunta dõmin ku ci wani yanki daga dũkiyõyin mutãne da zunubi alhãli kuwa kũ, kuna sane.

Wannan aya mai albarka tana yin nuni zuwa ga wasu manyan laifuka biyu, da suke jawo yaduwar rashin adalci da rashin tsaro a cikin rayuwar al’umma da attalin arzikinsu, inda ake yi wa musulmi gargadi da su guje su. Na daya shi ne cin dukiyar wani ta hanyar da ba ta dace ba, na biyu bayar da rashawa ga alkalai domin mallake dukiyoyin jama’a, lamarin da ya sa aka hani musulmi da yin hakan hani mai tsanani, tare da bayyana shi a matayin babban zunubi. Ayyukan da shari’a ta hana, ko a hankalce za a ga ba su dace da dabi’a ta dan adam ba, da ma yanayin zamantakewarsa ba, duk da cewa wasu suna bayar da cin hanci da rashawa a matsayin kyauta ko ihsani, wanda hakan ba ya taba halasta rashawa, matukar dai manufar hakan ita ce rashawar amma ta wata hanya ta daban. Abubuwan da za mu koya acikin wannan aya: 1- Muslunci yana girma mutane da abin da suka malakka, saboda haka ba ya bayar da dama ga wani ya yi tasarrufi da dukiyar wani ba bisa ka’ida ba. 2- Mallakar abu dole ne ya zama ta ingantacciyar hanya ta halas, mallakar dukiyar jama’a ta wata hanya wadda ba wannan ba, ba ta halasta dukiyar, ko da kuwa alkali ya halasta ta. 3- Karbar rashawa da bayar da ita haramun ne, ko da kuwa an bayar da ita ne da waniu suna ba cin hanci da rashawa ba.

Aya ta (189) Baqarah

يَسْأَلُونَكَ عَنِ الأهِلَّةِ قُلْ هِيَ مَوَاقِيتُ لِلنَّاسِ وَالْحَجِّ وَلَيْسَ الْبِرُّ بِأَنْ تَأْتُوْاْ الْبُيُوتَ مِن ظُهُورِهَا وَلَـكِنَّ الْبِرَّ مَنِ اتَّقَى وَأْتُواْ الْبُيُوتَ مِنْ أَبْوَابِهَا وَاتَّقُواْ اللّهَ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ Kuma suna tambayar ka daga jirajiran wata. Ka ce: "Su lõkatai ne dõmin mutãne da haji, kuma bã addini ba ne ku je wa gidãje daga bãyansu: kuma amma abin da yake addini shi ne wanda ya yi takawa. Kuma ku je wa gidãje daga kõfõfinsu, kuma ku bi Allah da takawa: tsammãninku, ku ci nasara.

Wani abu da musulunci ya shahara da shi, shi ne tsari a cikin dukkanin lamurra, da suka hada da hukunce-hukuncensa da sauran lamurran na zamantakewar mabiyansa. Misali, loktan salla an sanya su zama daga lokacin fitowar alfijir, ko gushewar rana, ko faduwarta da dai makamantan hakan, azumi na wajibi daga farkon watan ramadan zuwa karshensa, tare da yinsa a daga fitowar alfijir zuwa bayan faduwar rana, lokacin aikin haji a cikin wata na musamman wato zul hijja, tare da ka’idoji da hanyoyi na musamman da ake yinsa. Dangane da batun ganin wata ma musulunci yama ka’idoji da ake yin la’akari da su, ta yadda za su dace da yanayi na kwanan wata na shekara. Abu na biyu shi ne batun aikin hajji, akwai ayyukan da wasu daga cikin musullmi suke yi wadanda ada kafin musulunci suke yi a lokacin da suke zuwa Ka’aba, a lokacin musulunci ma suna yin wadannan ayyukan a lokacin aiki haji, sai aka bayyana musu hakan da cewa surkulle ne na jahiliyya da ba shi da wuri a cikin addinin muslunci. Abubuwan koyoo a cikin wannan aya mai albarka: 1- Dole ne mutum ya saka rayuwarsa bisa tsari, domin ubangiji bai bar lamarin bayanisa a sake ba babu tsari, ta yadda bayinsa za su ci gajiyar rayuwarsu ta duniya a rayuwa ta har abada, haka nan mutumzai iya cin ribar rayurwa ne idan ya tsara ta kan biyayya ga umurnin Allah, tare da aikata kyawawan ayyuka, da tsara loktansa na ibada da ayyuaknsa na neman halas domin ya samu abin da zai rayu da shi da iyalansa. Kyakkyawan aiki a koda yaushe hankali da shari’a suke yin umurni da shi, domin kuwa shi ne ke ga ma’abocinsa zuwa ga samun taqawa, ba hada ayyuka n shirme da ayyuka na kwarai, domin kuwa sabin na kwarai ba su kai ma’abocinsu ga taqawa, alhali kur’ani mai tsarki ya gaya mana cewa: Allah yana karbar ayyuka ne kawai daga masu taqawa, wadanda suka yi aiki dominsa, domin samun yardarsa, ba wai domin haka suka ga mutane na yi, ba domin haka suka tashi suka ga a gidansu ana yi ba.

Suratul Bakara; Aya Ta 190-195 (Kashi Na 53)

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai.

Assalamu alaikum jama’a masu saurare, barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda, a yau shirin namu zai fara ne da yin dubi a cikin wannan aya mai albarka, a cikin suratul Baqarah, aya ta ta 190.

Aya ta ( 190 ) Baqarah

وَقَاتِلُواْ فِي سَبِيلِ اللّهِ الَّذِينَ يُقَاتِلُونَكُمْ وَلاَ تَعْتَدُواْ إِنَّ اللّهَ لاَ يُحِبِّ الْمُعْتَدِينَ

Kuma ku yãki wadanda suke yãkinku, a cikin hanyar Allah, kuma kada ku yi tsõkana, lalle ne Allah bã Ya son mãsu tsõkana.

Kare kai daga harin makiya daya ne daga cikin hakkokin mutum, amma kur’ani mai tsarki duk da karfafawar da ya yi wajen kare kai, ya jaddada wajabci kan kada a wuce iyaka wajen kare kai. Haka nan kuma kur’ani ya nusar da mu cewa, kafin yin kira ga makiya addinin musulunci zuwa ga addinin Allah, kada a dauki takobi a kansu, kada a fara yaki da su, a lokacin yaki kuma kada a taba kanan yara da mata da tsoffi,kare hakkokin dan adam a lokacin yaki, sai dai wanda ya yi shishigi a kan musulmi ne kawai za a yaka. A cikin wannan aya mai albarka za mu koyi cewa: 1- Dole ne yaki ya kasance an yi a tafarkin Allah, saboda Allah, ba domin kabilanci ko abin da ya yi kama da haka ba. 2- A mahangar musulunci kiyaye hakkoki da yin adalci wajibi ne koda a cikin yaki ne, musulunci ya hana wuce gona da iri.

Aya ta (191) da (192)

وَاقْتُلُوهُمْ حَيْثُ ثَقِفْتُمُوهُمْ وَأَخْرِجُوهُم مِّنْ حَيْثُ أَخْرَجُوكُمْ وَالْفِتْنَةُ أَشَدُّ مِنَ الْقَتْلِ وَلاَ تُقَاتِلُوهُمْ عِندَ الْمَسْجِدِ الْحَرَامِ حَتَّى يُقَاتِلُوكُمْ فِيهِ فَإِن قَاتَلُوكُمْ فَاقْتُلُوهُمْ كَذَلِكَ جَزَاء الْكَافِرِينَ{191} فَإِنِ انتَهَوْاْ فَإِنَّ اللّهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ{192}

Kuma ku yãke su inda kuka sãme su, kuma ku fitar da su daga inda suka fitar da ku. Kuma fitina ita ce mafi tsanani daga kisa. Kuma kada ku yãke su a wurin Masallãci Tsararre (Hurumin Makka) fãce fa idan sun yãke ku a cikinsa. To, idan sun yãke ku, sai ku yãke su. Kamar wancan ne sakamakon kãfirai yake. Sa'an nan idan sun hanu, to, lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin kai.

Wadannan ayoyi suna umurtar musulmi da su mayar kwatankwacin abin da mushrikan makka suka yi a kansu, domin kuwa sun fitar da musulmi daga gidajensu da kuma birnin, sun mayar da su ‘yan gudun hijira, sun saka musulmi cikin azaba ta fitina, inda Allah ya bayyana wannan fitar da aka jefa musulmi a cikinta da cewa tafi yaki tsanani. Ko da yake Allah madaukakin sarki ya ce da musulmi kada su yaki mushrikai a dakin ka’aba saboda alfarmar wannan wuri mai tsarki, sai dai idan mushrikan ne suka fara yakar musulmi a cikinsa, idan kuwa har suka kai hari kan musulmi a masallaci mai alfarma, Allah madaukakin sarki ya ba musulmi damar su kare kansu ta hanyar yakar kafirai mushrikai, domin kuwa a wannan lokacin musulmi suna matsayin masu kariyar kai ne, ba masu kai harin yaki ba. Abubuwan da za mu koya a cikin wannan ayar: 1- A yi amfanin dukknin hanyoyi da makiya suke yin amfani da su wajen cutar da musulunci da musulmi, domin a mayar da kwatankwacin aikinsu a kansu. 2- Dakin Allah yana da alfarma da aka hana yaki a cikinsa, amma saboda alfarmar jinin mumini Allah ya halasta a yaki kafirai a cikinsa matukar dai suka yaki muminai a cikinsa. 3- Sakawa da kwatankwaci a kan makiya ba tare da wuce goda da iri ba, daya ne daga cikin hanyoyin da musulunci ya koyar da mabiyansa.

Aya ta ( 193 ) Baqarah

وَقَاتِلُوهُمْ حَتَّى لاَ تَكُونَ فِتْنَةٌ وَيَكُونَ الدِّينُ لِلّهِ فَإِنِ انتَهَواْ فَلاَ عُدْوَانَ إِلاَّ عَلَى الظَّالِمِينَ

Kuma ku yãke su har ya zama wata fitina bã zã ta kasance ba, kuma addini ya zama na Allah. Sa'an nan idan sun hanu to bãbu tsõkana fãce a kan azzãlumai.

Manufar jihadi a musulunci ba ‘yan kasanci ko kabilanci ko wariya neman ganima ba ce, babbar manufar jihadi a musulunci ita ce tabbatar da kalmar Allah da fadarsa a bayan kasa, kawo karshen fitina da zalunci da shirka da kafirci da surkulle, du kuwa da cewa dukkanin yakokin da musulmi suka yi a lokacin ma’aiki, sun yi su ne domin kare kai daga masu cutar da muslunci da musulmi, an fara yakin ne a kan ma’aaki da mabiyansa, ba su ne suka fara yaki ba, domin kuwa sun dauki tsawon shekaru ana cutar da su ana yakar ba su ce komai illa isar da sakon Allah madaukakin sarki, tare da jurewa wahalwahu da azabtarwa saboda Allah, amma bayan hijirar manzo an yi wa wadanda suka yi imani izini da su yi yaki domin su kare kansu saboda zaluncin da ake yi musu ya kai matukarsa, to wannan shi ne jihadi a musulunci kamar yadda manzo ya koyar da musulmi. Abubuwan koyo daga wannan aya mai albarka: 1- Domin tattabar da adalci da kawar da zalunci da daukaka kalmar da kawar da azzaluman jagorori a cikin al’umma ne ake yin jihadi daidai da sharudda da aka shimfida kan haka a musulunci. 2- Kofar tuba da komawa zuwa ga Allah a bude take ga bayi baki daya, har da kafirai da ba su yi imani ba, idan suka dawo suka yi imani suka tuba suka daina cutar da musulmi, to Allah zai gafarta musu.

Aya ta ( 194 ) Baqarah

الشَّهْرُ الْحَرَامُ بِالشَّهْرِ الْحَرَامِ وَالْحُرُمَاتُ قِصَاصٌ فَمَنِ اعْتَدَى عَلَيْكُمْ فَاعْتَدُواْ عَلَيْهِ بِمِثْلِ مَا اعْتَدَى عَلَيْكُمْ وَاتَّقُواْ اللّهَ وَاعْلَمُواْ أَنَّ اللّهَ مَعَ الْمُتَّقِينَ

Watan alfarma da wani watan alfarma alfarmõmi mãsu dũkar jũna ne. Sabõda haka wanda ya yi tsõkana a kanku, sai ku yi tsokana a kansa da misãlin abin da ya yi tsõkana a kanku. Kuma ku bi Allah da takawa. Kuma ku sani cẽwa lalle ne, Allah Yana tãre da mãsu takawa.

A cikin addinin muslunci yaki a cikin watanni hudu haramun ne, wato watanni Rajab, Zul Ki’ida, Zul Hijja da kuma Muharram, mushrikai sun san cewa musulmi ba su da izinin yin yaki a cikin wadannan watanni, an kuma kulla yarjejeniya da su a cikin wadannan watanni babu yaki, saboda haka sai suka yi amfani da wannan damar domin shishigi kan musulmi, saboda sun san cewa dai ba za a rama ba, to amma Allah madaukakin sarki ya umurci musulmi da su mayar da kwatankwaci akan mushrikai, domin su kare kansu daga shishiginsu. Abubuwan da za mu koya daga wannan aya mai albarka: 1- Makiya suna neman damar da za su mami musulmi domin su cutar da su a kowane lokaci, ka da musulmi su ba su damar yin hakan. 2- Dole ne a rike alkawali da yarjejeniya matukar dai daya bangaren ba yana nufin yin amfani da wannan damar ne ba domin cimma wata bakar manufa. 3- Dole a kiyaye adalci da gaskiya koda kuwa a lokacin kwamawa ne da makiya.

Aya ta (195) Baqarah

وَأَنفِقُواْ فِي سَبِيلِ اللّهِ وَلاَ تُلْقُواْ بِأَيْدِيكُمْ إِلَى التَّهْلُكَةِ وَأَحْسِنُوَاْ إِنَّ اللّهَ يُحِبُّ الْمُحْسِنِينَ

Kuma ku ciyar a cikin hanyar Allah. Kuma kada ku jefa kanku da hannayenku, zuwa ga halaka. Kuma ku kyautata; lalle ne, Allah Yana son mãsu kyautatãwa.

Ayar da ta gabaci wannan tana bayani kan yakar mushrikai da kwatankwacin abin da suka yi kan muminai, amma a cikin wannan ayar za mu iya fahimta a fili cewa kowane irin yaki ne dole sai da kudade da za a yi amfani da su wajen bukatun mayaka, da kuma abin da yakin ke bukata na kudade, a kan haka ya rataya kan muminai su bayar da abin da ya sawaka na daga dukiyoyinsu. Amma lokacin sulhu da zaman lafiya, wato lokacin da ba cikin yaki ake ba, wajibi ne ma’abuta dukiyoyi su bayar da hakkin Allah na zakka da khumusi, domin yin aiki da su a tafarkin Allah da kuma taimakon raunana. Imam Ali (AS) yana cewa: ku kare dukiyoyinku ta hanyar fitar musu da zakka, wato lokacin da aka bayar da ahkkin Allah daga dukiya a lokacin ne za ta kara albarka da bunkasa. Abubuwan koyo daga wannan aya mai albarka: 1- A duk lokacin da rowa da boye dukiya suka yi yawa acikin al’umma, hakan zai jefa rayuwar wannan al’umma cikin mawuyacin hali, kuma Allah zai debe albarka a cikinta. 2- Duk wani aiki da zai cutar da ran wani mutum, tare da jefa shi cikin halaka haramun ne a addini, kuma wajibi ne a yi abin da zai hana afkuwar hakan.

Suratul Bakara; Aya Ta 196-199 (Kashi Na 54)

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai.

Assalamu alaikum masu saurare barkammu da sake saduwa cikin shirimmu na hannunka mai sanda shirin wanda ya nazari cikin wasu ayoyin al-kur’ani mai girma don su zama fitala a garemu cikin rayuwarmu. Da fatan masu saurare zasu kasance tare da mu a cikin wannan shirin.

A cikin ayoyin da suka gabata mun fara magana dangane da jihadi da kuma ciyarwa kan tafarkin Allah. Amma a cikin ayoyin da zamu yi nazarinsu a yau suna magana ne kan ayyukan Hajja. Muna rokon Allah ta’ala ya sanya mu cikin wadanda suke da rabon ziyarar dakinsa. Da farko bari mu fara sauraren aya ta 196 cikin surar bakara kamar haka:

وَأَتِمُّواْ الْحَجَّ وَالْعُمْرَةَ لِلّهِ فَإِنْ أُحْصِرْتُمْ فَمَا اسْتَيْسَرَ مِنَ الْهَدْيِ وَلاَ تَحْلِقُواْ رُؤُوسَكُمْ حَتَّى يَبْلُغَ الْهَدْيُ مَحِلَّهُ فَمَن كَانَ مِنكُم مَّرِيضاً أَوْ بِهِ أَذًى مِّن رَّأْسِهِ فَفِدْيَةٌ مِّن صِيَامٍ أَوْ صَدَقَةٍ أَوْ نُسُكٍ فَإِذَا أَمِنتُمْ فَمَن تَمَتَّعَ بِالْعُمْرَةِ إِلَى الْحَجِّ فَمَا اسْتَيْسَرَ مِنَ الْهَدْيِ فَمَن لَّمْ يَجِدْ فَصِيَامُ ثَلاثَةِ أَيَّامٍ فِي الْحَجِّ وَسَبْعَةٍ إِذَا رَجَعْتُمْ تِلْكَ عَشَرَةٌ كَامِلَةٌ ذَلِكَ لِمَن لَّمْ يَكُنْ أَهْلُهُ حَاضِرِي الْمَسْجِدِ الْحَرَامِ وَاتَّقُواْ اللّهَ وَاعْلَمُواْ أَنَّ اللّهَ شَدِيدُ الْعِقَابِ

Kuma ku cika hajji da umra dõmin Allah. To idan an kange ku, to, ku bãyar da abin da ya saukaka na hadaya. Kuma kada ku aske kãnunku, sai hadaya ta kai wurinta. To, wanda ya kasance majinyaci daga cikinku, kõ kuwa akwai wata cũta daga kansa (ya yi aski) sai fansa (fidiya) daga azumi ko kuwa sadaka ko kuwa yanka. To, idan kuna cikin aminci to, wanda ya ji dãdi da umra zuwa haji, sai ya biya abin da ya saukaka daga hadaya, sa'an nan wanda bai sãmu ba, sai azumin yini uku a cikin haji da bakwai idan kun kõma, wadancan gõma ne cikakku. Wancan yana ga wanda iyãlinsa ba su kasance mazaunan Masallãci Tsararre ba. Kuma ku bi Allah da takawa. Kuma ku sani cewa Allah Mai tsananin ukũba ne.

Kamar yadda kuka sani Annabi Ibrahim (a ) shi ne ya assasa ayyukan hajji, sannan ko bayansa ma larabawa sun ci gaba da ibada ta Hajji. Kuma addinin musulunci ya zo ya tabbatar da ayyukan hajji. Ya wajabtawa ko wani musulmi baligi ya ji aikin hajji akalla sau daya a rayuwansa idan ya shika sharuddan da ake bukata na wajibcin aikin. Sannan shi Umra kuma yana zama wajibi ne ga wanda ya shiga birnin Makka. Dole ne ya yi dawafin dakin ka’aba sannan ya bishi da sallar raka’o’i biyu. Domin gabatar da ayyukan hajji da Umra Allah ya sassautawa wadanda suke fadawa cikin matsaloli a cikin wannan tafiyar ta ibada. Don musulunci baya dorawa mutum abinda ba zai iya ba. Don haka daga cikin wannan ayar muna iya fahintar cewa idon mai hajji ko umra ya kasa yin wasu ayyuka an bashi zabin na azumi, bada sadaka ko kuma yanka, ko kuma dai kosar da wasu miskinai gorgodon irin ayyukan da ya kasa kawo su ko kuma yanayinsa na tattalin arziki.

A yanzu kuma bari mu saurari aya ta 197 daga cikin surara bakara.

الْحَجُّ أَشْهُرٌ مَّعْلُومَاتٌ فَمَن فَرَضَ فِيهِنَّ الْحَجَّ فَلاَ رَفَثَ وَلاَ فُسُوقَ وَلاَ جِدَالَ فِي الْحَجِّ وَمَا تَفْعَلُواْ مِنْ خَيْرٍ يَعْلَمْهُ اللّهُ وَتَزَوَّدُواْ فَإِنَّ خَيْرَ الزَّادِ التَّقْوَى وَاتَّقُونِ يَا أُوْلِي الأَلْبَابِ

Hajji watanni ne sanannu. To, wanda ya yi niyyar hajji a cikinsu to bãbu jimã'i kuma bãbu fãsikanci, kuma bãbu jãyayya a cikin hajji. Kuma abin da kuka aikata daga alhẽri, Allah Ya san shi. Kuma ku yi guzuri. To, mafi alhẽrin guzuri yin takawa. Kuma ku bi Ni da takawa, ya ma'abuta hankula

Ayyukan Hajji sau guda ne ake gabatar da su a ko wace shekara. Kuma a cikin lokaci kebantacce. Duka wanda ya yi anniyar zuwa aikin hajji dole ne tun da farko wa fara tsarakake kansa da kuma shiri na ayyukan alkhairi a cikin wannan tafiyar ta neman kusanci ga mahaliccinsa. Don haka garin Makka gari ne wanda yaka kasance cibiyar aminci da hadin kai tsakanin musulmi da kuma bautar Allah. Don haka ne aka bukaci mahajjaci da ya nisanci jayayya da jidali a lokacin Hajji. Ya nisanci wasu ayyuka na jin dadin rayuwa kamar kusantar mata da sauransu. Wanda hakan zai share masa fage na samun kusancin da ubangiji da ake buakata a cikin wannan aikin na ibada mai tsarki da alfarma.

Yanzu kuma mu saurari ayoyi na 198 da kuma 199 kamar haka.

لَيْسَ عَلَيْكُمْ جُنَاحٌ أَن تَبْتَغُواْ فَضْلاً مِّن رَّبِّكُمْ فَإِذَا أَفَضْتُم مِّنْ عَرَفَاتٍ فَاذْكُرُواْ اللّهَ عِندَ الْمَشْعَرِ الْحَرَامِ وَاذْكُرُوهُ كَمَا هَدَاكُمْ وَإِن كُنتُم مِّن قَبْلِهِ لَمِنَ الضَّآلِّينَ{198} ثُمَّ أَفِيضُواْ مِنْ حَيْثُ أَفَاضَ النَّاسُ وَاسْتَغْفِرُواْ اللّهَ إِنَّ اللّهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ{199}

-Bãbu laifi a kanku ga ku nẽmi falala daga Ubangijinku. Sa'an nan idan kun malãlo daga Arafãt, sai ku yi ta ambatar Allah a wurin Mash'aril Harãmi kuma ku tuna Shi kamar shiriyar da Ya yi muku kuma lalle ne kun kasance a gabãninsa, hakĩka, daga batattu. -Sa'an nan kuma ku malãlo daga inda mutãne suke malalowa. Kuma ku nemi gafara ga Allah. Lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin kai.

Mun ji a cikin ayar da ta gabata cewa yi ayyuka wadanda zasu kawo rashin aminci da rarraba kan musulmi a cikin ayyukan Hajji ya haramta. Amma a cikin wannan ayar musulunci ya warware wasu aqidun laraban jahiliyya wadanda suka haramta hatta mu’amala da kasuwanci a lokacin ayyukan hajji. Musulunci ya halatta mu’amala ta kasuwanci a lokacin ayyukan hajji. Sanna a lokacinda ya ambaci tsayuwan arfa da kuma tafiya zuwa ga masha’aril haram, Allah ya bukaci muminai da su tuna Allah da rahamarsa da kuma yadda ya fitar da su daga hanyar bata zuwa hanyar gaskiya, kuma su gudanar da ayyukansu a tare da sauran musulmi ba tare da nuna wariya ma. Daga karshe muna iya daukan darussa cikin wadan nan ayoyi kamar haka. 1) Musulunci addini ne wanda ya tattara kome, hatta a cikin ayyukan ibada na hajji bai manta da rayuwar tattalin arziki na musulmi ba. 2) Sanna kamar yadda musulmi yake neman samun kusanci ga Allah a cikin wannan aikin ibada to kada ya manta da neman arzikin duniya ma. Sai dai ya kasance cikin tunanin Ubangijinsa a ko da yauce. 3) A cikin ayyukan hajji babu fifiko a cikin mutane. Dole ne a aiwatar da wadan nan ayyuka na hajji tare. Da wanda yake balarabe a makka da wanda ya zo daga waje daya suke. Daga karshe muna rokon Allah ta’ala ya yi mana muwafaka cikin sanin dokokinsa da kuma binsu yadda suke ba tare da wata tawaya ba. Kafin wani shirin Tahir Amin yake cewa mu huta lafiya. Wassalamu alaikum.

Suratul Bakara; Aya Ta 200-205 (Kashi Na 55)

Assalamu alaikum masu saurare barkammu da sake saduwa cikin shirimmu na hannunka mai sanda shirin wanda ya nazari cikin wasu ayoyin al-kur’ani mai girma don su zama fitala a garemu cikin rayuwarmu. Da fatan masu saurare zasu kasance tare da mu a cikin wannan shirin.

A cikin shirin da ya gabata mun fara maganar ayyukan Hajji da hukunce hukuncen sa. Da yar dar Allah a cikin shirimmu na yau zamu ci gaba da magana kansa kuma zamu kammalashi a shirin na yau idan Allah ya yarda. Da farko bari mu saurari karatun ayoyi na 200 zuwa 2002 daga cikin bakara kamar haka:

فَإِذَا قَضَيْتُم مَّنَاسِكَكُمْ فَاذْكُرُواْ اللّهَ كَذِكْرِكُمْ آبَاءكُمْ أَوْ أَشَدَّ ذِكْراً فَمِنَ النَّاسِ مَن يَقُولُ رَبَّنَا آتِنَا فِي الدُّنْيَا وَمَا لَهُ فِي الآخِرَةِ مِنْ خَلاَقٍ{200} وِمِنْهُم مَّن يَقُولُ رَبَّنَا آتِنَا فِي الدُّنْيَا حَسَنَةً وَفِي الآخِرَةِ حَسَنَةً وَقِنَا عَذَابَ النَّارِ{201} أُولَـئِكَ لَهُمْ نَصِيبٌ مِّمَّا كَسَبُواْ وَاللّهُ سَرِيعُ الْحِسَابِ{202}

-To, idan kun kãre ayyukan hajji, sai ku ambaci Allah kamar ambatarku ga ubanninku, kõ kuwa mafi tsanani ga ambato. To, daga cikin mutãne akwai wanda yake cẽwa: "Ya Ubangjinmu! Ka bã mu a cikin dũniya! Kuma bã ya da wani rabo a cikin Lãhira. -Kuma daga gare su akwai wanda yake cẽwa: "Yã Ubangijinmu! Ka bã mu mai kyau a cikin dũniya da mai kyau a cikin Lãhira, kuma Ka tsare mana azãbar Wuta!" -Wadannan suna da rabo daga abin da suka sanã'anta; kuma Allah Mai gaggãwar sakamako da yawa ne.

Kafin bayyanar musulunci bayan kammala ayyukan Hajji kabilun larabawa sukan yi gangami a wani wuri inda ko wace kabila ko dange suke bayyana daraja da martaban kabilansu suna alfahiri da ita suna mabatob manya manyan mutanenta. Don haka a cikin wadan nan ayayi Alla ya umurci mahajjata idon sun kammala ayyukansu na hajji su mai makon su yi abinda suka saba a jihiliyya su ambaci Allah mai yawa su tuna da ni’imomin da ya yi masu sannan su roke shi karin falala a cikin yelwarsa. Dana nan sai Alkur’ani mai girma ya bayyana cewa a lokacin, bayan kammala ayyukan Hajja mutane sun kasu kashi biyi-akwai wadanda suke tunanin abin duniya kadai da bukatunsu na jin dadin duniya. Su basa neman wani abu a wajen Allah in banda wadan nan abubuwa. Amma kashi na biyu sune wadanda suke neman duniya wacce ta kasance wasilace ta samun lahira, sannan suna neman lahiri wanda shi ne makomarsu ta karshe. Daga karshe a cikin wannan ayar muna iya daukan darisa kamar haka; 1) A lokacinda muke adu’a muke tunawa da Ubangijimmu kada mu nemi duniya kadai wacce zata wuce nan da nan kadai ba, mu rokeshi lahari tare da duniya don lahira ne makomanmu na karshe. 2) Addinin musulunci ya na himmatuwa da duniya da kuma lahiran musulmi a lokaci guda, ya tanadi hanyar kyautata rayuwarsu a cikin duniya da lahira. 3) Idan muna rokon Allah mu nemi alkhairi da sa’ada ta duniya da lahira, kada mu takaita bukatarmu da wani sashe mu bar wani. Don bamu san abinda yake gabammu ba na alkhairi da sharri.

Yanzu mu saurari aya ta 203 daga cikin sura ta bakara kamar haka.

وَاذْكُرُواْ اللّهَ فِي أَيَّامٍ مَّعْدُودَاتٍ فَمَن تَعَجَّلَ فِي يَوْمَيْنِ فَلاَ إِثْمَ عَلَيْهِ وَمَن تَأَخَّرَ فَلا إِثْمَ عَلَيْهِ لِمَنِ اتَّقَى وَاتَّقُواْ اللّهَ وَاعْلَمُوا أَنَّكُمْ إِلَيْهِ تُحْشَرُونَ

-Kuma ku ambaci Allah a cikin kwanuka kidayayyu. To, wanda ya yi gaggawa a cikin kwana biyu, to, bãbu laifi a kansa, kuma wanda ya jinkirta, to, bãbu laifi a kansa, ga wanda ya yi takawa. Kuma ku bi Allah da takawa, kuma ku sani cewa lalle ne kũ, zuwa gare Shi ake tãrã ku.

A cikin ayoyin da suka gabata an ambaci yadda kafin musulunci larabwa suke tarurruka bayan hajja don ambatun iyaye da kakanni da kuma alfakhari da su. Awannan ayar alkur’ani mai girma ya bayyana abubuwan da yakamata mahajjaci ya yi a ranakun 10,11,12 da 13 bayan kammala ayyukan hajji a mina. Amabton Allah mai yawa da kuma tunani cikin ayoyin Allah na daga cikin muhimman abubuwan da yakamata mahajjaci yawaitsu a wancan lokacin. Don haka daga cikin wannan ayar muna iya fahintar cewa, idan mutum mai tsoron Allah ne, yana sawwake masa lamuransa. Kuma yana karban ayyukansa ya gafarta masa kurakuran da yake yi a cikinsu, ya boye nakasa da ke cikinsu.

A halin yanzu mu saurari aya ta 204 kamar haka.

وَمِنَ النَّاسِ مَن يُعْجِبُكَ قَوْلُهُ فِي الْحَيَاةِ الدُّنْيَا وَيُشْهِدُ اللّهَ عَلَى مَا فِي قَلْبِهِ وَهُوَ أَلَدُّ الْخِصَامِ

Kuma akwai daga mutãne wanda maganarsa tana bã ka sha'awa a cikin rãyuwar dũniya, alhãli yanã shaidar da Allah a kan abin da yake cikin zuciyarsa, kuma shi mai tsananin husũma ne.

Wanna ayar tana ishara da munafurcin wasu munafukai. Wadanda idan muminai sun ji maganganunsu zasu dauke su a matsayin wani ne daga cikinsu. Amma Allah ya san abinda yake cikin zuciyarsu na munafurci da kuma kiyayya ga mumini. Don haka anan Alkur’an yana gargadi ga muminai cewa kada ku dauke cewa duk wanda ya bayyana cewa yan tare da ku gaskiya ne yana tare da ku ba, wasu daga cikinsu suna matukar adawa daku cikin zukatansu.

Sai kuma mu saurari aya ta 205 kamar haka.

وَإِذَا تَوَلَّى سَعَى فِي الأَرْضِ لِيُفْسِدَ فِيِهَا وَيُهْلِكَ الْحَرْثَ وَالنَّسْلَ وَاللّهُ لاَ يُحِبُّ الفَسَادَ

-Kuma idan ya jũya sai ya yi gaggawa a cikin kasa dõmin ya yi barna a cikinta, kuma ya halaka shũka da 'ya'yan dabbõbi. Kuma Allah bã Ya son barna.

Wadan nan mutane wadanda suke bayyana maganganu masu kyau, suna ta yin alkawalin cewa idan sun sami hali zasu kwautata halin rayuwar mutane zasu kyautata bangarorin rayuwar mutane daban daban. Amma da zaran sun kai ga manufofinsu sai kaga cewa sun fara barna a bayan kasa, suna lalata tsarin tattalin arzikin mutane suna lalata rayuwan matasa suna janyesu zuwa hanyoyin bata da lalacewa. A wata ayar kur’anin yana mana bayanin salihan bayi idan sun karbi iko da kasa suna tsaida sallah wacce take mahadar mutum da ubangijinsa, wato zasu kyautata dangartakan mutane da Allah ta hanyar tsaida sallah cikin mutane da kuma bada zakka, wanda zai zama gyara ne ga rayuwar talakawa da kuma kyautata yanayinsu na tattalin arziki. Sabanin su munafukai wadanda suka boye munafurci suka bayyana imani. Ga wasu muhimman abubuwan da zamu iya dauka a cikin wadan nan ayoyin da muka karanta. 1) Idan muna mu’amala da musulmi ba zancensu kadai zamu lura da su ba, mu lura da ayyukansu shin suna kyautata rayuwar mutane ne ko kuma suna yada fasadi a bayan kasa. Daga karshe muna rokon Allah ya sanya mu cikin wadanda abinda yake cikin zukatansu da harussansu na imani su ne suke aiwatarwa a bayyana.. Da wannan kuma muka kawo karshen shirimmu na yau wassalamu alaikum warahmatullah.

Suratul Bakara; Aya Ta 206-210 (Kashi Na 56)

Assalamu alaikum masu saurare barkammu da sake saduwa cikin shirimmu na hannunka mai sanda shirin wanda ya nazari cikin wasu ayoyin al-kur’ani mai girma don su zama fitala a garemu cikin rayuwarmu. Da fatan masu saurare zasu kasance tare da mu a cikin wannan shirin.

      • .

A cikin shirimmu na yau zamu fara sauraron ayoyi na 206 da kuma 207 daga cikin sarar bakara kamar haka;

وَإِذَا قِيلَ لَهُ اتَّقِ اللّهَ أَخَذَتْهُ الْعِزَّةُ بِالإِثْمِ فَحَسْبُهُ جَهَنَّمُ وَلَبِئْسَ الْمِهَادُ{206} وَمِنَ النَّاسِ مَن يَشْرِي نَفْسَهُ ابْتِغَاء مَرْضَاتِ اللّهِ وَاللّهُ رَؤُوفٌ بِالْعِبَادِ

-Kuma idan an ce masa: "Ka ji tsõron Allah," sai girman kai da yin zunubi ya dauke shi To abin da yake mai isarsa Jahannama ce. Kuma hakĩka, shimfida tã munana. Kuma akwai daga mutãne wanda yake sayar da ransa, dõmin nẽman yardar Allah: KumaAllah Mai tausayi ga bãyi.

A cikin ayoyin da suka gabata alkur’ani ya yi maganar munafukai wadanda suke yada fasadi a bayan kasa idan sun sami iko. A cikin ayata 206 ma yana kara bayyana halayensu na girman kai a lokacinda aka tunatarda su Allah. Aka kirasu da dakatar da fasadi a bayan kasa, ba wai kawai basa karban nasiha ba, sai ma su kara dulmuyawa cikin yada barna da fasa. Sannan banda wadan nan akwai kuma muminai wadanda, ba wai kyautata rayuwa da kuma shafe barna kawai suke yi a bayan kasa ba, sai dai suna saida ransu don neman yardar ubangijinsu. Suna bada mafi daraja na abinda suka mallaka don neman amincewar ubangijinsu. Malaman tafsiri na dama sun kawo cewa a daren da mushrikan makka suka tsaida shawara kasashe manzon Allah (s ) don su kawo karshen addininsa, sai Allah ya sanarda shi makirsu kuma ya umurce shi da yin hijira. Amma don kada mushrikai su gano fitarsa sai Aliyu bin Abitalib ( a) ya kwanta a shimfidarsa don su zaci cewa yana nan. A sannan ne wannan ayar ta 207 ta sauka, kuma daren ya zama dare mai muhimmanci, daren da aka bashi suna “lailatul mabit” wato daren da Aliyu ya kwanta a shimfadar manzon Allah ( s) don bashi damar yin hijira ba tare da mushrikai sun sani ba. Daga cikin wadannan ayayoyi muna iya fahintar cewa; 1) Girman kai na daga cikin abubuwan da ke kara nisantar da mutum daga ayyukan alkhairi, kuma ya kara dulmuyashi cikin sabon Allah. Ya hana shi karban gaskiya. 2) Mumini yana mu’amala da Allah ne don haka a ko yauce yana neman yardarsa ne a yayinda munafuki kuma yana mu’amala da duniya, a ko auce yana neman yardar mutane.

Yanzu kuma sai mu saurari ayoyi na 208 zuwa 209 daga cikin surar bakara kamar haka.

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُواْ ادْخُلُواْ فِي السِّلْمِ كَآفَّةً وَلاَ تَتَّبِعُواْ خُطُوَاتِ الشَّيْطَانِ إِنَّهُ لَكُمْ عَدُوٌّ مُّبِينٌ{208} فَإِن زَلَلْتُمْ مِّن بَعْدِ مَا جَاءتْكُمُ الْبَيِّنَاتُ فَاعْلَمُواْ أَنَّ اللّهَ عَزِيزٌ حَكِيمٌ{209}

208-Yã ku wadanda suka yi ĩmani! Ku shiga cikin Musulunci gabã daya; kuma kada ku bi zambiyõyin Shaidan; lalle ne shĩ a gare ku makiyine, bayyananne. 209-To, idan kun karkace daga bayan hujjõji bayyanannu sun zo muku to ku sani cẽwa lalle ne Allah, Mabuwãyi ne, Mai hikima.

Wadan nan ayoyi suna kira ga muminai su kasance masu zaman lafiya a tsakaninsu da kuma mika kai ga dokokin Allah, su nisanci jayayya da sabani don sune makaman da shaitan yake amfani da su don samar da rarraba a tsaknainsu. A wajen Allah, kabila, launin fata, jinsin mace ko namiji, dukiya da suransu duk basu da kima. Ibinda yake da kima a wajen ubangiji shi ne tsoron Allah. Kuma imani ne da Allah da mika kai ga dokoinsa sune suke iya hada kan mutane karkashin tuta guda. Don hake, kamar yadda mutum mai hankali zai fahinta da kuma yadda ya zo cikin alkur’ani duk abinda zai kawo rarraba tsakanin musulmi ya rikita lamarinsu to aikin shaitan ne. Daga cikin wadan nan ayoyi muna iya fahintar cewa : 1) Sulhu da zaman lafiya na samuwa ne kadai a karkashin inuwar imani da Allah. A karkashin bin umurni da dokokin ubangiji. Wanin wannan bai isa ya samar da zaman lafiya a duniya ba. 2) Shaitan mai adawa da hadin kai ne, don haka duk abinda yake kai ga rabuwan kai tsakanin musulmi aikin shaitan ne.

Yanzu kuma mu saurari karatun aya ta 210 daga cikin surar bakara kamar haka.

هَلْ يَنظُرُونَ إِلاَّ أَن يَأْتِيَهُمُ اللّهُ فِي ظُلَلٍ مِّنَ الْغَمَامِ وَالْمَلآئِكَةُ وَقُضِيَ الأَمْرُ وَإِلَى اللّهِ تُرْجَعُ الأمُورُ

210-Shin suna jira, fãce dai Allah Ya je musu a cikin wasu inuwõyi na girgije, da malã'iku, kuma an hukunta al'amarin? Kuma zuwa ga Allah al'amurra ake mayar da su.

Da dama daga cikin mutane suna bukatar ganin Allah da mala’iku, su ji maganarsu kafin su yi imani da su. Amma gaskiyan lamarin hakan ba mai yiyuwa bane. Don Allah da mala’ikunsa ba jikunkuna bane wadanda mutane ke iya sanya ido a kansu. Kuma Allah ya bawa mutum hankali kuma ya aiko da annabawa wadanda suka yi bayanai gamsassu ga mai buakta, to da wani dalili ne kuma wasu mutane suka dage sai sun ga Allah da Mala’iku kafin su yi imani?. Muna iya fahinta daga cikin wannan ayr cewa-ganin Allah da ido ba mai yuwa bane, kuma bai kamata mai hankali ya bukaci haka ba. Imani da sanin Allah suna samuwa ne ta hanyar hankali da kuma fahintar da ke cikin asalin halittar mutum (Fitra) ake samunsu. Daga karshe muna rokon Allah ya bamu damar amfani da baiwan da ya yi mana na hankali da kuma fahintar ayoyinsa don mu kasance masu imani na gaskiya. Kafin shirimmu na gaba wassalamu alaikum warahmatullah.

Suratul Bakara; Aya Ta 211-214 (Kashi Na 57)

Assalamu alaikum masu saurare barkammu da sake saduwa cikin shirimmu na hannunka mai sanda shirin wanda ya nazari cikin wasu ayoyin al-kur’ani mai girma don su zama fitala a garemu cikin rayuwarmu. Da fatan masu saurare zasu kasance tare da mu a cikin wannan shirin.

A cikin shirimmu na yau zamu karanta ayayo 211 zuwa 214 daga cikin surar bakara. Da fatan zamu amfana da darussan da suke cikin wadan nan ayoyi.

A halin yanzu bari mu fara da saurareron karatun aya ta 211 kamar haka:

سَلْ بَنِي إِسْرَائِيلَ كَمْ آتَيْنَاهُم مِّنْ آيَةٍ بَيِّنَةٍ وَمَن يُبَدِّلْ نِعْمَةَ اللّهِ مِن بَعْدِ مَا جَاءتْهُ فَإِنَّ اللّهَ شَدِيدُ الْعِقَابِ

Ka tambayi Banĩ Isrã'ila, da yawa Muka bã su daga ãyõyi bayyanannu. Kuma wanda ya musanya ni'imar Allah daga bãyan tã je masa, to, lalle ne Allah Mai tsananin ukũba ne.

Tarihi shi ne abin lura mafi muhimmanci ga mutum. Allah ta’ala ya nunawa bani-isra’ila ayoyi masu yawa, karkashin jagorancin Annabi Musa (a) kuma ya yi masu ni’imomi masu yawa. Da farko ya kubutar da su daga damkar Fir’auna, sannan ya kyautata rayuwarsu ta duniya, ya basu jagoranci irin na annabi musa (a) . Amma duk da wannan baiwa da Allah ya yi masu sun zabi kauce tafarkin Ubangijinsu sun zami sabawa Allah, sun yi amfani da ni’imomin da Allah ya yi masu ta hanyar sabamasa. Maimakon su bautawa Allah sun riki dan maraki abin bauta, maimakon sun saurari abinda annabawansu Annabi Musa da Haruna (a) suke fada masu, sun koma bin Samiri. Wannan rashin godiyarsu ya jawo masu fushin Allah da rashin yardarsa. Hatta a cikin rayuwarsu ta duniya Allah ya kaikantasu. Sannan hatta a cikin wannan zamanin namu, Allah ya huwace mana ni’imomi da dama, amma abin bakin ciki ana amfani da mafi yawan wadan nan ni’imomi wajen samon Allah da kuma yada fasadi da zalunci a bayan kasa. Yanzu kuma mu saurarin aya ta 212 cikin surar bakara kamar haka:

زُيِّنَ لِلَّذِينَ كَفَرُواْ الْحَيَاةُ الدُّنْيَا وَيَسْخَرُونَ مِنَ الَّذِينَ آمَنُواْ وَالَّذِينَ اتَّقَواْ فَوْقَهُمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ وَاللّهُ يَرْزُقُ مَن يَشَاءُ بِغَيْرِ حِسَابٍ

An kawata rãyuwar dũniya ga wadanda suka kãfirta, kuma suna izgili daga wadanda suka yi ĩmãni, alhãli wadanda suka yi takawa suna bisa gare su, a Rãnar ¡iyãma. Kuma Allah Yana azurta wanda Yake so, bã da lissãfi ba.

Ni’imomi da kawan duniya ya dauke hankalin wadanda basu yi amini da lahira ba. Wannan halin da suke ciki ya gadar masu da girman kai da rudu har ya sa suna wawaita muminai suna isgili da su. Amma gaskiyan lamarin mizanin daukaka da kuma fifiko sune imani da tsoron Allah wadanda zasu bayyana a ranar kiyama. A cikin wannan ayar muna iya fahintar cewa. 1) Son duniya yana gadar da girman kai da walakanta wasu mutane. 2) Son Allah da tsoronsa yana gadarda sa’ada ta duniya da lahira, da kuma saukar rahamar ubangiji.

Yanzu kuma bari mu saurari karatun aya ta 213 daga surar bakara kamar haka:

كَانَ النَّاسُ أُمَّةً وَاحِدَةً فَبَعَثَ اللّهُ النَّبِيِّينَ مُبَشِّرِينَ وَمُنذِرِينَ وَأَنزَلَ مَعَهُمُ الْكِتَابَ بِالْحَقِّ لِيَحْكُمَ بَيْنَ النَّاسِ فِيمَا اخْتَلَفُواْ فِيهِ وَمَا اخْتَلَفَ فِيهِ إِلاَّ الَّذِينَ أُوتُوهُ مِن بَعْدِ مَا جَاءتْهُمُ الْبَيِّنَاتُ بَغْياً بَيْنَهُمْ فَهَدَى اللّهُ الَّذِينَ آمَنُواْ لِمَا اخْتَلَفُواْ فِيهِ مِنَ الْحَقِّ بِإِذْنِهِ وَاللّهُ يَهْدِي مَن يَشَاءُ إِلَى صِرَاطٍ مُّسْتَقِيمٍ

Mutãne sun kasance al'umma guda. Sai Allah Ya aiki annabãwa suna mãsu bãyar da bishãra kuma mãsu gargadi; kuma Ya saukar da Littãfi da gaskiya tãre da su dõmin (Littãfin) ya yi hukunci a tsakãnin mutãnen a cikin abin da suka sãbã wa jũna a cikinsa. kuma bãbu wanda ya sãbã, a cikinsa, fãce wadanda aka bai wa shi daga bãyan hujjõji bayyanannu sun je musu dõmin zãlunci a tsakãninsu. Sai Allah Ya shiryar da wadanda suka yi ĩmani ga abin da suka sãbã a cikinsa daga gaskiya da izninSa. Kuma Allah Yana shiryar da wanda Yake so, zuwa ga hanya madaidaiciya.

Wannan ayar tana bayyana muhimmanci addini da dokokin ubangiji wajen shiryatar da dan adama da kuma rike hannunsa zuwa ga sa’ada ta duniya da lahiri. Farkon rayuwar mutum a duniya ta kasance irin rayuwar karkara rayuwar kaye, inda muatne yan kadan suke rayuwa. Amma bayan da mutane suka yawaita a duniya. Sai ya zama dole a samarda dokoki wadanda zasu tsara rayuwar mutane. Don haka sai Allah ya fara aiko da annabawa don isar da wadannan dokoki ga mutane dokoki wadanda zasu kyautata zamantakewa a tsakaninsu. Amma duk kokarin da wadannan annabawa suka yi cikin mutanensu don ganin wadannan dokoki sun tsaya suna tafiya a cikin al-ummunsu, sai dai akwai wadanda suka tsaya gaban tabbatar wadan nan dokoki. Sun ki karban da kuma yarda da dokokin. Muminai daga cikinsu ne kadai suka amince da dokokin da annabawa suka zo da su daga ubangijinsu. Don haka a cikin wannan halin mutane sun fada cikin sabani a tsakaninsu. Sabani tsakanin wadanda suka amince da umurnin da dokokin ubangiji da kuma wadanda suka kafirce suka bijire. Don haka muna iya daukan darasi daga cikin wannan ayar kamar haka: 1) Mutane suna bukatar dokoki wadanda zasu tsara rayuwansu ta duniya-kuma annabawa da shuwagabannin addini sune suka fi cancanta da shugabanci. 2) Mafificin hanyar warware sabanin da ke tasowa tsakanin mutane, sabanin tsakanin iayali guda ko kuma cikin al-umma shine biyayya ga dokokin ubangiji.

Yanzu kuma bari mu saurari aya ta 214 kamar haka:

أَمْ حَسِبْتُمْ أَن تَدْخُلُواْ الْجَنَّةَ وَلَمَّا يَأْتِكُم مَّثَلُ الَّذِينَ خَلَوْاْ مِن قَبْلِكُم مَّسَّتْهُمُ الْبَأْسَاء وَالضَّرَّاء وَزُلْزِلُواْ حَتَّى يَقُولَ الرَّسُولُ وَالَّذِينَ آمَنُواْ مَعَهُ مَتَى نَصْرُ اللّهِ أَلا إِنَّ نَصْرَ اللّهِ قَرِيبٌ

-Ko kuna zaton ku shiga Aljanna kuma tun misãlin wadanda suka shige daga gabãninku bai zo muku ba? Wahalõli da cũta sun shãfe su, kuma aka tsõratar da su har manzonsu da wadanda suka yi ĩmãni tãre da shi su ce: "Yaushe taimakon Allah zai zo?" To! Lalle ne, taimakon Allah yana kusa!

Ayan da ta zo kafin wannan ta bayyana muhimmancin imani da Allah da kuma shiryatarwar annabawansa wajen kauda sabani tsakanin mutane da kuma nisantar da su daga jayyaya. Amma wannan ayar tana bayyana cewa imani kadai bai isa ba-dole ne ayyukan mumini su tabbatar da imaninsa. Dole ne muminai su kiyaye imaninsu a cikin jarrabawa na wahalhali da musubu da zasu zo masu kan tafarin wannan imani. Darajar mumini da daukakarsa suna bayanna ne a cikin wannan jarrabawar. Muna iya daukar darussa daga cikin wannan ayar kamar haka. 1) Aljanna wanda Allah ya yi wa muminai alkawali bata samuwa sai da shiga jarrabawa masu tsanani a rayuwa ta duniya. 2) Jarrabawa a rayuwar duniya sunna ce ta Allah ga bayinsa gaba daya. Da shi ne yake bayyana matsayin ko wanne daga cikinsu. Daga karshen wannan shirin namu muna fatan zamu dauki darasi daga tarihi, mu godewa Allah cikin ni’imomin da ya yi mana a rayuwarmu ta duniya. Sannan mu yi hakura da dauriya cikin wahalhalu da musuibun da zasu same mu a cikin tafarkin biyayya ga annabawan Allah. Kuma mu yi tawakkali ga Allah kan wannan tafarkin. Masu saurare lokaci ya riskemu a nan zamu dakata sai kuma wani lokaci idan Allah ya kai mu wassalamu alaikum wa rahmatullahi wabarkatuhi.

Suratul Bakara; Aya Ta 215-218 (Kashi Na 58)

Assalamu alaikum masu saurare barkammu da sake saduwa cikin shirimmu na hannunka mai sanda shirin wanda ya nazari cikin wasu ayoyin al-kur’ani mai girma don su zama fitala a garemu cikin rayuwarmu. Da fatan masu saurare zasu kasance tare da mu a cikin wannan shirin.

Zamu bude shirimmu na yau da karatun aya ya 215 daga cikin surar bakara kamar haka:

يَسْأَلُونَكَ مَاذَا يُنفِقُونَ قُلْ مَا أَنفَقْتُم مِّنْ خَيْرٍ فَلِلْوَالِدَيْنِ وَالأَقْرَبِينَ وَالْيَتَامَى وَالْمَسَاكِينِ وَابْنِ السَّبِيلِ وَمَا تَفْعَلُواْ مِنْ خَيْرٍ فَإِنَّ اللّهَ بِهِ عَلِيم

-Suna tambayar ka mẽne nezã su ciyar. Ka ce: Abin da kuka ciyar daga alhẽri sai ga mahaifa da mafi kusantar dangantaka da marãyu da matalauta da dan hanya. Kuma abin da kuka aikata daga alhẽri, to, lalle ne, Allah gare shi Masani ne.

Daya daga cikin alamun imani shi ne taimakon mabukata, kamar yadda ayoyin alkur’ani da dama suka yi ishara da shi. Don haka ne ma musulman farko suka nemi karin bayani wajen manzon Allah (s ) suna tambayarsa irin abinda yakamata su bada taimako ga masu bukata, kuma ga wa yakamata su bayar. Anan Allah ya basu amsa da cewa, nauyi da kuma yawan abinda yakamata ku bada atimako bai da muhimmanci. Abinda ake bukata kowa ya bada abinda zai iya amma mai amfani ga wadanda za’a bawan. Sannan iyaye da dangi na kusa da kuma dukkan mabukata cikin musulmi sune wadanda suka cancanci taimakonku. Wani abu da yakamata ku sani shi ne cewa ku yi matukar kokari wajen boye taimakon da kuke bayarwa don Allah yana sane da duk abinda kuka aikata na alkhairi. Daga cikin wannan ayar muna iya fahintar abubuwa kamar haka. 1) A cikin taimakon mabukata yakamata a gabatar da iyaye da kuma dangi na kusa kafin sauran musulmi. 2) Ayyukan alkhairi ba zasu taba bacewa ba a bayyane aka yi shi ko a boye.

Yanzu kuma mu saurari karatun aya ta 216 na cikin surar ta bakara kamar haka:

يَسْأَلُونَكَ عَنِ الشَّهْرِ الْحَرَامِ قِتَالٍ فِيهِ قُلْ قِتَالٌ فِيهِ كَبِيرٌ وَصَدٌّ عَن سَبِيلِ اللّهِ وَكُفْرٌ بِهِ وَالْمَسْجِدِ الْحَرَامِ وَإِخْرَاجُ أَهْلِهِ مِنْهُ أَكْبَرُ عِندَ اللّهِ وَالْفِتْنَةُ أَكْبَرُ مِنَ الْقَتْلِ وَلاَ يَزَالُونَ يُقَاتِلُونَكُمْ حَتَّىَ يَرُدُّوكُمْ عَن دِينِكُمْ إِنِ اسْتَطَاعُواْ وَمَن يَرْتَدِدْ مِنكُمْ عَن دِينِهِ فَيَمُتْ وَهُوَ كَافِرٌ فَأُوْلَـئِكَ حَبِطَتْ أَعْمَالُهُمْ فِي الدُّنْيَا وَالآخِرَةِ وَأُوْلَـئِكَ أَصْحَابُ النَّارِ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ

An wajabta yãki a kanku, alhãli kuwa shi abin ki ne a gare ku, akwai fãtar cẽwa ku ki wani abu, alhãli shi ne mafi alhẽri a gare ku, kumaakwai fãtar cẽwa kuna son wani abu alhãli kuwa shi ne mafi sharri a gare ku. Kuma Allah ne Yake sani, kuma kũ ba ku sani ba.

Domin kare addini Allah ya wajabta jihadi kan muminai, amma dabi’ar mutum ne yana son hutu da nishadi. Baya son yaki wanda yake kaiwa ga mutuwa ko rauni ko kuma tawaya cikin dukiya da sauran abin ki dake cikin yaki da jihadi. Wannan ayar tana nuna mana cewa duk da yake akwai wahala da cutarwa cikin jahdi da yaki da makiya addini, amma Allah ya sanya alkairin duniya da lahira a cikinsa. Don haka kada ku biyewa abinda ranku yake so ko yake ki a abinda ya shafi umurnin Allah. Kada ku zama kamar karamin yaro wanda baya son ayi masa allura don gudun zafinsa, duk da cewa lafiyansa da rayuwarsa duk suna tare da yi masa alluran ne. Don haka yakamata ku gane cewa ba duk abinda kuke daukansa alkhairi ne alkjairin ba, kamar yadda ba dukkan abinda kuke ganin sa cuta ce mai cutarwa ba. A cikin wannan ayar muna iya daukan darussa kamar haka: 1) Mizanin gano alkhairi da sharri na tattare da umurni da hanin Allah ne, wadanda ya sanyasu da nufin kai mutum ga sa’adar duniya da lahira. Fahintar mutum bai kai ga fahintar wannan ba. 2) Ilmin dan adam takaitacce ne, a yayinda ilmin Allah bai da iyaka. Abin bukata shi ne mu mika wuya ga umurni da hanin Allah. Duk da cewa hankalimmu baya iya fahintar maslahar da ke cikin wasu dokokin ba, ko kuma aiwatar da su yana da matukar wahala.

Yanzu kuma mu saurari karatun aya ta 217 da kuma aya ta 218 daga cikin sura ta bakara kamar haka:

يَسْأَلُونَكَ عَنِ الشَّهْرِ الْحَرَامِ قِتَالٍ فِيهِ قُلْ قِتَالٌ فِيهِ كَبِيرٌ وَصَدٌّ عَن سَبِيلِ اللّهِ وَكُفْرٌ بِهِ وَالْمَسْجِدِ الْحَرَامِ وَإِخْرَاجُ أَهْلِهِ مِنْهُ أَكْبَرُ عِندَ اللّهِ وَالْفِتْنَةُ أَكْبَرُ مِنَ الْقَتْلِ وَلاَ يَزَالُونَ يُقَاتِلُونَكُمْ حَتَّىَ يَرُدُّوكُمْ عَن دِينِكُمْ إِنِ اسْتَطَاعُواْ وَمَن يَرْتَدِدْ مِنكُمْ عَن دِينِهِ فَيَمُتْ وَهُوَ كَافِرٌ فَأُوْلَـئِكَ حَبِطَتْ أَعْمَالُهُمْ فِي الدُّنْيَا وَالآخِرَةِ وَأُوْلَـئِكَ أَصْحَابُ النَّارِ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ{217} إِنَّ الَّذِينَ آمَنُواْ وَالَّذِينَ هَاجَرُواْ وَجَاهَدُواْ فِي سَبِيلِ اللّهِ أُوْلَـئِكَ يَرْجُونَ رَحْمَتَ اللّهِ وَاللّهُ غَفُورٌ رَّحِيمٌ{218}

-Suna tambayar ka game da Watan Alfarma: yin yãki a cikinsa. Ka ce: "Yin yãki a cikinsa babban zunubi ne, kuma hani daga hanyar Allah, da kuma kãfirci da Shi, da kuma da Masallaci Tsararre, da Kuma fitar da mutãnensa daga gare shi, shi ne mafi girman zunubi a wurin Allah." Kuma fitina ita ce mafi girma daga kisa. Kuma bã su gushẽwa suna yãkinku har su mayar da ku daga barin addininku idan za su iya. Kuma wanda ya yi ridda daga gare ku ga barin addininsa har ya mutu alhãli kuwa yana kãfiri, to, wadannan ayyukansu sun bãci a cikin dũniya da Lãhira. Kuma wadannan abõkan Wuta ne, sũ a cikinta madawwama ne. -Lalle ne wadanda suka yi ĩmãni, da wadanda suka yi hijira kuma suka yi jihãdi a cikin hanyar Allah wadannan suna fãtar (sãmun) rahamar Allah kuma Allah Mai gãfara ne, Mai jin kai.

Kamar yadda muka yi bayani a cikin shirye shiryemmu da suka gabata, larabawa tun zamanin Annabi Ibrahim (a ) suna da wata al’ada ta haramta yaki a cikin watanni hudu na shekarar kamariyya-addinin musulunci ya zo ya tabbatar da wannan al’adar - watannin sune, zulkida, zulhajji, muharram, da kuma Rajab. Amma dangane da wadan nan ayoyi ya zo cikin sira cewa, kafin yakin badar Manzon Allah (s) ya aiki sahabbai guda 8 zuwa kan hanyar makka don su zo masa da labarin mushrikai a boye ba tare da sun sani ba. Amma da suka je sai suka hadu da wani ayarin mushrikai. A cikinsu akwai daya daga cikin shuwagabannin kuraishawa. Wadan nan sahabbai sun gafala kan cewa ana cikin watannin hudu da aka haramta yaki ba, wanda kuma addinin musulunci ya tabbatar da hakan ba, sai suka fadawa ayarin kuraishawa ya yaki suka kashe wannan shugaba suka kama sauran wadanda suke tare da shi, da kuma ginima na dukiyoyin da ke wajensu suka zo da su gaban manzon Allah (s). Ganin cewa manzon Allah (s) bai umurcesu da yaki bai ya bata rai da wannan aikin nasu, ya ki karban ganimar da suka zo da su. Haka ma sauran musulmu sun kauracewa wadannan mutane da dukiyoyin da ke hannunsu. A bangaren mushrikai kuma, sun sami damar yada wani laifi wanda musulmi suka yi na yaki da zubar da jini cikin wata daga cikin watannin da aka haramta yaki. Duk cewa sun sanda cewa shugaban musulmi bai amince da abinda sahabbansa suka yi ba. Wadan nan ayoyi sun sauka suna maida martani ga ne ga mushrikai –inda aya ta 217 take bayyana cewa-mun san cewa zubar da jini cikin wata mai alfarma ba dai dai bane, amma kun san cewa an aikata haka ne ba tare da yardar manzon Allah (s) ba –sannan ai abinda ku kuka aikata na azabtar da musulmi, korarsu daga gidajensu a makka da toshe masu hanya zuwa dakin Allah ya fi muni kan zubar da jini. Daga nan sai aya ta gabat ta yi kira da muminai da su yi hankali da kafirai. Don bazasu taba kyaleku ba sai sun maidaku kafirci idan har zasu iya. Amma duk wanda ya yarda ya bar addininsa daga cikinku ya mutu kafiri, to aikinsa a duniya da lahira duk sun baci kuma makomarsa jahannama ce. A dayan bangaren kuma, tunda wadannan musulmai guda 8 wadanda suka sabawa umurnin manzon Allah kan abinda ya umurcesu, mutanene da suka yi hijira daga makka zuwa madina. Kuma abinda suka aikata din nan ba tare da nufin neman duniya ko sabawa umurnin manzon Allah(s) ba, aya ta 218 ta bayyana afwan da Allah ya yi masu. Daga cikin wadan nan ayoyi zamu dauki darussa kamar haka: 1) Dole ne mu zama masu kula kada mu aikata kurakuran da zasu bawa makiyammu damar suka da kuma aibata mu. 2) Idan zamu yi hukunci mu kula da asalin matsaloli ba reshe ba. Mai yuwa wata matsala ta bayyana a fili ammam ita reshe ce ga wata, don haka kada mu yaudaru da reshe mu bar jijiyar matsala a wajen bada hukunci. Masu daura re a nan kuma zamu dasa aya sai kuma wani lokacin idan Allah ya kaimu zasu sake jimmu tare da wani shirin na hannunka mai sanda. A huta lafiya wassalamu alaikum warahmatullahi wa barakatuhu.

Suratul Bakara; Aya Ta 219-221 (Kashi Na 59)

Assalamu alaikum masu saurare barkammu da sake saduwa cikin shirimmu na hannunka mai sanda shirin wanda ya nazari cikin wasu ayoyin al-kur’ani mai girma don su zama fitala a garemu cikin rayuwarmu. Da fatan masu saurare zasu kasance tare da mu a cikin wannan shirin.

A cikin shirimmu na yau zamu nazarin ayoyin alkur’ani mai girma cikin surra bara wadanad suke maga kan rayuwa tare a tsakanin musulmi da kuma iyali guda. Bari mu fara da sauraron ayoyi na 219 da 220 daga cikin surar bakara kamar haka:

يَسْأَلُونَكَ عَنِ الْخَمْرِ وَالْمَيْسِرِ قُلْ فِيهِمَا إِثْمٌ كَبِيرٌ وَمَنَافِعُ لِلنَّاسِ وَإِثْمُهُمَا أَكْبَرُ مِن نَّفْعِهِمَا وَيَسْأَلُونَكَ مَاذَا يُنفِقُونَ قُلِ الْعَفْوَ كَذَلِكَ يُبيِّنُ اللّهُ لَكُمُ الآيَاتِ لَعَلَّكُمْ تَتَفَكَّرُونَ{219} فِي الدُّنْيَا وَالآخِرَةِ وَيَسْأَلُونَكَ عَنِ الْيَتَامَى قُلْ إِصْلاَحٌ لَّهُمْ خَيْرٌ وَإِنْ تُخَالِطُوهُمْ فَإِخْوَانُكُمْ وَاللّهُ يَعْلَمُ الْمُفْسِدَ مِنَ الْمُصْلِحِ وَلَوْ شَاء اللّهُ لأعْنَتَكُمْ إِنَّ اللّهَ عَزِيزٌ حَكِيمٌ{220}

219-Suna tambayar ka game da giya da cãcã. Ka ce: "A cikinsu akwai zunubi mai girma da wasu amfãnõni ga mutãne, kuma zunubinsu ne mafi girma daga amfaninsu." Kuma suna tambayar ka mẽne ne zã su ciyar; ka ce: "Abin da ya rage." Kamar wancan ne Allah Yake bayyanawar ãyõyi a gare ku; tsammãninku, kuna tunãni. 220-A cikin dũniya da Lãhira. Kuma suna tambayar ka game da marãyu. Ka ce: "Kyautatãwa gare su ne mafi alhẽri, kuma idan kun hada da su (wajen abinci), to, 'yan'uwanku ne; kuma Allah Yana sanin mai bãtãwa daga mai kyautatãwa. Kuma dã Allah Yã so, dã Ya tsananta muku. Lalle ne Allah Mabuwãyi ne, Mai hikima.

A cikin wadan nan ayoyi musulmi sun tambayi manzon Allah (s) dangane da abubuwa ukku daban daban, wadanda suka shafi rayuwasu. Sannan manzon Allah (s ) ya basu amsa bisa kamar yadda Allah ta’ala ya sanarda shi a cikin wahayin da ya saukar masa. Daya ko biyu daga cikin al’adun larabawa kafin bayyar musulunci sun hada da shan giya da kuma chacha. Manzon Allah ya basu amsa da cewa – akwai amfani cikin noman inabi da kuma sayar dasu, tunda kuna samun kudadebn shiga ta hanyasu. Hakama yan chacha riba ce ga bangaren da ya yi nasara. Amma fa ku sanu sharrin da ke cikin wadan nan abubuwa guda biyu ya fi amfani da masu samu daga cikinsu suke samu. Don haka hukuncin Allah dangane da wadan nan abubuwa biyu shi ne kaurace masu. Wata tambaya da musulman suka yi wa manzon Allah (s) sun hada da abinda yakamata su bada shi sadaka ga mabukata daga cikinsu, da kuma irin mutanenda yakamat su bawa sadakar. Manzon Allah (s) har’ila yau ya basu amsa da cewa – abinda ya saura- abinda ya yi rara daga cikin bukatunku na yau da kullum. Ba dukiyarku gaba daya zaku bayar ba. Ku ma ku zama masu bukata. Mizanin ku ya zama tsaka tsaki wato baku bada dukkan abinda kuka mallaka ba, har ku zama mabukata, ba kuma tara dukiya mai yawa a dai dai lokacinda kwai masu bukatarsu a cikinsu ba. Wata tambaya ita ce dangane da kiyaye dukiyar maraya da kuma yadda za’a yi mu’amala da su. Wasu sahabban hatta kwano ko akushin cin abinci, da kuma abincin marayu sai da suka waresu suka fitar da su daga dukiyoyinsu don tsoron kada dukiyar maraya ya garwaya da dukiyarsu. Anan ma manzon Allah (s) bisa wahayin da aka yi masa ya basu amsa da cewa-Abin da ke da muhimmanci dangane da maraya shi ne kyautata masa a cikin kula da rayuwarsa da kuma dukiyarsa. Ya kasance baya cutuwa a yadda yake rayuwa da kuma yadda ake kiyaye masa dukiyarsa. Ba wai ku ware shi daga cikin wadanda kuke reno don tsoron kada dukiyarsa ya hadu da naku ba. Allah baya nufin wahadda ku dangane da rikon maraya ba. Don haka daga cikin wadan nan ayoyi muna iya fahintar wadan nan abubuwa: 1) Dangane da ayyukan neman abin rayuwa- kada mu nemi ayyuka wadanda zasu cutar da mu a zahiri ko badini ba. Kamar yadda saida giya da chacha suna daga cikin ayyuka masu samar da kudade masu yawa, amma ubangiji ya haramta wadan nan ayyuka. Don haka mu nisance su. 2) Mu kiyaye zaman lafiya da nutsuwa cikin mutane- Allah ya haramta shan giya kuma muna ganin yadda giya take lalata rayuwan yan uwammu. Ya rikita kwakwalensu ya maidasu musiba a cikin al-umma. Hakama chacha tana rikita tsarin tattalin arziki a cikin al-umma. Tana jawo aikata laifuffuka a cikin mutane da kuma samarda kiyayya da fasadi a cikin al-umma. Don haka duk munisance su. 3) Sannana cikin rarar dukiyarmu kuma, mu ciyar da mabukata ta yadda zai zama mun kubutar da rayuwar wasu, sannan mu kuma bamu barnata dukiya ba. 4) Hukunce hukuncen Allah gaba dayansu, an kafasu ne don maslahar daidakkummu ko kuma dukkan al-umma –haka yake ko mun sani ko bamu sani ba- don haka kada mu yi sakaci wayen kiyayesu. 5) Sanna daga karshe-bai kamata a bar marayu ba tare da wani yana kula da shi ba. Dole ne al-umma ta kula da rayuwarsa, kuma ta kiyaye dukiyarsa.

Yanzu kuma mua saurai karatun aya ta 221 kamar haka:

وَلاَ تَنكِحُواْ الْمُشْرِكَاتِ حَتَّى يُؤْمِنَّ وَلأَمَةٌ مُّؤْمِنَةٌ خَيْرٌ مِّن مُّشْرِكَةٍ وَلَوْ أَعْجَبَتْكُمْ وَلاَ تُنكِحُواْ الْمُشِرِكِينَ حَتَّى يُؤْمِنُواْ وَلَعَبْدٌ مُّؤْمِنٌ خَيْرٌ مِّن مُّشْرِكٍ وَلَوْ أَعْجَبَكُمْ أُوْلَـئِكَ يَدْعُونَ إِلَى النَّارِ وَاللّهُ يَدْعُوَ إِلَى الْجَنَّةِ وَالْمَغْفِرَةِ بِإِذْنِهِ وَيُبَيِّنُ آيَاتِهِ لِلنَّاسِ لَعَلَّهُمْ يَتَذَكَّرُونَ

Kuma kada ku auri mãtã mushirikai sai sun yi ĩmãni: Kuma lalle ne baiwa mũminaita ce mafi alhẽri daga diya kãfira,kuma kõ da tã bã ku sha'awa. Kuma kada ku aurar wa maza mushirikai sai sun yi ĩmãni, kuma lalle ne bãwa mũmini shi ne mafi alhẽri daga da mushiriki, kuma kõ da yã bã ku sha'awa, wadannan suna kira ne zuwa ga wuta kuma Allah Yana kira zuwa ga Aljanna da gãfara da izninsa. Kuma Yana bayyana ãyõyinsa ga mutãne; tsammãninsu suna tunãwa.

Musulunci ya bada muhimmanci sosai dangane da aure da kuma samarda iyali. Don haka ne ya kafa sharudda na zaben wanda ko wacce za’a aura. Sharadi na farko shi imani da ingantacciyar akida. Ko wa yasan yadda halaye, muganganu da kuma tunanin iyaye yake da tasiri a cikin tarbiyyan yaro. Abin bakin ciki a yau ma muna ganin yadda dukiya da matsyin da mutum yake da shi a cikin al-umma sun zama abin lura wajen zaben wanda za’a aura – Halaye masu kyau, mutunci da tsoron Allah basu da wani kima a cikin mafi yawan al-ummar mu. Amma a mahangar musulunci – bawa mai imani wanda ya fi kaskanci a cikin al-umma ya fi – mutum mai enci amma mara imani. Mizanin fifiko a musulunci shi ne karfin imani da tsarkin zuciya. Don haka zamu dauki darussa a cikin wannan ayar kamar haka.: 1) Aure a musulunci –dole ne ya kasance an gina shi bisa asasin imani don a haifarwa al-umma yaya salihai masu tsoron Allah. 2) A lokacin zaben wanda zamu aura-mu dubi bangaren halaye masu kyau da tsoron Allah. Kada mu mu rudu da kyauwun zahiri, da kuma wasu lamura masu gushewa ko a nan duniya ko kuma ya zame mana mummunar makoma a lahira. Daga karshe masu saurare mu na rokon Allah madukakin sarki da ya sanya mu musu biyayya ga umurninsa da kuma dokokinsa. Wadanda sune tafarkin sa’adarmu a duniya da lahiri. A nan zamu dakata sai kuma wani shirin idan Allah ya akimu. Wassalamu ..................

Suratul Bakara; Aya Ta 222-227 (Kashi Na 60)

Assalamu alaikum masu saurare barkammu da sake saduwa cikin shirimmu na hannunka mai sanda shirin wanda ya nazari cikin wasu ayoyin al-kur’ani mai girma don su zama fitala a garemu cikin rayuwarmu. Da fatan masu saurare zasu kasance tare da mu a cikin wannan shirin.

A cikin shirimmu da ya gabata mun karanta ayoyi dangane da aure a cikin addinin musulunci. Amma a cikin shirimmu na yau zamu ci gaba da magana a kan hukunce hukuncen da suka shafi zamantakewa tsakanin ma’aurata. Kafin haka bari mu sauri karatun ayoyi na 222 da kuma 223 daga cikin surar bakara kamar haka.

وَيَسْأَلُونَكَ عَنِ الْمَحِيضِ قُلْ هُوَ أَذًى فَاعْتَزِلُواْ النِّسَاء فِي الْمَحِيضِ وَلاَ تَقْرَبُوهُنَّ حَتَّىَ يَطْهُرْنَ فَإِذَا تَطَهَّرْنَ فَأْتُوهُنَّ مِنْ حَيْثُ أَمَرَكُمُ اللّهُ إِنَّ اللّهَ يُحِبُّ التَّوَّابِينَ وَيُحِبُّ الْمُتَطَهِّرِينَ{222} نِسَآؤُكُمْ حَرْثٌ لَّكُمْ فَأْتُواْ حَرْثَكُمْ أَنَّى شِئْتُمْ وَقَدِّمُواْ لأَنفُسِكُمْ وَاتَّقُواْ اللّهَ وَاعْلَمُواْ أَنَّكُم مُّلاَقُوهُ وَبَشِّرِ الْمُؤْمِنِينَ{223}

222-Kuma suna tambayar ka game da haila Ka ce: Shi cũta ne. Sabõda haka ku nĩsanci mãta a cikin wurin haila kuma kada ku kusance su sai sun yi tsarki. To, idan sun yi wanka sai ku je musu daga inda Allah Ya umurce ku. Lalle ne Allah Yana son mãsu tũba kuma Yana son mãsu tsarkakẽwa. 223-Mãtanku gõnaki ne a gare ku, sabõda haka ku je wa gõnakinku yadda kuka so. Kuma ku gabãtar (da alheri) sabõda kanku, ku bi Allah da takawa. Kuma ku sani cẽwa lalle nekũ mãsu haduwa da Shi ne. Kuma ka bãyar da bishãra ga mũminai.

Daya daga cikin manufar aure shi ne samun haihuwa don wanzuwar jinsin dan adam a bayan kasa. Sannan miji da kuma matarsa duk suna da rawan da suke takawa don tabbatar da wannan buaktar. Mahaifiya tana tanadi da kuma shiri na renon ‘ya’ya - tun ma kafin zuwansa duniya. Don dafarko sai ta rene shi a cikin cikinta na tsawon watannin 9 . A lokacinne yake iya rayuwa da kans a duniya ba tare da bukatar taimako mai yawa ba. Sannan sai ta haife shi. Alkur’ani mai girma a nan a cikin wannan ayar ya ambaci macce a batsayin gona. Mun san cewa manomi yana bukatar gyaran gona ya tanadi bukatun kafin saukar dama ko kuma wata hanyar shayarwa da yake da ita kafin ya fara shuka. Jinin haila da mafi yawan mata suke fitarwa a ko wani wata, wani shiri ne kyautawa da kuma tanadi don shuga ‘ya’ya. Don haka alkur’ani ya yi umurni ga maji da nisanci matarsa a cikin yan kwanakin da take wannan tanadin, take wanke cikinta don karban ciki. Don kusantarta a lokacin cutarwa ce ga jikinku. Banda wannan kusantanta a lokacin laifi ne wanda yana da tasiri a cikin dangantakarku da ubangijinku. Don haka ku ji tsoron Allah ku kasance masu biyayya ga umurnin Allah. A cikin wadan nan ayaoyi zamu dauki darussa kamar haka: 1) Musulunci addini ne da ya gama dukkan bangarorin rayuwar dan adam. Don haka yana da amsa kan tambayoyi da kuma tsarin rayuwar ma’aurata da kuma abinda zasu haifa. 2) Dokokin addini suna tafiya tare da irin halittar dan adam. Duk abinda ya kasance na cutarwa ne ga macce ko na miji ko ga sauran mutane, dokokin addini sun hana, don kiyaye lafiyar daddaiku mutane da kuma dan’adam gaba daya. 3) Dole ne musulmi ya kasance yana da iko a kan sha’awarsa. Ya kiyaye lafiyar kansa da iyalansa ta hanyar jan linzamin son zuciyar ga iyakokin Allah. 4) Macce a muslunci wasilace ta samarda nutsuwa da mijinta da kuma renon yaya salihai ga al-ummar musulmi.

Yanzu kuma mu saurari ayoyi na 224 da kuma 225 daga cikin surar bakara kamar haka.

وَلاَ تَجْعَلُواْ اللّهَ عُرْضَةً لِّأَيْمَانِكُمْ أَن تَبَرُّواْ وَتَتَّقُواْ وَتُصْلِحُواْ بَيْنَ النَّاسِ وَاللّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ{224} لاَّ يُؤَاخِذُكُمُ اللّهُ بِاللَّغْوِ فِيَ أَيْمَانِكُمْ وَلَكِن يُؤَاخِذُكُم بِمَا كَسَبَتْ قُلُوبُكُمْ وَاللّهُ غَفُورٌ حَلِيمٌ{225}

224-Kuma kada ku sanya Allah kambu ga rantsuwõyinku dõmin kada ku yi wani alhẽri, kuma ku yi takawa, kuma ku yi wani gyara tsakãnin mutãne, kuma Allah Mai jĩ ne, Masani. 225-Allah ba Ya kãmã ku da laifi sabõda yãsasshiya a cikin rantsuwõyinku. Kuma amma Yana kama ku sabõda abin da zukãtanku suka sanã'anta. Kuma Allah Mai gãfara ne, Mai hakuri.

Kamar yadda yazo cikin tafsirai da dama sabano ya shiga tsakanin wani da wata yarinyan da yake daukan nauyinta da wasu na kusa da ita, sai ya rantse da Allah cewa ba zai sake taimaka masu ba a nan ne wannan ayar ta sauka tana nasiha ga musulmi kada su sanya rantsuwa a zama katanga tsakanisu da aikata alkhairi. Rantsuwa a cikin bacin rai ko wani hali mara kyau baya hana mutum ya dawo ga aikin alkhairi. Kuma babu laifi a cikin irin wannan halin mutum ya koma ga aikin alkhairi da yake yi. Wadan ayoyi suna karantar da mu abubuwa kamar haka; 1) Kada mu sanya rantsuwa ya zama katanga ga ayyukan alkhairi da muke yi. Mu mutunta rantsuwa da sunan Allah kuma kada mu yi amfani da rantsuwa a duk inda muka ga dama. 2) Mu ma kamar yadda al-kur’ani ya koya mana mu yi afwa ga wadanda suka yi kurakurai bisa jahilci ka da gafala ko bacin rai. Kada mu yi kokarin daukar fansa kansu.

Sai kuma mu saurari aya ta 226 zuwa aya ta 227 daga cikin surar ta bakara kamar haka.

لِّلَّذِينَ يُؤْلُونَ مِن نِّسَآئِهِمْ تَرَبُّصُ أَرْبَعَةِ أَشْهُرٍ فَإِنْ فَآؤُوا فَإِنَّ اللّهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ{226} وَإِنْ عَزَمُواْ الطَّلاَقَ فَإِنَّ اللّهَ سَمِيعٌ عَلِيمٌ{227}

226-Ga wadanda suke yin rantsuwa daga matansu akwai jinkirin watã hudu. To, idan sun kõma, to, lalle ne Allah Mai gãfara ne, Mai jin kai. 227-Kuma idan sun yi niyyar saki, to, lalle ne, Allah Mai ji ne, Masani.

Daya daga cikin mummunan al’adun larabawa kafin musulunci shi ne mutum yakan kauracewa matarsa don ya sanyata cikin damuwa da wahala. Sai ya rantse cewa bazai kusanceta ba kuma ba zai saketa ba. Don haka sai ya sa ta cikin tsaka mai wuya, ita ba a sake ba ta kama gabanta, kuma ba cikekken mai zaman aure ba. Musulunci ya tsaida hukunci a nan inda ya bawa mijin wata hudu daga lokacin rantsuwar na ya dawo ga matarsa su gaba da rayuwa da mata fa mijinta ko kuma ya sake ta ta kama gabanta. Darussa daga wadan nan ayoyi sun hada da : 1) Kawarda al’adu mara kyau cikin mutane na daga cikin ayyukan annabawa. 2) Duk da cewa hakkin kula da gida yana hannun miji, amma bai da hakkin cutar da matarsa ko jefata cikin tsaka mai wuya. 3) Musulunci ya amince da saki ko rabuwar miji da matarsa idan har shi ne masalaha ga iyalan gidan. Saki wanda ake yi shi bisa son zuciya na mijin ko kuma matan – su san cewa Allah zai tambayesu dangane da shi a ranar kiyama. Musulunci bai amince da cutar da macce don kawai haka mijin ya ga dama ba. Da wannan kuma masu saurare muka kawo karshen shirimmu na yau sai kuma wani lokaci idan Allah ya kai mu. Kafin hakan wassalamu alaikum warahmatullah.

Suratul Bakara; Aya Ta 228-232 (Kashi Na 61)

Bismillahar rahamanir rahim Jama'a masu saurare Assalamu Alaikum barkanku da warhaka da kuma sake saduwa da mu acikin wani sabon shiri na hannunka mai sanda, wanda acikinsa muke kawo muku fassarar ayoyin Al'kurani mai girma kana daga baya mu yi karin bayani game da su, idan masu saurare za su tuna a shirin da ya gabata mun yi bayani game da yadda musulunci ya jaddada kan kare hakkin mata acikin iyali ne, kuma ya hana duk wani nauyin cutarwa ta jiki ko ta jinsi ga mata, don haka ne ma yake nuna cewa matukar miji ya ga ba zai iya ci gaba da rayuwa da matarsa ba to saki shi ne yafi dacewa mai makon yabarta tamkar ratayayya ba ta san matsayinta ba, ko kuma ya yi ta cutar da ita. da fatan masu saurare za su kasance tare damu domin jin cikakken shirin amma fa bayan an saurari abin da aka yi mana tanadi a bisa fai-fai.

            • ****

To madalla A yau shirin na mu na yau zai maida hankali ne game da hukumce - hukumcen saki don haka bari muji abin da aya ta 228 a cikin saratul bakara take cewa .

وَالْمُطَلَّقَاتُ يَتَرَبَّصْنَ بِأَنفُسِهِنَّ ثَلاَثَةَ قُرُوَءٍ وَلاَ يَحِلُّ لَهُنَّ أَن يَكْتُمْنَ مَا خَلَقَ اللّهُ فِي أَرْحَامِهِنَّ إِن كُنَّ يُؤْمِنَّ بِاللّهِ وَالْيَوْمِ الآخِرِ وَبُعُولَتُهُنَّ أَحَقُّ بِرَدِّهِنَّ فِي ذَلِكَ إِنْ أَرَادُواْ إِصْلاَحاً وَلَهُنَّ مِثْلُ الَّذِي عَلَيْهِنَّ بِالْمَعْرُوفِ وَلِلرِّجَالِ عَلَيْهِنَّ دَرَجَةٌ وَاللّهُ عَزِيزٌ حَكُيمٌ

Sakakkun mataye kuwa suna dakatar da kansu (ba za su yi aure ba sai sun ga) har jini uku. Kuma bai halatta ba a gare su su boye abin da Allah ya halitta a cikin mahaifarsu, in sun kasance masu ba da gaskiya da Allah da ranar lahira; kuma mazajensu su suka fi cancantar mai da su a cikin wannan lokaci idan suka yi nufi zaman lafiya; suna da hakkoki a kan mazajensu kamar (yadda mazajensu suke da hakkoki) a kansu na aikin alheri (kamar zaman lafiya da rashin cutar juna); kuma mazaje suna da fifiko a kansu. Allah kuwa Mabuwayi ne (a kan komai) Gwani ne.

Wannan aya tana baya ni ne game da kare martabar iyali da yara, wato ko bayan an saki mace akwai bukatar ta yi hakuri ta tsaya na tsawon watanni Uku ba tare da ta yi wani aure ba saboda wasu abubuwa kamar haka na farko idan akwai da acikin mahaifarta to za'a gane a cikin wadannan watannin, kuma za'a kare hakkokin jaririn, kuma kila ma wannan jaririn ya zama sanadiyar warware sabanin dake tsakin ma'auratan guda biyu, domin kila a tsawon wannan lokacin mijin ko matar wani daga cikinsu ya yi nadama ya canza tunani ya ga yana sha'awar ya ci gaba da rayuwa da abokin zamansa . daga karshe ayar ta bayyana wani batu mai muhimmanci a matsayin wata hanya ta kawar da rikici da sabani dake tsakanin ma'auratan, da kuma yin sulhu tsakaninsu, da farko ta na Magana da namiji cewa duk da yake cewa matayenku suna da nauyin da ya rataya a wuyansu game da kula da gida da iyali to kuma akwai hakkokiinsu da ya rataya a wuyanku, don haka ya zama dole ku yi aiki da nauyin da ya rataya a wunyanku, kamar yadda ya dace. A daya hannu kuma ya yi Magana da mata inda yake cewa tafiyar da alamuran gida baki daya nauyi ne daya rataya a wuyan namiji, don haka a wannan bangaren maza su ne suka fi cancanta da dacewa da wannan aiki.

Yanzu kuma bari mu saurari aya ta 229 a cikin suratul bakara inda All. Madaukakin sarki yake cewa.

الطَّلاَقُ مَرَّتَانِ فَإِمْسَاكٌ بِمَعْرُوفٍ أَوْ تَسْرِيحٌ بِإِحْسَانٍ وَلاَ يَحِلُّ لَكُمْ أَن تَأْخُذُواْ مِمَّا آتَيْتُمُوهُنَّ شَيْئاً إِلاَّ أَن يَخَافَا أَلاَّ يُقِيمَا حُدُودَ اللّهِ فَإِنْ خِفْتُمْ أَلاَّ يُقِيمَا حُدُودَ اللّهِ فَلاَ جُنَاحَ عَلَيْهِمَا فِيمَا افْتَدَتْ بِهِ تِلْكَ حُدُودُ اللّهِ فَلاَ تَعْتَدُوهَا وَمَن يَتَعَدَّ حُدُودَ اللّهِ فَأُوْلَـئِكَ هُمُ الظَّالِمُونَ

Saki daya (wanda ake kome bayansa) sau biyu ne. (Bayan haka yana da zabin) rike ta kamar yadda ya kamata ko kuma rabuwa da ita cikin girma da arziki. Bai halatta ba a gare ku ku karbi wani abu daga abin da kuka ba su sai idan (mijin da matar) suna jin tsoron ba za su bi dokokin Allah ba, to idan kuka ji tsoron cewa ba za su bi dokokin Allah ba, to babu laifi a kansu cikin abin da ta fanshi (kanta) da shi, Wadannan dokokin Allah ne, kada ku karya su; wadanda suka karya dokokin Allah kuwa su ne azzalumai.

Wannan aya ta ci gaba da bayani ne kamar yadda wadda ta zo kafinta take bayani inda take nuna cewa mata suna da dammar yin hakuri na tsawon watanni Uku bayan saki, wanda idan akwai da acikin mahaifarsu to zai bayyana zuwa wannan lokacin, kuma idan mijin ya yi nadama akan sakin da ya yi akwai yiyuwar a sulhunta kenan, to amma wannan ayar tana cewa ne shi namiji sau biyu kawai yake da hakkin sake dawowa da matarsa da ya saki, domin idan ya kasance saki na uku ne to daga nan ba shi da hakkin sake dawowa da ita, To anan akwai wani muhimman abu na asasi da ya shafi tafiyar da iyali da ya kamata ajawo hankali mazaje akai, wato anan akwai bukatar ya dauki rayuwar da daske ya zauna da matarsa lafiya cikin mutunci da kyautatawa ko koma idan yana ganin akwai wasu dalilai da zai hana ya ci gaba da rayuwa da matarsa to ya sallameta cikin mutunci da kyautatawa amma fa anan dole ne ya biyata sadakinta, Hakazalika idan ita ma mace ta bukaci rabuwa da mijinta tana iya yafemasa sadakinta sai ya saketa, sai dai anan namiji ba shi da hakkin ya takurawa matarsa ta hanyar kuntata mata da cutar da ita domin ya tilastamata ta yafemasa sadakinta domin ya saketa. To a nan akwai abubuwa da za mu koya acikin wadannan ayoyi. na farko: baya ga hakkin dan adamtaka da mace take da shi, dole ne a kiyaye hakkin hakkin dukiyarta namiji bashi da hakkin tauye wani abu daga cikin sadaki ko dukiyarta, Na biyu: idan saki ya zama dole to ya kamata a yi shi ne cikin kyautatawa ba da cuta da daukar fansa ba. Na Uku: iyalin dake cikin sa'ada shi ne wanda bangarorinsa suke rayuwar bisa kiyaye hukumce-hukumcen ubangiji, amma idan za su ci gaba da rayuwa bisa sabo to rabuwa shi yafi dacewa da ci gaba da rayuwar wannan iyalin . To yanzu kuma bari mu saurari abinda ayoyi na 230 da na 231 da kuma 232 dake cikin sura ta bakara suke cewa:

فَإِن طَلَّقَهَا فَلاَ تَحِلُّ لَهُ مِن بَعْدُ حَتَّىَ تَنكِحَ زَوْجاً غَيْرَهُ فَإِن طَلَّقَهَا فَلاَ جُنَاحَ عَلَيْهِمَا أَن يَتَرَاجَعَا إِن ظَنَّا أَن يُقِيمَا حُدُودَ اللّهِ وَتِلْكَ حُدُودُ اللّهِ يُبَيِّنُهَا لِقَوْمٍ يَعْلَمُونَ{230} وَإِذَا طَلَّقْتُمُ النَّسَاء فَبَلَغْنَ أَجَلَهُنَّ فَأَمْسِكُوهُنَّ بِمَعْرُوفٍ أَوْ سَرِّحُوهُنَّ بِمَعْرُوفٍ وَلاَ تُمْسِكُوهُنَّ ضِرَاراً لَّتَعْتَدُواْ وَمَن يَفْعَلْ ذَلِكَ فَقَدْ ظَلَمَ نَفْسَهُ وَلاَ تَتَّخِذُوَاْ آيَاتِ اللّهِ هُزُواً وَاذْكُرُواْ نِعْمَتَ اللّهِ عَلَيْكُمْ وَمَا أَنزَلَ عَلَيْكُمْ مِّنَ الْكِتَابِ وَالْحِكْمَةِ يَعِظُكُم بِهِ وَاتَّقُواْ اللّهَ وَاعْلَمُواْ أَنَّ اللّهَ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمٌ{231} وَإِذَا طَلَّقْتُمُ النِّسَاء فَبَلَغْنَ أَجَلَهُنَّ فَلاَ تَعْضُلُوهُنَّ أَن يَنكِحْنَ أَزْوَاجَهُنَّ إِذَا تَرَاضَوْاْ بَيْنَهُم بِالْمَعْرُوفِ ذَلِكَ يُوعَظُ بِهِ مَن كَانَ مِنكُمْ يُؤْمِنُ بِاللّهِ وَالْيَوْمِ الآخِرِ ذَلِكُمْ أَزْكَى لَكُمْ وَأَطْهَرُ وَاللّهُ يَعْلَمُ وَأَنتُمْ لاَ تَعْلَمُونَ{232}

Idan ya sake ta (bayan wancan shika biyu da ya yi mata) ba za ta kuma halatta a gare shi ba. Idan (mijin da ta aura ya sake ta) babu laifi a kansu (matar da mijinta na farko) su mai da (aurensu) idan suka yi zaton za su bi dokokin Allah. Wadancan dokokin, Allah ne yake bayyana su ga mutane wadanda suke tunani. Kuma idan kun saki mãta, sa'an nan suka isa ga ajalinsu (iddarsu), sai ku rike su da alheri ko ku sallame su da alheri, kuma kada ku rike su a kan cũtarwa dõmin ta tsawaita idda. Kuma wanda ya aikata wancan, to, hakĩka, yã zãlunci kansa. Kuma kada ku riki ãyõyin Allah da izgili. Kuma ku tuna ni'imar Allah da abin da Ya saukar a kanku na Littãfi da hikima. Yana yi muku wa'azi da shi. Kuma ku bi Allah da takawa kuma ku sani cewa lalle ne Allah ga dukan kõme Masani ne. Kuma idan kuka saki mãta, har suka isa ga ajalinsu (iddarsu), to, kada ku (waliyyansu) hana su, su auri mazansu (da suka sake su) idan sun yarda da jũna a tsakãninsu (tsõhon miji da tsõhuwar mãta) da alheri. Wancan ana yin wa'azi da shi ga wanda ya kasance daga gare ku yana ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. Wancan ne mafi mutunci a gare ku,kuma mafi tsarki. Kuma Allah masani ne, amma kũ ba ku sani ba.

Daga nan zamu fahimci cewa Musulunci yana yana girmama bukatu na dabi'a da suka dace da sharia kuma yana karbar duk wata hanya ta yin sulhu na komawar mace zuwa ga mijinta da kuma ci gaban yara tsakanin iyayensu, saboda haka ne ma aka bada izinin cewa ida mace ta auri wani mutum daban sai kuma suka rabu to idan suka cimma matsaya da mijinta na farko za su iya komawa su ci gaba da rayuwa tare, wala'alla ma rayuwa tafi zama mai kyau da dadi tsakaninsu, kuma anan a fili yake cewa iyayen mace ko wasu danginta basu da hakkin hanata sake komawa wajen mijinta na farko, kuma amincewar da suka yi tsakaninsu na sake yin aure tare ya wadatar wajen kulla akadin aure. acikin wannan ayar za mu koyi cewa ra'ayin mace wajen zaben miji abin girmamawa ne, kuma dole ne, kai bisa asali ma shika shikan aure sun doru ne akan yarda tsakanin bangarorin biyu bisa zabi. A karshen wannaN shirin muna fatan dukkan mata da maza za su ci gaba da kiyayewa tare da girmama hakkokin iyali, kuma kada wani daga cikinsu ya bada dama a raba yara daga tausayi da kulawar da suke samu daga iyayensu a jefa su cikin kuncin rayuwa da kadaici ko kuma ya kai ga rabuwa da juna. A nan kuma zan yi bankawana da ku sai a wata saduwar idan mai duka ya kaimu za ku ji mu dauke da ci gaban shirin amma kafinn nan nake cewa wasallamu alaikum.

Suratul Bakara; Aya Ta 233-237 (Kashi Na 62)

Bismillahair rahamanir rahim Jama'a masu saurare Assalamu Alaikum barkanku da warhaka da kuma sake saduwa damu acikin wani sabon shiri na hannunka mai sanda wanda acikinsa muke kawo muku bayanai da suka shafi ayoyin alkura'ani mai girma domin ya zama darasi garemu, a shirinn mu da ya gabata mun bijiro muku da bayani ne da ya shafi alakar iyalai da kuma alaka tsakanin miji da mata, sai dai wannan ayar za ta ci gaba da bayani ne game da muhimmancin kare hakkin yaya hatta ma bayan rabuwar Aure. sai a biyo mu domin jin abin da ayar take cewa amma bayan an saurari abin da aka tanadar mana a bisa fai-fai

                  • *****

To yanzu kuma sai a gyara zama domin jin abin da aya ta 233 cikin suratul bakra take cewa.

وَالْوَالِدَاتُ يُرْضِعْنَ أَوْلاَدَهُنَّ حَوْلَيْنِ كَامِلَيْنِ لِمَنْ أَرَادَ أَن يُتِمَّ الرَّضَاعَةَ وَعلَى الْمَوْلُودِ لَهُ رِزْقُهُنَّ وَكِسْوَتُهُنَّ بِالْمَعْرُوفِ لاَ تُكَلَّفُ نَفْسٌ إِلاَّ وُسْعَهَا لاَ تُضَآرَّ وَالِدَةٌ بِوَلَدِهَا وَلاَ مَوْلُودٌ لَّهُ بِوَلَدِهِ وَعَلَى الْوَارِثِ مِثْلُ ذَلِكَ فَإِنْ أَرَادَا فِصَالاً عَن تَرَاضٍ مِّنْهُمَا وَتَشَاوُرٍ فَلاَ جُنَاحَ عَلَيْهِمَا وَإِنْ أَرَدتُّمْ أَن تَسْتَرْضِعُواْ أَوْلاَدَكُمْ فَلاَ جُنَاحَ عَلَيْكُمْ إِذَا سَلَّمْتُم مَّا آتَيْتُم بِالْمَعْرُوفِ وَاتَّقُواْ اللّهَ وَاعْلَمُواْ أَنَّ اللّهَ بِمَا تَعْمَلُونَ بَصِيرٌ

Kuma mãsu haihuwa (sakakku) suna shãyar da abin suka Haifa na tsawon shekara biyu cikakku ga wanda ya yi nufin ya cika shãyarwa. Kuma ciyar da su da tufãtar da su yana a kan wanda aka haifar masa da kyautatawa. Bã a kallafa wa rai fãce iyãwarsa. Bã a cũtar da uwa game da danta, kuma bã a cũtar da uba game da dansa, kuma a kan magãji akwai misãlin wancan. To, idan suka yi nufin yãye, a kan yardatayya tsakanin su, da shãwartar jũna, to bãbu laifi a kansu. Kuma idan, kun yi nufin ku bãyar da 'yayanku shãyarwa, to, bãbu laifi a kanku idan kun mĩka abin da kuka zo da shi bisa al'ãda. Kuma ku bi Allah da takawa. Kuma ku sani cewa lalle ne Allah, ga abin da kuke aikatawa, Mai gani ne.

Iyali shi ne ginshinkin duk wata alumma duk lokacin da ya girgiza to zai iya haifar da matsaloli a cikin alumma, wanda idan mai saurare zai iya tunawa a ayyoyin da suka gabaata mun yi Magana ne game da rabuwa tsakanin miji da mata to a nan za'a bayyana makomar yaro karami musamman ma jariri bayan saki, saboda tausayin uwa da muhimmanacin shayar da mama ga yaro ya sa wannan ayar take wasiyya da a shayar da yaro har na tsawon shekaru 2 wanda ko da ma iyaye sun rabu ko kuma uba ya rasu ya bar duniya to ayi la'akari da hakkin da akan uwa domin kada sabanin da ke tsakanshi da matarsa ya cutar da jikin ko ruhin jariri, sai dai akwai nauyin da ya rataya a wuyan mahaifi acikin wannan yanayin na samar masa da abin da yake bukata na rayuwa da ya shafi abincin da ya dace ga mahaifiyarsa da shi kan shi dan, dole ne ya yi duk abin da zai iya don kada su cutu, A nan zamu iya koyon darussa kamar haka: Na farko kula da hakkokin yaro wajibi ne akan iyaye kuma ko da iyayen sun rabu bai kamata matsalar su ta shafi yaron ba. Na biyu: A tsarin musulunci namiji shi ne ke da alhakin samar da dukkan abubuwan asasi da iyali yake bukata, amma ita mace ba ta da hakkin samar da abubuwan da iyali ke bukata na rayuwa.

To yanzu kuma bari mu saurari aya ta 234 a cikin wannan sura ta bakara:

وَالَّذِينَ يُتَوَفَّوْنَ مِنكُمْ وَيَذَرُونَ أَزْوَاجاً يَتَرَبَّصْنَ بِأَنفُسِهِنَّ أَرْبَعَةَ أَشْهُرٍ وَعَشْراً فَإِذَا بَلَغْنَ أَجَلَهُنَّ فَلاَ جُنَاحَ عَلَيْكُمْ فِيمَا فَعَلْنَ فِي أَنفُسِهِنَّ بِالْمَعْرُوفِ وَاللّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ خَبِيرٌ

Kuma wadanda suke mutuwa daga gare ku suna barin mãtan aure, mãtan suna jinkiri da kansu wata hudu da kwãna goma. To, idan sun isa ga ajalinsu, to, bãbu laifi a kanku a cikin abin da suka aikata game da kansu ga al'ãda. Kuma Allah ga abin da kuke aikatawa Masani ne.

Baya ga saki, ko mutuwar Aure, daya daga cikin abubuwan da ke tilasta rabuwa tsakanin miji da mata ita ce mutuwa, haka nan lafiya lau idan ajali ya cika ko kuma sakamakon rashin lafiya ko hadari ko dai abubuwan da suka saba faruwa a cikin alumma dake jawo mace ta rasa mijinta, kamar yadda muka sani ne akwai matakai masu karo da juna da ake dauka game da wannan batun, wasu sun yi amanna cewa dole ne idan mace mijinta ya mutu itama ta bishi, a bizne ta tare da mijinta din a kabari daya. Wasu kuma suna hana matan sake yin wani auren, wasu kuma sun halatta yin auren anan take bayan mutuwar mijinta. To game da wannan wuce gona da irin ko kuma zurfafawa ko azarbabi, domin kare martabar mata musulunci ya lizimtawa mata sauraro na tsawon wani lokaci domin tantance halin da suke ciki game da yiyuwar ko tana dauke da juna biyu, amma musulunci ya bawa mace yancin auren duk wanda ya kwanta mata a rai bayan kammala wannan muddar ko lokacin, sai dai anan yana da kyau a kare ra'ayoyinsu akan batun:

Yanzu kuma bari mu saurari abin da aya ta 235 take cewa.

وَلاَ جُنَاحَ عَلَيْكُمْ فِيمَا عَرَّضْتُم بِهِ مِنْ خِطْبَةِ النِّسَاء أَوْ أَكْنَنتُمْ فِي أَنفُسِكُمْ عَلِمَ اللّهُ أَنَّكُمْ سَتَذْكُرُونَهُنَّ وَلَـكِن لاَّ تُوَاعِدُوهُنَّ سِرّاً إِلاَّ أَن تَقُولُواْ قَوْلاً مَّعْرُوفاً وَلاَ تَعْزِمُواْ عُقْدَةَ النِّكَاحِ حَتَّىَ يَبْلُغَ الْكِتَابُ أَجَلَهُ وَاعْلَمُواْ أَنَّ اللّهَ يَعْلَمُ مَا فِي أَنفُسِكُمْ فَاحْذَرُوهُ وَاعْلَمُواْ أَنَّ اللّهَ غَفُورٌ حَلِيمٌ

Kuma bãbu laifi a kanku a cikin abin da kuka gitta da shi daga nẽman auren mãtã ko kuwa kuka bõye a cikin zukatanku. Allah Ya san cewa lalle ne ku za ku ambata musu (shi). Kuma amma kada ku yi wa jũna alkawari da shi a bõye, fãce dai ku fadi magana sananniya. Kuma kada ku kulla niyyar daurin auren sai littãfin (idda) ya kai ga ajalinsa. Kuma ku sani cewa lalle ne Allah Yana sanin abin da yake cikin zukatanku, sabõda haka ku ji tsõronsa. Kuma ku sani cewa Allah Mai gãfara ne, Mai hakuri.

Har yanzu dai wannan ayar kamar wadda ta gabaceta ne tana magana ne game da batun matar da ta rasa mijinta da kuma yancin da aka bata na zabar mijin da ya kwanta mata a rai domin tayi aure da shi, ita kuwa wannan ayar ta na ci gaba da cewa ne duk da yake cewa daura aure a wannan lokacin bai halatta ba amma dai babu damuwa masu sonta su fara zuwa nemanta da fara tattaunawa da ita na neman amincewarta amma dole ne ganawar ta kasance akan tsarin da ya dace. Anan akwai abubuwa da zamu ko ya kamar haka. Na farko Musulunci addini ne na fidira, kuma fidirar kowanne mutum tana karkatar da shi zuwa ga yin Aure, wannan yasa musulunci ba ya nuna rashin amincewa da wannan bukatar ba, ya ma tanadar da halatacciyar shimfida ne domin cimma wannan muradi tsakanin mace da namiji. Na biyu: Yana kira da a nisanci yin maganganu da kula yarjeniyoyi a boye da nuna wasu halaye da basu dace ba kafin yin Aure.

To yanzu kuma bari mu saurari abin da aya ta gaba ta 236 da ta 237 suke cewa

لاَّ جُنَاحَ عَلَيْكُمْ إِن طَلَّقْتُمُ النِّسَاء مَا لَمْ تَمَسُّوهُنُّ أَوْ تَفْرِضُواْ لَهُنَّ فَرِيضَةً وَمَتِّعُوهُنَّ عَلَى الْمُوسِعِ قَدَرُهُ وَعَلَى الْمُقْتِرِ قَدْرُهُ مَتَاعاً بِالْمَعْرُوفِ حَقّاً عَلَى الْمُحْسِنِينَ{236} وَإِن طَلَّقْتُمُوهُنَّ مِن قَبْلِ أَن تَمَسُّوهُنَّ وَقَدْ فَرَضْتُمْ لَهُنَّ فَرِيضَةً فَنِصْفُ مَا فَرَضْتُمْ إَلاَّ أَن يَعْفُونَ أَوْ يَعْفُوَ الَّذِي بِيَدِهِ عُقْدَةُ النِّكَاحِ وَأَن تَعْفُواْ أَقْرَبُ لِلتَّقْوَى وَلاَ تَنسَوُاْ الْفَضْلَ بَيْنَكُمْ إِنَّ اللّهَ بِمَا تَعْمَلُونَ بَصِيرٌ{237}

Kuma bãbu laifi a kanku idan kun saki mãtã matukar ba ku shãfe su ba, kuma ba ku yanka musu sadãki ba. Kuma ku bã ku yi musu alheri (daga cikin dukiyarku ba) mawadãci gwargwadon karfinsa, haka kuma matalauci gwargwadon karfinsa; Yin alheri dai dai gwargwado wajibi ne ga amsu kyautatawa. Kuma idan kuka sake su daga gabãnin ku shãfe su, alhãli kuwa kun yanka musu sadãki, to, rabin abin da kuka yanka fãce idan sun yãfe, kõ wanda daurin auren yake ga hannunsa ya yãfe. Kuma ku yãfe din ne mafi kusa da takawa. Kuma kada ku manta da falala a tsakãninku. Lalle ne Allah ga abin da kuke aikatãwa Mai gani ne.

Wadannan ayoyin guda biyu suna karfafawa ne game da kare hakkin dukiyar mace a lokacin saki, yana cewa koda ma tun asalin auren ba'a ayyana sadaki ba to ya bayar da kyautar da ta dace gwargwadon karfin dukiyarsa domin hakan zai rage zafin rabuwar, wannan wata hanya ce ta kyautatawa. Idan kuma an ayyana sadakin tun da fari, kuma ya kwanta da matar to dole ne ya biyata dukkan sadakinta, koda ya kasance na kwana daya ne idan basu sadu da juna ba to abin da yafi dacewa shi ne ya bata sadakinta duka baki daya, wanda hakan alamace ta kyautatawa akalla dai koda rabin sadakin ne ya biyata, sai dai idan shi ne yake son ya bata dukkan sadakinta baki daya. To yanzu kuma zamu yi dubi game da darrusan da za mu dauka kamar haka, iyalai a mahangar Al'kur'ani, shi ne wanda ko a halin rabuwa ko saki to ba sa mantawa da kyawawan halaye da karamar dan adam, a batun saki dole ne dukkan bangarorin biyu, baya ga biyan hakokin wajibi na juna, to su rabu cikin mutunci da girmama juna ba cikin wulakanci da cin mutunci ba. To kuma anan shirin na mu zai kammala saboda lokacin da aka dibar mana ya karato sai a wata saduwar za ku ji mu dauke da ci gaban shirin amma kfin nan nake cewa wasalamu alaikum warahamtullahi ta'ala wabara katuhu.

Suratul Bakara; Aya Ta 238-244 (Kashi Na 63)

Bismillahir rahmanir rahim Jama'a masu saurare barkanku da warhaka da kuma sake saduwa daku acikin shirin hannunka mai sanda wanda acikinsa yake kawo muku fassara Al'kur'ni cikin hanya mafi sauki domin ya zama darasi garemu baki daya. A shirin namu na yau za mu ci gaba da bayani ne game da hukumce-hukumce musulunci a bangarori daban-daban na rayuwar daidaiku da ta iyali da kuma na jama'a sai a gyara zama domin jin yadda shirin zai kasance amma bayan an saurari wannan.

                • ******

To madalla yanzu kuma bari mu saurari aya ta 238 da kuma ta 239 kamar haka.

حَافِظُواْ عَلَى الصَّلَوَاتِ والصَّلاَةِ الْوُسْطَى وَقُومُواْ لِلّهِ قَانِتِينَ{238} فَإنْ خِفْتُمْ فَرِجَالاً أَوْ رُكْبَاناً فَإِذَا أَمِنتُمْ فَاذْكُرُواْ اللّهَ كَمَا عَلَّمَكُم مَّا لَمْ تَكُونُواْ تَعْلَمُونَ{239}

Ku kiyaye yin salloli da kuma sallar tsarkiya . Kuma ku tsayu kuna mãsu kankan da kai ga Allah To, idan kun ji tsõro, to (ku dai yi salla gwargwadon hali) da tafiya kasa kõ kuwa a kan dabbobi. Sa'an nan idan kun amince sai ku ambaci Allah, kamar yadda Ya sanar da ku abin da ba ku kasance kuna sani ba.

Lafiyayyen mutum shi ne wanda yake bawa jikinsa da ruhinsa irin abincin da ya dace, domin duk lokacin da muka kasa bawa jikinmu abinci mai gina jiki da ya dace mukan samu rauni ko muyi rashin lafiya to haka shi ma ruhin mutum, shi ma yana da bukatuwa zuwa ga abinci da ya dace domin neman kusanci ga mahaliccin komi da kowa, da kuma samun ci gaba, don haka tsai da sallah kamar abinci da muke bukatuwa zuwa gareshi ne a kullum sau uku domin mu samu karf ia jikinmu da ruhinmu, da kuma habaka, da kamala da kuma nisantar da ruhi daga abubuwa marasa tsarki da samun nishadi da natsuwa. Akan haka ne wan nan ayar take jaddadawa game da muhimmancin kiyayewa da dukufa akan wannan wajibi na ubangiji a kowanne hali hattama a lokacin yaki da tsoron makiya, domin gudanar da sallah acikin wadannnan yanayin abu ne mai yiyuwa don haka ne ma yasa musulunci yake amincewa da yadda aka gudanar da ita . A cikin wannan ayar zamu koyi cewa bukatar da mutum yake da shi zuwa ga sallah na ko yaushe ne kuma na dindin, hattama a lokacin yaki domin sallah ba tana hana kare kai da yaki ba ne a'a tana ma kara karfin ruhi ne wajen tunkarara makiya.

Yanzu kuma bari mu saurari ayoyi na 240 da 241 da kuma 242 a cikin wanna sura ta bakra kamar haka:

وَالَّذِينَ يُتَوَفَّوْنَ مِنكُمْ وَيَذَرُونَ أَزْوَاجاً وَصِيَّةً لِّأَزْوَاجِهِم مَّتَاعاً إِلَى الْحَوْلِ غَيْرَ إِخْرَاجٍ فَإِنْ خَرَجْنَ فَلاَ جُنَاحَ عَلَيْكُمْ فِي مَا فَعَلْنَ فِيَ أَنفُسِهِنَّ مِن مَّعْرُوفٍ وَاللّهُ عَزِيزٌ حَكِيمٌ{240} وَلِلْمُطَلَّقَاتِ مَتَاعٌ بِالْمَعْرُوفِ حَقّاً عَلَى الْمُتَّقِينَ{241} كَذَلِكَ يُبَيِّنُ اللّهُ لَكُمْ آيَاتِهِ لَعَلَّكُمْ تَعْقِلُونَ{242}

Wadanda kuma suka mutu daga cikinku suka bar mata, to su bar wasiyya ga matayensu har zuwa tsawon shekara, kada su fitar da su, idan suka fita don kansu babu laifi akanku game da abin da suka aikata don kansu na alheri Allah kuwa mabuwayi ne kuma gwani mai hikima. Kuma wadanda aka saki suna da wani abu na alheri wajibi ne akan masu tsoron Allah Kamar haka ne Allah Yake bayyana muku ãyõyinsa, don ku hankalta.

To wannan ayar ma tana bayani ne kan batun iyali, haka ma ya yi ishara game da matar da mijinta ya bar duniya ko kuma suka rabu ta hanyar saki, inda yake cewa: idan mace ta tsaya har na tsawon shekara 1 ba ta yi aure ba domin girmama mijinta, kuma ta bukaci ta ci gaba da zama a gidansa to dole ne a samar da hanyar da ta dace da za ta rika biyan bukatun rayuwarta kuma babu wanda yake da hakkin korarta daga gidan mjinta. To amma idan ta bukaci ta yi Aure bayan cikar watanni hudu da kwanaki 10 to babu wanda yake da hakkin hanta yin Auren, kuma tana da yanci zabar ma kanta mijin da take so, a kan haka ne ma yake cewa su mutane mu'aminai baya ga biyan sadaki da suke yi a lokacin rabuwa to suna bada wata kyauta ga matayen nasu, domin ya rage musu wani bangare na damuwar da take ciki da karyewar zuciya. To yanzu kuma bari mu yi dubi game da darussan da zamu koya acikin wadannan ayoyin, Na farko: Musulunci ya bada muhimmanci sosai game da hakkokin mace a cikin iyali, kuma ya nuna wajibcin daukar nauyin rayuwarta hattama bayan mutuwar mijinta ko kuma bayan rabuwarsu. Na biyu: Mace tana da hakki wajen zabarma kanta mijin da take so da ya dace da ita kuma dole ne a kare mutuncinta a cikin iyali.

To sai mu sake gyara zama domin sauraran ayata ta 243 da kuma 244 a cikin suratul bakra kamar haka:

أَلَمْ تَرَ إِلَى الَّذِينَ خَرَجُواْ مِن دِيَارِهِمْ وَهُمْ أُلُوفٌ حَذَرَ الْمَوْتِ فَقَالَ لَهُمُ اللّهُ مُوتُواْ ثُمَّ أَحْيَاهُمْ إِنَّ اللّهَ لَذُو فَضْلٍ عَلَى النَّاسِ وَلَـكِنَّ أَكْثَرَ النَّاسِ لاَ يَشْكُرُونَ{243} وَقَاتِلُواْ فِي سَبِيلِ اللّهِ وَاعْلَمُواْ أَنَّ اللّهَ سَمِيعٌ عَلِيمٌ{244}

Shin, ba ka gani ba, zuwa ga wadanda suka fita daga gidãjensu, alhãli kuwa sũ dubbai ne, dõmin tsõron mutuwa? Sai Allah Ya ce musu: "Ku mutu." Sa'an nan kuma Ya rãyar da su, lalle ne Allah, hakĩka Ma'abũcin falala a kan mutãne ne, kuma amma mafi yawan mutãne bã su gõdewa Kuma ku yi yãki a cikin hanyar Allah, kuma ku sani cewa lalle ne, Allah Mai jĩ ne, Masani.

Da farko wannan ayar ta kawo kisssar wasu mutane ne da ba'a shirye suke su kare addininsu daga farmakin makiya ba, wanda saboda tsoron mutuwa ma suka tsere daga gadajensu amma domin Allah ya nuna musu cewa mutuwa ba wai a filin daga take ba ka wai domin ako ina ma suke tana iya riskar mutum, sai All. ya kashe su kana kuma ya sake rayasu domin su zama darasi ga na gaba. Akan haka ne yake Magana da musulmai cewa ku koyi darsi akan wannan abin da ya faru kum ku sani cewa gujema yaki ba yana nufin kujema mutuwa ba ne, domin gudun da suka yi ya zama sanadiyar saukar musu da azabar ubangiji don haka kada ku saurarama makiya Addinin ubangiji kuma kusani cewa Allah yana sane da dukkan wahalhalun da kuke fuskanta sakamakon jihadi da kuke yi da makiya kuma da sannu za'a basu ladan abin da suka aikata. To a wadannan ayoyin zamu iya koyon darussa kamar haka, Na farko : sake rayar da mutane a ranar kiyama lamarine me yiyuwa da babu makawa acikinsa, domin tun a duniyar nan ma All. ya sake rayar da wasu mutane bayan ya kashesu, Na biyu: wata kila zaka iya tserewa daga filin daga amma gudu daga ikon Allah ko ganin dammarsa wato mashi'arsa ba shi da wata ma'ana. Na uku: Ana jihadi a musulunci ne domin kare addini Allah ba wai fadada fadin kasa ba da karfi ko kuma mamaya da zalunci. To kuma a karshen wannan shirin muna fatan All. Mdaukakin sarki ya sanya mu daga cikin bayinsa masu biyayya gare shi, a dukkan bangarorin rayuwa a cikin ibada ne kamar salla ko kuma wajen kare hakkokin iyali ta fuskacin zamantakewa ne ko kuma wajen kare ababe masu daraja na Addini, To masu saurare ganin lokacin da aka dibar mana ya kawo jiki sai a wani shirin in Allah ya sake sa da mu zaku ji mu dauke da ci gaban shirin amma kafin nan nake cewa wassAllah...

Suratul Bakara; Aya Ta 245-248 (Kashi Na 64)

Bismillahari rahamanir rahim Jama'a masu saurare Assalamu Alaikum barkanku da warhaka da kuma sake saduwa da mu a cikin shirin hannun ka mai sanda wanda acikinsa muke kawo muku bayanai game fassara ayoyin alkur'ani mai girma a cikin hanyar mafi sauki domin ya zama darasi garemu da fatan masu saurare za s kasance tare da mu domin jin cikakken shirin amma kafin nan bari mu saurari abin da aka yi mana tanadi a bisa fai-fai.

                • *****

To Madalla yanzu kuma bari mu saurari aya ta 245 acikin suratul bakra kamar haka.

مَّن ذَا الَّذِي يُقْرِضُ اللّهَ قَرْضاً حَسَناً فَيُضَاعِفَهُ لَهُ أَضْعَافاً كَثِيرَةً وَاللّهُ يَقْبِضُ وَيَبْسُطُ وَإِلَيْهِ تُرْجَعُونَ

Wãne ne wanda zai bai wa Allah rance, rance mai kyau, dõmin Ya ribanya masa, ribanyãwa mai yawa? Kuma Allah Shi ne ke damkewa, kuma yana shimfidawa, kuma zuwa a gare Shi ake mayar da ku.

Idan masu saurare suna iya tunawa ayar da muka karanto muku a cikin shirin da ya gabata ta yi bincike ne game da kiran da aka yi wa mu'aminai zuwa ga jihadi a tafarkin Allah to sai dai duk da yake cewa a jihadi ana bukatar sadaukar da kai, haka ma ana bukatar mutane su taimaka da kudin da Allah ya basu, don haka wannan ayar tana amfani da kalma mai kyau wato na bawa All. rance domin karfafa guiwar mu'aminai na su bada dukiyoyinsu a hanyar Allah, to sai dai bawa Allah rance bai takaita alokacin jihadi ba, domin duk wani bada taimako ko ciyar da marasa galihu a cikin alumma a kowane lokaci shi ma yana dai dai da hukumcin bawa Allah rance, kuma Allah zai nununka masa akan abin da ya bayar a duniya da lahira, domin kwanakinmu suna hannunsa ne, kuma duk abin da muka bayar akan hanyarsa ladanmu yana wajensa kuma zai saka mana alokacin da ya dace. Idan har mun san cewa yalwatawa ko kuntatawa a arzikinmu na yau da kullum duk yana hannun Allah ne to za mu ciyar a kan hanyarsa, cikin sauki ko kuma akalla za mu rika bada rance ga wasunsu, kuma basa yin gori ga kowa wajen aikata wannan aiki ,domin sun san cewa ladansu yana wurin Allah ne.

To yanzu kuma bari mu saurari aya ta 246 da ta 247 acikin wannan sura ta bakara kamar haka.

أَلَمْ تَرَ إِلَى الْمَلإِ مِن بَنِي إِسْرَائِيلَ مِن بَعْدِ مُوسَى إِذْ قَالُواْ لِنَبِيٍّ لَّهُمُ ابْعَثْ لَنَا مَلِكاً نُّقَاتِلْ فِي سَبِيلِ اللّهِ قَالَ هَلْ عَسَيْتُمْ إِن كُتِبَ عَلَيْكُمُ الْقِتَالُ أَلاَّ تُقَاتِلُواْ قَالُواْ وَمَا لَنَا أَلاَّ نُقَاتِلَ فِي سَبِيلِ اللّهِ وَقَدْ أُخْرِجْنَا مِن دِيَارِنَا وَأَبْنَآئِنَا فَلَمَّا كُتِبَ عَلَيْهِمُ الْقِتَالُ تَوَلَّوْاْ إِلاَّ قَلِيلاً مِّنْهُمْ وَاللّهُ عَلِيمٌ بِالظَّالِمِينَ{246} وَقَالَ لَهُمْ نَبِيُّهُمْ إِنَّ اللّهَ قَدْ بَعَثَ لَكُمْ طَالُوتَ مَلِكاً قَالُوَاْ أَنَّى يَكُونُ لَهُ الْمُلْكُ عَلَيْنَا وَنَحْنُ أَحَقُّ بِالْمُلْكِ مِنْهُ وَلَمْ يُؤْتَ سَعَةً مِّنَ الْمَالِ قَالَ إِنَّ اللّهَ اصْطَفَاهُ عَلَيْكُمْ وَزَادَهُ بَسْطَةً فِي الْعِلْمِ وَالْجِسْمِ وَاللّهُ يُؤْتِي مُلْكَهُ مَن يَشَاءُ وَاللّهُ وَاسِعٌ عَلِيمٌ{247}

Shin, ba ka gani ba zuwa ga wasu mashãwarta daga Bani Isrã'ĩla daga bãyan Mũsã, a lõkacin da suka ce ga wani annabi nãsu: "Nadã mana sarki, mu yi yãki a cikin hanyar Allah." Ya ce: "me yiyuwa ne idan an nada muku sarkin ba za ku yi yaki ba, Suka ce: "Kuma mene ne a gare mu, ba zã mu yi yãki ba, a cikin hanyar Allah, alhãli kuwa, hakika, an fitar da mu daga gidãjenmu da 'ya'yanmu?" To, a lõkacin da aka wajabta yãkin a kansu, suka jũya, sai kadan daga cikin su. Kuma Allah Masani ne ga azzãlumai. Kuma Annabinsu ya ce musu: "Lalle ne, Allah ya nada muku Dãlũta ya zama sarkinku." Suka ce: "Yãya ne sarauta zã ta kasance a gare shi, a kanmu, alhãli kuwa mũ ne mafi cancanta da sarauta daga gare shi, kuma ba a bã shi wata wadata ba daga dũkiya?" Ya ce: "Lalle ne, Allah Yã zãbe shi a kanku, kuma Ya kãra masa yalwa a cikin ilmi da jiki. Kuma Allah Yana bãyar da mulkinsa ga wanda Yake so, kuma Allah Mawadaci ne, Masani.

A Bayan Annabi Musa bani isra'il saboda son jindadin rayuwa da son jikinsu sun sake komawa karkashin hukumar dagutu, kuma sun rasa kasarsu, har sai da wani gungun daga cikinsu domin ya kubutar da su daga gudun hijira da samar musu da yanci ya yanke shawarar yin yaki don haka suka bukaci Annabin wannan lokacin da ya zabar musu jagora kuma kwamanda a cikinsu domin su yi yaki da dagutu, duk da yake cewa wannan Annabin yasan su bani Isra'ila ba ma'abota yaki ba ne saboda irin abubuwan da suka aikata a baya, amma don ya tabbatar da hujja akansu sai ya nada musu wani matashi talaka da ba'a san shi ba mai suna Daluta a matsayin jagoransu to da yake dama su suna jiran ne a nada daya daga cikin shuwagabannin alumma akan wannan mukami, don haka suka nuna rashin amincewarsu da Daluta a matsayin jagoransu, har ma suka yi da'awar cewa su kansu ma sun fi shi cancanta, domin yaki yana bukatar jarunta da karfi da sanin dabarun yaki amma daluta ya kasance ba shi da wata wadatar dukiya amma duk da haka All. Ya zabe shi ya bashi a matsayin sarkinmu, Abubuwan da za mu koya acikin wannan ayar su ne Na farko Jihadi domin kare kai, ko iyali ko kuma kare kasa shima wani nau'I ne na jihdi akan tafarkin Allah. Na biyu . Addini da siyasa tare suke tafiya ba'a rarrabe wa, a tsawon tarihi annabawan Allah sun yi kokari so sai wajen yanto mutane daga zalunci mahukumta azzalumai da kuma tabbatar da gwamnatin salihai, Na Uku ma'auinin gaskiya na shugabanci shi ne karfin jiki da na ilimi wajan gudanar da aiki ba kasancewa ma'abocin dukiya da suna da mukami ba.

Yanzu kuma bari mu saurari ayata 248 acikin suratul bakra kamar haka.

وَقَالَ لَهُمْ نِبِيُّهُمْ إِنَّ آيَةَ مُلْكِهِ أَن يَأْتِيَكُمُ التَّابُوتُ فِيهِ سَكِينَةٌ مِّن رَّبِّكُمْ وَبَقِيَّةٌ مِّمَّا تَرَكَ آلُ مُوسَى وَآلُ هَارُونَ تَحْمِلُهُ الْمَلآئِكَةُ إِنَّ فِي ذَلِكَ لآيَةً لَّكُمْ إِن كُنتُم مُّؤْمِنِينَ

Kuma annabinsu ya ce musu: "Lalle ne alãmar mulkinSa ita ce akwatin nan ya zo muku, a cikinsa akwai natsuwa daga Ubangijinku da sauran abubuwan da Gidan Mũsã da Gidan Hãrũna suka bari malã'iku suna dauke da shi. Lalle ne a cikin wancan akwai alãma a gare ku (ta nadin Dãlũta daga Allah ne) idan kun kasance mãsu ĩmãni."

Sai 'lin da bani isra'ila mabaota taurinkai suka ki amincewa da jagorancin Daluta sai annabinsu da yake kokarin gamsar da su domin su mika wuya ga jagoran da Allah. Ya zabarmusu, sai yace ku sani cewa Allah madaukakin sarki zai bude muku akwati mai tsarki na bani isra'la ta hannun Daluta, kumashi ne akwatin da mahaifiyar Annabin musa ta sanya jaririnta a ciki kuma ta sanya ta acikin tekun Nilu bisa umarnin ubangiji domin ya tsira daga hannun yan bangan fir'auna amma da yake akwatin ya fada a hannun fir'auna ne da kansa sai kauna Annabi musa ya shiga zuciyar fir'auna da matarsa don haka sai suka rike shi a matsayin da, an boye wannan akwatin a fadar fir'auna ne lokacin da Annabi musa ya kai matsayin Annabta sai ya sanya allunan attaura a ciki, don haka lokacin da zai yi tafiya sai ya sanya wasu abubuwa na tarihi a ciki ya mika shi ga alummarsa, kuma wannan akwatin tana da tsarki sosai a tsakanin bani isra'ila wanda a lokacin yakukka da aka yi kwamandojinsu sun kan dauki wannan akwatin domin sojojinsu su samu natsuwa da karfin zuciya amma daga karshe wannan akwatin ya fada hannun makiya, kuma ya jefa bani isra'ila cikin damuwa har zuwa zamanin Daluta, wanda bisa taimakon ubangiji ya sake dawowa da bani israila shi, wanda hakan ya sanya su suke alfahari. A karshen shirin namu muna fatan Allah ya sanyamu cikin wadanda za su bada jininsu tare da sadaukar da dukiyarsu a hanyar kare addininsu da kasarsu kuma ya ba mu taufiki wajen zaben jagorori wadanda za su jagoranci alumma su kasance mutane da suka dace ba ma'abota son duniya mai karewa ba . to kuma anan shirin namu zai kamala sai a wata saduwar amma kafin nan nake cewa wassallamu Alaikum warahammm

Suratul Bakara; Aya Ta 249-252 (Kashi Na 65)

Bismillahir rahamanir rahim Jama'a masu saurarre Assalamu Alaikum barkanku da warahaka da kuma sake saduwa damu a cikin wani sabon shiri na hanunka mai sanda wanda muke kawo muku fassarar ayyoyin alkur'ani mai garima domin su zama darasi garemu baki daya, idan masu suarare suna iya tunawa a shirin da ya gabata muna bayani ne kan kissar zaben Daluta da aka yi a matsayin kwamandan bani isra'ila, sai lokaci ya yi mana halinsa yanzu shirin na mu zai ci gaba daga inda muka kwana sai a biyo mu sannu a hankali.

          • *********

To Madalla yanzu kuma sai mu saurari abin da aya ta 249 acikin suratul bakra take cewa.

فَلَمَّا فَصَلَ طَالُوتُ بِالْجُنُودِ قَالَ إِنَّ اللّهَ مُبْتَلِيكُم بِنَهَرٍ فَمَن شَرِبَ مِنْهُ فَلَيْسَ مِنِّي وَمَن لَّمْ يَطْعَمْهُ فَإِنَّهُ مِنِّي إِلاَّ مَنِ اغْتَرَفَ غُرْفَةً بِيَدِهِ فَشَرِبُواْ مِنْهُ إِلاَّ قَلِيلاً مِّنْهُمْ فَلَمَّا جَاوَزَهُ هُوَ وَالَّذِينَ آمَنُواْ مَعَهُ قَالُواْ لاَ طَاقَةَ لَنَا الْيَوْمَ بِجَالُوتَ وَجُنودِهِ قَالَ الَّذِينَ يَظُنُّونَ أَنَّهُم مُّلاَقُو اللّهِ كَم مِّن فِئَةٍ قَلِيلَةٍ غَلَبَتْ فِئَةً كَثِيرَةً بِإِذْنِ اللّهِ وَاللّهُ مَعَ الصَّابِرِينَ

Sannan lokacin da Daluta ya fita da rundunarsa sai yace hakika Allah zai jarrabeku da korama, duk wanda ya sha daga gareta to baya daga jama'ata, wanda kuma bai dandana ta ba to hakika shi yana daga jama'ata sai dai wanda ya dan kamfata sau daya da hannunsa, sai suka sha daga gareta sai kadan daga cikinsu , Sa'anan yayin da ya ketara shi da wadanda suka bada gaskiya da shi sai suka ce ba mu da iko akan jaluta da rundunarsa a yau, sai wadanda suka sakankance cewa su lallai za su sadu da All. Suka ce sau da yawa yan kungiyar kadan ta rinjayi kungiya mai yawa da yardar Uabnagiji., Allah kuma yana tare da masu hakuri.

A shirin mu da ya gabata mun bayyana cewa lokacin da Allah Madaukakin sarki ya zabi Daluta a matsayin jagoran bani isra'ila sai manyansu suka nuna cewa ba'a shirye suke ba su karbe shi a matsayin jagora ba, sai suka bijiro da wani dalili mara karfi domin tserema yaki. To a mataki na gaba bangaren da suka amince dashi a matsayin jagora sai suka fita wajen gari tare da shi, to domin ya gwada iyakar cika alkawarinsu da biyayyarsu gare shi sai Daluta ya sanya wata korama ta zama wajen da zai gwadasu, sai yace : Magoya bayana na gaskiya su ne wadanda duk da kishirwar da suke ji amma ba za su cika cikinsu da wannan ruwan ba, za su sha kamfato daya da hannunsu. To a nan wannan ayar tana cewa ne a wannan jarabawar akwai mutane da dama sa duka fadi wanda lokacin da suka ga ruwa sai kishi ya yi galaba a akansu suka kasa yakar kishin ruwansu, kuma a mataki na uku suka kasa tunkarar makiya suka nuna gazawa a gaban rundunar Jaluta, sai dai mu'aminai kawai wadanda suke da imani na gaskiya, kuma su ne suka tsaya akan kafafunsu basu bari yawan da rundunar makiya suke da shi ba ya sanya musu tsoro a zuciya.

To a nan akwai darussa da za mu iya koya a cikin wannan aya na farko yana da kyau mu sani cewan abubuwan ci da sha suna daga cikin jarabawar ubangiji gare mu, ba wai akan na haram ba kawai, wani lokacin ma hatta abubuwa na halal yana da kyau mu nisancesu domin a bambance tsakanin mabiyan jagoran alummar musulmi na hakika da wadanda bana hakika ba. Na biyu Imani da ranar lahira da alkawuran ubangiji yana kara ma mutum karfin zuciya wajen tunakarar matsaloli da wahalhalu. Na uku abin da yake da muhimmanci a lokacin gwagwarmaya shi ne juriya da tsayin daka akwai masu irkirari da yawa game da yaki da dagutu kan abin da ya faru tsakanin Daluta da Jaluta, amma sai ga shi adadi kadan ne suke shirye su tsaya kyam wajen tunkarar makiya.

To yanzu kuma bari mu saurari aya ta 250 a cikin suratul bakra kamar haka.

وَلَمَّا بَرَزُواْ لِجَالُوتَ وَجُنُودِهِ قَالُواْ رَبَّنَا أَفْرِغْ عَلَيْنَا صَبْراً وَثَبِّتْ أَقْدَامَنَا وَانصُرْنَا عَلَى الْقَوْمِ الْكَافِرِينَ

Lokacin da suka yi fito na fito da Jaluta da rundunarsa sai suka ce ya ubangijinmu ka zubo mana hakuri ka tabatar da dugaduganmu ka kuma taimake mu akan jama'ar kafirai.

kamar yadda muka fadi ne mutanen bani Isra'ila lokacin da suka ga rundunar Jaluta sai suka firgita, sai mu'minai na hakika ne kawai suka tsaya domin yin yaki, amma sun sani cewa dab a don taimakon ubangiji ba da ba su yi galaba a kan runduna mai karfi irin wannan ba, don haka suka nemi taimakon ubangiji da hakuri da juriya akan dukkan wahalhalun yaki da kuma tsayawa kyam a gaban makiya. Wannan ayar tana koyar damu cewa Addu'a tare da kokari da motsi suna tafiya daidai ne, ba wai takaita da yin addu'a ba kawai ba tare da kokari ba, dakarun Daluta sun bayyana a filin daga kana suka roki ubangiji ya basu nasara. Na biyu: hadafin ma'abota Imani shi ne gaskiya ta yi nasara akan karya, ba wai neman suna ko kuma ace wata alumma ko wani jinsi yafi wani ba, don haka ne ma rundunar Daluta ta roki All ya ba su nasara akan kafirai.

Yanzu kuma lokaci ya yi da zamu gyara zama domin mu saurari a ya ta 251 da kuma ta 252 a cikin suratul bakra kamar haka.

فَهَزَمُوهُم بِإِذْنِ اللّهِ وَقَتَلَ دَاوُودُ جَالُوتَ وَآتَاهُ اللّهُ الْمُلْكَ وَالْحِكْمَةَ وَعَلَّمَهُ مِمَّا يَشَاءُ وَلَوْلاَ دَفْعُ اللّهِ النَّاسَ بَعْضَهُمْ بِبَعْضٍ لَّفَسَدَتِ الأَرْضُ وَلَـكِنَّ اللّهَ ذُو فَضْلٍ عَلَى الْعَالَمِينَ{251} تِلْكَ آيَاتُ اللّهِ نَتْلُوهَا عَلَيْكَ بِالْحَقِّ وَإِنَّكَ لَمِنَ الْمُرْسَلِينَ{252}

Sai suka karyasu da yardar Allah Dawuda ya kashe Jaluta All. Kuma ya ba shi mulki da hikima, ya sanar da shi daga abin da yaso, da ba don kariyar Allah daga sharrin wadansu mutane akan wadansu ba to da kasa ta baci . sai dai Allah ma'abocin falala ne ga talikai. Wadancan ayoyin Allah ne muke karanta maka su da gaskiya hakika kai kuwa kana cikin manzanni.

To daga karshe dai kokarin da mu'aminai suka yi da taimakon ubangiji ya sanya wadannan mutanen yan kalilan sun yi galaba akan runduna mai karfi, kuma wani matashi me karancin shekaru mu'amini gwarzo mai suna Dawud ne ya kashe jagoran makiya. Don haka bisa la'akari da gwarzontaka da imani da ya nuna sai Allah madaukikin sarki ya kai shi zuwa ga matsayi na Annabta kuma ya sanar da shi ilimi da hikima kana ya ba shi izza da kwarjini wanda Annabi suleman ma yana daga cikin yayansa, An kawo wannan kissar acikin aya ta 5 domin karfafa ruhi da kuma gargadin musulmai da suka bar gidajensu a makka a lokacin su yan kalilan ne ba su da dukiya da kudi, kuma suna bayyanawa mushrikan makka cewa menene Muhammad yake da shi na fifiko da har zai zama Annabinmu, alhali muna da mutane masu gwarzantaka da karfi da yawa kai da duk wani abu da ake bukata mutum ya samu a cikin makka muna da shi.. A nan za mu iya koyan cewa so da yawa idan mutum bai nuna irin baiwar da yake dashi ba to ba ya zamatowa cikin wadanda ludfin ubangiji na musamman yake lullube shi, Dawud ta hanyar kokari a tafarkin Allah Ya kai zuwa ga matsayi na Annabta, Na biyu, idan jihadi da kafirai ba wajibi ba ne to da fasadi ya cika kasa, ka ga kenan da bai kamata mu damu da kashe maujahidai a akan tafarkin Allah ba. Na uku wannan yasa mun koyi cewa akwai wasu abubuwa da suke taimakawa wajen samun nasar su ne. 1 Samun shugaba da ya dace kuma jarumi. 2 samun magoya bayan mua'aminai. 3 dogaro da karfin Allah 4 Hakuri da juriya. 5 sanya Allah a zuciya a lokacin yaki. To daga karshe muna muku bankawana sai a wata saduwar idan mai kowa mai komai ya kaimu za ku ji mu dauke da wani sabon shirin amma kafin nan ni dana kasance tare da ku nake cewa wassalamu Alaikum wa raham…

Suratul Bakara; Aya Ta 253-255 (Kashi Na 66)

Bismillahir rahamanir rahim Jama'a masu saurare Assalamu Alaikum barkanku da warhaka da kuma sake saduwa damu a cikin wani sabon shiri na hannunka mai sanda wanda a cikinsa muke kawo muku fassarar ayoyin alkur'ani mai girma kana daga bisani mu yi sharhi akan su, yadda za su zama abin koyi garemu domin samun sa'adar duniya da lahira. Sai dai kafin mu shiga cikin kwaryar shirin bari mu saurari abin da aka tanadar mana

            • ****

To yanzu kuma bari mu saurari aya ta 253 a cikin wannan sura ta bakra kamar haka.

تِلْكَ الرُّسُلُ فَضَّلْنَا بَعْضَهُمْ عَلَى بَعْضٍ مِّنْهُم مَّن كَلَّمَ اللّهُ وَرَفَعَ بَعْضَهُمْ دَرَجَاتٍ وَآتَيْنَا عِيسَى ابْنَ مَرْيَمَ الْبَيِّنَاتِ وَأَيَّدْنَاهُ بِرُوحِ الْقُدُسِ وَلَوْ شَاء اللّهُ مَا اقْتَتَلَ الَّذِينَ مِن بَعْدِهِم مِّن بَعْدِ مَا جَاءتْهُمُ الْبَيِّنَاتُ وَلَـكِنِ اخْتَلَفُواْ فَمِنْهُم مَّنْ آمَنَ وَمِنْهُم مَّن كَفَرَ وَلَوْ شَاء اللّهُ مَا اقْتَتَلُواْ وَلَـكِنَّ اللّهَ يَفْعَلُ مَا يُرِيدُ

Wadancan Manzannin mun fifita sashinsu akan sashi daga cikinsu akwai wanda Allah ya yi Magana da shi ya kuma daukaka darajojin wadansunsu, muka kuma bawa isan dan maryam mu'ajizozi mabayyana, muka kuma karfafa shi da ruhi mai tsarki wato mala'ika jibril da kuwa Allah Yaso da wadanda suka zo bayansu da ba su yi yake-yake ba, bayan mu'jizozi wato bayyana ta zo musu sai dai suna sassabawa da junansu, daga cikinsu akwai wadanda suka bada gaskiya daga cikinsu kuma akwai wadanda suka kafirta, da Allah ya so da basu yi yake-yake ba sai dai kum Allah yana aikata abin da yake so.

Ayar da ta gabata ta yi ishara game da wannan cewa Allah madaukakin sarki ya bawa Dawud (As) hikima da mulki, don haka wannan ayar za ta yi ishara ne game da banbamcin matsayin Annabawa inda take cewa : ko shakka babu dukkan Annabawan Allah ba a kan mataki daya suek ba, wasu sun fi wasunsu fifiko domin Annabi Musa As ya yi Magana da Allah kai tsaye ba tare da wani shamaki ba, ko kuma Annabi isa an karfafa da mala'ika jibril. Don haka wannan ayar tana bayani ne game da sunnar Allah mai muhimmanci, data shafi mutane, yana cewa mutane suna da yanci wajen zabar hanyar da suke son bi, ko dai su yi imani ko kuma su zama mushrikai, su ki yin imani da wannan Annabin ko kuma su yi imani da sakon da wancan Annabin yake dauke da shi, ko shakka babu idan da Allah ya so zai iya hana sabanin da rashin jituwa tsakanin mutane kuma ya tilastama dukkansu bin hanya daya, amma sunnar Allah ta tafi akan cewa ko dai mutane su karbi Addini ko kuma su ki karba amma da zabi ya rage na su . To a wannan ayar ma akwai darrussan da za mu iya koya na farko Addinin yana da kima, kuma yana da kyau a karbe shi bisa zabi, saboda haka sabanin tsakanin mutane, wani lamari ne da aka saba da shi da yake karkashin zabinsu. Na biyu: Allah Madaukakin sarki yana aiko Annabawa ne da dalilai bayyanannu don haka rashin karbar sakon daga bangaren wasu mutane yana tasowa ne sakamakon son zuciyarsu wasu kuma saboda jahilci da rashin bayanai.

Yanzu kuka bari mu saurari Aya ta 254 cikin wannan sura ta Bakara kamar haka:

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُواْ أَنفِقُواْ مِمَّا رَزَقْنَاكُم مِّن قَبْلِ أَن يَأْتِيَ يَوْمٌ لاَّ بَيْعٌ فِيهِ وَلاَ خُلَّةٌ وَلاَ شَفَاعَةٌ وَالْكَافِرُونَ هُمُ الظَّالِمُونَ

Ya ku wadanda kuka bada gaskiya ku ciyar daga abin da muka azurtaku tun kafin wata rana ta zo wadda babu fansar kai babu ceto acikinta kafirai kuma su ne Azzalumai.

Wannan ayar tana gargadin mu'minai ne da tun anan duniya su ci amfanin damar da suke da shi, su tanadi guzuri domin lahirarsu domin su yi mua'mala da Ubangiji, ku ciyar da mutane daga dukiyoyinku, domin a kiyama babu abokantaka da za ta iya zama sanadin samun sa'ada ko kubutar da ku daga kotun da kuka siya da kanku, kada ya sanya fatansa akan abokai da magabatansa, domin babu wani daga cikinsu da zai iya tabuka masa komai, kuma babu shiga tsakani babu kuma ceto. To anan darussan da za mu koya a cikin wannan ayar su ne : Na farko akwai wasu abubuwa muhimmai da Allaha ya zana su domin ya kara karfafa ruhin ciyarwa a zukatanmu, su ne A dukkan abin da kake da shi ba kai ne ka samar da shi ba mu ne muka baka. B ka ciyar daga abin da muka azurtaka da shi gwargwadon iko ba wai da dukkan dunkiyarka ba. C wannan ciyarwar don lahirarka yafi akan dukkan abokanka da masoyanka.

To yanzu kuma bari mu saurari aya ta 255 a cikin wannan sura ta Bakra kamar haka:

اللّهُ لاَ إِلَـهَ إِلاَّ هُوَ الْحَيُّ الْقَيُّومُ لاَ تَأْخُذُهُ سِنَةٌ وَلاَ نَوْمٌ لَّهُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الأَرْضِ مَن ذَا الَّذِي يَشْفَعُ عِنْدَهُ إِلاَّ بِإِذْنِهِ يَعْلَمُ مَا بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَمَا خَلْفَهُمْ وَلاَ يُحِيطُونَ بِشَيْءٍ مِّنْ عِلْمِهِ إِلاَّ بِمَا شَاء وَسِعَ كُرْسِيُّهُ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضَ وَلاَ يَؤُودُهُ حِفْظُهُمَا وَهُوَ الْعَلِيُّ الْعَظِيمُ

Allah babu wani sarki abin bautawa da gaskiya sai shi rayayye tsayyye da kansa baya neman taimakon kowa, gyangyadi baya daukarsa, kamar yadda barci baya kama shi, abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin kassai duka nasa ne babu wanda yake ceto a wurinsa sai da izininsa yana sane da abin da ke gabansu da abin da ke bayansu ba sa kuma sanin wani abu daga iliminsa sai abin da yaso kursiyyunsa ta yalwaci sammai da kassani, kuma kiyayesu baya yi masa nauyi shi ne kuma madaukaki mai girma.

A wannan ayar. saboda zuwan kalmar Kursiyu ne acikinta a ke kiranta da suna ayar kursiyyu, wadda take bayyana kadaitakar Allah Madaukakin sarki, a cikin zatinsa da siffofinsa, Tauhidi shi ne tushen sakon da dukkan addinan sama suke dauke da shi, Tauhidi shi ne kashin bayan tsirar dan Adam daga bautama gumaka da wanin Allah , Tauhidi hanyar yanci da yantattu ne, da kuma kubuta daga takurar dagutu da Azzaluman mahukumta, da kuma isa zuwa ga sa'ada da samun dacewa. Kalmar la'ilaha illallah kalmace sananna da take shiga kunne da zuciyar duk wani jariri musulmu bayan haihuwarsa da take ba shi natsuwa da kwanciyar hankali, kuma kullum aka kira salla tana kara samun wurin zama ne a zuciyarsa Lailahaillallah tana nufin bayan shi babu wani mahaluki da ya cancanci a bautamasa, kamala da jalala duka sun kebanta da shi ne, bayan shi babu wani da yake da kamala da buya irin ta shi, kuma shi muke bautama kuma shi ne muke so. Rayuwa ta hakika itace wadda ba ta karewa kuma bayan shi dukkan abin da ke da samuwa mai karewa ne, shi ne kawai wanda bai jingina da kowa ba don haka bayan shi kowa mabukaci ne zuwa gareshi, baya samun rauni ko gajiya kuma ba ya barci ko gyangyadi wanda idan da zai bar duniya da kanta koda da kiftawar ido ne to babu abin da zai yi saura, shi ne mamallakin samuwa baki daya, kuma dukkan abin da ke cikinta suna karkashin ikonsa ne, to anan me yasa abin halitta yake bautawa waninsa? me yasa baya bautama mahalicci da mamallakinsa amma yake neman wani abu wajen wasu ba shi ba? Ko da ake mushrikai sun yarda cewa Allah Shi ne mahaliccin duniya amma suna ganin gumaka a matsayin masu cetonsu, don haka wannan ayar take fadin cewa su rabu da abin da suka kerawa suke ganinsu a matsayin mafaka garesu su sani cewa ceto yana hanun masoyansa ne kawai, su ma a lokacin da Allah ya basu Izini, karshen wannan ayar ta siffata ilimi da kudurar ubangiji da bata da karshe a matsayin kursiyyu da take nufin gadon mulki domin mu fahimta cewa bawai ubangiji ba wai mahaliccin samuwa ba ne kawai, a'a shi ne mai iko akan dukkan komai kuma babu wani abu da zai kasance a wajen kudurarsa da ikonsa. Don haka a wanan ayar zamu koyi cewa Allah shi ne abin bautawa da gaskiya kuma dukkan iko da ilimi da kamala sun takaita gare shi . kuma duk wani rauni ko nakasu ko aibi sun barranta gareshi. To kuma da yake lokacin da aka dibarma shirin ya kawo jiki bari in dasa aya anan sai a wata saduwar zaku ji mu dauke da ci gaban shirin amma kafin nan nake cewa wasallamu Alaikum warahamtullah….

Suratul Bakara; Aya Ta 256-259 (Kashi Na 67)

Bismillahir rahamanir rahim Masu sauraro barkanmu da sake saduwa da ku. To a yau ma muna tare ne da ku a cikin wannan shirin da mu ke kawo muku tafsirin kur’ani mai girma . Za kuma mu fara ne daga aya ta 256 zuwa aya ta 257 a cikin suratul Bakara.

لاَ إِكْرَاهَ فِي الدِّينِ قَد تَّبَيَّنَ الرُّشْدُ مِنَ الْغَيِّ فَمَنْ يَكْفُرْ بِالطَّاغُوتِ وَيُؤْمِن بِاللّهِ فَقَدِ اسْتَمْسَكَ بِالْعُرْوَةِ الْوُثْقَىَ لاَ انفِصَامَ لَهَا وَاللّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ{256} اللّهُ وَلِيُّ الَّذِينَ آمَنُواْ يُخْرِجُهُم مِّنَ الظُّلُمَاتِ إِلَى النُّوُرِ وَالَّذِينَ كَفَرُواْ أَوْلِيَآؤُهُمُ الطَّاغُوتُ يُخْرِجُونَهُم مِّنَ النُّورِ إِلَى الظُّلُمَاتِ أُوْلَـئِكَ أَصْحَابُ النَّارِ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ{257}

“Babu tilasci acikin addini. Hakika shiriya ta bayyana daga bata. Wanda duk ya kafircewa dagutu ya yi imani da Allah to hakika ya yi riko da igiyar Allah mai kwari wacce ba tsinkewa. Allah mai ji ne kuma masani. Allah shi ne mai jibintar lamarin wadanda su ka yi imani yana kuma fitar da su daga cikin duhu zuwa ga haske. Wadanda su ka kafirta kuwa dagutu ne majibincin lamarinsu yana fitar da su daga haske zuwa duhu. Wadancanenka su ne ‘yan wuta, za su dawwama a cikinta”

Imani wani lamari ne a cikin zuciya wanda babu yadda za a iya cusawa mutum shi da karfi- Ta hanyar dalili da kyawawan halaye da wa’azi ne ake cusawa mutum akida da sa shi yin imani da ita. Domin shiriyar da mutane ne Ubangiji madaukaki ya aiko da annabawa da littatafai domin su shiryar da mutane akan tafarkin gaskiya, a daya gefen kuma ya baiwa mutane zabi saboda su zabi abinda su ke so. A bisa wannan dalilin hatta annabawa ba su yi wa mutane tilas akan su yi imani- domin kuwa imanin da aka tilasta mutum akanshi ba shi da wata kima. Idan mutum ya fice daga karkashin ikon dagutu ya zama cikakken bawan Allah, to wannan mutumin yana a karkashin jibintar lamari daga Allah, kuma Ubangiji ne mai jibintar tafiyar da lamurransa, ta yadda a kodayaushe a rayuwarsa ta ke tafiya a karkashin shiriyar Allah, kuma ya ke kiyaye shi daga dukkan hatsari. Amma a daya gefen kuwa, wanda duk ya damfaru da wani wanda ba Ubangiji ba, to ya kwana da sanin cewa ya jingina ne ajikin duhu da shirka da camfi, kuma babu wata hanya ta gaskiya da haske da ta saura a gabansa.

Abubuwan da za mu koya daga wadannan ayoyin su ne: 1-Addini yana da kimar da ta sa ya ginu bisa harsashin ilimi da sani kuma ya zamana an shige shi ne bisa zabi. 2-Hanyar gaskiya- guda daya ce- amma hanyoyin bata suna da yawa, saboda haka ne a cikin kur’ani aka yi amfani da sigar guda tilo akan haske. Aka kuma yi amfani da sigar jam’i akan Kalmar duhu. 3-Hanyar gaskiya, haske ce kuma ginshikin kamala- yunkuri ne mai cike da fata da kuma nutsuwa. Amma hanyar bata, duhu ce kuma ginshikin kauce hanya, jahilci ce da rashin nutsuwa.

Yanzu kuma za mu saurari aya ta 258 acikin suratul Bakara.

أَلَمْ تَرَ إِلَى الَّذِي حَآجَّ إِبْرَاهِيمَ فِي رِبِّهِ أَنْ آتَاهُ اللّهُ الْمُلْكَ إِذْ قَالَ إِبْرَاهِيمُ رَبِّيَ الَّذِي يُحْيِـي وَيُمِيتُ قَالَ أَنَا أُحْيِـي وَأُمِيتُ قَالَ إِبْرَاهِيمُ فَإِنَّ اللّهَ يَأْتِي بِالشَّمْسِ مِنَ الْمَشْرِقِ فَأْتِ بِهَا مِنَ الْمَغْرِبِ فَبُهِتَ الَّذِي كَفَرَ وَاللّهُ لاَ يَهْدِي الْقَوْمَ الظَّالِمِينَ

“Ashe baka yi dubi zuwa ga wanda ya yi jayayya da Ibrahim ba acikin Ubangijinsa, don Allah ya ba shi mulki.? Yayinda Ibrahim ya fada masa cewa Ubangjina ne ya ke rayawa da matarwa. Sai ya ce: Ni ma ina rayawa da matarwa. Sai Ibrahim ya ce Allah yana fito da rana daga gabas ka zo da ita daga yamma, sai wanda ya kafirta ya yi kus. Allah ba ya shiryar da mutanen da su ke azzalumai.”

Kamar yadda ya zo a cikin tarihi Namrudu yana daga cikin sarakuna Babil wanda ya riya cewa shi Ubangiji ne, kuma yana daukar mutane a matsayin bayinsa. Da ya ji labarin cewa annabi Ibrahim yana kiran mutane zuwa bautar Allah makadaici sai ya kira shi yana tattaunawa da shi ya fada masa cewa; Duk wani abu da ubangijinka ya ke yi to nima ina aikatawa. Da fari annabi Ibrahim ya fara yin Magana akan batun mutuwa da rayuwa ya kuma yi ishara da cewa a hannun Ubangiji su ke. Namrud ya bada umarnin aka kawo ‘yan fursuna guda biyu, ya saki guda sannan ya sa aka kashe guda, ta wannan hanyar ne ya riya cewa ni ma ina iya kashe wanda na ga dama kuma in raya wanda na ga dama. Tare da cewa wannan aikin nashi soki burutsu ne, amma annabi Ibrahim ya yi ishara da fitowar rana daga gabas wanda yana daga cikin aikin Allah mai tsari, sannan ya tabaye shi cewa ko za ka iya fito da rana daga yamma? Namrud ya kasa bada jawabi ya fada cikin rudani. Sai dai duk da haka ba a shirye ya ke ya karbi gaskiya ba, kuma a bisa wasu ayoyin kur’ani ya bada umarni da a jefa annabi Ibrahim a cikin wuta. Acikin wadannan ayoyin za mu koyi abubuwa kamr haka. 1-Idan mutum ba shi da shiriya to idan ya zama mai mulki maimakon ya zama bawan Allah sai girman kai ya shige shi ya riya cewa shi ubangiji ne. 2-Annabawa suna kiran mutane ne ta hanyar dogaro da dalilai, amma wadanda su ke kan bata suna amfani da gurbatacce dalili da kuma sokoi burutsu.

Yanzu kuma za mu karanta aya ta 259 a cikin suratul Bakara.

أَوْ كَالَّذِي مَرَّ عَلَى قَرْيَةٍ وَهِيَ خَاوِيَةٌ عَلَى عُرُوشِهَا قَالَ أَنَّىَ يُحْيِـي هَـَذِهِ اللّهُ بَعْدَ مَوْتِهَا فَأَمَاتَهُ اللّهُ مِئَةَ عَامٍ ثُمَّ بَعَثَهُ قَالَ كَمْ لَبِثْتَ قَالَ لَبِثْتُ يَوْماً أَوْ بَعْضَ يَوْمٍ قَالَ بَل لَّبِثْتَ مِئَةَ عَامٍ فَانظُرْ إِلَى طَعَامِكَ وَشَرَابِكَ لَمْ يَتَسَنَّهْ وَانظُرْ إِلَى حِمَارِكَ وَلِنَجْعَلَكَ آيَةً لِّلنَّاسِ وَانظُرْ إِلَى العِظَامِ كَيْفَ نُنشِزُهَا ثُمَّ نَكْسُوهَا لَحْماً فَلَمَّا تَبَيَّنَ لَهُ قَالَ أَعْلَمُ أَنَّ اللّهَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِير

“Ko kuma kwatankwacin wanda ya wuce ta wata alkarya da ta zama kufai sai ya ce ko ya za a yi Allah ya rayata bayan mutuwarta. Sai Allah ya matar da shin a tsawon shekaru dari sannan ya farkar da shi. Sai ya ce tsawon wane lokaci ka zauna anan? Sai ya ce rana guda ko rabin rana. Sai ya ce bari! ka zauna ne shekara dari ka yi dubi ga abincinka da abin shanka bai jirkita ba. Ka yi dubi ga jakinka, za mu sanya ka zama aya ga mutane, ka yi dubi zuwa ga kasusuwa da yadda za mu harhadasu mu kuma lullube su da nama. Yayinda gaskiya ta bayyana a gare shi sai ya ce, na san cewa Allah mai iko ne akan komai.”

Kamar yadda ya zo a cikin tafsirai wannan labarin ya faru da Uzair wanda daya ne daga cikin annabawan Banu Isra’ila. Yana wucewa ne ta wani gari da ya zama kufai, kuma duk da cewa yana da imani da Allah ya bukaci samun nutsuwar zuciya da Allah ya nuna masa yadda zai tada matattu a ranar kiyama. A cikin wannan labarin Ubangiji ya nuna kudurarsa, ta yadda kayan abincin da zai iya baci saboda gushewar tsawon shekaru dari, amma ba su baci ba, amma kashi wanda ya ke da kwari ya rududduge sannan ya sake komawa halinsa na farko bisa ikon Allah. Abinda ya fi muhimmanci shi ne shi ne shi kanshi Uzair wanda ya mutum na tsawon shekaru dari amma gangar jikinsa ba ta sauya ba, kamar mutumin da ya kwanta bacci ya farka.

Abubuwan da za mu koya a nan. 1-Rayar da matattu a ranar kiyamu abu ne mai yiyuwa-Ubangiji ya bada misali akan hakan a nan duniya. 2-Ubangiji yana nuna kudurarsa ta hanyoyi daban-daban a duniya saboda mutane su san cewa babu wani abu da wanda ya fi karfin kudurar Allah, saboda haka babu abinda zai sa a yi shakku akan ranar kiyama. A karshen wannan shirin muna yin ban kwana da ku masu sauraro, muna kuma sauraron ra’ayinku. Sai kuma wani shirin na gaba na tafsirin ayoyin kur’ani.

Suratul Bakara; Aya Ta 260-263 (Kashi Na 68)

Da sunan Allah mai Rahama Mai Jin Kai.

Masu sauraro barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shirin. Za kuma mu ci gaba da yin nazari akan ayoyin kur’ani mai girma, domin yi wa rayuwa kyakkyawar fahimta ta hanyar zancen Ubangiji. Kuma mu gina rayuwarmu akan wannan hakika. Acikin labarin annabi Uzair mun fahimci cewa bayan gushewar shekaru dari a mace Ubangiji ya sake raya shi a cikin wannan duniyar saboda ya zama wani misali da ke nuni da karfin kudurar Allah na raya matattu a ranar kiyama. A cikin wannan shirin za mu yi ishara da labarin annabi Ibrahim. Wata rana yana wucewa ta gefen gabar ruwa sai ya ci karo da matacciyar dabba wacce ta rududduge rabin jikinta yana cikin ruwa rabi kuma akan kasa. Dabbobin ruwa da kuma na doron kasa suna cikin jikin wannan dabbar. Da annabi Ibrahim ya ga abinda ya ke faruwa sai ya fara tunani akan cewa idan irin haka ta faru da gangar jikin mutum, kuma gangar jikinsa ta zama naman dabbobin, to ya za a yi wannan mutumin ya sake dawowa da jikinsa? Tare da cewa Ibrahim annabin Allah ne kuma wanda ya yi imani da rayuwa bayan mutuwa, ya roki Allah da ya nuna masa yadda raya matacce.

Aya ta 260 a cikin suratul Bakara tattaunawa ce tsakanin annabi Ibrahim da Ubangiji:

مَّثَلُ الَّذِينَ يُنفِقُونَ أَمْوَالَهُمْ فِي سَبِيلِ اللّهِ كَمَثَلِ حَبَّةٍ أَنبَتَتْ سَبْعَ سَنَابِلَ فِي كُلِّ سُنبُلَةٍ مِّئَةُ حَبَّةٍ وَاللّهُ يُضَاعِفُ لِمَن يَشَاءُ وَاللّهُ وَاسِعٌ عَلِيمٌ

“Yayinda Ibrahim ya ce, Ubangiji ka nuna mani yadda ka ke raya matattu. Sai ya ce ba ka bada gaskiya ba ne? sai ya ce na bada gaskiya sai dai ina yin tambaya ne don zuciyata ta nutsu: Sai ya ce ka dauki tsuntsye hudu ka tattarasu zuwa gare ka, sai ka sanya yankin kowane daga cikinsu akan dutse, sannan ka kira su za su zo maka a guje. Ka sani cewa Allah gagari buwayi ne ma’abocin hikima.”

Abinda annabin Ibrahim ya aikata kenan. Ya yanka tsuntsye guda hudu mabanbanta sannan ya cakuda namansu ya kuma rarraba su akan duwatsu goma sannan ya kirayi sunanyen tsuntsayen guda hudu. Bisa kudurar Allah bangarorin wadannan tsuntsayen sun taso daga kan duwatsu daban-daban suka hade su ka koma yadda su ke tun da fari sannan su ka zo wurinsa. Aannabi Ibrahim ya sami jawabin abinda ya ke tambaya. Abubuwan da mu ke koya daga cikin wadannan ayoyin. 1-Rayuwa bayan mutuwa za ta kasance ne da gangar jiki, kuma Ubangiji madaukaki shi ne mai iko da dokokin dabi’a, saboda haka babu matsala wajen sake hada gabobin jikin a ranar kiyama. 2-Mandiki da dalilai suna gamsar da hankali, amma zuciya bata gamsuwa sai ta sami nutsuwa, wanda hanyar kaiwa ga hakan shi ne lura da ni’imomi da kuma kudurar Allah.

Yanzu kuma sai aya ta 261.

مَّثَلُ الَّذِينَ يُنفِقُونَ أَمْوَالَهُمْ فِي سَبِيلِ اللّهِ كَمَثَلِ حَبَّةٍ أَنبَتَتْ سَبْعَ سَنَابِلَ فِي كُلِّ سُنبُلَةٍ مِّئَةُ حَبَّةٍ وَاللّهُ يُضَاعِفُ لِمَن يَشَاءُ وَاللّهُ وَاسِعٌ عَلِيمٌ

"Kwatankwacin wadanda su ke ciyarwa saboda Allah, daidai ya ke da kwayar hatsi wacce ta tsiro da zangarniya bakwai. A cikin kowace zangarniya akwai kwaya dari. Allah yana rubanyawa wanda ya so. Allah mai yalwa ne, masani.”

Wannan ayar tare da aya ta 14 suna Magana ne akan ciyarwa da kuma haramta riba. Kamar yadda mu ka sani acikin kowace al’umma kudaden shigar da mutane su ke sami ya banbanta. Kuma a cikin al’umma ana samun bala’o’in dabi’a irin su ambaliyar ruwa da girgizar kasa da fari da gobara wadanda su ke sa wasu mutanen su yi asarar abinda su ke da shi, ta yadda ci gaba da rayuwa ya ke yi musu wahala. A cikin hali irin wannan ina mafita ta ke? Shin mutane irin wadannan za a barsu su ci gaba da zama cikin bakin talauci? Ko kuwa za su mika hannuwansu ne su roki masu dukiya wadanda za su rika karbar ruwa a hannunsa har tsawon rayuwarsu? Bashi da ruwa yana daga cikin illolin tattalin arziki acikin al’umma, domin kuwa masu dukiya da su ke karbar riba suna kara yawan dukiyarsu ne, su kuma talakawa da su ke bada riba suna kara talauci, sakamako shi ne karuwar tazarar da ta ke tsakanin aji-aji na mutane acikin al’umma. Musulunci ya haramta riba, maimakon haka sai ya farfado da ruhin ‘yan’uwantaka a tsakanin musulmi, ya karfafa su da su rika ciyarwa akan tafarkin Allah. Ubangiji kuma yana fadin cewa wanda duk ya ciyar saboda Allah to zai zami kari wanda zai iya rubanyawa zuwa dari bakwai. Kai da ka ciyar za ka sami bunkasa haka nan kuma dukiyar da ka ciyar da ita za ta taimaka wajen ci gaban al’umma da kuma kawar da talauci. Abubuwan da za mu koya daga cikin wadannan ayoyin. 1-Ciyarwa da taimakawa mabukata idan ya kasance akan tafarkin Allah ne kuma da kyakkyawar niyya sannan kuma daga halartacciyar dukiya, to ba zai rage yawan dukiya ba, kuma zai taimaka wajen ci gaba da bunkasar al’umma. 2-Jin kan Allah bashi da iyaka, kowane mutum zai sami jin kan Ubangiji gwargwadon kokarinsa da dacewarsa.

Yanzu kuma za mu saurari ayoyi na 262 da 263 daga suratul Bakara.

الَّذِينَ يُنفِقُونَ أَمْوَالَهُمْ فِي سَبِيلِ اللّهِ ثُمَّ لاَ يُتْبِعُونَ مَا أَنفَقُواُ مَنّاً وَلاَ أَذًى لَّهُمْ أَجْرُهُمْ عِندَ رَبِّهِمْ وَلاَ خَوْفٌ عَلَيْهِمْ وَلاَ هُمْ يَحْزَنُونَ{262} قَوْلٌ مَّعْرُوفٌ وَمَغْفِرَةٌ خَيْرٌ مِّن صَدَقَةٍ يَتْبَعُهَا أَذًى وَاللّهُ غَنِيٌّ حَلِيمٌ{263}

“Wadanda su ke ciyar da dukiyarsu akan tafarkin Allah sannan kuma ba su bi abinda su ke ciyarwa da gori ko cutarwa ba to suna da ladansu a wurin Ubangijinsu kuma babu damuwa da bakin ciki a tare da su. “Magana kyakkyawa da yin gafara shi ne mafi alheri daga sadakar da cutarwa za ta biyo baya. Allah mai wadatarwa ne kuma mai hakuri.”

Ci gaban ayar da ta gabata wacce ta ke kiran mutane zuwa ga ciyarwa saboda Allah, to wannan ayar tana yin bayani ne akan hanyar mafi dacewa ta fadin cewa: Idan kun ciyar da mabukata to kada ku yi musu gori kuma kada ku aikata abinda zai bakanta musu. Mabukata ne su ke da falala akanku saboda karbar abinda ku ka basu da su ka yi domin kuwa za ku sami lada. Abubuwan da za mu koya daga wadannan ayoyin. 1-Mu zama masu lura acikin ayyukan da mu ke yi saboda Allah kada ya zamana mun fada cikin jiji da kai da yin gori, da za su iya kawar da kimar wadannan ayyukan. 2-Kiyaye mutuncin mumini ta hanyar biya masa bukatunsa na abin duniya, maimakon zubar da mutuncin wani mutum. A karshen wannan shirin muna rokon Allah da ya tsarkake ruhinmu daga rowa da kwadayi domin ya zama ya share fagen samar da halin baiwa da kyauta a tare da mu.

Suratul Bakara; Aya Ta 264-267 (Kashi Na 69)

Da sunan Allah mai Rahama mai Jin kai.

Masu sauraron wannan shirin na “Hannunka Mai Sanda’ barkanmu da sake saduwa da ku. Muna kuma tare da ku ne acikin wannan shirin wanda mu ke kawo mu ku fassarar ayoyin kur’ani mai girma. Da fatan za mu kasance a tare da mu domin jin shirin.

Yanzu za mu saurari ayoyi na 264 da 265 acikin suratul Bakara.

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُواْ لاَ تُبْطِلُواْ صَدَقَاتِكُم بِالْمَنِّ وَالأذَى كَالَّذِي يُنفِقُ مَالَهُ رِئَاء النَّاسِ وَلاَ يُؤْمِنُ بِاللّهِ وَالْيَوْمِ الآخِرِ فَمَثَلُهُ كَمَثَلِ صَفْوَانٍ عَلَيْهِ تُرَابٌ فَأَصَابَهُ وَابِلٌ فَتَرَكَهُ صَلْداً لاَّ يَقْدِرُونَ عَلَى شَيْءٍ مِّمَّا كَسَبُواْ وَاللّهُ لاَ يَهْدِي الْقَوْمَ الْكَافِرِينَ{264} وَمَثَلُ الَّذِينَ يُنفِقُونَ أَمْوَالَهُمُ ابْتِغَاء مَرْضَاتِ اللّهِ وَتَثْبِيتاً مِّنْ أَنفُسِهِمْ كَمَثَلِ جَنَّةٍ بِرَبْوَةٍ أَصَابَهَا وَابِلٌ فَآتَتْ أُكُلَهَا ضِعْفَيْنِ فَإِن لَّمْ يُصِبْهَا وَابِلٌ فَطَلٌّ وَاللّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ بَصِيرٌ{265}

“Ya ku wadanda ku ka yi imani kada ku bata sadarku da gori da cutarwa kamar wanda ya ke ciyar da dukiyarsa saboda ganin idon mutane, kuma bai yi imani da Allah ba da ranar lahira. Kwatankwacinsa shi ne falalen dutsen da kasa ta ke kansa, sai ruwa mai tsanani ya sauka akanta ya barta fayau, ba su da iko akan abinda su ka aikata, Ubangji baya shiryar da kafirai.”. “Kwatankwacin wadanda su ke ciyar da dukiyarsu saboda neman yardarm Allah da kuma karfafa kawukansu, tamkar gona ce a tudun jigawa wacce mamakon ruwa ya same ta, ta bada amfanin cikinta ninki biyu, idan kuma mamakon ruwa bai same ta ba to za ta yi kyawu. Allah yana ganin abinda ku ke aikatawa.”

Wadannan ayoyin guda biyu suna ci gaba da yin bayani ne akan ciyarwa wacce Allah ya ke umartar muminai da su yi. Da kuma misalai na nauo’in ciyarwa. Aikin da ya ke tattare da riya da nuna kai yana kama da kasa mai taushi da karkashinta dutse ne mai karfi, wanda babu yadda za a yi a kutsa shi. Sai kuma ciyarwar da ake yi saboda Allah ba domin saboda nuna kai ba ko kuma saboda burge mutane, ana yi ne bisa tsarkin niyya da kyakkyawar manufa, ya yi kama da kwayar hatsi wacce aka shuka acikin turbaya mai kyau, wanda ya ke habaka da bunkasa ya kuma fitar da rassa masu karfi. Abubuwan da mu ke koya acikin wadannan ayoyi. 1-Aikin kwarai yana da kima idan ya kasance a tare da kyakkyawar niyya kuma ba a bata shi daga baya. 2-Karfara siffofin kwarai a cikin ruhin mutum da yin aiki bisa kyakkyawar manufa da yi wa mutane hidima shi ne abinda Allah ya ke farin ciki da shi. 3-Riya da nuna kai a aiki yana nuni ne da rashin karfin imani da Allah da kuma ranar kiyama.

Yanzu kuma za mu karanta aya ta 266 a cikin suratul Bakara.

أَيَوَدُّ أَحَدُكُمْ أَن تَكُونَ لَهُ جَنَّةٌ مِّن نَّخِيلٍ وَأَعْنَابٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الأَنْهَارُ لَهُ فِيهَا مِن كُلِّ الثَّمَرَاتِ وَأَصَابَهُ الْكِبَرُ وَلَهُ ذُرِّيَّةٌ ضُعَفَاء فَأَصَابَهَا إِعْصَارٌ فِيهِ نَارٌ فَاحْتَرَقَتْ كَذَلِكَ يُبَيِّنُ اللّهُ لَكُمُ الآيَاتِ لَعَلَّكُمْ تَتَفَكَّرُونَ

“Shin dayanku yana gurin cewa yana da gona ta dabinai da inabi, koramu suna gudana a karkashinta, yana da dukkan ‘ya’yan itace a cikinta, alhali tsufa ya riske shi, yana da zuriya raunana, kuma guguwa ta same ta da wuta ta ke cikinta,ta kone kurmus. Haka nan Allah ya ke yi mu ku bayanin ayoyinsa ko za ku yi tunani.”

Wannan wani misali ne a aikace akan wadanda su ke yin aikin kwarai sannan kuma su gurbata shi da riya da gori da cutar da wasu. Ciyarwa da taimakawa mabukata yana a matsayin shuka bishiya ce a cikin lambu na al’umma wanda ya ke da bukatar aiki sosai domin ya samar da ‘ya’ya. Sai dai idan ba a sanya ido ana kula da wannan aikin na kwarai ba to acikin kankanen lokaci zai iya baci ya lalace. Ya zo acikin riwaya cewa annabi ya fadawa musulmi cewa ku rika ambaton Allah, domin kuwane ambaton Allah yana tsiro mu ku da bishiya acikin aljanna. Wani ya yi tambaya cewa: “Ashe kenan za mu sami lambuna masu yawa a cikin aljanna. Manzon Allah ya ce, da wannan harshen da ku ke ambaton Allah da shi za ku iya cin naman wani wanda zai zama wutar da za ta kone wannan lambun. A lahira da mutum ya ke da bukatuwa da ayyukan kwarai, ba zai ji dadin ganin cewa ayyukansa sun rushe ba saboda riya da gori. Abinda mu ke koya daga wannan aya. Kada ayyukan kwarai da mu ka yi su zamar mada dalilin jiji da kai domin kuwa sau da yawa munanan ayyuka yana lalata aikin kwarai. Gina lambu yana daukar lokaci mai tsawo amma acikin kankanen lokaci wuta za ta lalata shi.

Yanzu kuma za mu karanta aya ta 267 a cikin suratul Bakara.

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُواْ أَنفِقُواْ مِن طَيِّبَاتِ مَا كَسَبْتُمْ وَمِمَّا أَخْرَجْنَا لَكُم مِّنَ الأَرْضِ وَلاَ تَيَمَّمُواْ الْخَبِيثَ مِنْهُ تُنفِقُونَ وَلَسْتُم بِآخِذِيهِ إِلاَّ أَن تُغْمِضُواْ فِيهِ وَاعْلَمُواْ أَنَّ اللّهَ غَنِيٌّ حَمِيدٌ

“Ya ku muminai ku ciyar daga mafi kyawun abinda ku ka samu da kuma abinda abinda mu ka fito muku daga kasa, kada ku nufi abinda ya ke mummuna ku ciyar da shi wanda ku kanku ba a shirye ku ke ba ku karbe shi, sai idan kun runtse idanu. Ku sani cewa Allah mawadaci ne, abin godewa.”

A kodayaushe musulmi sun rika yi wa manzon Allah tambaya akan abinda za su ciyar ga mabukata, wannan ayar ta zo da ka’ida ta bai daya. Tana fadin cewa ku ciyar daga abinda ya ke tsarkakke kuma wanda ya dace, kudi ko dukiyar da ku ka samu ko kuma abinci da amfanin gona wanda ku ka shuka, muhimmi shi ne ya zamana daga cikin abinda ku ka mallaka ne ta halartacciyar hanya. Ba kowane abinci ko tufafin da sun lalace za a zubar da su ba saboda sun lalace. Ya zo acikin rawayoyi cewa wasu mutanen madina suna bada dabinon da ya lalace ga talakawa mai kyau kuma su aje shi saboda kansu. Wannan ayar tana cewa shin idan ku ne aka baiwa abinda ku ke baiwa talakawa za ku karba? Darussan da za mu koya daga wannan aya. 1-Ayayin ciyarwa wajibi ne a kare mutuncin mabukata, kuma ciyar da abubuwan da su ka lalace bashi da wata kima sannan kuma wulakanci ne ga mutane. 2-Manufar ciyarwa shi ne yin ‘yantar da kai daga rowa, ba rabuwa da abinda aka ciyar da shi ba wanda ba shi da kima. 3-lamirin mutum shi ne mizani mafi dacewa wajen yin hulda da wasu, abinda ba ka so kada ka aikata shi akan wasu. A karshen wannan shirin muna fatan Allah ya bamu ruhin ciyarwa wanda shi ne ‘yan’uwantaka da daidaito, ya kuma nesanta rowa daga gare mu.

Suratul Bakara; Aya Ta 268-272 (Kashi Na 70)

Da sunan Allah mai Rahama mai jin kai.

Masu sauraro barkamu da sake saduwa da ku acikin wannan shirin na “Hannunka Mai Sanda” karo na 58. Ayoyin karshe da mu ka karanta suna Magana ne akan ciyarwa saboda Allah. To a yau ma shirin namu zai ci gaba da yin Magana akan ciyarwa.

Yanzu za mu saurari ayoyi na 268 da 269 na suratul Bakara.

الشَّيْطَانُ يَعِدُكُمُ الْفَقْرَ وَيَأْمُرُكُم بِالْفَحْشَاء وَاللّهُ يَعِدُكُم مَّغْفِرَةً مِّنْهُ وَفَضْلاً وَاللّهُ وَاسِعٌ عَلِيمٌ{268} يُؤتِي الْحِكْمَةَ مَن يَشَاءُ وَمَن يُؤْتَ الْحِكْمَةَ فَقَدْ أُوتِيَ خَيْراً كَثِيراً وَمَا يَذَّكَّرُ إِلاَّ أُوْلُواْ الأَلْبَابِ{269}

“Shaidan ne ya ke tsorata ku da talauci, ya ke umartarku da alfahasha. Allah yana yi muku alkawalin gafara daga gare shi da falala. Allah mai ji ne kuma masani.” “ Yana bada hikimarsa ga wanda ya so, wanda aka ba shi hikima, hakika an ba shi alheri mai yawa. Ba kowa ya ke wa’azatuwa ba sai ma’abota hankali.”

Shaidan da mutane masu siffofin shaidan suna hana mutum ya taimakawa wasu, wani lokacin suna fadin cewa kaima za ka bukatu da wannan kudin anan gaba- a wasu lokutan kuma cusa masa wasi-wasin cewa kai kana shan wahala amma za ka baiwa wani, idan da Allah ya so da bai zauna cikin talauci ba. Wadannan irin mutanen suna hana a yi wa mutane alheri da baiwa, suna kuma kiran mutum zuwa ga tara dukiya. Kuma suna tsoratar da shi da talauci, alhali bukatuwarmu da samun gafarar ubangiji a gobe kiyama iya ce tafi yawa akan bukatuwar da mu ke da ita da abin duniya. Kuma a hakikanin gaskiya Allah ya lamincewa wanda ya ke ciyarwa kyakkyawar rayuwa anan duniya ya kuma kare shi daga talauci, sai dai abin takaici ne cewa mutane basu maida hankali akan wannan hakika mai cike da hakima. Maimakon haka sai su mika kai ga wasi-wasin shaidan ta yadda ba su ganin wani alheri sai acikin tara dukiya. Hakikanin alheri yana tattare da ingantaccen tunani da sanin abinda ya ke daidai, ya zamana mutum ya gaskata alkawalin Allah maimakon ya rika sauraron zugar shaidan. Abubuwan da za mu koya daga wadannan ayoyin. 1-Kada mu zama masu rowa saboda tsoron talauci da wasi-wasin shaidan, ya zama ya hana mu ciyarwa, mu rika tunawa da falalar Allah domin magance wannan irin tsoron. 2-Daga cikin alamun ingantaccen hankali da akwai gaskata alkawalin Allah da yin watsi da wasi-wasin shaidan. A bisa mahanga ta addini, mai hankali shi ne wanda ya ke yin biyayya ga Ubangiji ba mai yin biyayya ga wasi-wasin shaidan da son zuciya ba.

Yanzu kuma za mu karanta ayoyi na 270 da 271 na suratul Bakara.

وَمَا أَنفَقْتُم مِّن نَّفَقَةٍ أَوْ نَذَرْتُم مِّن نَّذْرٍ فَإِنَّ اللّهَ يَعْلَمُهُ وَمَا لِلظَّالِمِينَ مِنْ أَنصَارٍ{270} إِن تُبْدُواْ الصَّدَقَاتِ فَنِعِمَّا هِيَ وَإِن تُخْفُوهَا وَتُؤْتُوهَا الْفُقَرَاء فَهُوَ خَيْرٌ لُّكُمْ وَيُكَفِّرُ عَنكُم مِّن سَيِّئَاتِكُمْ وَاللّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ خَبِيرٌ{271}

“Duk wata ciyarwa da ku ka yi ko kuma bakancen da ku ka yi to Allah yana sane das hi. Azzalumai ba su da mataimaki. Idan ku ka bayyana sadakoki to madalla da ita, idan kuwa ku ka boye ta ku ka baiwa talakawa to shi ya fi amfani a gare ku, kuma zai kankare muku miyagun ayyukanku. Allah masani ne akan abinda ku ke aikatawa.”

Abinda wannan ayar ta ke cewa shi ne, idan wani mahaluki bai ga aikin alherin da ku ka yi ba balle ya yi muku godiya to Allah ya gani kuma yana sane da shi. Ashe ba saboda Allah ku ka ciyar ba? To me zai sa sai kun damu da mutane su gani? Jin cewa Allah yana ganin aikin da mutum ya yi, ya isa ya ingiza shi ya yi aikin kwarai. A bisa fassarar kur’anin rashin damuwa da talakawa zalunci ne wanda ya ke hana mutum samun wani taimako a ranar kiyama, ya kuma hana shi samun ceton waliyan Allah. Dangane da yadda ciyarwa za ta kasance kuwa, a bisa riwayoyi, ya fi dacewa ga mutum ya bayar da zakka da ta ke wajibi a fili, amma sadaka wacce ta ke mustahabbi ya bayar da ita a asurce. Watakila dalilin yin hakan shi ne cewa aikin da ya ke wajibi wani abu ne da ake yinsa nesa da riya. Abubuwan da za mu koya daga cikin wadannan ayoyin. 1-Ubangiji madaukaki yana da masaniya akan ciyarwar da mu ke yi- saboda haka mu ciyar da dukiya mafi kyawu cikin sakankancewa akan tafarkin Allah. 2-Ciyarwarmu ta zama a fili wani lokacin kuma a asurce. Ciyarwa a fili yana karfafawa wasu guiwa su ma su ciyar. Ciyarwa a asurce kuwa tana nesanta mutum daga yin riya, sannan kuma yak are mutuncin wanda aka ciyar da shi. 3-Ciyarwa hanya ce ta samun gafara daga zunubai da kuma tuba.

Yanzu kuma sai aya ta 272 a cikin suratul Bakara.

لَّيْسَ عَلَيْكَ هُدَاهُمْ وَلَـكِنَّ اللّهَ يَهْدِي مَن يَشَاءُ وَمَا تُنفِقُواْ مِنْ خَيْرٍ فَلأنفُسِكُمْ وَمَا تُنفِقُونَ إِلاَّ ابْتِغَاء وَجْهِ اللّهِ وَمَا تُنفِقُواْ مِنْ خَيْرٍ يُوَفَّ إِلَيْكُمْ وَأَنتُمْ لاَ تُظْلَمُونَ

“Shiryar da su ba akanka ya ke ba, sai dai Allah yana shiryar da wanda ya ga dama ne, duk abinda ku ka ciyar na alheri to saboda kanku ne, kada ku ciyar sai don neman yardarm Ubangiji, kuma duk abinda ku ka ciyar za a cika muku sakamakonsa, ba za a tauye muku komai ba.”

Kamar yadda ya zo a cikin tafsirai, musulmi sun kasance cikin shakku dangane da ciyar da talakawan mushrikai, alokacin da su ka yi wa ma’aiki tambaya akan haka ne sai wannan ayar ta sauka. Tana nufin cewa ba da tilasci ne ake karbar addini ba, ta yadda talakawa za su musulunta saboda suna su sami abinda za su ci daga wurin musulmi. Kuma kamar yadda rahamar Allah anan duniyar ta shafi muminai da kafiri, to ciyarwar da musulmi za su yi ta shafi mabukata muminai da wadanda ba muminai ba, domin kuwa dukkanin mutane halittar Allah ne. Ku ciyar da su Allah zai ba ku lada cikakke. Shakka babu sanannen abu ne ciyar da wadanda ba musulmi ba zai kasance idan har ba zai kai ga karfafa kafirci ba, ko kuma ya sa manufofin makiya su karfafa, ya zamana saboda su fahimci ruhin ‘yanadamtaka na musulunci. Abubuwan da mu ka koya daga cikin wannan aya. 1-Babu tilasci acikin karbar addini- babu wanda ya ke da hakki hatta annabi da zai tilasta wani ya karbi musulunci. 2-Musulunci addini ne na ‘yanadamtaka, baya amincewa da talauci da rashi koda kuwa a tsakanin wadanda ba musulmi ba ne. 3-Idan har saboda Allah ne aka ciyar, to mutum zai ga sakamakon aikinsa na alheri a duniya da kuma lahira. A karshen wannan shirin muna rokon Allah da ya rayar da ruhin taimakawa mabukata da talakawa acikin zukatanmu, ya zamana muna daukar sauran mutane amatsayin wani sashe namu domin mu rika jin cewa bukatunsu namu ne.

Suratul Bakara; Aya Ta 273-277 (Kashi Na 71)

Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin kai.

Masu sauraro barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shirin. Bisa yardar Allah mun sake samun wata dama ta karanta ayoyin kur’ani da sanin ma’anarsu domin mu amfana da su ta hanyar aiki da su a cikin rayuwarmu.

To a wannan rana za mu karanta ayoyi na 273 da kuma 274 ne na suratul Bakara.

لِلْفُقَرَاء الَّذِينَ أُحصِرُواْ فِي سَبِيلِ اللّهِ لاَ يَسْتَطِيعُونَ ضَرْباً فِي الأَرْضِ يَحْسَبُهُمُ الْجَاهِلُ أَغْنِيَاء مِنَ التَّعَفُّفِ تَعْرِفُهُم بِسِيمَاهُمْ لاَ يَسْأَلُونَ النَّاسَ إِلْحَافاً وَمَا تُنفِقُواْ مِنْ خَيْرٍ فَإِنَّ اللّهَ بِهِ عَلِيمٌ{273} الَّذِينَ يُنفِقُونَ أَمْوَالَهُم بِاللَّيْلِ وَالنَّهَارِ سِرّاً وَعَلاَنِيَةً فَلَهُمْ أَجْرُهُمْ عِندَ رَبِّهِمْ وَلاَ خَوْفٌ عَلَيْهِمْ وَلاَ هُمْ يَحْزَنُونَ{274}

“Ciyarwa saboda talakawa wadanda su ke a killace akan tafarkin Allah, wadanda ba su da damar yin tafiya adoron kasa, wanda bai san halinsu ba yana zaton su mawadata ne saboda kame kai, kana saninsu da alamunsu ba sa rokon mutane wani abu. Duk abinda ku ka ciyar da shi to Allah yana sane da shi.” “Wadanda su ke ciyar da dukiyarsu da dare da rana a asirce da kuma bayyane ladansu yana wurin Ubangijinsu, babu tsoro a tare da su ko bakin ciki.”.

Kamar yadda mu ka ambata, musulunci yana yin kira zuwa ga samar da daidaito acikin al’ummar musulmi wanda ciyarwa tana daga cikinsu. Wato masu wadata da wadanda su ke da dama su taimakawa da mabukata da dukiyar da su ke da ita. Wannan ayar tana yin ishara ne akan wani yanayi mai muhimmanci wanda ya shafi muhajirun da masu jihadi, wadanda su ka zama ‘yan gudun hijira bayan sun baro gidajensu, suna rayuwa acikin bakunta ba tare da kudi ba kuma basu da damar yin kasuwanci, sai dai duk da wannan irin halin da su ke ciki sun kame kai ba su yin bara, kuma basu bayyana bukatunsu a fili. Saboda haka dukkanin mutane su ke daukar cewa su mawadata ne, alhali wajibi ne ga dukkanin muminai su zama masu yin tunani akan yadda za su kare mutuncin ‘yan’uwansu na addini kada su barsu cikin wahala. Kamar yadda ya zo acikin tarihi, a farkon musulunci wani gungu na sahabban annabi sun yi hijira a tare da shi daga makka zuwa madina, amma ba su da gidaje acikin madina kuma basu da hanyar samun kudin shiga, domin kuwa mushrikan makka sun kwace musu gidaje da dukiya. Mutanen madina sun baiwa wasu daga cikin muhajirun wuri acikin gidajensu, amma mafi yawancinsu suna rayuwa ne a kusa da masallacin annabi a wani wuri da ake kira Sifah. Wannan ayar tana kiran muminai ne da su taimaka musu da warware matsalolin da su ke ciki. Abubuwan da za mu koya a cikin wadannan ayoyin. 1-Ubangiji ya sanya hakkin mabukata acikin dukiyar mawadata. 2-Acikin al’ummar musulmi wajibi ne a biyawa mabukata bukatunsu tun kafin su kai ga yin koke akansu. Ta hanyar biya musu bukatunsu za a hana mutuncinsu zubewa da kuma kare musu shi da hana su fadawa cikin kaskanci. 3-Talaka a bisa ma’anar da kur’ani ya ba shi ne wanda ya ke da gajiyawa ta jiki saboda wata matsala da ta bijiro masa kamar rashin lafiya ko bala’oi na dabi’a kamar ambaliyar ruwa ko girgizar kasa ko yaki, amma duk da haka ya kare mutuncinsa wanda ya ke dauka a matsayin wajibin da ya dara abin duniya. Saboda haka wadanda su ke bara da son rokon mutane ba a daukarsu a matsayin talakawa. 4-Ubangiji ya bada lamuni ga rayuwar wadanda su ke ciyarwa akan tafarkinsa ya kare su daga talauci matukar ba su yi nadama ba akan ciyarwar da su ka yi saboda Allah, ko su yi bakin ciki.

Yanzu kuma za mu karanta ayoyi na 275 da 276 a cikin suratul Bakara.

الَّذِينَ يَأْكُلُونَ الرِّبَا لاَ يَقُومُونَ إِلاَّ كَمَا يَقُومُ الَّذِي يَتَخَبَّطُهُ الشَّيْطَانُ مِنَ الْمَسِّ ذَلِكَ بِأَنَّهُمْ قَالُواْ إِنَّمَا الْبَيْعُ مِثْلُ الرِّبَا وَأَحَلَّ اللّهُ الْبَيْعَ وَحَرَّمَ الرِّبَا فَمَن جَاءهُ مَوْعِظَةٌ مِّن رَّبِّهِ فَانتَهَىَ فَلَهُ مَا سَلَفَ وَأَمْرُهُ إِلَى اللّهِ وَمَنْ عَادَ فَأُوْلَـئِكَ أَصْحَابُ النَّارِ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ{275} يَمْحَقُ اللّهُ الْرِّبَا وَيُرْبِي الصَّدَقَاتِ وَاللّهُ لاَ يُحِبُّ كُلَّ كَفَّارٍ أَثِيمٍ

“Wadanda su ke cin riba ba za su tashi ba sai dai kamar wanda shaidan ya ke buge shi saboda hauka. Wannan abinda ya same su saboda su sun ce shi dai cinika kamar riba ne. Allah ya halarta ciniki ya kuma haramta riba. Wanda duk wa’azi ya so masa daga Ubangijinsa sannan ya hanu to abinda ya wuce gaban hani ya halarta gare shi, kuma al’amarinsa yana wurin Allah. Wadanda su ka koma kuwa wadancanenka ‘yan wuta ne za su dawwama a cikinta. Allah yana shafe wa riba albarka yana kuma kara sadaka. Allah ba ya son dukkanin kafiri mai laifi..”

A cikin ayoyi goma sha hudu ajere a cikin suratul Bakara Ubangiji yana kiran muminai zuwa ga ciyarwa, sannan kuma su ka yi bayanin amfanin ciyarwar akan daidaikun mutane da kuma al’umma. Manufa shi ne a cusawa mutane ruhin ciyarwa da kuma rage yawan damfaruwar zukatansu da son abin duniya, sannan kuma a rage tazarar da ta ke tsakanin aji-aji na mutane da cusa ruhin daidaito a cikin al’ummar musulmi. To a ci gaba da bayani akan wannan jigo wadannan ayoyin suna Magana akan halin cin riba, wanda ya ke hargitsa tsarin tattalin arziki acikin al’umma. Haka nan kuma yana hargitsa daidaiton ruhin daidaikun mutane masu cin riba. A wani gefen kuma yana haddasa gaba da kiyayya daga marasa-shi da kuma masu-shi. Ya kuma ingiza al’umma zuwa fashewa, sannan kuma ya haukata masu dukiya su zamana ba su da wani tunani sai tara dukiya da zinare, ya zamana ba su son kowa da komai ba, ba su da tausayi ko jin kan mutane, kudi su ne komai a wurinsa. Sakamakon cin riba shi ne raunana mai rauni da kuma karfafa mai karfi. Wannan kuma shi ne nau’in zalunci mafi girma ga marasa-shi. Wannan shi ne ya sa acikin dukkanin saukakkun addinai aka haramta cin riba,kuma su ka yi tanadin ukuba akan masu cin riba. Tare da cewa a zahiri, riba tana karawa mutum dukiya, yin sadaka kuwa yana ragewa mutum dukiya, sai dai Allah shi ne wanda ya ke sanya albarka a cikin dukiya, saboda haka dukiyar da aka sameta ta hanyar riba, maimakon ta kawo wa mai ita sa’ada, to Allah zai raba shi da kwanciyar hankali da nutsuwa domin kuwa ya sami wannan dukiyar ne ta hanyar cutar da marasa-shi. Kuma sau da yawa wannan dukiyar ta ke rushewa ta lalace. Idan kuwa mutum ya yi sadaka baya ga samun kauna da zai yi a cikin al’umma, zai kuma rayu cikin kwanciyar hankali da nutsuwa, kuma zai sami damar ci gaba. Abubuwa da za mu koya daga wadannan ayoyin. 1-Cin riba yana hargitsa daidaito na ruhin daidaikun mutane da kuma na tattalin arzikin al’umma, ta yadda kiyayya da gaba su ke maye gurbin kauna da soyayya. 2-Musulunci addini ne da ya ke da tsari na rayuwa, saboda haka ne ya ke da shiri na tattalin arziki ga mutane, ba addini ne da ya tsaya acikin ibada ba kadai sannan ya kyale mutane su yi yadda su ka ga dama da rayuwarsu ta duniya. 3-Cin riba yana nufin rashin yin godiya domin kuwa dukiyar da Allah ya sa a hannumu amana ce, rashin ciyar da mabukata kuwa yana nufin rashin godewa Allah akan wannan ni’ima, kuma shi ne kafircewa ni’ima.

Yanzu kuma za mu karanta aya ta 277 a cikin suratul bakara.

يَمْحَقُ اللّهُ الْرِّبَا وَيُرْبِي الصَّدَقَاتِ وَاللّهُ لاَ يُحِبُّ كُلَّ كَفَّارٍ أَثِيمٍ{276} إِنَّ الَّذِينَ آمَنُواْ وَعَمِلُواْ الصَّالِحَاتِ وَأَقَامُواْ الصَّلاَةَ وَآتَوُاْ الزَّكَاةَ لَهُمْ أَجْرُهُمْ عِندَ رَبِّهِمْ وَلاَ خَوْفٌ عَلَيْهِمْ وَلاَ هُمْ يَحْزَنُونَ

“Wadanda su ka yi imani su ka yi ayyukan kwarai suka tsaida salla su ka bada zakka, ladansu yana wurin Ubangijinsu, babu tsoro a tare da su babu bakin ciki.”.

Wannan ayar tana bayyana mumini na hakika da cewa shi ne wanda ya ke da kyakkyawar alaka da Ubangiji sannan kuma a lokacin guda ya ke da kyakkyawar alaka da halittun Ubangiji ta hanyar bada zakka. Addini bai takaita a cikin busasshiyar ibada ba ba tare da tunani akan taimakon mutane ba.

A karshen wannan shiri muna fatan cewa yaduwar al’adar ciyarwa acikin al’umma za ta kawar da cin riba da zalunci, a kuma kare hakkin talakawa da kuma shimfida adalci na hakika.

Suratul Bakara; Aya Ta 278-282 (Kashi Na 72)

Da sunan Allah mai Raham Mai Jin Kai.

Masu sauraro barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shirin wanda mu ke karanto ayoyin al’kur’ani mai girma da kuma fassarasu da harshen hausa. A cikin shirin da ya gabata mun karanta ayoyin da su ke magana ne akan cin riba da kuma illarta ga rayuwar daidaikun mutane da kuma al’umma baki daya. To a cikin wannan shirin za mu ci gaba da yin magana ne da akan batun na cin hanci da rashawa kamar yadda ya ke acikin ayoyin kur’ani mai girma. Sai a kasance a tare da mu domin jin yadda shirin zai kasance.

A yanzu za mu karanta ayoyi na 278 da 279 a cikin suratul Bakara.

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُواْ اتَّقُواْ اللّهَ وَذَرُواْ مَا بَقِيَ مِنَ الرِّبَا إِن كُنتُم مُّؤْمِنِينَ{278} فَإِن لَّمْ تَفْعَلُواْ فَأْذَنُواْ بِحَرْبٍ مِّنَ اللّهِ وَرَسُولِهِ وَإِن تُبْتُمْ فَلَكُمْ رُؤُوسُ أَمْوَالِكُمْ لاَ تَظْلِمُونَ وَلاَ تُظْلَمُونَ{279}

“Ya ku wadanda ku ka yi imani ku ji tsoron Allah ku bar abinda ya ragu na daga riba idan kun kasance muminai.” “Idan kuwa ba ku aikata abinda aka umarce ku ba, to ku sani cewa kun shelanta yaki ga Allah da manzonsa. Idan ku ka tuba to asalin dukiyarku na gare ku, ba za ku yi zalunci ba, ba za a zalunce ku ba.”

A lokacin da ayoyin da su ke magana akan riba su ka sauka wasu musulmi suna bin wasu mutanen abinda ya saura na riba. Saboda haka ne su ka yi wa annabi tambaya akai. Sai ayoyin da su ka gabata su ka sauka. Manzon Allah ya sanar da cewa duk wata yarjejeniya ta kasuwanci da aka kulla a baya mai riba acikinta ta rushe, kuma daga yanzu dole ne musulmi su daina cin riba. A cikin ayoyin da su ka gabaci wadannan mun karanta cewa taimakawa marasa-shi da ba su bashi yana a matsayin baiwa Allah bashi ne, kuma Allah madaukaki zai biya yi sakamako akai. Bugu da kari wannan ayar ta yi gargadi ga masu bada bashi da riba aciki ga marasa-shi, sannan kuma ta yi gargadin cewa idan mai yin hakan bai daina ba to, ya shelanta yaki akan Allah da manzonsa wadanda su ke kare marasa-shi. Abubuwan da za mu koya daga cikin wadannan ayoyin. 1-Imani bai tsaya acikin salla da azumi ba kadai, ya kuma shafi nesantar tara dukiyar haram, da hakan ya ke a matsayin alamar imani da kuma tsoron Allah. 2-Musulunci addini ne wanda ya ke girmama hakkin mallaka, amma a lokaci guda baya bada dama ga masu dukiya su sarrafa mutane yadda su ke so ko su bautar das u. 3-Danniya da kuma mika kai ga danniya abubuwa ne guda biyu wadanda a ke yin Allah wadai da su. Cin riba haramun ne haka nan kuma bada riba.

Yanzu kuma za mu karanta ayoyi na 280 da kuma 281 a cikin suratul Bakara.

وَإِن كَانَ ذُو عُسْرَةٍ فَنَظِرَةٌ إِلَى مَيْسَرَةٍ وَأَن تَصَدَّقُواْ خَيْرٌ لَّكُمْ إِن كُنتُمْ تَعْلَمُونَ{280} وَاتَّقُواْ يَوْماً تُرْجَعُونَ فِيهِ إِلَى اللّهِ ثُمَّ تُوَفَّى كُلُّ نَفْسٍ مَّا كَسَبَتْ وَهُمْ لاَ يُظْلَمُونَ{281}

“Idan- wanda ya karbi bashi- yana cikin kunci, to a yi masa jinkiri zuwa lokacin samun wadata. Idan ku ka yi sadaka shi ne mafi alheri idan da ace kun sani.” “Ku ji tsoron ranar da za ku koma zuwa ga Allah sannan a sakawa kowace rai da abinda ta aikata, ba kuma za a zalunce su ba.”.

A ci gaban ayoyin da su ke kiran muminai da su rika ciyarwa da kuma bada bashi, sannan kuma kada su dora musu kudin ruwa akai, to wannan ayar tana yin Magana ne akan wani batu mai muhimmanci ta fuskar kyawawan halaye. Tana cewa ba bashin da babu ruwa ne kadai ya kamata ku baiwa talakawa ba, idan ma wanda aka baiwa bashin ba zai iya biya ba a lokacin da aka tsaida saboda rashi, to ku daga masa kafa, sannan kuma ku yafe masa. Ku kuma san cewa wannan yafiyar da za ku yi tana da sakamako a wurin Allah a ranar kiyama. A hakikanin gaskiya idan har za a yi aiki da wannan hukuncin na addini acikin al’umma, ruhin ‘yan’uwantaka da kauna za su watsu. Mabukata za su wadata masu wadata kuma za su daina kwadayi da dogon guri.

Abinda za mu koya daga wadannan ayoyin. 1-Manufa acikin ciyarwa da bada bashi ita ce , samar da jin dadi a tsakanin marasa-shi, saboda haka kada a yi abinda zai sa su sake fadawa cikin takura saboda biyan bashin da su ka ci. 2-Musulunci addini ne wanda ya ke damuwa da marasa-shi, saboda haka ya haramta kudin ruwa sannan kuma ya ke karfafa guiwa akan ciyarwa- domin yin hakan zai cike gurbin da ake da shi ta fuskar tattalin arziki acikin al’umma. 3-Gamsar da bukatun marasa-shi yana nufin samun yardar Ubangiji, shi ne kuma wanda ya ke da fifiko akan tara dukiya.

Yanzu kuma za mu karanta aya ta 282 acikin suratul Bakara.

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُواْ إِذَا تَدَايَنتُم بِدَيْنٍ إِلَى أَجَلٍ مُّسَمًّى فَاكْتُبُوهُ وَلْيَكْتُب بَّيْنَكُمْ كَاتِبٌ بِالْعَدْلِ وَلاَ يَأْبَ كَاتِبٌ أَنْ يَكْتُبَ كَمَا عَلَّمَهُ اللّهُ فَلْيَكْتُبْ وَلْيُمْلِلِ الَّذِي عَلَيْهِ الْحَقُّ وَلْيَتَّقِ اللّهَ رَبَّهُ وَلاَ يَبْخَسْ مِنْهُ شَيْئاً فَإن كَانَ الَّذِي عَلَيْهِ الْحَقُّ سَفِيهاً أَوْ ضَعِيفاً أَوْ لاَ يَسْتَطِيعُ أَن يُمِلَّ هُوَ فَلْيُمْلِلْ وَلِيُّهُ بِالْعَدْلِ وَاسْتَشْهِدُواْ شَهِيدَيْنِ من رِّجَالِكُمْ فَإِن لَّمْ يَكُونَا رَجُلَيْنِ فَرَجُلٌ وَامْرَأَتَانِ مِمَّن تَرْضَوْنَ مِنَ الشُّهَدَاء أَن تَضِلَّ إْحْدَاهُمَا فَتُذَكِّرَ إِحْدَاهُمَا الأُخْرَى وَلاَ يَأْبَ الشُّهَدَاء إِذَا مَا دُعُواْ وَلاَ تَسْأَمُوْاْ أَن تَكْتُبُوْهُ صَغِيراً أَو كَبِيراً إِلَى أَجَلِهِ ذَلِكُمْ أَقْسَطُ عِندَ اللّهِ وَأَقْومُ لِلشَّهَادَةِ وَأَدْنَى أَلاَّ تَرْتَابُواْ إِلاَّ أَن تَكُونَ تِجَارَةً حَاضِرَةً تُدِيرُونَهَا بَيْنَكُمْ فَلَيْسَ عَلَيْكُمْ جُنَاحٌ أَلاَّ تَكْتُبُوهَا وَأَشْهِدُوْاْ إِذَا تَبَايَعْتُمْ وَلاَ يُضَآرَّ كَاتِبٌ وَلاَ شَهِيدٌ وَإِن تَفْعَلُواْ فَإِنَّهُ فُسُوقٌ بِكُمْ وَاتَّقُواْ اللّهَ وَيُعَلِّمُكُمُ اللّهُ وَاللّهُ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمٌ

“Ya ku wadanda ku ka yi imani idan ku ka yi mu’amala ta bashi zuwa ajali abin Ambato, to ku rubuta shi. Marubuci a tsakaninku ya rubuta da adalci. Kada marubucin ya ki rubutawa kamar yadda Allah ya sanar da shi, wanda hakki ya ke kansa ya yi shifta, ya ji tsoron Allah ubangijnsa kada ya tauye komai. Idan wanda hakkin nan ya ke kansa ya kasance wawa ko rarrauna ko wanda ba ya iya yin shifta, to waliyinsa ya yi shifta da adalci, kuma ku kafa shaidu guda biyu daga balagaggun ‘ya’yanku, idan kuma babu balagaggun mutane biyu to namiji daya da mata biyu daga wadanda ku ka yarda da su, saboda idan daya ta manta to dayar wacce bata manta ba ta tunatar da ita. Kada shaidun su ki idan an kirawo su, kada ku kosa daga rubuta hakkin da su ka yi shaida akansa, kankane ne ko mai yawa ya zuwa ajalinsa. Wannan rubutawar shi ya fi adalci a wurin Allah shi ne ya fi daidai ga sheda, shi ne kuma ya fi daidai ya hana su yi kokonto. Sai ko idan ya kasance ciniki da ku ke mu’amala akansa, to babu laifi akanku idan ba ku rubuta ba, ku saidar idan kun yi mu’amala ta ciniki. Kada a cuci marubuci kada a cuci shaida. Idan ku ka aikata to wannan fasikanci a gare ku. Ku ji tsoron Allah sai Allah ya sanar da ku. Allah masani ne akan kwane abu.”

Wannan ita ce guda daya mafi tsawo acikin kur’ani mai girma. Tana kuma yin Magana ne akan hakkin mutane wato kare hakkokin mutane na dukiya. Ta kuma zo ne a ci gaban ayoyin da su ka yi Magana akan hukunce-hukuncen tattalin arziki da kuma yin kira zuwa ga ciyarwa da bada bashi sannan kuma haramta karbar kudin ruwa. Wadannan hukunce-hukunce ne da su ke yin bayani akan yadda za a kare hakkokin mutane ba tare da wani shakku ko kokonto ya shiga ciki ba. Sharuddan mu’amala da su ka zo a cikin wannan aya. 1-Duk wani bashi da za a bayar-kadan ne ko mai yawa- dole ne- wajibi ne ya zamana akwai rubutattun bayanai. 2-Wanda zai rubuta kada ya zamana daga cikin daya daga cikin bangarori biyu, amma abinda za a rubuta ya zamana abinda wanda ya ci bashi ya fada ne. 3-Mai cin bashi da mai rubutu su ji tsoron Allah kada su tsallake iyaka. 4-Bayan an rubuta kuma wajibi ne a kafa shaidu guda biyu wadanda dukkanin bangarorin biyu su ka yarda da su. 5-Alokacin yin ciniki na kudi nakadan, ba dole ne sai an yi rubutu ba. Darussan da za mu koya acikin wannan aya. 1-Musulunci addini ne da ya tattara komai da komai, baya ga yin Magana akan abinda ya shafi daidaikun mutane da kuma kula da tarbiyyar mutum yana kuma yin Magana akan dokoki na tattalin arziki na al’umma ta hanya mai zurfi. 2-Yin wasici da rubutu- a cikin zamanin da mafi yawancin mutane basu iya rubutu ba, yana nuni ne da yadda addini ya damu da ilmantarwa da ci gaban ilimi. 3-Yin wasici da rubuta yarjejeniya domin karfafa amincewa da juna a tsakanin mutane, ba yana nufin rashin amincewa da yarda ba ne. Domin kuwa da akwai batutuwa da su ka shafi mantuwa da kuskure, wadanda za su iya kawar da yarda da kwanciyar hankali. 4-Rubuta bayanai da tsara su akan mu’amala yana da amfani guda uku. Na farko shi ne aiwatar da adalci. Na biyu shi ne samar da bayanan da za a iya amfani das hi domin kafa shaida. Na uku shi ne zai hana mummunan zato da kawar da rashin amincewa da juna.

A karshe muna fatan cewa ta hanyar aiki da hukunce-hukuncen musulunci masu tsari mu yi nisa da cutar juna da kuma dannen hakkin juna.

Sai kuma mun sake haduwa a wani shirin.

Suratul Bakara; Aya Ta 283-286 (Kashi Na 73)

Da sunan Allah mai Raham Mai Jin Kai.

Masu sauraro barkanmu da sake saduwa da ku acikin wannan shirin. Muna kuma tare da ku ne a cikin fassarar ayoyi na karshe acikin suratul Bakara. Acikin shiri na karshe da mu ka gabatar kuwa mun bijiro da ayoyin da su ke yin Magana ne akan tsara da rubuta bayanai da su ka shafi mu’amala ta kasuwanci wacce babu kudi lakadan acikinta, haka nan kuma bashi. To a cikin shirinmu na wannan rana za mu ci gaba da sauraron umarnin Allah.

Da fari aya ta 283 a cikin suratul Bakara.

وَإِن كُنتُمْ عَلَى سَفَرٍ وَلَمْ تَجِدُواْ كَاتِباً فَرِهَانٌ مَّقْبُوضَةٌ فَإِنْ أَمِنَ بَعْضُكُم بَعْضاً فَلْيُؤَدِّ الَّذِي اؤْتُمِنَ أَمَانَتَهُ وَلْيَتَّقِ اللّهَ رَبَّهُ وَلاَ تَكْتُمُواْ الشَّهَادَةَ وَمَن يَكْتُمْهَا فَإِنَّهُ آثِمٌ قَلْبُهُ وَاللّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ عَلِيمٌ

“Idan kun kasance akan tafiya kuma ba ku sani marubuci ba, to a karbi jingina, idan sashenku ya amince da sashe to wanda aka amince da shi ya biya bashin nan nashi, ya ji tsoron Allah ubangijinsa, kada kuma ku boye shaida. Wanda duk ya boye ta hakika zuciya mai sabo ce. Allah masani ne akan abinda ku ke aikatawa.”

A cikin shirin baya mun ambata cewa, musulunci yana yin wasici da akiyaye hakkokin mu’alama ta cinikayya wacce babu kudi lakadan aciki haka nan kuma a cikin bada bashi, ta yadda za a rubuta su, kuma a kafa shedu guda biyu, saboda ya zamana an warware matsala idan aka sami kuskure ko mantuwa ko kuwa daya bangaren ya yi inkari. Yadda musulunci ya bada muhimmanci akan wannan lamarin ta kai ga yana yin wasici da a rubuta bashi koda ana kan tafiya ne. Idan kuma ba a sami wanda zai rubuta ba to a karbi jingina, sai dai wajibi ne ga wanda ya karbi jingina da wanda ya bayar su san da cewa abinda ya ke hannuwansu amana ce, kuma wajibi ne su maida wannan amanar a lokacin da ya dace ga mai ita. Jinginar da ta ke hannun wanda ya bada bashi amana ce kuma bashi da hakkin cin moriyarta ta hanyar da bata dace ba. Kuma wajibi ne a gare shi ya yi kokarin kiyayeta ta yadda idan wanda ya karbi bashi ya biyashi bashinsa ya maida masa abinda ya karba jingina sumul kalau kamar yadda ya ke. Shi ma wanda ya ci bashi abin amincewa ne a wurin wanda ya ba shi bashi, saboda haka wajibi ne ya cika alkawalii ya maida amanar da aka bashi, kada ya cutar da wanda ya bashi bashin, musamman mai ace wanda ya bashi bashin nan ya amince masa matuka, idan kuma babu wannan to ya ji tsoron Allah kada ya take masa hakki. A karshen ayar an yi kira ga dukkanin muminai da kada su yi sassauci da hakkokin mutane, domin kuwa Allah yana da masaniya akan abinda ya ke yawo acikin zukata. Take hakkin wani kuwa zunubi ne mai girman gaske. Domin kuwa yana gurbata ruhin mutum.

Abubuwan da za mu koya daga wannan aya. 1-Mua’mala wacce ba ta kudi lakadan ba, ba a yin ta da fatar baki kadai, ana yinta ne ta hanyar rubutawa da kuma kafa shaidu, idan kuma bukata ta taso a karbi jingina, saboda a karfafa mu’amala. 2-Abiya bashi akan lokaci, kada a bari amanar da ta ke tsakanin mutane ta kau ko kuma a rusa aminci na tattalin arziki acikin al’umma.

Yanzu kuma za mu karanta aya ta 284 acikin suratul Bakara.

لِّلَّهِ ما فِي السَّمَاواتِ وَمَا فِي الأَرْضِ وَإِن تُبْدُواْ مَا فِي أَنفُسِكُمْ أَوْ تُخْفُوهُ يُحَاسِبْكُم بِهِ اللّهُ فَيَغْفِرُ لِمَن يَشَاءُ وَيُعَذِّبُ مَن يَشَاءُ وَاللّهُ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ

“Abubuwan da su ke cikin sammai da kassai na Allah ne. In ku ka bayyana abinda ya ke cikin zuciyarku ko ku ka boye shi, Allah zai yi mu ku hisabi da shi, ya gafartawa wanda ya ga dama ya kuma yi azaba ga wanda ya ga dama. Allah mai iko ne akan komai.”

Wannan ayar tana yin gargadi ne ga muminai cewa kada ku zaci cewa akan laifukan da gabobinku irin su idanu da kunne suke aikatawa ne kadai za a yi mu ku hisabi akansu, to Allah yana da masaniya akan abinda ya ke yazo acikin zukatanku. Za kuma a yi muku hisabi akan laifukan da za ku aikata ta hanyar ruhinku. Shakka babu abinda ake nufi da laifukan ruhi da za a yi hisabi akansu anan shi ne kudurce kafirci da boye hakkokin mutane da a ka yi maganarsu a ayoyin baya. Amma idan wasi-wasin shaidan ne ko kuma tunani akan aikata sabo amma ba a kai ga aikatawa ba to, ba shi da sakamako. Tare da cewa yin tunani akan aikata laifi acikin zuci yana iya ingiza mutum ya aikata. Abinda za mu koya daga wannan aya. 1-Ba idanu da kunnuwa ne kadai ya zama wajibi ga mutum ya rika kula da su ba, haka nan ma abinda ya ke yawo acikin zuciyarsa, saboda kada ta kai ga gurbata. Idan haka ta faru to shaidan zai sami iko akan mutum ya kuma share masa fagen aikata kowane irin zunubi.

Yanzu kuma sai aya ta 285 acikin suratul bakara.

آمَنَ الرَّسُولُ بِمَا أُنزِلَ إِلَيْهِ مِن رَّبِّهِ وَالْمُؤْمِنُونَ كُلٌّ آمَنَ بِاللّهِ وَمَلآئِكَتِهِ وَكُتُبِهِ وَرُسُلِهِ لاَ نُفَرِّقُ بَيْنَ أَحَدٍ مِّن رُّسُلِهِ وَقَالُواْ سَمِعْنَا وَأَطَعْنَا غُفْرَانَكَ رَبَّنَا وَإِلَيْكَ الْمَصِيرُ

“Manzo ya yi imani da abinda aka saukar masa daga Ubangijinsa haka nan muminai sun gaskata Allah da mala’ikunsa da littatafansa da manzanninsa. Ba mu sanya banbanci a tsakanin daya daga cikin manzanninsa. Sai su ka ce mun ji mun yi bi,. Muna rokonka gafararka ya Ubangijinmu, izuwa gare ka ne makoma.”

A mahanga ta musulunci, duniya ta yi kama da makaranta wacce a tsawon tarihi Ubangiji ya ke aiko da malamai da su ne manzanni domin su shiryar da mutane da kuma yi musu tarbiyya. Kowane daga cikin wadannan annabawan sun koyar da mutane a cikin wani aji na tarihi sun kuma daukaka matsayinsu daidai gwargwado har zuwa lokacin da hankalin mutum ya kai munzalin da zai iya karbar cikakken tsari daga Ubangiji, sai Ubangiji ya aiko da cikamakin annabawa, manzon Allah Muhammad (s.a.w.a)

A saboda haka duk wani musulmi ya yi imani da dukkanin annabawan Allah da kuma dukkanin littatafan da ya saukar kuma baya banbanta tsakanin manzannin Allah.

Yanzu kuma sai aya ta karshe acikin suratul Bakara da ita ce aya ta 286.

لاَ يُكَلِّفُ اللّهُ نَفْساً إِلاَّ وُسْعَهَا لَهَا مَا كَسَبَتْ وَعَلَيْهَا مَا اكْتَسَبَتْ رَبَّنَا لاَ تُؤَاخِذْنَا إِن نَّسِينَا أَوْ أَخْطَأْنَا رَبَّنَا وَلاَ تَحْمِلْ عَلَيْنَا إِصْراً كَمَا حَمَلْتَهُ عَلَى الَّذِينَ مِن قَبْلِنَا رَبَّنَا وَلاَ تُحَمِّلْنَا مَا لاَ طَاقَةَ لَنَا بِهِ وَاعْفُ عَنَّا وَاغْفِرْ لَنَا وَارْحَمْنَا أَنتَ مَوْلاَنَا فَانصُرْنَا عَلَى الْقَوْمِ الْكَافِرِينَ

“ Allah ba ya kallafawa rai sai abinda za ta iya. Abinda ta aikata na gare ta, abinda ta aikata yana kanta. Ya ubangijinmu kada ka rike mu idan mun mun yi mantuwa ko mun yi kuskure. Ya ubangijinmu kada ka dora mana nauyi tamkar yadda ka dora shi akan wadanda su ka gabace mu. Ubangijinmu kada ka dora mana abinda ba mu da ikonsa. Ka yi mana afuwa, ka yi mana gafara, ka rahamshe mu. Kai ne shugbanmu sai ka taimake mu akan mutane kafirai.”

Ubangiji ya halicci mutane mabanbanta. Wani yana da hazaka da kaifin kwanya, wani kuma mai karancin hazaka. Wani mai karfi wani kuma mai rauni. Wani fari wani kuma baki. Kuma ya wani namiji ya halicci mace. Sai dai wajibi ne mu fahimci cewa wadannan banbance-banbancen na halitta suna a matsayin lalura ce ta wanzuwar jinsin bil’adama. Wasu banbance-banbancen kuwa sun samo asali ne daga zaluncin da mutum ya ke yi wa dan’uwansa mutum. Abu ne da ya ke a fili cewa wadannan banbance-banbancen da ake da su na hakika ne ko wadanda ba na hakika ba su yi tasiri akan jikin mutum da tunaninsa. Saboda haka Allah madaukaki ba azzalumi ba ne da ya ke tsammanin sakamako guda daya daga dukkanin mutane. A dalilin haka wannan ayar tana yin ishara da daya daga cikin siffofin Ubangiji da shi ne adalci. Abinda ayar ta ke cewa shi ne Allah baya dorawa mutum abinda ya fi karfinsa da ikonsa. Saboda haka sakamako da ukuba wanda ya ke damfare da aiki, ya banbanta. A ranar kiyama Allah zai yi wa kowane mutum sakamako ne bisa karfin fahimtarsa da riskarsa da dokokin addini. Idan mutum ya yi mantuwa ko kuwa ya aikata sabo bisa kuskuren ba da ganganci ba to Allah ba zai rike shi ba.

Abubuwan da za mu koya daga wannan aya. 1-Musulunci addini ne na ‘yan’adamtaka, baya dorawa mutane abinda ya fi karfinsu. Kamar yadda annabin musulunci (a.s.w.a) ya ke fadin cewa: An aiko ni ne da addini mai sauki.” 2-Sakamako da ukuba za su kasance ne bisa aiki shi kuwa aiki yana bin niyya ne. Saboda haka aikin da ba ayi ba saboda mantuwa ko kuma kuskure ba a yi wa mutum ukuba akansa ba. 3-Ubangiji yana mu’amala ne da mutum bisa jin kansa da tausayinsa da gafararsa. Saboda haka idan mutum ya tuba, to za a gafarta masa zunubansa, kuma a tsarkake zuciyarsa daga gurbata. A karshen wannan shirin da mu ka kamala suratul bakara muna rokon Allah da ya bamu dace mu ci gaba da tafiya akan wannan tafarkin. Sai mun sake haduwa acikin wani shirin.

Contents