Toggle menu
24K
663
183
158K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Quran/5/IRIB Hausa Tafsir

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations

Suratul Ma'ida, Aya Ta 1-2 (Kashi Na 154)

Bismillahir Rahmanir Rahim. Assalamu alaikum jamaa masu saurare. Barkan mu da sake saduwa a shirin Hannunka mai Sanda shirin da yake kawo muku sharhi na ayoyin Alkurani mai girma. A yau sharhin namu zai fara ne daga farkon surar Maaida, sura ta biyar a cikin Alkurani mai girma. Surar Maidah ta sauka ne a karshe-karshen rayuwar Manzon Allah (s.a.w). An sanya mata suna Maidah ne, wato kabaki, domin an ambaci wannan kalma a aya ta 114 in da Allah Madaukakin Sarki ya kawo hikayar Annabi Isa (a.s.) inda ya yi addu'ar Allah ya sauko da kabaki daga sama.

To madalla. Da farko bari mu saurari ayar farko:

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُواْ أَوْفُواْ بِالْعُقُودِ أُحِلَّتْ لَكُم بَهِيمَةُ الأَنْعَامِ إِلاَّ مَا يُتْلَى عَلَيْكُمْ غَيْرَ مُحِلِّي الصَّيْدِ وَأَنتُمْ حُرُمٌ إِنَّ اللّهَ يَحْكُمُ مَا يُرِيدُ{1}

"Yã kũ wadanda suka yi ĩmãni! ku cika alkawurra. An halatta muku dabbobin jin dãdi fãce abin da ake karantãwa a kanku, bã kunã mãsu halattar da farauta ba alhãli kuwa kunã mãsu harama. Lalle ne, Allah Yanã hukunta abin da yake nufi."

Da yake wadannan ayoyi na farkon surar Maidah an saukar da su ne gabanin tafiyar Annabi zuwa aikin haji, suna koya wa Musulmi wasu hukunce hukuncen aikin haji kuma wannan aya ta yi bayanin haramcin farauta a yayinda mutum ya duara haramin haji. Amma ta fara da wani muhimmin batu tukuna, wato umurnin da Allah ya yi wa mutane da cika alkawari ko yarjejeniya, kuma wannan ya hada dukkan yerjejeniyoyi ko na baki ko wadanda a ke rubutawa, ko da masu karfi ko iko ne, ko kuma da raunana ne aka kulla su, ko da abokan arziki ko kuma da abokan gaba, ko alkawarin ayyukan addini ne tsakanin bawa da Ubangijinsa ko kuma alkawuran da suka shafi dukiya da tattalin arziki ne, ko na zaman iyali ne ko kuma na zamantakewar alumma. A wasu nassosin addini hatta mushrikai da fajira ma, cika musu alkawari wajibi ne idan dai ba su suka karya alkawarin ba. Wannnan aya tana kloyar da mu darusa kamar haka: 1-Wajibi ne Musulmi ya cika alkawura da yarjejeniyoyin da ya kulla a ko da yaushe, kuma wannan sharadi ne ingancin imani. 2- A cikin yankin hurumin Makka kowa yana cikin aminci, hatta dabbobi, kuma farautarsu haramun ne a wannan wuri mai albarka.

Sai mu saurari aya ta 2:

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُواْ لاَ تُحِلُّواْ شَعَآئِرَ اللّهِ وَلاَ الشَّهْرَ الْحَرَامَ وَلاَ الْهَدْيَ وَلاَ الْقَلآئِدَ وَلا آمِّينَ الْبَيْتَ الْحَرَامَ يَبْتَغُونَ فَضْلاً مِّن رَّبِّهِمْ وَرِضْوَاناً وَإِذَا حَلَلْتُمْ فَاصْطَادُواْ وَلاَ يَجْرِمَنَّكُمْ شَنَآنُ قَوْمٍ أَن صَدُّوكُمْ عَنِ الْمَسْجِدِ الْحَرَامِ أَن تَعْتَدُواْ وَتَعَاوَنُواْ عَلَى الْبرِّ وَالتَّقْوَى وَلاَ تَعَاوَنُواْ عَلَى الإِثْمِ وَالْعُدْوَانِ وَاتَّقُواْ اللّهَ إِنَّ اللّهَ شَدِيدُ الْعِقَابِ{2}

"Ya kũ wadanda suka yi ĩmãni! kada ku halattar da ayyukan ibãdar Allah game da hajji, kuma da watã mai alfarma, kuma da hadaya, kuma da rãtayar rakuman hadaya, kuma da mãsu nufin ¦ãki mai alfarma, sunã neman falala daga Ubangijinsu da yarda. Kuma idan kun kwance harama, to, ku yi farauta. Kuma kada kiyayya da wasu mutãne ta dauke ku, dõmin sun kange ku daga Masallãci Mai alfarma, ga ku yi zãlunci. Kuma ku taimaki junã a kan aikin kwarai da takawa. Kuma kada ku taimaki juna a kan zunubi da zãlunci, kuma ku bi Allah da takawa. Lalle ne Allah Mai tsananin ukũba ne."

Wannan aya tana ci gaba da bayyana hukunce hukuncen haji. Ta na cewa: abubuwan da suke da alaka da aikin haji ko wurin da ake yin sa sun ada tsarki kuma dole ne a kiyaye alhurmarsu. Kama daga dabbobi hadaya, har zuwa wurare masu tsarki da suke alamomi ne na ibadar Allah da kuma lokutan da ake gudanar da ayyukan haji wato watannin masu alfarma, da mahajjatan da suka kai wad akin Allah ziyara saboda neman yardarsa, dukkan wadannan ababen girmamawa ne kuma wajibi a girmama su.

Ayar ta kuma yi ishara da abubuwan da suka faru a shekar a ta shida bayan hijirar Maaki (s.a.w.), a shekarar da Msusulmi suka raka Manzon Allah zuwa makka domin aikin haji amma mushrikan Makka suka hana su shiga birnin, kuma saboda hana aukuwar yaki bangarorin biyu suka kulla yarjejeniyar sulhu a wuri na ake kira Hudaybiyah. Amma bayan da Annbi ya ci garin Makka da yaki sai wasu Musulmi suka yi nufin daukar fansa a kan mushrikai, sai wannan aya ta sauka domin hana su aikata wannan aiki, tana cewa: a maimakon daukar fansa kamata ya yi ku shirin yin taimakekeniya, kuma da haka suma wadancan sai ku ja hankalinsu zuwa addinin Ubangiji madaukakin sarki da aikata ayyukan kwarai, kuma da haka ne zaku yi shimfida domin bunkasa ayyukan na gari a cikin alumma.

Ko da yake an yi maganar taimakekeniya ne a cikin bayanan aikin haji, amma taimakekeniya bai kebanta da lokacin aikin haji. Taimakekeniya tana daga cikin manyan koyarwar da adddinin Muslunci yake horo da a yi riko da su, a alamuran zaman iyali, da siyasa. A karkashin wannan kaida Musulmi suna hada kai ne a wajen ayyukan kwarai da ake jin tsoron Allah a cikinsu, ba zalunci da keta haddi da aikin sabo kamar yanda mutane da dama suke da raayion cewa ya kamata mutum ya taimaka wa dan uwansa ko dan kasarsa ko da shi aka zalunta ko shi ya yi zalunci ba.

A wannan aya muna koyar darussa kamar haka:

1- Duk abin da ya danganci alamarin Ubangiji yana samun tsarkikum adole ne a girmama shi, ko da dabbar da za a yanka saboda hadaya. 2- Idan mutum ya yi gaba da wani a baya, baya hujja ce da zata sa mutun ya zalunce shi ba. 3- Daukar matakai a zamantakewa da ma alamuran kasa da kasa, ya kamata ya dogara ne a kan gudanar da adalci da tsoron Allah, ba kare dan kasanci ko jinsi ko yare ba.

      • To a nan zamu dakata a shirin Hannunka mai Sanda sai kuma shiri na gaba da yardar Allah zaku ji bayanai akan wasun ayoyin na surar Maidah. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi taala wa barakatuhu.

Suratul Ma'ida, Aya Ta 3 (Kashi Na 155)

Bismillahir Rahmanir Rahim. Assalamu alaikum jamaa masu saurare. Barkan mu da sake saduwa a shirin Hannunka mai Sanda shirin da yake kawo muku sharhi na ayoyin Alkurani mai girma. A yau sharhin namu zai yi bayani a kan aya ta 3 na wannan sura ta Maidah da fatar zaku kasance tare da mu.

To madalla. Da farko bari mu saurari karatun wannan aya ta 3:

حُرِّمَتْ عَلَيْكُمُ الْمَيْتَةُ وَالْدَّمُ وَلَحْمُ الْخِنْزِيرِ وَمَا أُهِلَّ لِغَيْرِ اللّهِ بِهِ وَالْمُنْخَنِقَةُ وَالْمَوْقُوذَةُ وَالْمُتَرَدِّيَةُ وَالنَّطِيحَةُ وَمَا أَكَلَ السَّبُعُ إِلاَّ مَا ذَكَّيْتُمْ وَمَا ذُبِحَ عَلَى النُّصُبِ وَأَن تَسْتَقْسِمُواْ بِالأَزْلاَمِ ذَلِكُمْ فِسْقٌ الْيَوْمَ يَئِسَ الَّذِينَ كَفَرُواْ مِن دِينِكُمْ فَلاَ تَخْشَوْهُمْ وَاخْشَوْنِ الْيَوْمَ أَكْمَلْتُ لَكُمْ دِينَكُمْ وَأَتْمَمْتُ عَلَيْكُمْ نِعْمَتِي وَرَضِيتُ لَكُمُ الإِسْلاَمَ دِيناً فَمَنِ اضْطُرَّ فِي مَخْمَصَةٍ غَيْرَ مُتَجَانِفٍ لِّإِثْمٍ فَإِنَّ اللّهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ{3}

"An haramta muku cin mũshe da jini da nãman alade da abin da aka yanka shi da sũnan wanin Allah, da dabba wadda aka shake da wadda aka doke da wadda ta gangaro da wadda yar uwarta ta sõka da kaho da abin da namun dãgi suka ci, sai dai abin da kuka sami damar yankawa. Kuma an haramta muku abin da aka yanka da sunan gumaka. Kuma (an haramta muku yin) camfi ta hanyar yin kuri'a da kyamare; wadancan fãsikanci ne. Daga yau wadanda suka kãfirta sun yanke kauna daga (karya) addininku, sabõda haka kada ku ji tsõronsu, ku ji tsõrona. A yau Nã cika muku addininku, Nã kuma cika ni'imata a kanku, Nã kuma zabar muku Musulunci shi ne addini a gare ku. To, wanda ya matsu (ya ci daga wadancan abubuwa da aka haramta) don tsananin yunwa, bã yana mai karkata zuwa ga yin sabo ba, to hakika Allah Mai gãfara ne, Mai rahama."

Wannan aya tana bayanin batutuwa biyu daban daban. Na farko yana ci gaba ne da bayani kan hukunce hukuncen abubuwan da suke haramun ne a ci, ya ambaci abubuwa goma da suka haramta a ci. Wasu daga cikinsu dabbobi ne da suka mutu haka nan ko kuma wani hadari ya jawo mutuwarsa, kuma saboda ba a yanka su ba cin namansu haramun ne. Wasu kuma, ko da yake cin namansu halal ne kuma an ma yanka su, amma da yake an yanka su ne da sunan wani ba Allah ba, namansu ya haramta.

Wannan yanan bayyana cewa hukuncin halasci ko haramcin da Allah yake yiwa abubuwa ba wai kawai bisa amfani ko cutarwarwa da suke yi wa jikin mutane bane, saboda idan ba haka ba ai naman dabbar da aka yanka da sunan Allah da na wacce aka yanka da sunan wani ba Allah ba bashi da bambanci a zahiri amma yana da babban tasiri a ruhin dan Adam da har ya sa Allah ya haramta naman dabbar da a ba a yanka da sunansa ba. Sai kamar yanda wasu ayoyin Alkurani suke bayyanawa, idan mutum ya matsu ya rasa abinda zai ci ya halatta ya ci irin wannan nama domin kare kansa daga mutuwa.

Bangare na biyu na wannan aya kuma yana bayani a kan wata rana mai matukar muhimmanci a tarihin Musulunci, ranar da kafirai suka yanke kaunar sake samun galaba akan Musulmi, ranar da addinin Musulunci ya kammala kuma niimar Allah ga muminai ta cika. Wace rana ce wannan? A wace rana ce a tarihin Musulunci ko kuma a lokacin da Annabi ya ke raye take da wadannan sifofin da babu kamarsu? Shin ranar da Allah ya aiko da Annabi, duk da muhimmancinta, ita ce ranar da aka kammala addini? Ko kuma ranar da Maaiki ya kaura daga Makka zuwa Madina ce take da wadannan sifofi?

Domin amsa wadannan tambayoyi dole ne sai mun san a wani lokaci ne aka saukar da wannan aya. Dukkan malaman tafsiri sun ce ayar ta sauka ne hajjin bankwana da Annabi ya yi a shekara ta 10 bayan hijira wato kusan kartshen rayuwarsa ayar ta sauka. Wasu malamai sun ce a ranar Arafa wato 9 ga watan Zulhijja ayar ta sauka wasu kuma suka ce a ranar 18 ga wata ne a wani wuri da ake kira Ghadir Khum.

Riwayoyi masu yawa sun bayyana cewa a ranar 18 din ne ta sauka kuma Annabi ya gabatar da jawabi mai tsawo wa mahajjata, ya kuma bayyana abubuwa masu yawa, mafi muhimmanci daga cikinsu kuwa shi ne nada magajinsa da ya yi. Maaiki ya daga hannun Imam Ali dan Abu Talib (a.s.) a gaban dubun dubatan mahajjata sannan ya ce: Duk wanda nake shugabansa to Aliyu shugabansa ne. Dangane da wannan muhimmin aiki ne wannan bangare na ayar ta 3 ta sauka. Allah yana cewa a yau kafirai da a da suke fatar cewa idan Annabi ya bar duniya da yake ba shi da da na miji balle ya gaje shi, ba kuma wanda ya ayyana a matsayin magajinsa, zasu iya samun galaba a kan Musulmi kuma Musuluncin m,a baki daya zasu tuge shi gaba daya. Sai da ayar ta sauka sai murna ta koma ciki, kafirai suka debe kauna.

Ta wani gefe kuma da yake addini ya na da dokoki da hukjunce hukunce, idan ba a an sami jagora mai adalci da tsoron Allah lallai wannan addini ragagge ne. Saboda haka nada magajin da zai jagoranci alumma a bayan Annabi shi ne cikan addini da kammalarsa. Niimar da Allah ya farota daga aiko da Annabi da saukar da Alkurani ta cika ta da nada Imam Ali dan Abu Talid (a.s.) a matsayin halifan Manzon Allah, kuma da haka ne addinin ya zama abinda Allah ya zaba ya yarje wa Musulmi.

Wannan aya tana kunshe da darusa da yawa amma zamu yi ishara da kadan daga cikinsu:

1-Samuwar jagora adali mai tsaron Allah yana da muhiommancin da har ma idan ba bu shi to adddini bai cika ba saboda idan ba adalin jagora dukanin niimomi da karfi da alumma ta kunsa za a yi asararsa. 2-Tabbatar addinin Musulunci ya dogara ne a kan biyayya ga jagora na gaskiya, wato imamanci da jagorancin limamai goma sha biyu wadanda Annabi ya ayyanasu domin su zama halifofinsa, wadanda kuma na karshensu shi ne Imam Mahdi (a.s.) wanda yanzu yake rayuwa a cikin gaiba wato ba a ganinsa.

        • To a nan zamu dakata a shirin Hannunka mai Sanda sai kuma shiri na gaba da yardar Allah zaku ji bayanai akan wasun ayoyin na surar Maidah. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi taala wa barakatuhu.

Suratul Ma'ida, Aya Ta 4-6 (Kashi Na 156)

Bismillahir Rahmanir Rahim. Assalamu alaikum jamaa masu saurare. Barkan mu da sake saduwa a shirin Hannunka mai Sanda shirin da yake kawo muku sharhi na ayoyin Alkurani mai girma. A yau shirin zai yi bayani a kan aya ta 4 da ta 5 da ta 6 na wannan sura ta Maidah da fatar zamu sami dacewa.

To madalla. Da farko bari mu saurari aya ta 4:

يَسْأَلُونَكَ مَاذَا أُحِلَّ لَهُمْ قُلْ أُحِلَّ لَكُمُ الطَّيِّبَاتُ وَمَا عَلَّمْتُم مِّنَ الْجَوَارِحِ مُكَلِّبِينَ تُعَلِّمُونَهُنَّ مِمَّا عَلَّمَكُمُ اللّهُ فَكُلُواْ مِمَّا أَمْسَكْنَ عَلَيْكُمْ وَاذْكُرُواْ اسْمَ اللّهِ عَلَيْهِ وَاتَّقُواْ اللّهَ إِنَّ اللّهَ سَرِيعُ الْحِسَابِ{4}

"Suna tambayar ka cewa mene ne aka halatta musu? Ka ce: "An halatta muku tsarkakan abũbuwa da kuma abin da dabbobin masu farauta kuka wadanda kuka koyar (suka kama amma) ku koya musu daga abin da Allah Ya sanar da ku, sai ku ci daga abin da suka kama muku, kuma ku ambaci sunan Allah a kansa. Kuma ku ji tsoron Allah. Hakika Allah Mai saurin hisabi ne."

Ayar da ta gabata ta yi bayani ne akan abubuwan da suke haramun ne a ci, ita kuma wannan aya ta hudu tana bayyana cewa sauran dabbobi halal ko wadanda aka yanka ko kuma wadanda aka horarrun dabbobin farauta suka kama. Wani abin lura a wannan aya kuma shi ne fadar Allah madaukakin Sarki cewa dabbobi masu farauta da mutane suke horaswa kamar karnukan da ake amfani da su wajen farauta, bisa hakika mutane suna koyar da su ne daga ilimin da Allah ya sanar da su. Wajibi a san cewa Allah ne yake horas da karen da yake kamo dabbar wanda kuma yake aikata duk abin da aka sa, kuma suna yi wa mutane biyayya ne da ikon Allah. Wannan aya tana koyar da mu darusa kamar haka: 1-Babbar kaida dangane da abubuwan ci shi ne duk abin da dabi'ar dan Adam take karbarsa take jin dadinsa halas ne idan ba an bayyana haramcinsa a fili ba. 2-Wajibi ne a ji tsoron Allah wajen abubuwan ci, kuma a nisanci duk abubuwan da aka haramta domin da gaggawa ne ukubar Allah tana samun masu cin haramun.

Sai mu saurari aya ta 5:

الْيَوْمَ أُحِلَّ لَكُمُ الطَّيِّبَاتُ وَطَعَامُ الَّذِينَ أُوتُواْ الْكِتَابَ حِلٌّ لَّكُمْ وَطَعَامُكُمْ حِلُّ لَّهُمْ وَالْمُحْصَنَاتُ مِنَ الْمُؤْمِنَاتِ وَالْمُحْصَنَاتُ مِنَ الَّذِينَ أُوتُواْ الْكِتَابَ مِن قَبْلِكُمْ إِذَا آتَيْتُمُوهُنَّ أُجُورَهُنَّ مُحْصِنِينَ غَيْرَ مُسَافِحِينَ وَلاَ مُتَّخِذِي أَخْدَانٍ وَمَن يَكْفُرْ بِالإِيمَانِ فَقَدْ حَبِطَ عَمَلُهُ وَهُوَ فِي الآخِرَةِ مِنَ الْخَاسِرِينَ{5}

"A yau an halatta muku abũbuwa tsarkaka; abincin ma'abuta Littãfi halal ne a gare ku, kuma abincinku halal ne a gare su, (haka) kuma an halatta muku auren 'ya'ya daga muminai da 'yã'ya daga wadanda aka bai wa Littãfi a gabãninku idan kuka basu sadãkinsu, kuna mãsu niyar aure, ba masu yin zina ba, kuma bã mãsu yin dadiro ba. Kuma wanda ya yi ridda tohakika ayyukansa sun watse, kuma shĩ a lãhira yanã daga tababbu."

Wannan aya tana bayani a kan batutuwa guda biyu dangane da Ahlul Kitab wato wadanda aka basu littafi kamar Yahudu da Nasara; wato cin abincinsu da kuma auren matansu. Bisa laakari da hukunce hukuncen da suka gabata na naman da ake ci, bai halatta Musulmi ya ci abincin Ahlul Kitabi ba idan nama ne, amma ana iya cin sauran nauoin abincinsu. Dangane da aure kuwa, ya halatta Musulmi ya auri mace ta Ahlul Kitabi amma bai halatta a aurar musu da mata Musulmi ba, hala saboda galibi mace ta kan sami tasiri wajen mijinta saboda soyayya da saukin halin mata. Kuma sau da yawa ana samun yarinyar mabiya addinin yahudanci ko Kiristanci itan ta auri Musulmi sai ta fahimci addinin Musulunci har ta musulunta.

Har wala yau wannan aya tana kwadaitar da Musulmi da yin aure har ma tana nuni da cewa idan da Musulmi zai so mace Kirista to ya aure ta, a maimakon su yi alakar da ta haramta, ko kuma Musulmin ya bar addininsa saboda ita.

Wannan aya tana koyar da mu darussa kamar haka:

1-Mace mai kamewa tana da daraja ko a wane addini kuwa take, kamar yadda shi ma na miji wajibi ne ya zama mai kamewa ya nisanci alakoki na fasikanci da mata. 2-A mahangar Alkurani mai girma abubuwa biyu ne ake lura da su wajen zabar mijin aure ko matar aure: sune imani da kamewa.

Yanzu kuma sai aya ta 6:

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُواْ إِذَا قُمْتُمْ إِلَى الصَّلاةِ فاغْسِلُواْ وُجُوهَكُمْ وَأَيْدِيَكُمْ إِلَى الْمَرَافِقِ وَامْسَحُواْ بِرُؤُوسِكُمْ وَأَرْجُلَكُمْ إِلَى الْكَعْبَينِ وَإِن كُنتُمْ جُنُباً فَاطَّهَّرُواْ وَإِن كُنتُم مَّرْضَى أَوْ عَلَى سَفَرٍ أَوْ جَاء أَحَدٌ مَّنكُم مِّنَ الْغَائِطِ أَوْ لاَمَسْتُمُ النِّسَاء فَلَمْ تَجِدُواْ مَاء فَتَيَمَّمُواْ صَعِيداً طَيِّباً فَامْسَحُواْ بِوُجُوهِكُمْ وَأَيْدِيكُم مِّنْهُ مَا يُرِيدُ اللّهُ لِيَجْعَلَ عَلَيْكُم مِّنْ حَرَجٍ وَلَـكِن يُرِيدُ لِيُطَهَّرَكُمْ وَلِيُتِمَّ نِعْمَتَهُ عَلَيْكُمْ لَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ{6}

"Yã ku wadanda suka yi ĩmãni, idan kun yi nufin salla, to ku wanke fuskõkinku da hannuwanku zuwa ga gwiwowinsu, kuma ku shãfi kãwunanku da kafãfuwanku zuwa idãnun sãwu. Kuma idan kun kasance mãsu janaba, to sai ku yi wanka, idan kuma kun kasance marasa lafiya kõ cikin tafiya, kõ kuwa dayanku ya dawo daga bayan gari, kõ ku ka taba mata sannan ba ku sami ruwa ba, to sai ku yi taimama a ban kasa mai tsarki, sai ku shafi fuskõkinku da hannuwanku da shi. Allah bã Ya son Ya dora muku wahala ba ne, a'a, Yanã so ne Ya tsarkake ku Ya kuma cika ni'imarsa a gare ku, don ku gõde."

Wannan aya kuma tana cewa mutane su yi godiya ga Allah da niimomin da Allah ya bai wa mutane na abubuwan ci na halal da aure domin biyar bukatunsu na dabi'a, kuma wannan godiya ta hada da yin salla da sauran ibadu. Amma sharadin shiga farfajiyar Ubangiji wato yin salla shi ne tsrakin jiki da ruhi. Kafin salla sai a yi alwala, a wanke fuska da hannaye, a shafi kai da kafafuwa. Idan kuma mutum yana tare da janaba sai ya yi wanka.

Ayar ta ci gaba da cewa, ko da yake abinda ya zama wajibi a tashin farko shi ne alwala ko wanka amma idan ba a sami ruwa ba ko kuma ana tsoron ruwan zai cutar, to sai mutum ya yi taimama da kasa a yi salla. Da ma daga kasa mutum ya ke kuma gare ta zai koma.

Akwai darusa a cikin wannan aya kamar haka:

1-Kazantar jiki da ruhi suna hana mutum samun kusantar Ubangiji (s.w.t.), saboda haka tsabta da tsarki sharadi ne na samun wannan kusanta. 2-Addinin Musulunci ba shi ta matsin da mutum zai rasa mafita domin ana iya sauki a hukunce hukuncen ko da yake ba a dauke su baki daya. 3-Wasu hukunce hukuncen addini sun hadu a yanayi na dabi'a, alal misali, da ruwa da kasa ake alwala ko taimama, lokatan salla kuma suna da alaka da fitowar rana da faduwarta, alkiba kuwa ana gane tad a rana da kuma taurari.

        • To a nan zamu dakata a shirin Hannunka mai Sanda da fatar mun amfana da bayanan hukunce hukuncen shari'a da muka ji. Sai kuma shiri na gaba da yardar Allah zaku ji bayanai akan wasun ayoyin na surar ta Maidah. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi taala wa barakatuhu.

Suratul Ma'ida, Aya Ta 7-11 (Kashi Na 157)

Bismillahir Rahmanir Rahim. Assalamu alaikum jamaa masu saurare. Barkan mu da sake saduwa a shirin Hannunka mai Sanda shirin da yake kawo muku sharhi na ayoyin Alkurani mai girma. A yau sharhin namu zai yi bayanin ayoyi daga ta 7 zuwa ta 11 na wannan sura ta Maidah da fatar zaku kasance tare da mu.

To madalla. Da farko bari mu saurari aya ta 7:

وَاذْكُرُواْ نِعْمَةَ اللّهِ عَلَيْكُمْ وَمِيثَاقَهُ الَّذِي وَاثَقَكُم بِهِ إِذْ قُلْتُمْ سَمِعْنَا وَأَطَعْنَا وَاتَّقُواْ اللّهَ إِنَّ اللّهَ عَلِيمٌ بِذَاتِ الصُّدُورِ{7}

"Kuma ku tuna ni'imar Allah a gare ku da alkawarinsa wanda ya yi muku alkawari da shi a lokacin da kuka ce, 'Mun ji mun kuma bi'. Ku kuma ji tsoron Allah. Hakika Allah Masanin abin da ya ke cikin zukata ne."

A cikin ayoyinda suka gabata mun saurari wasu hukunce hukuncen abubuwan da ake ci, da zaman iyali da kuma wasu ibadu, a wannan aya kuma Allah Madaukakin Sarki yana bayyana mana cewa wannnan shiuriya ce daga gare shi kuma babbar niima ce da Allah ya yi wa muminai saboda haka wajibi ne har a kullum su tyuna da wadannan niimomi. Aya ta uku ta yi bayani kan nada Imam Ali dan Abu Talin (a.s.) a matsayin halkifabn Manzon Allah kuma hakan ya zamna shi ejn kammalar addinin da cikarb niima. Wannan aya ta 7 ma tana tunatar da muminai wannan babban niima tare kuma da yi musu hannun ka mai sanda da cewa: ku kun ji maganar Annabi a Ghadir Khumm inda ya nada Imam Ali kuma kun amince, kuma kun yiu mubayaa, to ku maida hankali kada wata rana ku kwance wannna bubayaar da kuka yi masa.

Da akwai darussa kamar haka a cikin wannan aya:

1- Ni'imar Musulunci da kuma samun jagoranci da Allah ya nada tafi dukm niimomi na zahiri saboda haka ya kamata a kullum Musulmi su sanda wannan kuma su yi godiya a kan haka. 2- Dukkan Musulmi sun daukan ma Ubangiji alkawari ko dai ta hanyar hankali da dabi’ar da Allah ya kimsa wa mutum ko kuma ta hanyar magana a sasari, a kan cewa zasu aikata abinda dokokinsa suka tanada saboda haka duk wani sakacin da zasu yi a wajen gudanart da dokokin Allah tamkar karya alkawari ne.

Sai mu saurari aya ta 8:

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُواْ كُونُواْ قَوَّامِينَ لِلّهِ شُهَدَاء بِالْقِسْطِ وَلاَ يَجْرِمَنَّكُمْ شَنَآنُ قَوْمٍ عَلَى أَلاَّ تَعْدِلُواْ اعْدِلُواْ هُوَ أَقْرَبُ لِلتَّقْوَى وَاتَّقُواْ اللّهَ إِنَّ اللّهَ خَبِيرٌ بِمَا تَعْمَلُونَ{8}

"Yã ku wadanda kuka yi ĩmãni, ku zama mãsu tsayawa sosai da hakkokin Allah, mãsu ba da shaidar gaskiya kada kin wasu mutane ya hana ku yin adalci. Ku yi ãdalci, shĩ ne ya fi kusa da tsoron Allah. Kuma ku ji tsoron Allah. Hakika Allah masanin abin da kuke aikatãwa ne."

Mun riga mun karanta wata aya kama da wannan, ko da yake da dan bambamci kadan, wato aya ta 135 a surar Nisa’i. A waccar aya Allah ya yi umarni da cewa: ku bada sheda ta gaskiya ko da kuwa zata cutar da ku ko danginku, a wanna kuwa yana cewa ku bada sheda ta gaskiya ko da zata amfani abokan gabanku ne. Wato kada ku karkace wa hanyar gaskiya har a wajen abin da ya shafi abokin gaba, kuma kada kiyayya ta jawo muku daukar fansa da take hakkokin wani mutum ko wane ne shi. A muamalar zaman tare dole ne mu yi adalci ga kowa, masoyi ne ko makiyi, kuma wajibi mu dubi Ubangiji mu ji tsoronsa mu kuma sani cewa Allah yana ya sanda dukkan ayyukanmu kuma zai sakanta mana da adalci ko lada zai bayar ko kuma ukuba. Wannan aya tanakoyar da darusa kamar haka:

1-Adalcin zamnatakewa yana yiwuwa ne kadai idan alumma ta yi imani da Allah ta yi biyayya ga dokinsa. 2-Adalci bawai wata kima ce ta fuskar kyawawan dabi’u kadai, umarni ne ma daga Allah kuma a dukkan alalmuran rayuwa, ko a zaman iyali, ko cikin alumma, ko a tsakanin masioya ko makiya wajibi a yi adalci. 3-Takawa da tsoron Allah tana bukatar a nisanci tsaurin raayi wajen goyon bayan alummar mutum ko jinsin ko kabila, wadanda sune kuma suke haifar da makauniyar kiyayya da gaba.

Yanzu kuma sai aya ta 9 da ta 10:

وَعَدَ اللّهُ الَّذِينَ آمَنُواْ وَعَمِلُواْ الصَّالِحَاتِ لَهُم مَّغْفِرَةٌ وَأَجْرٌ عَظِيمٌ{9} وَالَّذِينَ كَفَرُواْ وَكَذَّبُواْ بِآيَاتِنَا أُوْلَـئِكَ أَصْحَابُ الْجَحِيمِ{10}

"Allah Yã yi wa wadanda suka ba da gaskiya suka yi aiki na gari alkawarin yi musu gãfara da ba su lãda mai girma." "Wadanda kuma suka kãfirce suka kuma karyatã ãyõyinmu, wadancan su ne yan wuta."

Wadannan ayoyi guda biyu suna kam ada wasu ayoyi da dama na Alkurani kuma suna jaddada wani batu mai muhimmanci wato maaunin ba da lada ko kuma ukuba shi ne yin imani ko kafircewa, da kuma aikata ayyukan na gari ko munana ne, kuma shi kun kiyaye wadannan abubuwa biyu to kun zama muminai na hakika kuma zamu shiga aljanna, idan kuma ba haka ba, to sakamakonku zai zama azabar wuta.

Darusan zamu koya daga wadannan ayoyi:

1-Sakamakon aljanna da jahannama alkawari ne Allah kuma alkawarin Allah baya tashi. 2-Ayyuka na gari suna gyara abinda ya baci a baya kuma su sa a yafe shi, sannan kuma suna kawo ladan Allah.

Sai mu saurari aya ta 11:

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُواْ اذْكُرُواْ نِعْمَتَ اللّهِ عَلَيْكُمْ إِذْ هَمَّ قَوْمٌ أَن يَبْسُطُواْ إِلَيْكُمْ أَيْدِيَهُمْ فَكَفَّ أَيْدِيَهُمْ عَنكُمْ وَاتَّقُواْ اللّهَ وَعَلَى اللّهِ فَلْيَتَوَكَّلِ الْمُؤْمِنُونَ{11}

"Yã kũ wadanda kuka yi ĩmãni, ku tuna ni'imar Allah a gare ku lõkacin da wasu mutãne suka miko hannayensu gare ku don su cuce ku, sai Allah ya kange hannayensu. To ku ji tsoron Allah, kuma ga Allah ne muminai suke dogara."

A tarihin Musulunci an sami lokuta da dama da abokan gaba suka shirya makarkashiya da yaki domin rusa Musuluncin ma baki daya amma a koda yaushe Allah. Madaukakin sarki yana kare Musulmi saboda ludufinsa da rahamarsa. Wannan aya tana kira ga Muuslmi da cewa kada su mance da ludufin da Allah yake musu, kuma su san cewa hanyar yin godiya ga wadannan niimomi shi ne tsoron Allah da nisantar sabo, wadanda kuma su ne suke wanzar da saukowar taimakon Allah. Hakazalika ayar tana cewa muminai su gane cewa a maimakon dogara da wani karfi na dan Adam da kuma tsoronsa ko kwadayin wani abin da yake alkawirin bayar da shi, lallai su dogara kacokam da ikon Allah maras iyaka, su ji tsoronsa shi kadai, idan suka yi haka zasu sami wani irin karfin da zasu sami nasara a kan duk wani karfi na mutum a kowane fage na rayuwa.

Wannann aya tana koya mana:

1-Tuna niimomin Allah da ludufinsa yana nisantar da mutum daga gururi da gafala da jiji da kai, kuma yana kara wa m,utum kaunar Ubangiji (SWT). 2-Kariyar da Allah yake yi wa Musulmi daga abokan gabarsu da basu da iyaka tana cikin manyan niimominsa a gare su, saboda haka dole ne su uyi masa godiya da harsunansu da kuma ayyukansu.

        • To a nan zamu dakata a shirin Hannunka mai Sanda da fatar Allah ya taimaka mana wajen jin tsoronsa da yi masa godiya da kiyaye dokokinsa. Amin. Sai kuma shiri na gaba da yardar Allah zaku ji bayanai akan wasun ayoyin na surar Maidah. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi taala wa barakatuhu.

Suratul Ma'ida, Aya Ta 12-14 (Kashi Na 158)

Bismillahir Rahmanir Rahim. Assalamu alaikum jamaa masu saurare. Barkan mu da sake saduwa a shirin Hannunka mai Sanda shirin da yake kawo muku sharhi na ayoyin Alkurani mai girma. A yau sharhin namu zai yi bayani a kan aya ta 12 da ta 13 da ta 14 na wannan sura ta Maidah da fatar zaku kasance tare da mu.

To madalla. Da farko bari mu saurari aya ta 12:

وَلَقَدْ أَخَذَ اللّهُ مِيثَاقَ بَنِي إِسْرَائِيلَ وَبَعَثْنَا مِنهُمُ اثْنَيْ عَشَرَ نَقِيباً وَقَالَ اللّهُ إِنِّي مَعَكُمْ لَئِنْ أَقَمْتُمُ الصَّلاَةَ وَآتَيْتُمُ الزَّكَاةَ وَآمَنتُم بِرُسُلِي وَعَزَّرْتُمُوهُمْ وَأَقْرَضْتُمُ اللّهَ قَرْضاً حَسَناً لَّأُكَفِّرَنَّ عَنكُمْ سَيِّئَاتِكُمْ وَلأُدْخِلَنَّكُمْ جَنَّاتٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الأَنْهَارُ فَمَن كَفَرَ بَعْدَ ذَلِكَ مِنكُمْ فَقَدْ ضَلَّ سَوَاء السَّبِيلِ{12}

"Hakika kuma Allah yã dauki alkawari daga Banu lsrã'ĩla, Muka kuma aiko musu shugabanni gõma shã biyu daga cikinsu. Kuma Allah Ya ce: "Hakika Nĩ, inã tãre da ku, Na rantse in har kuka tsai da salla, kuka kuma bã da zakka, kuka kuma ba da gaskiya da manzannĩNa, kuma kuka taimake su, kuka kuma a kuka bai wa Allah rance kyakkyawa, to lallai zan kankare zunubbanku kuma lallai zan shigar da ku aljannoni (wadanda) kõramu suke gudãna ta karkashinsu. Sannan wanda ya kãfirta daga cikinku bãyan wannan, to hakika yã kauce wa madaidaiciyar hanya."

Wannan aya da kluima ayoyin da suka gabace suna bayani ne aka akawuran alummomin nda suka gabata suka daukan ma Allah ta hanyar annabawansa tana cewa:- Allah ya aiki Annabiu Musa don yan kazance jagora ga Banu Israila, ya kuma zabi jagorori goma sha biyu domin su shugabanci dangogin Banu Israila 12 domin su isar da sakon Allah, wanda suka koty adaga Annabi Musa zuwa dangogin nasu. Alkawura tsakanin Allah da Banu Israila sun hada da cewa:-sharadin kariyar da Allah zai yi musu daga abokan gabarsu shi ne su yi riko da umarnin Allah da kiyaye dokokin addinin da Allah ya sauka musu. Wanda zai sami taimakon Allah shi ne mutumin da yake da imani da Allah da Annabawansa, yake kuma yin salla da bayar da zakka, yake kuma kyautatawa da ciyar da dukiyarsa ga masu bukata. Irin wadannan mutane, a duniya suna samun jin kan Allah da rahamarsa, a lahira kuma zasu sami babbar niima da aljanna.

Wasu hadisai suna cewa adadin halifofin Maaikin Allah Muhammadu (s.a.w.) daidai yake da asdadin nuqaba’un Banu Israila wato jagororin da da suka taimaka wa Annbi Musa. Na farkon halifofin Annabi Muhammadu shi ne Imam Ali dan Abu Talib (a.s.) na karshensun kuma Imam Mahdi (a.s.).

Wanna aya tana koyar da mu cewa:

1-Yin imani kadai baya isa sai mutum ya hada da aikata kyawawan ayyuka, saboda haka imani da Annbi kadai ba ya isa, dole ne mutum ya taimaka masa, ya taimaka wa addinsa. 2-Duk wani alherin da mutum ya yi wa bayin Allah tamkar mutum ya yi wa Allah aiki ne, saboda haka bai kamata mutum ya yi gori ba wa wadanda yake taimakawa ba.

Sai mu saurari aya ta 13:

فَبِمَا نَقْضِهِم مِّيثَاقَهُمْ لَعنَّاهُمْ وَجَعَلْنَا قُلُوبَهُمْ قَاسِيَةً يُحَرِّفُونَ الْكَلِمَ عَن مَّوَاضِعِهِ وَنَسُواْ حَظّاً مِّمَّا ذُكِّرُواْ بِهِ وَلاَ تَزَالُ تَطَّلِعُ عَلَىَ خَآئِنَةٍ مِّنْهُمْ إِلاَّ قَلِيلاً مِّنْهُمُ فَاعْفُ عَنْهُمْ وَاصْفَحْ إِنَّ اللّهَ يُحِبُّ الْمُحْسِنِينَ{13}

"Sabõda warware alkawarinsu Muka la'ance su, Muka kuma kekasar da zukãtansu, sunã sauya zancen Allah daga wurinsa, suka kuma bar rabon da aka umurce su da shi. Kuma ba zã ka gushe ba kana ganin ha'inci daga gare su, sai kadan daga cikinsu. To sai ka yi musu afuwa, ka kuma yi rangwame. Hakika Allah Yanã son mãsu kyautatãwa."

Bayan ayar da ta gabata ta yio bayanai kan imani da Allah wannan kuma tana sharhi ne a kan karya alkawarin da yahudawa suka yi. Ayar ta ce sun karya alkawari sun kuma nisantar da kansu daga rahamar Allah, wato Allah ya la'ancesu, kuma daga karshe sai suka ki gaskiya kuma sannu a hankali sai zukatansu suka rufe domin kuwa banda karya alkawari da suka yi sun ma karkatar da ayoyin Allah na littafin da aiko wa annabawansu domin halasta munanan ayyukan da suke yi, lamarin ya kai ga sun fitar da wasu ayoyin ma daga cikin littafi mai tsarki sun mance da su. Ayar tana cewa ba wai Yahudawan zamanin da kadai suka yi wadannan manayan laifuka ba, hatta Yahudawan da suka yiu zamani da Annabin Rahama ma sun yi ta yin ha’inci da kulla makirci wa Musulmi, sun yi koyi da kakanninsu na wancan zamani. Wannan aya tana kjoya mana: 1-Zukata masu tsarki da tsabta sune suke karbar maganar Allah. Su kuma wadanda suke da kazanta, baicin rashin karbar gaskiya suna ma yin kokarin karkatar da lafazi da kuma maanar maganar Allah har ma su shafe ta daga littatafansa idan zasu iya. 2-A tarihance an san da dangin Banu Israila da karya alkawari da aikata hainci.

Yanzu kuma sai aya ta 14:

وَمِنَ الَّذِينَ قَالُواْ إِنَّا نَصَارَى أَخَذْنَا مِيثَاقَهُمْ فَنَسُواْ حَظّاً مِّمَّا ذُكِّرُواْ بِهِ فَأَغْرَيْنَا بَيْنَهُمُ الْعَدَاوَةَ وَالْبَغْضَاء إِلَى يَوْمِ الْقِيَامَةِ وَسَوْفَ يُنَبِّئُهُمُ اللّهُ بِمَا كَانُواْ يَصْنَعُونَ{14}

"Haka kuma dauki alkawari daga wadanda suka ce: "Mu Nasãra ne", sannan su ma suka bar rabon da aka umarce su da shi, sai Muka cusa gaba da kiyaye a tsakãninsu har zuwa ranar alkiyãma. Da sannu kuwa Allah zai bã su lãbarin abin da suke aikatawa."

Wannan ayua kuma ta na bayanin karya alkawarin da nasara suka yi, tana cewa: masu kiran kansu mabiya Al-Masihu su ma sun dauki alkawarin cewa zasu taimaka wa addinin Allah kuma zasu tsaya kyam a kan haka, amma su ma sun karya alkawari kuma sun bi tafarkin Yahudawa da suka gabace su. Su ma sun karkata maganar Allah sun kuma fitar da wani yanki nata daga littafi mai tsarki, sakamkon haka kuma gaba da kiyayya sun auku a tsakaninsu kuma ba zasu rabu da su har tashin alkiyama. Karkacewar da ta fi bayyana a addinin Nasara ko Kiristanci shi ne akidar salus mai cewa Allah uba, Allah da da Allah ruhin mai tsarki, (ko kuma Maryamu) wanda suka maye shi a gurbin tauhidi da kataida Allah Ubangijin da ba shi da abokin tarayya. Wannan aya tana koyar da mu darusa kamar haka:

1-Masu daaawar imani suna da yawa amma masu masu biyayya tab gaskiya ga addini suma da karancin gaske. 2-Tushen sassaba wa da rarraba a cikin alumma shi ne mance wa da Allah, hadin kan alumma kuma yana tabbata idan jammaa suka yi riko da tauhidi na gaskiya. 3-Mu Musulmi mu dauki darasi daga mummunan sakamakon da ya alummomin da suka gabace mu suka sami saboda karya alkawarin da suka yi. Saboda haka mu yi tsayin daka wajen aiwatar da wajibobin addini.

        • To a nan zamu dakata a shirin Hannunka mai Sanda da fatar Allah ya taimaka mana wajen cika alkawarin da muka dauka masa na kasancewa bayinsa masu biyayya da tsoron Allah. Sai kuma shiri na gaba da yardar Allah zaku ji bayanai akan wasun ayoyin na surar Maidah. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi taala wa barakatuhu.

Suratul Ma'ida, Aya Ta 15-17 (Kashi Na 159)

Bismillahir Rahmanir Rahim. Assalamu alaikum jamaa masu saurare. Barkan mu da sake saduwa a shirin Hannunka mai Sanda shirin da yake kawo muku sharhi na ayoyin Alkurani mai girma. A yau sharhin namu zai yi bayani a kan aya ta 15 da ta 16 da ta 17 na wannan sura ta Maidah da fatar zaku kasance tare da mu.

To madalla. Da farko bari mu saurari aya ta 15:

يَا أَهْلَ الْكِتَابِ قَدْ جَاءكُمْ رَسُولُنَا يُبَيِّنُ لَكُمْ كَثِيراً مِّمَّا كُنتُمْ تُخْفُونَ مِنَ الْكِتَابِ وَيَعْفُو عَن كَثِيرٍ قَدْ جَاءكُم مِّنَ اللّهِ نُورٌ وَكِتَابٌ مُّبِينٌ{15}

"Yã ku ma'abuta littãfi, hakika manzonmu yã zo muku yanã bayyana muku da yawa daga abubuwan da kuka kasance kunã bõyewa daga littãfi, yanã kuma kyale abubuwa da yawa. Hakika haske haske yã zo muku daga Allah da kuma littafi mabayyani. "

Ayoyin da suka gabata sun yi mana bayani kan karya alkawari da Yahudawa da nasarawa suka yi, da kuma karkata maganar ALLAH har ma da boye wasu ayoyin littafan da ALLAH ya saukar wa annabawansu ko ma fitar da su baki daya daga littatafan. Ita kujma wanna aya tana cewa da su: ku da da kuke kiran kanku mutanen littafikuma kun karanta littafan ALLAH da suka gabata, ku yi imani mana da wannan annabi wanda shi ma haske ne kuma littafin da ya kawo baya bayyana bayanan da aka sauko da su a cikin litafan ALLAH da suka gabata amma kuma boye su. Darusa: 1-Musulunci addini ne duk duniya kuma yana kiran dukan mabiyan addinan da suka gabace shi da su yi imani da litafinsa wato Alkurani. 2-Koyarwar ALLAH haske ce kuma idan duniya ta rasa wannan koyarwa to lallai tana cikin duhu.

Sai mu saurari aya ta 16:

يَهْدِي بِهِ اللّهُ مَنِ اتَّبَعَ رِضْوَانَهُ سُبُلَ السَّلاَمِ وَيُخْرِجُهُم مِّنِ الظُّلُمَاتِ إِلَى النُّورِ بِإِذْنِهِ وَيَهْدِيهِمْ إِلَى صِرَاطٍ مُّسْتَقِيمٍ{16}

"Da shĩ Allah yake shiryar da wanda ya bi yardarsa zuwa ga hanyõyin aminci, yake kuma fitar da su daga duffai zuwa ga haske da izninsa, yake kuma shiryar da su zuwa tafarki madaidaici."

Ayar da ta gabata ta bayyana Alkurani da cewa littafi ne mai haskakawa, ita kuma wanna aya tana karbar shirirya tana da sharuda kuma mafi muhimanci daga cikinsu shi ne nemna gaskiya da kaunarta. Mai karbar shiriyar Alkurani, to ya karbeta ba don neman dukiya ko mukami ko wasu burace buracen zuciyarsa ba, karbar shiriya ta kasance tsantsa saboda neman gaskiya da kuma yardar Ubangiji mahalicci. Idan wannan sharadi ya tabbata to ALLAH zai fitar da mutum daga duhun sabo da batar da yake haifarwa, sannan zai shiagr da shi farfajiyar haske da annurin imani da ayyukan kyawawa. A sarari yake cewa wannan shiryarwa shimfida ce ga samuwar aminci da lafiyar ruhin mutum da tunaninsa, zai kuma kare shi ndaga kowane irin hadari, a ranar alkiyama za ayi wa kuma mutumq zai shiga aljanna aminci da izinin Ubangiji. Darusa: 1-Ana samun lafiya da aminci ne a jamaar da suke biyayya ga hanyar ALLAH, kuma biyayya ga Alkurani hanya ce da zata kai mutumn wancan manufa. 2-Bil Adam suna samun zama tare cikin aminci da kaunar juna ne kawi idan suka yi riko da addinan da ALLAH ya aiko ta hanyar Annbawansa. 3-Ayyukan da suke kai mutum cikin yardar ALLAH suna bambamta, aikin kwarai suna iya bambamta daga zamani zuwa zamani, amma idan manufar ita ce samun yardar ALLAH to dukkan mutanen masu aika ayyukan kwarai suna kan tafarki ne guda, kuma shi ne tafarki madaidaici.

Yanzu kuma sai aya ta 17:

لَّقَدْ كَفَرَ الَّذِينَ قَآلُواْ إِنَّ اللّهَ هُوَ الْمَسِيحُ ابْنُ مَرْيَمَ قُلْ فَمَن يَمْلِكُ مِنَ اللّهِ شَيْئاً إِنْ أَرَادَ أَن يُهْلِكَ الْمَسِيحَ ابْنَ مَرْيَمَ وَأُمَّهُ وَمَن فِي الأَرْضِ جَمِيعاً وَلِلّهِ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا يَخْلُقُ مَا يَشَاءُ وَاللّهُ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ{17}

"Hakĩka wadanda suka ce wai Allah shĩ ne Al-Masĩhu Isa dan Maryamu sun kãfirta. Ka ce: "Wa ya isa ya hana idan Allah yã yi nufin ya hallaka Al-Masĩhu Isa dan Maryamu da mahaifiyarsa da ma duk wanda yake bayan basa gabã daya?" Kuma mulkin sammai da kasa da abin da ke a tsakãninsu na Allah ne. Yanã halittar abin da ya so. Kuma Allah Mai ĩko ne a kan kõme. "

Wannan aya taan akiran illahirin maabuta littafi da su karbi addinin Musulunci wanda bisa hakika kammala ce ga dukkan addinan ALLAH da suka gabace shi. Ayar tana cewa: me ya sa Kirista suke daukar Annbi Isa (a.s.) a matsayin ALLAH kuma abokin tarayyar ALLAH makadaici? Shin Annbai Isa ba uwa mnai suna Maryam ce ta haife shi ba? To ta yaya zai kasance ALLAH? Ita ma Maryam (a.s.) ba diya ce ga wasu mutane ba? T ta yaya za a ce ita ALLAH ce daga cikin alloli uku? Shin ba ALLAH yana da ikon halaka Isa da Maryamu (a.s.) ba idan yana so? Wadanne irin alloli ne wadannan da ba su iya kare kansu daga mutuwa da shafewa daga wani? Idan aka yi nazarin wannan akida da kyau za a ga cewa wani nau’ii ne na kafirce wa ALLAH domin kuwa daukar wani mutum a matsayin ALLAH yana nufin sauko da matsayin ALLAH. ne zuwa matsayin dan Adam. Daga karshe ayar tana cewa: ai kasancewa Ugabniji ba a raba shi da mallakar sani da iko da mulki marasa iyaka, wanda kuma Annabi Isa (a.s.) da mahaifiyarsa Maryamu (a.s.) basu da wadanna sifofi, kuma ALLAH mahalicci ne kawai yake da san komai yake da iko a kan komai kuma yake mulkin komai, saboda haka da shi ne kadai allanta ta dace. Darusa: 1-Ayyukan nda Musulunci nya sa gaba sun hada da tinkarar duk wata karkatacciyar akida mai surkulle da ta aka shigo da ita cikin addinan da ALLAH ya saukar a gabanin Annabi Muhammadu (s) da kuma tsarkaake wadannan addinai daga bidi’o’i da karkatarwa. 2-Annabawan ALLAH., kowane mukami suka kai, su ‘yan Adam ne kuma ba zasu taba ficewa daga da’irar dan Adam ba, saboda haka gluwi ko wuce gona da iri dangane da wani annabi ya saba wa tauhidin da addinan ALLAHsuka ke koyarwa. 3-Idan da Al-Masihu Isa dan Maryamu alla ne ta yaya makiyansa Yahudawa suka kashe shi suka kuma tsire shi, kamar yanda Kirista suke cewa? Ta yaya halittun alla zasu iya cutar da shi?

        • To a nan zamu dakata a shirin Hannunka mai Sanda da fatar ALLAH. ya tsatkake mana imani da akidar mu. Sai kuma shiri na gaba da yardar ALLAH. zaku ji bayanai akan wasun ayoyin na surar Maidah. Wassalamu alaikum wa rahamatullah wa barakatuhu.


Suratul Ma'ida, Aya Ta 18-22 (Kashi Na 160)

Jama'a masu saurare Asslamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannuka mai sanda, inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki, tare da yin bayani gwargawdon iko kan abin da suke koyar da mu, tare da yi mana hannuka mai sanda a cikin lamurran rayuwa. Har yanzu muna cikin surat Ma'ida, sai a biyo mu sannu a hankali a cikin shirin.

Aya ta (18) surat Ma’idah

وَقَالَتِ الْيَهُودُ وَالنَّصَارَى نَحْنُ أَبْنَاء اللّهِ وَأَحِبَّاؤُهُ قُلْ فَلِمَ يُعَذِّبُكُم بِذُنُوبِكُم بَلْ أَنتُم بَشَرٌ مِّمَّنْ خَلَقَ يَغْفِرُ لِمَن يَشَاءُ وَيُعَذِّبُ مَن يَشَاءُ وَلِلّهِ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا وَإِلَيْهِ الْمَصِيرُ{18}

Kuma Yahudu da Nasãra sun ce: "Mu ne diyan Allah, kuma masõyansa." Ka ce: "To, don me Yake yi muku azãba da zunubanku? Ã'a ku mutãne ne daga wadanda Ya halitta, Yanã gãfartãwa ga wanda ya s0, kuma Yanã azabtar da wanda ya so. Kuma Allah ne da mulkin sammai da kasa da abin da ke tsakãninsu kuma zuwa gare shi makomã take."

A cikin ayoyin da suka gabata mun karanta cewa nasara sun kai annabi Isa matsayin Allantaka, yayin da su kuma su da yahudawa suke kiran kansu ‘ya’yan Allah kuma abokansa, saboda haka azabar Allah ba ta taba shafarsu ba a lahira.

Yahudawa sun dauka su ne suka fi kowa a bayan kasa, su ne fiyayyun halitta, kur’ani ya ba su amsa da cewa inda su ‘yan lele ne a wurin to me ya sanya ya azabtar da su kuma ya tsine musu bayan da suka yi barna a bayan kasa?

Darussan da za mu dauka a nan su ne:

1 – Nuna bangaranci ko wariyar launin fata ko jinsi ko kabilanci ba ya halatta a cikin addinin musulunci.

2 – Ruduwa da matsayi na tare da babban hadari, domin kuwa karshen mutum shi ne a rayuwarsa.

3 – Rabon ajanna da wuta yana hannun Allah, babu wanda zai yanke hukunci ya ce wane dan aljanna wane ne dan wuta.

Aya ta (19) surat Ma’idah

يَا أَهْلَ الْكِتَابِ قَدْ جَاءكُمْ رَسُولُنَا يُبَيِّنُ لَكُمْ عَلَى فَتْرَةٍ مِّنَ الرُّسُلِ أَن تَقُولُواْ مَا جَاءنَا مِن بَشِيرٍ وَلاَ نَذِيرٍ فَقَدْ جَاءكُم بَشِيرٌ وَنَذِيرٌ وَاللّهُ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ{19}

Yã Mutãnen Littãfi! Lalle Manzonmu yã je muku yanã bayyana muku, a kan lõkacin fatara daga manzanni, dõmin kada ku ce: "wani mai bayar da bushãra bai zo mana ba, kuma haka wani mai gargadi bai zo ba." To, hakĩka, mai bãyar da bushãra da mai gargadi sun je muku. Kuma Allah ne, a kan dukkan kõme, Mai ĩkon yi.

Bisa dalilai da aka dogara da su na tarihi, an haifi manzon Allah ne a cikin shekara ta 570 miladiyya, kuma an ba shi sakon annabci a cikin shekara ta 610 miladiyya, wato kusan shekaru 600 daga lokacin annabi Isa zuwa lokacin haihuwar manzon Allah ba aiko wani annabi ba, to amma kuma akwai malamai masana bayin Allah da suke kan tafarkin annabawn Allah da suke shiryar da mutane, suna yi msu wa'azi.

Wannan ayar tana yanke duk wani hanzari ga ahlul kitab bayan zuwan manzon Allah (SAW) dauke da sakon kur'ani mai tsarki, domin kafin zuwan manzo suna da labarin annabawa, kuma suna da labarinsa a cikin littafansu, saboda haka su ne ya kamata su fara yin imani da shi kafin wasu mutane.

Darussan koyo daga wannan aya mai albarka:

1 – Zuwan annabawa ya rufe duk wani hanzarin da mutum zai iya kawo na rashin yin imani da Allah.

2 – Sakon da annabawa suke dauke da shi ga dan Adam yana dauke da bushara ga wadanda suka yi imani kuma suka yi ayyuka na gari, hakan nan kuma yana dauke da gargadi ga wadanda suka baya ga bin tafarkin kadaita Allah. Aya ta (20) surat Ma'idah

وَإِذْ قَالَ مُوسَى لِقَوْمِهِ يَا قَوْمِ اذْكُرُواْ نِعْمَةَ اللّهِ عَلَيْكُمْ إِذْ جَعَلَ فِيكُمْ أَنبِيَاء وَجَعَلَكُم مُّلُوكاً وَآتَاكُم مَّا لَمْ يُؤْتِ أَحَداً مِّن الْعَالَمِينَ{20}

Kuma a lõkacin da Musa ya ce wa mutãnensa: "Yã ku mutãnena! Ku tuna ni'imar Allah a kanku; dõmin Yã sanya annabãwa a cikinku, kuma Yã sanya ku sarãkuna, kuma Yã bã ku abin da bai bai wa kõwa ba daga tãlikai."

Annabi Musa (AS) yan atunatar da Bani Isra'ila da kada su manta da irin ni'imomin da Allah ya yi musu, ya aiko musu annabawa masu yawa, ya ba wasu daga cikin annabawansu mulki, wato ishara ga Annabi Sulaiman da kuma Annabi Yusuf (AS) ya kuma baiwa Bani Isar'ila abubuwa da dama da bai baiwa sauran mutanen duniya ba a lokacin, saboda haka ba su da wani dalili na yi shakku kan da ayoyin Allah, ko kuma zargin gazawa daga annabi Musa ko zargin Allah da kasa taimakonsu a kan danniyar Fir'auna.

Darussan koyo daga wannan aya:

1 – Ni'aimar aiko annabawa na daga cikin ni'imomin da suka wajabta wad an adam yin godiya ga Allah madaukakin sarki.

2 – Dole ne sauran al'ummomi su dauki darasi daga tarihin yahudawa wato Bani Isra'ila, domin kuwa Allah ya daukaka su, ya yi musu dukkanin ni'imomi, amma kuma suka butulce masa, suka kashe annabawa da dama da aka aiko musu, lamarin da ya kai su ga fadawa cikin kaskanci a lokacin mulkin Fir'ana.

Aya ta (21) da (22) surat Maidah

يَا قَوْمِ ادْخُلُوا الأَرْضَ المُقَدَّسَةَ الَّتِي كَتَبَ اللّهُ لَكُمْ وَلاَ تَرْتَدُّوا عَلَى أَدْبَارِكُمْ فَتَنقَلِبُوا خَاسِرِينَ{21} قَالُوا يَا مُوسَى إِنَّ فِيهَا قَوْماً جَبَّارِينَ وَإِنَّا لَن نَّدْخُلَهَا حَتَّىَ يَخْرُجُواْ مِنْهَا فَإِن يَخْرُجُواْ مِنْهَا فَإِنَّا دَاخِلُونَ{22}

"Yã mutãnena! Ku shiga kasar nan abar tsarkakewa, wadda Allah Ya rubuta sabõda ku, kuma kada ku kõma da bãya, har ku juya kunã mãsu hasara."

Suka ce: "Ya Musã! a cikinta akwai wasu mutãne mãsu karfi kuma lalle ne bã zã mu shige ta ba sai sun fice daga gare ta, to, idan sun fice daga gare ta, to lalle ne mu, masu shiga ne."

Annabi Musa (AS) ya kirayi Bani Isra'ila bisa umurnin Allah, da su shiga biranan Shamat da Qods su yaki azzauman mahukuntan da ke cikinsu, kada su juya baya daga umurnin Allah sai su fada cikin hasara da tabewa ta duniya da talahira, amma Bani Isra'ila saboda taurin kai da kuma tsabar tsoro, da kuma tunanin wahalar da suka sha a hannun Fir'auna, hakan ya sanya su yin tababa wajen shiga wadannan birane, daga karshe dai suka ce ma Annabi Musa ba za su taba shiga cikin Shamat da qods ba matukar dai sarakunansu suna cikinsu, amma idan sarakunan da kansu ne suka fita suka bar shamat da Quds to tabbas za su shiga, amma ba za su yi yaki ba da kowa ba.

Darussan koyo daga wadanna ayoyi:

1 – Duk mutanen da suke da'awar Imani da Allah da yin biyayya ga manzaninsa, dole ne su tsarkake wurare masu tsarki daga zaluncin azzalumai.

2 – Daya daga cikin abin da ke saurin rusa mayaka shi ne tashin farko su tsorata daga abokan gabarsu, domin kuwa hakan zai raunana su kuma ya yi sanadiyar juyawarsu.

Da wannan ne muka kawo karshen shirin namu na yau, sai idan Allah ya kai mu a shiri na gaba za a ji mu daga inda muka tsaya, kafin lokacin nake yi muku fatan alkhairi, wassalamu alaikum wa rahmatullah.

Suratul Ma'ida, Aya Ta 23-26 (Kashi Na 161)

Jama'a masu saurare Asslamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannuka mai sanda, inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki, tare da yin bayani gwargawdon iko kan abin da suke koyar da mu, tare da yi mana hannuka mai sanda a cikin lamurran rayuwa. Har yanzu muna cikin surat Ma'ida, sai a biyo mu sannu a hankali a cikin shirin.

Aya ta (23) surat Ma’idah

قَالَ رَجُلاَنِ مِنَ الَّذِينَ يَخَافُونَ أَنْعَمَ اللّهُ عَلَيْهِمَا ادْخُلُواْ عَلَيْهِمُ الْبَابَ فَإِذَا دَخَلْتُمُوهُ فَإِنَّكُمْ غَالِبُونَ وَعَلَى اللّهِ فَتَوَكَّلُواْ إِن كُنتُم مُّؤْمِنِينَ{23}

Wasu maza biyu daga wadanda suke tsõron Allah, Allah Yã yi ni'ima a kansu, suka ce: "Ku shiga gare su daga kõfar birnin, idan kuka shige ta, to, lalle ne ku mãsu rinjãya ne, kuma sai ku dogara ga Allah idan kun kasance muminai."

Idan masu saurare suna tune, a cikin shirin da ya gabata mun ji ayar da ke bayani kan yadda annabi Musa (AS) ya bukaci Bani Isar'ila da su yi yaki domin su kwato birninsu da wasu azzaluman sarakuna suka kwace kuma suka mamaye, amma Bani Isra'ila sun tsorata da su sakamakon azabar da suka dandana a karakshin mulkin Fir'auna, sai suka ce su ba za su yi yaki ba, sai idan sarakunan sun fita daga birnin to a lokacin za su shiga ba tare da yaki ba.

A lokacin sai wasu mutane biyu daga cikinsu wadanda suka yi imani na gaskiya, wadanda aka ambaci sunayensu a cikin littafin Attaura wato Yusha, da kuma Kalib, suka ce me ya sanya za ku yi musu da annabin Allah, ku shiga cikin wannan gari ku yaki, idan har kuka shiga birnin kuna masu biyayya ga umurnin Annabin Allah to tabbas za ku galaba, ku yi dogaro ga Allah za ku samu nasar, domin kuwa Allah madogara ga masu imani.

Darussan koyo daga wannan ayar:

1 – Duk wanda ya ji tsoron Allah, to babu wani abu a cikin duniya da zai iya tsorata shi, imani shi ne gishikin karfin zuciya da daukaka.

2 – Idan mutane sun mike da kansu ne za su samu taimakon Allah, amma tawakkali ga Allah ba tare da mikewa ba ba shi da ma'ana.

Aya ta (24) surat Ma'idah

قَالُواْ يَا مُوسَى إِنَّا لَن نَّدْخُلَهَا أَبَداً مَّا دَامُواْ فِيهَا فَاذْهَبْ أَنتَ وَرَبُّكَ فَقَاتِلا إِنَّا هَاهُنَا قَاعِدُونَ{24}

Suka ce: "Ya Musa! Lalle ne mu, bã za mu shige ta ba har abada matukar sun dawwama a cikinta, sai ka tafi kai da Ubangijinka dõmin ku yi yãki. Lalle ne mu munã a nan zaune."

Duk da kiran da annabi Musa (AS) ya yi ma Bani Isra'ila, tare da karfafa gwiwarsu da wasu manya daga cikinsu suka yi musu, na su yi tawakkali da Allah su shiga birnin su yaki kamar yadda annabi Musa ya ba su umurni, amma Bani Isra'ila saboda tsabar taurin kai sun ki bin umurnin Annabi Musa, maimakon haka ma sai suka koma suna yi masa izgili suna cewa; su kam ba za su taba shiga birnin Qods da shamat su yi yaki ba, in ya so Annabi Musa da shi da ubanjinsa su tafi su biyu su yakin, su za su zauna jira su, idan sun yi nasara to su a lokacin su kuma za su shigo birnin.

Darussan koyo daga wannan aya mai albarka:

1 – Bani Isra'ila sun bar mummunan misali na mutane masu tananin musu da jayyaya da umurnin Allah, kuma makomarsu babban darasi ne ga sauran al'ummomi, domin kuwa hakan ne ya kais u ga fadawa cikin fushin Allah da tsinuwarsa har zuwa tashin kiyama, sai dai wadanda suka tuba suka dawo suka yi imani da gaskiya.

2 – Aikin annabawan Allah shi ne shiryar da mutane da gaya musu sakon Allah, saura kuma ya rage ne ga su mutane su yi biyayya ko su saba, duk wanda suka yi yana tattare da sakamakonsa. Aya ta (25) surat Ma'idah

قَالَ رَبِّ إِنِّي لا أَمْلِكُ إِلاَّ نَفْسِي وَأَخِي فَافْرُقْ بَيْنَنَا وَبَيْنَ الْقَوْمِ الْفَاسِقِينَ{25}

Ya ce: "Yã Ubangijina! Lalle ne nĩ, bã ni mallakar kõwa fãce kaina da dan'uwãna, Ka rarrabe a tsakãninmu da tsakãnin mutãne fãsikai."

Bani Isra'ila sun kasance karkashin zalunci da danniyar Fir'ana na tsawon shekaru, Allah ya aiko Annabi Musa ya 'yantar da su daga bautar Fir'auna ya mayar da su mutane, to amma kuma su wadannan mutanen aka wayi gari suna yi ma Annabi Musa tsaurin kai da Izgili, ta yadda har ya yanke kauna kan cewa ba za su bi umurninsa na shiga birnin Qods ba ,domin yin yaki da kwato birnin daga hannun azzaluman sarakuna, saboda haka ya sheda ma Allah cewa shidai ya yi iyakacin yinsa kuma Allah ya san haka, saboda haka yanzu ba shi da wani abin yi ba shi da iko kan kowa a cikinsu da shi sai dan uwansa Haruna, sai ya roki da ya shiga tsakaninsu da wadannan fasikan mutane.

Darussan koyo daga wannan aya mai albarka:

1 – Annabawa ba su taba gazawa wajen isar da sakon Allah ba, sai dai mutane suke kin yin aiki da sakon da annabawan suka zo da shi daga Allah.

2 – Annabawa suna dogaro ne da Allah tare da mayar da komai gare shi a kowane lokaci, ko mutane sun bi su ko ba su bi su ba.

Aya (26) surat Ma'idah

قَالَ فَإِنَّهَا مُحَرَّمَةٌ عَلَيْهِمْ أَرْبَعِينَ سَنَةً يَتِيهُونَ فِي الأَرْضِ فَلاَ تَأْسَ عَلَى الْقَوْمِ الْفَاسِقِينَ{26}

(Allah) Ya ce: "To, lalle ne ita abar haramtãwa ce a gare su, shekara arba'in sunã yin dimuwa a cikin kasa. Sabõda haka kada ka yi bakin ciki a kan mutãne fãsikai."

Wasu lokuta Allah yak an ladabtar da mutane saboda wani mumman aiki da suka aikata tun a nan duniya, ta yadda wata kila hakan ya sanya su yi nadama su koma ga Allah, wani lokaci kuma ya kan kyale su har sai sun koma gare shi.

Bayan da annabi Musa ya yanke kauna kan Bani Isra'ila ba za su bi umurninsa na shiga birnin Quds su yi yaki ba, sai Allah madaukakin sarki ya ladabtar su ta hanyar saka musu dimuwa, suka rasa ha inda suke suna ragaita a cikin sahar Sina'a har tsawon shekaru arba'in.

Ya zo a cikin ruwayar tarihi cewa a lokacin da suke cikin wannan dimuwar ne Allah madaukakin sarki ya karbi ran annabi Musa, kuma daga bisani ala tilas sai da suka yi yaki domin shiga Qods, alhali da sun bi umurnin annabi Musa tun farko sun yi yakin kamar yadda umurce dab a su shiga cikin fushin Allah ba.

Darussan koyo daga wannan aya:

1 – Saba umurnin manzannin Allah yana jawo fushin ubangiji da janyewar albarka a cikin rayuwar mutane.

2 – Idan musiba ta zo ta kan shafi mutane baki daya sakamakon abin da wasu daga cikinsu suka aikata.

Da wannan ne muka kawo karshen shirin namu na yau, sai idan Allah ya kai mu a shiri na gaba za a ji mu daga inda muka tsaya, kafin lokacin nake yi muku fatan alkhairi, wassalamu alaikum wa rahmatullah.

Suratul Ma'ida, Aya Ta 27-31 (Kashi Na 162)

Jama'a masu saurare Asslamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannuka mai sanda, inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki, tare da yin bayani gwargawdon iko kan abin da suke koyar da mu, tare da yi mana hannuka mai sanda a cikin lamurran rayuwa. Har yanzu muna cikin surat Maida, sai a biyo mu sannu a hankali a cikin shirin.

Aya ta (27) surat Ma’idah

وَاتْلُ عَلَيْهِمْ نَبَأَ ابْنَيْ آدَمَ بِالْحَقِّ إِذْ قَرَّبَا قُرْبَاناً فَتُقُبِّلَ مِن أَحَدِهِمَا وَلَمْ يُتَقَبَّلْ مِنَ الآخَرِ قَالَ لَأَقْتُلَنَّكَ قَالَ إِنَّمَا يَتَقَبَّلُ اللّهُ مِنَ الْمُتَّقِينَ{27}

Kuma karantã musu lãbãrin diya biyu na Ãdamu da gaskiya, a lõkacin da suka bãyar da baiko, sai aka karba daga dayansu kuma ba a karba daga dayan ba, ya ce: "Lalle ne zan kashe ka." ya ce: "Abin sani dai, Allah yana karbã daga mãsu takawa ne."

Ya zo a cikin ruwayar tarihi cewa, annabi Adamu (AS) yana da wasu 'ya'ya biyu, Habila da Kabila, Habila yana yin kowon dabbobi, shi kuma kabila manomi ne, sai Habila ya gabatar da dabbar da ya fi so a cikin dabbobinsa a matsayin layya domin Allah, yayin da shi kuma Kabila ya gabatar da mafi kyau daga abin da ya noma, sai Allah ya karbi layyar Habila shi kuma Kabila ba a karbi abi da ya gabatar ba, wannan ya sanya Kabila yin hassada a kan dan uwansa Habila, domin kuwa kamar yadda ya zo a cikin ruwaya, shi ya kasance mai zafin rai ne da fushi, saboda haka sai shiga yin barazanar kisa a kan dan uwansa habila, shi kuma sai ya ce masa karbar lamarin duka yana hannun Allah neb a yin a ba ne, kuma duk abin da ya yi akwai hikima a cikinsa, saboda haka kada ka yi fushi da ni, domin kuwa Allah yana karba ne daga wadnda suka yi takawa, suka yi aiki domin sa shi kadai.

Darussan koyo daga wannan aya:

1 – Tarihi tamkar filita ne da ke haskaka ma 'yan baya su san abin da ya faru ga magabata, domin su yi koyi da mai kyau daga cikin ayyukansu, kuma su guji maimaita kurakuransu.

2 – Yin aiki aiki shi kadai ba zai wadatar ba, har sai niyya ta zama domin Allah. 3 – Hassada na kai mutum zuwa ga aikata manyan laifuka da suka hada da kisan kai, kamar yadda ta faru da annabi Yusuf da 'yan uwansa.

Aya ta (28) da (29) surat Ma'idah

لَئِن بَسَطتَ إِلَيَّ يَدَكَ لِتَقْتُلَنِي مَا أَنَاْ بِبَاسِطٍ يَدِيَ إِلَيْكَ لَأَقْتُلَكَ إِنِّي أَخَافُ اللّهَ رَبَّ الْعَالَمِينَ{28} إِنِّي أُرِيدُ أَن تَبُوءَ بِإِثْمِي وَإِثْمِكَ فَتَكُونَ مِنْ أَصْحَابِ النَّارِ وَذَلِكَ جَزَاء الظَّالِمِينَ{29}

"Lalle ne idan ka shimfida hannunka gare ni dõmin ka kashe ni, ban zan shimfida hannuna gare ka ba dõmin in kashe ka. Lalle ne nĩ inã tsõron Allah Ubangijin tãlikai.

"Lalle ne nĩ inã nufin ka kõma da zunubina game da zunubinka, har ka kasance daga abõkan wuta. Kuma wannan shĩ ne sakamakon azzãlumai."

Habila yana ma dan uwansa Kabila hannuka mai sanda kana bin da yake so ya aikata na kisan kai, da cewa hakan babban sabon Allah, saboda haka ko da shi ya kudiri aniyar kashe shi, to ba zai hakan saboda tsoron Allah, yana tsoron hisabi a gaban Allah a ranar kiyama.

Habila ya san cewa dan uwansa Kabila zai kashe shi, amma kuma bai yi tunanin mayar da martani kansa ba, illa dai kawai yana jima dan uwansa tsoron abin da ke jiransa na azabar wutar jahannama matukar dai ya aikata kisan kai, kamar yadda shaidan ke sawwala masa da ya yi.

Darussan koyo daga wadannan ayoyi:

1 – A lokacin da mutum salihi yake magana da mai hassada da ke neman aikata wani danyen aiki, to ya yi masa magana ta hankali domin ya fadakar da shi hadarin da yake ciki.

2 – Idan mutum zai guji aikata wani aiki maras kyau to ya yi hakan domin Allah, kamar yadda Habila bai ce ma Kabila bai da karfin da shi ma zai kashe ba, a' a ya ce masa shi ba zai sanya hannusa ya kashe ba saboda tsoron Allah, ba wai don ba zai iya yin hakan ba.

Aya ta (30) da (31) surat Ma'idah

فَطَوَّعَتْ لَهُ نَفْسُهُ قَتْلَ أَخِيهِ فَقَتَلَهُ فَأَصْبَحَ مِنَ الْخَاسِرِينَ{30} فَبَعَثَ اللّهُ غُرَاباً يَبْحَثُ فِي الأَرْضِ لِيُرِيَهُ كَيْفَ يُوَارِي سَوْءةَ أَخِيهِ قَالَ يَا وَيْلَتَا أَعَجَزْتُ أَنْ أَكُونَ مِثْلَ هَـذَا الْغُرَابِ فَأُوَارِيَ سَوْءةَ أَخِي فَأَصْبَحَ مِنَ النَّادِمِينَ{31}

Sai ransa ya kawãta masa kashe dan'uwansa, sai kuwa ya kashe shi, sa'an nan ya wayi gari daga mãsu hasãra.

Sai Allah Ya aiki wani hankãka, yanã tõno a cikin kasa dõmin ya nuna masa yadda zai turbude gãwar dan'uwansa. Ya ce: "Kaicõna! Nã kãsa in kasance kamar wannan hankãka dõmin in turbude gãwar dan'uwana?" Sai ya wãyi gari daga mãsu nadãmã.

Duk da irin nasiha da kuma jawo hankalin Kabila da Habila ya yi, amma dai zuciyarsa ta raya masa cewa babu abin da ya kamata ya yi illa ya kashe dan uwansa Habila sai kuma ya kashe shi. Bayan da ya aikta wannan danyen aiki sai kuma duniya ta yi masa kunci, ya rasa inda zai sanya kansa, domin kuwa ga shi ya yi kisan kai, kuma wanda ya kashe dan uwansa ne da suke tare uwa daya uba daya, kuma ga gawarsa ya rasa yadda zai yi da ita, amma daga bisani Allah ya aiko wani hankaka domin ya nuna masa yadda zai yi ya bizne gawar dan uwansa a cikin kasa.

Wannan mummunan aiki da Kabila ya aikata na kisan kai, shi ne irinsa na farko da aka fara aikatawa a bayan kasa, wanda kuma tun daga lokacin da ya yi hakan ya shiga cikin yanayi na nadama da kunci har ya bar gidan duniya, abu mafi muni kuma shi ne fushin Allah da azabarsa da ya saya da kansa.

Darussan koyo daga wadannan ayoyi:

1 – Kiyayya da gaskiya na tsawon tarihi tun daga mutanen farko, kuma mutuwar farko dad an adam ya yi ya fara ne da yin shahada a tafarkin gaskiya.

2 – Wasu lokuta Allah kan sanya dabbobi da tsuntsaye su zama masu nuna ma dan Adam hanya idan ya shiga cikin wani hali gazawa.

3 – Bisa umurnin Allah dole ne a bizne gawar dan Adam, kone shi ko abin da ya yi kama da haka, ya saba wa koyarwa ta dukkanin addinan da aka safkar daga sama.

Da wannan ne muka kawo karshen shirin namu na yau, sai idan Allah ya kai mu a shiri na gaba za a ji mu daga inda muka tsaya, kafin lokacin nake yi muku fatan alkhairi, wassalamu alaikum wa rahmatullah.

Suratul Ma'ida, Aya Ta 32-35 (Kashi Na 163)

Jama'a masu saurare Asslamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannuka mai sanda, inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki, tare da yin bayani gwargawdon iko kan abin da suke koyar da mu, tare da yi mana hannuka mai sanda a cikin lamurran rayuwa. Har yanzu muna cikin surat Ma'ida, sai a biyo mu sannu a hankali a cikin shirin.

Aya ta (32) surat Ma’idah

مِنْ أَجْلِ ذَلِكَ كَتَبْنَا عَلَى بَنِي إِسْرَائِيلَ أَنَّهُ مَن قَتَلَ نَفْساً بِغَيْرِ نَفْسٍ أَوْ فَسَادٍ فِي الأَرْضِ فَكَأَنَّمَا قَتَلَ النَّاسَ جَمِيعاً وَمَنْ أَحْيَاهَا فَكَأَنَّمَا أَحْيَا النَّاسَ جَمِيعاً وَلَقَدْ جَاءتْهُمْ رُسُلُنَا بِالبَيِّنَاتِ ثُمَّ إِنَّ كَثِيراً مِّنْهُم بَعْدَ ذَلِكَ فِي الأَرْضِ لَمُسْرِفُونَ{32}

"Saboda haka muka rubuta a kan Banĩ lsrã'ĩla cewa, lalle ne wanda ya kashe rai bã da wani rai ba, ko barna a cikin kasa, to kamar yã kashe mutãne duka ne, kuma wanda ya rãya rai, to, kamar yã rãyar da mutãne ne gabã daya. Kuma lalle ne Manzanninmu sun je musu da hujjõji bayyanannu, sa'an nan kuma lalle ne, mãsu yawa daga gare su a bãyan wannan, mãsu barna ne a cikin kasa."

A cikin shirin da ya gabata mun ji abin da ya faru tsakanin 'ya'yan Annabi Adamu (AS) wato Kabila da Habila, inda Kabila ya yi dan uwansa hassada, saboda an karbi abin da ya gabatar na layya domin Allah, yayin da ba a karbi abin da Kabila ya gabatar ba, saboda haka hasada da son zuciya suka kai shi ga kisan dan uwansa Habila.

Allah madaukakin sarki a cikin wannan aya saboda wannan abin da ya faru, aka saka shi ya zama doka a cikin addinin Allah ta hanayar Annabawa cewa, duk wanda ya kashe mutum ba bisa hakki na shari'a ba, to kamar ya kashe mutane ne baki daya, haka nan kuma duk wanda ya daya tseratar da mutum tamkar ya tseratar da mutane ne baki daya.

Kur'ani mai tsarki yana nuni da wani lamari mai matukar muhimmanci a cikin rayuwar dan Adam, inda yake nuni da cewa matsayin mutane tamkar jiki guda ne, a duk lokacin wani abu ya sami wani bangare to ya samu sauran bangarorin jikin ne baki daya, domin babu dalili na kashe ran mutum ba tare da hakki na shari'a ba, kuma yin hakan laifi ne a wajen Allah.

Wani abu muhimmi a nan shi ne, duk da hani mai tsanani da musulunci ya yi kan kisan ran dan Adam, amma kuma ya halasta hakan a wurin hukunci na shari'a, kamar yin kisasi a wurin hukunci, a lokacin da wani ya kashe wani da gangan, to hukuncinsa na kisasi shi ne shi ma a kasha shi, amma shari'a c eke hakkin zartar da hakan ba mutane ne daidaiku za su dauki hukunci a hannunsu ba.

Karshen ayar ya yi nuni da irin taurin kan Bani Isra'ila, da kuma yadda suka rika bijire ma ayoyin Allah, ta yadda sukan yi shishigi har a kan annabawan Allah, inda suka kashe da dama daga cikinsu saboda tsananin kiyayya da gaskiya.

Darussan koyo a nan su ne:

1 – Dukkanin mutane tamkar wata sarka ce da bangarorinta suke hade da juna, idan aka balle wani bangare daga cikinta, to an rage karfinta da girmanta da kuma yawanta.

2 – Gwargwadon matsayin aiki a wurin Allah gwargwadon tasirinsa a cikin al'umma, kisan kai da ganganci tamkar kasha mutane ne baki daya, yayin da kashe wanda ya yi kisan kai na ganganci ta hanyar kisasi, raya al'umma ne baki daya.

3 – Yin duk wani aikin taimakon jama'a tamkar tseratar da su ne, tamkar raya su ne.

Yanzu kuma sai a saurari karatun ayoyi na (33) da (34) a cikin surat Ma'idah

إِنَّمَا جَزَاء الَّذِينَ يُحَارِبُونَ اللّهَ وَرَسُولَهُ وَيَسْعَوْنَ فِي الأَرْضِ فَسَاداً أَن يُقَتَّلُواْ أَوْ يُصَلَّبُواْ أَوْ تُقَطَّعَ أَيْدِيهِمْ وَأَرْجُلُهُم مِّنْ خِلافٍ أَوْ يُنفَوْاْ مِنَ الأَرْضِ ذَلِكَ لَهُمْ خِزْيٌ فِي الدُّنْيَا وَلَهُمْ فِي الآخِرَةِ عَذَابٌ عَظِيمٌ{33} إِلاَّ الَّذِينَ تَابُواْ مِن قَبْلِ أَن تَقْدِرُواْ عَلَيْهِمْ فَاعْلَمُواْ أَنَّ اللّهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ{34}

Abin sani kawai sakamakon wadanda suke Yãkin Allah da Manzonsa, kuma sunã aiki a cikin kasa dõmin barna, a kashe su ko kuwa a gicce su, kõ a kakkãtse hannuwansu da kafãfunsu daga sãbãni, ko kuwa a kõre su daga kasa. Sannan wulakanci ya tabbata a gare su a cikin rãyuwar duniya, kuma a Lãhira sunã da wata azãba mai girma.

Fãce wadanda suka tuba tun a gabãnin ku sãmi ĩko akansu, to ku sani cewa lalle ne, Allah Mai gãfara ne, Mai jin kai.

Ayar da ta gabata tana yin Magana ne kan matsayin mutum da kuma alfarmarsa, yayin da wadannan ayoyi suke yin ishara da cewa, idan wani bai girmama ran dan adam to shi ma bai cancanci wannan matsayi na a girmama ransa ba, domin kuwa zubar da jinin mutum naui ne na barna a bayan kasa, naui na yin hawan kawara da a kan dokokin Allah, kuma wadanda suke yin fatali da dokokin Allah suna yin fito na fito da Allah ne.

Ayar ta ce akwai sakamo kashi hudu a kan masu yada barna da shelanta yaki kan Allah da manzonsa, na daya dai ko a kashe su, ko a gicce su, ko a yanke hannayensu da kafafunsu bisa sabani, wato hannun dama da kafar hagu, ko kuma hannun hagu da kafar dama, ko kuma kuma a kore su daga kasar musulmi, domin kuwa su suna cikin tabewa ta duniya da lahira, sai dai wadanda suka tuba daga cikinsu kafin a cimma su, to su wadannan za su iya samun afuwa, domin kuwa Allah mai tausayi ne da rangwame.

To amma abin la'akari da shi a nan shi ne, kamar yadda muka fada a baya cewa, jagoran musulmi (Hakim Shar'i) shi ne zai duba ya ga girman laifin kafin yanke hukunci daya daga cikin wadannan abubuwa hudu da aka ambata.

Darussan koyo a nan su ne:

1 – Domin gyara a cikin al'umma, dole ne a samu masu wa'azi da shiryarwa, kuma dole ne kotun shari'a su yi hukunci da adalci.

2 – Wadanda suke kawo matsaloli da cutar da ak'umma wajibi ne kan mahukunta su yi maganinsu domin sauran al'umma ta samu salama.

3 – Zartar hukunci irin na musulunci na bukatar tsarin gwamnati da na shari'a su yi daidai na musulunci, domin abubuwa ne biyu da suke tafiya tare da juna.

Sai a saurari karatun aya ta (35) a cikin surat Ma'idah

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُواْ اتَّقُواْ اللّهَ وَابْتَغُواْ إِلَيهِ الْوَسِيلَةَ وَجَاهِدُواْ فِي سَبِيلِهِ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ{35}

"Yã ku wadanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da takawa, kuma ku nemi tsari zuwa gare shi, kuma ku yi jihãdi a cikin hanyarsa, tsammãninku, za ku ci nasara."

Tsoron Allah madaukakin sarki shi ne babban abin da ke taimaka ma mutum wajen kauce ma fadawa cikin aikin sabon Allah, domin shi tsoron Allah tamkar mai gadi ne a cikin ruhin mutum, yana hana shi ketare iyaka, tare da yi masa jagora zuwa ga sahihiyar hanya. Zamu iya daukar misali daga rayuwar manzon Allah (SAW) da iyalan gidansa da kuma sauran salihan bayi da waliyan Allah, inda rayuwarsu take misalta abin da ake nufi da tsoron Allah a aikace, yin koyi da su zai dora mutum kan sahihin tafarki na yin riko da koyarwar kur'ani da kuma sunnar manzon Allah da iyalan gidansa, wanda hakan shi ne takawa ta hakika.

Darussan koyo a nan su ne:

1 – Kafin mutum ya kai ga matsayin tsoron Allah (taqawa) yana bukatar ya nisanci duk abin Allah ya yi hani a kansa.

2 – Tsoron Allah da kuma tawassuli, abubuwa ne biyu da suke kai mutum ga sa'ada ta duniya ta lahira.

Da wannan ne muka kawo karshen shirin namu na yau, sai idan Allah ya kai mu a shiri na gaba za a ji mu daga inda muka tsaya, kafin lokacin nake yi muku fatan alkhairi, wassalamu alaikum wa rahmatullah.

Suratul Ma'ida, Aya Ta 36-40 (Kashi Na 164)

Jama'a masu saurare Asslamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannuka mai sanda, inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki, tare da yin bayani gwargawdon iko kan abin da suke koyar da mu, tare da yi mana hannuka mai sanda a cikin lamurran rayuwa. Har yanzu muna cikin surat Ma'ida, sai a biyo mu sannu a hankali a cikin shirin.

Aya ta (36) da (37) surat Ma’idah

إِنَّ الَّذِينَ كَفَرُواْ لَوْ أَنَّ لَهُم مَّا فِي الأَرْضِ جَمِيعاً وَمِثْلَهُ مَعَهُ لِيَفْتَدُواْ بِهِ مِنْ عَذَابِ يَوْمِ الْقِيَامَةِ مَا تُقُبِّلَ مِنْهُمْ وَلَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ{36} يُرِيدُونَ أَن يَخْرُجُواْ مِنَ النَّارِ وَمَا هُم بِخَارِجِينَ مِنْهَا وَلَهُمْ عَذَابٌ مُّقِيمٌ{37}

Lalle ne wadanda suka kãfirta, dã sunã da abin da ke a cikin kasa gabã daya da misãlinsa tãre da shi, dõmin su yi fansa da shi daga azãbar Rãnar kiyãma, bã a karbarsa daga gare su, kuma sunã da azãba mai radadi.

Sunã nufin su fita ne daga wuta, kuma ba su zama mãsu fita daga gare ta ba, kuma sunã da azãba zaunanniya.

Wadannan ayoyi masu albarka suna jan hankalin muminai ne da kada dukiyoyin makiya da jin dadinsu da walwalar da suke yi a cikin gidan duniya hakan ya rude su, domin dukiyoi da kuma ikon da kafirai suke da shi iyakarsa nan gidan duniya, domin kuwa babu wani wanda dukiyarsa za ta yi masa amfani a lahira, sai mumini da ya yi amfani da ita kamar yadda Allah ya umurce shi, domin kuwa a ranar kiyama kafirai za su shiga wuta, kuma tarin dukiyarsu a gidan ba ta amfane su alahira ba.

Darussan koyo a nan su ne:

1 – Babu abin da mutum zai bayar a matsayin fansa a ranar kiyama domin kubuta daga adalcin ubangiji.

2 – Babban abin da zai amfanar da mutum a ranar kiyama shi ne imaninsa da Allah, da kuma kyautata ayyuka domin Allah da neman rahmarsa.

3 – Duk wanda ya yi wa Allah girman kai tare da kafirce masa saboda dukiyar da yake da ita a gidan duniya, azabarsa ta har abada ce.

Aya ta (38) surat Ma'idah

وَالسَّارِقُ وَالسَّارِقَةُ فَاقْطَعُواْ أَيْدِيَهُمَا جَزَاء بِمَا كَسَبَا نَكَالاً مِّنَ اللّهِ وَاللّهُ عَزِيزٌ حَكِيمٌ{38}

Kuma barãwo da barauniya sai ku yanke hannuwansu, bisa sakamako ga abin da suka tsiwirta, azãba daga Allah. Kuma Allah Mabuwãyi ne, Mai hikima.

A cikin shirin da ya gabata an yi bayani kan hukunci na bai daya ga mutanen da suke bayyana laifi na shishigi, kam adaga kisa da makami da gangan, ko satar dukiyoyin jama'a ta hanyar yin amfani da makami ko kuma hanyar da za ta iya cutar da dubbai ko miliyoyin mutane, inda aka bayyana hukunci hudu za a yi musu daidai da girman barnar da suka aikata.

Ita kuma wannan ayar tana magana a kan hukunci guda daya na laifin sata a kan barawo ko barauniya, wadanda suke yin sata a boye ko a bayyane, suke dauke kaddarorin mutane ba bisa hakki ba, to wadannan hukuncinsu shi ne a yanke hannayensu, bisa la'akari da dukaknin sharudda wadanda hukuncin addini ya shardanta yin la'akari da su kafin yanke ko zartar da kowane irin hukunci.

Sau da yawa wasu kan soki addinin Musulunci da cewa yana da hukunci mai tsauri kan wasu laifuka, kuma hakan a mahangarsu yana cutar da dan adam ko tauye hakkinsa. A wurare da dama alkur'ani mai tsarki yana bayar da amsa ga mutane masu irin wannan tunani da ke nuni a cewa, hakkokin mutane babban lamari ne da addinin Musulunci baya saku-saku da shi, kamar yadda ba ya saku-saku da duk abin da ya shafi batun ran dan adam, domin kare rayuka da dukiyoyi da hakkokin jama'a da mutuncinsu, shi ne babban abin da ke wanzar da zaman lafiya da tsaro a cikin rayuwar jama'a ta zamnatakewa, domin addinin muslunci addini mai tsari a cikin dukaknin sassa na rayuwar mutane, saboda haka yake kare hakkokinsu da dukiyoyinsu da rayukansu da mutuncinsu, kuma yake yin hukunci mai tsanani kan duk wanda ya keta hurumin wadannan abubuwan da aka ambata.

Darussan koyo a nan su ne:

1 – Sau da yawa ana tsaurara wani hukuncin ne a cikin addini domin ya zama darasi ga masu niyyar aikata irin wannan laifi.

2 – Kare kaddarorin mutane da tsaro a cikin al'umma, na daga cikin abubuwan da Musulunci ke ba da muhimmanci a kansu.

3 – Musulunci addini ne na mutane baki daya, domin kuwa duk inda Musulunci yake da iko yana kare hakkokin mutane ne baki daya, musulmi da wanda ba musulmi ba.

Aya ta (39) Da (40) surat Ma'idah

فَمَن تَابَ مِن بَعْدِ ظُلْمِهِ وَأَصْلَحَ فَإِنَّ اللّهَ يَتُوبُ عَلَيْهِ إِنَّ اللّهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ{39} أَلَمْ تَعْلَمْ أَنَّ اللّهَ لَهُ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ يُعَذِّبُ مَن يَشَاءُ وَيَغْفِرُ لِمَن يَشَاءُ وَاللّهُ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ{40}

To, wanda ya tuba a bãyan zãluncinsa, kuma ya gyãra (halinsa), to, lalle ne Allah Yanã karbar tubarsa. Lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin kai.

Shin, ba ka sani ba cewa, Allah Shi ne da mulkin sammai da kasa, Yanã azãbtar da wanda Ya so, kuma Yanã yin gãfara ga wanda ya so, kuma Allah a dukkan kõme Mai ĩkon yi ne?

Duk da gargadin da Allah madaukakin sarki yake mana dangane da azaba mai tsanani da ke akwai ga masu aikata sabo, amma kuma a kowane lokaci rahamar Allah tana tattare da mu, domin bayan aikata laifi Allah a shirye yake ya gafarta mana, kuma ya ba mu lada ta musamman kan tubar da muka yi daga aikata wani sabo.

A kan haka ne ma wannan aya mai labarka take yi mana hannunka mai sanya da kada mu dauka cewa shi Allah ba ya da rangwame a cikin lamarinsa, domin kuwa ba haka lamarin yake ba a cikin lamarin Allah, idan an saba to yana karbar hanzari da istigfari, matukar dai aka yi tuba ta gaskiya. Amma kuma wannan a lokaci guda ba ya nufin mutum ya yi wani kamar samar sata, sai bayan kai shi gaban kuliya sai ya tuba, a lokacin Allah zai karbi tubarsa ta aikata sabo, amma kuma hukuncin alkali yana daram. Idan kuma mutum ya tuba ne kafin lamarinsa ya bayyana, to sai mayar da hakkokin mutane, ko kuma ya nemi yafiyarsu idan ya salwatar da hakkokin nasu. Darussan koyo a nan su ne;

1 – Tuba ba wai kawai yin nadama kan aikata laifi ba ne, a a dole ne kudirce cewa ba za a sake aikata laifin ba.

2 – Idan mutum ya tuba daga aikata wani laifi kuma ya daina aikata laifin, to Allah zai karbi tubarsa.

3 – A kowane lokaci kofofin rahamar Allah da tausayinsa a bude suke ga bayinsa.

Da wannan ne muka kawo karshen shirin namu na yau, sai idan Allah ya kai mu a shiri na gaba za a ji mu daga inda muka tsaya, kafin lokacin nake yi muku fatan alkhairi, wassalamu alaikum wa rahmatullah.

Suratul Ma'ida, Aya Ta 41-43 (Kashi Na 165)

Jama'a masu saurare Asslamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannuka mai sanda, inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki, tare da yin bayani gwargawdon iko kan abin da suke koyar da mu, tare da yi mana hannuka mai sanda a cikin lamurran rayuwa. Har yanzu muna cikin surat Ma'ida, sai a biyo mu sannu a hankali a cikin shirin.

Aya ta (41) da (42) surat Ma’idah

يَا أَيُّهَا الرَّسُولُ لاَ يَحْزُنكَ الَّذِينَ يُسَارِعُونَ فِي الْكُفْرِ مِنَ الَّذِينَ قَالُواْ آمَنَّا بِأَفْوَاهِهِمْ وَلَمْ تُؤْمِن قُلُوبُهُمْ وَمِنَ الَّذِينَ هِادُواْ سَمَّاعُونَ لِلْكَذِبِ سَمَّاعُونَ لِقَوْمٍ آخَرِينَ لَمْ يَأْتُوكَ يُحَرِّفُونَ الْكَلِمَ مِن بَعْدِ مَوَاضِعِهِ يَقُولُونَ إِنْ أُوتِيتُمْ هَـذَا فَخُذُوهُ وَإِن لَّمْ تُؤْتَوْهُ فَاحْذَرُواْ وَمَن يُرِدِ اللّهُ فِتْنَتَهُ فَلَن تَمْلِكَ لَهُ مِنَ اللّهِ شَيْئاً أُوْلَـئِكَ الَّذِينَ لَمْ يُرِدِ اللّهُ أَن يُطَهِّرَ قُلُوبَهُمْ لَهُمْ فِي الدُّنْيَا خِزْيٌ وَلَهُمْ فِي الآخِرَةِ عَذَابٌ عَظِيمٌ{41} سَمَّاعُونَ لِلْكَذِبِ أَكَّالُونَ لِلسُّحْتِ فَإِن جَآؤُوكَ فَاحْكُم بَيْنَهُم أَوْ أَعْرِضْ عَنْهُمْ وَإِن تُعْرِضْ عَنْهُمْ فَلَن يَضُرُّوكَ شَيْئاً وَإِنْ حَكَمْتَ فَاحْكُم بَيْنَهُمْ بِالْقِسْطِ إِنَّ اللّهَ يُحِبُّ الْمُقْسِطِينَ{42}

"Yã kai Manzo! Kada wadanda suke gaugawa a cikin kãfirci su bãta maka rai, daga wadanda suka ce: "Mun yi ĩmãni" da bãkunansu, alhãli zukatansu ba su yi ĩmãnin ba, kuma daga wadanda suka tuba mãsu yawan saurare ga wasu mutane na dabam wadanda ba su je maka ba, sunã karkatar da zance daga wurarensa, sunã cewa: "Idan an bã ku wannan, to, ku karba, kuma idan ba a bã ku shĩ ba, to, ku yi sauna."Kuma wanda Allah Ya yi nufin fitinarsa, to bã zã ka mallaka masa kõme ba daga Allah. Wadannan ne wadanda Allah bai yi nufin Ya tsarkake zukãtansu ba. Sunã da kunyata a cikin duniya, kuma sunã da wata azãba mai girma a cikin 1ãhira.

Mãsu yawan saurãre ga karya ne, mãsu yawan ci ga haram, to, idan sun zo maka, sai ka yi hukunci a tsakãninsu kõ ka kyale su. Kuma idan ka bijire daga gare su, to, bã zã su cutar da kai da kõme ba, kuma idan ka yi hukunci, to, sai ka hukunci a tsakãninsu da ãdalci. Lalle ne, Allah Yanã son mãsu ãdalci."

Wannan ayar ta safka ne kan wasu yahudawan birnin Madina, a lokacin da wani babba daga cikinsu ya aikata laifin zina, kuma a cikin littafin attaura duk wani wanda ya aikata wannan laifi yana da aure, to hukuncinsa shi ne a kashe shi ta hanyar jifa da duwatsu, saboda haka sai yahudawan suka shaawara kan cewa su tafi wurin manzon Allah, su tambaye shi huuncin wannan laifi a cikin kur'ani, da nufin idan hukuncin kur'ani ya fi sauki za su yarda a aiwatar da hukuncin kur'ani a kansa, a lokacin da suka zo sai manzon Allah ya gaya musu hukuncin kur'ani kan wannan laifi, sai suka ji cewa babu bambanci da hukuncin da ke cikin Attaura, sai suka juya suna bubutai, sai wannan aya ta safka tana ba manzon Allah hakuri da kada ya damu da abin da wadannan yahudawa suka aikata a yin watsi da ayoyin Allah da kuma izgili, domin kuwa kafinsa ma sun yi watsi da ayoyin Allah da yi musu izgili, har ma da kashe annabawan Allah da suka zo musu da shiriya, domin kuwa ba duk wanda ya zo wajen sa ne ya zo da niyyar ya yarda da gaskiya ba, wasu sun zo da niyyar hakan, wasu kuma sun zo da wata niyyar ta daban.

Darussan koyo a nan su ne:

1 – Imani lamari ne na zuciya ba zahiri kawai ba.

2 – Dole ne mu bi abin da Allah ke so, ba Allah ne zai bi mu abin da muke so ba.

3 – Yin izgili da ayoyin Allah a wurin yahudawa, lamari ne mai tabbatacce a cikin tarihinsu.

Aya ta (43) Mai'dah

وَكَيْفَ يُحَكِّمُونَكَ وَعِندَهُمُ التَّوْرَاةُ فِيهَا حُكْمُ اللّهِ ثُمَّ يَتَوَلَّوْنَ مِن بَعْدِ ذَلِكَ وَمَا أُوْلَـئِكَ بِالْمُؤْمِنِينَ{43}

Kuma yãya suke gabãtar da kai ga hukunci, alhãli a wurinsu akwai Attaura, a cikinta akwai hukuncin Allah, sa'an nan kuma sunã karkacewa a bãyan wannan? wadannan bã muminai ba ne!

Kamar yadda muka ambata a cikin bayanin ayar da ta gabata cewa, wani babba daga cikin yahudawan Madina ya yi zina, kuma yahudawan sun so su ji hukuncin kur'ani kan wannan laifi, da suka ji ya yi daidai da na su sai suka watsi da biyun baki daya. Yahudawan sun tura wani mutum ne da suke girmamawa mai suna Suriya, a lokacin da suka nuna rashin gamsuwarsu da wannan hukunci na kur'ani, sai manzon Allah ya tambaye su cewa shin hukuncin jefe mazinaci bai zo cikin Attaura ba, sai Suriya ya ce lallai ya zo kamar yadda ya zo cikin kur'ani, sai manzon Allah ya ce to yasa ba za ku yi aiki da shi ba? Sai ya ce: wannan hukuncin ana aiwatar da shi ne kan mutanen gari ba wai manya gada cikinmu ba, saboda haka sai muka yi ma wannan hukunci kwaskwarima, inda muke yi ma mutum bula arba'in a cikin shekara daya idan ya yi zina yana da aure.

Sai manzon Allah (SAW) ya ce: Ya Allah ka sheda, wannan hukuncin da aka manta a cikin addinin yahudawa na raya shi.

Darussan koyo a nan su ne:

1 – A mahangar kur'ani ba dukkanin abubuwan ad sue cikin littafin Attaura ba ne birkita, akawi wasu hukunce-hukuncen da suna nan kamar yadda aka safkar annabi Musa da su, sai dai yahudawa sun yi watsi da su.

2 – Yin watsi da ayoyin da Allah da yin izgili a kansu alama ce ta rashin imani.

3 – Zaman lafiya da manzon Allah ya yi da ma'bota littafi a Madina ya tabbatar da cewa addinin Musulunci addinin zaman lafiya da da fahimtar juna ne tsakaninsa da sauran addinai, domin yadda kiristoci da yahudawan Madinasuke komawa zuwa ga manzon Allah a cikin wasu lamurransu ya isa ya zama dalilikan cewa, sun ga kyawawan halaye da girmama dan adam daga manzon Allah (SAW).

Da wannan ne muka kawo karshen shirin namu na yau, sai idan Allah ya kai mu a shiri na gaba za a ji mu daga inda muka tsaya, kafin lokacin nake yi muku fatan alkhairi, wassalamu alaikum wa rahmatullah.

Suratul Ma'ida, Aya Ta 44-47 (Kashi Na 166)

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa cikin shirin namu na hannunka mai sanda shiri wanda yake dubi cikin wasu ayoyin alkur'ani mai girma don su zama fitila a cikin rayuwarmu. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.

      • .

To bari mu fara shirimmu na yau tare da sauraron karatun aya ta 44 daga cikin surar ma'ida kamar haka:

إِنَّا أَنزَلْنَا التَّوْرَاةَ فِيهَا هُدًى وَنُورٌ يَحْكُمُ بِهَا النَّبِيُّونَ الَّذِينَ أَسْلَمُواْ لِلَّذِينَ هَادُواْ وَالرَّبَّانِيُّونَ وَالأَحْبَارُ بِمَا اسْتُحْفِظُواْ مِن كِتَابِ اللّهِ وَكَانُواْ عَلَيْهِ شُهَدَاء فَلاَ تَخْشَوُاْ النَّاسَ وَاخْشَوْنِ وَلاَ تَشْتَرُواْ بِآيَاتِي ثَمَناً قَلِيلاً وَمَن لَّمْ يَحْكُم بِمَا أَنزَلَ اللّهُ فَأُوْلَـئِكَ هُمُ الْكَافِرُونَ{44}

Lalle ne Mu, Mun saukar da Attaura, a cikinsa akwai shiriya da haske, Annabãwa wadanda suke sun sallamã, sunã yin hukunci da shi ga wadanda suka tuba (Yahudu), da mãlaman tarbiyya, da manyan malamai ga abin da aka neme su da su tsare daga Littãfin Allah, kuma sun kasance, a kansa, mãsu bã da shaida. To, kada ku ji tsõron mutãne, ku ji tsõroNa kuma kada ku sayar da ãyoyiNa da 'yan kudi kadan. wanda bai yi hukunci da abin da Allah Ya saukar ba, to, wadannan su ne kafirai.

Kamar yadda muka bayyana a cikin shirin da ya gabata wasu yahudawa wadanda suka aikata wani laifi, wanda kuma hukuncin wanda ya aikata irin wannan laifin yana nan cikin littafin Attaura, amma sai dai hukuncin ya yi masu tsanani, don haka suka zo wa manzon Allah (s) da nufin, mai yuwa su sami wani hukunci mai sasauci. Amma manzon Allah (s) ya fada masu hukuncin nan da ke cikin Attaura.

Don haka wannan ayar da kuma wacce ta biyo ta, duk suna Magana ne kan wannan batun. Tana bayanin cewa, ba wai annabawa da suka zo bayan annabi Musa (a) kadai ne suka yi riko da hukunce hukuncen Attaura ba, hatta malaman da suka biyo baya ma, sun yi riko da littafin Allah da kuma hukunce hukuncesa. Basu ji tsoron sabawa mutane wadanda basa son kiyaye dokokin Allah ba. Ssannan basu saida hukunce hukuncen attaura don neman abin duniya ba. Kuma basu boye hukuncin Allah ba, basu kuma sauya shi ba, don yin haka wani nau'ee ne na kafirci.

Wannan ayar yana bayyana irin nauyin da ke kan malaman addini, na yin gwagwarmaya wajen kare hukunce hukunce Allah. Da kuma fada da son zuciyarsu, da kuma na sauran mutanen wadanda zasu bukacesu da kaucewa hukunce hukuncen Allah.

A cikin wannan ayar muna iya daukan darussa kamar haka .

1. Malaman addini dole ne su sa ido kan dukkan ayyukan shuwagabanni. Sannan kada su ji tsoron kowa a kan tafarkin nasu na kare addinin Allah. Kuma kada su yi kodayin samun abin duniya kan wannan tafarkin. 2. Bayan samun dokokin Allah, baya halatta ga wani ya nemi dokoki kirkiran dan adam. Yin haka kafirci ne.

Yanzu kuma bari mu saurari karatun aya ta 45 daga cikin surar Ma'ida kamar haka:

وَكَتَبْنَا عَلَيْهِمْ فِيهَا أَنَّ النَّفْسَ بِالنَّفْسِ وَالْعَيْنَ بِالْعَيْنِ وَالأَنفَ بِالأَنفِ وَالأُذُنَ بِالأُذُنِ وَالسِّنَّ بِالسِّنِّ وَالْجُرُوحَ قِصَاصٌ فَمَن تَصَدَّقَ بِهِ فَهُوَ كَفَّارَةٌ لَّهُ وَمَن لَّمْ يَحْكُم بِمَا أنزَلَ اللّهُ فَأُوْلَـئِكَ هُمُ الظَّالِمُونَ{45}

Kuma Mun rubuta a kansu, a cikinsa cewa, lalle (anã kashe) rai sabõda rai, kuma (anã debe) idõ sabõda idõ, kuma (ana katse) hanci sabõda hanci, kuma kunne sabõda kunne kuma hakori sabõda hakõri kuma a raunuka kuma a yi kisasi, wanda ya yi sadaka da shi, to, shi kaffãra ce a gare shi. Kuma wanda bai yi hukunci ba da abin da Allah Ya saukar ba, to, wadannan su ne azzãlumai.

Hukuncin kisasi na daga cikin hukunce hukuncen Allah wadanda malaman yahudawa basa bayyanasu, ko kuma basa aiwatar da su. A wasu lokutan kuma sakan tabbatar da hukuncin a kan mutane masu rauni, sannan su sauke hukuncin kan masu hali.

Alkur'ani mai girma ya tabbatar da hukuncin kisasi a cikin addinin musulunci. Sannan kafin Alkur'ani wannan hukuncin ya zo a cikin littafin Attaura. Gwargwadon raunin da aka yi wa wani kwatankwacin sa ne za'a rama masa. Babu wanda aka kebe daga aiwatar da hukuncin kisasi a kansa.

Irin bangaren da kuma girman jikin mutum da wani ya cire, wannan bangaren da kuma girman ne za'a cire a wajensa, idan rauni ne kuma gwagwadonsa.

Sai dai duk da wanna, kofar yin afwa a bude take ga wanda aka yiwa laifi. Don haka ne Alqur'ani mai girma ya bayyana cewa, duk wanda ya yi afwa ga wani wanda ya yi masa laifi, to shi ma Allah zai gafarta masa zunubansa, ko kuma wannan zai zame masa kamar ya bada sadaka, ko kuma kaffara ga zunubansa. Muna iya daukan darussa a cikin wadannan ayoyi kamar haka.

1. Dukkan mutane, matsayinsu dai dai ne a gaban hukunce hukuncen Allah. Fari ko baki, mai arziki ko talaka, malami ko jahili. 2. Hukuncin kisasi bai kebanta da addinin musulunci ba, tun zamani Annabi Musa (a) hukuncin yana nan bai sauya ba. 3. Sadaka bai takaita da bada dukiya ko kudi ba, gafartawa wanda ya yi maka laifi ma sadaka ce. 4. Addinin musulunci ya bukaci a aiwatar da hukunci kisasi kan duk wanda ya cancanci hakan, amma ya bude wata kofa ta tausayawa ga mai laifi. Wato kofar samun afwa daga wanda aka yiwa laifi. 5. Hukuncin dauri ko kuma biyan kudi basu wadatar wajen daukar fansa kan masu laifi ba. Hukuncin kisasi shi ne ke tabbatar da aminci da zaman lafiya a cikin al-umma.

Yanzun kuma mu saurari karatun aya ta 46 da kuma ta 47 daga cikin surar Ma'ida kamar haka:

وَقَفَّيْنَا عَلَى آثَارِهِم بِعَيسَى ابْنِ مَرْيَمَ مُصَدِّقاً لِّمَا بَيْنَ يَدَيْهِ مِنَ التَّوْرَاةِ وَآتَيْنَاهُ الإِنجِيلَ فِيهِ هُدًى وَنُورٌ وَمُصَدِّقاً لِّمَا بَيْنَ يَدَيْهِ مِنَ التَّوْرَاةِ وَهُدًى وَمَوْعِظَةً لِّلْمُتَّقِينَ{46} وَلْيَحْكُمْ أَهْلُ الإِنجِيلِ بِمَا أَنزَلَ اللّهُ فِيهِ وَمَن لَّمْ يَحْكُم بِمَا أَنزَلَ اللّهُ فَأُوْلَـئِكَ هُمُ الْفَاسِقُونَ{47}

46-Kuma Muka biyar a kan gurãbansu da Ĩsa dan Maryama, yãnã mai gaskatãwa ga abin da yake a gaba gare shi na Attaura, kuma Muka bã shi Injĩla a cikinsa akwai shiriya da haske, yanã mai gaskatãwa ga abin da yake a gaba gare shi daga Attaura, kuma shi shiriya ne da wa'azi ga mãsu takawa. 47-Kuma sai mutãnen injĩla su yi hukunci da abin da Allah ya saukar a cikinta. Kuma wanda bai yi hukunci ba da abin da Allah ya saukar ba, to, wadannan su ne fãsikai.

A ci gaba da kawo hukunce hukuncen Allah da ke cikin littafin Attaura, wadannan ayoyi sun bukaci yahudawa da su yi aiki da hukunce hukunce da suka zo cikinsa. Har'ila yau wadannan ayoyi suna Magana ne da kiristoci mabiya Annabi Isa (a). Suna bayyana cewa littafin Linjila ma na Allah ne, kuma yana dauke da shiriya zuwa tafarkin Allah. Kuma yana gasgata ayoyin da suka zo cikin Attaura. Sannan Annabi Isa (a), wanda Allah ya aiko, ya yi aiki da ayoyin da suka zo cikin attaura. Don haka ku ma ko zama masu cika alkawari. Kada ku sabawa umurnin Allah. Don yin haka zai maida ku fasikai.

Sai dai a fili yake, litattafan Attaura da Linjila da wadannan ayoyi suka bukaci ayi amfani da su, su ne wadanda ba'a sauyasu ba. Attaura da Linjila na asali. Wadancan littafai sun yi umurni da bin manzon karshe Annabi Muhammad (s) da kuma llittafin da ya zo da shi.

Don haka muna iya daukan darussa a cikin wadannan ayoyi kamar haka:

1. Dukkan littafan Allah sun yi kira ga mutum ya tsarkake zuciyarsa ya ji tsoron Allah. 2. Dukkan Annabawan Allah suna kan tafarki guda ne, ko wadanda suka zo baya suna gasgata na gaba da su. Sannan babu wani sabani a tsakaninsu. 3. Littafan sama ba wai kawai don karatu aka saukar dasu ba. Dole ne a yi amfani da su a cikin rayuwar daddaikun mutane, da kuma al-umma gaba daya To masu sauraro a nan zamu dasa aya sai kuma wani shirin idan Allah ya kaimu. Da fatan Allah ya bamu dammar amfani da dokokinsa wanda ta hanyarsu ne kadai zamu sami sa'ada ta duniya da lahira gaba daya. Assalamu alaikum warahmatullah.

Suratul Ma'ida, Aya Ta 48-50 (Kashi Na 167)

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa cikin shirin namu na hannunka mai sanda shiri wanda yake dubi cikin wasu ayoyin alkur'ani mai girma don su zama fitila a cikin rayuwarmu. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.

To bari mu fara shirimmu na yau tare da sauraron karatun aya ta 48 daga cikin surar Ma'ida kamar haka.

وَأَنزَلْنَا إِلَيْكَ الْكِتَابَ بِالْحَقِّ مُصَدِّقاً لِّمَا بَيْنَ يَدَيْهِ مِنَ الْكِتَابِ وَمُهَيْمِناً عَلَيْهِ فَاحْكُم بَيْنَهُم بِمَا أَنزَلَ اللّهُ وَلاَ تَتَّبِعْ أَهْوَاءهُمْ عَمَّا جَاءكَ مِنَ الْحَقِّ لِكُلٍّ جَعَلْنَا مِنكُمْ شِرْعَةً وَمِنْهَاجاً وَلَوْ شَاء اللّهُ لَجَعَلَكُمْ أُمَّةً وَاحِدَةً وَلَـكِن لِّيَبْلُوَكُمْ فِي مَا آتَاكُم فَاسْتَبِقُوا الخَيْرَاتِ إِلَى الله مَرْجِعُكُمْ جَمِيعاً فَيُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمْ فِيهِ تَخْتَلِفُونَ{48}

48-Kuma Mun saukar da Littãfi zuwa gare ka da gaskiya, yanã mai gaskatãwa ga abin da yake a gaba gare shi daga Littãfi na(Attaura da Injĩla), kuma mai rinjaye a kansa. sai ka yi hukunci a tsakãninsu da abin da Allah Ya saukar, kuma kada ka bĩ son zũciyõyinsu da barin abin da ya zo maka na gaskiya. Ga kõwanne daga gare ku Mun sanya masa sharĩa da hanya. Kuma dã Allah Yã so, dã Yã sanya ku al'umma guda, amma dõmin Ya jarraba ku a cikin abin da Ya bã ku. Sai ku yi tsere kan ayyukan alheri. Zuwa ga Allahne makõmarku take gabã daya. Sa'an nan Zai bã ku lãbãri n abin da kuka kasance kunã sãbãni a cikinsa.

Kamar yadda ya zo cikin shirimmu da ya gabata cewa Ubangiji ya tada da Annabawa da manzanni da dama a tsawon tarihin dan'adam. Sannan ya aiko tare da su shari'o'i. Amma abin bakin ciki wadannan shari'o'ee sun shiga hannun malamai wadanda suka boyesu ga mutane ko kuma suka sauya masu ma'ana. A wasu lokutamma su kan maye gurbinsu da wasu dokoki na daban. Wannan ayar da muka saurara tana bayanin matsayin Alqur'ani mai girma a cikin littafan da Allah ya saukar kafinsa. Alku'anin da farko yana gasgata littafan da suka sauka kafinsa, sannan yana kiyaye da sakonnin da wadancan littafan suke dauke da su. Sai kuma banada wannan, Alkur'ani yana nan kan tafarkin nan da sauran annabawan Allah suka zo da shi kafin musulunci. Kai alkur'ani karashe ne da kuma ciko ga sakonnin da sauran littafan da Allah ya saukar da su. Sannan ayar ta bada amsar tamabaya wacce take cewa, shin me ya sa Ubangiji bai aiko da sako guda, da shari'a guda ba a duk tsawon tarihi, wanda yin hakan zai kare mutane daga fadawa cikin sabani a tsakaninsu?. Shi ne ayar ta amsa da cewa, Allah yana iya maida mutane gaba daya al-umma guda, masu bin addinin guda ta yadda sabani ba zai shiga tsakaninsu ba. Amma hakan ya tsabawa sunnarsa ta tarabiyyan dan adam da kuma cikar hankalinsa da fahintarsa. Wayewar al-ummar fako ba daya take da wacce ta zo daga baya. Misalin makaranta ce, dalibi sai ya wuce aji na farko kafin ya fahinci abinda yan aji na gaba suke karatu. Banda wannan kuma Allah yana saukar da shari'a ne bisa sabanin da ke cikin yanayin da mutane suke rayuwa, da kuma don jarrabawa. Don haka ayar ta yi kira ga kowa ya shiga tsere na aikata ayyukan alkhairi. Don Allah yana sane duk abinda kowannenku yake aikatwa. Babu abinda ya boyu a gareshi. Don haka cikin wannar ayar muna iya daukan darussa kamar haka. 1. Alkur'ani mai girma yana da daukaka kan dukkan sauran littafan da Allah ya saukar. Kamar fifikon da littafan karatu a jami'o'ee suke da shi na makarantun kasa da su. Su sun kasance karashen karatu ne na littafin makarantun da suke kasa da jami'a. 2. Hatsarin da ke fuskanatar shuwagabannin al-umma shi ne rashin kula da hukunce hukuncen Allah don nemen yardar mutanensu da kuma bin sun zuciyarsu. 3. Bambance bancen da ke cikin addinan Allah, wata hanya ce ta jarrabawan Allah ga su mutanen. Da wannan ne ya ke bayyana, wanda yake bin gaskiya da kuma wanda yake karkata zuwa ga kabilanci ko yan kasanci ko kuma yake nuna taurin kai. Yanzu kuma sai mu saurari karatun aya ta 49 da kuma ta 50 daga cikin surar Ma'aida kamar haka:

وَأَنِ احْكُم بَيْنَهُم بِمَا أَنزَلَ اللّهُ وَلاَ تَتَّبِعْ أَهْوَاءهُمْ وَاحْذَرْهُمْ أَن يَفْتِنُوكَ عَن بَعْضِ مَا أَنزَلَ اللّهُ إِلَيْكَ فَإِن تَوَلَّوْاْ فَاعْلَمْ أَنَّمَا يُرِيدُ اللّهُ أَن يُصِيبَهُم بِبَعْضِ ذُنُوبِهِمْ وَإِنَّ كَثِيراً مِّنَ النَّاسِ لَفَاسِقُونَ{49} أَفَحُكْمَ الْجَاهِلِيَّةِ يَبْغُونَ وَمَنْ أَحْسَنُ مِنَ اللّهِ حُكْماً لِّقَوْمٍ يُوقِنُونَ{50}

49-Kuma ka yi hukunci a tsakãninsu da abin da Allah Ya saukar, kuma kada ka bĩyewa son zũciyõyinsu, kuma ka yi hankali da su don kada su fitineka daga sãshen abin da Allah Ya saukar zuwa gare ka. To, idan sun juya bãya, ka sani cewa, kawai Allah yana nufin Ya azabtar da su da wata masĩfa ne sabõda sãshen zunubansu. Kuma lalle ne, mãsu yawa daga mutãne, hakĩka, fãsikai ne.

50-Shin, hukuncin Jãhiliyya suke nema? Kuma wane ne mafi kyautata hukunci banda Allah ga mutãne wadanda suke da sakankancewa?

Kamar yadda ya zo a cikin wasu littafan tarihi, wasu shuwagabannin yahudawa sun zo wajen manzon Allah (s) sun ce masa, mu shuwagabannin yahudawa ne, idan mun yi imani da kai sauran yahudawa ma zasu yi imani da kai. Amma muna da sharadi na yin imani da kai, kuma shi ne a duk lokacinda zaka yi hukunci a tsakanimmu da wani ka bamu gaskiya. A lokacin ne wannan ayar ta sauka tana fahintar da manzon Allah (s) makircin da ke cikin wannan mu'amalar. Kuma ya gargade shi da kada ya yarda ya shiga irin wannan ma'amalar da su. A ci gaba ayar ta kawo yadda zunubi yake maida mai sabo idan ya doge akaisa. Zunubi zai busar da zuziyarsa ta yadda bazata taba karban gaskiya ba. Banda hakan ma, sai ya sa shi kokarin amfani da gaskiyar don cimma manufofinsa na duniya. Sai kuma wani abu mai muhimmanci wanda ayar ta bayyana shi ne cewa, idan wani mutum yana neman tafarkin rayuwa ne da gaskiya, shin wa y a fi Allah ajiye dokokin da suka dace da tsarin rayuwa mai kyau? Don ya san abinda yake bayyane da kuma abinda ke boye. Babu kuskure cikin tsarin rayuwar da ya aza. Kuma baya nemen wani abu ko wani irziki a wajen mutane . Daga karshe ayar ta aza tamabaya mai cewa, me yasa bazaku amince da dokokin Allah? Kuna bin dokoki da tsarin rayuwa irin ta masu bin son zuciyarsu da kuma kariya. Don haka muna iya daukan darussa a cikin wadannan ayoyi biyu kamar haka. 1. Duk sanda mutum ya ki karban gaskiya to dole zai fada jahilci ko da kuwa a zahiri ana ganinsa masani malami. Sannan alamar malanata ta hakika ita ce fahinta da kuma amincewa da gaskiya. 2. Alamar Imani shi ne yarda da amincewa da dokokin Allah, duk wanda yake bin dokokin kirkiran mutum, to ku yi shakka cikin imaninsa da Allah. 3. Kuma muyi hankali da makircin makiya, don suna iya fito maku ta hanyar addini da wasu hanyoyi daban daban don jawo hankalinku ko hankalin shuwagabanninku zuwa ga son zuciyarsu. 4. Abinda yake hana kafirai amincewa da gaskiya shi ne zunubansu da yawan fasikanci, ba wai don akwai aibi ko nakasa tattare da addninin musulunci ba. Da wannan kuma masu sauraro zamu dasa aya a cikin shirimmu na yau sai kuma shirimmu na gaba idan Allah ya kai mu. Wassalami alaikum warahmatullah.

Suratul Ma'ida, Aya Ta 51-54 (Kashi Na 168)

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa cikin shirin namu na hannunka mai sanda shiri wanda yake dubi cikin wasu ayoyin alkur'ani mai girma don su zama fitila a cikin rayuwarmu. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.

        • .

To bari mu fara shirimmu na yau da sauraron karatun aya ta 51 daga cikin surar Ma'ida kamar haka.

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُواْ لاَ تَتَّخِذُواْ الْيَهُودَ وَالنَّصَارَى أَوْلِيَاء بَعْضُهُمْ أَوْلِيَاء بَعْضٍ وَمَن يَتَوَلَّهُم مِّنكُمْ فَإِنَّهُ مِنْهُمْ إِنَّ اللّهَ لاَ يَهْدِي الْقَوْمَ الظَّالِمِينَ{51}

51-Yã ku wadanda suka yi ĩmãni! Kada ku riki Yahudu da Nasãra majibinta. Sãshensu majibinci ne ga sãshe. Kuma wanda ya jibince su daga gare ku, to, lalle ne shĩ, yanã daga gare su. Lalle Allah bã Ya shiryar da mutãne azzãlumai.

Tun farkon Al-kur'ani mai girma, har zuwa ayoyin da muke karatunsu a yanzu, mun karanta ayoyi da dama wadanda suka yi zancen rayuwa tare da kuma rayuwar siyasa da ta jagoranci acikin Addinin musulunci. Wannan yana tabbatar mana cewa, Alkur'ni mai girma ya tattara duk abinda ake bukata na tafiyar da rayuwar dan'adam da kuma lamunce masa aminci a rayuwarsa ta duniya da ta lahira gaba daya. A cikin wannan ayar Allah ya yi nuni ga daya daga cikin muhimman harsasshe na rayuwar dan'adam. Inda yake garganin muminai da kada ko da wasa su riki kafirai abin dogaro da aminci. Don duk abinda mumini zai yi na bayyana yarda da so garesu, to su fa bazasu taba amincewa da shi ba. Mabiya addininsu kawai suke so. Ayar ta kara bayanin cewa, duk wanda ya riki kafirai musamman yahudu da nasara majibinci, to fa makomarsu da ya ce. Don rikonsu majibantar lamari zai bude kofar munafurci da kafirci a cikin zuciyar mumini. Don haka a cikin wannan ayar muna iya daukan darussa kamar haka. 1. A cikin mu'amalar kasashen musulmi da kasashen kafirai duk wata hulda wacce zata bawa kafirai iko kan musulmi bai halatta ba. 2. Yarda da kafirai a matsayin majibanta al-amari yana fitar da mumini daga waliyar Allah. Kuma daga nan ne yake ficewa daga cikin masu samun Allah. 3. Musulunci ya amince musulmi da wadanda ba musulmi ba su rayu tare su yi mu'amala tare. Abinda ya haramta shi ne karban ikonsu akan musulmi.

Yanzu kuma bari mu saurari karatun aya ta 52 da ta 53 daga cikin surar ma'ida kamar haka.

فَتَرَى الَّذِينَ فِي قُلُوبِهِم مَّرَضٌ يُسَارِعُونَ فِيهِمْ يَقُولُونَ نَخْشَى أَن تُصِيبَنَا دَآئِرَةٌ فَعَسَى اللّهُ أَن يَأْتِيَ بِالْفَتْحِ أَوْ أَمْرٍ مِّنْ عِندِهِ فَيُصْبِحُواْ عَلَى مَا أَسَرُّواْ فِي أَنْفُسِهِمْ نَادِمِينَ{52} وَيَقُولُ الَّذِينَ آمَنُواْ أَهَـؤُلاء الَّذِينَ أَقْسَمُواْ بِاللّهِ جَهْدَ أَيْمَانِهِمْ إِنَّهُمْ لَمَعَكُمْ حَبِطَتْ أَعْمَالُهُمْ فَأَصْبَحُواْ خَاسِرِينَ{53}

52-Sai ka ga wadanda a cikin zukatansu akwai cuta, sunã tseren gaugawa a cikinsu, sunã cewa: "Munã tsõron kada wata masĩfa ta sãme mu." To, akwai tsammãnin Allah Ya zo da budi, kõ kuwa wani umurni daga wurinSa, har su wãyi gari a kan abin da suka bõye a cikin zukatansu, sunã mãsu nadãmã.

53-Kuma wadanda suka yi ĩmãni sunã cewa: "Shin, wadannan ne wadanda suka yi rantsuwa da Allah iyãkar rantsuwõyinsu, cewa su, lalle sunã tãre da ku?" Ayyukansu sun bãci, sabõda haka suka wãyi gari sunã mãsu hasãra.

Duk da cewa Ubangiji ya hana rikon kafirai a matsayin abokai, wannan bai hana wasu munafikai da kuma masu raunin imani suna binsu ba. Suna neman taimakonsu. Anan ne ayoyin nan suka sauka suna bayanin cewa, lokaci na zuwa sanda musulunci zai daukaka ya yi nasara. Allah zai daukaka muminai, a lokacinda wadannan da suke tare da kafirai don wai kada su cutar da su zasu ji kunya. Sannan abinda suke boye da shi a cikin zukatansu zai kara bayyana. A lokacinne muminai zasu ce wa masu irin wannan halin, ashe duk abinda kuke bayyanawa na imani ba gaskiya ba ne? Muna iya daukan darussa a cikin wadannan ayoyi kamar haka. 1. Abokantaka da kafirai da kuma jan ra'ayinsu don neman yardarsu alama ce ta munafurci. 2. Raunin imani ne yake sa musulmi ya mika kai ga kafirai ya zama su ke tafiyar da rayuwar sa. 3. Daukaka da shugabanci, ko na siyasa, da ta tattalin arziki da kuma na karfin soje duk suna hannun Allah ne. Allah yana bada su ga muminai da sharadin su tabbata kan imaninsu. 4. Karshen munafurci shi ne, lalacewar ayyukan shi munafuki da kuma asara da jin kunya.

Yanzu kuma mu saurari karatun aya ta 54 daga cikin surar Ma'ida kamar haka:

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُواْ مَن يَرْتَدَّ مِنكُمْ عَن دِينِهِ فَسَوْفَ يَأْتِي اللّهُ بِقَوْمٍ يُحِبُّهُمْ وَيُحِبُّونَهُ أَذِلَّةٍ عَلَى الْمُؤْمِنِينَ أَعِزَّةٍ عَلَى الْكَافِرِينَ يُجَاهِدُونَ فِي سَبِيلِ اللّهِ وَلاَ يَخَافُونَ لَوْمَةَ لآئِمٍ ذَلِكَ فَضْلُ اللّهِ يُؤْتِيهِ مَن يَشَاءُ وَاللّهُ وَاسِعٌ عَلِيمٌ{54}

54-Yã ku wadanda suka yi ĩmãni! wanda ya yi ridda daga gare ku daga addininSa, to, Allah zai zo da wasu mutãne, Yanã son su kuma sunã son Sa, mãsu tawãlu'i a kan muminai mãsu izza a kan kãfurai. Sunã yin, jihãdi a cikin hanyar Allah, kuma bã su tsõron zargin wani mai zargi. Waccan falalar Allah ce, Yanã bãyar da ita ga wanda Yake so. Kuma Allah Mayalwaci ne, Mai ilmi.

A cikin ayoyin da suka gabata Allah ya yi kashedi wa muminai kada su jibanci kafirai, su amince da ikonsu akansu. Wannan ayar kuma ta kara gargadi ga irin wadannan masu raunin imani da cewa, ci gaba rikon kafirai majibantan lamuransu zai sanya ku yi ridda daga musulunci. Kuma ku sani cewa idon kun yi ridda kuka koma kofirai, addinin Allah, addinin musulunci ba zai cutu ba. Don Allah zai kawo wadansu mutane masu imani zasu yi jihadi a kan tafarkin Allah basa jin tsoron zargin masu zargi. Wani abin lura a nan shi ne ayar ta ce, suna masu kafuwa a gaban kafirai basa bada kai, kuma suna son Allah shi ma suna sonshi. A cikin Sahihu Muslim babin falalar sahabbai, sannan karkashin fafalar farisa, daga Abuhurai ya ce, a lokacinda wannan ayar ta sauka, manzon Allah (s) ya dafa hannunsa masu albarka kan kafadar Sahabinsa Salman Farisa yana cewa, " Da addinin yana Thurayya da wani namiji daga farisa zai dawo da shi". ko kuma " da wani namiji daga yayan farisawa zai dawo da shi. Don haka daga cikin wannan ayar muna iya daukan darussa kamar haka: 1. Duk wani muminin da yake tunanin ficewa daga addinin musulunci, ya san cewa yin haka yana da mummunan karshe a nan duniya da lahira. 2. Abinda yake sanya wani musulmi ya fice daga addinin musulunci shi ne rashin sanin Allah, sani na gaskiya, wanda zai gadar masa da son Allah. 3. Allah baya bukatar taimakon kowa don kare addininsa. Idan wani ya fice daga addinin musulunci wannan ba zai hana addinin tabbata ba. Don Allah yana da masoya wadanda shima yake sonsu zasu kare wanna addinin. 4. Ka'ida shi ne su muminai masu tausayawa juna ne, sannan suna tsanantawa kafirai, sai dai ko wannen su na da yanayi da halin da ake bukatar hakan. 5. Falalar Allah bai takaita ga bada dukiya da mukami ba, jihadi a tafarkin Allah, son Allah da kuma yin kokari a tafarkinsa suma falalar Allah ne manya manya. Masu sauraro da wanna kuma muka kawo karshen shirimmu na yau sai kuma wani shirin idan Allah mai kowa da kome ya kai mu. Wassalamu a laikum wa rahamatullah.

Suratul Ma'ida, Aya Ta 55-59 (Kashi Na 169)

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barakammu da sake saduwa a cikin shirimmu na hannunka mai sanda shi wanda yake dubi a cikin wasu ayoyin alkur'ani mai girma don su zama fitialla a cikin rayuwarmu da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mua.

      • .

To bari mu fara shirimmu na yau da sauraron karatun aya ta 55 da kuma ta 56 daga cikin surar ma'idakamar haka:

إِنَّمَا وَلِيُّكُمُ اللّهُ وَرَسُولُهُ وَالَّذِينَ آمَنُواْ الَّذِينَ يُقِيمُونَ الصَّلاَةَ وَيُؤْتُونَ الزَّكَاةَ وَهُمْ رَاكِعُونَ{55} وَمَن يَتَوَلَّ اللّهَ وَرَسُولَهُ وَالَّذِينَ آمَنُواْ فَإِنَّ حِزْبَ اللّهِ هُمُ الْغَالِبُونَ{56}

55-Abin sani kawai, majibincin lamarinku Allah ne da ManzonSa da wadanda suka yi ĩmãni, wadanda suke sunã tsayar da salla kuma sunã bãyar da zakka alhali ruku'i.

56-Kuma wanda ya jibinci Allah da ManzonSa da wadanda suka yi ĩmãni, to, kungiyar Allah sune mãsu rinjãya.

Ya zo a cikin ruwayoyi da dama da kuma littafan tarihi cewa, wani mabukaci ya ciga masallacin manzon Allah (s) yana neman taimako. Amma babu wanda ya bashi wani abu. Anan ne Amirul muminina Aliyu bin AbiTalib (a) ya mika masa hannunsa don ya cire zoben da ke kan yatsarsa alhali yana ruku'ee a cikin sallarsa. Wannan ayar ta sauka tana yabawa wannan aikin nasa. Ammar dan yasar (r) daya daga cikin sahabban manzon Allah (s). ya ce bayan saukar wannan ayar ne manzon Allah ya ke cewa "Duk wanda ni shugabansa ne to Aliyu shugabansa ne". Sannan a fili yake ma'anar maula a nan yana nufin shugabanci da jaroranci. Ba zai dauki ma'anar so da kauna ba. Don shi so da kauna ya ta'allaka da dukkan musulmi. Sannan ayar tana nufin Aliyu Bin Abitalib (a) kadai, duk da cewa ta zo da kalmar jam'ee. Wato الذين آمنوا. Kamar yadda a cikin alkur'ani mai girma sau da dama kalmomi irin wannan sun zo amma suna nufin mutim guda. Daga cikin wannan ayar muna iya daukan darussa kamar haka. 1. Musulunci addinin ne na bara'a da kuma wilaya. Ayayoyin da suka zo kafin wannan ayar suna Magana kan baranta daga kafirai da kuma rashin amincewa da ikonsu akan musulmu. Amma wannan ayar tana maganar wilaya da jagoranci na Allah da Manzonsa da kuma muminai. 2. Duk wadanda ba masu imani ba, ba masu sallah ba kuma ba masu bada zakka ba to basu cancanci zama shugabannin muminai ba. 3. Ba laifi ko a cikin salla mutum ya bada taimako ga masu bukata. Musamman idan bai fi mika hannu ne ko makamancinsa. Wato ba aiki mai yawa wanda zai bata sallara ba. 4. Duk wanda yanayin rayuwar talaka da mabukata bai dame shi ba bai cancanci shugabanci ba. 5. Idan musulmi sun takaita walayarsu ga Allah da manzonsa da kuma muminai to a yanke take sune a sama, sune masu nasara.

Yanzun kuma bari mu saurari karatun ayoyi na 57 da kuma 58 daga cikin surar Ma'aida kamar haka.

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُواْ لاَ تَتَّخِذُواْ الَّذِينَ اتَّخَذُواْ دِينَكُمْ هُزُواً وَلَعِباً مِّنَ الَّذِينَ أُوتُواْ الْكِتَابَ مِن قَبْلِكُمْ وَالْكُفَّارَ أَوْلِيَاء وَاتَّقُواْ اللّهَ إِن كُنتُم مُّؤْمِنِينَ{57} وَإِذَا نَادَيْتُمْ إِلَى الصَّلاَةِ اتَّخَذُوهَا هُزُواً وَلَعِباً ذَلِكَ بِأَنَّهُمْ قَوْمٌ لاَّ يَعْقِلُونَ{58}

57- Yã ku wadanda suka yi ĩmãni! Kada ku riki wadanda suka riki addininku bisa izgili da wãsa, daga wadanda aka bai wa Littãfi daga gabãninku da kãfirai, masõya, Kuma ku bi Allah da takawa idan kun kasance muminai.

58- Kuma idan kuka yi kira zuwa ga salla, sai su rike ta bisa izgili da wãsa. Wannan dõmin lalle ne su, mutãne ne (wadanda) bã su hankalta.

Wadannan ayoyi ma har'ila yau suna gargadin muminai masu saukin hali, wadanda suke son kulla dangantaka da kafirai musamman ma'abuta littafi daga cikinsu. Ayoyin suna karfafa rashin nuna soyayya a garesu musamman idan suna izgila da wasa da addininku. Bai kamata ga mumini ya yarda da wulakanta addininsa da kuma izgili da shi ba. Musamman sallah wanda yake daga cikin ganshikan addinin musulunci. Don haka daga cikin wadannan ayoyi muna iya daukan darussa kamar haka. 1. Yana daga cikin sharuddan zama mumini musulmi ya kasance mai kishin addininsa, baya barin aya isgili da wasa da addininsa. 2. Kada mu yi kodayin wani abin duniya daga kafirai. Mu dogara ga Allah mu ji tsoransa shi kaidai ya wadarta mu duniya da lahira. 3. Kafirai suna tsoron Sallah wanda musulmi suke yi, don haka ne ma suke isgili da musulmi masu sallah. Don haka ku daga da yinta a ko ina kuke.

Yanzu kuma mu saurari karatun aya ta 59 daga cikin sura ma'aida kamar haka.

قُلْ يَا أَهْلَ الْكِتَابِ هَلْ تَنقِمُونَ مِنَّا إِلاَّ أَنْ آمَنَّا بِاللّهِ وَمَا أُنزِلَ إِلَيْنَا وَمَا أُنزِلَ مِن قَبْلُ وَأَنَّ أَكْثَرَكُمْ فَاسِقُونَ{59}

59-Ka ce: "Ya Mutãnen Littãfi! Shin, kunã ganin wani laifi daga gare mu? Fãce dai dõmin mun yi ĩmãni da Allah da abin da aka Saukar zuwa gare mu da abin da aka saukar daga gabãni?, kuma dõmin mafi yawanku fãsikai ne."

Wannan ayar tana Magana da manzon Allah (s) da kuma muminai, ku cewa su kafirai, ay baku yi asgila da mu da addinimmu ba, kuna wulakanta mu ba fashe don mun yi imani da Alkur'ani da kuma littafan da suka zo kafin san a Attaura da linzila, amma gashi ku bakwa mutunta littafinlku wanda kuke da'awar kun yi imani da shi. Daga cikin wannan ayar muna iya daukan darussa kamar haka.

1. Yana da kyau mu rika tattaunawa da makiya, muna jefa masu tambayoyi masu ma'ana. Wadansa zasu taimaka masu wajen shiga tunani cikin halin da suke ciki. Amma tattaunawan ta kasance a kebe ko kuma wacce zata mana na fahintarwa ne. 2. Kada mu yi shakka cikin addinimmu. Don mu ne kan gaskiya. Su makiya kafirai basa nuna adalci da kuma amfani da hanakali a cikin yadda suka Magana da mu. To masu sauraro anan kuma zamu dasa aya a cikin shirimmu na yai sai kuma wani lokacin idan Allah ya kai mu , Wassalamu alaikum warahamatullahi wa barakatu.

Suratul Ma'ida, Aya Ta 60-63 (Kashi Na 170)

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barakammu da sake saduwa a cikin shirimmu na hannunka mai sanda shi wanda yake dubi a cikin wasu ayoyin alkur'ani mai girma don su zama fitialla a cikin rayuwarmu da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.

      • .

To bari mu fara shirimmu na yau da sauraron karatun aya ta 60 daga cikin surar Ma'ida kamar haka.

قُلْ هَلْ أُنَبِّئُكُم بِشَرٍّ مِّن ذَلِكَ مَثُوبَةً عِندَ اللّهِ مَن لَّعَنَهُ اللّهُ وَغَضِبَ عَلَيْهِ وَجَعَلَ مِنْهُمُ الْقِرَدَةَ وَالْخَنَازِيرَ وَعَبَدَ الطَّاغُوتَ أُوْلَـئِكَ شَرٌّ مَّكَاناً وَأَضَلُّ عَن سَوَاء السَّبِيلِ{60}

60- Ka ce: "Shin, in gaya muku mafi sharri daga wannan, dõmin sakamako daga wurin Allah? wanda Allah Ya la'ane shi kuma Ya yi fushi da shi, kuma Ya sanya daga gare su birai da aladai, kuma ya bauta wa dãguta. Wadannan su ne mafiya sharrin wuri, kuma mafiya bata daga tsakar hanya." َ A shirin da ya gabata mun yi maganara kan yadda wasu ma'abuta littafi da kuma mushrikai suke abokantaka da wasu muslmi, amma kuma suke isgili da nuna wulakanci da musulmi a lokacinda suke sallah. Wannan ayar ma ta dora ne kan wancan, inda ta kara da cewa- me yasa ku ma'abuta littafi bakwa dubi zuwa ga mummunan tarihin iyayenku wadanda don tsananin sabon Ubanguji da suka yi da kuma isgili da wulakanci da suka yi da dokokin Allah said a ya maida su aladu da birrai. Me yasa bakwa daukan darasi daga abinda ya faru da kakanninku. Sai gashi ku ma kuna isgila da wasu da addinin Allah. Ko wa yasan yadda Allah maida wasu masu sabo daga cikin bani'isra'ila a lokacinda suka sabawa annabawansu. Amma don su suna daukar kansu kabila guda ce, don haka suna alfahir da kasancewarsu yayan annabi ya'akub ne. Amma sun manta da cewa a cikin kakanninsu ne aka sami masu sabon Allah wadanda Allah aka maida su birrai da alkhanzir. Wani abin alfakhari kuma ya rege masu da wannan mummunar makoma ga kakanninsu. Har'ila yau me ya fi muni ga mutanen, kamar la'anar Allah da fushinsa a kansu. Don tsananain sabonsa da zunubansa. Duk wanda Allah ya la'ane shi ya yi fushi da shi to ya haramta masa rahamarsa kenen. Don haka kakannin bani'isra'ila wadanda suka sabi Allah ba abin alfakhari ne ba. Muna iya daukan darussa a cikin wannan ayar kamar haka. 1. Maida mutum wanda Allah ya kyautata halittansa, ya maida shi wata dabba-biri ko alkhanzir- yana nuna cewa ya rasa mutuncin da dan'adam yake da shi. Kuma yin hakan yana daga cikin sakamakon da Allah yakewa wasu masu sabonsa. 2. Wadanda Allah ya yi fushi da su kuma ya la'anesu to basu da wani matsayi a cikin muminai.

Yanzun kuma bari mu saurrai karatun aya ta 61 da kuma 62 daga cikin surar Ma'ida kamar haka.

وَإِذَا جَآؤُوكُمْ قَالُوَاْ آمَنَّا وَقَد دَّخَلُواْ بِالْكُفْرِ وَهُمْ قَدْ خَرَجُواْ بِهِ وَاللّهُ أَعْلَمُ بِمَا كَانُواْ يَكْتُمُونَ{61} وَتَرَى كَثِيراً مِّنْهُمْ يُسَارِعُونَ فِي الإِثْمِ وَالْعُدْوَانِ وَأَكْلِهِمُ السُّحْتَ لَبِئْسَ مَا كَانُواْ يَعْمَلُونَ{62}

61-Kuma idan sun zo muku sai su ce: "Mun yi ĩmãni." Alhãli kuwa hakĩka, sun shigo da kãfirci,kuma hakika sun, fita da shi, kuma Allah ne Mafi sani ga abin da suka kasance sunã bõyewa.

62-Kuma kana ganin mãsu yawa daga gare su, sunã gaugawa a cikin zunubi da zãlunci. Sannan da cin haram. Hakĩka, tir da abin da suka kasance suna aikatãwa.

Har yanzun dangane da yadda ma'abuta littafi suke ma'amala da muminai, wannan ayar tana Magana kan cewa, duk da irin halayen da suke nunawa muminai, suma suna ganin kansu muminai ne, alhali babu imani a cikin zukatansu. Zukatansu na cike da kafici suna tare da muminai ko sun fice daga garesu. Alamar haka kuma shi ne cewa suna gaggawar fadawa cikin sabon Allah da zunubi. Har'ila gasu da cin haramun, da kuma aikata zalunci da wuce iyakoki. Sai dai anan alkur'ani mai girma bai yi wa ma'abuta littafi kudin goro a cikin hukuncinsa ba, akwai masu imani daga cikinsu. Amma mafi yawansu haka suke. Daga cikin wadannan ayoyi muna iya daukan darussa kamar haka. 1. Bayyana imani kadai bai water wajen tabbatar da imanin wanda yake cewa shi mumini neb a, sai ya hada da ayyukan alkhairi. 2. Yaduwar Fasadi da mummunar halaye a cikin al-umma. Musamman cin hanci da rashawa da neman daukaka da tara dukiya suna lalata al-umma, su maida ita ba abakin kome be. 3. Alamun al-umma musulma sune aikata ayyukan alkairi, da kuma yin gaggauwa wajen aikata shi, a yayinda alamun al-umma kafirci da munafurci sune gaggawa wajen aikata sharri da yaduwar fasadi. 4. Abinda ya fi muni daga cikin sabo shi ne bayyana shi a fili ba tare da jin kunya ba. Sabo da aikata sabo da kuma dulmuya cikin sabon Allah a bainal jama'a.

Yanzun kuma mu saurari karatun aya ta 63 daga cikin surara ma'aida kamar haka.

لَوْلاَ يَنْهَاهُمُ الرَّبَّانِيُّونَ وَالأَحْبَارُ عَن قَوْلِهِمُ الإِثْمَ وَأَكْلِهِمُ السُّحْتَ لَبِئْسَ مَا كَانُواْ يَصْنَعُونَ{63}

63-Don me Malaman Tarbiyya da manyan malamai (na Yahudu) ba su hanã su daga fadar sabo da cinsu ga haram ba? Hakika, tir daga abin da suka kasance sunã sanã'antãwa.

Wannan ayar tana bayyana nauyi mai girma da ya hau kan masana da malaman tarbiyya da ke cikin al-umma. A lokacinda mutane suna sabo suna aikata zunubi me ya sa basa hana su, hatta ko da fatar baki basa hana su. Me yasa. Malamai masana masu fahinta da wayewa, kauracewarsu daga sabon Allah kadai bai isa ba, dole sai sun hada da hana masu sabo sabo. Rashin hana sabo kamar amincewa da shi ne. Don haka ne idan azabar Allah ta zo takan hada har da su. Wannan ayar tana karantar da mu darussa kamar haka. 1. Yin shiru da rashin damuwa da sabon da wasu suke aikatawa a cikin alumma ba uzuri bane a wajen Allah. Yin shiru a gaban mai sabo taimaka masa ne. 2. Nauyin fadakarwa da hana sabo a cikin al-umma a daraja ta farko, yana hawa kan masana malaman addini ne. 3. Kimar ilmi da sani shi ne bayyana shi don kawo karshen sabo da fasata a cikin al-umma. To masu sauraro anan zamu dasa aya kuma sai wani lokaci idan Allah ya kai mu. Da fatan Allah ya bamu damar barin sabon Allah da kuma taimakawa masu sabo kuma barinsu. Tahir Amin yake cewa mu huta lafiya.

Suratul Ma'ida, Aya Ta 64-66 (Kashi Na 171)

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barakammu da sake saduwa a cikin shirimmu na hannunka mai sanda shi wanda yake dubi a cikin wasu ayoyin alkur'ani mai girma don su zama fitialla a cikin rayuwarmu da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.

      • .

To bari mu fara shirimmu na yau da sauraron karatun aya ta 64 daga cikin surar Ma'ida kamar haka.

وَقَالَتِ الْيَهُودُ يَدُ اللّهِ مَغْلُولَةٌ غُلَّتْ أَيْدِيهِمْ وَلُعِنُواْ بِمَا قَالُواْ بَلْ يَدَاهُ مَبْسُوطَتَانِ يُنفِقُ كَيْفَ يَشَاءُ وَلَيَزِيدَنَّ كَثِيراً مِّنْهُم مَّا أُنزِلَ إِلَيْكَ مِن رَّبِّكَ طُغْيَاناً وَكُفْراً وَأَلْقَيْنَا بَيْنَهُمُ الْعَدَاوَةَ وَالْبَغْضَاء إِلَى يَوْمِ الْقِيَامَةِ كُلَّمَا أَوْقَدُواْ نَاراً لِّلْحَرْبِ أَطْفَأَهَا اللّهُ وَيَسْعَوْنَ فِي الأَرْضِ فَسَاداً وَاللّهُ لاَ يُحِبُّ الْمُفْسِدِينَ{64}

64- Kuma Yahudu suka ce: "Hannun Allah abin yi wa kukumi ne. " An sanya hannuwansu a cikin kukumi! Kuma an la'ane su sabõda abin da suka fada. Ã'a, hannuwanSa biyu shimfidaddu ne, Yanã ciyarwa yadda Yake so. Kuma lalle ne abin da aka saukar zuwa gare ka yanã kãra wa mãsu yawa daga gare su, girman kai da kãfirci. Kuma Mun jefa a tsakãninsu, kiyayya da keta, zuwa Rãnar kiyãma, kõ da yaushe suka hura wata wuta dõmin yãki, sai Allah Ya bice ta. Sunã aiki a cikin kasa dõmin barna, alhãli kuwa Allah bã Ya son mãsu fasãdi.

A cikin shirimmu da ya gabata mun ayoyin da dama sun yi maganar yadda yahudawa suke yasa barna da fasadi a cikin al-umma, ta hanayar cin hanci da rashawa, da rashin hana fasadi. Amma wannan ayar tana Magana ne kan wata mummunar akidar su dangane da ubangihi, inda suke cewa, a cikin farkon halitta hannun Allah a bude suke duk abinda bayinsa suke so suna samu, amma a yanzu kama hannayensa a daure suke basa bayarwa, mai yuwa halittunsa sun fi karfinsa. Wannan mummunar tunani ya zo masu a lokacinda ayoyinda suka yi Magana a kan ciyarwa da kuma bada sadaka ga mabukata suka sauka. Da kuma ayoyin da suke Magana kan bada bashi da sharussa suka sauka. Suka ce wannan alamace na cewa hannayensa daure suke. Idan da yana iya ciyar da su da bai bukace mum u ciyar da su ba. Allah ta'ala ya basu amsar wannan zancen nasu na kafice da cewa, hannayen kudurarasa basu taba rufewa ba a bude suke, kuma bazasu taba rafewa. suna ciyarwa ga wanda ya dama gwagwadon abinda ya ga dama. Umurnin da Allah ya bayar na ciyarwa da kuma bada bashi bai nuna cewa hannayen kudurar ciyarwansa a rufe suke ba. A'a suna suna imanin muminai ne, da kuma binsu ga umrnin Allah. Ayar ta kara bayanin cewa, wannan halin nasu ya sa kiyayya da gaba ya yadu a cikinsu. Sanna ga musulmi kuma a ko yauce suna burin ganin bayansu. Amma a duk lokacinda suka kunna wutan yaki don ganin bayan musulmi, a farkon musulunci, sai Allah ya maida shi nasara ga musulmi. Wannan a fili yake bayan nasarar da musulmi suka samu a yakin Khaibara. Daga cikin wanana ayar muna iya daukan darussa kamar haka. 1. Tsarkake Allah daga dukkan aibi, nakasa da gazawa na daga cikin sharuddan imani. Yahudawa sun amince da samuwar Allah amma kuma suna danganta rashin kyauta ga Allah, wanda alkur'ani mai girma ya kore hakan ga Allah ta'ala. 2. Tada fitina da wutan yaki na daga cikin halayen da yahudawa suka kebantu da su, amma duk sanda suka kunna wutar fitina ko yaki, sai Allah da hikimarsa ya maida shi alkairi ga muminai. Sai wannan yana faruwa ne a dai sai lokacinda musulmu suka yi riko da imaninsu suna bin tafarkin gaskiya.

Yanzun kuma mu saurari karatun aya ta 65 da kuma yara ta 66 daga cikin surar ma'aida kamar haka.

وَلَوْ أَنَّ أَهْلَ الْكِتَابِ آمَنُواْ وَاتَّقَوْاْ لَكَفَّرْنَا عَنْهُمْ سَيِّئَاتِهِمْ وَلأدْخَلْنَاهُمْ جَنَّاتِ النَّعِيمِ{65} وَلَوْ أَنَّهُمْ أَقَامُواْ التَّوْرَاةَ وَالإِنجِيلَ وَمَا أُنزِلَ إِلَيهِم مِّن رَّبِّهِمْ لأكَلُواْ مِن فَوْقِهِمْ وَمِن تَحْتِ أَرْجُلِهِم مِّنْهُمْ أُمَّةٌ مُّقْتَصِدَةٌ وَكَثِيرٌ مِّنْهُمْ سَاء مَا يَعْمَلُونَ{66}

65-Kuma dã dai lalle Mutãnen Littãfi sun yi ĩmãni, kuma sun yi takawa, hakĩka, dã Mun kankare miyãgun ayyukansu daga gare su, kuma dã Mun shigar da su gidãjen Aljannar Ni'ima.

66- Kuma dã dai lalle sun tsayar da Attaura da Injĩla da abin da aka saukar zuwa gare su daga Ubangijinsu, hakĩka, dã sun ci daga samansu da kuma daga karkashin kafãfunsu. Daga gare su akwai wata al'umma mai tsakaitãwa kuma mãsu yawa daga gare su, abin da suke aikatawa yã munana.

Bayan da ayoyin da suka gabata sun bayyana irin mummunan halayen yahudawa wadanda suka jawo masu fushi da nisanta daga rahamar Allah. Wadan nan ayoyi suna nuna masu cewa, tafarkin Allah fa ba rufe yake a garesu, ko yanzu ne idan zasu tuba su dawo kana tafarkin Allah. Su bar mummunar halayensu Ubangiji mai rahama ne zai gafarta masu zubansu da suka gabata, kuma ya kyautata gabansu. Zai wadatar da su a rayuwar su ta duniya. Ya ciyar da su albarkansa ta sama da kasa. Sannan zai sa su a aljannarsa ranar kiyama. Daga karashe ayoyin suna bayanin cewa, a cikin yahudawa akwai wasu muminai daga cikinsu wadanda suke kan tafarkin matsakaici. Babu wuce gonad a iri ko kuma taksiri a cikin ayyukansu, sai dais u kadan ne sosai a cikinsu. Mafi yawan mutane suna tafiya sabanin tafarkinsu. Duk da cewa wadannan ayoyi suna magane da yahudawa da kuma nasara. Amma lamarin haka yake a cikin musulmi ma. Duk sanda suka yi riko da tafarkon Allah da manzonsa Allaha zai buda masu arzikinsa ta sama da kasa. Sannan idan suka kaucewa tafarkinsa kuma zasu fada cikin kunci da wahalhalu masu yawa. Sunnan Allah haka take, babu sauyi a cikin sunnarsa. Muna iya daukan darussa cikin wadannan ayoyi kamar haka. 1. Imanin da tare da takawa ba ko tsoron Allah ba bai da amfani- takwa shi ne yane nuna tabbacin imani a cikin zuciyar musulmi. 2. Ubangiji mai rahama ne banda gafartawa masu zunubi zunubansu, yakan saukar da rahamarsa da albarkansa bayan sun tuba. 3. Yin imani da Allah da kuma aikata ayyuka na gari suna lamuncewa mumini rayuwan sa'ada ta duniya da lahaira tare. Sai dai sa'adara duniya falala ce. Don rayuwa ta gaskiya itace ta lahira. 4. Karatun littafin Allah bai wadatarba, aiki da abinda yake ciki a dukkan bangarorin rayuwa wajibi ne. Da fatan masu sauraro sun ji dadin wannan shirin. Anan zamu dasa aya sai kuma wani shirin idan Allah ya kaimu. A huta lafiya wassalamu alaikum warahmatullah.

Suratul Ma'ida, Aya Ta 67-68 (Kashi Na 172)

Masu sauraro barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shirin da mu ke kawo mu ku tafsirin al'kur'ani mai girma. Da fatan za a kasance tare da mu domin jin yadda shirin zai kasance.

Yanzu sai a saurari aya ta 67 a cikin suratu ma'idah.

يَا أَيُّهَا الرَّسُولُ بَلِّغْ مَا أُنزِلَ إِلَيْكَ مِن رَّبِّكَ وَإِن لَّمْ تَفْعَلْ فَمَا بَلَّغْتَ رِسَالَتَهُ وَاللّهُ يَعْصِمُكَ مِنَ النَّاسِ إِنَّ اللّهَ لاَ يَهْدِي الْقَوْمَ الْكَافِرِينَ{67}

"Ya kai manzo ka isar da abinda aka saukar maka daga Ubangijinka. Idan ba ka yi ba to ba ka isar da sakonsa ba. Allah zai kiyaye ka daga mutane. Allah ba ya shiryar da mutanen da su ke kafirai."

Wannan ayar ta kebanta da ayoyin da su ka gabata ce ta da kuma wadanda za su zo bayanta. Tana a matsayinta aya ce mai dauke da ma'anoni na musamman. Daga cikin abinda ta kebanta da su da akwai yadda ta fara da yin kira da cewa: "Ya kai manzo." Wato tana magana ne da manzon Allah kai tsaye. Wannan irin nau'in na yin magana da maznon Allah kai tsaye sau biyu kadai ya zo a cikin kur'ani, kuma dukkaninsu sun zo ne acikin wannan sura ta ma'idah.

Abu na biyu da ayar ta kebanta da shi shi ne yin kira ga manzon Allah da ya isar da wani sako na musamman wanda ya ke da nauyi daidai da dukkanin sakon aka aiko shi da shi, ta yadda idan bai isar da shi ba to daidai ya ke da cewa bai isar da wani sako ba.

Abu na uku shi ne cewa wannan batun yana da muhimmanci matuka, ta yadda manzon Allah yana cikin damuwar cewa mutane ba za su amince da wannan sakon ba idan ya isar da shi, su kuma yi inkarinsa.

A karshen ayar kuwa ana yin gargadi da jan kunne ga wadanda su ka yi inkarin wannan sakon da fadin cewa: Mutane irin wadannan sun haramtawa kansu samun rahamar Allah."

Yanzu kuma ya zama wajibi mu yi dubi akan wannan sakon mai muhimmanci da ayar ta ke yin magana akansa. Tare da yin la'akari da cewa ayar ta sauka ne a shekarar karshe ta rayuwar manzo, ya fito a fili cewa ba ana nufin aikin haji da azumi da jihadi ba ne, domin kuwa a tsawon lokacin rayuwar annabi ta shekarun da su ka gabaci wannan lokacin ya isar da wadannan sakonnin.

Wane abu ne mai muhimmanci irin haka wanda aka bijirowa da manzo da shi a lokacin karshe na rayuwarsa, wanda kuma ake jaddadawa, kuma manzaon Allah ya ke jin cewa za a iya yin inkarinsa?

Babu wani abu da zai zama yana da muhimmanci har haka idan ba, halifancin manzon Allah ba da kuma makomar al’ummar musulmi bayansa. Wannan ne ya sa manyan malaman fassara na ahlussunah, kamar fakharurrazy su ka bayyana cewa abu ne mai yiyuwa ya zama wannan ayar tana da alaka da hakan. Kuma su ka bijiro da riwayoyi na tarihi dangane da hakan acikin tafsiransu Tabbas da akwai wasu mafassara kur’ani ma shi’a da su ke fassara ayoyin kur’ani bisa ka’idoji na ahlul-Bayti da su ka yi imani da cewa wannan ayar tana yin magana ne akan ayyana Ali a matsayin halifa da manzon Allah ya y a hajinsa ta karshe a lokacin da ya yi huduba a ghadir. Ya tsaida musulmi sannan ya hau wani wuri mai tudu sannan ya bada labarin karatowar ajalinsa, sannan kuma ya bayyana Ali Dan Abi Talib wanda ya ke sahabinsa mafi biyayya a gare shi a tsawon shekaru 23 na manzanci, da cewa shi ne halifarsa. Ya fadi cewa: “Duk wanda na kasance ni jagora ne a gare shi, to Ali ma jagora ne a gare shi” Dagan an kuma ya ci gaba da cewa, duk wanda ya ke a wannan wurin to ya bada labari ga wanda ba ya nan. Manyan sahabban ma’aiki da su ke a wannan wurin sun taya Ali Dan Abi Talib murna.

Wasu kuwa sun fassara ma’anar ‘maula” da cewa tana nufin abin kauna ba jagora ba.

Sai dai wani abu ne da ya ke sananne cewa babu wani musulmi wanda bai san cewa annabi yana kaunar Ali ba, balle ya zamana annabi ya bukatu da ya tara mutane ya fada musu hakan, kuma a kwanakin karshe na rayuwarsa. Saukar wannan ayar da kuma yanayi na musamman na suakarta, suna nuni da cewa, abinda aka kumarci manzon Allah da shi a cikinta ya sha kan ya tara mutane ya fada musu cewa yana kaunar Ali. Batu ne wanda ya shafi makomar al’ummar musulmi wanda shi ne jagorantar al’ummar musulmi da shiryar da su bayan ma’aiki. Abubuwan da za mu koya daga cikin wannan aya. 1-Idan har jagororin al’ummar musulmi ba su kasance salihai ba wadanda Allah ne ya ayyana su, to ginshikin addini zai kasance a cikin hatsari. 2-Abinda manzon Allah ya ke da damuwa akansa dangane da musulmi ba hatsarin makiya ne daga waje ba, hatsari ne na fitinar cikin gida da nuna adawa da kuma kin bin umarni.

Yanzu kuma sai aya ta 68 a cikin wannan sura ta Ma'ida.

قُلْ يَا أَهْلَ الْكِتَابِ لَسْتُمْ عَلَى شَيْءٍ حَتَّىَ تُقِيمُواْ التَّوْرَاةَ وَالإِنجِيلَ وَمَا أُنزِلَ إِلَيْكُم مِّن رَّبِّكُمْ وَلَيَزِيدَنَّ كَثِيراً مِّنْهُم مَّا أُنزِلَ إِلَيْكَ مِن رَّبِّكَ طُغْيَاناً وَكُفْراً فَلاَ تَأْسَ عَلَى الْقَوْمِ الْكَافِرِينَ{68}

" Ka ce ya ku ma'abota littafi ba ku da wani matsayi har sai idan kun yi aiki da Attaurah da Linjila da kuma abinda aka saukar mu ku daga Ubangijinku. Tabbas abinda aka saukar maka daga Ubangijinka zai karawa da dama daga cikinsu dagawa da kafirci. Babu jin takaici akan mutanen da su ke kafirai."

Abinda ya ke kunshe acikin wannan ayar ya yi kama da wanda ya zo a cikin aya ta 66 a cikin shirin da aka saurara a baya. Tana kuma sake yin bayani ne akan matsayar ma'abota littafi dangane da Musulunci da kuma manzon Allah. An kuma umarnci manzo da ya sanar da su cewa, yin bugun kirjin da su ke yi na cewa su mabiya annabawa ne kamar Musa da Isa bai wadatar ba, imani na gakiya yana kunshe a cikin yin aiki da hukunce-hukuncen Ubangiji a cikin rayuwar yau da kullum.

Sunna ce ta Allah a tsawon tarihi aiko da annabawa da ya yi, saboda haka yin imani da wani annabi sannan kuma da kin imani da wanda ya zo bayansa yana a matsayin nuna wariya ne na banbancin launin fata da kuma addini wadanda su ke yi wa mutum shingen kaiwa ga shiriya. Su ke kuma sa shi yin dagawa da kuma boye gaskiya. Saboda haka ne Ubangiji acikin wannan ayar ya jaddada wajabcin yin imani da dukkanin saukakkun littatafai sannan kuma ya ke magana da annabi yana cewa: " Da dama daga cikin ma'abota littafi ba a shirye su ke ba su yi imani da kur'ani, kuma wannan irin tunanin nasu ne ya ke ingiza su zuwa ga kafirci domin kuwa sun zabi yin hakan ne cikin sani. Saboda haka kada ka ji wani takaici akan kafircinsu domin kuwa Allah zai yi musu hisabi.

Abubuwan da za mu koya daga wannan aya. 1-Riya imani kadai bai isa ba, wajibi ne a yunukura kuma a yi aiki. Wanda duk baya aikata hukunce-hukuncen addini ba shi da addini. 2-Matsayin mutane a wurin Ubangiji yana da alaka ne da rikonsu da hukunce-hukuncen addini kuma wajibi ne acikin al'umma ma matsayin mutane ya kasance bisa wannan ma'aunin. 3-Kada mu zama masu bakin kishi na ido rufe, mu zama masu girmama hakkin wasu da kuma girmama akidojinsu, kuma a lokaci guda mu gabatar da tafarkinmu.

Da wannan ne mu ka kawo karshen wannan shirin da fatan Allah ya ba mu dacewa mu zama masu sanin gaskiyar addini da kuma aiki da hukunce-hukuncen Ubangiji.

Sai kuma mu sake haduwa aciki wani shirin.

Suratul Ma'ida, Aya Ta 69-71 (Kashi Na 173)

Masu sauraro barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shirin da mu ke kawo musu fassarar ayoyin kur'ani mai girma.

Da fatan za a kasance a tare da mu domin a saurari shirin daga inda mu ka tsaya a baya.

Yanzu sai a saurari a ya ta 69 a cikin suratu ma'idah.

إِنَّ الَّذِينَ آمَنُواْ وَالَّذِينَ هَادُواْ وَالصَّابِؤُونَ وَالنَّصَارَى مَنْ آمَنَ بِاللّهِ وَالْيَوْمِ الآخِرِ وعَمِلَ صَالِحاً فَلاَ خَوْفٌ عَلَيْهِمْ وَلاَ هُمْ يَحْزَنُونَ{69}

"Tabbas wadanda su ka bada gaskiya da yahudawa da Sa'ibawa da kiristoci, duk wanda ya yi imani da Allah da ranar kiaywa ya kuma yi aikin kwarai, babu tsoro a tare da su kuma ba za su yi bakin ciki ba."

A cikin shirin da ya gabata a cikin aya ta 68 an bayyana cewa mabiya kowane addini ba su da wani matsayi a wurin Ubangiji har sai idan sun yi aiki da littafin da aka saukar musu, su kuma tafiyar da al'ummarsu akan turbarsa.

To abinda wannan ayar ta ke yin magana akansa shi ne cewa: Mabiya addinai ba su da wani fifiko akan junansu, musulmi da yahudawa da Sai'bawa ( su ne mabiya annabawan baya irin su annabi Nuhu da Yahya) hatta dadewa wajen riko da koyarwar annabawan baya ba ya a matsayin ma'auni na fifikon wani daga cikinsu. Wanda ya ke da matsayi a wurin Ubangiji shi ne wanda ya ke da imani da Allah da ranar kiyama da kuma aikin kwarai acikin al'umma.

Sai dai abu ne da ya ke a fili cewa a duk lokacin da wani annabi ya zo to wajibi ne masu bin annabin da ya gaba ce shi su rungumi koyarwar wannan annabin da ya zo daga baya. Su kuma zama masu aiki da hukunce-hukuncen da ya zo da su. Idan kuwa ba haka ba to ayyukansu za su zama a banza. Kuma kasantuwar annabi Muahmmad (s.a.w) shi ne cikamakin annabawa wajibi ne yin imani da shi.

Abubuwan da za mu koya daga wannan aya.

1-Ma'auni sa'ada a cikin dukkanin saukakkun addinai shi ne imani da kuma aiki, ba riyawa da fatar baki ba. 2-A karkashin imani da Allah da ranar kiyama ne ne kadai mutane za su sami nutsuwa da kwanciyar hankali.

Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 70 a cikin suratu ma'idah.

لَقَدْ أَخَذْنَا مِيثَاقَ بَنِي إِسْرَائِيلَ وَأَرْسَلْنَا إِلَيْهِمْ رُسُلاً كُلَّمَا جَاءهُمْ رَسُولٌ بِمَا لاَ تَهْوَى أَنْفُسُهُمْ فَرِيقاً كَذَّبُواْ وَفَرِيقاً يَقْتُلُونَ{70}

"Hakika mun riki alkawali daga Banu Isra'ila mu ka aike musu da manzanni. A duk lokacin da wani manzo ya zo musu da abinda zuciyarsu ba ta so sai su karyata wani sashe su kuma kashe wani sashe."

Bayan da annabi Musa ya fitar da Banu Isra'ila daga danniyar fir'auna, ubangiji ya umarce shi da ya karbi alkawali daga gare su akan cewa za su yi aiki da umarnin Ubangiji. Sai dai kamar yadda aka yi ishara a cikin wata aya ba su rike wannan alkawalin ba, sun yi watsi da hukunce-hukuncen Allah, sun kuma rika karyata annabawan da Allah ya aiko saboda sun zo da abinda ya sabawa son zuciyarsu, sun kuma rika kashe wasu annbawan.

To wannan ayar tana a matsayin gargadi ne ga musulmi da su fadaka kada su ki aiki da umarnin annabi akan wadanda zai yi wasici da su. Su zama masu riko da alkawalin da su ka dauka a Ghadir wanda ya zo acikin ayar da ta zo a wannan sura. Abubuwan da za mu koya daga wannan aya.

1-Kafiran da su ka karyata sakwannin annbawa ba su dogara da wani dalili na hankali ba. Abinda ya sa su ke kin bin annabawa shi ne son zuciyarsu da aikata abinda su ka ga dama. Alhali addini yana daidaita bukatun mutum ne domin ya sami kaiwa ga kamala. 2-A cikin gurbatacciyar al'umma ana kashe mutanen kwarai ko kuma a karyata su.

Yanzu kuma sai aya ta 71 a cikin suratu Ma'idah.

وَحَسِبُواْ أَلاَّ تَكُونَ فِتْنَةٌ فَعَمُواْ وَصَمُّواْ ثُمَّ تَابَ اللّهُ عَلَيْهِمْ ثُمَّ عَمُواْ وَصَمُّواْ كَثِيرٌ مِّنْهُمْ وَاللّهُ بَصِيرٌ بِمَا يَعْمَلُونَ{71}

"Sun tsammaci cewa fitina ba za ta afku ba, sai su ka rufe idanunsu- daga ganin gaskiya-, su ka done kunnuwansu-daga jinta, amma Allah ya yi musu gafara, sai kuma wasu da dama daga cikinsu su ka sake makancewa su ka kuma kurumta. Allah yana ganin abinda su ke aikatawa."

Kamar yadda mu ka fada a cikin shirin da ya gabata, yahudawa suna jin cewa suna da fifiko akan sauran al'ummu, suna kuma jin cewa su ne wadanda Allah ya fi kauna kuma sun fi kowa kusanci a wurinsa. Adalilin haka ne su ke tsammanin cewa za su kasance a cikin kwanciyar hankali, kuma duk abinda za su aikata Allah ba zai azabtar da su ba kuma ba zai jarrabe su ba, ko kuma idan ma an jarabce su to na wani kankanen lokaci ne.

Wannan jiji da kai din ne da kuma girman kan ya sa suka rufe idanuwansu da dode kunnuwansu. Ba a shirye su ke su ji gaskiya ba balle su karbe ta akan cewa jarabawa wata sunna ce ta Ubangiji da bai toge wani mahaluki guda ba wajen aiwatar da ita akansa. Dukkanin mutane za su fuskanci jarabawa daidai gwargwado domin hakikanin badininsu ya fito fili.

Sai dai shakka babu Ubangiji mai rahama ne da jin kai, saboda haka ba ya rikon bayaninsa da laifi guda. Yana bada dama ga mutum ya tuba kuma yana karbar tuba. Sai dai wasu suna kawar da damar da rahamar Allah da jin kansa za su sauka a gare su da kansu.

Abubuwand a za mu koya daga wannan aya.

1-Tsammani ba akan abinda ya dace ba da kuma jiji da kai suna hana mutum fahimtar hakikanin gaskiya. 2-Koda mutum zai yi inkarin samuwar Ubangiji ya kuma rufe idanuwansa daga ganin samuwarsa, to Ubangijin yana ganinsa.

Wannan shi ne karshen wannan shirin. Muna masu fatan mu zama masu imani da kuma riko da alkawalin Ubangiji.

Sai wani shirin.

Suratul Ma'ida, Aya Ta 72-75 (Kashi Na 174)

Masu sauraro barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shirin da mu ke kawo mu ku fassarar ayoyin kur'ani mai girma. Da fatan za a kasance a tare da mu domin a ji ci gabansa daga inda mu ka tsaya a baya.

Yanzu sai a saurari aya ta 72 a cikin wannan sura ta ma'idah.

لَقَدْ كَفَرَ الَّذِينَ قَالُواْ إِنَّ اللّهَ هُوَ الْمَسِيحُ ابْنُ مَرْيَمَ وَقَالَ الْمَسِيحُ يَا بَنِي إِسْرَائِيلَ اعْبُدُواْ اللّهَ رَبِّي وَرَبَّكُمْ إِنَّهُ مَن يُشْرِكْ بِاللّهِ فَقَدْ حَرَّمَ اللّهُ عَلَيهِ الْجَنَّةَ وَمَأْوَاهُ النَّارُ وَمَا لِلظَّالِمِينَ مِنْ أَنصَارٍ{72}

"Hakika wadanda su ka ce Allah shi ne almasihu Dan Maryam sun kafirta. Almasihu ya ce ya ku Bani Isra'ila ku bautawa Allah wanda shi ne ubangijina kuma Ubangijinku. Wanda duk ya tara Allah da wani to hakika Allah ya haramta masa aljanna, kuma makomarsa wuta. Azzalumai ba su da mataimaka."

A baya acikin wasu shirye-shiryenmu alkur'ani ya yi ishara da yadda yahudawa su ke da karkataccen tunani ya kuma yi ishara da tarihinsu na baya sannan ya yi gargadi a gare su da su daina taurin kai su bada gaskiya.

To wannan ayar da kuma ayoyin da su ka zo bayanta suna magana ne da kiristoci da fada masa cewa: Ya za a yi ku dauki almasihu wanda yana cikin annabawan Allah, a matsayin Ubangiji? Shin shi almasihu ne da kansa ya fadi hakan? Ko kuma saboda ku nuna cewa akidarku tana da girma ne da fifiko akan ta yahudawa ku ke yin magana irin wannan?

Daga nan kuma kur'ani ya yi ishara da akidoji irin wannan sannan ya fadi cewa: Zurfafawar da ku ke yi akan almasihu, ba kawai ya fitar da ku daga imani ba ne, yana ma a tsayin shirka ne da kuma yin nisa daga tauhidi. Irin wannan akidar da ku ke da ita ba za ta kusanta ku da Allah ba domin kuma kun zama masu shirka ta hanyar daukar almasihu a matsayin Ubangiji wanda ya sa ku ka nesanta daga Allah, wannan kuma shi ne zai sa ku yi nisa da aljanna a ranar lahira da kuma rahamar Allah. Ku kuma shiga wuta mai kuna da radadi kuma babu wadanda za su taimaka mu ku.

Wani abu mai jan hankali nan shi ne cewa hatta a cikin Bible babu inda aka ambato almasihu yana fadin cewa shi Ubangiji ne. A cikin Bani na 12 aya ta 29 a linjilar Markus, almasihu da kansa ya fadi cewa: Ubangijinmu guda daya ne tilo."

Abubuwan da za mu koya daga wannan aya. 1-Kamar yadda gajiyawa wajen cika imani da iki ba karbabben abu ba ne, haka nan ma wuce gona da iri akan bayin Allah ba abu ne karbabbe ba. Yana kuma a matsayin wani nau'i ne na shirka da kafirci, duk yadda masu wannan tunanin za su riya cewa abinda su ke yi imani ne. 2-Babu wani mutum- koda kuma annabi Isa ne da zai iya tseratar da 'yan wuta daga azabar Allah, saboda haka ku yi watsi da tunanin cewa annabi Isa ya sadaukar da kansa saboda ya tserarar da ku.

Yanzu kuma za mu saurari ayoyi na 73 da 74 acikin suratu ma'idah.

لَّقَدْ كَفَرَ الَّذِينَ قَالُواْ إِنَّ اللّهَ ثَالِثُ ثَلاَثَةٍ وَمَا مِنْ إِلَـهٍ إِلاَّ إِلَـهٌ وَاحِدٌ وَإِن لَّمْ يَنتَهُواْ عَمَّا يَقُولُونَ لَيَمَسَّنَّ الَّذِينَ كَفَرُواْ مِنْهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ{73} أَفَلاَ يَتُوبُونَ إِلَى اللّهِ وَيَسْتَغْفِرُونَهُ وَاللّهُ غَفُورٌ رَّحِيمٌ{74}

" Hakika wadanda su ka ce Allah dayan Alloli uku ne sun kafirta. Babu wani Ubangiji sai Allah guda daya. Idan ba su daina fadin abinda su ke fada ba to azaba mai radadi za ta shafi wadanda su ka kafirta daga cikinsu. Shin ba za su tuba ga Allah ba, su nemi gafararsu? Allah mai gafara ne mai rahama."

A cikin aya ta baya an yi magana akan akidar da kiristoci su ke da ita akan almasihu da su ka daukaka shi fiye da matsayin mutane su ka kai shi matsayin ubangiji. Wannan ayar tana yin suka ne akan akidar ta kiristoci dangane da Ubangiji da kuma maida shi zuwa dayan iyayengiji uku, alhali allantaka da Ubangijintaka abu ne guda daya da basu rabuwa. Wato Allah shi ne mahalicci kuma guda daya ya ke tilo. Saboda haka kasantuwarsa Ubangiji ne guda daya abin bauta.

Har ila yau wannan ayar tana bayyana karkacewar tunanin wadannan mutanen tare da yin gargadi a gare su. Tana fadin cewa:

Wadanda ba a shirye su ke ba su gyara tunaninsu za su fuskanci azabar Allah mai tsanani, idan kuma su ka tuba su ka koma ga Allah to shakka babu rahamar Allah za ta lullube su.

Abubuwan da za mu koya a cikin wadannan ayoyin. 1- Kur'ani bai kore addinai da annabawan da su ka gabata ba, ya karbe su sannan kuma ya maida hankali akan kawar da gurbatawar da aka shigar a cikinsu.

2-Kafirci bai takaita acikin inkarin samuwar Ubangiji ba, yin imani da wani abin tarayya ga Allah ma nau'i ne na kafirci.

3-Ubangiji yana yin gafara ga laifukan baya, kuma Allah cikin rahamarsa da jin kansa yana gyara rayuwa ta gaba, sai dai sharafin hakan shi ne tuba.

Yanzu kuma sai aya ta 75 acikin wannan sura ta Ma'idah.

مَّا الْمَسِيحُ ابْنُ مَرْيَمَ إِلاَّ رَسُولٌ قَدْ خَلَتْ مِن قَبْلِهِ الرُّسُلُ وَأُمُّهُ صِدِّيقَةٌ كَانَا يَأْكُلاَنِ الطَّعَامَ انظُرْ كَيْفَ نُبَيِّنُ لَهُمُ الآيَاتِ ثُمَّ انظُرْ أَنَّى يُؤْفَكُونَ{75}

"Almasihu Dan Maryama ba shi da wani matsayi da ya wuce annabi kuma annabawa sun gabace shi. Mahaifiyarsa mai gaskiya ce, kuma shi da ita sun kasance masu cin abinci. Ka duba ka ga yadda mu ke yi musu bayanin ayoyi, kuma ka duba ka ga yadda su ke karyatawa."

Ci gaban bayani ne na akodojin kiristoci akan annabi Isa (a.s) ya zo acikin wannan ayar haka nan kuma a yoyin da su ka gabata. Kur'ani ya kawo dalilai guda uku da su ke rusa cewa annabi Isa ubangiji ne. Na farko shi ne cewa mace ce ta haifeshi alhali Ubangiji ba shi da mahaifa. Na biyu shi ne cewa an yi annabawa da dama da su ka gabace shi kamar annabi Adamu wanda ba shi da mahaifiya balle mahaifi, amma duk da haka babu wanda ya dauke shi a matsayin Ubangiji. Na uku: Yana cin abinci shi da mahaifiyarsa domin yana da bukatuwa da abincin saboda ya rayu, idan kuma Ubangiji ne shi babu yadda za a yi ya bukatu da wani abu.

Abubuwan da za mu koya daga wannan aya. 1-Siffofi na musamman da wani mutum ya ke da su ba su maida shi ya zama Ubangiji, hatta mu'ujizar da annabawa su ka zo da su ba ya nufin cewa su iyayengiji ne. 2-Fadar gaskiya da kuma aikata ta su ne siffofi na koli a wurin Ubangiji, Ubangiji yana yabawa maryam saboda wannan. 3-Maryam da danta annabi Isa mutane ne duk da cewa suna da siffofi na kamala.

Muna kawo karshen wannan shirin cikin fatan Allah ya bamu sanin annabi ta hanya mafi inganci da kuma zama masu madaidaiciyar akidar da babu wuce gona da iri acikinta, haka nan kuma a cikin ayukanmu.

Sai mu sake hadewa a cikin shiri na gaba.

Suratul Ma'ida, Aya Ta 76-80 (Kashi Na 175)

Masu sauraro barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shirin wanda mu ke kawo mu ku fassarar ayoyin kur’ani mai girma. Da fatan za a kasance a tare da mu domin jin ci gabansa daga inda mu ka tsaya.

Yanzu sai a saurari aya ta 76 a cikin suratu ma’idah.

قُلْ أَتَعْبُدُونَ مِن دُونِ اللّهِ مَا لاَ يَمْلِكُ لَكُمْ ضَرّاً وَلاَ نَفْعاً وَاللّهُ هُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ{76}

“Ka ce shin za ku bautawa wanin Allah wanda ba shi da abinda zai cutar da ku ko ya amfane ku? Allah shi ne mai ji kuma masani.”

Idan ba ku mance ba a shirin da ya gabata mun yi magana ne akan akidojin kiristoci dangane da yadda su ke daukar annabi Isa (a.s) a matsayin Ubangiji kuma su ke bauta masa.Alhali kuwa ba zai iya amfana ko cutar da su da wani abu ba. Idan ya zamana wani annabin Allah ba zai iya taka wata rawa a rayuwar mutum ba, ba tare da izinin Allah ba, to a fili ya ke cewa, shi bai cancanci a bauta masa ba. Abubuwan da za mu koya daga wannan ayar. 1-Tafarkin shirka bata ne, wanda idan har aka sa hankali za a iya fahimtar hakan. Saboda haka ne Allah ya ke yi wa mutum tambayar da ta ke cewa, shin wannan abinda ake bauta zai iya amfana ko cutarwa? 2-Idan ba Allah ba babu wani abin bauta wanda zai iya ji ko gani ko fahimtar bukatun mutum, balle kuwa ya biya masa su. Yanzu kuma sai aya ta 77 acikin wannan sura ta Ma’idah.

قُلْ يَا أَهْلَ الْكِتَابِ لاَ تَغْلُواْ فِي دِينِكُمْ غَيْرَ الْحَقِّ وَلاَ تَتَّبِعُواْ أَهْوَاء قَوْمٍ قَدْ ضَلُّواْ مِن قَبْلُ وَأَضَلُّواْ كَثِيراً وَضَلُّواْ عَن سَوَاء السَّبِيلِ{77}

“Ka ce ya ku ma’abota littafi kada ku zurfafa acikin addininku ba bisa gaskiya ba, kuma kada ku biyewa son zuciyar mutanen da sun riga sun bace tun tuni, kuma sun batar da –mutane- masu yawa, kuma sun karkace daga kan tafarki.”

A karkashen ayoyin da su ke yin bayani akan wuce gona da iri na ma’abota littafi akan annabawan da aka aiko musu, ayoyin suna kuma yin bayani akan cewa wadannan mutanen ba su aiki da ilimi kuma ba su riko da wani addini. Haka nan kuma tana bayyana cewa kamalar da annabawan Allah su ke da ita bai kamata ta sa ku wuce gona da iri akansu ba ya zamana suna fadin abinda ba gaskiya ba dangane da su. Tarihin bil’adama a cike ya ke da wuce gona da iri da zurfafawa haka nan kuma halin sassauci mai yawa. Wani gungun na mutane sun sauko da annabawa kasa daga kan matsayin da su ke da shi suna bayyana su a matsayin mahaukata. Wasu kuma sun kai annabawan inda Allah bai kaisu ba su ka kaisu matsayin iyayengiji. Annabawa mutane kamar sauran mutane wadanda tsarkin niyya da aikinsu ya sa su ka zama masu cancantar karbar sakon Ubangiji na wahayi. Ci gaban wannan ayar yana bayyana cewa wuce gona da irin yahudawa da Kiristoci yayi daidai da akidojin mushrikai da su ka yi imani da cewa abubuwan da su ke bauta suna da tasiri acikin dabi’a da kuma rayuwarsu. Abinda za mu koya daga wannan aya. 1-Addini ya ginu ne akan matsakaicin tafarki ba wuce gona da iri ko sakwa-sakwa ba. Zurfafawa akan shugabannin addini ko su wanene su, kuma ta kowace fuska yana cin karo da ginshikin addini.

Yanzu kuma sai ayoyi na 78 da 79 acikin wannan sura ta Ma’idah.

لُعِنَ الَّذِينَ كَفَرُواْ مِن بَنِي إِسْرَائِيلَ عَلَى لِسَانِ دَاوُودَ وَعِيسَى ابْنِ مَرْيَمَ ذَلِكَ بِمَا عَصَوا وَّكَانُواْ يَعْتَدُونَ{78} كَانُواْ لاَ يَتَنَاهَوْنَ عَن مُّنكَرٍ فَعَلُوهُ لَبِئْسَ مَا كَانُواْ يَفْعَلُونَ{79}

“An la’anci wadanda su ka kafirta daga cikin Banu Isra’ila a bisa harshen Dauda da Isa Dan Maryam, saboda abinda su ka aikata na sabo da kuma ketare iyaka. Sun kasance wadanda ba su hana junansu munanan ayyukan da su ke aikatawa. Tir da abinda su ka rika aikatawa.”

Tare da cewa annabawa suna a matsayin hanyoyin rahama ne da kuma shiriya, sai dai a lokaci guda su ba masu nuna wariya ba ne ga wani jinsin mutane sabanin wasu, kuma su ba masu bakin kishin kasa ba ne, balle ya zamana sun kau da kai daga abinda mutanen al’ummarsu su ke yi, ko kuma su yi shiru, balle kuma su amince da shi. Ya zo a cikin riwayoyi na tarihi cewa a lokacin da Bani Isra’ila su ka ki yin aiki da umarnin Ubangiji na yin hutu daga gudanar da duk wani aiki a ranar asabar, annabi Dauda ya la’ance su. Haka nan kuma a lokacin da su ka bukaci Allah ya sauko musu da abinci daga sama, kuma annabi Isa ya yi addu’a abincin ya sauko, wasu daga cikinsu sun ki amincewa da wannan karramawar da Allah ya yi musu saboda haka annabi Isa (a.s) ya la’ance su. Ci gaban ayar yana yin ishara ne da wani batu mai muhimmanci a cikin rayuwar zamantakewa wanda shi ne cewa. Idan masu aikata saboda da tafka laifi a cikin al’umma suna da laifi to mutanen kwarai ma suna aikata laifi idan su ka yi shiru su ka zura musu idanu. Kuma tsinuwar Ubangji da za ta sauka akan masu sabo da laifi za ta shafi wadannan mutanen kwarai din da su ka zama ‘yan kallo. Abubuwan da za mu koya daga wadannan ayoyin. 1-Annabawa suna a matsayin rahama ne, amma alokaci guda suna la’anatar masu aikata laifi da wuce gona da iri. 2-Take doka da sakin hanya shi ne abinda Banu Isra’ila su ke yi a tsawon tarihinsu. 3-Ba masu laifi ba ne kadai la’antar Allah ta ke sauka akansu, haka nan wadanda su ke yin shiru kuma sanya idanu ta yadda masu laifi za su sami karfin guiwar ci gaba da abinda su ke yi. 4-Hani da aikata munana nauyi ne da ya rataya a wuyan kowane mutum.

Yanzu kuma sai aya ta 80 acikin wannan sura ta Ma’idah.

تَرَى كَثِيراً مِّنْهُمْ يَتَوَلَّوْنَ الَّذِينَ كَفَرُواْ لَبِئْسَ مَا قَدَّمَتْ لَهُمْ أَنفُسُهُمْ أَن سَخِطَ اللّهُ عَلَيْهِمْ وَفِي الْعَذَابِ هُمْ خَالِدُونَ{80}

“Za ka ga dama daga cikinsu suna jibintar wadanda su ka kafirta. Tir da abinda rayukansu su ka gabatar–wanda ya sa – Allah ya yi fushi da su, kuma za su dawwama acikin azaba.”

Wannan ayar tana ci gaba da yin bayani ne akan tarihin Bani Isra’ila, tana fadawa manzon Allah cewa: Ba wai a zamanin baya da ya rigayi zuwan musulunci ba ne kadai wadannan mutane su ke hada kai da kafirai da fifita su akan muminai, a wannan lokacin ma haka su ke. Wannan kuwa shi ne daya aga cikin dalilan da ya sa annabawan Allah su ka la’ance su. Abubuwan da za mu koya daga wannan aya. 1-Jibintar kafirai ta kowace fuska yana daga cikin abinda ke jawo fushin Ubangiji. 2-Lahira ce wurin girbar ayyukan da mutum ya yi a duniya. Wutar lahira kuwa mutum ne ya ke kunnata da rurutata da hannuwansa ta hanyar ayyukansa a duniya. Masu sauraro, mun kawo karshen wannan shirin cikin fatan Allah ya ba mu lafiya ya kuma ba mu dacewa. Sai mun sake haduwa a cikin shiri na gaba.

Suratul Ma'ida, Aya Ta 81-83 (Kashi Na 176)

Masu sauraro barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shirin na Hannunka Mai Sanda. Da fatan za a ci gaba da kasancewa tare da mu domin a saurari ci gaban shirin daga inda mu ka tsaya a baya.

Yanzu sai a saurari aya ta 81 a cikin suratu Ma’idah.

وَلَوْ كَانُوا يُؤْمِنُونَ بِالله والنَّبِيِّ وَمَا أُنزِلَ إِلَيْهِ مَا اتَّخَذُوهُمْ أَوْلِيَاء وَلَـكِنَّ كَثِيراً مِّنْهُمْ فَاسِقُونَ{81}

“Da ace sun bada gaskiya da Allah da annabi da kuma abinda aka saukar zuwa gare shi, to da ba su dauke su abin jibinta ba. Sai dai mafi yawancinsu fasikai ne.”

A cikin shirin baya mun karanta aya ta 80 da aciki Ubangiji ya bayyana cewa mafi yawancin yahduawa suna kaunar kafirai da kuma jibintarsu, wanda hakan ne ya janyo musu fushin Ubangiji. To aci gaba da bayani akan wannan batun wannan ayar da mu ka saurara yanzu tana cewa: Wannan kaunar da yahduawa su ke yi wa kafirai da kuma jibintar lamarinsu yana nuni ne da cewa a hakikanin gaskiya ba su yi imani da Allah da annabi da saukakken littafi ba. Ya za a yi a hada yin imani da Allah da kuma jibintar kafirai? Wannan ayar tana ci gaba da cewa: Ba wai imani da annabi da musulunci da saukakken littafi ne kadai wadannan mutane ba su yi ba, ba su ma yi imani na hakika ba kuma aikin da su ke yi yana cin karo da na masu imani.

Abubuwan da za mu koya daga wannan aya.

1-Yin imani da Allah da kuma saukakken littafinsa shi ne hanyar samun ‘yanci daga mulkin kafirai da kuma kaiwa ga cin cin gashin kai. 2-Mika kai ga kafirai yana daga cikin alamun rashin imani kuma fasikanci ne.

Yanzu kuma sai aya ta 82 a cikin suratu Ma’idah wanda kuma shi ne farkon juzu’i na bakwai acikin alkur’ani mai girma.

لَتَجِدَنَّ أَشَدَّ النَّاسِ عَدَاوَةً لِّلَّذِينَ آمَنُواْ الْيَهُودَ وَالَّذِينَ أَشْرَكُواْ وَلَتَجِدَنَّ أَقْرَبَهُمْ مَّوَدَّةً لِّلَّذِينَ آمَنُواْ الَّذِينَ قَالُوَاْ إِنَّا نَصَارَى ذَلِكَ بِأَنَّ مِنْهُمْ قِسِّيسِينَ وَرُهْبَاناً وَأَنَّهُمْ لاَ يَسْتَكْبِرُونَ{82}

“Hakika za ka iske cewa yahudawa da mushrikai su ne mafi tsananin gaba da wadanda su ka bada gaskiya. Hakika kuma za ka iske cewa wadanda su ka fi zama masu kaunar wadanda su ka bada gaskiya su ne wadanda su ka ce mu kiristoci ne. Dalili kuwa shi ne cewa a cikinsu da akwai malamai da masu ibada wadanda ba su yin girman kai.”

A bisa riawaya ta tarihi a shekara ta biyar daga aiko ma’aiki, manzon Allah ya bada umarni ga wasu musulmi da su yi hijira zuwa Habasha saboda su kaucewa cutarwar da mushrikai su ke yi musu. Sarkin Habasha kirista ne amma ya yi wa musulmi kyakkyawar tarba, kuma ya ki ya mika su ga wakilin da mushrikan makka su ka aike zuwa gare shi. Bugu da kari malaman kiristoci da su ka ji jagoran tawagar musulmi Ja’afar Dan Abu Talib ya karanta ayoyin suratu Maryam sun zubar da hawaye, su ka baiwa musulmi kariya. Amma bayan da musulmi su ka yi hijira zuwa madina, yahudawa da su ke mazauna wannan birnin sun karya yarjejeniyar da su ka kulla da musulmi, su ka shiga kitsa makirci da shirya kutunguila ga musulmi tare da hadin baki da mushrikai. Har ta kai su ga shelanta yakin da aka fi sani da na “Ahzab”. A dailin haka ne anan kur’ani mai girma ya ke kwatanta matsayin wadannan bangarorin guda biyu sannan ya ke yanke hukunci da cewa: “Kiristoci su ne su ka fi kusanci da ku domin kuwa a cikinsu da akwai masana masu adalci wadanda idan sun ga gaskiya ba su yi mata girman kai suna kasakantar da kawunansu a gabanta. Amma yahudawa wadanda ba goyon bayan da su ke nuna mu ku, suna ma hada kai ne da mushrikai su rika kitsa muku makirci. Abubuwan da za mu koya acikin wannan aya. 1-Gabar da yahudawa su ke nunawa musulmi dadaddiya ce tun daga farkon musulunci. Idan a wannan lokacin Isra’ila ta mamaye kasar palasdinu kuma ta kori palasdinawa daga cikin kasarsu, to a farkon bayyanar musulunci ba abinda su ka shirya yi kenan wato su kori musulmi daga madina, amma ba su sami dace ba. 2-Masana da masu ibada suna taka gagarumar rawa wajen ayyana halayyar mutane acikin al’umma. Idan su ka gyaru to al’umma za ta gyaru, idan kuma su ka baci to al’umma za ta baci. 3-Musulunci bai aminta da yi wa wata al’umma kudin goro ba, yana hulda ne da mabiya sauran addinai cikin adalci. Acikin aya mai zuwa Ubangiji yana yin jinjina ga malamai da masu ibada na addinin kiristanci.

Yanzu sai mu saurari aya ta 83 a cikin wannan sura ta Ma’idah.

وَإِذَا سَمِعُواْ مَا أُنزِلَ إِلَى الرَّسُولِ تَرَى أَعْيُنَهُمْ تَفِيضُ مِنَ الدَّمْعِ مِمَّا عَرَفُواْ مِنَ الْحَقِّ يَقُولُونَ رَبَّنَا آمَنَّا فَاكْتُبْنَا مَعَ الشَّاهِدِينَ{83}

“Idan su ka saurari abinda aka saukarwa da manzo, za ka ga maganansu suna zubar da hawaye saboda sanin gaskiya da su ka yi, suna masu fadin cewa, Ubangijinmu mun yi imani ka rubuta mu a cikin wadanda su ka shaida.”

A baya mun ambaci cewa a lokacin da Ja’afar Dan Abu Talib ya karantawa kiristoci ayoyin suratu maryam, sun yi kuka saboda shauki. To bayan da musulmi su ka baro Habasha su ka koma makka wasu kiristocin sun biyo su domin su hadu da manzon Allah. A lokacin da su ka saurari ayoyin suratu Yasin idanunsu sun zubar da hawaye. Alkur’ani mai girma yana jinjinawa ruhin da ya ke a shirye ya karbi gaskiya na kiristoci da kuma tsarkin zuciyarsu, wacce da jin gaskiya sai ta sauya. Shakka babu hawayen da za a zubar suna da kima ne idan sun kasance cikin sani da ilimi. Idan kuwa ba haka ba zai zama wani abu ne na motsin rai mai gushewa ba tare da zurfafawa ba. Wannan ayar tana tabbatar da cewa mutum bisa dabi’arsa yana son gaskiya idan har zuciyarsa tana da tsarki, kuma yana sane da gaskiya kamar yaron da ya ke haduwa da mahaifiyarsa bayan lokaci mai tsawo na rabuwa, zai zubar da hawaye idan ya ga gaskiya. Abubuwan da za mu koya daga wannan aya. 1-mutum yana kaiwa ga kamala ne a karkashin aiki da ilimi da kuma nuna kauna. Ya zamana zuciyarsa tana damfare da gaskiya kuma alokaci guda yana da kyakkyawan sani akanta. 2-Idan har zuciya ta kasance cikin shiri to mutum zai yi tafiyar shekaru dari cikin dare guda. Da dama daga cikin musulmin da su ka kasance a tare da ma’aiki ba su fahimci gaskiya kamar yadda ta ke ba, kuma imaninsu bai wuce harshe ba. Amma wasu kiristoci da su ka saurari ayoyin kur’ani sun kamu da shauki har ubangiji ya jinjina musu akan hakan. Wannan shi ne karshen shirinmu na wannan lokacin. Muna masu fatan Allah ya bamu dacewa mu san gaskiya da aiki da ita. Sai mun sake haduwa acikin wani shirin.

Suratul Ma'ida, Aya Ta 84-88 (Kashi Na 177)

Masu sauraro barkanu da sake saduwa da ku acikin wannan shirin. Kuma muna fatan za a kasance a tare da mu domin a ji ci gabansa daga inda mu ka tsaya a baya.

Yanzu sai a saurari ayoyi na 84 zuwa 86 a cikin wannan sura ta Ma’idah.

وَمَا لَنَا لاَ نُؤْمِنُ بِاللّهِ وَمَا جَاءنَا مِنَ الْحَقِّ وَنَطْمَعُ أَن يُدْخِلَنَا رَبَّنَا مَعَ الْقَوْمِ الصَّالِحِينَ{84} فَأَثَابَهُمُ اللّهُ بِمَا قَالُواْ جَنَّاتٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا وَذَلِكَ جَزَاء الْمُحْسِنِينَ{85} وَالَّذِينَ كَفَرُواْ وَكَذَّبُواْ بِآيَاتِنَا أُوْلَـئِكَ أَصْحَابُ الْجَحِيمِ{86}

“ Me zai hana mu yi imani da Allah da abinda ya riske mu na daga gaskiya, muna kuma fatan Ubangijinmu ya shigar da mu cikin mutane salihai. Saboda da abinda su ka fada sai Allah ya basu aljanna wacce koramu su ke gudana a karkashinta suna masu dawwama acikinta har abada. Hakan shi ne sakamakon masu kyautatawa. Wadanda su ka kafirce kuma su ka karyata ayoyinmu, su ne ‘yan wuta”

Kamar yadda mu ka fada a shirin da ya gabata, a lokacin da kiristoci su ka ji wasu ayoyi na suratu Maryam sun zubar da hawaye, sun kuma bada shaida akan gaskiyar kur'ani.

To ci gaban wancan bayani ya zo a cikin wannan ayar da cewa: Saboda yadda wadannan mutane su ke nutse wajen mika kai ga gaskiyar kur'ani suna fadawa kawunansu cewa: Me zai hana mu yin imani da wannan zancen na gaskiya wanda ya zo daga Allah? Ashe ba muna son shiga cikin salihan mutane ba saboda mu aljanna ba? Ubangiji madaukaki kuwa ya sakawa wannan furucin nasu da shigar da su aljannarsa madawwamiya, wacce nan ne wurin mutane masu aikin kwarai, waninsu kuwa ba zai shige ta ba. Abubuwan da za mu koya daga wadannan ayoyi. 1-Idan har mutum ya fahimci gaskiya to ba shi da wani uzuri da zai yi watsi da ita. 2-Yin imani da samuwar Ubangiji yana hade da yin imani da wahayin da ya saukar. Babu ma'ana a yi imani da Ubangiji ba tare da an yi imani da cewa shi ne mai shiryarwa ba. 3-Komawa ga lamiri yana bude hanyar karbar gaskiya da kuma yin tafiya akan tafarkin kamala wanda Ubangiji ya ke yabon masu yin hakan.

Yanzu kuma za mu saurari aya ta 87 acikin wannan sura ta Ma'idah.

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُواْ لاَ تُحَرِّمُواْ طَيِّبَاتِ مَا أَحَلَّ اللّهُ لَكُمْ وَلاَ تَعْتَدُواْ إِنَّ اللّهَ لاَ يُحِبُّ الْمُعْتَدِينَ{87}

"Ya ku wadanda ku ka bada gaskiya kada ku haramta abubuwa masu dadi da Allah ya halarta muku, kada ku ketare iyaka. Hakika Allah ba ya son masu ketare iyaka."

Ya zo acikin riwayoyin tarihi cewa: Wata rana manzon Allah-tsira da aminci a gare shi da iyalansa- ya bada labarin abinda zai faru a kiyama, wanda ya yi tasiri a cikin mutane har wasu su ka yi kuka su ka kuma sha alwashin cewa daga wannan lokacin ba za su sake cin abinci mai dadi ba. Su ka kuma haramtawa kawunansu hutu da jin dadi. Idan dare ya yi su kwana a tsaye suna salla, da rana kuma suna azumi. Sun kuma nesanci matansu na aure. Sun kuma yi rantsuwa akan cewa haka za su tafiyar da rayuwarsu ta duniya. A lokacin da manzon Allah ya ji labarin abinda ya ke faruwa sai ya tara mutane a masallaci ya fadi cewa: "Addaninmu (musulunci) ba addini ne na killace kai da nutsewa cikin ibada kadai ba. Ni kaina da na ke manzon Allah ban kauracewa gida da iyali ba, ina cin abinci a tare da su kuma ina saduwa da iyalina. Ku sani cewa duk wanda ya ke rayuwa sabanin yadda na ke rayuwa ba musulmi ba ne. Wannan ayar tana kira ne zuwa ga tafiyar da rayuwa daidai wa daidai ba tare da wuce gona da iri ba. Kamar yadda ubangiji ya haramta muku wasu abubuwa da aikata su baya halarta, haka nan kuma ya halarta muku wasu abubuwan da bai halarta ku haramta su ba. Mutumin da ya ke mumini yana mika wuya ne ga dukkanin abinda Ubangiji ya yi umarni da shi. Yana kuma tsayawa ne a cikin iyakokin da Allah ya tsaida shi da kuma aiki da dokokinsa. Ya halarta abinda Allah ya halara ya kuma haramta abinda Allah ya halarta. Wuce gona da iri baya tafiya kafada da kafada da imani. Abubuwan da za mu koya daga wannan aya. 1-Ubangiji ya ayyanawa muminai ci da shan abubuwa masu dadi, saboda haka yin watsi da su yana nufin kin yin furuci da nimi'omi da jin kai na Ubangiji. 2-Musulunci addini na fidhira wanda baya dacewa da yin watsi da amfani da dadadan abubuwa na fidhirar mutum. 3-A addini an hana wuce gona da iri da kuma sassauci, domin kuwa owane daya daga cikinsu yana nufin ketare iyakokin Allah. Haramta abinda ya ke halaliya ba ya halarta, haka nan kuma halarta abinda ya ke haramun. Allah ne mai halartawa da haramtawa ba mutum ba. 4- Tare da cewa baya halarta mu haramta abinda haramun, sai dai kada mu zama masu israfi wajen amfani da abinda ya ke halaliya.

Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 88 acikin wannan surata Ma'idah.

وَكُلُواْ مِمَّا رَزَقَكُمُ اللّهُ حَلاَلاً طَيِّباً وَاتَّقُواْ اللّهَ الَّذِيَ أَنتُم بِهِ مُؤْمِنُونَ{88}

"Kuma ku ci daga abinda mu ka azurtaku na halaliya mai dadi, ku ji tsoron Allah wanda ku ka bada gaskiya da shi."

Ci gaba ne na ayar da ta gabata wacce ta ke hana mutane haramtawa kawunansu abubuwa masu dadi kuma tsarkaka da Allah ya halarta. Tana cewa: Kada ku zaci cewa amfanuwa da abubuwa masu dadi na duniya ba karbabben abu ba ne ko kuma abin zargi ne. Allah ya halicci dukkanin ni'imomin duniya ne saboda ku, saboda haka ku amfana da su. Sai abu da ya ke mai muhimmanci shi ne cewa, a sa tsoron Allah aciki da kuma yin adalci wajen cin moriyar wannan ni'imar. Saboda haka ne Allah ya ke yin kiran muminai da su ci su kuma sha amma kada su yi israfi. A cikin wata ayar yana fadin cewa: " Ku ci, ku yi aikin kwarai." Wato ku ci sannan kuma ku ciyar. Abubuwan da za mu koya daga wannan aya. 1-Babu cin karo da juna tsakanin imani da kuma amfanuwa da ni'imomin duniya. Yana ma nufin yin amfani da ni'imomin ubangiji ne. 2-Tsoron Allah, baya nufin sakin duniya, yana nufin cin moriyarta ta ingatacciyar hanya domin gina lahira. A karshe muna rokon Allah da ya sanar damu addininsa da kuma tsayuwa akansa. Sai wani lokacin idan mun hadu a cikin wani shirin.

Suratul Ma'ida, Aya Ta 89-91 (Kashi Na 178)

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shiri na hannunka mai sanda, shirin da a cikinsa muke dubi a ayoyin alkur'ani mai girma domin su kasance mana jagora a rayuwa, sai a biyo mu don jin abin da shirinmu na yau ya kunsa.

A shirinmu na yau zamu fara ne da ambaton aya ta 89 da ke cikin suratul-Ma'idah kamar haka:-

لاَ يُؤَاخِذُكُمُ اللّهُ بِاللَّغْوِ فِي أَيْمَانِكُمْ وَلَـكِن يُؤَاخِذُكُم بِمَا عَقَّدتُّمُ الأَيْمَانَ فَكَفَّارَتُهُ إِطْعَامُ عَشَرَةِ مَسَاكِينَ مِنْ أَوْسَطِ مَا تُطْعِمُونَ أَهْلِيكُمْ أَوْ كِسْوَتُهُمْ أَوْ تَحْرِيرُ رَقَبَةٍ فَمَن لَّمْ يَجِدْ فَصِيَامُ ثَلاَثَةِ أَيَّامٍ ذَلِكَ كَفَّارَةُ أَيْمَانِكُمْ إِذَا حَلَفْتُمْ وَاحْفَظُواْ أَيْمَانَكُمْ كَذَلِكَ يُبَيِّنُ اللّهُ لَكُمْ آيَاتِهِ لَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ{89}

"Allah bã Ya kãmã ku sabõda yãsassun rantse-rantsenku, sai dai Yanã kãmã ku da abin da kuka kudurta rantsuwa a kansa. To, kaffãrarsa ita ce ciyar da miskĩnai gõma daga matsakaicin abin da kuke ciyar da iyãlanku, kõ tufãtar da su, kõ kuma 'yantã bayi. Sannan wanda bai sãmi {yin wadancan} ba, sai {ya yi} azumin kwãna uku. wannan shi ne kaffãrar rantsuwarku idan kun rantse. Kuma ku kiyãye rantse-rantsenku. Kamar haka ne Allah Yake bayyana muku ãyoyinsa, ko zaku dinga gõdewa".

A cikin shirin da ya gabata mun fahimci cewa wasu jama'ar musulmi bayan jin bayanin Manzon Allah dangane da al'amarin lahira, sai suka yi rantsuwar haramta wa kansu barci, cin abinci da kauracewa matansu, don haka sai Manzon Allah ya gargade su da cewa wannan hanya ta Musulunci ba hanya ce irin ta takurawa kai ba, da kauracewa duk wata rayuwar duniya wato ruhbaniyanci, sai wadannan jama'ar suke tambayar Manzon Allah cewa; to ya ya matsayin rantsuwar da muka yi? Don haka wannan aya ta sauko tana magana da su da cewa; kasancewar rantsuwar da kuka yi a kan lamari ne maras muhimmanci kuma yasasshe, saboda haka rantsuwarku bata da kima, don haka Allah ba zai kama ku da wannan rantsuwar ba, amma ku sani kada haka kawai ku yi rantsuwa domin zai zame dole ne ku aiwatar da abin da kuka yi rantsuwa a kai, sannan karya rantsuwar {wato rashin aiwatar da abin da kuka yi rantsuwa a kansa} baya ga cewa haramun ne, akwai kuma kaffarar karya rantsuwar.

Yana daga cikin abin da addinin Musulunci ya kebanta da shi, a duk lokacin da mutum ya aikata kuskure ko ya sabawa al'amarin addini sai a bukaci da ya kyautatawa marassa galihu daga cikin al'umma, don haka mutumin da ya karya rantsuwarsa dole ne ya ciyar da mabukata ko tufatar da su ko 'yantar da bawa, idan kuma duk ba zai iya hakan ba, to sai ya gudanar da azumi.

A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-

{1} Kasancewar Allah Madaukaki yana yafe kuskure da rantsuwar da mutane suka yi, to yana da kyau mu dauki matakin yafiya a tsakaninmu.

{2} Dokokin addinin Musulunci har a fagen ukuba suna kula da matsalar mabukata da marassa galihu.

{3} Hukuncin biyan kudi {a Musulunci} yana duba irin karfin mutum ne da matsayinsa, kuma ana bai wa mutum zabin irin kaffarar da zai yi kan laifin da ya gudanar.

{4} Kada mu yi rantsuwa da sunan Allah mai girma, idan kuma har muka yi rantsuwar, to dole ne mu aikata ko kuma mu gudanar da kaffara.

Shirinmu zai ci gaba ne ta hanyar ambaton aya ta 90 da ke cikin suratul-Ma'idah kamar haka:

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُواْ إِنَّمَا الْخَمْرُ وَالْمَيْسِرُ وَالأَنصَابُ وَالأَزْلاَمُ رِجْسٌ مِّنْ عَمَلِ الشَّيْطَانِ فَاجْتَنِبُوهُ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ{90}

"Ya ku wadanda suka yi ĩmãni! Iyaka dai giya da cãca da refu da kiban kuri'a, kazanta ne daga aikin shaidan, sai ku nĩsance su, ko zaku rabauta".

A lokacin da addinin Musulunci ya bayyana bautan gumaka, caca, shan giya sune muggan ayyukan da suka watsu a tsakanin al'umma, don haka kur'ani yake danganta wadannan al'amura da lokacin jahiliyar farko, amma a yau ma caca da shan giya sun watsu a wannan duniya, kuma bautan gumaka yana ci gaba da gudana cikin wani sabon salo, don haka sharadi ne na imani a nisanci duk wani aikin shaidan da duk wata dabi'a da bata dace ba, kuma addinin Musulunci ya haramta su. Kuma kasancewar shan giya tana kawar da hankali, caca kuma lamari ne da ke janyo tara kudi ta hanyar bulus da babu wani kokari na tunani da na jiki don haka addinin ya yi tsananin suka da hani a kansu.

A wancan lokacin Larabawa suna da tsananin alaka da wake-wake da shan giya, don haka a dauki matakin haramta su a lokaci guda, zai yi wuya su yi saurin amincewa da wannan hukuncin, sakamakon haka aka saukar da hukuncin haramcin shan giyar da hana caca cikin matakai hudu, kuma aka a cikin wannan aya aka sanya shan giya a sahu daya da bautan gunki.

A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-

{1} Hikimar haramta irin abubuwan da suke sanya maye, kokari ne na tsarkake mutane daga daudar ruhi da ta jiki.

{2} Sharadi ne na imani nisantar ayyukan shaidan, kuma ibada ita kadai bata isarwa har sai an kiyaye ciki daga haramun da biye wa sha'awa.

{3} Dukkanin koyarwar Musulunci kokari ne na kai mutum ga jin dadi da tabbata a kan gaskiya. Lalle wasu daga cikinsu muna ganinsu da wahala amma wadannan al'amura lamari ne da iyaye zasu dauki matakin tarbiyantar da yaransu a kai.

Yanzu kuma zamu saurari aya ta 91 da ke cikin suratul-Ma'idah kamar haka:-

إِنَّمَا يُرِيدُ الشَّيْطَانُ أَن يُوقِعَ بَيْنَكُمُ الْعَدَاوَةَ وَالْبَغْضَاء فِي الْخَمْرِ وَالْمَيْسِرِ وَيَصُدَّكُمْ عَن ذِكْرِ اللّهِ وَعَنِ الصَّلاَةِ فَهَلْ أَنتُم مُّنتَهُونَ{91}

"Iyaka dai Shaidan yanã nufin ya jefa adãwa da kiyayya a tsakãninku ta hanyar giya da cãca, kuma ya kange ku daga ambaton Allah da gudanar da sallah. To, shin, ku mãsu hanuwa ne?".

A cikin ayar da ta gabata Allah Madaukaki ya bayyana caca da shan giya daga cikin ayyukan shaidan, a wannan ayar kuwa yana bayyana cewa ne; ta hanyar wadannan abubuwa biyu shaidan zai raba alakar zumuncin da ke mutane da cusa kiyayya da gaba a tsakaninsu, haka nan kuma zai yanke alakar da ke tsakaninku da Allah Madaukaki tare da mantar da ku ambaton Allah da gudanar da salla.

Har ila yau shan giya tana gadar da cututtuka ta jiki da ta kwakwalwa, amma alkur'ani da yake bayani kan hikimar haramcinta sai ya takaita da ambaton al'amura biyu; matsalar cutuwa a halin zamantakewa da ta ruhi.

A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-

{1} Duk mai haifar da matsalar kiyayya da gaba a tsakanin mutane, to shaidan ne koda kuwa a ido ana masa ganin mutum.

{2} Salla ita ce babbar alama ce ta ambaton Allah da tuna shi, don haka duk abin da zai gafalar da mu daga ambaton Allah al'amari ne marassa kyau da dacewa kuma dole ne mu nisance shi, koda kuwa misalin kasuwanci ne ko karatu.

To a nan ne shirin na mu ya zo karshe, sai kuma a gamo na gaba. Wassalamu alaikum warahmatullah.

Suratul Ma'ida, Aya Ta 92-94 (Kashi Na 179)

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shiri na hannunka mai sanda, shirin da a cikinsa muke dubi a ayoyin alkur'ani mai girma domin su kasance mana jagora a rayuwa, sai a biyo mu don jin abin da shirinmu na yau ya kunsa.

A shirinmu na yau zamu fara ne da ambaton aya ta 92 da ke cikin suratul-Ma'idah kamar haka:-

وَأَطِيعُواْ اللّهَ وَأَطِيعُواْ الرَّسُولَ وَاحْذَرُواْ فَإِن تَوَلَّيْتُمْ فَاعْلَمُواْ أَنَّمَا عَلَى رَسُولِنَا الْبَلاَغُ الْمُبِينُ{92}

"Ku yi dã'a ga Allah, kuma ku yi dã'a ga Manzo, kuma ku kiyãye. To, idan kun jũya baya, to, ku sani abin da kawai yake kan ManzonMu, isarwa ce bayyananniya".

Muna tune da cewa a ayoyin da muka ambata a shirin da ya gabata sun yi bayanin wasu daga cikin umurnin Allah Madaukaki ne dangane da nisantar caca da shan giya. Don haka a cikin wannan aya Allah Madaukaki yana bayyana cewa ne: Yin biyayya ga wadannan umurnin Allah amfani ne da zai koma gare ku, kuma ku ji tsoron mummunar sakamakon irin wadannan maggan ayyuka, sannan kada ku taba tsammanin yin tawaye ga hukuncin Allah wata cutarwa ce ga Allah da Manzonsa, iyaka dai aikin da ya hau kan Manzon Allah shi ne isar da sakon Allah, kuma gudanar da umurnin Allah da ya rataya a wuyarku ba amfani ne da zai koma kan Manzon Allah ba, sannan rashin gudanar da umurnin ba zai cutar da shi ba.

A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-

{1} Aikin Manzanni shi ne isar da sako, ba wai tilasta mutane kan yin biyayya ba, iyaka dai Manzanni su fadakar da mutane ne, su kuma mutane suke da 'yancin zabin hanyar da zata tsiratar da su.

{2} Biyayya ga Allah tana tare ne da biyayya ga Manzonsa, don haka baya ga dokokin da suka zo cikin alkur'ani, dole ne mu bi koyarwar Manzon Allah da suka zo mana ta hanyar sunnarsa.

Shirinmu zai ci gaba ne ta hanyar ambaton aya ta 93 da ke cikin suratul-Ma'idah kamar haka:-

لَيْسَ عَلَى الَّذِينَ آمَنُواْ وَعَمِلُواْ الصَّالِحَاتِ جُنَاحٌ فِيمَا طَعِمُواْ إِذَا مَا اتَّقَواْ وَّآمَنُواْ وَعَمِلُواْ الصَّالِحَاتِ ثُمَّ اتَّقَواْ وَّآمَنُواْ ثُمَّ اتَّقَواْ وَّأَحْسَنُواْ وَاللّهُ يُحِبُّ الْمُحْسِنِينَ{93}

"Bãbu laifi a kan wadanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan kwarai, a cikin abin da suka ci, idan sun ji tsoron Allah kuma suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan kwarai, sannan suka ji tsoron Allah kuma suka yi ĩmãni, sannan kuma suka ji tsoron Allah kuma suka kyautata. Kuma Allah Yana son mãsu kyautatãwa".

Kamar yadda ya zo cikin ruwaya: Bayan saukar ayoyin haramta shan giya wasu daga cikin musulmai sun yi tambaya kan wadanda suka sha giya kafin saukar ayoyin, sai wannan aya ta sauka a matsayin amsar tambayarsu tana cewa: Abin da ya faru kafin saukar hukunci babu ukuba a kansa, amma da sharadin ba za a sake kusantar abin da aka haramta ba, don haka sai a yi riko da tsoron Allah, kuma maimakon caca da shan giya sai a gudanar da ayyuka masu kyau da suka dace, sannan a tabbata a kansu.

A cikin wannan aya kalmomin tsoron Allah da imani sun zo har sau uku lamarin da ke nuni da cewa suna da muhimmanci a bangarorin rayuwa saboda kudirta imani a zuciya da aiwatar da tsoron Allah a gabobi da ayyuka lamari ne da ke kai mutum ga samun amincin duniya da lahira.

A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-

{1} Kyautatawa ga mutane tana daga cikin matakan imani mai girma, kuma tana kai mutum ga samun kusanci a wajen Allah.

{2} Kudirta imani shi kadai baya isarwar har sai an rubanya shi da gudanar da aiki, don haka imani shi ne gudanar da kyakkyawan aiki da nisantar duk wani abu mummuna maras kyau.

{3} Imani na wani lokaci da yake yankewa baya amfani, don haka wanzuwar imani a dukkanin tsawon rayuwa da aiwatar da shi a dukkanin bangarorin rayuwa shi ne samun babban rabo.

Yanzu kuma zamu saurari aya ta 94 da ke cikin suratul-Ma'idah kamar haka:-

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُواْ لَيَبْلُوَنَّكُمُ اللّهُ بِشَيْءٍ مِّنَ الصَّيْدِ تَنَالُهُ أَيْدِيكُمْ وَرِمَاحُكُمْ لِيَعْلَمَ اللّهُ مَن يَخَافُهُ بِالْغَيْبِ فَمَنِ اعْتَدَى بَعْدَ ذَلِكَ فَلَهُ عَذَابٌ أَلِيمٌ{94}

"Yã ku wadanda suka yi ĩmãni! Lalle ne Allah zai jarrabe ku da wani abu daga farauta, {wanda} hannuwanku da mãsunku za su iya farautarsa, dõmin Allah Ya san wanda yake tsoron Sa a fake. To, wanda ya karya doka {ya yi farauta} a bãyan wannan, to, yanã da azãba mai radadi".

Wannan aya da kuma ayoyin da zasu biyo bayanta suna magana ne kan hukunce- hukuncen hajji da mutumin da ya daura haramin aikin na hajji ya shiga birnin Makkah. A cikin ranakun hajji mahajjaci bayan daura harami baya da hakkin gudanar da farauta, abin mamaki a wannan ranakun a wasu lokuta mutum zai ga dabbobin farauta sun kusato shi wanda cikin sauki zai iya kame su da hannunsa, amma hakan yana daga cikin jarabawar Allah domin ganin wane ne zai mika kai ga umurninsa, kuma wane ne zai biye wa son ransa.

A cikin kur'ani za a ga misalai na jarabawar Allah, mafi muhimmanci daga cikinsu shi ne jaraba Adam da Hauwa'u da aka yi a cikin aljanna, sai dai abin bakin ciki sun fadi a wannan jarabawar ta hanyar cin bishiriyar da aka hane su, amma abin lura a nan shi ne lalle Allah yana sane da duk wani aikinmu a cikin iliminsa na gaibu, jaraba mu da yake yi, ba don ya nemi sani da fahimtar irin ayyukan da zamu gabatar ba ne, iyaka dai dalilin jaraba mu shi ne domin ya bamu damar gina kanmu ta hanyar irin baiwar da ya bamu, kuma mu fahimci kanmu domin kada mu yi da'awar aiki fiye da matsayinmu, sannan duk ayyukan da mutun ya gudanar a karkashin jarabawar da aka masa Allah Madaukaki zai saka masa da alheri ko ukuba, saboda ukuba ko lada da ta ake sakawa mutum da ita maimakon aikinsa da ya aikata ne da kansa, ba wai Allah ke tilasta mutum a kan aiki ba sannan ya azabtar da shi ko ya ba shi lada a kai. Kamar haka ne yake gudana a rayuwarmu ta yau da kullum, inda mutumin da yake sana'a haka kawai ba mu ba shi ladar wani aiki har sai ya gudanar mana da aikin da muke so, sannan ya cancanci lada daga gare mu.

Koma dai yaya lamarin yake muminai suna da'awar su masu biyayya ne ga umurnin Allah, amma wannan da'awa bata tabbata matukar ba su shiga cikin jarabawa ba, idan har Allah ya yi umurni da aikata wani abu, kuma wannan umurnin ya yi hannun riga da bukata ta, amma duk da haka na amince da umurnin, to a nan ne za a fahimci lalle na mika wuya ga Allah Madaukaki, ba wai kawai kauracewa shan giya da sauran abubuwan da aka haramta shan su ba. Kai dole ne ma abubuwan da suke halal mutum ya kaurace musu idan bukatar hakan ya taso domin ya kasance ya mika kai ga Allah, ba ga son ransa da sha'awarsa ba.

A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-

{1} Jarabawa daya ce daga cikin sunnonin Allah tabbatattu da yake jaraba dukkanin mutane da ita musamman muminai da suke da'awar imani.

{2} Hakikanin tsoron Allah da imani al'amari ne na boye, ba kawai rayuwa ce ta zahiri ba da mutum zai kaurace wa aikata laifi a idon jama'a.

{3} A lokacin aikin hajji Allah Madaukaki ya hana mutum aikata abubuwa da dama da suke halal ne gare shi domin ya tarbiyantar da ruhinsa kan mika wuya ga al'amarin Allah.

To a nan ne shirin na mu ya zo karshe, sai kuma a gamo na gaba. Wassalamu alaikum warahmatullah.

Suratul Ma'ida, Aya Ta 95-97 (Kashi Na 180)

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shiri na hannunka mai sanda, shirin da a cikinsa muke dubi a ayoyin alkur'ani mai girma domin su kasance mana jagora a rayuwa, sai a biyo mu don jin abin da shirinmu na yau ya kunsa.

A shirinmu na yau zamu fara ne da ambaton aya ta 95 da ke cikin suratul-Ma'idah kamar haka:-

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُواْ لاَ تَقْتُلُواْ الصَّيْدَ وَأَنتُمْ حُرُمٌ وَمَن قَتَلَهُ مِنكُم مُّتَعَمِّداً فَجَزَاء مِّثْلُ مَا قَتَلَ مِنَ النَّعَمِ يَحْكُمُ بِهِ ذَوَا عَدْلٍ مِّنكُمْ هَدْياً بَالِغَ الْكَعْبَةِ أَوْ كَفَّارَةٌ طَعَامُ مَسَاكِينَ أَو عَدْلُ ذَلِكَ صِيَاماً لِّيَذُوقَ وَبَالَ أَمْرِهِ عَفَا اللّهُ عَمَّا سَلَف وَمَنْ عَادَ فَيَنتَقِمُ اللّهُ مِنْهُ وَاللّهُ عَزِيزٌ ذُو انْتِقَامٍ{95}

"Yã ku wadanda suka yi ĩmãni! Kada ku kashe abin farauta alhãli kunã {cikin} harami. Kuma wanda ya kashe shi daga cikinku da gangan, to ramuwar gwargwadon abin da ya kashe na daga dabbõbi {ya wajaba a kansa} ma'abuta ãdalci biyu ne daga cikinku za su yi masa hukunci da shi, kuma ya zama hadaya mai isa ga Ka'aba, ko kuma ya yi kaffãrar ci da miskĩnai ko kuma ya yi azumi a matsayinsa dõmin ya dandani sakamakon aikinsa. Allah Yã yafe laifi daga abin da ya gabãta. Kuma wanda ya kõma, to, Allah zai yi azãbar rãmuwa daga gare shi, kuma Allah Mabuwãyi ne, ma'abũcin azabãr rãmuwa.

A shirin da ya gabata mun bayyana cewa: Allah Madaukaki ya gabatar da wasu umurni kan wanda ya tafi aikin hajji wanda umurnin suke matsayin jarrabawa ga mahajjacin da ya daura harami, daga cikin umurnin akwai haramcin gudanar da farautar dabbobi; a cikin wannan ayar kuwa baya ga jaddada umurnin an kuma kara da bayanin hukuncin mahajjacin da ya gudanar da farautar da gangan tare da bayyana irin ukubar da ke kansa, inda zai gabatar da hadayar dabba misalin dabbar da ya yi farauta kuma a wajen dakin Allah na Ka'aba sannan ya gabatar da namar hadayar ga mabukata da marassa galihu, idan kuma mutum baya da ikon gabatar da hadaya, to sai ya ciyar da mabukata guda sittin ta hanyar kosar da su, haka nan idan baya da ikon ciyarwa saboda matsalar tattalin arziki, to sai ya gudanar da azumin kwanaki sittin don jin irin halin yunwa da mabukata ke dandanawa kuma hakan ya zame ukubar abin da ya aikata na rashin dacewa.

A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-

{1} A lokacin harami ba kawai mutum ba har ma dabbobi suna cikin aminci, kuma a lokacin aminci na hakika ne ke lullube rayuwa.

{2} Babban aikin laifi mafi hatsari shi ne yin tawaye ga umurnin Allah da gangan wanda hakan yana janyo tsananin ukuba.

{3} A karkashin dokokin addinin Musulunci mafi yawan ukuba ta kudi amfaninta ke komawa ga mabukata da marassa galihu, yayin da a mafi yawan dokokin da dan Adam ke kirkirowa ukubar kudi amfaninta ke komawa ga gwamnati.

Shirinmu zai ci gaba ne ta hanyar ambaton aya ta 96 da ke cikin suratul-Ma'idah kamar haka:-

أُحِلَّ لَكُمْ صَيْدُ الْبَحْرِ وَطَعَامُهُ مَتَاعاً لَّكُمْ وَلِلسَّيَّارَةِ وَحُرِّمَ عَلَيْكُمْ صَيْدُ الْبَرِّ مَا دُمْتُمْ حُرُماً وَاتَّقُواْ اللّهَ الَّذِيَ إِلَيْهِ تُحْشَرُونَ{96}

"An halatta muku farautar ruwa da abincinsa dõmin jin dãdi a gare ku, da kuma matafiya. Kuma an haramta muku farautar tudu matukar kuna cikin harami. Kuma ku ji tsoron Allah wanda zuwa gare Shi ne za a tattara ku".

A ayar da ta gabata an yi bayanin haramcin gudanar da farautar dabbobin da suke rayuwa a kan doron kasa yayin da a cikin wannan ayar kuma ake bayyana cewa; Allah ya halatta muku farautar dabbobin ruwa da abincin da ke cikinsa, wato ba a toshe muku dukkanin hanyoyin samun abinci ba.

Hikimar irin wannan umurni na Allah, wata jarabawa ce da ke tantance karfin imani da tsoron Allah da mutum ke dauke da shi don sanin mutanen da suka mika kansu ga umurnin Allah da kuma wadanda suka mika kai ga son ransu, don haka Allah ya bude hanya guda ya toshe guda.

A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-

{1} Halittun cikin ruwa musamman wadanda ba su rayuwa a wajen ruwa an daba dama ga dukkanin mutane su yi amfani da su.

{2} Gudanar da farautar dabbobin ruwa domin amfani da su a matsayin abinci halal ne {amma kada farautar ta kasance domin sharholiya ce wato mutum yana gudanar da farautar dabbar ce don jin dadin daukan ranta}.

{3} Sanin cewa akwai ranar kiyama da tsayiwa a gaban mahalicci don gudanar da shari'a yana daga cikin dalilan da suke katange mutum daga aikata laifi da yin tawaye ga umurnin Allah.

Yanzu kuma zamu saurari aya ta 97 da ke cikin suratul-Ma'idah kamar haka:-

جَعَلَ اللّهُ الْكَعْبَةَ الْبَيْتَ الْحَرَامَ قِيَاماً لِّلنَّاسِ وَالشَّهْرَ الْحَرَامَ وَالْهَدْيَ وَالْقَلاَئِدَ ذَلِكَ لِتَعْلَمُواْ أَنَّ اللّهَ يَعْلَمُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الأَرْضِ وَأَنَّ اللّهَ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمٌ{97}

"Allah Ya sanya Ka'aba daki ne mai alfarma madogarar addini ga mutane, kuma Yã sanya watã mai alfarma da hadaya da kuma {hadaya} mai rãtaye. Wannan kuwa don ku sani cewa hakika Allah Yã san abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin kassai, kuma lalle Allah ga dukkan kõmai Masani ne".

A cikin ayoyin da suka gabata an tabo wasu ne daga cikin hukunce-hukuncen aikin hajji, a wannan ayar kuwa an tabo tushen aikin hajjin ne wato dakin Ka'abah, inda aka bayyana matsayinsa da cewa: Allah Madaukaki ya sanya dakin na Ka'abah ne a matsayin cibiyar aminci, ibada, hadin kai da sani, inda wadannan abubuwa suke ginshikin rayuwar mutane da ma al'umma baki daya.

Ka'abah daki ne da girmama shi da kare matsayinsa yake wajibi musamman a lokacin aikin hajji da yake cikin watanni masu hurumi da aka haramta yaki da zubar da jinin bil-Adama a ciki, kuma ba kawai dakin na Ka'abah da watan aikin hajji ne abin girmamawa ba, har ma dabbobin da aka kebance domin hadayar aikin hajji suna da nasu matsayin saboda alakar da suke da shi da aikin hajji da mahajjata da suka ziyarci dakin Allah mai alfarma.

Har ila yau taruwar miliyoyin musulmai a dakin Ka'abah ba tare da nuna wani bambanci ko daukaka a tsakaninsu ba, da kuma hana jayayya na lafazi da duk wani rikici wani babban dalili ne na daukakan addinin Musulunci. Sannan zurfafa tunani a al'amarin aikin hajji za a fahimci cewa lalle umurni ne na mai zurfin ilimi da baya da iyaka wato Allah Madaukaki da iliminsa ya game dukkan komai. Tabbas ilimin dan Adam da ke da iyaka ba zai taba iya tunanin bada umurnin tara irin wannan babban taro na al'ummomi da tattaro zukatansu waje guda ba.

A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-

{1} Wasu wajaje da zamani suna da matsayi da daukaka a Musulunci wanda kare su yake matsayin ginshikin tabbatar al'ummomi.

{2} Masallaci da mayanka -da suke matsayin alamar ibada- wajaje ne da suke kare addini da rayuwar mutane, don haka Allah ya sanya su a matsayi daya a lokacin aikin hajji.

To a nan ne shirin na mu ya zo karshe, sai kuma a gamo na gaba. Wassalamu alaikum warahmatullah.

Suratul Ma'ida, Aya Ta 98-102 (Kashi Na 181)

Masu saurare assalamu alaikum,barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shiri na hannunka mai sanda, shirin da a cikinsa muke dubi a ayoyin alkur'ani mai girma domin su kasance mana jagora a rayuwa, sai a biyo mu don jin abin da shirinmu na yau ya kunsa.

A shirinmu na yau zamu fara ne da ambaton aya ta 98 zuwa ta 99 da suke cikin suratul-Ma'idah kamar haka:-

اعْلَمُواْ أَنَّ اللّهَ شَدِيدُ الْعِقَابِ وَأَنَّ اللّهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ{98} مَّا عَلَى الرَّسُولِ إِلاَّ الْبَلاَغُ وَاللّهُ يَعْلَمُ مَا تُبْدُونَ وَمَا تَكْتُمُونَ{99}

"Ku sani cewa lalle Allah Mai tsananin ukuba ne, kuma lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin kai. Bãbu abin da yake kan Manzo, sai isar da aike kawai, kuma Allah Yanã sane da abin da kuke bayyanãwa da abin da kuke bõyewa".

Wasu mutane suna tsammanin hukunce-hukuncen da Manzon Allah yake bayyana musu dangane da al'amuran addini ra'ayoyinsa ne kawai, kuma a duk lokacin da ya ga dama sai ya bayyana cewa akwai sakamako mai kyau ga wanda ya aikata da gargadin azaba kan duk wanda ya saba. Wadannan ayoyi suna mai da martani ne ga irin wannan mummunar tunani da cewa:

Da farko aikin Manzon Allah shi ne isar da sakon hukunce-hukuncen shari'a da suka zo daga wajen Allah, daga bangarensa babu abin da yake karawa ko ragewa.

Na biyu kyakkyawar sakamako da azaba dukkaninsu suna hannun Allah ne, babu hannun Manzon Allah a ciki. Don haka duk wanda ya bi umurnin Allah, to zai samu kyakkyawar sakamako, kuma duk wanda ya bijirewa umurnin Allah, to zai tarar da azabarsa.

Baya ga haka; Manzon Allah baya tilasta kowa a kan karbar sakon addini, kuma bai taba tilasta wani ba kan amincewa da sakon shiriyar da ya zo da shi, saboda imani al'amari ne na boye, Allah ne kawai ke sanin mai dauke da imani na gaskiya da wanda ya boye kafirci amma a zahiri yake bayyana imani.

A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-

{1} Dole ne mumini ya kasance tsakanin tsammani da tsoro, wato tsoron azabar da zai tarar kan kuskuren da ya aikata da tsammanin samun rahama da gafara daga wajen Allah.

{2} Aikin da ya hau kan Manzon Allah shi ne isar da sakon addini, ba tilastawa mutane karbar sakon addinin ba.

{3} Boye abu ko bayyana shi a wajen Allah duk daya suke, don haka munafunci da riya ba su da wani amfani.

Shirinmu zai ci gaba ne ta hanyar ambaton aya ta 100 da ke cikin suratul-Ma'idah kamar haka:-

قُل لاَّ يَسْتَوِي الْخَبِيثُ وَالطَّيِّبُ وَلَوْ أَعْجَبَكَ كَثْرَةُ الْخَبِيثِ فَاتَّقُواْ اللّهَ يَا أُوْلِي الأَلْبَابِ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ{100}

"Ka ce: "Mummuna da mai kyau bã su daidaita, kuma kõ dã yawan mummuan yã bã ka sha'awa. Sabõda haka sai ku ji tsoron Allah yã ma'abuta hankula don ko kwa rabauta".

Daga cikin abubuwan da suke raunana muminai da girgiza imaninsu dangane da addini da akida akwai batun cewa kafirai sun fi musulmai yawa a tsawon tarihi, to wannan aya tana magana da Manzon Allah da cewa: ba ta hanyar yawa ba ce ake fahimtar gaskiyar abu; idan da ace mafi yawan wasu al'umma zasu bijire wa hanyar addini da Annabawa, hakan ba zai taba sanya wa gaskiyar addini da Annabawar ta kasance ta fadi ba, saboda gaskiyarsu ta samo asali ce daga wajen Allah, kuma hankalin dan Adam yana kai ga gano kyaun abin da suke kira a kai, don haka Allah Madaukaki a karshen wannan aya yake magana da masu hankali da cewa: Idan har kuna son samun rabauta, to dole ne ku dauki matakin mika wuya ga Allah domin ya kasance muku jagora wajen bambance tsakanin gaskiya da karya.

Tabbas mummuna da mai kyau, dauda da tsarki, ba su daidaita, idan mafi yawan mutane suka rungumi mummunan aiki; shin zaku bi wannan hanyar saboda yawan masu binta, ku yi watsi da hanyar gaskiya mafi tsabta?. Misali idan a daki akwai mutane biyar, sai hudu daga cikinsu suka zabi su kunna taba sigari domin gurbata iskar dakin da hayaki, amma sauran mutum guda baya bukatar shan tabar, kuma yana neman shakar iska mai kyau, a nan wane ne daga cikin bangarorin biyu yake da hakki? Shin a nan sai a ce dole ne mutum guda da baya shan taba ya fice daga cikin dakin domin shakar iska mai kyau saboda shi daya ne tilo baya shan taba, amma sauran mutanen hudu su ci gaba da zama a dakin su gurbata iska da hayakin taba saboda sune mafiya rinjaye?.

A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-

{1} Yawan mabiya baya zama dalilin cewa abin da suke kai shi ne gaskiya, don haka tunanin masu cewa: Mutum a kullum ya kasance tare da mafiya rinjaye, tunani ne da sabawa hankali kuma ya yi hannun riga da koyarwar kur'ani.

{2} Dukkanin mutane suna da hankali amma da dama daga cikinsu ba su amfani da hankalin, suna gudanar da rayuwarsu ce kawai a kan tsari na al'ada da zamantakewar al'umma da kuma yana yin da suka samu kansu a ciki, don haka koda sune mafiya rinjaye dabi'unsu ba zai taba zama dalili ba wajen koyi.

{3} Bin hanyar gaskiya da samun rabauta dole ne su kasance a kan asasi na imani da tsoron Allah baya ga amfani da hankali da zurfin tunani domin mutum ya kasance yana tafiya ce a kan tsari na Allah tare da bambance tsakanin gaskiya da bata.

Yanzu kuma zamu saurari aya ta 101 zuwa 102 da suke cikin suratul-Ma'idah kamar haka:-

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُواْ لاَ تَسْأَلُواْ عَنْ أَشْيَاء إِن تُبْدَ لَكُمْ تَسُؤْكُمْ وَإِن تَسْأَلُواْ عَنْهَا حِينَ يُنَزَّلُ الْقُرْآنُ تُبْدَ لَكُمْ عَفَا اللّهُ عَنْهَا وَاللّهُ غَفُورٌ حَلِيمٌ{101} قَدْ سَأَلَهَا قَوْمٌ مِّن قَبْلِكُمْ ثُمَّ أَصْبَحُواْ بِهَا كَافِرِينَ{102}

"Yã ku wadanda suka yi ĩmãni! Kada ku yi tambaya game da wasu abubuwa wanda idan an bayyana muku (hukuncinsu) su bãta muku rai. Kuma idan kuka yi tambaya game da su a lõkacin da ake saukar da Alkur'ãni, to zã a bayyana muku su; Allah Yã yi ahuwã game da su, Allah Mai gãfara ne, Mai hakuri. Hakika wasu mutãne a gabaninku sun yi tambaya game da irinsu, sannan kuma suka zama masu kãfircewa da su".

Duk da kasancewar tambaya mabudi ce ta ilimi, amma wasu tambayoyin ba kawai ba su da amfani ba ne har ma suna haifar da matsaloli a tsakanin al'umma, misali kan haka; Idan wata kasa tana cikin yaki, sai aka tambayi gwamnatin yawan alkama da ta tanada? Tabbas amsar wannan tambaya zata janyo karancin gurasa da ake sarrafa wa a wannan kasar {saboda tsoron karewarta} kuma hakan zai kara matsin lambar makiya a kanta {saboda an san iyakan abincin da ta tanada}. Kamar haka matsalar take a al'amarin addini, don haka Manzon Allah yake bayyana wa muminai cewa; wasu tambayoyin zasu janyo wasiwasi ne kawai da kokwanto, kuma mafi yawan amsoshinsu su janyo bullar matsaloli a tsakanin al'umma.

Baya ga haka manufar gabatar da wasu tambayoyin tare da maimaita su, kokari ne kawai na neman gujewa hukuncin shari'a; kamar haka ne a zamanin Annabi Musa {a.s} da aka umurci Bani-Isra'ila kan su yanka saniya, saboda hakan ya yi musu nauyi, sai suka bukaci da a bayyana musu launinta, yana yinta da shekarunta, don haka a lokacin da aka fayyace musu amsar tambayoyinsu, sai suka kai ga matsayin da samun saniya irin wadda aka siffanta musu mafi zama matsala gare su.

Ya zo cikin ruwayoyi cewa; Manzon Allah yana bayanin hukunce-hukuncen aikin hajji ga mutane, sai wani mutum ya yi tambayar cewa: Shin a kowace shekara ce aikin hajji yake wajibi ko kuma sau daya ne kawai a tsawon rayuwa? Sai Manzon Allah ya yi shiru bai amsa masa tambayar ba. Sai mutumin nan ya yi ta maimaita gabatar da wannan tambayar, har Manzon Allah ya amsa masa da cewa: ko don mene ne ka dage da gabatar da wannan tambaya? Idan har wajibi ne gudanar da aikin hajji a kowace shekara, ai da tuni na bayyana.

A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-

{1} Ba dole ba ne sanin komai, kuma dole ba ne sai mun nemi ilimin komai, kamar yadda ba dole ba ne sanin al'amuran da saninsu zai janyo kunci da matsaloli a harkokin al'umma.

{2} Rashin wajabta wa mutane sanin duk wani rabe-raben hukunce-hukunce shari'a, yana daga cikin rahama da jin kai na Allah ga al'umma, haka nan rashin bayanin hakikanin wasu al'amura masu zurfi da saninsu ko fahimtarsu ya haura tunanin mutane wanda saninsu zai iya sanadiyyar wurga su cikin inkarin gaskiya da kafirci.

To a nan ne shirin na mu ya zo karshe, sai kuma a gamo na gaba. Wassalamu alaikum warahmatullah.

Suratul Ma'ida, Aya Ta 103-105 (Kashi Na 182)

Jama'a masu saurare Assalamu alaikum barkarku da sake saduwa da mu a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda ,inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki ,tare da yin bayani gwargwadon iko kan abin da suke koyar da mu ,tare da yi mana hannunka mai sanda a cikin lamurran rayuwa da zamantakewa.Amma kafin mu shiga cikin shirin gadan gadan ga abin da aka yi mana tanadi a kan inji.

To sai a saurari karatun aya ta 103 a cikin suratun Ma'idah kamar haka:

مَا جَعَلَ اللّهُ مِن بَحِيرَةٍ وَلاَ سَآئِبَةٍ وَلاَ وَصِيلَةٍ وَلاَ حَامٍ وَلَـكِنَّ الَّذِينَ كَفَرُواْ يَفْتَرُونَ عَلَى اللّهِ الْكَذِبَ وَأَكْثَرُهُمْ لاَ يَعْقِلُونَ{103}

Kuma Allah bai sanya wata bahĩra ba, kuma haka sã'iba, kuma haka wasĩla, kuma haka hãmi, amma wadanda suka kãfirta, su suke kirkira karya ga Allah, kuma mafi yawansu bã su hankalta.

Ya zo a cikin tarihin larabawa mushrikai sun haramta cin wani nauyin dabbobi da kuma suke danganta hakan da hukumcin Allah,kamar yadda a yau muke gani da jin abubuwan da suke wakana a wasu kasashe kamar A Indiya inda mabiya addinin Hindu suke girmama saniya da daukaka ta da hana cin namanta da kuma muzguna mata da haramta duk wani abu na kuntatawa wannan dabba kuma ba a cin namanta kuma mafi muni suna danganta hakan da addinin Allah.To ya kamata su sani muma mu sani halaliya da haramci ba ya hannu da ikon mutum da zai iya rika fitar da hukumci yadda ya ga dama, abin sani mutum da dabbobi dukansu Allah ne ya halicce mu saboda haka Shi ne ke da ikon zartar da hukumcin halaliya da haramci. Hasali ma amfanuwa da dabi'a da ya hada da tudde da tsirre da dabbobi halaliya ne kuma ya dace face abubuwan da hukumcin Allah ya haramta karkashin addininsa kuma abin lura akwai camfe camfe da ake dangantawa da addinin Allah don batar da mutane sai ayi takatsantsan.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda biyu akalla:

1-Kirkiro da dokoki da yarjejeniyoyi na zamantakewa da suka sabawa hukumce –hukumce da dokokin Allah wani nauyi ne na bidi'a da kuma hakan alama ce ta kafirci domin kafirci ba wai kawai kin amincewa da Allah ne ba kirkiro bidi'a da gangam kafirci ne.

2- Barin dabbobi ba tare da amfani ba bai dace ba

Sai a saurari karatun aya ta 104 a cikin suratul Ma'ida kamar haka:

وَإِذَا قِيلَ لَهُمْ تَعَالَوْاْ إِلَى مَا أَنزَلَ اللّهُ وَإِلَى الرَّسُولِ قَالُواْ حَسْبُنَا مَا وَجَدْنَا عَلَيْهِ آبَاءنَا أَوَلَوْ كَانَ آبَاؤُهُمْ لاَ يَعْلَمُونَ شَيْئاً وَلاَ يَهْتَدُونَ{104}

Kuma idan aka ce musu: "Ku zo zuwa ga abin da Allah Ya saukar, kuma zuwa ga Manzo," sai su ce: "Mai isarmu shi ne abin da muka iske ubanninmu a kansa." Shin, kuma kõ dã ubanninsu sun kasance bã su sanin kõme kuma bã su shiryuwa?

Wannan aya ci gaban ayar da ta gabata ce ta da ke galgadinmu cewa duk abin da aka danganta da mushrikai na camfe-camfe da kirkiro karya da dangantawa da Allah mu nisanta da su da aiki da su , mu koma ga hukumcin Allah da ma'aikinsa domin su Mushrikai a shirye suke su yi amfani da duk wata dama domin kare manufarsu kamar yadda a duk lokacin da Ma'aikin Allah ya gabatar masu da dalili na hankali karara sai su ce: ai uwaye da kakannunmu sun kasance suna aikatawa ma'ana sun yi gado daga kakannunsu muma mun kasance muna aikatawa.Alkur'ani ya maida masu da amsa cewa; shin duk sunnar iyaye da kakannu gaskiya ce da ku ke yin riko da ita to ku sani ayyukan da kakannnunku suka aikata babu wani hankali da ya amince da su.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda biyu akalla:

1-Tushe da karshe yana ga tafarkin Allah ba wai camfe-camfen wadanda suka gabata masu ayyukan riya da kafirci.

2-A kullum mu yi aiki da ilimi da shiriya ba dogaro da tushe ko asali na girman kai ba.

Sai kuma za mu ci gaba da sauraren aya ta 105 a cikin wannan sura ta Ma'idah:

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُواْ عَلَيْكُمْ أَنفُسَكُمْ لاَ يَضُرُّكُم مَّن ضَلَّ إِذَا اهْتَدَيْتُمْ إِلَى اللّهِ مَرْجِعُكُمْ جَمِيعاً فَيُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ{105}

Yã ku wadanda suka yi ĩmãni! Ku lazimci rãyukanku, wanda ya bace bã zai cuce ku ba idan kun shiryu, zuwa ga Allah makõmarku take gabã daya. Sa'an nan Ya bã ku lãbari ga abin da kuka kasance kunã aikatãwa.

Ayoyin da suka gabata suna kashedi da galgadin Mushrikai da su haramta kansu da camfe camfe da takalidin kafirai da mushrikan da suka gabata.To wannan aya tana magana ne ga mumunai cewa: duk da cewa nauyin da ya rataya kanku fadakarwa da shiryar da tababbu da umurta da aikata kyakkyawa da hani da mummuna to idan nasiha da kokarin shiryarwar da kuke ba ta tasiri kar gwiwarku ta yi sanyi sai ku yi kokarin ciyar da addininku sai Allah ya kare ku daga sharrinsu ,A gobe kiyama kuwa a yi maku hisabi kan ayyukan da kuka aikata na alheri suma a yi masu hisabi da ayyukan da suka aikata mummuna saboda haka sai ku kara jin tsoran Allah da ayyukan alheri.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda hudu akalla:

1- takatsantsan da abubuwan san rai yana da nauyi na farko mumuni dole ya lura da son zucciya.

2- Laifin wani ba ya hawan wani ko da muna rayuwa cikin al'umma fasika kawai mu kare kanmu daga aikata sabo.

3- A ranar kiyama kowa za a yi masa hisabi da aikin da ya aikata babu wanda laifin wani zai hau kansa.

4- Yin tuba da neman gafarar Allah na taimakawa mutum a ranar tashin kiyama. Da fatar Allah ya yi mana gafara amin.

Da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shirin na yau sai kuma shiri na gaba da yardar Allah kafin lokacin Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram na na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalamu alaikum warahmatullahi wa barkatuhu.

Suratul Ma'ida, Aya Ta 106-108 (Kashi Na 183)

Jama'a masu saurare Assalamu alaikum barkarku da sake saduwa da mu a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda ,inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki, tare da yin bayani gwargwadon iko kan abin da suke koyar da mu ,tare da yi mana hannunka mai sanda a cikin lamurran rayuwa da zamantakewa.Amma kafin mu shiga cikin shirin gadan gadan ga abin da aka yi mana tanadi a kan inji.

To sai a saurari karatun aya ta 106 a cikin suratun Ma'idah kamar haka:

يِا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُواْ شَهَادَةُ بَيْنِكُمْ إِذَا حَضَرَ أَحَدَكُمُ الْمَوْتُ حِينَ الْوَصِيَّةِ اثْنَانِ ذَوَا عَدْلٍ مِّنكُمْ أَوْ آخَرَانِ مِنْ غَيْرِكُمْ إِنْ أَنتُمْ ضَرَبْتُمْ فِي الأَرْضِ فَأَصَابَتْكُم مُّصِيبَةُ الْمَوْتِ تَحْبِسُونَهُمَا مِن بَعْدِ الصَّلاَةِ فَيُقْسِمَانِ بِاللّهِ إِنِ ارْتَبْتُمْ لاَ نَشْتَرِي بِهِ ثَمَناً وَلَوْ كَانَ ذَا قُرْبَى وَلاَ نَكْتُمُ شَهَادَةَ اللّهِ إِنَّا إِذاً لَّمِنَ الآثِمِينَ{106}

Yã ku wadanda suka yi ĩmãni! Shaidar tsakãninku, idan mutuwa ta halarci dayanku, a lõkacin wasiyya, maza biyu ne ma'abuta ãdalci daga gare ku, kõ kuwa wasu biyu daga wasunku idan kun tafi a cikin kasa sa'an nan masĩfar Smutuwa ta sãme ku. Kunã tsare su daga bãyan salla har su yi rantsuwa da Allah; idan kun yi shakka: "Bã mu sayen kudi da shi, kõ dã ya kasance ma'abucin zumunta kuma bã mu bõye shaidar Allah. Lalle ne mu, a lõkacin, hakĩka, munã daga mãsu zunubi."

Karkashin dokokin musulunci duk wanda ya mutu ya bar wannan duniya,kashi biyu cikin uku na dukiyarsa zai je ga magada da ya hada matarsa da yayansa da uwayansa saboda kowa yanada hakkin ya yi wasiyar kashi daya cikin uku na dukiyarsa da yin kaso yadda ya ga dama kafin rasuwarsa domin magada za su bukaci duka dukiyarsa ganin haka musulunci ya amince da wasiya tare da shaidun mutane biyu adilai da za su bada shaida tsakaninsa da magadansa.Wannan aya tana ta'akidi kan muhimmancin shaidu da wasiya idan suna cikin bulaguro ne sai su nemi mutane biyu daga abukan bulaguronsa da za su yi rantsuwa ba za su sabawa abin da suka rubuta ko boye gaskiya. Wasiya an yi bayaninta dalla dalla a cikin littafan fikihu da yadda kowa zai yi aiki da ita.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda biyu akalla:

1-Domin kare hakkin magada da hakkokin masu nasiha da sauran hakkokin mutane dole daya daga cikin hannyoyi masu inganci neman mutum biyu adilai da za su yi shaida.

2- Daga cikin abubuwan da ke sanya mutum kaucewa hanya son dukiya da danginsa ido rufe da ke sawa su manta Allah da rantsuwa kan karya.

Sai a saurari aya ta 107 a cikin wannan sura ta Ma'idah

فَإِنْ عُثِرَ عَلَى أَنَّهُمَا اسْتَحَقَّا إِثْماً فَآخَرَانِ يِقُومَانُ مَقَامَهُمَا مِنَ الَّذِينَ اسْتَحَقَّ عَلَيْهِمُ الأَوْلَيَانِ فَيُقْسِمَانِ بِاللّهِ لَشَهَادَتُنَا أَحَقُّ مِن شَهَادَتِهِمَا وَمَا اعْتَدَيْنَا إِنَّا إِذاً لَّمِنَ الظَّالِمِينَ{107}

To, idan aka gane cewa lalle sũ, sun cancanci zunubi to sai wasu biyu su tsayu matsayibsu daga wadanda suka karba daga gare su, mutãne biyu mafiya cancanta, sa'an nan su yi rantsuwa da Allah: "Lalle ne shaidarmu ce mafi gaskiya daga shaidarsu, kuma ba mu yi zãlunci ba. Lalle mu, a lõkacin hakĩka, munã daga azzãlumai."

A cikin ayar da ta gabata tana magana ne kan nemo shaidu guda biyu don kiyaye wasiya amma ita wannan aya tana cewa ne idan ya bayyana wadannan shaidu biyu za su iya boye gaskiya da yin ha'inci da rantsuwar karya,sai a nemo mutane biyu daga makusanta da magadan mamaci domin bada shaida da yin rantsuwa kan wasiyar mamaci ba sau yi ha'inci da boye gaskiya ba.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda biyu akalla:

1- Ana amincewa aiki da rantsuwa ne a inda babu dalili kuma babu bukatar yin shisshigi.

2-Yin shaida kan karya wani nauyi ne na wuce gona da iri da zalunci kan hakkokin mutane ko da kuma babu wani kudi ko ladan da za a ba shi.

Sai a kara zama domin sauraren aya ta 108 a cikin suratul Ma'idah:

ذَلِكَ أَدْنَى أَن يَأْتُواْ بِالشَّهَادَةِ عَلَى وَجْهِهَا أَوْ يَخَافُواْ أَن تُرَدَّ أَيْمَانٌ بَعْدَ أَيْمَانِهِمْ وَاتَّقُوا اللّهَ وَاسْمَعُواْ وَاللّهُ لاَ يَهْدِي الْقَوْمَ الْفَاسِقِينَ{108}

Wannan ne mafi kusantar su zo da shaida a kan fuskarta kõ kuwa su yi tsõron a tũre rantsuwõyi a bãyan rantsuwõyinsu. Kuma ku bi Allah da takawa kuma ku saurara, kuma Allah bã Ya shiryar da mutãne fãsikai.

Ayoyin da suka gabata sun yi bayani kan masu bada shaida kan wasiya to ita kuwa wannan aya tana cewa ne: nauyi ne kan kowa ya yi gaskiya da bada shaida kan gaskiya ba tare da ya tauye hakkin wani don wani ba kuma zartar da wannna hukumci da aiki da shi zai amfani kowa ne kuma tushe ne daga tsauran Allah.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda biyu akalla:

1- Abu ne mia kyau a yi rantsuwa a bainar jama'a domin kare hakkin jama'a.

2-Damuwa kan aikata sabo na daga cikin dalilan nisantar aikata sabo.

Da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shirin na yau sai kuma shiri na gaba da yardar Allah kafin lokacin Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram na na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalamu alaikum warahmatullahi wa barkatuhu.

Suratul Ma'ida, Aya Ta 109-113 (Kashi Na 184)

Jama'a masu saurare Assalamu alaikum barkarku da sake saduwa da mu a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda ,inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki ,tare da yin bayani gwargwadon iko kan abin da suke koyar da mu ,tare da yi mana hannunka mai sanda a cikin lamurran rayuwa da zamantakewa.Amma kafin mu shiga cikin shirin gadan gadan ga abin da aka yi mana tanadi a kan inji.

To sai a saurari karatun aya ta 109 da kuma 110 a cikin suratun Ma'idah kamar haka:

يَوْمَ يَجْمَعُ اللّهُ الرُّسُلَ فَيَقُولُ مَاذَا أُجِبْتُمْ قَالُواْ لاَ عِلْمَ لَنَا إِنَّكَ أَنتَ عَلاَّمُ الْغُيُوبِ{109} إِذْ قَالَ اللّهُ يَا عِيسى ابْنَ مَرْيَمَ اذْكُرْ نِعْمَتِي عَلَيْكَ وَعَلَى وَالِدَتِكَ إِذْ أَيَّدتُّكَ بِرُوحِ الْقُدُسِ تُكَلِّمُ النَّاسَ فِي الْمَهْدِ وَكَهْلاً وَإِذْ عَلَّمْتُكَ الْكِتَابَ وَالْحِكْمَةَ وَالتَّوْرَاةَ وَالإِنجِيلَ وَإِذْ تَخْلُقُ مِنَ الطِّينِ كَهَيْئَةِ الطَّيْرِ بِإِذْنِي فَتَنفُخُ فِيهَا فَتَكُونُ طَيْراً بِإِذْنِي وَتُبْرِئُ الأَكْمَهَ وَالأَبْرَصَ بِإِذْنِي وَإِذْ تُخْرِجُ الْمَوتَى بِإِذْنِي وَإِذْ كَفَفْتُ بَنِي إِسْرَائِيلَ عَنكَ إِذْ جِئْتَهُمْ بِالْبَيِّنَاتِ فَقَالَ الَّذِينَ كَفَرُواْ مِنْهُمْ إِنْ هَـذَا إِلاَّ سِحْرٌ مُّبِينٌ{110}

A ranar da Allah Yake tãra manzanni sa'an nan Ya ce: "Mene ne aka karba muku?" (zã) su ce: "Bãbu ilmi a gare mu. Lalle ne Kai, Kai ne Masanin abubuwan fake."

A lõkacin da Allah Ya ce: "Yã Ĩsã dan Maryama!Ka tuna ni'ima Ta a kanka, kuma a kan mahaifiyarka, a lõkacin da Na karfafa ka da Rũhul ¡udusi,kanã yiwa mutãne magana a cikin shimfidar jariri, da kuma kanã dattijo. Kuma a lõkacin da Na sanar da kai rubutu da hikima da Attaura da Injĩla, kuma a lõkacin da kake yin halitta daga lãkã kamar surar tsuntsu da izinĩNa, sa'an nan ka hura a cikinta sai ta zama tsuntsu da izinĩNa, kuma kanã warkar da haifaffen makaho da kuturu, da izinĩNa, kuma a lõkacin da kake fitar da matattu da izinĩNa, kuma a lõkacin da Na kange Banĩ Isrã'ĩla daga gare ka, a lõkacin da ka je musu da hujjõji bayyanannu, sai wadanda suka kãfirta daga cikinsu suka ce: 'Wannan bã kõme ba ne, fãce sihiri bayyananne.'

Wadannan ayoyi na bayani ne kan tattaunawar da ta wakana tsakanin Allah da ma'aikinsa kan ni'imomi da falolin Allah ga al'ummarsa.Manzonni sun yi tambaya kan adadi da karfi da yawan mutanan da suka amsa kiransu a lokaci da bayan rasuwarsu inda suka amsa da cewa; Ilimi na hakika yana gurin Allah masanin abubuwan da mutane suka boye a cikin zucciyarsu ,mu ba mu da masaniyar abin da mutane suka aikata a bayanmu shin sun yi aiki da wasiyarmu da galgadinmu. Har ila yau Kur'ani ya kawo yadda tattaunawa ta wakana tsakanin Allah da Annabi Isa (AS) daga farkon wadannan ayoyi da cewa;yana daga cikin ni'imomin Allah da yayi wa Manzonsa wanda tun yana cikin zanan goyo har zuwa karshen rayuwarsa a wannan duniya .Wanda aka haifa ba tare da uba ba ,yayi magana yana cikin zanan goyo. Ya tubra tsuntsu da laka ya hura masa rai da yardar Allah,ya warkar da maras lafiya da yardarsa da raya matattu duka wannan da sauransu suna daga cikin mu'ijizar da Annabi Isa (AS) ya zo da su kuma yana daga cikin ni'imomin Allah.Karshen Ayar na cewa: amma duk da wadannan ni'imomi da mu'ujizoji ba a shirye suke ba su yi imani da shi da danganta duka wannan da tsafi da sihiri da nuna kafirci a fili.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda hudu akalla:

1- Tsarkin uwa yana daga cikin hanyar samun falalar Allah da haifar da mai tsarki salihu mai gyaran al'umma.

2- Idan zucciyar mutum a kekashe take to tafi tutse da karfe tsanani duk wani kokari na kafiri mai irin wannan zucciya na ya yi imani ba zai yi ba.

3- idan Allah mai iko da kudura ya bawa waliyansa ikon shafa'a to za su iya warkar da maras lafiya da ikonsa.

4- Allah ya kubutar da Annabi Isa (AS) a lokacin da bani Isra'ila suka kulla da kudurta kashe shi inda ya tsirar da shi da ba shi aminci.

Sai kuma a saurari karatun aya ta 111 a cikin suratun Ma'idah

وَإِذْ أَوْحَيْتُ إِلَى الْحَوَارِيِّينَ أَنْ آمِنُواْ بِي وَبِرَسُولِي قَالُوَاْ آمَنَّا وَاشْهَدْ بِأَنَّنَا مُسْلِمُونَ{111}

"Kuma a lõkacin da Na yi wahayi zuwa ga Hawãriyãwa cewa ku yi ĩmãni da Ni, kuma da ManzoNa. Suka ce: "Mun yi ĩmãni, kuma ka shaida da cewa lalle mu, mãsu sallamãwa ne."

Wannan aya ta nuni ne da wata ni'imar daga cikin ni'imomin da Allah ya yi wa Annabi Isa (AS) da cewa; Ni ne na cusa tsarki a zukatan wasu da suka yi imani da kai da amsa kiran shiriya da ka yi masu . Karkashin ruwayoyin tarihi sahabban musamman daga cikin mabiya Annabi Isa (AS) su goma sha biyu ne masu tsarki masu kokarin kubutar d amutane daga gurbacewar zunufi da tabewa.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda biyu akalla:

1- idan zucciyar mutum ta tsarkaka za ta samu lutifi da karbar gaskiya da samin shiriya.

2- Alamar imani na gaskiya shi ne mika wuya da hukumcin Allah da manzonninsa da imani da kuma yin da'a ga Allah.

Har yau a saurari aya ta 112 da 113 a cikin suratul Ma'idah

إِذْ قَالَ الْحَوَارِيُّونَ يَا عِيسَى ابْنَ مَرْيَمَ هَلْ يَسْتَطِيعُ رَبُّكَ أَن يُنَزِّلَ عَلَيْنَا مَآئِدَةً مِّنَ السَّمَاءِ قَالَ اتَّقُواْ اللّهَ إِن كُنتُم مُّؤْمِنِينَ{112} قَالُواْ نُرِيدُ أَن نَّأْكُلَ مِنْهَا وَتَطْمَئِنَّ قُلُوبُنَا وَنَعْلَمَ أَن قَدْ صَدَقْتَنَا وَنَكُونَ عَلَيْهَا مِنَ الشَّاهِدِينَ{113}

A lõkacin da Hawarãyãwa suka ce: "Ya Ĩsa dan Maryam! shin, Ubangijinka Yanã iyãwa Ya saukar da kabaki a kanmu daga samã?" (Ĩsã) Ya ce: "Ku bi Allah da takawa idan kun kasance muminai."

Suka ce: "Munã nufin mu ci daga gare shi ne, kuma zukãtanmu su natsu kuma mu san cewa lalle ne, kã yi mana gaskiya, kuma mu kasance daga mãsu shaida a kansa."

Karkashin ayar da ta gabata Hawariyun sun yi imani da lutifi da falalar Allah da ya yi Annabi Isa (AS) amma sun kasa fadada imaninsu da nucuwar zucci . amaimakon su kara yin imani da mu'ujizar da ni'imar da Allah ya yi masu na sabkar masu da abinci daga sama sai suka ci gaba da gabatar da tambaya da ba su dace ba na izgili da rashin hankali da neman kure Allah don jahilcinsu.Ganin haka Hadarat Isa (AS) ya ce masu mi yasa kuke gabatar da irin wannan bukata sai suka ceai wannan don ya kara mana imani da tsaron Allah da kusanci da shaidawa a gurin mutane abubuwa da isa ya yi.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda biyu akalla:

1- Imani matsayi matsayi ne har zuwa zucciya ta nucu kuma mutum mumuni yana kokarin ganin ya isa ga wannan matsayi da daukaka.

2- Mumuni bai dace ba ya riki Allah abin izgili da cewa; idan Allah gaskiya ne to ya aikata abin da na ke bukata da sauran maganganu irin haka.

Da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shirin na yau sai kuma shiri na gaba da yardar Allah kafin lokacin Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram na na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalamu alaikum warahmatullahi wa barkatuhu.

Suratul Ma'ida, Aya Ta 114-117 (Kashi Na 185)

Jama'a masu saurare Assalamu alaikum barkarku da sake saduwa da mu a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda ,inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki ,tare da yin bayani gwargwadon iko kan abin da suke koyar da mu ,tare da yi mana hannunka mai sanda a cikin lamurran rayuwa da zamantakewa.Amma kafin mu shiga cikin shirin gadan gadan ga abin da aka yi mana tanadi a kan inji.

To sai a saurari karatun aya ta 114 a cikin suratun Ma'idah kamar haka:

قَالَ عِيسَى ابْنُ مَرْيَمَ اللَّهُمَّ رَبَّنَا أَنزِلْ عَلَيْنَا مَآئِدَةً مِّنَ السَّمَاءِ تَكُونُ لَنَا عِيداً لِّأَوَّلِنَا وَآخِرِنَا وَآيَةً مِّنكَ وَارْزُقْنَا وَأَنتَ خَيْرُ الرَّازِقِينَ{114}

Ĩsã dan Maryam ya ce: "Yã Allah. Ubangijinmu! Ka saukar da kabaki a kanmu daga sama dõmin ya zama ĩdi ga na farkonmu da na karshenmu, kuma ya zama ãyã daga gare Ka. Ka azurta mu, kuma Kai ne Mafĩfĩcin mãsu azurtawa."

A cikin shirin da ya gabata mun bayyana cewa;Hawariyun sahabban Annabi Isa (AS) domin samin nucuwar zucci da ta ruhi da karfafa imaninsu sun bukaci Annabi Isa (AS) da ya bukaci Allah da ya sabkar masu da Abinci daga sama bayan da Annabi Isa (AS) ya fahimci ba izgili suke ba da yin jayayya sai don karfafa imaninsu ne sai ya daga hannu sama ya fara addu'a yana rokon Allah da ya sabkar masu da abinci daga sama ya zama idi a gare su da zama hujja a gare su ga wadanda ba su nan tare da su.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda biyu akalla:

1- Raya idi da buki na addini da ciyar da mutane a dalilin shagulgula na addini abu ne mai kyau a addinin musulunci da sauran addinai.

2- Duk wani aiki na zahiri muna iya maida shi na ma'anawiya idan muna cin abinci mu godewa Allah da wannan arziki da ya yi mana da kuma fahimtar karfi da kudurarsa.

Sai a saurari aya karatun aya ta 115 a cikin suratul Ma'idah

قَالَ اللّهُ إِنِّي مُنَزِّلُهَا عَلَيْكُمْ فَمَن يَكْفُرْ بَعْدُ مِنكُمْ فَإِنِّي أُعَذِّبُهُ عَذَاباً لاَّ أُعَذِّبُهُ أَحَداً مِّنَ الْعَالَمِينَ{115}

Allah Ya ce: "Lalle ne Nĩ mai saukar da shi ne a kanku sa'an nan wanda ya kãfirta daga gare ku, to, lalle ne Nĩ, Inã azabta shi, da wata azãba wadda bã Ni azabta ta ga kõwa daga tãlikai."

Ganin wannan mu'ujizar ta zo ne karkashin bukatar Hawariyun ba Annabi Isa ba ne ya bukata saboda haka sai Allah ya masu kashedi da cewa: Kaican ku ku nuna shakku da kokwanto kan abin da Annabi Isa (AS) ya zo da shi na mu'ujiza .Amma duk da haka karkashin wasu ruwayoyin wasu daga cikinsu bayan sabkar abinci daga sama kamar yadda suka bukata sun kafircewa Allah kuma wannan alama ce ta rashin godiyar mutum na ni'imomin da Allah ya yi masu.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda biyu akalla:

1- Azabar malai tafi ta jahilai kuna ,duk wanda yanada ilimi na fahimtar gaskiya amma yaki bi da aiki da gaskiya, azabar da ke jiransa tayi muni.

2- Duk wanda yake da bukata mai yawa dole ya karfafa himma.

Har ila yau za mu ci gaba da sauraren aya ta 116:

وَإِذْ قَالَ اللّهُ يَا عِيسَى ابْنَ مَرْيَمَ أَأَنتَ قُلتَ لِلنَّاسِ اتَّخِذُونِي وَأُمِّيَ إِلَـهَيْنِ مِن دُونِ اللّهِ قَالَ سُبْحَانَكَ مَا يَكُونُ لِي أَنْ أَقُولَ مَا لَيْسَ لِي بِحَقٍّ إِن كُنتُ قُلْتُهُ فَقَدْ عَلِمْتَهُ تَعْلَمُ مَا فِي نَفْسِي وَلاَ أَعْلَمُ مَا فِي نَفْسِكَ إِنَّكَ أَنتَ عَلاَّمُ الْغُيُوبِ{116}

Kuma a lõkacin da Allah Ya ce: "Yã Ĩsã dan Maryama! Shin, kai ne ka ce wa mutãne, 'Ku rike ni, ni da uwata, abubuwan bautãwa biyu, baicin Allah?" (Ĩsã) Ya ce: "Tsarkinka yã tabbata! Bã ya kasancewa a gare ni, in fadi abin da bãbu wani hakki a gare ni. Idan nã kasance nã fade shi, to lalle Ka san shi, Kanã sanin abin da ke a cikin raina, kuma bã ni sanin abin da ke a cikin nufinKa. Lalle ne Kai Masanin abubuwan fake ne."

Wannan aya tana bayanin hikayar da za ta wakana tsakanin Allah da kuma Annabi Isa (AS) a ranar kiyama kan abin da kiristocin yau ke dangantawa da Annabi Isa (AS) cewa yana dayan alloli uku ,wasu a matsayin ruhun kudus wasu maryam daya daga cikin alloli uku wasu ma suna ibadarsu a gumkin siffarta da suka sassaka da girmamawa a coci-coci da fatar Allah ya kiyashe mu daga bata.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda uku akalla:

1- Annabi da kansa na damuwa da wannan mummunar akida ta danganta shi da Allah ko ba shi matsayin dan Allah ,kuma wannan akida ce ta bata da ta nisanta da waliyan Allah.

2- Annabawa da manzonni duk irin daukaka da matsayin da suka kai suna tunkahu da matsayinsu na bayun Allah.

3- Ilimin mutun hatta na Annabawa nada iyaka sabanin ilimin Allah masanin abin da ke boye.

Daga karshe za mu saurari aya ta 117 a cikin wannan sura ta Ma'idah kamar haka:

مَا قُلْتُ لَهُمْ إِلاَّ مَا أَمَرْتَنِي بِهِ أَنِ اعْبُدُواْ اللّهَ رَبِّي وَرَبَّكُمْ وَكُنتُ عَلَيْهِمْ شَهِيداً مَّا دُمْتُ فِيهِمْ فَلَمَّا تَوَفَّيْتَنِي كُنتَ أَنتَ الرَّقِيبَ عَلَيْهِمْ وَأَنتَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ شَهِيدٌ{117}

"Ban fada musu ba fãce abin da Ka umurce ni da shi; watau: 'Ku bauta wa Allah Ubangijina kuma Ubangijinku;' kuma nã kasance mai shaida a kansu matukar nã dawwama a cikinsu, sa'an nan a lõkacin da Ka karbi raina Kã kasance Kai ne mai tsaro a kansu, kuma Kai, a kan dukkan kõme, Halartacce ne.

A ci gaba da tattaunawa tsakanin Allah da Annabi Isa a ranar tashin kiyama da kur'ani ya hikayo mana .Annabi Isa (AS) ya fito fili ya kare sakon da Allah ya aiko sa da shi inda ya kirayi mutanansa zuwa ga tauhidi duk da a fili take Allah yana sa ido kan ayyukan Annabawa da Manzonninsa kuma ya shaida sun isar da sakonsa baki daya babu kari babu ragi saboda haka wannan lamari tamkar galgadi ga mutanan Annabi Isa (AS) da fadakar da su sanin akidarsu ta allolo uku ba koyarwa ba ce ta Annabi Isa kuma ta sabawa tauhidinsa na kadaita Allah.

Da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shirin na yau sai kuma shiri na gaba da yardar Allah kafin lokacin Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram na na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalamu alaikum warahmatullahi wa barkatuhu.

Suratul Ma'ida, Aya Ta 118-120 (Kashi Na 186)

Jama'a masu saurare Assalamu alaikum barkarku da sake saduwa da mu a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda ,inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki, tare da yin bayani gwargwadon iko kan abin da suke koyar da mu ,tare da yi mana hannunka mai sanda a cikin lamurran rayuwa da zamantakewa.Amma kafin mu shiga cikin shirin gadan gadan ga abin da aka yi mana tanadi a kan inji.

To sai a saurari karatun aya ta 118 a cikin suratun Ma'idah kamar haka:

إِن تُعَذِّبْهُمْ فَإِنَّهُمْ عِبَادُكَ وَإِن تَغْفِرْ لَهُمْ فَإِنَّكَ أَنتَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ{118}

"Idan Ka azabta su, to lalle ne su, bãyinKa ne, kuma idan Ka gãfarta musu, to, lalle ne Kai ne Mabuwayi Mai hikima."

A cikin shirin da ya gabata mun kawo bayanin tattaunwar da ta wakana tsakanin Allah da annbi isa (AS) da baranta kansa da maganganun da wasu ke dangantawa da shi na cewa shi allah ne da fifita shi kan sauran mutane wasu su ce shi dan Allah ne Allah ya gafirta mana amin kuma wannan fada tasu ta sabawa tauhidin da ya zo da shi to a wannan aya Annabi Isa (AS) domin kubutar da al'ummarsa sai ya nemi masu gafara da cewa; Ya kai Allah na idan ka azabtar da su sun cancanci hakan kuma kai ne mai zabi ,amma idan ka yafe masu da yi masu gafara wannan rahama da lutihinka ne kuma kai ne mai hikima da babu wani aiki da ke yi da ya sabawa hikima.

Shafa'ar Manzonni ga al'ummarsu bayanin kauna da damuwar halin da al'ummarsu ke ciki wadanda suka aikata saboda saidai wani hamzari duk wanda ceton Annabawa da manzonni ya shafa sun aikata aiki da zai kai su ga ceto da yin imani da manzonni da Annabawa. Misali dalibi ya samu daraja daidai da aikin da yayi yana bukatar malaminsa ya kara masa wata daraja da za ta kai shi ga matsayi na gaba sai kuma malamin yaga wannan dalibi ya cancanci a taimaka masa sai ya yi babu laifi amma duk wanda bai cancanta ba ba zai samu ceton ba. Ba wai kawai Annabi Isa (AS) sairan Annabawa ma musamman Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka yana yin addu'ar neman gafara da rahamar Allah ga al'ummarsa kamar yadda Abu zar daya daga cikin manyan sahabban Annabin musulunci ya nakalto cewa; a duk lokacin da Annabi (SWA) ya karanto wannan aya yana daga hannunsa sama cikin kuka da murya mai tausayawa yana nemarwa masu saboda daga cikin al'ummarsa gafarar Allah madaukakin sarki mai rahama da jin kai.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda uku akalla:

1-azaba da azabtarwa tana hannun Allah saboda haka bamu da hakki a wannan duniya mu ce wane dan wuta ne da kollonsa a matsayin konanne alhali mutum yana iya canzawa da tuba daga kafirci.

2-Fushi da rahamar Allah karkashi hikimarsa ce duk wanda zai shiga jahannama ko aljanna karkashin hikimarsa ne.

3-Annabawa an ba su matsayin shafa'a amma suna ceton wadanda suka cancanta ba dukan masu sabo ba.

Sai a saurari karatun aya ta 119 a cikin suratul Ma'idah:

قَالَ اللّهُ هَذَا يَوْمُ يَنفَعُ الصَّادِقِينَ صِدْقُهُمْ لَهُمْ جَنَّاتٌ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا أَبَداً رَّضِيَ اللّهُ عَنْهُمْ وَرَضُواْ عَنْهُ ذَلِكَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ{119}

Allah Ya ce: "Wannan ce rãnar da mãsu gaskiya, gaskiyarsu take amfãninsu. Sunã da gidãjen Aljanna, kõramu sunã gudãna daga karkashinsu, sunã madawwama a cikinsu har abada. Allah Yã yarda da su, kuma sun yarda da Shi. wannan ne babban rabo mai girma."

A cikin wannan aya Allah yana amsawa annabi Isa (AS) maganarsa cewa Allah gafara ga wadanda suka aikata sabo tana hannunsa idan ka so kana iya yi masu gafara da cewa; a yau ranar kiyama gaskiya ce ga amfanar masu gaskiya da kubutar da mutum daga fadawa cikin wutar jahannama mai zafin kuna.Gaskiya ke sawa mutum ya shiga aljanna da samin matsayi mai girma da daukaka a gurin Allah a wannan rana . Kuma sa'adar duniya da lahira tana karkashin imani da aikata aiki na alheri kamar yadda wannan aya da sauran ayoyin kur'ani suka yi bayani cewa sharadi ne na samin tsira da sa'ada.Ma'ana imani kawai bai wadatar ba sai an hada da aiki na gari da niya ta gari ta neman kusanci ga Allah ba wai aiki karkashin riya da girman kai da nuna kai da yin alfahari.Wannan tana yin nuni da lamari mai muhimmanci cewa duk wanda ya yi wani aiki don neman yardar mutane sai ya nemi ladansa ga mutane amma duk wanda ya yi aiki don neman yardar Allah zai samu yardar Allah da matsayi mai girma kuma Allah zai yarda da shi kuma wannan ita ce sa'ada mai girma duniya da lahira.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda biyu akalla:

1- Mumunai idan suka jurewa matsaloli a wannan duniya saboda riko da tafarkin gaskiya to za su samu rabo mai girma a ranar lahira saboda yin riko da gaskiya da sadaukarwa.

2- aiki na gaskiya ya bambanta da aikin riya kuma aiki da tunani da akida da aikin da mutum ke yi da fadarsa su zamanto daya ba wai abin da yake rayawa daban da abin da yake aikatawa.

Daga karshe za mu saurari aya 120:

لِلّهِ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ وَمَا فِيهِنَّ وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ{120}

Allah ne da mallakar sammai da kasa da abin da ke a cikinsu kuma shi, a kan dukkan kõme Mai ĩkon yi ne.

Wannan ita ce aya ta karshe a cikin wannan sura ta An'am da kuma take bayani kan girma da daukakara Allah da tunatar da mu cewa kar waninmu ya yi zaton zai iya kubuta daga saitar ta Allah babu wani da zai yi wani aiki ba tare da sanin Allah ba .Mu sani Allah ne mai ikon wannan duniya da abin da ke cikinta kuma komi bayun ne na Allah masu dogaro da kudurar Allah maras karewa.

Da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shirin na yau sai kuma shiri na gaba da yardar Allah kafin lokacin Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram na na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalamu alaikum warahmatullahi wa barkatuhu.

Contents