Toggle menu
24K
663
183
158.1K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Talk:adalci

Discussion page of adalci

Glosbe's example sentences of adalci [1]

  1. Misalin kalmar da jimlolin turanci da Hausa na kalmar adalci:
    1. (1 Timothawus 2:9; LMT) Ba abin mamaki ba ne, a littafi Ru’ya ta Yohanna, “linen mai-labshi, mai-walƙiya, mai-tsabta” yana wakiltan ayyuka masu adalci da Allah ya ɗauke su masu tsarki.
      (1 Timothy 2:9, The New English Bible) Not surprisingly, in the book of Revelation, “bright, clean, fine linen” is said to represent the righteous acts of ones whom God considers holy. [2]

    2. Tattaunawa Tsakanin Wani Mutum da Mashaidin Jehobah —Shin Dukan Masu Adalci Za Su Je Sama Ne?
      A Conversation With a Neighbor —Do All Good People Go to Heaven? [3]

    3. (Zabura 78:41) Ba ma so mu yi abin da zai sa a zagi hanyar bauta masa mai tsarki kuma mai adalci.
      (Psalm 78:41) We do not desire to act in a manner that will cause his holy and righteous way of worship to be spoken of abusively. [4]

    4. A dukan duniya, mutane sun iske cewa Littafi Mai Tsarki yana ba da wannan taimako mai girma a cikin iyalai, yana ba da tabbacin cewa da gaske Littafi Mai Tsarki “hurare daga wurin Allah ne mai-amfani ga koyarwa, ga tsautawa, ga kwaɓewa, ga horo kuma da ke cikin adalci.”
      Worldwide, people have found the Bible to be a great help in setting such family standards, providing living evidence that the Bible truly “is inspired of God and beneficial for teaching, for reproving, for setting things straight, for disciplining in righteousness.” [5]

    5. (2 Bitrus 3:10-13; Ayyukan Manzanni 5:41) Kamar Kiristoci na fari, mu ci gaba da ‘koyarwa da yin bishara cewa Yesu shi ne Almasihu’ da kuma Mulkinsa sa’ad da muke jiran sakamako a sabuwar duniya ta adalci ta Jehovah.—Ayyukan Manzanni 5:42; Yakubu 5:11.
      (2 Peter 3:10-13; Acts 5:41) Like the early Christians, may we continue “without letup teaching and declaring the good news about the Christ” and his Kingdom government while awaiting our reward in Jehovah’s righteous new world. —Acts 5:42; James 5:11. [6]

    6. 4 Don ya samu ceto, sai mutum ya (1) nemi Jehovah, (2) nemi adalci, na (3) ya nemi tawali’u.
      4 For preservation, then, a person had to (1) seek Jehovah, (2) seek righteousness, and (3) seek meekness. [7]

    7. Hakika, mala’iku masu adalci “ruhohi masu-hidima ne aikakku domin su yi hidima sabili da waɗanda za su gaji ceto.”
      The righteous angels are indeed “spirits for public service, sent forth to minister for those who are going to inherit salvation.” [8]

    8. Idan ba a bi da su da kyau ba ba zai yi daidai da nufin Allah ba, domin Kalmarsa ta ce: “Mai-adalci yana kula da ran dabbansa.”
      Cruel treatment of them is certainly against the will of God, for his Word states: “The righteous one is caring for the soul of his domestic animal.” [9]

    9. (1 Tasalonikawa 4:16; 1 Bitrus 3:22; Wahayin Yahaya 19:14–16) Ubansa ne ya ba shi iko ya halaka “dukkan sarauta da mulki da iko” da suke hamayya da ƙa’idodin adalci.
      (1 Thessalonians 4:16; 1 Peter 3:22; Revelation 19:14-16) He has been empowered by his Father to bring to nothing “all government and all authority and power” that oppose righteous principles. [10]

    10. 6 Ga dalili na uku da ya sa za mu yarda da hukuncin Jehobah: Yana bin mizanai na adalci ko zai yi hasara.
      6 Note a third reason to accept Jehovah’s judgments: He holds to his righteous standards even at great personal cost. [11]

    11. (Farawa 7:1; 15:6; Ayuba 1:1; Ezekiel 14:14; Yaƙub 2:25) To, tambayar ita ce: Bisa menene Allah ya lissafa waɗannan mutane masu adalci?
      (Genesis 7:1; 15:6; Job 1:1; Ezekiel 14:14; James 2:25) The question, then, is: On what basis were these individuals counted righteous by God? [12]

    12. A kasashe da yawa, tsarin kafa doka da yin hukunci sun kasance da wuya, kuma sun cika da rashin adalci, son zuciya, da kuma rashin jituwa, saboda haka kyamar dokar ta yi yawa.
      In many lands, legal and judicial systems are so complex, so rife with injustice, prejudice, and inconsistencies, that contempt for law has become widespread. [13]

    13. (Ayuba 34:10) Jehobah yana shari’a da adalci kamar yadda wani marubucin zabura ya ce: ‘Yana yi wa kabilu shari’ar gaskiya.’
      (Job 34:10) His judgments are upright, as the psalmist said when addressing Jehovah: “You will judge the peoples fairly.” [14]

    14. Maimako, Ayukan Manzanni 10:34, 35 ta ce: “Allah ba mai-tara ba ne: amma a cikin kowacce al’umma, wanda ya ke tsoronsa, yana aika adalci kuma, abin karɓa ne gareshi.”
      Rather, Acts 10:34, 35 states: “God is not partial, but in every nation the man that fears him and works righteousness is acceptable to him.” [15]

    15. “Alheri zai kai ga adalci zuwa rai na har abada.”—ROM.
      “Undeserved kindness [will] rule as king through righteousness with everlasting life in view.” —ROM. [16]

    16. (Ishaya 31:4) An kuma yi alkawari: “DUBA, wata rana wani sarki za ya yi mulki cikin adalci.”
      (Isaiah 31:4) There is also a promise: “Look! A king will reign for righteousness itself.” [17]

    17. Yesu ya ce wa mabiyansa su yi addu’a Mulkin ya zo domin Mulkin zai sa a sake samun zaman lafiya da kuma adalci a duniya.
      Jesus told his followers to pray for it to come because it will restore righteousness and peace to the earth. [18]

    18. “Gama, ga shi, sababbin sammai [sabuwar gwamnati na samaniya] da sabuwar duniya [da jami’iyyar ’yan adam masu adalci]; ni ke halitta: ba za a tuna da al’amura na dā ba, ba kuwa za su shiga zuciya ba.
      “I am creating new heavens [a new heavenly government] and a new earth [a righteous new human society]; and the former things will not be called to mind, neither will they come up into the heart. [19]

    19. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Inda ’ya’yan Allah sun bayyanu ke nan, da ’ya’yan Shaiɗan: dukan wanda ba shi aika adalci ba, ba na Allah ba ne, da wannan kuma wanda ba ya yi ƙaunar ɗan’uwansa ba.”
      The Bible says: “The children of God and the children of the Devil are evident by this fact: Whoever does not practice righteousness does not originate with God, nor does the one who does not love his brother.” [20]

    20. (Wahayin Yahaya 12:9) In ba an kawar da muguwar rinjayarsa ba, za a ci gaba da samun mutane da suka fuskanci bala’i da rashin adalci.
      (Revelation 12:9) Until his malign influence is removed, there will be victims of evil and injustice. [21]

    21. Da haka, 2 Bitrus 3:13 ya annabta: “Amma bisa ga alkawarinsa muna jiran sababbin sammai [Mulkin Allah na samaniya] da sabuwar ƙasa [sabuwar jam’iyyar duniya], inda adalci zai yi zamansa.”
      Thus, 2 Peter 3:13 foretells: “There are new heavens [God’s heavenly Kingdom] and a new earth [a new earthly society] that we are awaiting according to his promise, and in these righteousness is to dwell.” [22]

    22. 20:28) Wannan ya ba ’yan Adam ajizai damar yin rayuwa har abada kuma ya sa su zama masu adalci.
      20:28) This provided an opportunity for sinful humans to live forever, and it satisfied the demands of righteousness. [23]

    23. (Ibraniyawa 11:7; Farawa 6:13-22) Nuhu kuma ya kasance “mai-shelan adalci,” wanda ya yi shelar kashedi na Allah ga mutanensa.
      (Hebrews 11:7; Genesis 6:13-22) Noah was also “a preacher of righteousness” who courageously declared God’s warning to his contemporaries. [24]

    24. An ce game da Yesu: “Ka yi ƙaunar adalci, ka ƙi mugunta.”
      It was said with reference to Jesus: “You loved righteousness, and you hated lawlessness [wickedness].” [25]

    25. Shi ya sa suke zaune cikin salama kuma suke biɗan adalci.— Ishaya 60:17.
      That is why they are blessed with peace and why they pursue a righteous course. —Isaiah 60:17. [26]


Retrieved June 23, 2019, 6:10 pm via glosbe (pid: 19786)