Suratut Tauba, Aya Ta 1-3 (Kashi Na 289)
Jama'a masu saurare barkarmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikin wannan shiri muke yin bayani da hannunka mai sanda bayan mun kawo ayoyi da ke bayani da nasiha a lamurra da suka shafi rayuwarmu ta yau da kullum. To a yau za mu yi fara bayani ne da wasu ayoyi da suka zo a cikin suratul Tauba a cikin Alkur'ani mai girma da irin Nasihohin da suke cikin wadannan ayoyi.
To madalla, ita dai suratul Tauba a wani bangare ana kiranta da suratul Bara'a kuma wannan suna ya biyo bayan yadda surar ta fara da Kalmar bara'a wato yin baram-baram da mushirikai da kuma mika wuya ga Allah Madaukakin Sarki Abin Bauta Bil Hakki da Gaskiya da kuma mika wuya zuwa ga Manzonsa Manzon Rahama wanda aka yi duniya da lahira don shi. Kuma wannan Sura ta fara ne da Kalmar Bara'a ba tare da farawa da Bimillahi Rahmani rahimi kamar yadda sauran Surori 12 takwarorinta a cikin Alkur'ani suka fara da bismillar. Dalili kuwa Rahama kalma ce mai kumshe da sauki da albishir na rahama amma Bara'a nuna fushi da fusata da ba su haduwa ga kuma yanayin da wannan Sura ta sabka da kan wadanda ta sabka a kansu.An sabkar da wannan Sura ce a sheka ta tara bayan hijira wato kusan shekara guda kafin kaura da bankwana da wannan duniya da Manzon Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayansa ya yi .A cikin wannan sura akwai ayoyi da dama da ke magana da bayani kan tuba da komawa ga Allah madaukakin sarki da ta wannan hanya lutifi da rahamar Allah za su lullube dan adam, sabo da haka bari mu fara da aya ta farko (1) a cikin wannan sura ta Tauba kamar haka:
بَرَاءةٌ مِّنَ اللّهِ وَرَسُولِهِ إِلَى الَّذِينَ عَاهَدتُّم مِّنَ الْمُشْرِكِينَ{1}
Kubuta daga Allah da Manzonsa,zuwa ga mushrikan da kuka yi alkawari da su .Watau ba ruwan Allah shi da Manzonsa da wadannan mushrikai.
Su dai Mushrikan birnin Makka kafi zuwan musulunci da bayan zuwansa sun kasance suna gudanar da ayyukan ibadarsu kamar yadda suka saba da riko da sauran al'adar da suka gada iyaye da kakannu.Daga cikin wannan al'ada sun kasance idan suka yi dawafi suna kauta da rigar da suka yi dawafi da ita idan wani ba shi da wani riga ta biyu dole ya yi dawafi tsirara ba tare da wani abu a jikinsa.wannan mummunar al'ada ta dabbanci da shika kumci da Mushrikai ke yi tana takurawa musulmi da kasa amincewa da ita suna jiran umarni daga Allah madaukakin sarki har zuwa lokacin da ayar farko ta wannan sura ta sabka a birnin Madina sai Manzon Rahama Muhammadu dan Abdullahi tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayansa ya umarci Imam Ali (AS) day a wakilce shi da ya isar da sakon Allah zuwa ga mutanan birnin Makka inda karkashin wadannan ayoyi Mushrikan Makka ba su da hakkin shi ciki da falfajiyar Dakin Allah wato Ka'aba kuma uwa uba ba za su halarci ayyukan Hajji kuma duk wata yarjejeniya da aka kulla tsakaninsu da Musulmi an yi watsi da ita.Shi addinin musulunci addini ne mai kira da karfafa karfin gwuiwar aiki da cika alkawali da duk wata yarjejeniya amma wannan ka'ida tana aiki ne har zuwa lokacin da dayan bangare ya ci gaba da riko idan kuma ya saba da wuce gona da iri to Manzon Allah da musulmi ba su da wani zabi face watsi da wannan yarjejeniya da hakan ba yana nufin watsi da umarnin cika alkawali kamar yadda za mu gani a cikin aya ta hudu a cikin suratul Tauba a nan gaba . Music A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu kamar haka na farko:
Bayyana Bara'a ga wadanda suka kaucewa hanya na daya daga cikin tushen musulunci da bin tafarki na alkur'ani.shi mumuni dole ya bayyana matsayi da mahangarsa cikin sauki da hikima.
Abu na biyu Babu hani ko lahani akulla wata yarjejeniya da kafirai kuma babu wani hani kan hakan sai dai kar ya kasance wannan yarjejeniya ta ba su damar danne musulmi da wuce gona da iri kan musulmi saboda haka a duk lokacin da musulmi suka fuskanci matsi da tsanani suna iya watsi da wannan yarjejeniya da sanar da Kafirai matsayin da suka doka domin baubu takurawa a musulunci wato la darar wala durara kuma daukaka tana ga musulmi da addininsu da ya kare hakkin musulmi da wadanda ba musulmi ba.
Yanzu bari mu saurari aya ta 2 a cikin wannan sura ta Tauba kamar haka:
فَسِيحُواْ فِي الأَرْضِ أَرْبَعَةَ أَشْهُرٍ وَاعْلَمُواْ أَنَّكُمْ غَيْرُ مُعْجِزِي اللّهِ وَأَنَّ اللّهَ مُخْزِي الْكَافِرِينَ{2}
To sai ku tafi ku wala a bayan Kasa nan da wata hudu,kuma ku sani cewa ku ba za ku gagari Allah da kaairayinku ba,kuma hakika Allah mai wulakanta kafirai ne.
Yanzu kuma za mu saurari aya ta uku a cikin wannan sura ta Tauba kamar haka:
وَأَذَانٌ مِّنَ اللّهِ وَرَسُولِهِ إِلَى النَّاسِ يَوْمَ الْحَجِّ الأَكْبَرِ أَنَّ اللّهَ بَرِيءٌ مِّنَ الْمُشْرِكِينَ وَرَسُولُهُ فَإِن تُبْتُمْ فَهُوَ خَيْرٌ لَّكُمْ وَإِن تَوَلَّيْتُمْ فَاعْلَمُواْ أَنَّكُمْ غَيْرُ مُعْجِزِي اللّهِ وَبَشِّرِ الَّذِينَ كَفَرُواْ بِعَذَابٍ أَلِيمٍ{3}
3-Kuma da yekuma daga Allah da Manzon zuwa ga mutane a ranar haji babba cewa lalle ne Allah barrantacce ne daga masu shirki , kuma Manzon ( haka) .To , idan kun tuba, to , shi ne mafi alheri a gare ku , kuma idan kun juya ,to , ku sani lalle nu ku , ba masu buwayar Allah ban e . Kuma ka bayar da bishara ga wadanda suka kafirta , da azaba mai radadi .
Allah ya yi bara'a da masu shirka kuma haka ma ma'aikinsa tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da kuma alayan gidansa tsarkaka duk sun yi bara'a da Mushrikai kuma sanar da wannan kalubale da baranta ya z one a ranar haji babba .Amma duk wanda ya aikata wani sabo idan ya tuba ya koma kan hanyar madaidaiciya ta gaskiya shi ne mafi alheri a gare shi da kuma zai samu dacewa da makoma ta gari ammam idan mutum ya bujire to ya san da sanin ba zai gagari Allah ba da kuma azabar Allah mai radadi na jiransa ko shakka babu. A cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda biyu na farko fitar da zakka na nuni da gaskiyar mai raya imani saboda haka aka bata sunan Sadaka.
Na farko: Baranta da Kafirai da mushrikai ya zama wajibi a gare mu domin Allah da ma'aikinsa da kansu sun baranta da su.
Na biyu: dam u da mushirkai hanyarmu ta banbanta.
To madallah da wannan ne kuma muka kawo karshen wannan shiri na yau da muka fara sauraren aya ta farko tare da mukaddama kan suratul Tauba da dalilan sabkarta da irin darussan da ke cikinta da daidai sauransu.Sai kuma mako na sama inda za mu ci gaba da sauraren ci gaban wannan ayoyin da ke cikin wannan sura ta Tauba da yardar Allah Tabaraka wata'ala kafin makon na sama Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram na ke cewa wassalam Aalaikum warahmatullahi wa barkatuhu.
Suratut Tauba, Aya Ta 4-6 (Kashi Na 290)
Jama'a masu saurare barkarmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikin wannan shiri muke yin bayani da hannunka mai sanda bayan mun kawo ayoyi da ke bayani da nasiha a lamurra da suka shafi rayuwarmu ta yau da kullum. To a yau za mu yi fara bayani ne da wasu ayoyi da suka zo a cikin suratul Tauba a cikin Alkur'ani mai girma da irin Nasihohin da suke cikin wadannan ayoyi.
Yanzu bari mu saurari aya ta 4 ta cikin Suratut Tauba:
إِلاَّ الَّذِينَ عَاهَدتُّم مِّنَ الْمُشْرِكِينَ ثُمَّ لَمْ يَنقُصُوكُمْ شَيْئاً وَلَمْ يُظَاهِرُواْ عَلَيْكُمْ أَحَداً فَأَتِمُّواْ إِلَيْهِمْ عَهْدَهُمْ إِلَى مُدَّتِهِمْ إِنَّ اللّهَ يُحِبُّ الْمُتَّقِينَ{4}
4- Sai wadanda kuka yi wani alkawari daga shirki , sa'an nan kuma bas u rage da kome ba , kuma bas u taimaki kowa a kanku ba , to, ku cika alkawarin, zuwa gare su , har ga iyakar yarjejeniyarsu . Lalle ne Allah yana son masu takawa .
Su mushrikai nhalayansu ya bambanta akwai wadanda suke kasancewa suna taimakwa kafirai da makiyan musulmi wajen yakar Musulunci da musulmi a sauran yakokkin da musulmi suka yi da makiyansu a lokacinda suke zaune a birnin Madina da yi masu zagon kasa.To mushrikan dab a su yi wa muslmi zagon kasa ba za a oya yin Alkawari da su da cika masu alkwari da kiyaye yarjejeniyar da aka kulla da su.Kuma shi Allah a kullum yana so da kuma kasancewa da masu takawa ma'ana masu tsoransa.
A cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda biyu na farko fitar da zakka na nuni da gaskiyar mai raya imani saboda haka aka bata sunan Sadaka.
Na farko: duk wnada ya taimak maka ka iya taimaka masa ko da kuwa mashiriki da zarar ya kiya maka hakkinka.
Na biyu: yaudara ta yi muni ko da a tsakanin kafirai ne.
To madallah yanzu kuma zamu fara wannan shiri ne da sauraren aya ta 5 a cikin wannan sura ta Tauba kamar haka:
فَإِذَا انسَلَخَ الأَشْهُرُ الْحُرُمُ فَاقْتُلُواْ الْمُشْرِكِينَ حَيْثُ وَجَدتُّمُوهُمْ وَخُذُوهُمْ وَاحْصُرُوهُمْ وَاقْعُدُواْ لَهُمْ كُلَّ مَرْصَدٍ فَإِن تَابُواْ وَأَقَامُواْ الصَّلاَةَ وَآتَوُاْ الزَّكَاةَ فَخَلُّواْ سَبِيلَهُمْ إِنَّ اللّهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ{5}
Sannan idan watanni masu alfarma suka wuce sai ku yaki mushrikai a duk inda kuka same su kuma ku kama su ku tsare su ku kuma toshe musu kowace hanya. To amma idan sun tuba sun kuma . tsai da salla kuma sun bad a zakka, to sai ku kyale su .Hakika Allah Mai gafara ne Mai rahama.
Wannan aya tna bayani ne kan banbncin mushrikai d suk mutunta yarjejeniyar da suka kulla da musulmi da cika alkawari da mushrikan da suka yi watsi da alkawarin da suka dauka a cikin yarjejeniyar da suka sawa hannu tsakaninsu da musulmi da cewa: Wadanda suka saba yarjejeniya da alkawari suka kuma taimakawa makiyanku wajen yakarku ko suka yake da kansu,bayan cikar watanni ba su da hakkin zama a birnin Makka idan suka cika da kasancewa a cikin birnin Makka rayukansu da dukiyoyinsu ba za a ba su kariya ba.Amma wadanda suka share shekaru 13 Makka bayan Hijira ma ba su kullawa musulmi makirci to za a kare su da dukiyoyinsu.Amma wadanda suka zalumci musulmi da kulla masu makirci dama yakar su ko hada baki da makiyan musulmi to a kore su da yakarsu dama killace su da kama su idan sun yi turjiya a fafata das u mai tsanani ko su bar Makka ko su yi imani da yin bankwana da ayyukan shirka da bautawa gumaka.Su koma su bautawa Allah shi kadai kuma a maimakon yin bakance ga gumaka sai su fitar da zakka da abin da suka yi alkawari ga Talakawa da maras galihu da mabukata idan sun yi haka Allah zai yafe masu zunubbansu. A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda na farko:A lokacin kalubalantar makiya dole ya yi watsi da duk wata yarjejeniya da alkawari kuma a nuna kauna da rahama a tsakanin mumunai ya junansu a gefe daya a nuna tsanani kan makiya.
Abu na biyu addinin musulunci baya da iyaka kuma mutum zai iya tuba a kowane lokaci ko da a filin daga ne.
Yanzu kuma za mu saurari aya ta 6 a cikin wannan shiri na Hannunka mai sanda a cikin suratul Tauba.
وَإِنْ أَحَدٌ مِّنَ الْمُشْرِكِينَ اسْتَجَارَكَ فَأَجِرْهُ حَتَّى يَسْمَعَ كَلاَمَ اللّهِ ثُمَّ أَبْلِغْهُ مَأْمَنَهُ ذَلِكَ بِأَنَّهُمْ قَوْمٌ لاَّ يَعْلَمُونَ{6}
Idan wani daga mushirikai ya nemi makwabtakarka, to , ka ba shi makwabtakar har ya yi maganar Allah , sa'an nan ka isar da shi ga wurin amincewarsa .Wancan fa domin lalle ne su , mutane ne wadanda ba su sani ba .
A duk lokacin da mushiriki ya nemi zaman lafiya da makwabtaka da musulmi to yana iya yi da shi dad a ba shi aminci da hakan zai iya sawa ya gane da fahimtar gaskiya da daidai galgado da zaman lafiytar da aka yi da shi amma idan ya nuna wani hali mummuna to a maida masa aniyarsa da nuna masa iyakacinsa da hakan zai iya sawa ya zama cikin nucuwa da sanin iayaklacinsa.
A cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda biyu na farko fitar da zakka na nuni da gaskiyar mai raya imani saboda haka aka bata sunan Sadaka.
Na farko : komi yanada na shi rana da matsayi.
Na biyu: zaman lafiya ya danganta da bangarori biyu ne.
Sai kuma mako na sama inda za mu ci gaba da sauraren ci gaban wannan ayoyin da ke cikin wannan sura ta Tauba da yardar Allah Tabaraka wata'ala kafin makon na sama Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram na ke cewa wassalam Aalaikum warahmatullahi wa barkatuhu.
Suratut Tauba, Aya Ta 7-11 (Kashi Na 291)
Jama'a masu saurare barkarmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikin wannan shiri muke yin bayani da hannunka mai sanda bayan mun kawo ayoyi da ke bayani da nasiha a lamurra da suka shafi rayuwarmu ta yau da kullum. To a yau za mu yi fara bayani ne da wasu ayoyi da suka zo a cikin suratul Tauba a cikin Alkur'ani mai girma da irin Nasihohin da suke cikin wadannan ayoyi.
To madallah yanzu kuma zamu fara wannan shiri ne da sauraren aya ta 7 da 8a cikin wannan sura ta Tauba kamar haka:
كَيْفَ يَكُونُ لِلْمُشْرِكِينَ عَهْدٌ عِندَ اللّهِ وَعِندَ رَسُولِهِ إِلاَّ الَّذِينَ عَاهَدتُّمْ عِندَ الْمَسْجِدِ الْحَرَامِ فَمَا اسْتَقَامُواْ لَكُمْ فَاسْتَقِيمُواْ لَهُمْ إِنَّ اللّهَ يُحِبُّ الْمُتَّقِينَ{7} كَيْفَ وَإِن يَظْهَرُوا عَلَيْكُمْ لاَ يَرْقُبُواْ فِيكُمْ إِلاًّ وَلاَ ذِمَّةً يُرْضُونَكُم بِأَفْوَاهِهِمْ وَتَأْبَى قُلُوبُهُمْ وَأَكْثَرُهُمْ فَاسِقُونَ{8}
Yaya wani alkawari a wurin Allah a wurin ManzonSa yake kasansewa ga mushirikai , face ga wadanda kuka yi wa alkawar ? To , matukar sun tsayu sosai gare su . Lalle ne Allah Yana son masu takawa . Yaya , alhaki idan sun ci nasara a kanku , ba za su tsare wata zumunta ba a cikinku , kuma haka wata amana , suna yardarm da ku da bakunansu , kuma zukantansu suna ki ? kuma mafi yawansu fasikai ne .
Wadannan ayoyi masu magana kan kiyaye alkawali na nuni da yadda addinin Musulunci ke kiyaye alkawari ko da kuwa da kowane ne ya kulla matukar ba dayan bangaren ya kaita wannan yarjejeniya da alkawari da aka kulla ko ya kullawa musulmi makircin da zagon kasa kamar yadda ya faru a lokacin da musulmi suka kulla yarjejeniya tare da mushrikai amma suka saba alkawari da wannan yarjejeniya da suka kulla da su. A cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda biyu na farko fitar da zakka na nuni da gaskiyar mai raya imani saboda haka aka bata sunan Sadaka. Na farkoAlkawri abin kiyayewa ne. Na biyu cika alkawari yana da dadi ko da kuwa da mushrikai ne aka kulla shi.
Yanzu kuma za mu saurari aya ta 9 a cikin wannan sura ta Tauba kamar haka;
اشْتَرَوْاْ بِآيَاتِ اللّهِ ثَمَناً قَلِيلاً فَصَدُّواْ عَن سَبِيلِهِ إِنَّهُمْ سَاء مَا كَانُواْ يَعْمَلُونَ{9}
-Sun saya da ayoyin Allah , yan kudi kadan . sa'an nan suka kange daga hanyarAllah . Lalle ne su . abin da suka kasance suna aikatawa ya munana .
Duk wanda ya bi son rai da yan kudi wajen musanta ayoyin Allah lalle ne za a hukunta shi da fuskantar babbar matsala da fushin Allah kan haka.Wannan aya tana yin nuni ne da wandanda kan sayar da ayara Aya a dan kudi kankane ko yaudarar musulmi da addininsu saboda wani abu da bai taka kara ya karya ba kuma masu aikata irin wannan aiki aikinsu ya munana matuka gaya.
A cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda biyu na farko fitar da zakka na nuni da gaskiyar mai raya imani saboda haka aka bata sunan Sadaka.
Na farko: kwadai mai kai mutum makasa a wannan duniya.
Na biyu: duk wanda ya kiyaye addinin Allah yana da rabo mai girma a duniya da lahira.
Yanzu kuma za mu saurari aya ta 10 zuwa 11 a cikin suratul ta tauba kamar:
لاَ يَرْقُبُونَ فِي مُؤْمِنٍ إِلاًّ وَلاَ ذِمَّةً وَأُوْلَـئِكَ هُمُ الْمُعْتَدُونَ{10} فَإِن تَابُواْ وَأَقَامُواْ الصَّلاَةَ وَآتَوُاْ الزَّكَاةَ فَإِخْوَانُكُمْ فِي الدِّينِ وَنُفَصِّلُ الآيَاتِ لِقَوْمٍ يَعْلَمُونَ{11}
- Ba su tsaron wata zumunta a cikin muninai . kuma haka ba su tsaron wata amana : kuma wadannan ne masu ta'adi . - Sa'an nan idan sun tuba kuma suka tsayar da salla .kuma suka bayar da zakka . to yan uwanku ne a cikin addini , kuma muna rarrabe ayayi daki-daki , ga mutane wadanda suka sani .
Wadannan ayoyi biyu na magana ne kan yadda halayyar irin wadannan mutane masu sabawa duk wata yarjejeniya da suka kulla a tsakanin su da mumunai kan zumunta ko amana duk daya ne a gare su suna karyawa ne duk inda suka ga dama ba kan gaba bad a yin ta'adi a doran kasa.Amma a duk lokacin da suka tuba da komawa ga Allah yin nadama da tsayar da salla da faiatr da zakka sun zaman yan uwan mu a a cikin addini.Allah ya yi mana bayani dalla-dalla domin mu sani da fahimtar gaskiyar lamari.
A cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda biyu na farko fitar da zakka na nuni da gaskiyar mai raya imani saboda haka aka bata sunan Sadaka.
Na farko: Tuba ke wanke bawa daga Sabo da daidaita shi.
Na biyu: duk wanda ya yi laifi ya tuba da karbar tubarsa tamkar bai taba yin leifi ne ba.
Suratut Tauba, Aya Ta 12-16 (Kashi Na 292)
Jama'a masu saurare barkarmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda ,shirin da ke kawo maku bayanai da nasihohi a bangarorin rayuwa da zaman takewar jama' a dukan bangarorin da suka hada da akida,tattalin arziki,al'adu,kasuwanci da kare hakkoki da iya tafiyar da lamurra daidai wadaida ba tare da takurawa kai ko abukkan zama tare ba.Kuma kamar yadda masu saurare suka sani ne muna yin dubi ne kan bayan mun saurare ayoyin alkur'ani mai girma da yake madogara kuma garkuwar musulmi da duk dan adam baki daya matukar yana son yin rayuwa mai tsabta tsarkakekkiya a nuce cikin sauki duniya da lahira. A cikin shirin a makon day a gabata muna magana ne kan suratul Tauba da irin nasihohin da suka kumsa musamman kalubalantar mushrikai da irin matakin da musulmi ya dace su dauka kan mushrikai musamman a wannan guri da lokaci mai tsarki na lukuttan aikin Hajji mai girma da ke a matsayin daya daga cikin cikon na biyar na shika-shikan aikin hajji .A wannan guri da musulmi daga ko'ina a duniya don radin kaisu da kokarin sabke farali ke haduwa a wannan guri mai albarka da suke neman gafarar Allah madaukakin sarki da sanin halin da sauran yan uwansu a kusa da nesa suke ciki tare da tunanin hanyoyin da za su iya taimaka masu wajen kubuta daga cikin wannan mawuyacin halin na lahaula. To a yau ma za mu ci gaba da wannan shiri na hannunka mai sanda ne ta hanyar sauraren ayo ko ayoyin da ke cikin suratul Tauba ko Bara'a amma bayan mun saurari wannan abu da aka yi mana tanadi a kan inji .
Yanzu kuma za mu saurari aya ta 12 a cikin wannan sura ta Tauba kamar haka:
وَإِن نَّكَثُواْ أَيْمَانَهُم مِّن بَعْدِ عَهْدِهِمْ وَطَعَنُواْ فِي دِينِكُمْ فَقَاتِلُواْ أَئِمَّةَ الْكُفْرِ إِنَّهُمْ لاَ أَيْمَانَ لَهُمْ لَعَلَّهُمْ يَنتَهُونَ{12}
12- kuma idan suka warware rantsuwoyin amana daga bayan alkawarinsu , kuma suka yi suka a cikin addininku , to , ku yaki shugabannin kafirci . Lalle na su , babu rantsuwoyin amana a gare su :tsammaninsu suna hanuwa .
Dukan wadanda suka yi alkawari da yin rantsuwa amma sai suka warware wannan rantsuwa da suka yi da cin amanar abin da suka amince da kansu babu tilastawa da yin suka da zagon kasa wa addinin Allah ,to babu abin day a rage sai a yaki irin wadannan kafirai masu saba alkawari da su da shugabanninsu.babu wata magana makamanciyar yin ratsuwa da alakawari a tsakaninmu da su domin ko an kulla bas u kiyayewa da cika alkawarin.
A cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda biyu na farko fitar da zakka na nuni da gaskiyar mai raya imani saboda haka aka bata sunan Sadaka.
Na farko:yakar kafirai masu saba alkawari ya zama wajibi.
Na biyu:yaudara da munafinci makiya n eke sa musulmi yin yaki da su.
Yanzu kuma za mu saurari aya ta 13 a cikin wannan sura ta Tauba kamar haka:
أَلاَ تُقَاتِلُونَ قَوْماً نَّكَثُواْ أَيْمَانَهُمْ وَهَمُّواْ بِإِخْرَاجِ الرَّسُولِ وَهُم بَدَؤُوكُمْ أَوَّلَ مَرَّةٍ أَتَخْشَوْنَهُمْ فَاللّهُ أَحَقُّ أَن تَخْشَوْهُ إِن كُنتُم مُّؤُمِنِينَ{13}
13- shin, ba ku yakin mutane , wadanda suka warware rantsuwoyinsa ,kuma suka yi niyya ga fitar da Manzo , kuma sun e suka fara muku, tun a farkon lokaci? Shin , kuna tsoron su ne ? To Allah ne Mafi cancantar ku ji tsoronsa , idan kun kasance muminai .
A daidai lokacin da umarnin yakar wadanda suka sabawa rantsuwa da alkawarin da musulmi suka kulla da su ,sai wannan aya ta sabka da dora ayoyin tambaya na sanin dalilin sayin da musulmi ke yin a abkawa wadanda suka saba da alkawari bayan da suka warware rantsuwar da suka yi da yin niyar fatar da Manzon Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka.har ila yau sun e suka fara karya alkawari ba musulmi ba,idan suna tsoransu ne to su sani Allah ne Mafi cancantar mu ji tsoronsa idan mun kasance mumunai.
A cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda biyu na farko fitar da zakka na nuni da gaskiyar mai raya imani saboda haka aka bata sunan Sadaka.
Na farko:Allah shi ne yafi cancanta mu ji tsoransa ba waninsa.
Na biyu: sabawa yarjejeniya da alkawari yanada muni .
Yanzu kuma za mu saurari aya ta 14 da 15 a cikin wannan sura ta Tauba kamar haka:
قَاتِلُوهُمْ يُعَذِّبْهُمُ اللّهُ بِأَيْدِيكُمْ وَيُخْزِهِمْ وَيَنصُرْكُمْ عَلَيْهِمْ وَيَشْفِ صُدُورَ قَوْمٍ مُّؤْمِنِينَ{14} وَيُذْهِبْ غَيْظَ قُلُوبِهِمْ وَيَتُوبُ اللّهُ عَلَى مَن يَشَاءُ وَاللّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٌ{15}
-Ku yake su , Allah Ya yi musu azaba da hannayenku . kuma ya kunyatar da su, kuma ya taimake ku, kuma ya warkar da kirazan mutane muminai.
Kuma ya tafi da fushin zukatansu, kuma Ya karbi tuba a kan wanda Ya so. Kuma Allah ne Masani, Mai hikima.
Wadannan ayoyi na magana da bayani ne kan yadda Allah ke azabtar da wadanda suka kafirata da irin ayyukan da suka aikata kuma ya kunyatar da su a duniya da lahira da iske azabar da ke jiransu .a dabra da haka ya taiamakawa mutane da suka bada gaskiya da imani da kawo karshen irin fushin da ke cikin zukatansu kuma ya karbi tuba ga wanda ya so daga cikin bayinsa .Kuma Allah ne Masani Mai hikima.
A cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda biyu na farko fitar da zakka na nuni da gaskiyar mai raya imani saboda haka aka bata sunan Sadaka.
Na farko: kafiarai da mushrikai da wadanda suka sabawa alkawari da munafikai an yi masu tanadin azaba.
Na biyu: Allah yana yafewa wanda ya so daga cikin bayunsa.
Yanzu kuma za mu fara shirin ne da sauraren aya ta 16 a cikin suratul Tauba:
أَمْ حَسِبْتُمْ أَن تُتْرَكُواْ وَلَمَّا يَعْلَمِ اللّهُ الَّذِينَ جَاهَدُواْ مِنكُمْ وَلَمْ يَتَّخِذُواْ مِن دُونِ اللّهِ وَلاَ رَسُولِهِ وَلاَ الْمُؤْمِنِينَ وَلِيجَةً وَاللّهُ خَبِيرٌ بِمَا تَعْمَلُونَ{16}
- Ko kuna zaton a bar ku , tun Allah bai bayyana wadanda suka yi jihadi ba daga gare ku , kuma su ba su riki wani shige ba, baicin Allah da ManzonSa da muminai ? kuma Allah ne Mai jarrabawa ga abin da kuke aikatawa .
Da kuma wannan ne muka kawo karshen bayani a cikin wannan shiri na yau na hannunka mai sanda da ni Tidjani Malam Lawali Damagaram na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam alaikum warahmatullahi.
Suratut Tauba, Aya Ta 17-22 (Kashi Na 293)
Jama'a masu saurare barkarmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda ,shirin da ke kawo maku bayanai da nasihohi a bangarorin rayuwa da zaman takewar jama' a dukan bangarorin da suka hada da akida,tattalin arziki,al'adu,kasuwanci da kare hakkoki da iya tafiyar da lamurra daidai wadaida ba tare da takurawa kai ko abukkan zama tare ba.Kuma kamar yadda masu saurare suka sani ne muna yin dubi ne kan bayan mun saurare ayoyin alkur'ani mai girma da yake madogara kuma garkuwar musulmi da duk dan adam baki daya matukar yana son yin rayuwa mai tsabta tsarkakekkiya a nuce cikin sauki duniya da lahira. A cikin shirin a makon day a gabata muna magana ne kan suratul Tauba da irin nasihohin da suka kumsa musamman kalubalantar mushrikai da irin matakin da musulmi ya dace su dauka kan mushrikai musamman a wannan guri da lokaci mai tsarki na lukuttan aikin Hajji mai girma da ke a matsayin daya daga cikin cikon na biyar na shika-shikan aikin hajji .A wannan guri da musulmi daga ko'ina a duniya don radin kaisu da kokarin sabke farali ke haduwa a wannan guri mai albarka da suke neman gafarar Allah madaukakin sarki da sanin halin da sauran yan uwansu a kusa da nesa suke ciki tare da tunanin hanyoyin da za su iya taimaka masu wajen kubuta daga cikin wannan mawuyacin halin na lahaula. To a yau ma za mu ci gaba da wannan shiri na hannunka mai sanda ne ta hanyar sauraren ayo ko ayoyin da ke cikin suratul Tauba ko Bara'a amma bayan mun saurari wannan abu da aka yi mana tanadi a kan inji .
Yanzu kuma za mu fara shirin ne da sauraren aya ta 17 da 18 a cikin suratul Tauba
مَا كَانَ لِلْمُشْرِكِينَ أَن يَعْمُرُواْ مَسَاجِدَ الله شَاهِدِينَ عَلَى أَنفُسِهِمْ بِالْكُفْرِ أُوْلَئِكَ حَبِطَتْ أَعْمَالُهُمْ وَفِي النَّارِ هُمْ خَالِدُونَ{17} إِنَّمَا يَعْمُرُ مَسَاجِدَ اللّهِ مَنْ آمَنَ بِاللّهِ وَالْيَوْمِ الآخِرِ وَأَقَامَ الصَّلاَةَ وَآتَى الزَّكَاةَ وَلَمْ يَخْشَ إِلاَّ اللّهَ فَعَسَى أُوْلَـئِكَ أَن يَكُونُواْ مِنَ الْمُهْتَدِينَ{18}
17- Ba ya kasancewa ga masu shirki su raya masallatan Allah , alhali kuwa suna masu bayar da shaida a kan rayukansu da kafirci, wadannan ayyukansu sun baci , kuma a cikin wuta madawwama ne.
18- Abin sani kawai , mai raya masallatan Allah , shi ne wanda ya yi imani da Allah da Ranar Lahira , kuma ya tsayar da salla ya bayar da zakka , kuma bai ji tsoron kowa ba face Allah .To, akwai tsammanin wadannan su kasance daga shiryayyu .
Yin jihadi a farkon lokacin bayyanar Musulunci da kokarin kafuwar Musulunci ya zama wajibi kuma har duniya ta tashi jihadi ya zama wajibi da kuma banbanta wadanda suke jihadi da daga cikin musulmi da wadanda bas u yi dab a su matsayi mai girma da daukaka .masu kulla makirci ga musulmi da addininsu da yi masu zagon kasa da yaudara ko shakka babu za su gamu da mummunan sakamako da ke jiransu na shiga wutar Jahannama da dauwama a cikinta.Masu shirka da kafirai aikinsa ya munana matuka gaya. A cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda biyu na farko fitar da zakka na nuni da gaskiyar mai raya imani saboda haka aka bata sunan Sadaka. Na farko: aikin maushrikai da kafirai ya munana da ganin sakamako mai muni. Na biyu: su munafiki ba shi da banbanci da kafiri.
Wannan aya ta 18 tana magana ne da masu yin salla don riya wato masallata wadanda sun ke yin salla ,sun yi imani da ranar tashin kiyama da bada zakka bas u tsoran kowa sai Allah to irin wadannan musulmi akwai yuyuwar su kasance daga cikin shiryayya.Amma wadanda suka kasance su musulmi ne da yin raya bas u da wadannan siffofi ko shakka babu za su ya gamuwa da mummunan sakamako da azaba mai radi. A cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda biyu na farko fitar da zakka na nuni da gaskiyar mai raya imani saboda haka aka bata sunan Sadaka.
Na farko: masu riya masulmi ne amma da ke son burke wanin Allah ba Allah.
Yanzu kuma zafara shirin da sauraren aya ta 19 a cikin wannan sura ta Tauba kamar haka;
أَجَعَلْتُمْ سِقَايَةَ الْحَاجِّ وَعِمَارَةَ الْمَسْجِدِ الْحَرَامِ كَمَنْ آمَنَ بِاللّهِ وَالْيَوْمِ الآخِرِ وَجَاهَدَ فِي سَبِيلِ اللّهِ لاَ يَسْتَوُونَ عِندَ اللّهِ وَاللّهُ لاَ يَهْدِي الْقَوْمَ الظَّالِمِينَ{19}
19-Shin ,kun sanya shayar da mahallatadarayar da Masallaci Mai alfarma kamar wanda ya yi imani da Allah da Ranar Lahira , kuma ya yi jihadi a cikin hanyar Allah ? Ba su daidaita wurin Allah .Kuma ba Ya shiryar da mutane azzalumai .
Wannan aya tana bayyana mana irin banbancin da ke akwai a tsakanin masu salla da imani da ranar tashin kiyama da cewa ba za su taba zama daidai ba . Domin mai alheri yafi mai rowa kuma a kullum shi mai alhetri da aiki na gari ya dara wanda yake aikata banna da dagagwa a doran kasa. Har ila yau a kullum haka rayuwar take a doran kasa ayyukan mutane bas u taba zama daidai ba a rayuwa.
A cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda biyu na farko fitar da zakka na nuni da gaskiyar mai raya imani saboda haka aka bata sunan Sadaka.
Na farko: mutane a tsakanisu sun sha banban da aikinsu ya banbanta.
Na biyu: aikin mutum shi ne zai fushe shi.
Yanzu kuma za mu saurari ayoyi na 20 da 21 a cikin suratul Tauba kamar haka;
الَّذِينَ آمَنُواْ وَهَاجَرُواْ وَجَاهَدُواْ فِي سَبِيلِ اللّهِ بِأَمْوَالِهِمْ وَأَنفُسِهِمْ أَعْظَمُ دَرَجَةً عِندَ اللّهِ وَأُوْلَئِكَ هُمُ الْفَائِزُونَ{20} يُبَشِّرُهُمْ رَبُّهُم بِرَحْمَةٍ مِّنْهُ وَرِضْوَانٍ وَجَنَّاتٍ لَّهُمْ فِيهَا نَعِيمٌ مُّقِيمٌ{21}
- Wandanda suka yi imani , kuma suka yi hijira , kuma suka yi jihadi , a cikin hanyar Allah. Da dukiyoyinsu , da rayukansu , su ne mafi girma ga daraja . a wurin Allah , kuma wadannan sun e masu babban rabo.
- Ubangijinsu Yana yi musu bishara da wata rahama daga gare shi ,da yarda , da gidajen Aljjan. Suna da , a cikinsu , ni'ima zaunanniya
Wadannan ayoyi na bayani ne kan matsayi da daukaka ta mumuni da nuna darajarsu da fiffikon wadanda suka yi hijira da yin jihadi a kan hanyar Allah da dukiyoyinsu da rayukansu to irin wadannan mumunai sun e suka fi daraja da rabo a tsakanin bayun Allah. Irin wadannan mumunai Allah yana yi masu albishir da da wata rahama daga gare shi da yarda da shiga gidajen aljanna da aka yi masu tanadi da ni'imomi masu yawan gaske. A cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda biyu na farko fitar da zakka na nuni da gaskiyar mai raya imani saboda haka aka bata sunan Sadaka.
Na farko: daraja da daukaka a tsakanin mumunai ta biyo bayan ayyukansu na alheri.
Na biyu: an yi masu tanadi da gidan aljanna mai cike da ni'imomi.
Yanzu kuma za mu fara shirin na yau da sauraren aya ta 22 a cikin suratul Tauba:
خَالِدِينَ فِيهَا أَبَداً إِنَّ اللّهَ عِندَهُ أَجْرٌ عَظِيمٌ{22}
-Suna madawwama a cikinsu , har abada . Lalle Allaaah a wurinsa akwai lada mai girma .
Da kuma wannan ne muka kawo karshen bayani a cikin wannan shiri na yau na hannunka mai sanda da ni Tidjani Malam Lawali Damagaram na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam alaikum warahmatullahi.
Suratut Tauba, Aya Ta 23-27 (Kashi Na 294)
Jama'a masu saurare barkarmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda ,shirin da ke kawo maku bayanai da nasihohi a bangarorin rayuwa da zaman takewar jama' a dukan bangarorin da suka hada da akida,tattalin arziki,al'adu,kasuwanci da kare hakkoki da iya tafiyar da lamurra daidai wadaida ba tare da takurawa kai ko abukkan zama tare ba.Kuma kamar yadda masu saurare suka sani ne muna yin dubi ne kan bayan mun saurare ayoyin alkur'ani mai girma da yake madogara kuma garkuwar musulmi da duk dan adam baki daya matukar yana son yin rayuwa mai tsabta tsarkakekkiya a nuce cikin sauki duniya da lahira. A cikin shirin a makon day a gabata muna magana ne kan suratul Tauba da irin nasihohin da suka kumsa musamman kalubalantar mushrikai da irin matakin da musulmi ya dace su dauka kan mushrikai musamman a wannan guri da lokaci mai tsarki na lukuttan aikin Hajji mai girma da ke a matsayin daya daga cikin cikon na biyar na shika-shikan aikin hajji .A wannan guri da musulmi daga ko'ina a duniya don radin kaisu da kokarin sabke farali ke haduwa a wannan guri mai albarka da suke neman gafarar Allah madaukakin sarki da sanin halin da sauran yan uwansu a kusa da nesa suke ciki tare da tunanin hanyoyin da za su iya taimaka masu wajen kubuta daga cikin wannan mawuyacin halin na lahaula. To a yau ma za mu ci gaba da wannan shiri na hannunka mai sanda ne ta hanyar sauraren ayo ko ayoyin da ke cikin suratul Tauba ko Bara'a amma bayan mun saurari wannan abu da aka yi mana tanadi a kan inji .
Yanzu kuma za mu fara shirin na yau da sauraren aya ta 23 a cikin suratul Tauba:
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُواْ لاَ تَتَّخِذُواْ آبَاءكُمْ وَإِخْوَانَكُمْ أَوْلِيَاء إَنِ اسْتَحَبُّواْ الْكُفْرَ عَلَى الإِيمَانِ وَمَن يَتَوَلَّهُم مِّنكُمْ فَأُوْلَـئِكَ هُمُ الظَّالِمُونَ{23}
-Ya ku wadanda suka yi imanikada ku riki ubanninku day an uwanku masoya . idan sun nuna son kafirci a kan imani . Kuma wanda ya jibince sun e azzalumai .
Su mumunai da a ayoyin da suka gabata suna bayani kan matsayinsu da ayyukansu da irin sakamakon da ke jiransu na shiga gidan aljanna matukar suka shiga a cikin wannan gida mai ni'ima na aljanna za su dauwama a cikinta har abada da samun lada mai yawa a wurin Allah da lada mai girma. Tare da yin kashedi kan wadanda suka yi imani da kar su yi aiki day a yi kama da na mushrikai da kafirai kuma duk wanda ya aikata aiki irin nasu zai kasance tare da su .
A cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda biyu na farko fitar da zakka na nuni da gaskiyar mai raya imani saboda haka aka bata sunan Sadaka.
Na farko: shiga Aljanna shi ne yafi kowa ne irin rabo.
Na biyu:duk wanda ya aikata aiki irin na mushrikai zai tashi tare da su.
To shirin zai ci gaba da sauraren aya ta 24 a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda:
قُلْ إِن كَانَ آبَاؤُكُمْ وَأَبْنَآؤُكُمْ وَإِخْوَانُكُمْ وَأَزْوَاجُكُمْ وَعَشِيرَتُكُمْ وَأَمْوَالٌ اقْتَرَفْتُمُوهَا وَتِجَارَةٌ تَخْشَوْنَ كَسَادَهَا وَمَسَاكِنُ تَرْضَوْنَهَا أَحَبَّ إِلَيْكُم مِّنَ اللّهِ وَرَسُولِهِ وَجِهَادٍ فِي سَبِيلِهِ فَتَرَبَّصُواْ حَتَّى يَأْتِيَ اللّهُ بِأَمْرِهِ وَاللّهُ لاَ يَهْدِي الْقَوْمَ الْفَاسِقِينَ{24}
- Ka ce : Idan ubanninku da diyanku da yan uwanku da matanku da danginku da dukiyoyi ,wadanda kuka yi tsiwiwirinsu , da fatauci wanda kuke tsoro tasgaronsa , da gidaje wadanda kuke yarda da su , sun kasance mafiya soyuwa a gare ku daga Allah da ManzonSa , da yin jihadi ga hanyarSa , to, ku yi jira har Allah ya zo da umurninsa kuma Allah ba ya shirya mutane fasikai .
Har ila yau wannan aya tana ci gaba da bayani kan yadda wasu daga cikin bayun Allah ke banbanta da hada soyayyarsu kan yayansu da uwayensu da dukiyoyinsu da wanda ya halicce su day a kasance majibincin lamarinsu duniya da lahira kuma duk wanda yak e aika irin wannan hali ko shakka babu zai fuskanci fushi da azabar Allah. Kuma ko kusa ba za a taba hadawa a tsakanin mahalicci da wanda aka halitta da mai iko da maras ikon komi sai dai a yi masa.
A cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda biyu na farko fitar da zakka na nuni da gaskiyar mai raya imani saboda haka aka bata sunan Sadaka.
Na farko : babu wanda yafi soyuwa kamar Allah mahalici.
Na biyu: hada soyayya da Allah sabo ne mai girma.
Za mu fara wannan shiri ne da sauraren aya ta 25 a cikin wannan sura ta Tauba kamar haka:
لَقَدْ نَصَرَكُمُ اللّهُ فِي مَوَاطِنَ كَثِيرَةٍ وَيَوْمَ حُنَيْنٍ إِذْ أَعْجَبَتْكُمْ كَثْرَتُكُمْ فَلَمْ تُغْنِ عَنكُمْ شَيْئاً وَضَاقَتْ عَلَيْكُمُ الأَرْضُ بِمَا رَحُبَتْ ثُمَّ وَلَّيْتُم مُّدْبِرِينَ{25}
- Lalle ne , hakika , Alla Ya taimake ku a cikin wurare masu yawa , da Ranar Hunainu , a lokacin da yawanku ya ba ku sha'awa , sai bai amfanar da ku da kome ba , kuma kasa ta yi kunci a kanku da yalwarta sa'an nan kuma y kuka juya kuna masu bayaar da baya .
Wannan aya tana tunatar da mu da ni'imomin Allah masu yawan gaske da kuma yadda Allah ya taimaka mana a wurare masu yawan gaske a rayuwa da ranar Haifuwa. Duk mutuman day a fahimci wannan ni'ima da daraja ta Allah ga bayunsa ko shakka babu zai iya rayuwa cikin sauki da walwala a wannan duniya.Amma idan mutum ya kasa godewa Allah da wannan ni'ima day a yi masa ko shakka babu zai gamu da fushin Allah da kuma yin da na sani a rayuwarsa da shiga cikin kumci na rayuwa.
A cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda biyu na farko fitar da zakka na nuni da gaskiyar mai raya imani saboda haka aka bata sunan Sadaka.
Na farko: godewa ni'ima shi ke sawa a kara samin wata ni'imarsa.
Na biyu:Allah ya kiranmu dam u gode masa domin ya kara yi mana wata ni'imar.
Yanzu kuma za mu saurari aya ta 26 da 27 a cikin suratul Tauba kamar haka:
ثُمَّ أَنَزلَ اللّهُ سَكِينَتَهُ عَلَى رَسُولِهِ وَعَلَى الْمُؤْمِنِينَ وَأَنزَلَ جُنُوداً لَّمْ تَرَوْهَا وَعذَّبَ الَّذِينَ كَفَرُواْ وَذَلِكَ جَزَاء الْكَافِرِينَ{26} ثُمَّ يَتُوبُ اللّهُ مِن بَعْدِ ذَلِكَ عَلَى مَن يَشَاءُ وَاللّهُ غَفُورٌ رَّحِيمٌ{27}
- Sa'an nan kuma Allah Ya saukar da natsuwarSa a kan ManzonSa , kuma a kan miminai , kuma Ya saukar da rundunoni wadanda ba ku gan su ba , kuma Ya azabtar da wadanda suka kafirta : wancan ne sakamakon kafirai . -Sa'an nan kuma Allah Ya karbi tuba daga baya wancan a kan wand Ya so . Kuma Allah ne Mai gafara , Mai rahama .
Samun nucuwa da kanciyar hankali a rayuwa nada matukar muhimmanci da karawa mutum ruhi musamman a filin daga da jihadi. Kamar yadda a cikin tari da dalilan sabkar irin wannan ayoyi ke nuna yadda ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da kuma alayan gidansa ya samu nutsuwa da kuma yadda mumunai wadanda suke tare da shi a wannan fili na jihadi suka samu nutsuwa da kwanciyar hanakli daidai gwalgwado.Kuma da yadda Allah ya yi masu gafara da karbar tubarsu da yi masu rahama a rayuwarsu duniya da lahira.
A cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda biyu na farko fitar da zakka na nuni da gaskiyar mai raya imani saboda haka aka bata sunan Sadaka.
Na farko: samun nutsuwa a rayuwa yanada muhimmanci ainin.
Na biyu: Samun nuwa wata rahama ce daga Allah a tsakanin mbayunsa da ta samo asali daga imani da dogaro.
Da kuma wannan ne muka kawo karshen bayani a cikin wannan shiri na yau na hannunka mai sanda da ni Tidjani Malam Lawali Damagaram na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam alaikum warahmatullahi.
Suratut Tauba, Aya Ta 28-30 (Kashi Na 295)
Jama'a masu saurare barkarmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda ,shirin da ke kawo maku bayanai da nasihohi a bangarorin rayuwa da zaman takewar jama' a dukan bangarorin da suka hada da akida,tattalin arziki,al'adu,kasuwanci da kare hakkoki da iya tafiyar da lamurra daidai wadaida ba tare da takurawa kai ko abukkan zama tare ba.Kuma kamar yadda masu saurare suka sani ne muna yin dubi ne kan bayan mun saurare ayoyin alkur'ani mai girma da yake madogara kuma garkuwar musulmi da duk dan adam baki daya matukar yana son yin rayuwa mai tsabta tsarkakekkiya a nuce cikin sauki duniya da lahira. A cikin shirin a makon day a gabata muna magana ne kan suratul Tauba da irin nasihohin da suka kumsa musamman kalubalantar mushrikai da irin matakin da musulmi ya dace su dauka kan mushrikai musamman a wannan guri da lokaci mai tsarki na lukuttan aikin Hajji mai girma da ke a matsayin daya daga cikin cikon na biyar na shika-shikan aikin hajji .A wannan guri da musulmi daga ko'ina a duniya don radin kaisu da kokarin sabke farali ke haduwa a wannan guri mai albarka da suke neman gafarar Allah madaukakin sarki da sanin halin da sauran yan uwansu a kusa da nesa suke ciki tare da tunanin hanyoyin da za su iya taimaka masu wajen kubuta daga cikin wannan mawuyacin halin na lahaula. To a yau ma za mu ci gaba da wannan shiri na hannunka mai sanda ne ta hanyar sauraren ayo ko ayoyin da ke cikin suratul Tauba ko Bara'a amma bayan mun saurari wannan abu da aka yi mana tanadi a kan inji .
Za mu fara shirin na yau ne da sauraren aya ta 28 a cikin wannan sura ta Tauba kamar haka;
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُواْ إِنَّمَا الْمُشْرِكُونَ نَجَسٌ فَلاَ يَقْرَبُواْ الْمَسْجِدَ الْحَرَامَ بَعْدَ عَامِهِمْ هَـذَا وَإِنْ خِفْتُمْ عَيْلَةً فَسَوْفَ يُغْنِيكُمُ اللّهُ مِن فَضْلِهِ إِن شَاء إِنَّ اللّهَ عَلِيمٌ حَكِيمٌ{28}
-Ya ku wadanda suka yi imani , Abin sani kawai ,mushirikai najasa ne ,saboda haka su kusanci Masallaci Mai alfarma a baya shekararsu wannan . Kuma idan kun ji tsoron talauci , to da sannu Allah zai wadata ku daga falalarSa , Mai Ya so . Lalle Allah ne masani Mai hikima .
A nan Allah madaukakin sarki na ilmantar dam u da sanar dam u wadanda suka yi imani da cewa: su mushrikai najasa ne saboda haka mu han su kusantar masallaci mai alfarma saboda kasancewarsu najasa da ayyukan da suke aikatawa na shurka da saboda. Akwai daga cikin mumunai da musulmi masu tsoran Talauci don haka Allah yak e sanar da su da cewa kar ku ji tsoran talauci domin da sannu Allah zai arzuta mud a arzikinsa kuma arziki na Allah ne da falalarSa kuma Shi ne mai Hikima Masani.
A cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda biyu na farko fitar da zakka na nuni da gaskiyar mai raya imani saboda haka aka bata sunan Sadaka.
Na farko: Allah ne mai arzutawa da bawa kowa rabansa daidai gwalgwado.
Na biyu Tsoran Allah shi ne yafi ba tsoran talauci ba.
Yanzu kuma za mu saurari aya ta 29 da 30a cikin wannan sura ta Tauba kamar haka:
قَاتِلُواْ الَّذِينَ لاَ يُؤْمِنُونَ بِاللّهِ وَلاَ بِالْيَوْمِ الآخِرِ وَلاَ يُحَرِّمُونَ مَا حَرَّمَ اللّهُ وَرَسُولُهُ وَلاَ يَدِينُونَ دِينَ الْحَقِّ مِنَ الَّذِينَ أُوتُواْ الْكِتَابَ حَتَّى يُعْطُواْ الْجِزْيَةَ عَن يَدٍ وَهُمْ صَاغِرُونَ{29} وَقَالَتِ الْيَهُودُ عُزَيْرٌ ابْنُ اللّهِ وَقَالَتْ النَّصَارَى الْمَسِيحُ ابْنُ اللّهِ ذَلِكَ قَوْلُهُم بِأَفْوَاهِهِمْ يُضَاهِؤُونَ قَوْلَ الَّذِينَ كَفَرُواْ مِن قَبْلُ قَاتَلَهُمُ اللّهُ أَنَّى يُؤْفَكُونَ{30}
-Ku yaki wadanda ba su yin imani da Allah kuma ba su yin imani ranar lahira , kuma bas u haramta abin da Allah da ManzonSa suka haramta , kuma ba su yin addini , addinin gaskiya ,daga wadanda aka bai wa Littafi , har sai sun bayay da jizya daga hannu , kuma suna kaskantattu .
- Kuma Yahudawa suka ce :" Uzairu dan Allah ne " . Kuma Nasara suke ce :" Masihu dan Allah ne " . Wancan zancebsu ne da bakunansu . Suna kama da maganar wadand suka kafirta daga gabani.Allah Ya la'ance su , Yaya aka karkatar da su ?
Wadannan ayoyi na kiran mu zuwa ga jihadi da yakar wadanda suka kasance bas u yin imani da Allah da manzonSa Annabin Rahama Muhammadu dan abdullahi tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da kuma alayan gidansa tsarkaka.Kuma ba su yi imani da ranar tashin kiyama ba, bas u yin addinin nba gaskiya madaidaici da imani da littafin Allah to irin wadannan mutaner daga cikin ma'abuta littafi sai su bada jiziya ko a yake su. Daga ciki kuma akawai Yahudawa da suka ce wa ;iyazu billahi Uzairu dan Allah ne yayinda nasara suka ce Masihu dan Allah ne wannan magan ada ikirari da suke ambata da bakinsu ya munana kuma ya yi kama da maganganin wadanda suka kafirta daga gabaninsu Allah ya la'ance su .
A cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda biyu na farko fitar da zakka na nuni da gaskiyar mai raya imani saboda haka aka bata sunan Sadaka.
Na farko: kafiran farko da kafiran yanzu sun yi kama ta fuskar aiki da maganganu.
Na biyu: kirkira karya nada muni a rayuwa dan adam ta addini da kuma ta zamantakewa.
Da kuma wannan ne muka kawo karshen bayani a cikin wannan shiri na yau na hannunka mai sanda da ni Tidjani Malam Lawali Damagaram na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam alaikum warahmatullahi.
Suratut Tauba, Aya Ta 31-35 (Kashi Na 296)
Jama'a masu saurare barkarmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikin shirin wannan shiri muke yi wa junanmu nasiha ta hanyar ayoyin alkur'ani mai girma da hakan zai kasance mana jagora a rayuwa duniya da lahira.
To madalla yanzu kuma lokaci ne da za mu saurari aya ta 31 a cikin suratul Tauba kamar haka:
اتَّخَذُواْ أَحْبَارَهُمْ وَرُهْبَانَهُمْ أَرْبَاباً مِّن دُونِ اللّهِ وَالْمَسِيحَ ابْنَ مَرْيَمَ وَمَا أُمِرُواْ إِلاَّ لِيَعْبُدُواْ إِلَـهاً وَاحِداً لاَّ إِلَـهَ إِلاَّ هُوَ سُبْحَانَهُ عَمَّا يُشْرِكُونَ{31}
Sun dauki malamansu da fada-fadansu da Almasihu dan Maryamu iyayen giji maimakon Allah,alhali kuwa baa bin da aka umarce su sai su bauta wa Ubangiji Makadaicin Sarki,babu wani abin bauta wad a gaskiya sai Shi .Tsarki ya tabbata a gare Shi game da abin da suke hada da Shi.
Mabiya da magoya bayan Annabi Isa (AS) sun fice gona da iri watika saboda tsananin soyayya ko sun jahilce shi da Allan day a halicce shi, dalili kuwa suna fadi da bakinsu cewa: Isa dan Allah ne wa'iyazu billah,alhali yana da kyau su zurfafa tunani da hangen nesa da sanin matsayin Marya ma'aifiyar annabi Isa (AS) kafin su danganta shi da Allah da kai shi matsayin da Allah bai kai shi ba .kuma shi manzo ne daga Allah tabaraka wata'ala day a aiko shi da sako zuwa ga al'ummarsa.Kuma tarihi ya tabbatar Annabawa da Manzonni babu wani a wannan duniya da kuma lahira dad a za su yi wa biyayya face Allah madaukakin sarki da ya aiko shi.
Sai dai wani hamzari ba gudu ba maganar da ta shafi wuce gona da iri da kai wani daga cikin jagororin al'umma wani matsayi da dokaka shi kan karya ba wata matsala ba ce da ta kaibantu da addinin kiristanci,A'a kamar yadda mabiya addinin yahudanci suka yi haka wasu ma daga cikin Musulmai suke irin wannan maganganu da akida ta wuce gona da iri da dokaka wanda suke su kan wani daga cikin waliyan Allah mumunai ,alhali su waliyan Allah kowane irin matsayi da daukaka suka kai kuma a ko ina suke suna bayyana matsayinsu na bayun Allah tare da takama da bautawa Allah shi kadai abin bauta Kuma ko kusa bas u kusanta kansu da da matsayin Allah.
A cikin wannan aya za mu ilmantu da kuma fahimtar wasu abubuwa guda biyu .
Na farko: a kullum mu kwan da sani cewa babu wani mutum da shi ma yake bauta da zai zama abin bauta a gare mu ko mu rike shi a matsayin abin bauta da yin shirka don kawai a kafircewa mahalicci da ya halicci komi da kowa duniya da lahira.
To Madallah yanzu kuma za mu saurari aya ta 32 a cikin wannan sura ta Tauba:
يُرِيدُونَ أَن يُطْفِؤُواْ نُورَ اللّهِ بِأَفْوَاهِهِمْ وَيَأْبَى اللّهُ إِلاَّ أَن يُتِمَّ نُورَهُ وَلَوْ كَرِهَ الْكَافِرُونَ{32}
Suna so ne su dusashe hasken Allah da bakunansu, Allah kuwa ba zai yarda ba sai Ya cika haskensa ko da kuwa kafirai sun ki.Shi ne wanda Ya aiko manzonsa da shiriya da kuma addini na gaskiya don ya dora shi a kan dukannin addini,ko da kuma mushrikai sun ki.
A tsawon tarihi a daidai ku ko a jama'ance da kungiyoyi daban daban-daban da suka shude musamman mahukumta da azzaluman sarakuna da suka kaucewa hanyar adalci da daidaito da riko da gaskiya a kokarinsu na kawar da waliyan Allah da dakushe haskensu da na addinin Allah sun yi amfani da duk wata dama da suke da ita da salo irin makirci da daukan matakai mafi muni.Amma tarihi ya shaida har wannan rana kuma har lokacin da za mu kasance a gaban mai sama Ubangijin talikai za a ci gaba da ambaton suna da ayyukan manzonni da Annabawa da waliyan Allah kuma tarihinsu da duk wani abu da suka bari za su ci gaba da kasancewa tare da al'umma a tsawon lokaci kuma cikin mutumci da girmama su yayinda bah aka lamarin yake ba kan masu girman kai da nuna dagowa a doran kasa domin kuwa ba wai kawai tuna ayyukan da suka tabbaka ba hatta tuna suna da ambaton sunansu ana idasawa ne da la'antarsu da neman tsari da mummunan ayyukan da suka aikata.
Wannan aya tana nuni ne da sunnar Allah da cewa: wasu suna so ne ta hanyar maganganu da yada karya da jita-jita maras tushe su dashe hasken Allah wato hasken musulunci da na waliyansa hatta suna da tarihin ambaton wadannan bayun Allah tsarkaka suna son boyewa da dashewa.Shin suna zaton za su iya dakushe hasken Allah ko kuma ta hanyar kasha wani waliyin Allah sun kawo karshesa da sawa a manta ambatonsa ko sunansa, alhali suna sane hasken Allah ya mamaye ko'ina a duniya tamkar yadda hasken rana daya daga cikin bayunsa ya mamaye duniya baki daya.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da kuma fahimtar abubuwa guda biyu ,na farko shi ne mafi yawa makiya suna kokari ne domin durkushewa da kawo karshen yaduwar addinin Allah ta hanayra maganganu da farfagandar karya saboda haka kar jawabi da maganganu irin wadannan mutane ya yi mana tasiri a rayuwa da akida.
Na biyu yana da kyau koma dole makiya addinin Allah sun san cewa: Allah ya yi alkawarin tabbatar da addininsa a doran kasa kuma nasara ta karshe tag a mumunai da addinin gaskiya kuma duk wani kkari nasu ba zai ci nasara ba har abada.Da fatar za su gane da komo zuwa ga hanya madaidaiciya amin.
Yanzu kuma za mu saurari aya ta 34 a cikin suratul Tauba kamar haka:
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُواْ إِنَّ كَثِيراً مِّنَ الأَحْبَارِ وَالرُّهْبَانِ لَيَأْكُلُونَ أَمْوَالَ النَّاسِ بِالْبَاطِلِ وَيَصُدُّونَ عَن سَبِيلِ اللّهِ وَالَّذِينَ يَكْنِزُونَ الذَّهَبَ وَالْفِضَّةَ وَلاَ يُنفِقُونَهَا فِي سَبِيلِ اللّهِ فَبَشِّرْهُم بِعَذَابٍ أَلِيمٍ{34}
-Ya wadanda suka yi imani Lalle ne masu yawa daga Ahbar da Ruhbanawa , hakika suna cin duniyar mutane da karya , kuma suna kangewa daga hanyar Allah .Kuma wadanda suke taskacewa zinariya da azurfa , kuma bas u ciyar da ita a cikin hanyar Allah, to ka yi musu bushara da azaba mai radadi .
Ya kamata wadanda suka yi imani da bada gaskiya su sani cewa; daga cikin mutane na Ahnbar da Ruhbanawa a wannan duniya suna kirkiro karya da yaudara da hanya mutane bin hanyar Allah madaidaiciya a rayuwa da kuma yadda ya kamata mutum ya yi nazari da kansa domin zabar hanmyar day a gat a dace da rayyuwarsa a wannan duniya. Har ila yau sun kasance masu kin fitar da zakka ko ciyarwa daga abin da Allah ya arzuta sun a dukiya da zinariya da azurfa kuma ka yi masu bushara da azaba mai radadi. A cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda biyu na farko fitar da zakka na nuni da gaskiyar mai raya imani saboda haka aka bata sunan Sadaka.
Na farko:Yada karya na toshe hanyar Allah da addini na hakika.
Na biyu: yada karya wata al'ada ce da ta samo asali tun fil azal.
Yanzu kuma za mu saurari aya ta 35 a cikin wannan suratul Tauba kamar haka;
يَوْمَ يُحْمَى عَلَيْهَا فِي نَارِ جَهَنَّمَ فَتُكْوَى بِهَا جِبَاهُهُمْ وَجُنوبُهُمْ وَظُهُورُهُمْ هَـذَا مَا كَنَزْتُمْ لأَنفُسِكُمْ فَذُوقُواْ مَا كُنتُمْ تَكْنِزُونَ{35}
- A ranar da ake kona shi a kanta a cikin wutar jahannama , sai a yi lalas da ita ga goshinansu da sashinansu da bayayyakinsu , (a ce musu) " wannan ne sbin da kuka taskace domin rayukanku . To ,ku daidani abin da kuka kasan e kuna sanyawa a taska " .
Irin wadannan mutane masu yada karya da kirkiro karyar za su gamu da fushin Allah duniya da lahira da shiga cikin wutar jahannama da aka yi wa kafirai da mushrikai da munafika tanadi ,kuma la'antar Allah ta tabbata a kan wadannan mutane. wadanda za su gamu da fushin Allah a rayuwarsu ta duniya da lahira. A cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda biyu :
Na farko:Masu irin wannan hali karshensu ya munana.
Na biyu: shi makaryaci hatta wadanda suke tare da shi bas u son aikinsa.
Da kuma wannan ne muka kawo karshen bayani a cikin wannan shiri na yau na hannunka mai sanda da ni Tidjani Malam Lawali Damagaram na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam alaikum warahmatullahi.
Suratut Tauba, Aya Ta 36-39 (Kashi Na 297)
Jama'a masu saurare barkarmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda ,shirin da ke kawo maku bayanai da nasihohi a bangarorin rayuwa da zaman takewar jama' a dukan bangarorin da suka hada da akida,tattalin arziki,al'adu,kasuwanci da kare hakkoki da iya tafiyar da lamurra daidai wadaida ba tare da takurawa kai ko abukkan zama tare ba.Kuma kamar yadda masu saurare suka sani ne muna yin dubi ne kan bayan mun saurare ayoyin alkur'ani mai girma da yake madogara kuma garkuwar musulmi da duk dan adam baki daya matukar yana son yin rayuwa mai tsabta tsarkakekkiya a nuce cikin sauki duniya da lahira. A cikin shirin a makon day a gabata muna magana ne kan suratul Tauba da irin nasihohin da suka kumsa musamman kalubalantar mushrikai da irin matakin da musulmi ya dace su dauka kan mushrikai musamman a wannan guri da lokaci mai tsarki na lukuttan aikin Hajji mai girma da ke a matsayin daya daga cikin cikon na biyar na shika-shikan aikin hajji .A wannan guri da musulmi daga ko'ina a duniya don radin kaisu da kokarin sabke farali ke haduwa a wannan guri mai albarka da suke neman gafarar Allah madaukakin sarki da sanin halin da sauran yan uwansu a kusa da nesa suke ciki tare da tunanin hanyoyin da za su iya taimaka masu wajen kubuta daga cikin wannan mawuyacin halin na lahaula. To a yau ma za mu ci gaba da wannan shiri na hannunka mai sanda ne ta hanyar sauraren ayo ko ayoyin da ke cikin suratul Tauba ko Bara'a amma bayan mun saurari wannan abu da aka yi mana tanadi a kan inji .
Yanzu kuma za mu saurari aya ta 36 zuwa 37 a cikin wannan sura ta Tauba kamar haka;
إِنَّ عِدَّةَ الشُّهُورِ عِندَ اللّهِ اثْنَا عَشَرَ شَهْراً فِي كِتَابِ اللّهِ يَوْمَ خَلَقَ السَّمَاوَات وَالأَرْضَ مِنْهَا أَرْبَعَةٌ حُرُمٌ ذَلِكَ الدِّينُ الْقَيِّمُ فَلاَ تَظْلِمُواْ فِيهِنَّ أَنفُسَكُمْ وَقَاتِلُواْ الْمُشْرِكِينَ كَآفَّةً كَمَا يُقَاتِلُونَكُمْ كَآفَّةً وَاعْلَمُواْ أَنَّ اللّهَ مَعَ الْمُتَّقِينَ{36} إِنَّمَا النَّسِيءُ زِيَادَةٌ فِي الْكُفْرِ يُضَلُّ بِهِ الَّذِينَ كَفَرُواْ يُحِلِّونَهُ عَاماً وَيُحَرِّمُونَهُ عَاماً لِّيُوَاطِؤُواْ عِدَّةَ مَا حَرَّمَ اللّهُ فَيُحِلُّواْ مَا حَرَّمَ اللّهُ زُيِّنَ لَهُمْ سُوءُ أَعْمَالِهِمْ وَاللّهُ لاَ يَهْدِي الْقَوْمَ الْكَافِرِينَ{37}
- Lallai ne kidayayyun watanni a wurin Allah wata goma aha biyu ne cikin littafin Allah , a ranar da Ya halicci sammai da kasa cikinsu akwai masu alfarma . Wannan ne adini madidaici .Saboda haka kada ku zalunci kanku a cikinsu .Kuma ku yaki mushirikai gaba daya . kamar yafdda suke yakar ku gaba daya .Kuma ku sani cewa lallai Allah Yana tare da masu takawa .
- Abin sani kawai " Jinkirtawa kare ne a cikin kafirta , ana batar da wadanda suka kafirta game da shi : suna halattar da wat a wata shekara kuma su haramtar da shi a wata shekara domin su dace da adadin da Allah Ya haramta .Saboda haka suna halattar da abin da Allah Ya haramta. An kawace musu munanan ayyukansu .Kuma Allah ba Ya shiryar da mutane kafirai .
Yadda lissafin watanni ya zo a cikin kur'ani mai girma yana nuni da yadda addinin Musulunci yake da tsari kuma ya yi bayanin dalla-dalla a sauwake.Kuma tun ranar da aka halicci sammai da kasai haka lamarin yake akwai watani masu alfarma da hakan ke nuni da addini madaidaici.saboda haka kada mu zalunci kanmu a cikinsa da yakar mushrikai gaba daya kamar yadda suke yakarmu ga daya kuma mu sani cewa; lallai Allah Yana da masu takawa. Akwai watannin da aka hana yin yaki a cikinsu da kuma watannin da bai dace ba a zubar da jinni a cikinsu.
A cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda biyu.
Na farko: akwai watanni masu alfarma day a kama a girmama su.
Na biyu: Yin yaki ya danganta ga wani akwai watan da ba a yaki a cikinsa sai dai kariya da maida martani.
To yanzu kuma za mu saurari aya ta 37 zuwa 39 kamar haka:
إِنَّمَا النَّسِيءُ زِيَادَةٌ فِي الْكُفْرِ يُضَلُّ بِهِ الَّذِينَ كَفَرُواْ يُحِلِّونَهُ عَاماً وَيُحَرِّمُونَهُ عَاماً لِّيُوَاطِؤُواْ عِدَّةَ مَا حَرَّمَ اللّهُ فَيُحِلُّواْ مَا حَرَّمَ اللّهُ زُيِّنَ لَهُمْ سُوءُ أَعْمَالِهِمْ وَاللّهُ لاَ يَهْدِي الْقَوْمَ الْكَافِرِينَ{37} يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُواْ مَا لَكُمْ إِذَا قِيلَ لَكُمُ انفِرُواْ فِي سَبِيلِ اللّهِ اثَّاقَلْتُمْ إِلَى الأَرْضِ أَرَضِيتُم بِالْحَيَاةِ الدُّنْيَا مِنَ الآخِرَةِ فَمَا مَتَاعُ الْحَيَاةِ الدُّنْيَا فِي الآخِرَةِ إِلاَّ قَلِيلٌ{38} إِلاَّ تَنفِرُواْ يُعَذِّبْكُمْ عَذَاباً أَلِيماً وَيَسْتَبْدِلْ قَوْماً غَيْرَكُمْ وَلاَ تَضُرُّوهُ شَيْئاً وَاللّهُ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ{39}
Hakika jinkiri ba wani abu ba ne banda kari cikin kafirci,wanda da shi jinkirin ake batar da wadanda suka kafirta,suna halatta shi a wata shekarar,su kuma haramta shi a wata ,wai don su daidaita adadin abin da Allah ya haramta,sais u halatta abin da Allah ya haramta. An kawata musu munanan ayyukansu,Allah kuwa bay a shiryar da mutane kafirai.
Ya ku wadanda kuka ba da gaskiya, me ya same ku ne idan aka ce da ku ku fita yaki saboda Allah sai ku yi nauyin jiki? Yanzu kun zabi rayuwar duniya a kan ta lahira? ai jin dadin rayuwar duniya abu ne kankani dangane da na lahira.
Idan ba za ku fita yaki ba to Allah zai azabtar da ku da azaba mai radadi,ya kuma canja wasu mutanen daban,ba kuwa za ku cutar da Shi Allah da komai ba. Allah kuwa Mai iko ne a kan komai.
A shekara ta tara hijira kamariya labari ya zo cewa: daular Romaniyawa nada niya da shirin abkawa musulmi da hari.kan haka sai manzon Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayam gidansa ya shirya da tanadin rundunar tsaro ta yan sa kai domin kare kai da addininsu.Amma saboda tsawon lokaci,a bangare guda ana cikin lokacin zafi a wannan yanki na Saudiya bugu da kari kan wannan matsaloli da dalilai guda biyu lokaci ne na kalace abubuwan da aka noma ne .Saboda haka wasu daga cikin musulmi da munafukai suka yi tasiri a kansu a birnin Madina sai suka shiga neman hanyoyin kaucewa zuwa yakin Tabuka. Karkashin wannan dalili ne wadannan ayoyi suke magana kan irin wadannan musulmi da munafikai suka yi masu tasiri da cewa masu shin sun manta da ranar lahira ne da rungumar duniya mai karewa da ita da abubuwan da ke cikinta da juyawa umarnin Allah da zama a gidajensu da kin halartar filin daga da neman uzuri na karya da kaucewa hanya.Shin ba ku sani ba cewa duk ni'imomin da kuke gani a cikin wannan duniya wani bai kai daidai da kwayar zarra ba idan aka kwatamta da ni'imomi da aka yi wa mumunai tanadi a lahira.Kuma abin day a kamata a sani ko da wadannan musulmi ba su je filin daga ba addinin Allah ba zai kasa cin nasara ba kuma Allah zai maye gurin wadannan musulmi da munafikai suka yi tasiri a kansu da wasunsu masu imani da tsarkin zucciya saboda Allah mai iko da kudura wajen kare manzosa da addininsa kuma ba ya bukatar kowa daga cikin irin wadannan mutane.
A cikin wadannan ayoyi za mu iya ilmantuwa da amfanunwa da abubuwa masu yawan gaske ta fuskoki daban-daban na rayuwa da zamantakewa da akida. Daga cikin irin wannan abubuwa sun hada da cewa: gujewa da kaucewa zuwa jihadi da tun karar filin daga ta hanayar sabawa umarnin Allah Tabaraka WaTa'ala kaskanci ne a duniya da lahira da fuskantar mummunan sakamako a lahira.Kuma kar mu yi zaton ta hanyar kin halartar filin daga da jihadi za mu samu kanciyar hankali da wadata a wannan rayuwa ta duniya.
Abu na biyu:Ai water da umarnin Allah ko sabawa umarnisa amfani ko cutar da ke tattare da hakan yana kowa ne a gare mu ba wai ga Allan day a halicce mu ba domin Allah ba ya bukatar ibadarmu ko daidai da kwayar zarra illa iyaka ta hanyar bin umarnisa za mu samu daukaka da daraja duniya da lahira da kuma ta hanyar saba masa samu samu kaskanci da mummunar azaba a duniya da lahira.
To masu saurare da wannan ne kuma za mu dasa aya a cikin wannan shiri na yau da fatar Allah ya ba mu karfin iko da kudura ta aiwatar da umarnisa da karbar ibadodinmu da ta haka mu yi sa'ar gamuwa da ni'imarsa a duniya da lahira da kasancewa karkashin tafarkin ma'aikinsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayansa amin da wannan ne kuma nake cewa wassalamu alaikum warahmatullahi wa barkatuhu.
Suratut Tauba, Aya Ta 40-42 (Kashi Na 298)
Jama'a masu saurare barkarmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda ,shirin da ke kawo maku bayanai da nasihohi a bangarorin rayuwa da zaman takewar jama' a dukan bangarorin da suka hada da akida,tattalin arziki,al'adu,kasuwanci da kare hakkoki da iya tafiyar da lamurra daidai wadaida ba tare da takurawa kai ko abukkan zama tare ba.Kuma kamar yadda masu saurare suka sani ne muna yin dubi ne kan bayan mun saurare ayoyin alkur'ani mai girma da yake madogara kuma garkuwar musulmi da duk dan adam baki daya matukar yana son yin rayuwa mai tsabta tsarkakekkiya a nuce cikin sauki duniya da lahira. A cikin shirin a makon day a gabata muna magana ne kan suratul Tauba da irin nasihohin da suka kumsa musamman kalubalantar mushrikai da irin matakin da musulmi ya dace su dauka kan mushrikai musamman a wannan guri da lokaci mai tsarki na lukuttan aikin Hajji mai girma da ke a matsayin daya daga cikin cikon na biyar na shika-shikan aikin hajji .A wannan guri da musulmi daga ko'ina a duniya don radin kaisu da kokarin sabke farali ke haduwa a wannan guri mai albarka da suke neman gafarar Allah madaukakin sarki da sanin halin da sauran yan uwansu a kusa da nesa suke ciki tare da tunanin hanyoyin da za su iya taimaka masu wajen kubuta daga cikin wannan mawuyacin halin na lahaula. To a yau ma za mu ci gaba da wannan shiri na hannunka mai sanda ne ta hanyar sauraren ayo ko ayoyin da ke cikin suratul Tauba ko Bara'a amma bayan mun saurari wannan abu da aka yi mana tanadi a kan inji .
Za mu farad a sauraren aya ta 40 a cikin wannan sura ta Tauba kamar haka;
إِلاَّ تَنصُرُوهُ فَقَدْ نَصَرَهُ اللّهُ إِذْ أَخْرَجَهُ الَّذِينَ كَفَرُواْ ثَانِيَ اثْنَيْنِ إِذْ هُمَا فِي الْغَارِ إِذْ يَقُولُ لِصَاحِبِهِ لاَ تَحْزَنْ إِنَّ اللّهَ مَعَنَا فَأَنزَلَ اللّهُ سَكِينَتَهُ عَلَيْهِ وَأَيَّدَهُ بِجُنُودٍ لَّمْ تَرَوْهَا وَجَعَلَ كَلِمَةَ الَّذِينَ كَفَرُواْ السُّفْلَى وَكَلِمَةُ اللّهِ هِيَ الْعُلْيَا وَاللّهُ عَزِيزٌ حَكِيمٌ{40}
-Idan ba ku taimake shi ba , to lalle ne Allah ya taimake shi , a lokacin da wadanda suka kafirta suka fitar da shi , yana na biyun biyu , a lokacin da suke cikin kogon dutse . a lokacin da yake cewa da sahibinsa : Kada ka yi bakin ciki , lalle Allah yana tare da mu . Sai Allah Ya saukar da natsuwarsa a kansa , kuma ya taimake shi da wadansu rundunoni , ba ku gan su ba , kuma kafirta makaskanciya , kuma kalmar Allah ita ce madaukakiya . kuma Allah ne mabuwayi ,mai hikima .
Duk mutuman da yake tare da Allah ,Allah ne majibincinsa a rayuwa duniya da lahira har ila yau ya kuma taimake shi .kamar yadda Allah madaukakin sarki ya taimaka wa ma'aikinSa tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da kuma alayan gidansa tsarkaka lokacin da wadanda suka kafirta suka fitar da shi daga birnin Makka.Kuma hatta lokacin da yake tare da sahabinsa a cikin kogon dutse, sahabinsa yana cikin tsoro da fargabar kar masu biye da sahunsu kafire su riske su sai y ace masa kada ka yi bakin ciki ,Hakika Allah yana tare dam u Sai Allah Ya saukar da natsuwarsa a kansa,kuma ya taimake da wadansu rundunono, dab a su gansu bad a kuma kafirta makaskanci har ila yau a kullum kalmar Allah it ace madaukakiya kuma Allah ne mabuwayi mai hikima.
A cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda biyu :
Na farko; duk wanda ya ke tare da Allah to Allah yana tare da shi
Na biyu: natsuwa da dogaro da Allah yana sa kwaciyar hankali.
Yanzu kuma sau aya ta 41 a cikin surar ta Tauba:
انْفِرُواْ خِفَافاً وَثِقَالاً وَجَاهِدُواْ بِأَمْوَالِكُمْ وَأَنفُسِكُمْ فِي سَبِيلِ اللّهِ ذَلِكُمْ خَيْرٌ لَّكُمْ إِن كُنتُمْ تَعْلَمُونَ{41}
41- Ku fitaa masu saukakan kaya da masu nauyi , kuma ku yi jihidi da dukiyoyinku da kuma rayukanku a cikin hanyar Allah .Wancan ne mafi a;hri a gare ku , idan kun kasance kuna sani .
Shi Jihadi a kan musulmi ya wajawa ya yi da rayuwarsa da kuma dunkiyarsa saboda haka ba bu wani lokaci da musulmi ba zai iya yin jihadi ba .Ita dukiya tana taimakwa addini da akida da shi kansa mutm idan ya yi amfani da ita ta hanyar da ta dace da kuma za ta isar da shi zuwa ga madaidaiciyar hanya.To ita wannan duniya za ta iya wajen gwaji da yin guzurin da zai amfane mu a gobe kiyama da a ranar ne ake banbanta dan dima da dan kabewa ma'ana mai aikin alheri da kuma wanda ya aikata lala.
A cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda biyu:
Na farko: mu iya kokarin amfani da dukiyarmu ta hanyar da ta dace.
Na biyu: mu yi lakari da ayar da ke cewa; yayanku da dukiyarku fitina ne.
Za mu saurari aya ta 42 da 43 a cikin surar ta Tauba kamar haka:
لَوْ كَانَ عَرَضاً قَرِيباً وَسَفَراً قَاصِداً لاَّتَّبَعُوكَ وَلَـكِن بَعُدَتْ عَلَيْهِمُ الشُّقَّةُ وَسَيَحْلِفُونَ بِاللّهِ لَوِ اسْتَطَعْنَا لَخَرَجْنَا مَعَكُمْ يُهْلِكُونَ أَنفُسَهُمْ وَاللّهُ يَعْلَمُ إِنَّهُمْ لَكَاذِبُونَ{42} عَفَا اللّهُ عَنكَ لِمَ أَذِنتَ لَهُمْ حَتَّى يَتَبَيَّنَ لَكَ الَّذِينَ صَدَقُواْ وَتَعْلَمَ الْكَاذِبِينَ{43}
Da ya kasance wata sifar duniya ce , makusanciya , da tafiya mtsakaiciya , da sun bi ka . kuma amma fagen ya yi masu nisa . kuma za su yi ta yin rantsuwa da Allah . " Da mun sami dama . da mun tafi tare da ku " . Suna halakar da kansu da ( rantsuwar karya ) ne kuma Allah yana sanin lalle , hakika , su makaryata ne .
-Allah ya yafe maka laifi. Domin me ka yi musu izinin zama ? Sai wadanda suka yi gaskiya sun bayyana a gare ka , kuma ka san makaryata.
Wadannan ayoyi na magana ne kan yadda wasu daga cikin sahabban ma'aikin Allah suka fake da yaudara da karyayyaki domin kin zuwa filin jihadi da daga da kare Musulunci.Amma duk da ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da kuma alayan gidansa ya yafe musu sai Allah ya sanar da shi gaskiya da hakikanin abin da suka boye a cikin zukatansu da cewa suna yaudarar kansu da cutar da kansu ne kawai. Kuma da sannu zai fahimci wadanda suke kan gaskiya ba yaudara ba daga cikin makaryata masu yaudara da zagon kasa.
Da kuma wannan ne muka kawo karshen bayani a cikin wannan shiri na yau na hannunka mai sanda da ni Tidjani Malam Lawali Damagaram na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam alaikum warahmatullahi.
Suratut Tauba, Aya Ta 44-47 (Kashi Na 299)
Jama'a masu saurarenmu barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na Hannunka mai Sanda da a cikinsa muke yiwa junanmu mu masu gabatar da shiri da ku masu saurarenmu nasiha da hannunka mai sanda da fatar hakan ya zame mana jagora a rayuwarmu ta duniya da lahira kuma abokin zama a dukan lamuranmu domin babu wata hanya da iggiya mafi karfi da jiriya kamar alkur'ani mai tsarki da iyalan gidan manzo wadanda abu biyu ne da tushensu daya domin ba su rabuwa daya na fassara daya ne kan haka nema ya kawo mu ga wani hadisin Manzon rahama tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa da ke cewa: mafi fifiko a cikinmu shi ne wanda ya kasance rufe leifin dan uwansa yana kollon nasa leifin don ya gara . To wannan hadisi ya yi hannun riga da halayyarmu a yau da muka fi maida hankali wajen tsegumi da kace nace kan leifuffukan yan uwanmu ba tare da bincike bad a sanin hakikanin lamarin ko dalilin aikata hakan kuma ko da gaskiya ne abin da muke fada ko muka ji to ina yan uwantaka da rufawa juna asiri shin ko mu mun fi karfin aikata abin day a aikata da fatar Allah ya yi masa gafara da zama na gari duniya da lahira .To tsegumi da gulma ba su gyarawa sai dai batawa amma fadakarwa da fata ta gari da rufa asiri su ne siffofi na mutanan kirki bayun Allah masu hakuri da neman gafarar wanda ya zalumce su .Da fatar Allah ya ba mu wani abu daga cikin halayayn bayunsa na gari amin.
Yanzu kuma za mu saurari aya ta 44 zuwa 45 a cikin wannan sura ta tauba kamar haka;
لاَ يَسْتَأْذِنُكَ الَّذِينَ يُؤْمِنُونَ بِاللّهِ وَالْيَوْمِ الآخِرِ أَن يُجَاهِدُواْ بِأَمْوَالِهِمْ وَأَنفُسِهِمْ وَاللّهُ عَلِيمٌ بِالْمُتَّقِينَ{44} إِنَّمَا يَسْتَأْذِنُكَ الَّذِينَ لاَ يُؤْمِنُونَ بِاللّهِ وَالْيَوْمِ الآخِرِ وَارْتَابَتْ قُلُوبُهُمْ فَهُمْ فِي رَيْبِهِمْ يَتَرَدَّدُونَ{45}
- Wadanda suke yin imani da Allah da Ranar Lahira . ba za su nemi izininka ga yi jihadi da dukiyoyinsu da rayukansu ba . Kuma Allah ne masani ga masu takawa .
- Abin sani kawai ,wadanda ba sa imani da Allah da Ranar lahira , kuma zukatansu suka yi shakka , su ne ke neman izininka , sa'an nan a cikin shakkarsu suna ta yin kai kawo .
Wadanda suka yi imani daga cikin sahabban ma'aikin Allah ,annabin rahama Muhammadu dan Abdullahi tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da kuma alayan gidansa tsarkaka sun amince Ma'aiki day a sarra dukiyoyinsu wajen lamarin da ya shafi jihadi da addinin Musulunci ko zuwansu filin jihadi .Kuma Allah ne masani ga masu takawa Kuma wadanda bas u yi imani da Allah da Ranar lahira,kuma zukatansu suka yi shakka,sun e ke neman izininka,sa'an nan a cikin shakkarsu suna ta yin kao kawo. A cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda biyu:
Na farko:Wadanda suka yi imani na hakika sun bambanta da akasinsu.
Na biyu : Imani na hakika ya sha bamban da imani na jabu.
Yanzu kuma za mu saurari aya ta 46 da 47 a cikin wannan sura ta tauba kamar haka;
وَلَوْ أَرَادُواْ الْخُرُوجَ لأَعَدُّواْ لَهُ عُدَّةً وَلَـكِن كَرِهَ اللّهُ انبِعَاثَهُمْ فَثَبَّطَهُمْ وَقِيلَ اقْعُدُواْ مَعَ الْقَاعِدِينَ{46} لَوْ خَرَجُواْ فِيكُم مَّا زَادُوكُمْ إِلاَّ خَبَالاً ولأَوْضَعُواْ خِلاَلَكُمْ يَبْغُونَكُمُ الْفِتْنَةَ وَفِيكُمْ سَمَّاعُونَ لَهُمْ وَاللّهُ عَلِيمٌ بِالظَّالِمِينَ{47}
46-Da kuwa sun yi niyyar fita to da sun yi kyakkaywan tanadi saboda shi yakin ,sai dai kuma Allah Ya ki zaburar das u ,sai Ya dankwafar da su aka kuma ce das u : ku zauna tare da mazauna "gida kamar mata da yara ".
47-Da sun fito tare da ku din,to baa bin da za su kare ku das hi sai rudani,kuma ba shakka da sun yi ta shigi da fici a tsakaninku don haifar muku da fitina, a cikinku kuma akwai masu jin maganarsu. Allah kuwa Yana sane da Azzalimai.
Da kuma wannan ne muka kawo karshen bayani a cikin wannan shiri na yau na hannunka mai sanda da ni Tidjani Malam Lawali Damagaram na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam alaikum warahmatullahi.
Suratut Tauba, Aya Ta 48-52 (Kashi Na 300)
Jama'a masu saurare barkarmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda ,shirin da ke kawo maku bayanai da nasihohi a bangarorin rayuwa da zaman takewar jama' a dukan bangarorin da suka hada da akida,tattalin arziki,al'adu,kasuwanci da kare hakkoki da iya tafiyar da lamurra daidai wadaida ba tare da takurawa kai ko abukkan zama tare ba.Kuma kamar yadda masu saurare suka sani ne muna yin dubi ne kan bayan mun saurare ayoyin alkur'ani mai girma da yake madogara kuma garkuwar musulmi da duk dan adam baki daya matukar yana son yin rayuwa mai tsabta tsarkakekkiya a nuce cikin sauki duniya da lahira. A cikin shirin a makon day a gabata muna magana ne kan suratul Tauba da irin nasihohin da suka kumsa musamman kalubalantar mushrikai da irin matakin da musulmi ya dace su dauka kan mushrikai musamman a wannan guri da lokaci mai tsarki na lukuttan aikin Hajji mai girma da ke a matsayin daya daga cikin cikon na biyar na shika-shikan aikin hajji .A wannan guri da musulmi daga ko'ina a duniya don radin kaisu da kokarin sabke farali ke haduwa a wannan guri mai albarka da suke neman gafarar Allah madaukakin sarki da sanin halin da sauran yan uwansu a kusa da nesa suke ciki tare da tunanin hanyoyin da za su iya taimaka masu wajen kubuta daga cikin wannan mawuyacin halin na lahaula. To a yau ma za mu ci gaba da wannan shiri na hannunka mai sanda ne ta hanyar sauraren ayo ko ayoyin da ke cikin suratul Tauba ko Bara'a amma bayan mun saurari wannan abu da aka yi mana tanadi a kan inji .
Za mu fara sauraren shirin na yau ne da sauraren aya ta 48:
لَقَدِ ابْتَغَوُاْ الْفِتْنَةَ مِن قَبْلُ وَقَلَّبُواْ لَكَ الأُمُورَ حَتَّى جَاء الْحَقُّ وَظَهَرَ أَمْرُ اللّهِ وَهُمْ كَارِهُونَ{48}
48- Kuma lalle ne , hakika ,sun nemi fitina daga gabani, kuma suka juya maka al'amari, har gaskiya ta zo. kuma umurnin Allah Ya bayyana , alhali suna masu kyama.
Wannan aya tana ishara da halayyar munafike da yadda suka kaucewa zuwa filin daga don jihadi lokacin yakin Tabuka da yadda suka ki shiryawa yakin dagangam da neman izini zama a gidajensu a gurin manzon Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa damar zama a gida.A hakikanin gaskiya ba a shirye suke bas u tafi yaki.Saboda haka babu wata alama da niya da suka nuna ta zuwa yaki sabanin mutum mai imani da gaskiya ko dad a gaske wani dalili ya bijiro zai nemi yin aikin day a kamata ya yi don neman yardar Allah . Kuma a hakikanin gaskiya Allah bay a maraba da munafikai a filin daga domin ko sun tafi wata manufa ce ta kai su da yin zagon kasa.
A cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda biyu:
Na farko: komi yana son niya da kokarin mutum.
Na biyu: nasara tana tare ne da kokarin mutum.
Za mu saurari aya ta 49 da 50 a cikin suratul Tauba kamar haka:
وَمِنْهُم مَّن يَقُولُ ائْذَن لِّي وَلاَ تَفْتِنِّي أَلاَ فِي الْفِتْنَةِ سَقَطُواْ وَإِنَّ جَهَنَّمَ لَمُحِيطَةٌ بِالْكَافِرِينَ{49} إِن تُصِبْكَ حَسَنَةٌ تَسُؤْهُمْ وَإِن تُصِبْكَ مُصِيبَةٌ يَقُولُواْ قَدْ أَخَذْنَا أَمْرَنَا مِن قَبْلُ وَيَتَوَلَّواْ وَّهُمْ فَرِحُونَ{50}
-Kuma gada cikinsu akwai mai cewa . " Ka yi mini izinin zama . kuma kada ka fitine ni " . To , acikin fitinar suka fada . Kuma lalle ne Jahannama , hakika . mai kewayewa c ga kafiri .
- Idan wani alheri ya same ka , zai bata masu rai , kuma idan wata masifa ta same ka sai su ce , "Hakika , mun rike al'amarinmu daga gabani " . Kuma su juya . alhali kuwa suna masu farin ciki .
Hatta salon magana da salon yadda munafikai ke tunkarar ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa ya bambanta da yadda suke magana da jawabi da neman izininsa na su zauna a gidajensu a mai makon sun tafi filin daga da yaki da fakewa da karya da yaudara.
A cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda biyu:
Na farko: mai imani na hakika hatta salon maganarsa ya banbanta.
Na biyu: munafikai ana gane sun e ta hanyoyi da dama.
Yanzu kuma za mu saurari aya ta 51 zuwa 52 a cikin wannan sura ta Tauba kamar haka:
قُل لَّن يُصِيبَنَا إِلاَّ مَا كَتَبَ اللّهُ لَنَا هُوَ مَوْلاَنَا وَعَلَى اللّهِ فَلْيَتَوَكَّلِ الْمُؤْمِنُونَ{51} قُلْ هَلْ تَرَبَّصُونَ بِنَا إِلاَّ إِحْدَى الْحُسْنَيَيْنِ وَنَحْنُ نَتَرَبَّصُ بِكُمْ أَن يُصِيبَكُمُ اللّهُ بِعَذَابٍ مِّنْ عِندِهِ أَوْ بِأَيْدِينَا فَتَرَبَّصُواْ إِنَّا مَعَكُم مُّتَرَبِّصُونَ{52}
-Ka ce . " Babu abin da yake samun mu face abin da Allah Ya rubuta saboda mu shi ne Majibincinmu . Kuma ga Allah , sai muminai su dagara ".
- Ka ce . " Shin kuna dako ne da mu ? Face dai da dayan abubuwan biyu masu kyau , alhali kuwa mu , muna dako da ku , Allah Ya same ku da wata azaba daga gare Shi , ko kuwa da hannayenmu . To ku yi dako . Lalle ne mu . tare da ku masu dakon ne".
Idan mutuim ya yi dogaro da Allah babu wani abu da zai same shi sai alheri da sakamako na karfin imaninsa da taimakon Allah .To haka ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa ya kasance baya tsoron maganganu da makircin makiya kafirai mushrikai a lokacin yana birnin Makka da ma lokacin yana birnin Madina.
A cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda biyu:
Na farko; Babu wani abu da zai samu mutum sai abin da Allah ya so.
Na biyu: tsoron bala'i shi kansa bala'i ne kuma dogaro da takawa ke maganinsa.
Da kuma wannan ne muka kawo karshen bayani a cikin wannan shiri na yau na hannunka mai sanda da ni Tidjani Malam Lawali Damagaram na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam alaikum warahmatullahi.
Suratut Tauba, Aya Ta 53-55 (Kashi Na 301)
Jama'a masu saurare barkarmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda ,shirin da ke kawo maku bayanai da nasihohi a bangarorin rayuwa da zaman takewar jama' a dukan bangarorin da suka hada da akida,tattalin arziki,al'adu,kasuwanci da kare hakkoki da iya tafiyar da lamurra daidai wadaida ba tare da takurawa kai ko abukkan zama tare ba.Kuma kamar yadda masu saurare suka sani ne muna yin dubi ne kan bayan mun saurare ayoyin alkur'ani mai girma da yake madogara kuma garkuwar musulmi da duk dan adam baki daya matukar yana son yin rayuwa mai tsabta tsarkakekkiya a nuce cikin sauki duniya da lahira. A cikin shirin a makon day a gabata muna magana ne kan suratul Tauba da irin nasihohin da suka kumsa musamman kalubalantar mushrikai da irin matakin da musulmi ya dace su dauka kan mushrikai musamman a wannan guri da lokaci mai tsarki na lukuttan aikin Hajji mai girma da ke a matsayin daya daga cikin cikon na biyar na shika-shikan aikin hajji .A wannan guri da musulmi daga ko'ina a duniya don radin kaisu da kokarin sabke farali ke haduwa a wannan guri mai albarka da suke neman gafarar Allah madaukakin sarki da sanin halin da sauran yan uwansu a kusa da nesa suke ciki tare da tunanin hanyoyin da za su iya taimaka masu wajen kubuta daga cikin wannan mawuyacin halin na lahaula. To a yau ma za mu ci gaba da wannan shiri na hannunka mai sanda ne ta hanyar sauraren ayo ko ayoyin da ke cikin suratul Tauba ko Bara'a amma bayan mun saurari wannan abu da aka yi mana tanadi a kan inji .
Za mu fara da sauraren ayoyi na 53 da 54 a cikin suratul Tauba kamar haka:
قُلْ أَنفِقُواْ طَوْعاً أَوْ كَرْهاً لَّن يُتَقَبَّلَ مِنكُمْ إِنَّكُمْ كُنتُمْ قَوْماً فَاسِقِينَ{53} وَمَا مَنَعَهُمْ أَن تُقْبَلَ مِنْهُمْ نَفَقَاتُهُمْ إِلاَّ أَنَّهُمْ كَفَرُواْ بِاللّهِ وَبِرَسُولِهِ وَلاَ يَأْتُونَ الصَّلاَةَ إِلاَّ وَهُمْ كُسَالَى وَلاَ يُنفِقُونَ إِلاَّ وَهُمْ كَارِهُونَ{54}
- Ka ce,Ku ciyar akan yarda ko kuwa a kan tilas . Ba za a karba daga gare ku ba . Lalle ne ku kun kasance mutane fasukai. -Kuma babu abin da ya hana a karbi ciyarwarsu daga gare su face domin su , sun kafirta da Allah ManzonSa, kuma ba su zuwa ga salla face Luma suna masu kasala , kuma ba su ciyarwa face suna masu kyama.
Wadannan ayoyi na yin furici ne kan fasikai da cewa ko su ciyar kan yarda ko kuma su ciyar kan tilastawa ba a za a karbi wannan ciyarwa ta su ,Da hakan ke nufi da cewa komi mutum zai yi ya yi shi kan imani da dogaro da Allah da neman yardarsa matukar yana son ya samu cira da aminci da sakamako mai kyau na alheri a rayuwarsa da addininsa duniya da lahira.
A cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda biyu:
Na farko: fasikai komi za su yi suna sa fasikanci a cikinsa.
Yanzu kuma sai aya ta 55 a cikin suratul Tauba kamar haka:
فَلاَ تُعْجِبْكَ أَمْوَالُهُمْ وَلاَ أَوْلاَدُهُمْ إِنَّمَا يُرِيدُ اللّهُ لِيُعَذِّبَهُم بِهَا فِي الْحَيَاةِ الدُّنْيَا وَتَزْهَقَ أَنفُسُهُمْ وَهُمْ كَافِرُونَ{55}
- Saboda haka . kada dukiyoyinsu su ba ka sha'awa, kuma haka ya yansu.Abin sani kawai , Allah Yana nufin Ya yi musu azaba da su a cikin rayuwar duniya , kuma rayukansu su fita alhaki kuwa suna kafirai .
Dukiya da tarinta da kafirai da mushrikai suka tara kar sub a mu sha'awa da mamaki kuma haka yawan yaya da suka tara ya bam u sha'awa da birge mu domin abin fahimta a nan Allah yana iya yi masu azaba da dukiyar da suka tara ko yayan da suka tara saboda za a yi masu azaba da ta hanyar dukiyar da suka tara da yaya kamar yadda aya wata ayar ke cewa dukiyoyinku da ya yanku duka fitina ne a gare ku.
A cikin wannan aya za mu ilmantu da:
Na farko; ita dukiya a yi amfani da ita ta hanyar da ta dace da cecon mai ita. Haka yayan mutum .
Da kuma wannan ne muka kawo karshen bayani a cikin wannan shiri na yau na hannunka mai sanda da ni Tidjani Malam Lawali Damagaram na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam alaikum warahmatullahi.
Suratut Tauba, Aya Ta 56-59 (Kashi Na 302)
Jama'a masu saurarenmu barker da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke yi wa kawunanmu hannunka mai sanda karkashin ayoyin Alkur'ani mai tsarka da ke zama babban jagora a rayuwarmu ta addini da zamnatakewa da duk wani bangare na rayuwa a yau.
To madallah a yau za mu saurari aya ta 56 da ta 57 a cikin wannan sura ta Tauba kamar haka:
وَيَحْلِفُونَ بِاللّهِ إِنَّهُمْ لَمِنكُمْ وَمَا هُم مِّنكُمْ وَلَـكِنَّهُمْ قَوْمٌ يَفْرَقُونَ{56} لَوْ يَجِدُونَ مَلْجَأً أَوْ مَغَارَاتٍ أَوْ مُدَّخَلاً لَّوَلَّوْاْ إِلَيْهِ وَهُمْ يَجْمَحُونَ{57}
Sukan kuma rantse da Allah cewa: lallai suna tare da ku alhali kuwa bas a tare da ku,sai dai kuma su mutane ne da suka jin tsoron. Da za su sami wata mafaka ko wani kogo ko wani kurfi,to da sun juya zuwa gare shi suna masu gaggawa.
A cikin shirin da ya gabata mun yi nuni da munanan halayan munafikai ta bangarori daban-daban a lokacin da manzon Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayansa ke raye.Wannan aya tana nuni ne da raunin ruhinsu da nuna kasawa da cewa: duk da karfi da dunbin arziki da munafikai ked a su amma wani lokaci koma yancin lokaci duk da cewa bas u tare da ku amma suna tsananin tsoranku da rantse-rantsen karya da neman hanyar samun kubuta daga hannun Muminai ko amincin don tsoro amma bayan sun kasance suna kullawa Muminai makirci da yaudara .
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu na farko rantse-rantse da saukin yin rantsuwa babu dalili ma'ana yin rantsuwa kan karya alama ce ta ayyukan munafikai.
Abu na biyu: Munafinci yana wargaza al'umma da daidaita da kawo baraka a tsakanin jama'a da wargaza hadin kai a tsakani.
Yanzu kuma za mu saurari ayoyi na 58 zuwa 59 a cikin wannan sura ta Tauba kamar haka:
وَمِنْهُم مَّن يَلْمِزُكَ فِي الصَّدَقَاتِ فَإِنْ أُعْطُواْ مِنْهَا رَضُواْ وَإِن لَّمْ يُعْطَوْاْ مِنهَا إِذَا هُمْ يَسْخَطُونَ{58} وَلَوْ أَنَّهُمْ رَضُوْاْ مَا آتَاهُمُ اللّهُ وَرَسُولُهُ وَقَالُواْ حَسْبُنَا اللّهُ سَيُؤْتِينَا اللّهُ مِن فَضْلِهِ وَرَسُولُهُ إِنَّا إِلَى اللّهِ رَاغِبُونَ{59}
Daga cikinsu kuma akwai wadanda suke aibata ka game da rabon sadaka,da an bas u wani abu daga cikinta to da sai su gamsu,idan kuwa ba a bas u daga cikinta ba sai ka gan su suna fushi. Da kuwa za su yarda da abin da Allah da Manzonsa suka ba su, su kuma ce: Allah Shi ne Ma'ishinmu kuma Allah zai ba mu daga falalarsa tare da Manzonsa.Hakika mu masu kwadayi ne a wurin Allah.
Wadannan ayoyi suna nuni ne kan munanan halayen munafikai da cewa; lokacin raba Zakka ko kuma lokacin fitar da zakka don munafinci hatta Manzon Allah kuma Manzon rahama da adalci suna zarginsa da rashin adalci da yin suka da yada karya da munafinci kan haka a tsakanin jama'a don kawai kar su fitar da Zakka da ta rataya a wuyan duk wani musulmi mai hali. Kuma abin bakin ciki da ban hanushi ba suna haka neb a don neman adalci da gaskiya a tsakanin jama'a face makirci da yaudara kuma duk lokacin da suka samu wani abu daga cikin abubuwan da aka fitar na Zakka sai su yi shiru da nuna amincewarsu a fili karara babu kumya balantana tsoran Allah ,amma duk lokacin dab a su sami wani abu ba daga zakka sai su nuna fushi da kiyayyarsu a fili da fito da maitarsu a fili da fadin karyayyaki da bakunansu.
Ci gaban aya ta 59 na cewa: a maimakon nuna kwadayi da hadama kan kudaden Zakka da daya daga cikin falsafar fitar da ita taimakawa gajiyayyu da mabukata ,sai su godewa Allah da wannan lutufi da falala tasa da yin dogaro ga Allah da cewa mun godewa Allah day a bamu lafiya da karfi da wadata da kuma arzita mu da imani da kuma rahamominsa ba iyaka.
A cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa guda biyu abu na farko:kar mu damu da bakaken kalamai da batanci da ke fitowa daga bakin munafikai na ciki a tsakaninmu domin wannan it ace hanyarsu da suke amfani ta neman isa da munafincinsu na dodar duniya da arzikin da ke cikinta mai karewa ko su samu ko ba su samu ba wannan shi ne halinsu.
Abu na biyu: Mu ba mu bin Allah bashi duk abun da muka samu a wannan duniya da lahira da kuma halittarmu da ya yi wata falala da lutifinsa ne kawai don haka dole mu gamsu da kautar da ya yi mana da gode masa kan haka.Amma ga wanda ya fahimta da samin haka da kuma alfanon da ke tattare da gode masa ko dadi ko wahala da tsanani shi arziki ne.
Da fatar Allah ya kara fadakar dam u sanin hakan amin da kuma wannan fatar ce ni Tidjani Malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar da wannan shiri na yau na ke cewa sai mako na sama idan mai duka ya sada mud a alherinsa amin na ke cewa wassalamu alaikum warahmatullahi wabarkatuhu.
Suratut Tauba, Aya Ta 60-65 (Kashi Na 303)
Jama'a masu saurarenmu barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na Hannunka mia sanda da a cikin wannan shiri muke farawa da yi wa kawunanmu mu masu gabatar da shirin nasiha da hannunka mai sanda karkashin yin dubi da nasihohin da suka zo a cikin Alkur'ani mai girma kana daga bisani mu mika irin wadannan nasihohi da tunatarwa ga masu saurarenmu.Kuma kamar yadda muka yi gado a wajen jagorori da malummai da limaman gidan shiriya tsarakaka (AS) da kuma fiyayyan halitta manzon rahama Muhammadu dan Abdullahi tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa da a tsawon rayuwarsu suke fadakar da mu da nasihantar da mu a dukan bangarori na rayuwa da addini kamar yadda dama shi addini nasiha ne .A nan ba za mu manta da hadisin Manzon Allah (SW) da ke cewa: shi musulmi madibi ne ga dan uwansa ma'ana duk wani lahani na zahiri da na badini da ka gain gad an uwanka sai ka shaida masa da kuma rufa masa asiri illa iyaka ka yi kokarin tsarkake shi day aye masa wannan abu ba wai ka fallasa shi ku barin wannan abu ya cutar da shi da fatar Allah ya ba mu karfi da ikon taimakawa yan uwanmu na jinni da na addini da zama cikin hadin kai da kaunar juna amin.
To madallah yanzu kuma za mu ci gaba da shirin na yau na Hannunka mai sanda tare da sauraren aya ta 60 da 61 da 62a cikin suratul Tauba kamar haka:
إِنَّمَا الصَّدَقَاتُ لِلْفُقَرَاء وَالْمَسَاكِينِ وَالْعَامِلِينَ عَلَيْهَا وَالْمُؤَلَّفَةِ قُلُوبُهُمْ وَفِي الرِّقَابِ وَالْغَارِمِينَ وَفِي سَبِيلِ اللّهِ وَابْنِ السَّبِيلِ فَرِيضَةً مِّنَ اللّهِ وَاللّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٌ{60} وَمِنْهُمُ الَّذِينَ يُؤْذُونَ النَّبِيَّ وَيِقُولُونَ هُوَ أُذُنٌ قُلْ أُذُنُ خَيْرٍ لَّكُمْ يُؤْمِنُ بِاللّهِ وَيُؤْمِنُ لِلْمُؤْمِنِينَ وَرَحْمَةٌ لِّلَّذِينَ آمَنُواْ مِنكُمْ وَالَّذِينَ يُؤْذُونَ رَسُولَ اللّهِ لَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ{61} يَحْلِفُونَ بِاللّهِ لَكُمْ لِيُرْضُوكُمْ وَاللّهُ وَرَسُولُهُ أَحَقُّ أَن يُرْضُوهُ إِن كَانُواْ مُؤْمِنِينَ{62}
- Ita zakka ana ba da ita ne kawai ga matalauta da miskinai da ma'aikatanta da wadanda aka jawo hankulansu zuwa ga musulinci da kuma game da yenta bayi ,da wadanda bashi ya kewaye da kuma wajan jihadi saboda Allah da matafiyi wanda guzurinsa ya yanke. Wannan hukunci wajibi ne daga Allah.Allah kuwa Masani ne Gwani.
-Daga cikinsu kuma akwai wadanda suke cutar Annabi suna kuma cewa: "Shi mai saurare ne kawai" Ka ce da su 'Shi mai sauraren alheri ne don ya isar da shi gare ku; yana ba da gaskiya da Allah, yana kuma gaskata muminai, kuma rahama ne ga wadanda suka ba da gaskiya daga cikinku'. Wadanda kuwa suke cutar Manzon Allah suna da (sakamakon) azaba mai radadi.
- Suna rantsuwa da Allah saboda ku , domin su yarda da ku . Kuma Allah da ManzonSa ne mafi cancantar su yarda da shi , idan sun kasance muninai .
Wasu daga cikin mutane na kwadayin samu wani abu daga cikin abubuwan da aka fitar na Zakka kuma kamar yadda ayoyin da suka gabata munafikai na gunguni da fadin bakaken kalamai kan Manzon Adalci da Rahama (SW) kan Zakka. To wannan aya ta yi bayani dalla-dalla kan wadanda suka Cancanci da hakki a cikin abubuwan da aka fitar na Zakka kamar yadda wajibi ne a fitar wa dukiya Zakka haka kuma wajibi a bawa wadannan mutane da wannan aya ta ambato da cewa: Zakka ana fitar da ita ce daga dukiyoyi domin isar da ita ga talakkawa ko talakkan da talauci ya addabe shi da ba shi da karfin kula da rayuwarsa ko kuma ba shi da karfin iya neman nakansa.Har ila yau ana fitar da zakka da mai bulaguro da guzurinsa yak are masa a kan hanya.Kuma ana fitar da Zakka ga wadanda ba musulmai ba saboda a kwadaitar da zukatansu ,sai don saye da sayarwa, idan yaki ya fuskanci musulmi za a iya amfani da Zakka wajen kula da mujahidai, hatta masu aiki na tattaro da Zakka suna nasu kason a ciki.
Abin kayatarwa ne da lura cewa a cikin Alkur'ani yawanci duk inda aka yi maganar zakka tana tare da maganar Sallah kuma karkashin ruwayoyi karba da amincewa da sallolinmu ya ta'allaka da fitar da zakka.Wannan lamari yana kara kusanci tsakanin Allah da halittarsa bayunsa.Kuma ba don irin wadannan hanyoyi da babu wata halitta da za ta sami kusanci da Mahalicci.har ila yau karkashin ruwayoyi ,Allah madaukakin sarki ya cusa hakkin mabukata a cikin dukiyoyin masu kugi da arziki kuma da ace masu dukiya da hali na fitar da zakka kamar yadda ya dace da ba za a sami wani talakka a doran kasa ba .Allahu Akbar ka ji hikima ta Allah da kuma falalarsa amma kaiconmu da ba mu tausayawa kawunanmu da sanin hakkin day a rataya a wuyanmu da kuma amfanin na komawa ne a gare mu. Kuma Zakka tana kara yawan arziki ne da tsarkake shi daga gurbacewa da asara.
Ba dole Zakka ta kasance cikin abubuwa takwas tana iya kasancewa karkashin kulawar jagora maia dalci musulmi da zai sarrafa ta ta hanyar da ta dace daidai abin da ake bukata. Ita Zakka wata hanya ce daidaita al'umma da bambancin matsayinsu na rayuwa tsakanin talakka da mai kudi, ita Zakka ruhi ne na kawo kaunar juna a tsakanin dan adam da kawar da duk wani tunani na rungumar wannan duniya da dukiya.Zakka tana kara yawan arzikin rayuwar jama'a ta zamantakewa ta inda za a rage da ma kawar da matsaloli na dabi'a kamar talauci,bashi,rashin lafiya da sauran matsaloli na kudi da hakan zai sake bawa masu fama da irin wadannan matsaloli da na ambato dama da karfin guiwar sake rayuwa.Zakka tana daya daga cikin shika-shikan musulunci kuma it ace hanya mafi dacewa wajen yaki da talauci da aiwatar da adalci na zamantakewa.
Yanzu za mu saurari aya ta 63 a cikin wannan sura ta Tauba kamar haka:
أَلَمْ يَعْلَمُواْ أَنَّهُ مَن يُحَادِدِ اللّهَ وَرَسُولَهُ فَأَنَّ لَهُ نَارَ جَهَنَّمَ خَالِداً فِيهَا ذَلِكَ الْخِزْيُ الْعَظِيمُ{63}
-Shin , ba su sani ba cewa , "lalle ne wanda ya saba wa Allah da ManzonSa , hakika yana da wutar jahannama . yana madawwami a cikinta ? Waccan ita ce wulakantawa babba.
Daga ranar da aka aiko ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da kuma alayan gidansa tsarkaka har zuwa ranar tashin kiyama' ya zama wajibi a gare mum u bi da yin koyi da ma'aikin Allah da yin hani da haninsa amma a dabra da haka mu sani cewa duk wanda ya bijirewa umarnin ma'aikin Allah da haninsa makomarsa utar jahannama da kuma zai dauwama a cikin wutar da fatar Allah ya kiyashe mud a irin wannan mummunan karshe.
Abin fahimta a nan shi yin koyi da umarnin ma'aikin Allah ya zama wajibi.
Yanzu kuma za mu saurari aya ta 64 zuwa 65 a cikin wannan sura ta tauba kamar haka:
يَحْذَرُ الْمُنَافِقُونَ أَن تُنَزَّلَ عَلَيْهِمْ سُورَةٌ تُنَبِّئُهُمْ بِمَا فِي قُلُوبِهِم قُلِ اسْتَهْزِئُواْ إِنَّ اللّهَ مُخْرِجٌ مَّا تَحْذَرُونَ{64} وَلَئِن سَأَلْتَهُمْ لَيَقُولُنَّ إِنَّمَا كُنَّا نَخُوضُ وَنَلْعَبُ قُلْ أَبِاللّهِ وَآيَاتِهِ وَرَسُولِهِ كُنتُمْ تَسْتَهْزِئُونَ{65}
-Munafukai suna tsoron a saukar da wata sura akansu , wadda take ba su labari ga abin da yake cikin zukatansu. Ka ce , "ku yi izgili. Lallena, Allah ne , Mai fitar da abin da kuke tsoro .
-Kuma lalle ne , idan ka tambaye , su hakika , suna cewa " Abin sani kawai , mun kasance muna hira kuma muna wasa . " Ka ce , Shin da Allah , da kuma ayoyinSa da ManzonSa kuka kasance kuna izgili.
A kullum munafikai suna cikin tsoro da fargabar kar wata aya ta sabka da ke magana kan abubuwa da suka boye a cikin zukatansu mummuna da fahimtar hakikaninsu da ayyukan da suke aikatawa sabanin abin da suke bayyanawa a zahiri. Hatta a maganganunsu da jawabansu haka lamarin yake ana ganewa da ganin halin da suke ciki na tsoro da fargaba.
A cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda biyu:
Na farko: manufikai suna cikin fargaba kamar yadda maras gaskiya ko a cikin ruwa sai ya yi jibi.
Na biyu kwanciyar hankali tana ga mai gaskiya.
Da kuma wannan ne muka kawo karshen bayani a cikin wannan shiri na yau na hannunka mai sanda da ni Tidjani Malam Lawali Damagaram na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam alaikum warahmatullahi.
Suratut Tauba, Aya Ta 66-70 (Kashi Na 304)
Jama'a masu saurare barkarmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda ,shirin da ke kawo maku bayanai da nasihohi a bangarorin rayuwa da zaman takewar jama' a dukan bangarorin da suka hada da akida,tattalin arziki,al'adu,kasuwanci da kare hakkoki da iya tafiyar da lamurra daidai wadaida ba tare da takurawa kai ko abukkan zama tare ba.Kuma kamar yadda masu saurare suka sani ne muna yin dubi ne kan bayan mun saurare ayoyin alkur'ani mai girma da yake madogara kuma garkuwar musulmi da duk dan adam baki daya matukar yana son yin rayuwa mai tsabta tsarkakekkiya a nuce cikin sauki duniya da lahira. A cikin shirin a makon day a gabata muna magana ne kan suratul Tauba da irin nasihohin da suka kumsa musamman kalubalantar mushrikai da irin matakin da musulmi ya dace su dauka kan mushrikai musamman a wannan guri da lokaci mai tsarki na lukuttan aikin Hajji mai girma da ke a matsayin daya daga cikin cikon na biyar na shika-shikan aikin hajji .A wannan guri da musulmi daga ko'ina a duniya don radin kaisu da kokarin sabke farali ke haduwa a wannan guri mai albarka da suke neman gafarar Allah madaukakin sarki da sanin halin da sauran yan uwansu a kusa da nesa suke ciki tare da tunanin hanyoyin da za su iya taimaka masu wajen kubuta daga cikin wannan mawuyacin halin na lahaula. To a yau ma za mu ci gaba da wannan shiri na hannunka mai sanda ne ta hanyar sauraren ayo ko ayoyin da ke cikin suratul Tauba ko Bara'a amma bayan mun saurari wannan abu da aka yi mana tanadi a kan inji .
Yanzu kuma za mu saurari aya ta 66 zuwa da 67 a cikin wannan sura ta Tauba kamar haka:
لاَ تَعْتَذِرُواْ قَدْ كَفَرْتُم بَعْدَ إِيمَانِكُمْ إِن نَّعْفُ عَن طَآئِفَةٍ مِّنكُمْ نُعَذِّبْ طَآئِفَةً بِأَنَّهُمْ كَانُواْ مُجْرِمِينَ{66} الْمُنَافِقُونَ وَالْمُنَافِقَاتُ بَعْضُهُم مِّن بَعْضٍ يَأْمُرُونَ بِالْمُنكَرِ وَيَنْهَوْنَ عَنِ الْمَعْرُوفِ وَيَقْبِضُونَ أَيْدِيَهُمْ نَسُواْ اللّهَ فَنَسِيَهُمْ إِنَّ الْمُنَافِقِينَ هُمُ الْفَاسِقُونَ{67}
- Kada ku kawo wani uzuri , hakika , kun kafirta a bayan imaninku . Idan Mun yafe laile ga wata kungiya daga gare ku, za Mu azabta wata kungiya saboda , lalle , sun kasance masu laifi.
- Munafukai maza da munnafukai mata . sashensu daga sashe , suna umurni da abin ki . kuma suna hani daga alheri .Kuma suna damkewar hannuyensu .Sun mance Allah , sai Ya manta da su .Lalle ne munafukai su ne fasikai .
Akwai laifin da mutum idan ya aikata shi ya fe masa yanada wuya kuma ya dandangata da irin niyarsa kan wannan aiki da kuma hakikanin niyarsa ta tuba daga aikata wannan aiki,kuma wani lokaci mutane biyu za su aikata wani aiki mai muni amma sai a yafewa daya dayan kuma a azabtar da shi kamar yadda wannan aya ta ke bada misali da kungiyoyi biyu na munafikai da yadda suke yin kira zuwa ga aikata mummuna da hana aikata alheri kuma su munafikai akwai su a cikin maza kamar yadda akwai su a cikin mata.To irin wadannan mutane masu sha'afa da akwai Allah shi ma Allah yana mantawa da su wato ya kale su da aikinsu.
A cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda biyu :
Na farko; munafinci babu banbanci tsakanin mata da maza.
Na biyu: niyar mutum ita ce kimarsa da aikinsa.
Za mu saurari aya ta 68 a cikin wannan sura ta Tauba kamar haka:
وَعَدَ الله الْمُنَافِقِينَ وَالْمُنَافِقَاتِ وَالْكُفَّارَ نَارَ جَهَنَّمَ خَالِدِينَ فِيهَا هِيَ حَسْبُهُمْ وَلَعَنَهُمُ اللّهُ وَلَهُمْ عَذَابٌ مُّقِيمٌ{68}
Allah ya yi wa'adi ga munafukai maza da munafukai mata da kafirai da wutar Jahannama , suna madawwama a cikinta. Ita ce ma'ishiyarsu.Kuma Allah Ya la'ance su , kuma suna da azaba zaunanniya
A ranar tashin kiyama munafikai za su wayi gari da tayar da su tare da kafirai da mushrikai a cikin wutar jahannama alhali kuwa a lokacin suna rayuwa a wannan duniya a zahiri da yaudararsu suna nuna suna tare ne da musulmi da mumunai ashe a hakikanin gaskiya suna tare ne da kafirai don haka sai a tayar da su tare da su a gobe kiyama. Bugu da kari za su kasance masu dawwama a cikin wutar jahannama tare da la'antar Allah a kansu da yi masu tanadin azaba.
A cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda biyu :.
Na farko; duk abin da kake tare da shi da shi ne za a tayar da kai a kiyama.
Na biyu: kafirai da munafikai makomarsu daya duniya da lahira.
Yanzu kuma za mu saurari aya ta 69 zuwa 70 a cikin suratul Tauba kamar haka:
كَالَّذِينَ مِن قَبْلِكُمْ كَانُواْ أَشَدَّ مِنكُمْ قُوَّةً وَأَكْثَرَ أَمْوَالاً وَأَوْلاَداً فَاسْتَمْتَعُواْ بِخَلاقِهِمْ فَاسْتَمْتَعْتُم بِخَلاَقِكُمْ كَمَا اسْتَمْتَعَ الَّذِينَ مِن قَبْلِكُمْ بِخَلاَقِهِمْ وَخُضْتُمْ كَالَّذِي خَاضُواْ أُوْلَـئِكَ حَبِطَتْ أَعْمَالُهُمْ فِي الُّدنْيَا وَالآخِرَةِ وَأُوْلَئِكَ هُمُ الْخَاسِرُونَ{69} أَلَمْ يَأْتِهِمْ نَبَأُ الَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ قَوْمِ نُوحٍ وَعَادٍ وَثَمُودَ وَقَوْمِ إِبْرَاهِيمَ وِأَصْحَابِ مَدْيَنَ وَالْمُؤْتَفِكَاتِ أَتَتْهُمْ رُسُلُهُم بِالْبَيِّنَاتِ فَمَا كَانَ اللّهُ لِيَظْلِمَهُمْ وَلَـكِن كَانُواْ أَنفُسَهُمْ يَظْلِمُونَ{70}
- Kamar wadanda suke a gabaninku , sun kasance mafi tsananin karfi daga gare ku , kuma mafi yawan dukiyoyi da diya .Sai suka ji dadi da rabonsu ,sai kuka ji dadi rabonku kamar yadda wadanda suke a gabaninku suka ji dadi , da rabonsu, kuma kuka kutsa kamar kutsawarsu. Wadancan ayyukansu sun baci a duniya da Lahira , kuma wadannan su ne masu hasara .
-Shin , labarin wadanda suke a gabaninsu bai ja musu ba , mutanen Nuhu da Adaw DA Samudawa da mutanen Ibrahim da Ma'abuta Madyana da wadanda aka birkice? Manzanninsu sun je musu da ayoyi bayyanannu . To Allah bai kasance Yana zaluntar su ba , amma sun kasance rayukansu suke zalunta.
Wannan aya tana tunatar da kafirai ne da tambayarsu shin labarin kafirai da ma'abuta girman kai na mutanan annabi Nuhu (AS) da Adawa da samudawa da mutanan Annabi Ibrahima (AS) da ma'abuta Madyana mutanan Annabi Shu'aibu (AS) da sukansu aka azabtar da su da kawar da su daga doran kasa saboda da sabon.Domin kuwa Manzonni sun zo masu da ayoyi bayyanannu amma suka kafirce da nuna dagawa a doran kasa.Kuma Allah bai zalunce sub a sun kasance suna zaluntar kansu ne kawai.
A cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda biyu :
Na farko; jin labarin mutanan da suka gabata zai zame masu darasi.
Na biyu;ji da wane ya isa wane zoran Allah.
Da kuma wannan ne muka kawo karshen bayani a cikin wannan shiri na yau na hannunka mai sanda da ni Tidjani Malam Lawali Damagaram na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam alaikum warahmatullahi.
Suratut Tauba, Aya Ta 71-73 (Kashi Na 305)
Jama'a masu saurare barkarmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda ,shirin da ke kawo maku bayanai da nasihohi a bangarorin rayuwa da zaman takewar jama' a dukan bangarorin da suka hada da akida,tattalin arziki,al'adu,kasuwanci da kare hakkoki da iya tafiyar da lamurra daidai wadaida ba tare da takurawa kai ko abukkan zama tare ba.Kuma kamar yadda masu saurare suka sani ne muna yin dubi ne kan bayan mun saurare ayoyin alkur'ani mai girma da yake madogara kuma garkuwar musulmi da duk dan adam baki daya matukar yana son yin rayuwa mai tsabta tsarkakekkiya a nuce cikin sauki duniya da lahira. A cikin shirin a makon day a gabata muna magana ne kan suratul Tauba da irin nasihohin da suka kumsa musamman kalubalantar mushrikai da irin matakin da musulmi ya dace su dauka kan mushrikai musamman a wannan guri da lokaci mai tsarki na lukuttan aikin Hajji mai girma da ke a matsayin daya daga cikin cikon na biyar na shika-shikan aikin hajji .A wannan guri da musulmi daga ko'ina a duniya don radin kaisu da kokarin sabke farali ke haduwa a wannan guri mai albarka da suke neman gafarar Allah madaukakin sarki da sanin halin da sauran yan uwansu a kusa da nesa suke ciki tare da tunanin hanyoyin da za su iya taimaka masu wajen kubuta daga cikin wannan mawuyacin halin na lahaula. To a yau ma za mu ci gaba da wannan shiri na hannunka mai sanda ne ta hanyar sauraren ayo ko ayoyin da ke cikin suratul Tauba ko Bara'a amma bayan mun saurari wannan abu da aka yi mana tanadi a kan inji .
Yanzu kuma za mu saurari aya ta 71 a cikin suratul Tauba kamar haka;
وَالْمُؤْمِنُونَ وَالْمُؤْمِنَاتُ بَعْضُهُمْ أَوْلِيَاء بَعْضٍ يَأْمُرُونَ بِالْمَعْرُوفِ وَيَنْهَوْنَ عَنِ الْمُنكَرِ وَيُقِيمُونَ الصَّلاَةَ وَيُؤْتُونَ الزَّكَاةَ وَيُطِيعُونَ اللّهَ وَرَسُولَهُ أُوْلَـئِكَ سَيَرْحَمُهُمُ اللّهُ إِنَّ اللّهَ عَزِيزٌ حَكِيمٌ{71}
- Kuma mummunai maza da mummunai mata sashensu majibinsin sashe ne , suna umurni da alheri kuma suna hani daga abin da ba sa a so , kuma suna tsayar da salla , kuma suna bayar da zakka , kuma sanu da'a ga Allah da ManzonSA . Wadanda Allah zai yi musu rahama .Lalle ne Mabuwayi , Mai hikima .
Su mumunai maza da mumunai mata suna taimakawa junansu ne kamar yadda wani hadisi yake cewa: shi mumuni madubi ne ga mumuni idan ya ga wani abu da zai taimaka masa zai bayyana masa da kuma taimaka masa .idan kuma wani abu na alheri ne zai so dan uwansa ya samu da amfana da shi tamkar yadda yake sowa kansa.Suna tsayar da salla da fitar da zakka da yin da'a da biyayya ga Allah madaukakin sarki da ma'aikinsa tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka.Bugu da kari rahamar Allah ta lullube irin wadannan mutane mumunai ,kuma Allah mai Hikima da Mabuwayi.
A cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda biyu :
Na farko:Mumunai na taimakawa junansu a kullum.
Na biyu:akwai ayoyi da hadisai da dama da suka yi magana irin wannan.
Yanzu kuma za mu saurari aya ta 72 da 73
وَعَدَ اللّهُ الْمُؤْمِنِينَ وَالْمُؤْمِنَاتِ جَنَّاتٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا وَمَسَاكِنَ طَيِّبَةً فِي جَنَّاتِ عَدْنٍ وَرِضْوَانٌ مِّنَ اللّهِ أَكْبَرُ ذَلِكَ هُوَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ{72} يَا أَيُّهَا النَّبِيُّ جَاهِدِ الْكُفَّارَ وَالْمُنَافِقِينَ وَاغْلُظْ عَلَيْهِمْ وَمَأْوَاهُمْ جَهَنَّمُ وَبِئْسَ الْمَصِيرُ{73}
- Kuma Allah Yayi wa'adi ga mummunai maza da mummunai mata da gidajen Aljanna koramu suna gudana daga karkashinsu , suna madawwama a cikinsu , da wuraren zama masu dadia cikin gidajen Aljannar .Kuma yarda daga Allah ce mafi girma .Wancan shi ne babban rabo , mai girma .
- Ya kai Annabi Ka yaki kafirai da munafukai kuma ka tsaurara a kansu .Kuma matatararsu. JAHANAMA Ce Tir da ta zama makomar.
Aljanna makoma ce ga mumunai maza da mumunai mata da a cikinta koramu ke gudana karkashinta kuma za su dawwama a cikinta saboda Allah ne ya yi masu alkawali da a cikinta akwai guraren zama da gidaje masu kyayatarwa ga kuma babbar nasara yarda da amincewar Allah mai girma to wannan ai shi ne rabo kuma mai girma.Kan haka sai Allah ya umarci ma'aikinsa dfa ya yaki kafirai da munafikai da tsananta a kansu da kuma wutar jahannama ce makomarsu.
A cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda biyu:
Na farko:aljanna makoma ce ga mumunai.
Na biyu ita kuwa wutar jahannama makoma ce ga kafirai da munafikai.
Da kuma wannan ne muka kawo karshen bayani a cikin wannan shiri na yau na hannunka mai sanda da ni Tidjani Malam Lawali Damagaram na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam alaikum warahmatullahi.
Suratut Tauba, Aya Ta 74-79 (Kashi Na 306)
Jama'a masu saurare barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke yi wa kawunanmu mu masu gabatar da shirin hannunka mai sanda da kuma yiwa junanmu nasiha kan abubuwan da idan muka yi aiki da su ko shakka babu za mu inganta rayuwarmu a wannan duniya da kuma uwa uba addininmu da zamantakewarmu ta daidaiku ko ta cudani in cudeka. Kuma har yanzu muna cikin ci gaba da bayani da bin diddigin irin nasihohin da suka zo a cikin suratul Tauba da abubuwan da ayoyin wannan sura suka kumsa ba suka yi daidai da abubuwan da ke wakana a rayuwarmu ta yau da kullum da kuma daidai da abubuwan da suka wakana a tsawon tarihi don haka a nan idan muka yi aiki da abin day an iya magana Hausa ke fadi zai amfane mu wato gani da wane ya isa wane tsoran Allah da fatar Allah ya bamu karfin aiki da wannan Karin magana amin.
Yanzu kuma za mu saurari aya ta 74 a cikin suratul Tauba kamar haka:
يَحْلِفُونَ بِاللّهِ مَا قَالُواْ وَلَقَدْ قَالُواْ كَلِمَةَ الْكُفْرِ وَكَفَرُواْ بَعْدَ إِسْلاَمِهِمْ وَهَمُّواْ بِمَا لَمْ يَنَالُواْ وَمَا نَقَمُواْ إِلاَّ أَنْ أَغْنَاهُمُ اللّهُ وَرَسُولُهُ مِن فَضْلِهِ فَإِن يَتُوبُواْ يَكُ خَيْراً لَّهُمْ وَإِن يَتَوَلَّوْا يُعَذِّبْهُمُ اللّهُ عَذَاباً أَلِيماً فِي الدُّنْيَا وَالآخِرَةِ وَمَا لَهُمْ فِي الأَرْضِ مِن وَلِيٍّ وَلاَ نَصِيرٍ{74}
-Suna rantsuwa da Allah , ba su fada ba , alhali kuwa lalle ne hakika , sun fadi kalmar kafirci , kuma sun kafirta a bayan musuluntarsu , kuma sun yi himma ga abin da ba su samu ba .Kuma ba su zargi kome ba face domin Allah da ManzonSa Ya wadatar da su daga falarSa . To, idan sun tuba zai kasance mafi alheri gare su, kuma idan sun juya baya zai kasabce mafi alheri gare su , kuma idan juya baya, Allah zai azabta d da azaba mai radadi a cikin duniya da Lahira , kuma ba su da wani masoyi ko wani mataimaki a cikin kasa.
Bayan wasu munafikai da wadanda suka yi rida sun musanta cewa bas u furta kalmar kafirci Allah yana tabbatar masu da cewa; sun kafirta bayan musuluntarsu,kuma sun yi himma da kokari kana bin da ba su samu ba.Wannan kuwa ya biyo bayan irin ni'imar da Allah ya yi masu a maimakon su gode masa sai suka kafirta da wannan falala da Allah ya yi masu.To idan sun tuba zai kasance mafi alheri a gare su,kuma idan sun juya baya zai kasance mafi alheri a gare su duniya da lahira,kuma idan sun juya baya ,to su san cewa Allah zai azabtar da su azaba mai radadi da zafin kuna a cikin duniya da lahira ba tare da wani ya taimake sub a da kubutar da su.
A cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda biyu :.
Na farko:Yin rida nada mummunan sakamako.
Na biyu: shi Musulunci yana bukatar sibaci.
Yanzu kuma za mu saurari aya ta 75 zuwa 76 a cikin wannan sura ta Tauba kamar haka;
وَمِنْهُم مَّنْ عَاهَدَ اللّهَ لَئِنْ آتَانَا مِن فَضْلِهِ لَنَصَّدَّقَنَّ وَلَنَكُونَنَّ مِنَ الصَّالِحِينَ{75} فَلَمَّا آتَاهُم مِّن فَضْلِهِ بَخِلُواْ بِهِ وَتَوَلَّواْ وَّهُم مُّعْرِضُونَ{76}
- Kuma daga cikinsu akwai wadanda suka yi wa Allah alkawari , Lalle ne idan ya kawo mana daga falalarSa , hakika , muna bayar da sadaka , kuma lalle ne muna kasancewa daga salihai .
- To, a lokacin da Ya ba su daga falalarSa , sai suka yi rowa da shi, kuma suka juya baya suna masu bijirewa .
Yin Alkawari wani lokaci yana da dadi amma mafi muhimmanci shi ne cika alkawari, kuma babu alkawari da ked a hadari kamar wanda ake yi wad a kullawa tare da Allah madaukakin sarki .kamar yadda munafikae da wadanda suka yi rida suka yi wa Allah alkawari cewa; idan ya sabkar mana da falalarsa za mu yi sadaka da kuma uwa uba za su kasance daga cikin salihai.Amma a lokacin day a bas u daga falalarsa sai suka yi rowa da abin da aka bas u da kin cika alkawalin da suka yi da juya baya na zama mutane salihai.
A cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda biyu :.
Na farko: yin Alkawari nada dadi amma cikawar.
Yanzu kuma za mu fara wannan shiri na hannunka mai sanda da sauraren aya ta 77 zuwa da 78
فَأَعْقَبَهُمْ نِفَاقاً فِي قُلُوبِهِمْ إِلَى يَوْمِ يَلْقَوْنَهُ بِمَا أَخْلَفُواْ اللّهَ مَا وَعَدُوهُ وَبِمَا كَانُواْ يَكْذِبُونَ{77} أَلَمْ يَعْلَمُواْ أَنَّ اللّهَ يَعْلَمُ سِرَّهُمْ وَنَجْوَاهُمْ وَأَنَّ اللّهَ عَلاَّمُ الْغُيُوبِ{78}
- Sai Ya biyar musu da munafunci a cikin zakatansu har zuwa ga ranar da suke haduwa da shi , saboda saba wa Allah ga abin da suka yi Masa alkawari , kuma saboda abin da suka kasance suna yi na karya .
- Shin, ba su sani ba cewa lalle ne Allah Yana sanin asirinsu da ganawarsu , kuma lalle Allah ne Masanin abubuwan fake?
Akwai ranar kin dillalanci domin kuwa munafikai sun boye munafinci a cikin zukatansu inda a ranar kiyama za su hadu da Allah madaukakin sarki zai bayyana masu hakikanin abin da suka boye ba don komi ba saboda sun saba wa Allah ga abin da suka yi masa alkawari,kuma saboda abin da suka kasance suna yin a karya.Wannan ya nuna sun sha'afa da mantawa da cewa Allah ne masanin abubuwan da suka boye kuma shi masanin abubuwan da ke fake.
A cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda biyu:
Na farko:a lahira kowa zai bayyana da hakikaninsa na badini.
Na biyu: a wannan rana babu wani boye-boye da munafinci.
Yanzu kuma za mu saurari aya ta 79 a cikin wannan sura ta Tauba kamar haka:
الَّذِينَ يَلْمِزُونَ الْمُطَّوِّعِينَ مِنَ الْمُؤْمِنِينَ فِي الصَّدَقَاتِ وَالَّذِينَ لاَ يَجِدُونَ إِلاَّ جُهْدَهُمْ فَيَسْخَرُونَ مِنْهُمْ سَخِرَ اللّهُ مِنْهُمْ وَلَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ{79}
- Wadanda suke aibanta masu yin alheridaga mummunai a cikin dukiyoyin sadaka , da wadanda ba su samu face iyakar kokarinsu , sai suna yi musu izgili . Allah Yana yinizgili gare su .Kuma suns da azaba mai radadi.
A wannan lokaci akwai wasu mutane musamman wadanda suka yi rida da wadanda suke munafikai suna yi wa mumunai masu imani da bada sadaka izgili da yi masu habeci da kaskantar da su ,da kuma yi wa masu kokari daga cikinsu irin wannan izgili,to su sani Allah yana maida masu da izgilin da suke yi kuma za su samu mummunan sakamako da azabtar da su.
A cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda biyu:
Na farko:shi mai izgili abi san ana ganinsa ba.
Na biyu: yi wa mumuni dariya da izgili leifi ne mai girma.
Da kuma wannan ne muka kawo karshen bayani a cikin wannan shiri na yau na hannunka mai sanda da ni Tidjani Malam Lawali Damagaram na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam alaikum warahmatullahi.
Suratut Tauba, Aya Ta 80-85 (Kashi Na 307)
Jama'a masu saurare barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke yi wa kawunanmu mu masu gabatar da shirin hannunka mai sanda da kuma yiwa junanmu nasiha kan abubuwan da idan muka yi aiki da su ko shakka babu za mu inganta rayuwarmu a wannan duniya da kuma uwa uba addininmu da zamantakewarmu ta daidaiku ko ta cudani in cudeka. Kuma har yanzu muna cikin ci gaba da bayani da bin diddigin irin nasihohin da suka zo a cikin suratul Tauba da abubuwan da ayoyin wannan sura suka kumsa ba suka yi daidai da abubuwan da ke wakana a rayuwarmu ta yau da kullum da kuma daidai da abubuwan da suka wakana a tsawon tarihi don haka a nan idan muka yi aiki da abin day an iya magana Hausa ke fadi zai amfane mu wato gani da wane ya isa wane tsoran Allah da fatar Allah ya bamu karfin aiki da wannan Karin magana amin.
Yanzu kuma za mu saurari aya ta 80 a cikin suratul Tauba kamar haka;
اسْتَغْفِرْ لَهُمْ أَوْ لاَ تَسْتَغْفِرْ لَهُمْ إِن تَسْتَغْفِرْ لَهُمْ سَبْعِينَ مَرَّةً فَلَن يَغْفِرَ اللّهُ لَهُمْ ذَلِكَ بِأَنَّهُمْ كَفَرُواْ بِاللّهِ وَرَسُولِهِ وَاللّهُ لاَ يَهْدِي الْقَوْمَ الْفَاسِقِينَ{80}
80- Ko ka nema musu gafara ko ba ka nema musu ba , idan ka nema musu gafara sau saba'in , to , Allah ba zai gafarta musu ba .Saboda su , sun kafirta da Allah da ManzonSa . Kuma Allah ba Ya shiryar da mutane fasikai .
Wannan shi ne babban kalubalai da nuna kawo karshen kafircin munafikai domin Allah ya bayyana karara cewa ko da kuwa ma'aikin Allah mai rahama da jin kai zai nemarwa munafikai gafara sau saba'in ,Allah ba zai gafarta masu ba saboda sun kafirta da Allah da manzonsa ,kuma Allah ba Ya shiryar da mutea fasikai. Masu yaudarar kansu da kuma yaudarar wadanda suke rayuwa tare da su ,Alhali kuwa sun manta cewa wanda ya halicce yafi kowa sanin Abin da suka boye a zukatansu.
A cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda biyu :.
Na farko:kafirci da munafinci na kaiwa matsayin dab a a iya komowa baya.
Na biyu:kafirci yana kai wa wani matsayi da munafinci na karshe dab a a iya kai wag a tuba.
Yanzu kuma za mu saurari aya ta 81 zuwa 82 a cikin wannan sura ta Tauba kamar haka;
فَرِحَ الْمُخَلَّفُونَ بِمَقْعَدِهِمْ خِلاَفَ رَسُولِ اللّهِ وَكَرِهُواْ أَن يُجَاهِدُواْ بِأَمْوَالِهِمْ وَأَنفُسِهِمْ فِي سَبِيلِ اللّهِ وَقَالُواْ لاَ تَنفِرُواْ فِي الْحَرِّ قُلْ نَارُ جَهَنَّمَ أَشَدُّ حَرّاً لَّوْ كَانُوا يَفْقَهُونَ{81} فَلْيَضْحَكُواْ قَلِيلاً وَلْيَبْكُواْ كَثِيراً جَزَاء بِمَا كَانُواْ يَكْسِبُونَ{82}
- Wadanda aka bari sun yi farin ciki da zamansu a bayan Manzon Allah , kuma suka ki su yi jihadi da dukiyiyinsu da rayukansu a cikin hanyar Allah , kuma suka ce , : Kada ku fitA zuwa yaki a cikin zafi . " Ka ce , Wutar Jahannama ce mafi tsananin zafi. " Da sun kasance suna fahimta .
- Saboda haka su yi dariya kadan , kuma su yi kuka da yawa a kan sakamako ga abin da suka kasance suna tsirfatawa .
Wadanda suka ki zuwa jihadi da zama a gidajensu tamkar mata sun yi ta nuna farinciki da jin dadi saboda sun yi zamansu a gidajensu kuma suka ki su yi jihadi da dukiyoyinsu a rayukansu a cikin hanyar Allah, kuma suka ce ,kada ku fita zuwa yaki a cikin zafi ka ce, wutar jahannama ce mafi tsananin zafi,da sun kasance suna fahimta. Ma'ana su munafikai sun manta cewa wutar jahannama tafi komi zafi da tsananin kuna kuma duk wani zafi ai ba za a iya kwatamta shi bad a zafin ranar tashin kiyama da zafin wutar janahhama,saboda haka su yi dariya ta sun ki zuwa yaki da jihadi amma za su yi kuka mai yawa sakamakon wannan aiki nasu mummuna na kafirci da munafinci.
A cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda biyu:
Na farko; Karshen lamari shi ne yake da muhimmanci ba farkonsa ba.
Na biyu: sakamakon lahira shi ne yafi muhimmanci ba jin dadin wannan duniya ba.
Yanzu kuma za mu saurari aya ta 83 a cikin wannan sura ta Tauba kamar haka;
فَإِن رَّجَعَكَ اللّهُ إِلَى طَآئِفَةٍ مِّنْهُمْ فَاسْتَأْذَنُوكَ لِلْخُرُوجِ فَقُل لَّن تَخْرُجُواْ مَعِيَ أَبَداً وَلَن تُقَاتِلُواْ مَعِيَ عَدُوّاً إِنَّكُمْ رَضِيتُم بِالْقُعُودِ أَوَّلَ مَرَّةٍ فَاقْعُدُواْ مَعَ الْخَالِفِينَ{83}
To , idan Allah Ya mayar da kau zuwa ga wata kungiya daga gare su , sa'an nan suka neme ka izni domin su fita , to , ka ce , " ba za ku fita tare da ni ba har abada , kuma ba za ku yi yaki tare da ni ba akan wani mkiyi. Lalle ne ku , kun yarda da zama a farkon lokaci ,sai ku zauna tare da mata masu zaman gida ".
Wadanda suka yaudari kansu da farko suka kasance sun fake da lamari na karya domin ma'aikin Allah mai tsira da amincin Allah ya amince ya bas u izinin zama a gida domin kaucewa jihadi da rayukansu da kuma dukiyarsu,su sani da cewa ko da sun nemi izni a wajen ma'aikin Allah bayan wani lokaci da kasancewarsu a cikin wata kungiyar ta daban su sani ba za su samu wannan izini ban a zuwa jihadi domin sun bata baya da gaba ba za a taba amincewa da su ba za su ci gaba da zama a cikin gida ne har abada tare da mata.
A cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda biyu :.
Na farko;leifi daya na iya zama na har abada.
Na biyu;shinleifi ba shi da karami balantana babba.
Yanzu kuma za mu saurari aya ta 84 zuwa da 85 a cikin wannan sura ta tauba kamar haka;
وَلاَ تُصَلِّ عَلَى أَحَدٍ مِّنْهُم مَّاتَ أَبَداً وَلاَ تَقُمْ عَلَىَ قَبْرِهِ إِنَّهُمْ كَفَرُواْ بِاللّهِ وَرَسُولِهِ وَمَاتُواْ وَهُمْ فَاسِقُونَ{84} وَلاَ تُعْجِبْكَ أَمْوَالُهُمْ وَأَوْلاَدُهُمْ إِنَّمَا يُرِيدُ اللّهُ أَن يُعَذِّبَهُم بِهَا فِي الدُّنْيَا وَتَزْهَقَ أَنفُسُهُمْ وَهُمْ كَافِرُونَ{85}
- Kuma kada ka yi salla a kan kowa daga cikinsu wanda ya mutu , har abada . kuma kada ka tsaya a kan kabarinsa . Lalle ne su , sun kafirta da Allahda ManzonSA , kuma sun mutu alhali kuwa suna fasikai.
- Kuma kada dukiyoyinsu da diyansu su ba ka sha'awa . Abin sani kawai , Allah Yana nufin Ya yi musu azaba da su a cikin duniya , kuma rayukansu su fita alhali kuwa suna kafirai .
Hatta yi wa mamaci sallar gawa idan ya mutu Allah ya hana ma'aikinsa manzon tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da kuma Alayansa tsarkaka ya yi masu salla har abada,bugu da kari kar ya tsaya a kan kabarinsa domin yi masa addu'a domin lokacin suna raye sun kafirta da Allah da kuma ma'aikinsa da mutuwa cikin aikata fasikanci da sabo. Musulmi da mumunai kar dukiyoyin da yayansu manafikai da kafirai sub a ku sha'awa abin sani kawai Allah yana son yi masu azaba da su yayansu da dukiyoyinsu a cikin duniya ta inda wani lokaci yaynsu su zama makiyansu da adawa da su da kuma hana su shakatawa shakat.
A cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda biyu :.
Na farko;yi wa mutummsallah dole sai ya kasance musulmi.
Na biyu; kuma ana ziyarar kabarin musulmi ne domin yi masa addu'a.
Da kuma wannan ne muka kawo karshen bayani a cikin wannan shiri na yau na hannunka mai sanda da ni Tidjani Malam Lawali Damagaram na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam alaikum warahmatullahi.
Suratut Tauba, Aya Ta 86-90 (Kashi Na 308)
Jama'a masu saurare barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke yi wa kawunanmu mu masu gabatar da shirin hannunka mai sanda da kuma yiwa junanmu nasiha kan abubuwan da idan muka yi aiki da su ko shakka babu za mu inganta rayuwarmu a wannan duniya da kuma uwa uba addininmu da zamantakewarmu ta daidaiku ko ta cudani in cudeka. Kuma har yanzu muna cikin ci gaba da bayani da bin diddigin irin nasihohin da suka zo a cikin suratul Tauba da abubuwan da ayoyin wannan sura suka kumsa ba suka yi daidai da abubuwan da ke wakana a rayuwarmu ta yau da kullum da kuma daidai da abubuwan da suka wakana a tsawon tarihi don haka a nan idan muka yi aiki da abin day an iya magana Hausa ke fadi zai amfane mu wato gani da wane ya isa wane tsoran Allah da fatar Allah ya bamu karfin aiki da wannan Karin magana amin.
Yanzu kuma za mu saurari aya ta 86 a cikin suratul Tauba kamar haka;
وَإِذَا أُنزِلَتْ سُورَةٌ أَنْ آمِنُواْ بِاللّهِ وَجَاهِدُواْ مَعَ رَسُولِهِ اسْتَأْذَنَكَ أُوْلُواْ الطَّوْلِ مِنْهُمْ وَقَالُواْ ذَرْنَا نَكُن مَّعَ الْقَاعِدِينَ{86}
- Kuma idan aka saukar da wata sura cewa : Ku yi imani da Alla kuma ku yi jihadi tare da ManzonSa . Aai mawadata daga gare su su nemi izininka , kuma su ce Ka bar mu mu kasance tare da mazauna.
A duk lokacin da wata aya daga cikin ayoyin kur'ani ta sabka tana kiransu da su tafi jihadi da yakar kafirai da makiya musulmi da Musulunci domin anzuwar Addinin Musulunci ta hanyar Allah da manzonsa sai su nemi zama a gida da izinin barinsu a gidaje tare da mata kuma yawanci masu irin wannan mummunan hali sun e masu wadata daga cikin al'umma shin suna sha'afa da cewa Allah ne mai wadata da wadatar da kowa a wannan duniya.Kuma arziki da wadata duk nashi ne hatta raid a suke takama da shi nashi ne.
A cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda biyu :.
Na farko; Masu wadat suna kin zuwa jihadi ne fiye da wadanda bas u alhali jihadi ya wajaba kan kowa ne da mai arziki da talaka.
Na biyu;:hanyar jihadi tana da yawa ko ta rai ko kuma ta dukiya.
Yanzu kuma za mu saurari aya ta 87 a cikin wannan sura tavtauba kamar haka:
رَضُواْ بِأَن يَكُونُواْ مَعَ الْخَوَالِفِ وَطُبِعَ عَلَى قُلُوبِهِمْ فَهُمْ لاَ يَفْقَهُونَ{87}
87- Sun yarda da su kasance tare da mata masu zama (a cikin gidaje). Kuma aka rufe a kan zukatansu, saboda haka, su, ba su fahimta .
Munafikai suna yaudarar kansu a daidai lokacin da suke sha'afa da cewa; ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da kuma alayan gidansa manzo ne daga Allah madaukakin sarki da kuma ya san abin da suke boyewa a cikin zukatansu kuma neman izinin zama a gidajensu wani abu ne wanda tuni Allah ya san da haka da kuma ya sanar da ma'aikin Allah manzon rahama hakikanin abin da suka boye a zucci to idan haka suke so su zauna a gida to sai su zauna a gidajensu tare da mata mazauna gida.
A cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda biyu :.
Na farko;wani lokaci mutum na aiki dab a shi da banbanci da mace.
Na biyu; mace da ke zaune a gida da aikin kan hanyar Allah yafi namjin da ya zauna a gida daraja a gurin Allah madaukakin sarki.
To madallah yanzu kuma lokaci ne da za mu saurari aya ta 88 zuwa da 89 a cikin wannan sura ta Tauba kamar haka:
لَـكِنِ الرَّسُولُ وَالَّذِينَ آمَنُواْ مَعَهُ جَاهَدُواْ بِأَمْوَالِهِمْ وَأَنفُسِهِمْ وَأُوْلَـئِكَ لَهُمُ الْخَيْرَاتُ وَأُوْلَـئِكَ هُمُ الْمُفْلِحُونَ{88} أَعَدَّ اللّهُ لَهُمْ جَنَّاتٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا ذَلِكَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ{89}
-Amma shi Manzon da wadanda suka ba da gaskiya tare da shi sun yi yaki da dukiyoyinsu da kuma kawunansu.Wadannan kuwa suna da sakamakon alheri kuma wadannan sun e marabauta. -Allah ya tanadar musu aljannoni wadanda koramu suke gudana ta karkashinsu,madawwama a cikinsu. Wannan shi ne rabo mai girma.
Wannan aya tana bayani kan kan yadda mumunai da waliya gami da musulmai na hakika kai sadaukar da raid a rayuwarsu da dukiyoyinmu domin kare addinin musulunci da musulmi kuma suna bayar da dukiya da rayukansu wajen fuskantar kafirai da munafikai kuma wannan ne ya bambanta munikai dab a su iya sadaukar da raid a dukiyarsu don kare addini face ma suna rungumar kafirci ne da munafinci domin tara dukiyoyi da mallakar yaya ta kowace hanya da zalumci. Kuma wannan dabi'a ce ta wadanda suka yi imani da bada gaskiya na su rungumi gaskiya da abin da Allah ya yi masu tanadi a wannan duniya na imani da kuma lahira na gidan Aljanna da gujewa mummunan sakamako da aka yi wa munafikai da kafirai tanadi na gidan jahannama da azaba mai radadi mai kuna makomar wadanda suka karya da kafircewa da kuma uwa uba munafikai.
To a cikin wannan ayoyi za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu masu kima da daraja kamar haka: Na farko Munafikai tun farko bas u tare da Manzon Allah balantana su sadaukar da raid a dukiyoyinsu don kare addini da Manzon Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka. Sabanin muminai na hakika da a kullum suke tare da Manzon da kuma kare shi da addininsa.
Abu na biyu:Imani da Manzon Allah kadai bai wadatar ba yana bukatar lazimtarsa da nuna kokari da sadaukar da rayuwa da dukiya wajen yada addini da kare shi.
To madalla yanzu kuma za mu saurari aya ta 90 a cikin wannan sura ta tauba kamar haka:
وَجَاء الْمُعَذِّرُونَ مِنَ الأَعْرَابِ لِيُؤْذَنَ لَهُمْ وَقَعَدَ الَّذِينَ كَذَبُواْ اللّهَ وَرَسُولَهُ سَيُصِيبُ الَّذِينَ كَفَرُواْ مِنْهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ{90}
Masu kawo uzurin karya daga larabawan kauye kuma suka zo don a yi musu izini,sai kuma wadanda suka yiwa Allah da Manzonsa karya suka yi zamansu bad a kawo hanzari ba . To azaba mai radadi za ta sami wadanda suka kafirta daga cikinsu.
Wannan aya tana bayani kan rabuwar al'umma da kasa su gida biyu da cewa: kaso na farko suna da uzuri na hakika kuma idan suna da hali da karfi tabbas za su shiga a cikin jihadi da yakar kafirci da kafirai makiya Allah da addinsa.Amma kashi na biyu na wadannan al'umma da suka ki zuwa yaki da jihadi suka zauna a gida tamkar mata da yara kanana bas u da wani uzuri wato dalili za a gida da kin zuwa filin daga kuma hatta a cikin tunaninsu babu wani abu wai kare addini da Manzon Rahama tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayansa tsarkaka.Kur'ani dangane da kaso na farko yana cewa; wadanda suke da uzuri da dalili amma duk da haka suka nemi izini a wajen Manzon Allah na zama a gida ba don sun so ba domin mutunta matsayin da Manzon Allah yak e da shi a gurinsu da matsayinsa a addini.Amma kaso na biyu na munafikai masu bayyana karya da yaudara da bas u da wani uzuri na zama a gida sun duk da Manzon Allah ya ba su izinin zama amma a maimakon su zauna din sai suka ci gaba da aikata sana'ar da suka saba ta yin zagon kasa da kulla makirci da hada baki da kafirai.
To a cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu na farko Jihadi al'amari ne na hukuma ban a daidaikun mutane ban e saboda haka kowa ne daya daga cikin al'umma ba shi da hakki ba tare da jagora ko shugaba bay a dauki wani mataki day a saba.
Na biyu Karya ba wai kawai ta fatar baki bace wani lokaci ayyukan dan adam yana nuni da bayyana karyarsa da hakikaninsa da fatar Allah ya kiyashe mu amin summa amin.
Wassalamu alaikum warahamatullhi wa barkatuhu.
Suratut Tauba, Aya Ta 91-94 (Kashi Na 309)
Jama'a masu saurare barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke yi wa kawunanmu mu masu gabatar da shirin hannunka mai sanda da kuma yiwa junanmu nasiha kan abubuwan da idan muka yi aiki da su ko shakka babu za mu inganta rayuwarmu a wannan duniya da kuma uwa uba addininmu da zamantakewarmu ta daidaiku ko ta cudani in cudeka. Kuma har yanzu muna cikin ci gaba da bayani da bin diddigin irin nasihohin da suka zo a cikin suratul Tauba da abubuwan da ayoyin wannan sura suka kumsa ba suka yi daidai da abubuwan da ke wakana a rayuwarmu ta yau da kullum da kuma daidai da abubuwan da suka wakana a tsawon tarihi don haka a nan idan muka yi aiki da abin day an iya magana Hausa ke fadi zai amfane mu wato gani da wane ya isa wane tsoran Allah da fatar Allah ya bamu karfin aiki da wannan Karin magana amin.
To madallah yanzu kuma za fara ne da sauraren aya ta 91 a cikin wannan sura ta tauba :
لَّيْسَ عَلَى الضُّعَفَاء وَلاَ عَلَى الْمَرْضَى وَلاَ عَلَى الَّذِينَ لاَ يَجِدُونَ مَا يُنفِقُونَ حَرَجٌ إِذَا نَصَحُواْ لِلّهِ وَرَسُولِهِ مَا عَلَى الْمُحْسِنِينَ مِن سَبِيلٍ وَاللّهُ غَفُورٌ رَّحِيمٌ{91}
Babu wani laifi a kan raunana ko marasa lafiya ,ko kuma wadanda bas u sami abin da za su ciyar ba don talauci ,matukar dai sun tsarkake zuciyarsu ga Allah da Manzonsa. Babu wata hanya ta dora laifi ga masu kyautatawa.Allah kuwa Mai gafara ne Mai jin kai.
Wannan aya tan a nuni da yadda addini ya yi wa masu rauni da nakasassu da kuma wadanda wani dalili na rashin lafiya ko makamancin haka ya hana su da ba su damar halartar filin daga da jihadi da kuma yadda wannan aya ke nuni da yadda addinin Musulunci ya bawa kowa hakki da rataya masa nauyin day a rataya awuyansa kai tsaye.
Kuma wannan aya tana dauke da abubuwa masu yawan gaske day a kamata mu yi aiki da su a aikace kuma day a kamata mu yi la'akari da su cewa duk wannan ya yi imani da mmika wuya bay a bukatar fakewa da karya domin kaucewa gurin yaki da filin daga na jihadi. Kuma duk wata karya da fakewa da yaudaro za a gano shi kuma ko ba komi Allah masani ya san abin da ke boye a cikin zuciya.
To madallah yanzu kuma za mu saurari aya ta 92 a cikin wannan sura ta tauba :
وَلاَ عَلَى الَّذِينَ إِذَا مَا أَتَوْكَ لِتَحْمِلَهُمْ قُلْتَ لاَ أَجِدُ مَا أَحْمِلُكُمْ عَلَيْهِ تَوَلَّواْ وَّأَعْيُنُهُمْ تَفِيضُ مِنَ الدَّمْعِ حَزَناً أَلاَّ يَجِدُواْ مَا يُنفِقُونَ{92}
Haka kuma babu laifin a kan matalauta wadanda idan sun zo maka don ka dauki nauyinsu na abin hawa da guzuri sai ka ce da su: Ba ni da abin d azan dauki nauyinku da shi, sai suka juya idanuwansu suna kwararar da hawaye don bakin cikin ba su sami abin da za su ciyar ba.
Ita kuwa wannan aya tana ilmantar da mu yadda masu fama da talauci ke neman zuwa jihadi ruwa a jallo amma bas u da makami ko halinsa da kuma yadda suke zuwa gurin ma'aikin Allah domin ya fanshe su da makaman sabanin munafikai masu hannu da shuni amma sai su fake da karya domin kaucewa zuwa filin daga da jihadi.
A wannan aya za mu iya ilmantuwa da yadda al'ummomi a tun wancan lokaci na Manzon Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa suka rabu gida biyu.
To madalla yanzu kuma za mu saurari aya ta 93 a cikin wannan sura ta Tauba kamar haka:
إِنَّمَا السَّبِيلُ عَلَى الَّذِينَ يَسْتَأْذِنُونَكَ وَهُمْ أَغْنِيَاء رَضُواْ بِأَن يَكُونُواْ مَعَ الْخَوَالِفِ وَطَبَعَ اللّهُ عَلَى قُلُوبِهِمْ فَهُمْ لاَ يَعْلَمُونَ{93}
Zargi kawai yana ga wadanda suke neman izininka ,alhali kuwa suna mawadata. Sun yarda da su zamanto tare da masu zaman gida mata da yara.Allah kuma Ya tunke zukatansu saboda haka ba sa sanin gaskiya.
Wannan aya tana magana ne kan masu hannu da shuni ,masu kudi da dukiyoyi da jin dadin rayuwar duniya ta zahiri a tsakanin al'umma wadanda saboda kare dukiyoyinsu sun ki halartar filin daga da jihadi kuma sun yi ta neman hanyoyin kaucewa zuwa jihadin da yin suka mai tsanani da cewa: wadanda son abin duniya ya lullube zukatansu da kekashewar zucciya da ba su fahimtar hakikanin lamurra kuma a shirye suke su hada kai da masu adawa da bakar kiyayya da addinin Musulunci suna da cewa ayyukan da suke aikata mummuna ne da sakamakonsa gidan jahannama ne.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu akalla :
Na farko Matalauci da mai arziki a ta fuskar hukumce-hukumcen Allah daidai suke kuma ita dukiya ba ta fifita mai ita da komi a gurin Allah illa aikinsa na alheri.
Abu na biyu duk mai takama da dukiya da dogaro da ita za ta kai shi ta baro shi da yin nadama a duniya ko lahira.
To Yanzu kuma za mu saurari Aya ta 94 a cikin wannan sura ta Tauba kamar Haka;
يَعْتَذِرُونَ إِلَيْكُمْ إِذَا رَجَعْتُمْ إِلَيْهِمْ قُل لاَّ تَعْتَذِرُواْ لَن نُّؤْمِنَ لَكُمْ قَدْ نَبَّأَنَا اللّهُ مِنْ أَخْبَارِكُمْ وَسَيَرَى اللّهُ عَمَلَكُمْ وَرَسُولُهُ ثُمَّ تُرَدُّونَ إِلَى عَالِمِ الْغَيْبِ وَالشَّهَادَةِ فَيُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ{94}
-Suna kawo muku uzurinsu idan kuka dawo musu. Ka ce da su: Kada ku kawo wani uziri,mu ba za mu gaskata ku ba har abadan,hakika Allah Ya gaya mana labarinku,Allah kuwa zai ga ayyukanku Shi da manzonsa,sannan a komar da ku zuwa ga Allah Masanin boye da sarari,sannan Ya ba ku labarin abin da kuka kasance kuna aikatawa.
Karkashin ruwayoyi kimanin mutane tamanin daga cikin munafikai ta hanyar dalillai na karya da fakewa da yin karyayyaki iri-iri sun kaucewa zuwa yakin Tabuka kuma a lokacin da Ma'aikin Allah da sahabbansa da sauran musulmi ke dawowa daga filin daga da jihadi domin sun lullube wannan danyan aiki mummuna da suka aikata sun yi ta gabatar da maganganu iri-iri amma da wannan aya ta sabka ta fadakar da mumunai kan karbar uzirin irin wadannan mutane munafikai don su san da cewa ba za su iya yaudarar mumunai ba kuma ba su fi mai kora shafawa ba ma'ana sun ki halartar jihadi amma a yi murnar cin nasara da su wato riba biyu irin ta sabro ga cizo ga shan jini.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu na farko : yana da kyau karbar izurin mutane amma da sharadin ba karya suke ba ko fakewa da wani lamari na yaudara.
Abu na biyu: wadanda ke kin aiki da nauyin da ya rataya a wuyansu na addini da zamantakewa dole a ladabtar da su domin hakan ya zama darasi ga sauran.
Da kuma haka ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai kuma mako mai zuwa da yardar mai duka za ku ji mu dauke da ci gaban shirin kafin lokacin ni Tidjani Malam lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar nake cewa wassalam alaikum warahmatullahi wa barkatuhu.
Suratut Tauba, Aya Ta 95-99 (Kashi Na 310)
Jama'a masu saurarenmu barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na Hannunka mai sanda da a cikinsa muke bayani da kawo irin nasihohin da suke tattare da ayoyin alkur'ani mai girma da daukaka kuma dayan biyun manyan hanyoyi da duk wanda ya yi riko da su tabbas ko shakka babu zai samu tsira duniya da lahira kuma rayuwarsa za ta zama mai sauki a wannan duniya yayin da a gobe kiyama kuma ya samu dace da gidan Aljanna kamar yadda hadisan ma'aikin Allah mai rahama da jin kai masu yawa suka yi nuni da haka. Da fatar Allah ya sa mu yi dace da yin riko da umarni ko hanni na Alkur'ani da na ma'aikin Allah da limaman gidansa tsarkaka.
To yanzu kuma za mu saurari aya ta 95 a cikin wannan sura ta tauba kamar haka:
سَيَحْلِفُونَ بِاللّهِ لَكُمْ إِذَا انقَلَبْتُمْ إِلَيْهِمْ لِتُعْرِضُواْ عَنْهُمْ فَأَعْرِضُواْ عَنْهُمْ إِنَّهُمْ رِجْسٌ وَمَأْوَاهُمْ جَهَنَّمُ جَزَاء بِمَا كَانُواْ يَكْسِبُونَ{95}
Suna iya rantse muku da Allah idan kuka dawo wurinsu don ku kyale su . To ku kyale su din .Hakika su najasa ne .makomarsu kuma wutar jahannama ce sakamakon abin da suka kasance suna aikatawa.
Munafikan da suka kaucewa zuwa yakin tabuka sun yi zamansu a birnin Madina amma a daidai lokacin da manzon Rahama da tsira amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayansa ke komawa gida birnin Madina tare da mumunai sai suka isa a gurinsu suna yin karyayyakin karya iri-iri na yaudara da gabatar da a yafe musu zunubansu da duk wasu kura-kurai da suka aikata amma Allah gwani masani mabuwayi masanin duk wani abu da ke sarari da boye a cikin wannan aya yana cewa; ka kyale su domin su tuni aka kyale su da munanan ayyukansu kan haka ne ma'aikin Allah manzon rahama da adalci tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayansa tsarkaka ya bada umarnin da mutane su kauracewa wadanda suke gujewa jihadi kan karya kar su yi ma'amala da su. Ci gaban wannan aya tana nuni da dalili da ya sa Allah madaukakin sarki ya yi masu fushi a wannan duniya saboda mummunan aikin da suka boye a cikin zukatansu kuma a gobe kiyama za su gamu da bakar azaba mai radadi da zafin kuna.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu na farko :kar mu yi dogaro da kowace irin rantsuwa domin munafikai sun yaudarar mutane ta hanyar yin karya wajen yaudarar mumunai. Abu na biyu: mu yi nisa da kauracewa mutane da yanayi na fasikanci da yanke duk wata hulda da su domin shi munafinci wata cuta ce mai yaduwa don haka a guji mutane munafikai.
To madalla yanzu kuma lokaci ne da za mu saurari aya ta 96 kamar yadda aka yi mana tanadi.
يَحْلِفُونَ لَكُمْ لِتَرْضَوْاْ عَنْهُمْ فَإِن تَرْضَوْاْ عَنْهُمْ فَإِنَّ اللّهَ لاَ يَرْضَى عَنِ الْقَوْمِ الْفَاسِقِينَ{96}
Suna rantse muku don ku yarda da su,to idan ma kun yarda da su din hakika Shi Allah ba zai yarda da mutane fasikai ba.
A fili take cewa: munafikai ba su na yin rantse rantsen karya da yaudara domin faranta ran musulmi da bawa lamarinsu muhimmanci sai dai suna yin haka ne domin su kaucewa maida martani da fushin musulmi kansu domin ta haka ne za su kubuta da rayuwa irin ta zamantakewa da musulmi. Manzon Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi a cikin wata ruwaya yana cewa; duk mutuman da yake wani aiki don neman yardar Allah ko da mutane ba su gamsu da aikinsa ba ,to Allah zai yi sanadiyar da mutane za su gamsu da shi da aikinsa. Kuma duk mutuman da yake yin wani aiki domin neman yardar mutane ko da aikinsa Allah ya amince da shi to Allah zai yi sanadiyar mutane su kamaci aikinsa. To haka ayyukan munafikai yake na neman yardar mutane amma su mumunai tushen duk wani aiki na su shi ne neman yardar Allah amma yardar mutane ba shi ne tushe ba a gurinsu ba.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa masu yawa amma za mu takaita da guda biyu daga ciki. Na farko:Munafikai ba za su taba yin tuba da neman yardar Allah a ayyukansu kawai suna neman yaudarar mutane da yardarsu ba ta Allah ba.
Na biyu zucciya da bakunan mutane ta kowane lokaci da yanayi bai dace ba su karkata ga mutane fasikai masu saboda da neman yardarsu.
Da fatar Allah ya kare mu da duk wani aiki irin na munafikai da kafirai ya kuma sa mu dace da aikata aikin alheri da rahamarsa a duniya da lahira
To madalla yanzu kuma za mu saurari aya ta 97 a cikin suratul tauba kamar haka:
الأَعْرَابُ أَشَدُّ كُفْراً وَنِفَاقاً وَأَجْدَرُ أَلاَّ يَعْلَمُواْ حُدُودَ مَا أَنزَلَ اللّهُ عَلَى رَسُولِهِ وَاللّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٌ{97}
Larabawan Kauye sun fi tsananin kafirci da munafunci, kuma su suka fi dacewa da rashin sanin dokokin da Allah ya saukar wa Manzonsa,Allah kuwa Masani ne Gwani.
Al'ummar da ta rayu a lokacin manzon Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa ta kasu gida biyu wato wata al'umma tana rayuwa ne a biranai yayin da wata al'ummar take rayuwa a kauyuka da wajen biranai kuma ayoyin da suka gabata suna magana ne kan munafikan da ke zaune a biranai da kuma birnin Madina amma ita wannan aya da ayoyi guda biyu da suka gabace ta suna magana ne kan munafikai mazauna kauyuka kuma duk lokaci da aka yi amfani da A'arab ana nufin larabawa mazauna kauyuka inda aya ke cewa: kar ku gafala su larabawa da ke zaune a kauyuka sun yi nisa da adabi da al'adu na Musulunci kuma ba su da cikakkkiyar masaniya kan addini kuma cikin sauki makiya za su yaudare su da jan akalarsu .kalmar A'arab ba wai kawai ta ta'allaka da larabawan da ke zaune a kauyuka ba tanada ma'ana mai fadi da fahimta kamar yadda ya zo a cikin wasu ruwayoyi masu yawan gaske na Musulunci da hakan ke tabbatar da cewa kauyanci bai takaita da wani yanki illa ya shafi duk wanda ba shi da cikekkeiyar masaniya kan addini ko yin wani abu da ya yi hannun riga da hankali.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu kamar haka:
Na farko rayuwa a nesa da gurare da al'adun Musulunci ya yadu da kuma ilimin addini da hukumce-hukumce da ka'idodi da dokokin Allah kafirci da munafinci zai samu gindin zama da share masa hanyar wanzuwa.
Na biyu: wadanda suka nisa da adabi da kyawawan dabi'u na Musulunci kuma suka koma al'adarsu ta jahiliya a mahangar kur'ani sune kauyawa da ake kira da A'arab.
To madallah yanzu kuma za mu saurari aya ta 98 zuwa 99 a cikin wannan sura ta tauba.
وَمِنَ الأَعْرَابِ مَن يَتَّخِذُ مَا يُنفِقُ مَغْرَماً وَيَتَرَبَّصُ بِكُمُ الدَّوَائِرَ عَلَيْهِمْ دَآئِرَةُ السَّوْءِ وَاللّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ{98} وَمِنَ الأَعْرَابِ مَن يُؤْمِنُ بِاللّهِ وَالْيَوْمِ الآخِرِ وَيَتَّخِذُ مَا يُنفِقُ قُرُبَاتٍ عِندَ اللّهِ وَصَلَوَاتِ الرَّسُولِ أَلا إِنَّهَا قُرْبَةٌ لَّهُمْ سَيُدْخِلُهُمُ اللّهُ فِي رَحْمَتِهِ إِنَّ اللّهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ{99}
- Daga Larabawan kauye kuma akwai wadanda suke daukar abin da suke ciyarwa tare ne,suke kuma sauraron faruwar mummunan abu na kansu yake.Allah kuma Mai ji ne Masani. -Daga Larabawan kauye din kuwa akawai wadanda suke bada gaskiya da Allah da ranar Lahira suke kuma daukar abin da suke ciyarwa hanyoyi ne masu kusantarwa ga Allah da kuma addu'o'in Manzon. Allah zai shigar da su cikin Rahamarsa.Hakika Allah Mai gafara ne mai jin kai.
Wadannan ayoyi guda biyu suna magana ne kan mahangogi biyu mabambanta kan munafincin kauyawan larabawa da cewa; wadanda suka yi nesa da al'adun Musulunci da masaniya kan Musulunci,wadanda suka aikata munafinci munafincinsu iri-iri ne yayin da wasu a maimakon yin addu'a sai su yi tsinuwa da la'anta. Amma larabawa mazauna kauyuka da ke da masaniya kan al'adu na Musulunci sun yi imani da ranar kiyama ranar sakamako kuma duk wani abu da suka yi don neman yardar Allah sun san cewa wani babban jari ne suka saka da ajiyewa a gurin Allah da za su samu riba da sakamako mai yawa a gobe kiyama kuma a wannan duniya ayyukansu ya faranta rai da samun amincewar ma'aikin Allah manzon rahama aminci da yardar Allah ta tabbata a gare shi da alayan gidansa da yi masu addu'a da duk zai samar masu da dacewa da rahamar Allah a wannan duniya da lahira.
A cikin wadannan ayoyi za mu iya ilmantuwa da akalla abubuwa guda uku:
Na farko:Shi munafiki, munafincinsa zai ci shi saboda ya ha'anci kansa da zucciyarsa kuma a ranar kiyama ba shi da imani ma'ana ya boye kafircinsa a zucci da bayyana imaninsa a zahiri amma a ranar kiyama gaskiya za ta bayyana.
Na biyu: Munafiki yana haddasa sharri da mummunan aiki kan sauran mutane kuma ramin muguntan da y a gina shi zai fada ciki.
Na uku : Abu da ke kara kusanta bawa da mahaliccinsa shi ne ikhlasi ga Allah , ba wai tsagwaron aiki ba ,mumuni da munafiki dukansu biyu suna aika laifuka amma shi mumuni hatta kura-kuransa na fadakar da shi da ilmantar da shi da kara kusantar da shi ga Allah.
Da fatar Allah ya nisantar da mu daga aikata ayyuka irin na munafikai da ba mu karfin aikata ayyukan alheri irin na mumunai da bayunsa na gari amin da kuma wannan addu'a ce ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar nake cewa wassalamu alaikum warahmatullahi wa barkatuhu.
Suratut Tauba, Aya Ta 100-103 (Kashi Na 311)
Jama'a masu saurare barkarmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke farawa da kawo ayoyin alkur'ani mai tsarki a matsayinsa na babban jagora a rayuwarmu ta yau da kullum musamman ta fuskar addini da zamantakewa.Kuma kur'ani daya ne daga cikin igiyoyi biyu mafi karfi da duk wanda ya yi riko da su ko shakka babu zai samu cira duniya da lahira ya kuma ji dadin rayuwarsa cikin sauki da walwala.
To madallah yanzu kuma lokaci ya yi da za mu saurari aya ta 100 a cikin suratul Tauba kamar haka:
وَالسَّابِقُونَ الأَوَّلُونَ مِنَ الْمُهَاجِرِينَ وَالأَنصَارِ وَالَّذِينَ اتَّبَعُوهُم بِإِحْسَانٍ رَّضِيَ اللّهُ عَنْهُمْ وَرَضُواْ عَنْهُ وَأَعَدَّ لَهُمْ جَنَّاتٍ تَجْرِي تَحْتَهَا الأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا أَبَداً ذَلِكَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ{100}
Magabata kuwa na farko,wadanda suka yi hijira da mutanan Madina da kuma wadanda suka biyo bayansu a kyautatawa duka Allah ya yarda da su su ma sun yarda da shi,ya kuma tanadar musu aljannoni wadanda koramu suke gudana ta karkashinta,madawwama a cikinsa har abada. Wannan shi ne rabo mai girma.
A cikin shirye-shiryen da suka gabata ayoyi na bayani ne kan halayyar munafikai na Madina da yadda suka suka kumtatawa ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da muminai Amma wannan aya tana magana ne kan muminai da ke zaune a birnin Madina da Allah ya amince da gamsuwa da ayyukansu dari bisa dari.Wadanda suka yi hijira daga Makka zuwa Madina inda suka yi hijira karkashin umarnin Ma'aikin Allah inda suka tarda yan uwansu Ansariyan mazauna birnin Madina da su ma ma'aikin Allah ya umarce su da su zama yan uwan juna masu kaunar juna.Wannan aya tana magana kan wadanda suka fara yin imani da ma'aiki da bada gaskiya da shi daga cikin mazauna birnin Makka da mazauna birnin Madina sunada rabo mai yawa.Inda ana maganar wadanda suka fara yin imani da ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi ba za mu taba mantawa da mace ta farko da ta yi imani da shi ta bada gaskiya da taimakawa ma'aiki da kuma addinin Allah da dukiyarta da jurewa duk wani kumci da wulakancin mushirikan makka kuma ta taimakawa muminai wato matar ma'aikin Allah Hadizatul Kubra (AS) sai kuma imam Ali mutum na farko a cikin mazaje day a bada gaskiya da imani da manzoncin ma'aikin Allah Muhammadu dan Abdullah (SWA) kuma imam Ali ya sadaukar da rai da rayuwarsa wajen kare ma'aiki da adddinin Musulunci hatta lokacin yin hijira shi ne ya kwanta a kan shimfidarsa a daidai lokacin da makiya mushirikai ke neman kashe ma'aikin Allah.
A Cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu na farko: yin gaggawa wajen aikata alheri abu ne mai kyau abin kauna da daraja kuma matsayin wadanda suka fara aikata aikin alheriri abin girmamawa ne da bayyana matsayinsu.
Na biyu:Yin hijira don aikin alheri abu ne da ke tattare da aminci da yardar Allah madaukakin sarki da kuma ke tattare da sakamako na alheri.
To yanzu kuma za mu saurari aya ta 101 a cikin wannan sura ta Tauba kamar haka;
وَمِمَّنْ حَوْلَكُم مِّنَ الأَعْرَابِ مُنَافِقُونَ وَمِنْ أَهْلِ الْمَدِينَةِ مَرَدُواْ عَلَى النِّفَاقِ لاَ تَعْلَمُهُمْ نَحْنُ نَعْلَمُهُمْ سَنُعَذِّبُهُم مَّرَّتَيْنِ ثُمَّ يُرَدُّونَ إِلَى عَذَابٍ عَظِيمٍ{101}
Kuma daga Larabawan kauye wadanda suke kewaye da ku akwai munafukai,haka kuma daga mutanan Madina,sun yi zurfi cikin munafunci,ku ba ku san su ba, Mu muka san su.to za mu azabtar da su sau biyu,sannan a komar da su zuwa ga azaba mai girma.
Itama wannan aya kamar sauran da muka gabata a baya tana magana kan hadarin kasancewar munafikai a tsakanin al'umma da cewa: a tsakanin musulmin birnin Madina da kewaye akwai masu raya imani da kuma kuke lissafa su a cikin mumunai amma a gaskiya su munafikai ne ba su yi imani da Allah da ranar kiyama ta sakamako ba. Kuma ko da yake ba ku sansu ba amma Allah masanin komi da kowa ya sansu da abin da suka boye a zucciyarsu. Har ila yau a wannan duniya za su fuskanci kaskanci da tsanani kamar yadda a lahira za su fuskanci azaba mai radadi.Sun tabe duniya da lahira kamar yadda suka azabtar da zucciya da rayuwarsu domin sun boye munafinci a zuuciya da bayyana imani a tsakanin jama'a idan mutuwa ta riske su sai gaskiya ta bayyana ma'ana kafircinsu ya bayyana kamar yadda aya ta 50 a cikin suratul Anfal ta yi nuni da haka. To Allah ya kiyashe mud a aikin munafinci amin kuma wannan aya tana ilmantar da mu abubuwa biyu na farkonsu shi munafinci matsayi matsiyi ne ma'ana iri-iri ne wani laokaci mai rauni wani lokaci a zurfafa da tsanantawa kuma duk wanda ya tsananta azabarsa tafi tsanani idan ya sausauta ya sami sausauci. Na biyu: Ko da yake zato abin kama ne amam yin takatsantsan abin lura ne saboda munafikai suna rayuwa tare da mumunai da raya suma muminai ne.
To madallah yanzu kuma za mu saurari aya ta 102 a cikin wannan sura ta tauba kamar haka:
وَآخَرُونَ اعْتَرَفُواْ بِذُنُوبِهِمْ خَلَطُواْ عَمَلاً صَالِحاً وَآخَرَ سَيِّئاً عَسَى اللّهُ أَن يَتُوبَ عَلَيْهِمْ إِنَّ اللّهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ{102}
Wasu kuwa da suka yi kirari da laifinsu sun gauraya kyakkyawan aiki da wani mummuna,to Allah yana karbar tubarsu.Hakika Allah yana karbar tubarsu.Hakika Allah Mai Gafara ne Mai rahama.
Karkashin ruwayoyi na tarihi da suka zo, wasu daga cikin sahabban ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka saboda kwadayin duniya sun kaucewa zuwa filin daga da jihadi a lokacin yakin Tabuka.Amma lokacin da wannan aya ta sabka ta bayyana mummunan halinsu sai suka yi nadama da wannan aiki da suka aikata da nema gafara da tuba inda suka rufe da yin zaman dirshen a masallacin ma'aiki har zuwa lokacin da Allah ya karbi tubarsu da kuma Ma'aikin Allah (SWA) ya yi masu bushara da wannan labari na rahamar Allah.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa biyu a cikin wannan aya kamar haka: na farko:a duk lokacin da mutum zai yi nazari kan ayyukansa na alheri kar ya yi la'akari kawai da bangare mai kyau na aikinsa a'a ya yi kokarin gyara kura-kurai da rauninsa a cikin wannan aiki nasa na alheri.
Na biyu:Yin nadama hanya ce ta kai wag a gafarar Allah kuma hanaya ce da ke sawa kofar tuba ta bude.
To madallah yanzu kuma za mu saurari aya ta 103 a cikin wannan sua ta Tauba kamar:
خُذْ مِنْ أَمْوَالِهِمْ صَدَقَةً تُطَهِّرُهُمْ وَتُزَكِّيهِم بِهَا وَصَلِّ عَلَيْهِمْ إِنَّ صَلاَتَكَ سَكَنٌ لَّهُمْ وَاللّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ{103}
Ka karbi sadaka daga dukiyoyinsu da za ka tsarkake su kuma wanke su da ita ,ka kuma yi musu addu'a.Hakika addu'arka kwanciyar rain e a gare su.Allah kuwa Mai ji ne Masani.
Musulunci ba addini ban e kawai na ibada da yin zikiri da addu'a a'a addinini day a hada komi da komi na rayuwa na daidaiku da ta jama'a hatta neman halaliya addini ne kuma ya shafi gina tattalin arziki daya daga cikin dalilai wajabta fitar da zakka domin binkasa karfi da samun mutane da daidaito tsakanin masu kudi da mabukata da kuma yin sadaka a matsayin mustahabbi abin kauna. Duk da cewa wannan aya ta sabka ne sheakara ta biyu bayan Hijira tafi maida hankali kan fitar da Zakka da cewa; tsarkake ruhi da zuuciyar musulmi daga son rai da zucci da mantawa da halin da wani ke ciki na rayuwa daga cikin falalar masu fitar da zakka shi ne suna daga cikin wadanda ma'aikin Allah tsira da maincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka ya yi wa addu'a.
A cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda biyu:
Na biyu duk wanda ya aikata alheri a jijina masa da gode masa kan haka nema ma'aiki yake jinjinawa wadanda suka fitar da zakka duk da cewa wajibice a kansu da yi masu addu'a.
Da fatar Allah madaukakin sarki ya bamu karfi da ikon aiki da duk wani nauyi da ya rataya a wuyanmu da sabke shi kamar yadda Allah da ma'aikinsa ya umarce mu.
Da kuma wannan ne Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram Ke cewa wassalamu alaikum warahmatullahi wa barkatuhu.
Suratut Tauba, Aya Ta 104-107 (Kashi Na 312)
Jama'a masu saurarenmu barkarmu da sake saduwa da ku a ciki wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke yi wa kawunanmu da kuma ku masu sauurarenmu hannunka mai sanda da kuma muke fatar yin aiki da irin wadannan nasihohi kuma matukara muka yi aiki da su ko shakka babu za mu samu dacewa da saukin rayuwa mai inganci a wannan duniya da samun sakamako na alheri na shiga gidan Aljanna da kowa ne dan adam a doran kasa ke fatar shiga .
To madallah yanzu kuma za mu saurari aya ta 104 a cikin suratul Tauba kamar haka:
أَلَمْ يَعْلَمُواْ أَنَّ اللّهَ هُوَ يَقْبَلُ التَّوْبَةَ عَنْ عِبَادِهِ وَيَأْخُذُ الصَّدَقَاتِ وَأَنَّ اللّهَ هُوَ التَّوَّابُ الرَّحِيمُ{104}
Shin yanzu ba su sani ba ne cewa; Allah shi Yake karbar tuba daga bayinsa Yake kuma karbar sadakoki,kuma hakika Allah ne mai yawan karbar tuba ,Mai yawan Rahama?
A cikin ayar da ta gabata tana magana ne kan umarnin Allah madaukakin sarki kan fitar da Zakka amma ita wannan aya tana cewa ne ;idan ma'aikin Allah ya karbi zakkar da kuka fitar zai raba ta ne ga mabukata amma a hakikanin lamarin mai karbar wannan zakka shi ne Allah madaukakin sarki da kuma ma'aikinsa da take bi ta hannusa karkashin umarnin mahaliccin komi da kowa a sararri da boye.Ma'aiki yana karbar zakkar da kuka fitar kamar yadda ya zo a cikin ruwayoyi Sadaka tana fadawa a hannun Allah ne kafin ta fada a hannun mabukaci ko talakka da masaki da wani bawon Allah ya bawa wani dan uwansa bawon Allah.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da fahimtar abubuwa masu yawan gaske kamar haka:
Na farko a lamari da ya shafi tuba ba kawai yin nadama ya wadatar ba a'a ana bukatar ka yi kokarin gyara wannan aiki da ka aikata da kyautata baya idan da hali.
Na biyu; Zakka wani lamari ne da ya yi kama da fitar da wani bangare na dukiya da ke da matsayi da daraja a cikin addini domin ko ba komi mai karbar wannan sadaka ko zakka Allah ne kuma tamkar wani tanadi da guzuri ne bawan Allah ya yi wa kansa a wannan duniya da ganin sakamakonsa a gobe kiyama.
To madallah yanzu kuma lokaci ne da za mu saurari aya ta 105 a cikin wannan sura ta Tauba.
وَقُلِ اعْمَلُواْ فَسَيَرَى اللّهُ عَمَلَكُمْ وَرَسُولُهُ وَالْمُؤْمِنُونَ وَسَتُرَدُّونَ إِلَى عَالِمِ الْغَيْبِ وَالشَّهَادَةِ فَيُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ{105}
Ka kuma ce da su : Ku yi aiki ,Allah ne zai ga aikin naku,Shi da manzonsa da kuma muminai,kuma za a mayar da ku zuwa ga Masanin boye da sarari,sannan Ya ba ku labarin abin da kuka kasance kuna aikatawa.
A wani bangare wannan aya tana yiwa munafikai da masu bijirewa dokokin Allah barazana da cewa: kar ku yi zaton ayyukanku suna boyuwa ga Allah da manzonsa da kuma muminai. kuma ba da jimawa ba a wannan duniya kowa zai fahimta da gane ayyukan da kuke aikatawa bugu da kari a ranar tashin kiyama Allah zai bayyana masu a fili karara munanan ayyukan da suke aikatawa a boye. Karkashin ruwayoyi masu yawa ilimin ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi bai ta'allaka da kebantuwa da lokacin yana raye ba a'a hatta bayan korarsa kuma har wannan lokaci da ranar tashin kiyama yana lura da sanin hali da ayyukan al'ummarsa kamar yadda muminai da bayun Allah na gari da ma'asumai suna ana nuna masu ayyukan sauran bayun Allah bayan rasuwarsu Allah ya ba su wata falala ta isar da labarin bayunsa da suka aikata aikin alheri ko lala a kunnuwansu.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu na farko: ya kamata mu lura da cewa muna karkashin iko da iradar Allah da Ya halicce mu da iko a kanmu da masaniya kan aikin da muke aikatawa kuma shawara a nan ita ce mu nisantar da kanmu daga aikata mummunan aiki da sabo a hannu daya mu yi riko da ruhin takkawa.
To madallah yanzu kuma za mu fara da sauraren aya ta 106 a cikin wannan sura ta Tauba kamar haka:
وَآخَرُونَ مُرْجَوْنَ لِأَمْرِ اللّهِ إِمَّا يُعَذِّبُهُمْ وَإِمَّا يَتُوبُ عَلَيْهِمْ وَاللّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٌ{106}
Wasu kuwa an jinkirtar da lamarinsu ne ga hukuncin Allah,ko dai Ya azabtar da su ko kuma Ya karbi tubarsu.Allah kuwa Masani ne Gwani.
A cikin shirin da ya gabata ayoyin da muka gabatar suna magana da bayani ne wasu halaye na musamman na ayyukan munafikai to wannan aya tana magana da nuni da cewa; sabanin munafikai masu riko da nacewa kan ayyukansu amma sun tuba da yin nadama kan ayyukan da suka aikata amma akwai wani rukunin munafikai su ba su yi riko da ayyukansu na munafinci kuma su ba su yi tuba ba to makomarsu tana hannun Allah madaukakin sarki shin su kafirai ne ko kuma an yi masu afuwa.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu:
Na farko : Duk wani lamari day a shafi yin afuha ko azabtar da wanda ya aikata sabo yana hannun Allah madaukakin sarki ko ya yi masu afuwa da yi masu rahama ko kuma ya azabtar da su kan ayyukan da suka aikata kuma kar mu yi shisshigi a cikin lamurran Allah madaukakin sarki.
Madallah bayan sauraren wannan abu da aka yi mana tanadi a kan inji za mu saurari aya ta 107 a cikin wannan sura ta tauba kamar haka:
وَالَّذِينَ اتَّخَذُواْ مَسْجِداً ضِرَاراً وَكُفْراً وَتَفْرِيقاً بَيْنَ الْمُؤْمِنِينَ وَإِرْصَاداً لِّمَنْ حَارَبَ اللّهَ وَرَسُولَهُ مِن قَبْلُ وَلَيَحْلِفَنَّ إِنْ أَرَدْنَا إِلاَّ الْحُسْنَى وَاللّهُ يَشْهَدُ إِنَّهُمْ لَكَاذِبُونَ{107}
Wadanda kuwa suka gina masallaci don cuta da kafirci da rarraba kawunan muminai da kuma bad a mafaka ga wanda ya yaki Allah da Manzonsa tun da can,suna bas u yi nufin komai ba,sai kyautatawa,alhali kuwa Allah Yana bad a shaidar cewa; su makaryata ne.
Wannan aya tana magana ne kan massalacin cutarwa da aka gina domin takuwa a birnin madina kuma a jumulce ka tarihin abin day a faru; munafikai karkashin fakewa da taimakawa mutane masu rauni da kuma maras lafiya .A gaf da masallacin Kuba suka gina masallaci da sunan masallaci suna taruwa da tara mutane da zama wani sansani na taruwa kuma a daidai lokacin fara yakin Tabuka sun bukaci ma'aikin Allah da ya jagoranci salla da bude wannan masallaci.Amma sai aya ta sabka da sanar da shi hakikanin manufa da niyar munafikai na gina wannan masallaci ba don yin salla da ibada a cikinsa ba ne sai don zama wani sansani don kulla makirci da rarrabuwar kawunan al'umma.Nan take ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi ya bada umarnin rusa wannan masallaci da maida gurin gurin subar da shara.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu:
Na farko: manufar munafikai da makiya ita ce amfani da masallaci da ruhiya ta addini domin cimma mummunar manufarsu kan addini na hakika saboda haka mu kasance a kullum masu fahimta da yin takatsantsan kar munafinci da yaudara ya cutar dam u da sunan addini ko mazhaba.
Na biyu: Ruguza hadin kai a tsakanin al'ummar musulmi da haddasa sabani da rarrabuwar kawunan musulmi daya yake da kafircewa Allah ko da kuwa Masallaci ne da zai zama dalilin rabuwar kawunan musulmi kamar wannan masallaci na cutarwa dole a rusa shi kuma it ace hanyar mafita da magance wannan matsala ta makirci.
Da fatar Allah ya kiyashe mu da ayyukan munafinci amin kuma kafin wani shirin Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar nake cewa wassalamu alaikum warahmatullahi wabarkatuhu.
Suratut Tauba, Aya Ta 108-112 (Kashi Na 313)
Jama'a masu saurarenmu barkarmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shirin na hannunka da sanda da a cikinsa muka faraway da ayoyin alkur'ani mai girma da kuma yin dubu kan nasihohi da galgadin da ke cikin irin wadannan ayoyi na alkur'ani mai girma .kuma kamar yadda Hausawa kan ce ne gyara kayanka ba zai taba zama sabke mu raba ba musamman duk wanda ya gyara addininsa da rayuwarsa a wannan duniya ko shakka babu szai ga sakamakonsa wannan aiki nasa a gobe kiya yayin da kuma duk wanda ya shagaltu da yin biris da nasihohin Annabawa da manzonni da kuma waliyan Allah da kuma yin la'akari da munanan ayyukan da wadanda suka gabace shi suka aikata da yadda azabar da aka sabkar masu to ko shakka babu a wannan duniya da kuma gobe kiyama zai yi nadama da aikin da na sani da fatar Allah ya kiyashe mu da aikin da na sani duniya da lahira.
To madallah yanzu kuma za mu saurari aya ta 108 a cikin suratul Tauba kamar haka:
لاَ تَقُمْ فِيهِ أَبَداً لَّمَسْجِدٌ أُسِّسَ عَلَى التَّقْوَى مِنْ أَوَّلِ يَوْمٍ أَحَقُّ أَن تَقُومَ فِيهِ فِيهِ رِجَالٌ يُحِبُّونَ أَن يَتَطَهَّرُواْ وَاللّهُ يُحِبُّ الْمُطَّهِّرِينَ{108}
Kada ka yi salla a cikinsa har abada .Ba shakka masallacin da aka sanya harshashinsa tun daga ranar farko a bisa tsoron Allah shi ya cancanci ka yi sallah a cikinsa. .A cikinsa akwai wasu mazaje da suke so su tsarkaka. Allah kuwa Yana son masu yawan son tsarkaka.
A cikin shirin da ya gabata mun bayyana cewa munafikan madina sun gina masallaci da niyar gudanar da ayyukansu kuma karkashin umarnin Allah Manzonsa ya ruguza wannan masallaci da aka gina don cutarwa. To wannan aya tana magana da Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da kuma alayansa da kuma magana da muminai da cewa; masallaci yanada daraja da matsayi idan an gina shi karkashin tsoro da neman yardar Allah.ba masallacin da aka gina don kawo rarrabuwar jama'a da kulla makirci. A ci gaban ayar tana nuni da farkon masallaci da aka gina a Musulunci da a lokacin da ma'aiki ke yin hijira daga Makka zuwa madina a yankin Kubba da aka gina kuma a tsawon zamansa a madina a kowane mako yana zuwa wannan masallaci domin yin salla a cikinsa.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu ba farkonsu shi ne ita ibada ba za a iya raba ta da siyasa ba. Sallah a masallaci abin yi ne da kuma yake da armashi amma ba masallacin da makiya addinin Musulunci za su gima domin wata manufa ta boye mummuna ba.
Na biyu:Darajar masallaci daya yana da dangantaka da masallata masu tsoran Allah da tsarki ba wai kyawon gini da tsarinsa na zahiri ba.
To madallah yanzu za mu saurari aya ta 109 da 110 a cikin wannan sura ta tauba kamar haka;
أَفَمَنْ أَسَّسَ بُنْيَانَهُ عَلَى تَقْوَى مِنَ اللّهِ وَرِضْوَانٍ خَيْرٌ أَم مَّنْ أَسَّسَ بُنْيَانَهُ عَلَىَ شَفَا جُرُفٍ هَارٍ فَانْهَارَ بِهِ فِي نَارِ جَهَنَّمَ وَاللّهُ لاَ يَهْدِي الْقَوْمَ الظَّالِمِينَ{109} لاَ يَزَالُ بُنْيَانُهُمُ الَّذِي بَنَوْاْ رِيبَةً فِي قُلُوبِهِمْ إِلاَّ أَن تَقَطَّعَ قُلُوبُهُمْ وَاللّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٌ{110}
- Yanzu wanda ya sanya harshashin gininsa a kan tsoron Allah da yardarsa shi ya fi ko kuwa wanda ya sanya harshashin gininsa a gefen rami mai zabtarewa,sai ya ruguza da shi cikin wutar jahannama? Allah kuwa ba Ya shiryar da mutane azzalumai. -Ginin nasu da suka yi ba zai daina zama abin kokwanto a zukatansu ba har sai zukatan nasu sun tsuntsunke. Allah kuwa Masani ne Gwani.
Wadannan ayoyi suna nuna bambancin da ke akwai a tsakanin wadannan masallatai wato masallacin Kubba da masallacin cutarwa da cewa: zahirin aiki ba shi ne ke da muhimmanci ba a'a niya da burin da ake son cimma a cikin wannan aiki.Kuma wannan shi ne ke da muhimmanci. Wani na gina gidan asibici da mutane za su amfana amma saboda burin ginawar neman yardar mutane da burgewa ba zai ga sakamakon wannan aiki nasa ba a gurin Allah ko ya gina ko kar ya gina duk daya ne a gurin Allah domin riya da neman yaradar mutane ne ya sa shi ginawa ba Ikhilasi da neman yardar Allah ba kuma irin wannan aiki ba ya dauwama kuma karshensa halaka.
A cikin wadannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda uku
Na farko: girma da darajar duk wani aiki ya ta'allaka da kyaukyawar niya mai aikata wannan aiki ba wai zahirin aikin ba.
Na biyu:Gina masallaci yana bukatar niya ta gari da tsarkin zucci ba wai hadafi na cimma wata manufa ta siyasa ko riya ba.
Na uku: makiya musamman munafikai a kullum suna gina wani abu da a zahirinsa na kirki ne amma a badini don kawo shaku da rudani a tsakanin jama'a ne.
To Madallah yanzu kuma za mu saurari aya ta 111 a cikin wannan aya ta tauba kamar haka:
إِنَّ اللّهَ اشْتَرَى مِنَ الْمُؤْمِنِينَ أَنفُسَهُمْ وَأَمْوَالَهُم بِأَنَّ لَهُمُ الجَنَّةَ يُقَاتِلُونَ فِي سَبِيلِ اللّهِ فَيَقْتُلُونَ وَيُقْتَلُونَ وَعْداً عَلَيْهِ حَقّاً فِي التَّوْرَاةِ وَالإِنجِيلِ وَالْقُرْآنِ وَمَنْ أَوْفَى بِعَهْدِهِ مِنَ اللّهِ فَاسْتَبْشِرُواْ بِبَيْعِكُمُ الَّذِي بَايَعْتُم بِهِ وَذَلِكَ هُوَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ{111}
Hakika Allah Ya sayi rayuka da dukiyoyin muminai daga wurinsu cewa; suna da Aljanna.suna yin yaki saboda Allah,suna kashewa ana kashe su.Alkawari ne nasa gaskatacce a cikin Attaura da Linjila da Kur'ani.Ba wanda ya fi Allah cika alkawari.Saboda haka sai ku yi farin ciki da cinikin nan naku da kuka yi da Shi.Wannan kuwa shi ne rabo mai girma.
A cikin al'adar kur'ani duniya tamkar kasuwa ce , mutane su ne masu sayarwa,a cikin wannan lamari na saye da sayarwa da abubuwan da ake sayarwa su ne dukiya da rayuwa kuma mai saye shi ne Allah madaukakin sarki kuma idan mutum ya sayarwa da Allah abu na gari zai mayar masa da gidan Aljanna da kuma amfana da abubuwan more rayuwa a tsawon rayuwarsa .amma idan kuma bai shibka wani abin kirki ba zai gamu da fushin Allah da azaba mai radadi ta shiga gidan jahannama.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda uku na farko : daya daga cikin hanyoyin shiga gidan Aljanna it ace yin jihadi ta hanyar Allah tabaraka wata'ala,sai dai jihadi da rai yafi jihadi da dukiya. Na biyu; sabke nauyi a hanyar Allah aka kashe mutum ko ya rayu daya babu wani bambanci.
Na uku:Mu babu da wani hakki day a rataya a wuyan Allah amma Allah yanada hakki da ya rataya a wuyanmu.
To madallah yanzu kuma za mu saurari aya ta 112 a cikin wannan sura ta tauba kamar haka;
التَّائِبُونَ الْعَابِدُونَ الْحَامِدُونَ السَّائِحُونَ الرَّاكِعُونَ السَّاجِدونَ الآمِرُونَ بِالْمَعْرُوفِ وَالنَّاهُونَ عَنِ الْمُنكَرِ وَالْحَافِظُونَ لِحُدُودِ اللّهِ وَبَشِّرِ الْمُؤْمِنِينَ{112}
Masu tuba ,masu bauta,masu godiya.masu azumi,masu ruku'I,masu sujjada,masu yin umarni da aikin alheri da masu hani ga mummunan aiki,da masu kiyaye iyakokin Allah. To sai ka yi wa muminai masu irin wadannan siffofin,albishir.
Ayar da ta gabata tana magana ne kan shirin mumunai na zuwa jihadi kan hanyar Allah to wannan aya tana yi wa mumunai mujahidai bayanin abubuwa tara domin kar wani ya yi tunani da takaita cewa su muminai kawai jihadi da takobi suka sani a'a duk wata kamala da daukaka tana tare da su sabke nauyin day a rataya a wuyansu na addini ko a daidaiku ko a jumulce wajibi ne na imani.
Bautawa Allah ta hanyar yin sallah ,azumi,ambatonAllah da yin du'a'i da ibadodi hanyoyi ne na isar mutum zuwa ga kamala da gina kansa da tsarkake shi daga son zucci da girman kai kuma hakan ya taimaka masa don kan takobi domin yin jihadi don neman yardar Allah ba don son rai da amfanin kansa da kansa ba. Kawai abin day a sag a shi ne gyaran al'umma da kansa ta hanyar aikata aikin alheri suna daga cikin ayyukan da suka rataya a wuyan mumunai.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu na farko: tsarake kai da zucci shi ne babban jihadi day a fi jihadi makiya girma kuma jihadi da makiya an ba shi sunan karamin jihadi.
Na biyu: Munminai a kullum suna fada da gwagwarmaya da masu banna da kiyayya na cikin gida kamar yadda suke fada da fafatawa da makiya na waje domin tabbatar da dokokin Allah da kare lamarin Ubangiji madaukakin sarki.
Da fatar Allah ya ba mu karfi da ikon gyara kanmu da kanmu da amfanu da duk wani alheri da ke wannan duniya da kuma cimma moriyarsa a gobe kiyama amin da kuma wannan addu'a ce ni Tidjani malam Lawali damagaram da na shirya kuma na gabatar nake cewa wassalam alaikum warahmatunllahi wa barkatuhu.
Suratut Tauba, Aya Ta 113-119 (Kashi Na 314)
Jama'a masu saurarenmu barkarmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikin wannan shiri muke bayani bayan mun fara sauraren ayar kur'ani mai girma da kuma fassararta a cikin harshen Hausa kana daga bisani mu yi dubi a cikin irin nasihohi da galgadin da suka zo a cikin wannan aya ko ayoyi kuma babu wani abu madogari da yafi kur'ani da hadisan ma'asumai da ke zama abubuwa biyu da ba su rabuwa kuma duk wanda ya yi riko da igiyar Allah har abada ba zai tabe ba da yin da na sani a rayuwarsa duniya da lahira.
To madallah a yau za mu saurari aya ta 113 a cikin wannan sura ta tauba kamar haka:
مَا كَانَ لِلنَّبِيِّ وَالَّذِينَ آمَنُواْ أَن يَسْتَغْفِرُواْ لِلْمُشْرِكِينَ وَلَوْ كَانُواْ أُوْلِي قُرْبَى مِن بَعْدِ مَا تَبَيَّنَ لَهُمْ أَنَّهُمْ أَصْحَابُ الْجَحِيمِ{113}
Bai kamata ba ga Annabi shi da wadanda suka bada gaskiya da su nema wa mushirikai gafara,ko da kuwa sun kasance dangi ne,bayan kuwa sun riga sun gane cewa su yan wuta ne.
Neman gafarar Annabi Ibrahima kuwa ga abbansa ya faru ne kawai don alkawarin da ya yi masa.To lokacin da ya tabbatar da cewa shi makiyin Allah ne sai ya rabu da shi. Hakika Ibrahimu ya tabbata mai yawan bautar Allah ne ,mai yawan hakuri.
Daga lokacin da bawa ya nemu gafara da tuba alama ce ta bukatar zucciya da bayyana haka a baki.Wadannan ayoyi biyu tana magana ne ga mumunai da cewa da kar su newa mushirikai gafara ko da kuwa makusantansu ne dalili kuwa duk wanda ya mutu cikin kafirci da shirka babu wata makoma a gare shi da ta wuce shiga azaba da wuta mai radadi da zafin kuna da babu mai shigarta sai makiyin Allah da manzonsa da zuriyarsa tsarkaka. A cikin aya ta biyu tana magana ne kan alkawarin da Annabi Ibrahima ya yi wa abbansa wanda ya rike shi na nemar masa da gafara tun lokacin da bai fahimci cewa ba zai yi imani da barin shurka ba wato hasken tsira da shiriya ba zai riske shi har abada ga shi kuma ya yi masa alkawarin cewa idan ya bar shirka da kafirci zai nemar masa gafarar Allah madaukakin sarki ya yafe masa sauran zunubai da sabo da kafircin da ya aikata a baya.Amma da yake ya yi nisa a cikin shirka kuma duk kokarin da Annabi Ibrahima ya yi na ganin wannan abba nasa ya komo ga madaidaiciyar hanya ta gaskiya da shiriya ya ci tura, Annabi Ibrahima sai ya yi hakuri da jurewa lamarin.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu na farkonsa mu sani shirka babban leifi da sabo ne da ba a yafewa mai aikata shi ko da kuwa ma'aikin Allah ne zai nema wa zuriya ko wani daga cikinta mai aikata shirka. Ko da kuwa ya nemar masa da gafara ,neman gafararsa ba za ta yi tasiri ba da yi masa gafara ana bukatar shi da kansa ya tuba da yin nadama.
Na biyu : Mu sani cewa abubuwa na addini su ne masu kima da daraja ba abubuwa na son rai da zucci ba ko kusanci da yan uwantaka.
To yanzu kuma za mu saurari ayoyi na 115 da 116 a cikin wannan sura ta tauba:
وَمَا كَانَ اللّهُ لِيُضِلَّ قَوْماً بَعْدَ إِذْ هَدَاهُمْ حَتَّى يُبَيِّنَ لَهُم مَّا يَتَّقُونَ إِنَّ اللّهَ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمٌ{115} إِنَّ اللّهَ لَهُ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ يُحْيِـي وَيُمِيتُ وَمَا لَكُم مِّن دُونِ اللّهِ مِن وَلِيٍّ وَلاَ نَصِيرٍ{116}
- Allah kuwa ba zai taba batar da wasu mutane ba bayan Ya riga ya shirye su ,har sai Ya bayyana musu abin da za su kiyaye. Hakika Allah Masanin komai ne. -Hakika Allah Shi ne Mai mulkin sammai da kassai, Yana rayawa kuma Yana kashewa.Ba ku da wani majibincin lamarinku in ban da Allah,ba ku kuma da wani mataimaki.
Allah madaukakin sarki gwani mai hikima domin isa ga shirya da kamala ya samarwa da dan adam hanya mai inganci da sauri wato amfani da hankali da kuma wahayi .Kuma abubuwa biyu ne da har abada ba za su rabu ba ko kuma barin mai aiki da su kamar yadda ya kamata kaucewa hanya da shiriya.sai dai idan mutane sun fahimci da masaniya kan hukumcin Allah da takalifin da ya ratawa a kansu daga mahalicci amma su yi aiki da sabanin hukumcin Allah da hankalinsu.to dole su kaucewa aiikata irin wannan mummunan aiki.daya daga cikin babban hadarin da ke yi wa ma'abuta imani baraza shi ne su yi zato da ttabbacin cewa su ma'abuta shiga gidan aljanna ne da samun tsira duniya da lahira kuma su rika jiji da kai cewa babu wani abu da ke iya yi masu baraza alhali akullum barazana tana tare da su wato suna iya zama rasa addini ma'ana mumuni na iya zama kafiri kamar yadda kafiri na iya zama mumuni matukar suna raye a wannan duniya saboda haka ba abu ban e mai wuya kafiri ya zama mumuni ya samu tsira da shiriya.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda uku na farko bujirewa umarnin Allah da dangam na rusa duk wata shiriya da tsira gad an adam kuma wannan lamarai ne da ke yi wa duk wani mumuni barazana.
Na biyu: Kafircewa Allah ya na zowa ne bayyana an bayyanawa al'umma hukumce-hukumce da takalifinta da sauran hujjoji.
Na uku: mu sani cewa a maimakon kokarin kyautata dangantakarmu da makusantanmu mushirika mu yi kokari da tunanin inganta dangantakarmu da mahaliccci da rayuwarmu da mutuwarmu tana hannunsa.
Da fatar Allah ya bam u karfi da ikon fahimtar gaskiya da aiki da ita ya kuma kara mana karfin imani amin.
To madallah yanzu kuma za mu saurari aya ta 117 a cikin wannan sura ta tauba:
لَقَد تَّابَ الله عَلَى النَّبِيِّ وَالْمُهَاجِرِينَ وَالأَنصَارِ الَّذِينَ اتَّبَعُوهُ فِي سَاعَةِ الْعُسْرَةِ مِن بَعْدِ مَا كَادَ يَزِيغُ قُلُوبُ فَرِيقٍ مِّنْهُمْ ثُمَّ تَابَ عَلَيْهِمْ إِنَّهُ بِهِمْ رَؤُوفٌ رَّحِيمٌ{117}
Hakika Allah Ya yafe wa annabi da wadanda suka yi hijira da kuma mutan Madina wadanda suka bi shi a lokacin tsanani bayan har zukatan wasu kungiyoyi daga cikinsu sun kusan karkata,sannan Allah Ya karbi tubarsu. Hakika shi Mai tausayawa ne Mai jin kai a gare su.
Wannan aya tana nuni ne da yanayi na kumci da wahala da musulmi suka samu kansu a ciki a lokacin yakin tabuka saboda nisan hanya da yanayi na zafin rana da kuma zafin saharar saudiya a lokacin kuma a lokacin da zafi yafi tsanani a yankin kuma wasu daga cikin mumunai ba a shirye suke ba na zuwa filin daga da jihadi ta hanyar fakewa da dalilai iri-iri sun nemi zama a Madina da gidajensu don lura da gonakinsu.Amma lutifin Allah ga manzonsa ya hana su zama munafikai da kaicewa hanya ya umarce su da sun tafi filin daga da kasancewa tare da mumunai da kar su kuskura su yi riko da hanyar bata da tabewa ta hanyar kin yin umarni da umarni da hukumcin Allah.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa biyu na farko; alamar imani na hakika bin umarnin jagororin addini a cikin ko wane irin yanayi na dadi ko na wahala ba wai kawai a cikin yanayin da aka saba.
Na biyu: dukan dan adam hatta ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shiyana bukatar lutifin Allah da yi ma al'ummar gafara da hakan ke zama daya daga cikin lutifi da rahamar Allah.
To madallah yanzu kuma za mu saurari aya ta 118 da 119 a cikin wannan sura ta tauba;
وَعَلَى الثَّلاَثَةِ الَّذِينَ خُلِّفُواْ حَتَّى إِذَا ضَاقَتْ عَلَيْهِمُ الأَرْضُ بِمَا رَحُبَتْ وَضَاقَتْ عَلَيْهِمْ أَنفُسُهُمْ وَظَنُّواْ أَن لاَّ مَلْجَأَ مِنَ اللّهِ إِلاَّ إِلَيْهِ ثُمَّ تَابَ عَلَيْهِمْ لِيَتُوبُواْ إِنَّ اللّهَ هُوَ التَّوَّابُ الرَّحِيمُ{118} يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُواْ اتَّقُواْ اللّهَ وَكُونُواْ مَعَ الصَّادِقِينَ{119}
-Kuma Ya karbi tuba ga mutanen nan guda uku wadanda suka ki fita,har yayin da duniya ta yi musu kunci duk da yalwarta,kuma zukantansu suka kuntata,suka san cewa dai babu wata matsewa daga Allah sai dai zuwa gare Shi.Sannan sai Ya yi musu muwafakar tuba don su tuba. Hakika Allah Shi ne Mai yawan karbar tuba mai jin kai. -Ya ku wadanda suka yi imani Ku bi Allah da takawa , kuma ku kasance tare da masu gaskiya .
Karkashin ruwayoyi da tarihin Musulunci mutane uku neb a su halarci yakin Tabuka ba sai suka zo gurin ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da layan gidansa suna nadama amma ma'aikin Allah bai ce ko mai ba sai ya bada umarni da cewa: kar wanda ya yi magan ada su ko ya kusance su sai suka yi gudun hijira da barin birnin Madina suna masu nadama da neman gafarar Allah har zuwa lokacin da Allah ya karbi tubarsu kuma ma'aikin Allah mai rahama da daukaka tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidan ya bada labarin yi masu afuwa da karbar tubarsu.
A cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa guda biyu na farko: Daya daga cikin hanyoyin kalubalantar masu bijirewa umarni da hukumce hukumce na zamantakewa shi kaurace masu.
Na biyu:bayan jurewa da gwagwarmaya da abubuwa maras kyauta da takunkumi hanya za ta bude da zama alheri ga wadanda suka yi nadama. Da fatar Allah ya kiyashe mu da yin nadama duniya da lahira amin.
Kuma a nan ne nake dasa aya kafin wani shirin Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram na ke cewa wassalamu alaikum warahmatullahi wa barkatuhu.
Suratut Tauba, Aya Ta 120-122 (Kashi Na 315)
Jama'a masu saurarenmu barkarmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikin wannan shiri muke bayani bayan mun fara sauraren ayar kur'ani mai girma da kuma fassararta a cikin harshen Hausa kana daga bisani mu yi dubi a cikin irin nasihohi da galgadin da suka zo a cikin wannan aya ko ayoyi kuma babu wani abu madogari da yafi kur'ani da hadisan ma'asumai da ke zama abubuwa biyu da ba su rabuwa kuma duk wanda ya yi riko da igiyar Allah har abada ba zai tabe ba da yin da na sani a rayuwarsa duniya da lahira.
Yanzu kuma za mu farad a sauraren aya ta 120 a cikin suratul Tauba kamar haka:
مَا كَانَ لِأَهْلِ الْمَدِينَةِ وَمَنْ حَوْلَهُم مِّنَ الأَعْرَابِ أَن يَتَخَلَّفُواْ عَن رَّسُولِ اللّهِ وَلاَ يَرْغَبُواْ بِأَنفُسِهِمْ عَن نَّفْسِهِ ذَلِكَ بِأَنَّهُمْ لاَ يُصِيبُهُمْ ظَمَأٌ وَلاَ نَصَبٌ وَلاَ مَخْمَصَةٌ فِي سَبِيلِ اللّهِ وَلاَ يَطَؤُونَ مَوْطِئاً يَغِيظُ الْكُفَّارَ وَلاَ يَنَالُونَ مِنْ عَدُوٍّ نَّيْلاً إِلاَّ كُتِبَ لَهُم بِهِ عَمَلٌ صَالِحٌ إِنَّ اللّهَ لاَ يُضِيعُ أَجْرَ الْمُحْسِنِينَ{120}
120- Ba ya kasancewa ga mutanen Madina da wada yake a gefensu , daga kauyawa , su saba daga bin Manzon Allah, kuma kada su yi gudu da rayukansu daga ransa .Wancan , saboda kishirwa ba ta samun su , haka kuma wata wahala, haka kuma wata yunwa, a cikin hanyar Allah , kuma ba su takin wani mataki kuma ba su samun wani samu daga makiya face an rubuta musu da shi. Ladar aiki na kwarai .Lalle neAllah ba Ya tozarta ladar masu kyautatawa.
Bin umarnin ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa ya zama wajibi ga mutanan birnin Madina da kuma wadanda suke zaune a kewayen birnin,kuma kar su sabawa masa da jin tsoran rayukansu da dukiyoyinsu a lokacin da aka bukace su zuwa jihadi na kare addinin Musulunci da tabbatar da shi.tsoron kishirwa ko wahala haka kuma yunwa ba za ta same su ba kuma ko ba komi yunwa ko kishirwa kan hanyar Allah ai wani abu ne da ya kamata a runguma da maraba da shi domin samun tsira duniya da lahira.Idan kuma suka rungumi makiya to babu abin da za su samu face bakion ciki da huzuni amma lada da sakamako na karshe na Allah ne da ba ya tozarta ladan masu kyautatawa.
A cikin wannan aya za mu ila ilmantuwa da abubuwa guda biyu masu muhimmanci kamar haka:
Na farko:Yin jihadi ya wajaba kan kow musamman a lokacin ma'aiki kan mutane da suyke tare da shi da kewaye.
Na biyu:tsoro ba ya hana abkuwar lamarin da zai abku.
To madallah yanzu kuma za mu saurari ayoyi na 121 da 122 a cikin suratul ta Tauba:
وَلاَ يُنفِقُونَ نَفَقَةً صَغِيرَةً وَلاَ كَبِيرَةً وَلاَ يَقْطَعُونَ وَادِياً إِلاَّ كُتِبَ لَهُمْ لِيَجْزِيَهُمُ اللّهُ أَحْسَنَ مَا كَانُواْ يَعْمَلُونَ{121} وَمَا كَانَ الْمُؤْمِنُونَ لِيَنفِرُواْ كَآفَّةً فَلَوْلاَ نَفَرَ مِن كُلِّ فِرْقَةٍ مِّنْهُمْ طَآئِفَةٌ لِّيَتَفَقَّهُواْ فِي الدِّينِ وَلِيُنذِرُواْ قَوْمَهُمْ إِذَا رَجَعُواْ إِلَيْهِمْ لَعَلَّهُمْ يَحْذَرُونَ{122}
-Kuma ba su ciyar da wata ciyarwa , karama ko babba , kuma ba su keta wani rafi sai an rubuta musu , domin Allah Ya saka musu da mafi kyawon abin da suka kasance suna aikatawa . -Kuma ba ya kasancewa ga muminai su fita zuwa yaki gaba daya. Saboda haka , don me ne wata jama'a daga bangare daga gare su ba ta fita (zuwa neman ilimi ba) domin su nemi ilimi ga fahimtar addini kuma domin su yi gargadi ga mutanensu idan sun koma zuwa gare su, tsammaninsu, suna yin sauna?
Duk alheri da mutum ya aikata zai ga ladansa da sakamakonsa komin kankantarsa,idan kaciyar da wani bayan Allah ko da daidai da dan dabino guda ne to shakka babu za ka ga alherin wannan aiki naka idan kuma ka yi rowa to haka lamarin yake mutum zai ga sakamakon aikinsa mummuna. Kuma wannan albishir ne ga wadanda suka aikata aikin alheri daga Allah na sakawa wadanda suka yi aikin alheri da sakayya da tanadi mai kyau.A ci gaban ayar tana magana ne kan salon yaki da dubarun yaki da yadda ya kamata mumunai su rabu wasu su tafi wajen yaki wasu kuma su tsaya domin kare wadanda bas u da damar zuwa yaki kamar mata da kananan yara da neman ilimi domin neman ilimi da fahimtar addini da gargadi mutanansu idan sunkoma zuwa gare su .
A cikin wannan aya za mu ila ilmantuwa da abubuwa guda biyu masu muhimmanci kamar haka:
Na farko: shi dan adam a kullum yana fatar yin wani abu da zai ga sakamakonsa,don haka babu abin da yafi kyau kamar taimakawa addini ta hanyar Allah.
Na biyu: a kullum addinin Musulunci yana nuna mana tsari da hanyoyin da suka dace.
Da kuma wannan ne muka kawo karshen bayani a cikin wannan shiri na yau na hannunka mai sanda da ni Tidjani Malam Lawali Damagaram na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam alaikum warahmatullahi.
Suratut Tauba, Aya Ta 123-126 (Kashi Na 316)
Jama'a masu saurarenmu barkarmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikin wannan shiri muke bayani bayan mun fara sauraren ayar kur'ani mai girma da kuma fassararta a cikin harshen Hausa kana daga bisani mu yi dubi a cikin irin nasihohi da galgadin da suka zo a cikin wannan aya ko ayoyi kuma babu wani abu madogari da yafi kur'ani da hadisan ma'asumai da ke zama abubuwa biyu da ba su rabuwa kuma duk wanda ya yi riko da igiyar Allah har abada ba zai tabe ba da yin da na sani a rayuwarsa duniya da lahira.
Yanzu kuma za mu fara wannan shiri ne da sauraren aya ta 123 da 124 a cikin suratul ta tauba kamar:
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُواْ قَاتِلُواْ الَّذِينَ يَلُونَكُم مِّنَ الْكُفَّارِ وَلْيَجِدُواْ فِيكُمْ غِلْظَةً وَاعْلَمُواْ أَنَّ اللّهَ مَعَ الْمُتَّقِينَ{123} وَإِذَا مَا أُنزِلَتْ سُورَةٌ فَمِنْهُم مَّن يَقُولُ أَيُّكُمْ زَادَتْهُ هَـذِهِ إِيمَاناً فَأَمَّا الَّذِينَ آمَنُواْ فَزَادَتْهُمْ إِيمَاناً وَهُمْ يَسْتَبْشِرُونَ{124}
- Ya ku wadanda suka yi imani Ku yaki wadanda suke kusantar ku daga kafirai . Kuma su sami tsanani daga gare ku . Kuma ku sani cewa Allah Yana tare da masu takawa . - Kuma idan aka saukar da wata sura , to, daga gare su akwai wadanda suke cewa. " wane a cikin ku wannan sura ta kara masa imani ?" Yo amma wadanda suka yi imani , kuma su , suna yin bushara (da ita ).
A lokacin gazzawa tsakanin rundunoni biyu na mumunai da na kafirai an umarci rundunar mumunai da ta yaki rundunar kafirai da ke kusa da su da kuma kar su yi masu da sausauci wato su tsananta masu tare da fadakar da su cewa su sani a kullum Allah madaukakin sarki yana tare da masu takawa.Kuma idan aka saukar da wata sura sai wasu daga cikinsu su fara bayyana cewa; cikin izgili wane ne a cikinku wannan sura ta kara masa imani da takawa yayin da kafirai da munafikai suke irin wannan izgili da kaskantawa sai su kuma mumunai sai ga wannan sura tana yi masu bushara ne .
A cikin wannan aya za mu ila ilmantuwa da abubuwa guda biyu masu muhimmanci kamar haka:
Na farko: shi munafikai a tsakanin mumunai yana izgili ne da yin zagon kasa.
Na biyu: shi kuma mumuni a kullum imani da takawa ya ke kara samu.
To Madallah yanzu kuma lokaci ne da za mu saurari aya ta 125 da 126
وَأَمَّا الَّذِينَ فِي قُلُوبِهِم مَّرَضٌ فَزَادَتْهُمْ رِجْساً إِلَى رِجْسِهِمْ وَمَاتُواْ وَهُمْ كَافِرُونَ{125} أَوَلاَ يَرَوْنَ أَنَّهُمْ يُفْتَنُونَ فِي كُلِّ عَامٍ مَّرَّةً أَوْ مَرَّتَيْنِ ثُمَّ لاَ يَتُوبُونَ وَلاَ هُمْ يَذَّكَّرُونَ{126}
- Amma kuma wadanda suke a cikin zukatansu akwa cuta, to, ta kara musu kazanta zuwa ga kazantarsu, kuma su mutn alhalin kuwa suna kafirai. -Shin, ba su ganin cewa ana fitinar si a cikin kowace shekara: sau daya ko kuma sau biyu, sa'an nan kuma ba su tuba , kuma ba su zama suna tunani ba?
Su kuma kafirai da munafikai masu cuta a cikin zukatansu babu abin da suke kara samun face kazamta a kan kazamantarsu haka za su ci gaba da rayuwa har lokacin da mutu ta riske su suna cikin gafala, kuma basira da hankali ya gushe masu domin bas u la'akari da fahimtar ana fitinar da su a cikin kowace shekara sau daya ko kuma sau biyu,sa'an nan kuma bas u tuba daga ayyukan da suke aikatawa da zama suna tunani.
A cikin wannan aya za mu ila ilmantuwa da abubuwa guda biyu masu muhimmanci kamar haka:
Na farko:munafikai da kafirai kazammai ne da zucciyarsu cuta ta mamaye ta.
Na biyu: cutar da ba su warkewa daga ita sai ma ta kara mamaye zucciyarsu.
Da kuma wannan ne muka kawo karshen bayani a cikin wannan shiri na yau na hannunka mai sanda da ni Tidjani Malam Lawali Damagaram na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam alaikum warahmatullahi.
Suratut Tauba, Aya Ta 127-129 (Kashi Na 317)
Jama'a masu saurarenmu barkarmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikin wannan shiri muke bayani bayan mun fara sauraren ayar kur'ani mai girma da kuma fassararta a cikin harshen Hausa kana daga bisani mu yi dubi a cikin irin nasihohi da galgadin da suka zo a cikin wannan aya ko ayoyi kuma babu wani abu madogari da yafi kur'ani da hadisan ma'asumai da ke zama abubuwa biyu da ba su rabuwa kuma duk wanda ya yi riko da igiyar Allah har abada ba zai tabe ba da yin da na sani a rayuwarsa duniya da lahira.
Za mu fara shirin ne da sauraren aya ta 127 a cikin suratul Tauba kamar haka:
وَإِذَا مَا أُنزِلَتْ سُورَةٌ نَّظَرَ بَعْضُهُمْ إِلَى بَعْضٍ هَلْ يَرَاكُم مِّنْ أَحَدٍ ثُمَّ انصَرَفُواْ صَرَفَ اللّهُ قُلُوبَهُم بِأَنَّهُمْ قَوْمٌ لاَّ يَفْقَهُون{127}
- Kuma idan hakika aka saukar da wata sura , sai sashensu ya yi dubi zuwa ga wani sashe , ( su ce ) " Shin , wani mutum yana ganin ku?" . Sa'an nan kuma sai su juya . Allah Ya juyar da zukatansu , domin , hakika , su mutane ne, ba su fahimta .
A duk lokacin da wata aya ta sabka sai munafikai su n gudanar da taro da kollon junansu da yin maganganu kasa kasa cikinn tsoro irin na munafinci da yin dubi zuwa ga wani sashe da tambayar junansu shin babu wani da ke ganinsu sa an nan kuma sai su juya bayan,Allah kuma sai ya juyar da zukatansu da kasancewa mutane dab a su fahimta da sanin abubuwan azaba da aka yi masu tanadi da kuma ke jiransu.
A cikin wannan aya za mu ila ilmantuwa da abubuwa guda biyu masu muhimmanci kamar haka:
Na farko: maras gaskiya ko a ruwa yana jibi da zarguwa to haka halin munafiki yake.
Na biyu:shi munafiki yana kara rura wutar azabar da ke jiransa ne.
To Madallah yanzu kuma za mu saurari ayoyi na 128 da 129 a cikin suratul ta Tauba kamar haka:
لَقَدْ جَاءكُمْ رَسُولٌ مِّنْ أَنفُسِكُمْ عَزِيزٌ عَلَيْهِ مَا عَنِتُّمْ حَرِيصٌ عَلَيْكُم بِالْمُؤْمِنِينَ رَؤُوفٌ رَّحِيمٌ{128} فَإِن تَوَلَّوْاْ فَقُلْ حَسْبِيَ اللّهُ لا إِلَـهَ إِلاَّ هُوَ عَلَيْهِ تَوَكَّلْتُ وَهُوَ رَبُّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ{129}
- Lalle ne, hakika Manzon daga cikinsu ya je muku. Abin da kuka wahala da shi mai nauyi ne a kansa . Mai kwadayi ne saboda ku . Ga muminai Mai tausayi ne, Mai jin kai . - To , idan sun juya , sai ka ce " Ma'ishina Allah ne. Babu abin bautawa face Shi. A gare Shi nake dogara. Kuma Shi ne Ubangijin A'arshi mai girma.
Hakika Manzon daga cikinsu ya je muku,ma'ana Allah ba ya turo wani manzo da ma'aiki sai daga cikin mutanan da aka turowa wannan annabi. Kuma mai kwadayi ne saboda da shiryar da mutanen da suke tare da shi kuma ga muminai mai tausayi ne mai jin kai. To idan sun juya, sai ka ce ma'ishina Allah ne, kuma hakika babu abin bautawa face sai Allah madaukakin sarki.
A cikin wannan aya za mu ila ilmantuwa da abubuwa guda biyu masu muhimmanci kamar haka:
Na farko: ana ruro Annabi ne daga cikin mutanansa.
Na biyu: duk dan adan yana son shiriya sai dai wanda ya kafirce da shi ma idan ya ga bala'i yana saduda.